Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ashraf tace "Ya Ashraf yanzu me wannan zata maka? "

Cikin rashin damuwa yace "to ko zakiyi? "

Da sauri tai shiru dan ba abinda ta tsana irin aiki, Ashraf ya kallesu yace "Little kuje."

Little wacce dariya ta kusa kamata da yaba Aneesa amsa ta mike itama Nafi ta mike, har sun fara tafiya Nafi ta juyo tanasan tambayarsa.

Kallanta yai yace "d'azu yaushe kika tafi? "

Aneesa ta kalla cikin tsoro tace " ban dade ba ai. "

Kai ya d'aga kawai, ta daure tace "Goben karfe nawa zanzo? "

"Sanda kika gama abinda kike.
"

Juyawa tai bayan ta amsa da to.

Aneesa ta rakata da hararar tsana....

Suna fita ta shagwab'e ma Ashraf wai ya dizgata a gaban nafi.

Murmushi yai yace "kinsan banasan irin tambayoyin nan ai amma naga in bakimin ba bakyajin dad'i.

*THE INNOCENT TEAM*

*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com

1⃣5⃣

Gun Mumy suka je suka gaida ita suna fitowa Nafi ta kalli Little tace "nikam Maryam haka Ya Ashraf yakema yayarki? Kuma naga alama kamar batajin haushi. "

Little tai dariya tace "yayata ko? Lalai Nafi bama kara? "

Da sauri Nafi ta tsuke bakinta dan ita kanta batasan ya akai tace hakan ba, murmushi little tai tace "haka suke, ni ai ina ganin kokarinta, Nafi kinga Ya Ashraf yayanane ko? Kuma ina bala'in sanshi sai dai ko a mafarki ban tab'a addu'a Allah yaban miji shigenshi ma bare irinshi ba. "

Nafi tad'an yi turus sannan tace "amma randa mukazo tabbas naji ba da irin wannan lafazin ya mata magana ba. "

Little tace "ba kuka tai ba? "

Nafi ta d'aga kai alamar eh.
Little tacigaba "duk duniya abu d'aya ne ke karya zuciyar Yaya yaga mace tana kuka to fa inyanada hali komeye zai iya yi."


Nafi tai shiru sai dai ta tafi tunani akan itama kukan datai agabansa ne hala yasashi taimaka mata, jitai Little tace "shiyasa Ya Neesa takemai saurin kuka intai haka kwantar dakai yake sosai. "

Baki kawai Nafi ta motsa batace komai ba, tunani takeyi kenan da safe duk yaji abinda ya faru? To meyasa bai nuna mata ba? Yai kamar bai farfad'o ba?


Har suka isa ciki kawai dai tafiya take amma zuciyarta na wani gun.




_Wahegari_

Da safe yau little ta fita sai dai harta tafi bataga Nafi ba, bata kawo kumai a ranta ba ganin dama ba baccin safe take ba.

Itakam Nafi ta zake sai taimaka musu takeyi yau kam har su b'are maggi ace ta zuba tayi, tana yi fuskarta a sake kamar mai farin ciki da aikin, Goggo ce ta kalleta tace "Nafi kamar bakya gajiya da aiki? "

Dariya tao tace "Goggo nikam ai na godema Umma data sa ni a nan nake aiki, inasan in iya abinci wlh ga abincinku nanan kanshi ma kad'ai ya isa mutum."

Goggo tai murmushin farinciki tace "insha Allahu kuwa Nafi ni zan koya miki girki kala kala wanda duk ya kuskura yaci abincinki to lalai kashinshi ya bushe. "

Da mamaki Nafi tace "kashe kuma bushashe? "

Dariya suka mata Goggo tace "dolene inyaci abincinki sai ya kara. "

Cikin tsananin farin ciki Nafi tace "ai kuwa Goggo danaji dad'i sosai. "

Bayan sun gama ta karasa gurin wata a gun masu wanke wanke tad'an fita sai dai ba sosai ba, nan ta shiga tambayarta yanda ake gyaran d'aki, zama tai tamata bayanni sosai da yanda zatai mopping da goge_goge da wanke band'aki.

Nafi tai godiya ta mike sunata tsokanar ta wai yanda take hausa kanaji kasan na bafullatana ce.
Dariya kawai tai ta fito.

