Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

" karka damu ganinan ma shigowa gun."

Suna gama wayar dama yana kokarin ajiye mota ne, nan ya fito hankalinsa a kwance yai ciki.

Anisa ya gani a bakin kofar da Umma sun zauna a kasa kamar marayu, Anisa tana ganin Ashraf ta taho da gudu ta rungumeshi tana kuka, Ashraf yadan zare jikinsa tare da ce mata "Nisa a waje fa muke."

Da kyar ta d'agashi sai dai haryanzu kuka take, Umma ta mike ta kama hannun Ashraf tace " Ashraf ka taimaka ka anso mana yaron can, da alama Mahaifinsa bashida niyar ansoshi."

Ashraf ya kalleta cikin kulawa yace " karki damu Umma bari naje naji yanda ake ciki, amma ku me kuke anan?"

Umma tace " banasan shiga ne, bansan da wani ido zan kalli Asim a cikib wannan gun ba."

Ashraf yace " bari na shiga naji."

Nan yai cikin station din.

D'akin da suke ya kwankwasa, Kawu ya sake Asim sannan yace ya shigo.

Ashraf ya shiga cikin nuna kulawa yace " Kawu meke faruwa?"

Kawu ya kalli Ashraf sannan ya kalli Asim cikin takaici yace "ohon masa, nema yake kawai ya zubarmin da mutunci."

Ashraf ya kallu Asim yace " Asim a ina ka samu takardun filayen? Wannan ita kadaice hanyar da zaisa a warware komai."

Asim ya hadiye yawon wahala, ina zai iya furtawa da bakinsa yace shi ya turo 'yan fashi.



Kawu takaici ya kamashi a zuciye yai waje.

Asim ya matso kusa da Ashraf yace " Ashraf dan Allah ka taimakeni wlh bazan iya zama anan ba ko da na awannine ka taimaken dan Allah."

Ashraf yace " karka damu zamusan yanda za'ai."

Ya fito waje.

Kawu ya gani yanawa Kabir magana, nan ya matsa gun, yanaji Kawu yace " kana nufin kudin Company din ma sai na biya double?"

Kabir yace " sry sir amma haka ka'ida take, duk wanda yai embezzlement din kudin Company dolene ya biya double."

Gumi ne ya karyoma Kawu, nan yai gaba ba tare da yace komai ba, aransa fadi yake lalai Asim bashida hankali, haka kawai baici ba baisha ba asashi biyan kudi har million 200 a yini d'aya?


Ashraf ne ya d'au wayarsa dake aljihunsa ya turamai voice note din Auwal Max daya d'auka.

Kawu yana ganin sako gabansa ya fadi, da sauri yai waje yanaji su Umma namai magana amma ko sauraransu baiyi ba yai waje, ya kunna sakon.

_Ai ko layin bamu fita ba na sa matata ta kirani a waya akan batada lafiya dan nasan yallabai zai barni, da alama dai Mansir ya manta da hakan._


Gaban kawu ne yai mugun faduwa, cikin tsananin rikicewa ya shiga waiwaigawa, zuciyarsa ce tacemai Ashraf.

Nan ya koma cikin station din da sauri, can yaga Ashraf zaune kusa da Kabir suna magana, matsawa yai gunsu jiyai Ashraf yace "Yanzu Officer ba yanda za'ayi?"

Kabir yace" dolene sai ya biya kud'ad'an nan dan kuwa hakkin jama'a ne."

Kawu yai ajiyar zuciya da alama dai ba Ashraf bane nan yai waje.

Kabir ya kalli Ashraf ya sa dariya.

Shima dariya Ashraf din yai yace " Kb ka tabbatar ka tsareshi dakyau."

Kabir yace " karka damu mutumina."

Ashraf yazo ya lallaba Umma da Anisa ya kaisu gida, yana fitowa zai shiga b'angaren Mumy ya hango Nafi daga nesa.

Ta sha kwalliya sosai da sosai, ya shagala sosai wajen kallanta tana tafe tana lallatsa waya, gani yai kamar ta kara wani irin mugun kyau.