D'aki ta shiga ganin Little ta fita yasa ta leka toilet tai sa'a ta tara mata ruwa, kulle kofar d'akin tai sannan ta shiga wanka, kaya tasa sannan ta shafa mai kamar yanda ta saba, har ta mike sai kuma ta koma tad'au tirare ta kalli kanta a madubi tace "in fesa? "

Fesawa tai jin wani kanshin dadi, ido ta rufe sai kuma ta bud'e da sauri tace "Nafi me kikeyi hakan? "

Mikewa tai tsaye da sauri ta hard'e hannayenta tai waje.




√√√√√√

A d'aki Kuwa Umma ce zaune kusa da Aneesa ta kalleta cikin takaici tace "Me kike nufi? Kinfi san Ashraf akan yayanki Asim? "

Aneesa tad'an turo baki tace "Umma ni da kaina zansa Ashraf ya fara aikinsa, ai company d'insa ne bana Ya Asim ba. "

Cikin takaici Umma tace "wato ke miji dadi ko? Lalai Aneesa bakida hankali."

Kai Aneesa ta juya cikin rashin damuwa, ta kula Umma farin cikinta bai wuce ace Ashraf ya hakura da aikinsa ba. "

Umma ta mike sannan ta nunata da 'yatsa tace " wallahi ki shiha hankalinki Namiji ba d'an goyo bane balle a mazan ma irin Ashraf wanda baisan darajar d'an adam ba banda kansa wannan wa ya sani? "

Aneesa ta juya kai tace " Umma Kema kinsani tunda na taso nake san Ashraf shima kuma haka, babu abinda zai rabani dashi, ni zan goya kayana. "

Tana fad'a ta mike, Umma ta kalleta tare da rike hab'a cikin mamaki tace "lalai Aneesa kin girma, to wlh ki shiha hankalinki da wannan banzan san."

Fita Aneesa tai batace komai ba, Umma ta bita da tsaki tace "Wai ni Aneesa ke cema zata goya Ashraf?" tai wata dariyar bakin ciki tace "Lalai Aneesa dadai ban sanki bane, ina nan a zaune Soyayya zata dawo dake hanyar danake so. "




¤¤¤¤¤¤¤


Nafi ta karasa b'angaren Ashraf da tsintsiya,a bin kwashe shara, mopper ne da sauransu ajiyewa tai sannan ta kwankwasa kofar, ta dade a tsaye kafin Ashraf ya bud'e mata, yana bud'ewa ko kallanta baiyi ba ya koma ciki, Nafi ta kinkimi shirginta tai ciki, ajiyewa tai sannan ta dukursa ta gaidashi.

Lafiya kawai yace sannan ya karasa kan kujera, matsawa tai sannan tace "Yaya a fara da d'aki? "

Eh Nafisa, kawai yace.
Tai murmushi sannan ta d'au tsintsiyar laushi data kwakwa, harta je kusa da d'akin taji yace " Nafisa kar ki tab'amin kaya ki barsu a inda suke. "

Kallansa tai cikin mamaki saidai bata iya cewa komai ba banda to, nan ta shiga da ban d'aki ta fara sai data wanke shi fes iya karfinta take sakewa saboda san ta burge Ashraf, nan ta dawo d'akin, aiki take iya karfinta tana gamawa da d'aki ta fito falo me zata gani?


Ashraf ta gani a zaune a kasa jikinsa Dana Aneesa har suna tab'a juya, da alama kuka take yana bata hakuri, jin sheshekar kuka.

Jitai wata irin zufa na zubo mata, ga wani abu ya tokare mata a makogaro idanunta kawai take kiftawa da sauri da sauri, sai bakinta da take ta motsawa.

Jitai Ashraf yace "Aneesa meye abin kuka to? "

Cikin kuka tace "taya zamuyi aure amma haryanzu baka fara aiki ba kullum kana zaune a gida yaya kasan me nakeji a raina kuwa? "

Yace "ba dai aikin anayinsa bane saboda kudi ba? Ke kinsan inada kudi to meye abin tashin hankali. "

Hannunsa ta rike cikin kuka tace "baka tsoron a kwace company d'in da mahaifinka ya gina da guminsa? "

Ashraf ya mata murmushi yace "ya isa haka daina kuka kinji? "

Ta kara narkewa tare da kankameshi.