Ya shagala sosai da kallanta yaji alamar sako a wayarsa.

Nan ya duba, daga Nafi ne, _Yaya zanje gidansu Ferry._


D'agowa yai da sauri dan ya kara ganinta sai dai me? Wayam ya gani ba Nafi.

Da sauri ya matso yana nemanta, sai dai bai ganta ba.

Gun mai gadi ya nufa da sauri yace " Nafisa ta fita ne?"

Mai gadin yace " eh yanzun nan."

Ashraf ya leka waje da sauri, yana ganinta ta shiga motar Nabil, jiyai ransa ya sosu sai dai kafin ya karasa fitowa sunyi gaba.

Motar yabi da kallo sannan ya juya jiki a sanyaye.

B'angaren Mumy ya shiga, tana zaune a falo tana cin abincin rana.

Fuska ya daure tamau sannan ya zauna suka gaisa.

Ta amsa a hankali tace " kaje gun Asim ne?"

Bai amsa tambayarta ba sai cewa yai, passport dinki nake so."

Kallan mamaki tamai tace " me za'ai dashi?"

Yace " umara zakije kida Nafisa."

Tace " Umara?"

Ya kalleta yace " garin nake so ki bari, saboda in na barki anan Kawu zai yi tunanin amfani dake wajen tsaidani daga kamashi, sai dai banaji akwai abinda zai tsaidani, shiyasa nakesan ki bar garin in na kamashi sai ku dawo."

Kallan sa tai cikin wani yanayi, yace " karkiyi tunanin yafe maki laifinki nai, in kika dawo kema zaki je kuto a miki naki hukuncin."

Hawayenta ta maida sannan ta d'aga kai tace " ni naji nawa dalilin amma nafisa fa?"

Yace " Tsoro nake kar wani abu ya sameta, duk da na juya mata baya saboda banasan mutanen gidan su damu da ita, amma a zuciyata kullum da ita nake kwana nake tashi, ku tafi tare ko Allah zaisa ma taga mahaifiyarta."

Mumy ta jinjina kai alamar gamsuwa tace " Ya Hisham fa?"


Yace " Duk wanda yai laifi dole ne ya karbi hukuncin shi a duniya, shine kadai gatan da zan iya muku."

Yana kaiwa nan yai waje.

B'angarensu Little ya nufa, dan yanasan ganinta.

Daga lungun kofar ya ganta tsaye itada Habib, kasa karasawa yai yatsaya kawai jikinsa duk yai sanyi, ya zasuji in komai ya fito? Ya sani Habib ba wai san Little yake ba amma ita fa? Gata yarinya ya zatai???


*************



Nafi kam Nabil na jan mota yace mata " mutuminki fa ya fito, ina kallansa ta madubi."

Murmushi tai tace " share kawai Ya Nabil, shima hidimar gabansa ta mai yawa."

Nabil yai dariya yace " ko dai fadan masoya kuke?"

Tai dariya tace " ba wani fada, ko dan kaga nace inzaka wuce kazo mu tafi? Wannan ma ai dan naji kana anguwarmu ne."

Nabil yai murmushi yace " Feenah Allah nikam Ashraf ya gama kwafsamin, da ya kwaceki."

Harararsa tai tace " Ya Nabil ba nace ka daina min wannan zancen ba? Nifa kanwarka ce."

Yai ajiyar zuciya yace "ya zanyi tunda an maidani yayan karfi da yaji."

Zatai magana taji sako ya shigo wayarta.

Ashraf ne hakan yasa ta bud'e da sauri _Wajen karfe 4 za'azo a d'aukeki akwai inda za'akaiki._

Ta dan turo baki tace " ina za'a kaini???


Nabil ya kalleta yace " ya akai?"

Tace "bakomai."

Shikam Ashraf Dan Litti ya kira ya sanar dashi karfe 4 yaje ya d'auki Nafisa ya kaita inda akeyin passport akwai wani abokinsa daya kira yace suje 4 lokacin mutane duk sun ragu.