Da sauri Nafi ta juya ta koma cikin d'aki ta tsaya jitake kamar zuciyarta zata fashe ga wani abu ya tsaya mata a makogaro, ganin robar ruwa a gefen gadonsa kawai ta d'auka batare da tunanin komai ba kawai ta kafa kai ta kama sha, sai datasha sosai sannan ta ajiye, ji tai idanunta nata lumshewa batasan sanda ta zube a kasa ba tahau bacci sadidan.


Shikam Ashraf dakyar ya lallab'a Aneesa ta hakura sannan ya sallamata waje, da sauri ya shigo d'akin yana fatan Allah yasa bata gansu ba.

Ganinta a kwance a kasa yasa ya karasa gun da sauri ya d'agota ya fara jijigawa sai dai inaaa bacci take sosai kamar mataciya da sauri ya kalli robar ruwan maganin baccinsa wanda idan ciwonsa ya tashi yake sha dan samun bacci.

Kai ya dafe sannan ya kalli Nafi tare da girgiza kai.

D'agata yai cak ya d'aurata akan gadonsa sannan yaja mata kofa ya rufe.




Can da Yamma Ashraf yana kwance a falo shima bacci ne ya zare shi, sama sama yaji murya kamar ta Habib a kusa dashi, idanunsa ya bud'e a hankali ganin Habib yasa ya bud'e idan gaba d'aya.

Murmushi ya sakar mai sannan ya kanne mai ido d'aya yace "Hi Buddy! "

Ashraf ya rufe idansa yace "a naci ka iso? "

"to ya zanyi? Na kula in ma dade ban ganka ba zazzabine ke neman shigata. "

Ashraf ya d'anyi wani murmushi yace "Shugaban yaudara kenan, to ban shiga ba. "

Hanin ya zauna a kusa da Ashraf tare da sakin ajiyar zuciya yace "Kai mutumin wlh da akacemin wai an rasaka jinai kamar zam mutu. "

Kai Ashraf ya girgiza, Habib Yace "yanzu Mumy zata iso da abincinmu tace d'azu ta aiko anata knocking baka bud'eba. "

Baya Ashraf ya juya yace "ai tunda kazo shikenan rayuwata ta gama canzawa. "



Dariya sukai a tare, jin an kwankwasa Habib ya mik'e ya bud'e Mumy tana shigowa cikin falon, Nafi wacce ta farka sai dai baccin bai gama sakinta ba ga kanta ba d'ankwali ta fito daga d'akin Ashraf tana tafe tana murza ido irin alamar baccin bai gama sakinta ba.


Tiren juice d'in dake hannun Mumy ne ya fad'i wanda hakan ne ya kai hankalin Habib gun, hakan ne kuma yasa Ashraf dake kwance ya mike dan ganin meye, sam ya manta da Nafi na d'aki, idanu ya runtse cikin tsananin takaicin abinda zai biyo baya.

Nafi wacce hankalinta ya fara dawowa ta kurama Mumy ido sannan sai a lokacin tasan a inda ma take.........

*THE INNOCENT TEAM*

*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HERE IS UR PAGE DEAR RAFEE'AT SAKONKI YA ISO GARENI NA GODE SOSAI DA KAUNA DA KUMA KULAWA.....* *ILYSM😍*
1⃣6



Habib shima mamakin ganin Yarinya ta fito daga d'akin Ashraf yake, itakam Nafi duk ta rikice duk da bata kawo komai a ranta ba amma ganin ga mumy da su Ashraf yasa jikinta ya shiga tsuma.

Mumy a zuciye tace"Ashraf wani salon iskanci ne kuma hakan? Kanada hankali kuwa? "

Ashraf ya mike tsaye sannan yai wani murmushi ya kalli Mumy sannan ya kalli Nafi yace "Me kike nufi da kalamanki Mumy? "

Cikin takaici da fada tace "au tambaya ma kake? Yarinyar da ka kawo inganta ta fito daga d'akinka kace wai me nake nufi? "

A zuciye ta karaso kusa da Nafi wace ta rakub'e da jikin bango jikinta banda tsuma ba abinda yake, hannu ta d'aga a zuciye zata kai mata mari, Ashraf da sauri ya rike hannunta sannan ya kalli Nafi wacce kana gani kasan a gigice take ya maida dubansa gun Mumy yace "in kuma kika daketa ba da hakkinta ba fa? "

Mumy ta kalleshi cikin takaici tace "hakkinta?"

Ashraf cikin takaici yace "kina tunani ni Ashraf zanyi tarayya da wacce ba matata ba? Bare wannan? Me take dashi? Me kuma nagani? Dan kawai yarinya ta fito daga d'akina bazakiyi tunanin komai ba sai zargi??"

Mumy ta kuramai ido sai dai da alama bata gamsu ba.

Ashraf ya runtse ido zuciyarshi ba dadi, Habib ya kalla ya mai alama daya fita da Nafi, nan Habib ya matso yace mata muje.

Nafi duk ta gama rud'ewa tama manta mai ma ya kawota Ashraf kawai take kallo idanunta a hankali suka fara zubarda ruwa.

Suna fita Ashraf ya kalli Mumy idanunsa shima sun kada sosai ya shafi kansa sannan ya matsa kad'an daga inda take, yace " Ko a mafarki ban tab'a tunanin haka kika d'aukeni ba. "

Yana kainan yai waje a zuciye, jikin Mumy ne yai sanyi sai dana sani ya shigar mata, sai a lokacin ta kula da tsintsiya da abin mopping, kai ta dafe tace "dama yana nisanta kansa dani yanzu kuma na kara jan wani layin. "


Nafi kam suna fita kanta kp d'ankwalli babu tafiya kawai take, Habib ya kalleta yace " Karki damu ba abinda zai faru. "

Juyowa tai ta kalli Habib sannan ta tsaya tace "Ba abinda Mumy zata mai ko? "

Hawaye suka biyo bayan kalamanta, dariya Habib yai yace "wa? Ashraf? Ke kiji da kanki bawai ki tsaya tunanin wanda kila yanzu yama manta abinda akai ba. "

Juyawa tai kawai ta cigaba da tafiya, Habib ya matso yace "ban sanki ba amma. "

Nafi tace "tare muka dawo da yaya taimakona yai. "

Dariya sosai Habib yasa anda sai da Nafi ta tsaya tana mai kallan mamaki tace "menene? "

Sai daya tsagaita yace "taimako? Wa? Ashraf? Don't make me laugh. "

Nafi ta juya batace komai ba dan bata fahimceshi ba.

Habib yace daga wani gari kike?
Rigar Datti.

Maimaitawa yai cikin mamaki yace " ina kenan? "

Ita kanta batasan ina zata ce ba dan bata sani ba, ganin sun iso ta kalleshi tace "Nagode."

Murmushi ya sakar mata sannan yace "in Little ta dawo kice mata Habib yazo sai dai yanzu zan koma zan dawo nextwk. "

Kallansa tai a ranta tace "shine Habib d'in kenan? "

Ido d'aya ya kashe mata yace "what? Badai har kinji labari na ba? " ya d'aga mata gira yace "ahh kinsan nid'in akwai farin jini ga masoya. "

Batasan sanda ta murmusa ba, Habib ya nuna ta da hannu yace" kinyi dariya ko? "

Juyawa tai da sauri tai ciki wani sansanyan murmushi ya saki yace " she is soo beautiful and funny. " gashin kanta ya tuno wanda aka mai kitso manya sak dai ya kwanta har bayanta, yai murmushi sannan ya juya a ransa yace "inta girma za'ai mace anan. "


Nafi kam tana shiga ta zauna a kasa, kalaman Ashraf ne kawai ke dawo mata, Me take dashi? Me na gani? Me yake nufi da kalamansa?

Shiru tai kawai, Jitai ana kwankwasa kofar cikin zafi, ta mike da sauri ta bud'e, batai auni ba bakuma ta kula da waye ba taji mari gauu a fuskarta, da sauri ta rike gun wanda marin taji kwarai kuma har idanta na hago, dage idan tai cikin tsoro ta d'ago, jitai ance "Dan kut........ Ke har kin isa in saki aiki yau ki k'i zuwa? "

Nafi ta kalli Umma sai dai ta kasa cewa komai sai kai kawai datake jijigawa, Umma ta sa kafa ta turata ciki, tace"wlh kinji ma fada miki ko da wasa akace kinyi fashin zuwa gun aiki sai na sa an kwantar dake a asibiti saboda duka. "

Tana kainan ta juya, Nafi ta zube a gun sai kuka, sosai take kuka tana kuma tuno mahaifinta da mahaifiyarta, sai dataci kuka ta koshi sannan ta mike tai kitchen dan basu hakuri.

Sai dai me? Idanta kankace me ya kumbura saboda marin datasha a gun.





A b'angaren Ashraf kuwa yana fita ya fizgi mota da gudu kawai yana tafiya meyasa Mumy zata mai haka? Ita fa Mahaifiyarsa ce inda wani ne da sauki amma mahaifyarsa? Meta d'aukeshi? Ko zinar zaiyi mai zaiyi da wannan kwailar? Yar kauye? Wacce kila bama tasan me tarayya yake nufi ba.

A zuciye yai wani Rv ya kwantar da kansa a kan sitiyari wanda yaji yana saramai sosai.




Nafi kam bayan taje kitchen Goggo ta taso da sauri ta karaso gunta tace "Nafi me ya sami idanki? "

Nafi tai murmushi tace "bigewa nai. "

Shiru Goggo tai sannan tace "d'azu Hajiya tazo nemanki, amma da alama wani munafikin ne a nan ya fada mata bakizo ba. "

Nafi tai murmushi tace " Laifinane ai Goggo daban zo ba "

Cikin tausayi Goggo tace "Nafi idan nan naki fa ya kamata ko kankara asa a tsumma ki dan gasa ko kuma kisa lemon tsami kiyi ta mulmulawa. "

Nafi tai kasa da kai tace "Kiyi hakuri Goggo. "

Hannunta ta kama tace "kamar 'yata haka nakejinki karki damu da komai kinji? Ki kula da kanki. "

Nafi ta d'aga kai sai ha hawaye sun silalo mata, nan Goggo ta shiga bata hakuri, ta dad'e kafin ta amso abincinsu itada little ta fito.

Tazo wucewa ta ga motar Ashraf ya gangara yai parking tsayawa tai tare da yin kasa dakai dan karyagaidanta, sai dai ga mamakinta gani tai ya d'auke kai yayi gaba, Nafi ta kakaro murmushi kawai tayi tabi bayansa da kallo, ta sani laifinta ne mai ya kaita yin bacci? Ita kanta batasan ya akai ba.

Tana shiga d'aki Little tace "Nafi tun d'azu nake jiranki. "

Nafi ta ajiye abinci, zata zauna Little ta taso da sauri ta riketa tace "Nafi meye hakan? Meya sameki? "
Nafi tace "bigewa nai. "

Little zatai magana taji karar wayarta ta d'aga ganin Yaya, bayan sun gaisa yace "Little in anyi magrib ki d'au Nafi kuje asibiti sannan kice ta bar aikin sai ta warke. " abinda ya fada kenan ya kashe wayar.

Nan Little ta fada mata gani tai Nafi ta shiga yin murmushi tana kasa da kai, zuciyarta taji tayi wasai kenan ba haushinta yaji ba? Kenan zata cigaba da mai aiki? "

Little ta saki baki tana kallanta, me kenan? "

*THE INNOCENT TEAM*

*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com

*Sry jiya nayi mistake zansa 16 nakara sa 15.*
*Nagode kwarai da tunatar dani.... LYSM*


1⃣7⃣



Kwanaki sun d'an tafi yau kwanar Nafi 10 sai dai abubuwa dayawa sun canza, sam yanzu Ashraf yadaina mata magana tundaga wannan ranar ko gaisheshi tai kai kawai yake d'agawa, tana zuwa gyaramai d'aki duk bayan kwana biyu sai dai daga ta shiga yake fitowa, wannan abu na damun Nafi iya tsanani, gida ya mata zafi ga Little yanzu suna jarabawa ba zaman gida take ba, sannan cikin gida kowa zancen biki ne a gabansa, shiyasa yanzu zamanta yafi yawa a kitchen, sosai ta fara iya abinci dan yanzu tana nata iya kokarin.


Kamar yanda ta saba yau ma a ka'ida zataje ta gyara b'angaren Ashraf suna gama aiki a kitchen tai wanka ta d'au abincinsa tai gaba, ya bata makuli saboda wani sa'in in bayannan hakan yasa data kwankwasa taji shiru kawai tasa makuli ta bud'e, karfe goma ne shiyasa kanta tsaye tai d'aki ta d'auka ya fita, me zata gani?

Ashraf ta gani kwance ya dukunkune jikinsa da bargo, lekawa tai cikin tsoro idanunsa a rufe suke hakan yasa ta karasa kusa dashi, numfarfashi yake fitarwa sama sama, Nafi ta tsuguna saitin fuskarsa, hucin da yake fitowa daga bakinsa yasa tasan yanajin jiki, kuramai ido tai kawai hawaye ne suke zubo mata wanda ita kanta batasan tanayi ba, a hankali yad'an bud'e ido ganin Nafi yasa ya ciro hannunsa da niyyar yi mata bayani, itakam ganin yana miko hannu tai saurin rike hannun, ya kara daurewa ya bud'e ido, yayi mamakin ganin yanda take zubar da hawaye sai dai abinda yakeji yasa ya d'aure yace " rub zaki mikon."

Mikewa tai da sauri ta shiga dube dube, hannunsa ya sa ya nuna mata inda yake, da sauri ta d'auko ta mikamai, nuna mata kafad'ar hagunsa yai ya d'aure da kyar yace shafamin anan. "

Kallan mamaki tamai sai dai gani tai idanunsa a rufe suke, mikewa tai a hankali ta rasa ta ina zata fara, ganin yanda yake hucci yasa ta d'aure a hankali ta d'an yaye bargon daga b'angaren sa na haggu.


Vest ne a jikinshi shiyasa tana iya ganin gun, mamaki ne ya kamata ganin gun ya kumbura, da alama bigewa yai ko kuma wani abun lalai wannan ciwon ne ya sa mai zazzab'i, kallansa tai cikin tsananin tausayi wanda bata tab'a ji ba, yau ce rana ta farko da takeji inama ciwon ya dawo jikinta, a hankali ta d'ebi rub d'in ta fara kokarin shafawa, sai dai daga takai hannunta kan jikinsa sai tai sauri ta d'auke, tasan magani ne da alama kuma yanda takeji maganin zafi zai mai.

Cikin wani yanayi wanda Ita kanta bata sani ba tace " Yaya baka ganin zaiyi xafi? "

A hankali yace " Nafeesa samin ba zaiyi ba. "

Idanu ta rufe kamkam kamar ita za'a sawa a haka ta samai, sam batasan hawayenta na d'iga akan gun ba, Ashraf kam ido ya rufe dan akwai zafi sai dai jin hawayen nafi agun ciwon yasa jikinsa yai sanyi, meyasa? Menene dalilinta? Wata zuciyar tace kasan Nafi da tausayi.



Tana gamamai ta maida bargon ta rufe shi sannan ta share hawayenta wanda ita kanta tana mamakin yanda suke zuba haka, cikin sanyin murya tace " Yaya ka tashi ko wani abin kaci. "

Kai ya girgiza mata alamar a'a, idanunta suka kara cicikowa tace "Yaya dan Allah, in kumaa da wani abu da kakeso sai in maka yanzu. "

Idanu ya bud'e a hankali ya kakaro murmushi sannan yace " me kika iya?"

Da sauri tace "duk abinda kakeso na iya kaji. "

Ganin baiyi magana ba yasa tace "Dankali aka soyama da farfesun kayan ciki, xaka iya ci? "


Kallanta ya sakeyi sannan yace "eh"

Da sauri ta mike tai falo ta dan zubo a plate, tazo kusa dashi, kallanta yai baice komai ba.

Itama tsayawa tai rike da abinci batasan ya zatai ba.


Suna nan a haka har bacci yai gaba dashi, kuramai ido tai a hankali tace "Kayi bacci sau biyu kenan Ina tsaye. "

Tai murmushi sannan tace "sai dai duk banajin haushin hakan. "

Falo ta fito ta maida abincin sannan ta shiga gyara, har ta gama bai farka ba, itakam zuciyarta na raya mata taje ta sanar da mumy halin da Ashraf ke ciki, sai dai tana tsoro dan kuwa tasan halinsa, ta kuma kula kamar ba wani shakuwa sukai ba.


Gashi ta gama aiki kuma sam batasan ta

2 Comments On ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA
avatar
sadiyayunusa

1 year ago

Reply

Inaso sosai

avatar
khadija-murtala

17 days ago

Reply

Yayi dadi sosae

Please Login or Register in order to submit comment