Dan Litti yace "da alama yau zanga Nafinmu kenan."


Nace lalai anfa dade ba'a gamu ba.....Lol😄




*#ASHRAFEENAH TEAM*

*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

_Sakonku ya isa gareni masoyana, insha Allah zanyi kokarin kammalawa zuwa sallah, ni kaina nakosa ingama, fatana dai kutayani addu'a Allah ya bani ikon gamawa lafiya...._ *Nagode kwarai!*


*79*

Da yamma kuwa Dan Litti ya nufi addreshin da Ashraf ya turomai na gidan su Ferry.

Nan ya kira Ashraf ya sanar dash ya isa shikuma ya ma Nafi sako akan ta fita wanda zai kaita ya iso.

Sunyi sallama dasu Umma sannan ta fito itada Ferry, ganin motar Ashraf yasa ta nufi motar.

Dan Litti yana ganinsun iso ya fito sanye da sunglasses, zaresu yai ya kallesu, Nafi kallansa take cikin mamaki shima kallanta yake.

Fuska ya hade tamau yace "malama lafiya?"

Nafi tace " bangane ba?"
Dan litti ya maida glass dinsa ya kalleta yace " Na fada miki bai kamata ki dinga bin mijin dake da aure ba, a kalla dai mutum ya dinga sanin darajarsa."

Nafi ta hade rai itama tace " kai kuma a wani matsayin kenan kake sanar dani haka?"

Mota ya bud'e yace " malama dan Allah kiyi gaba akwai wacce nake jira ne, tunda kinga ba mai motar bane ai sai ki kara mai."

Nafi da Ferry suka kallu juna, ferry tace " ruwa zata kara ba mai ba, sannan kai wanene ma?"

Ya kalli Ferry cikin isa yace " The Hand Right of Ashaf."

Dariyarsu suka guntse Ferry ta kalli Nafi tace " ke kuma fa?"

Nafi ta kalli Dan Litti tace " As his wife."

Duk da kalmar taba Ferry mamaki sai dai ta dauka ko dan ta kular da Dan Litti ne yasa ta fadan haka.

Idanu Dan Litti ya zaro yace " matarsa? Amma matan Ashraf ai na sansu."

Kai ta juya, da sauri ya kira wayar Ashraf yasa a hands free.

Ashraf ya daga yace " mutumin ya akai?"

Dan Litti ya kalli Nafi yace " wata ce take tutiya wai matarka ce."

Yace " wata kamar ya?"

Ferry ta fizge wayar ta mikama Nafi.

Nafi tace " Hello."

Ashraf yace " Nafisa? Ya akai? Kinga Dan Littin?"

Kallan juna sukai daga ita har Dan littin.
Cikin mamaki tace " Dan Litti?"

Shima yace " Nafisa?"

Ashraf yai murmushi yace " Da alama baku hadu ba sai yau." ya kashe wayar.

Dan Litti tsananin mamaki ya kamashi, kallan Nafi ya shiga yi.

Nafi cikin mamaki tace " Dan Littin gayu? Kaine?"

Kansa ya sosa yai kasa da kai yace " Hajiya Nafi wannan ko a mafarki naganki akacemin kece ai bazan yarda ba."

Dariya tai, Ferry tace " au dama kunsan juna?"

Nafi tace " Kauyenmu d'aya."

Ferry tai dariya tace " lalai yau akwai hirar gida kenan, ni nayi ciki."

Nan ta musu sallama tai gaba.

Ashraf ya bud'ema Nafi gidan baya ta shiga.
Mamaki har yanzu bai barsu ba.
Ya ja mota yana tambayarta ya akai bai taba ganinta ba?

Tace " wai da gaske a nan gida kake? Nima ban taba haduwa dakai ba a gidan mayb shiyasa bamu fahimci juna ba."

Hira suke sosai har suka isa inda zasu, waya ya kira akace su shiga.
Nan suka shiga ciki aka mata hoto sannan aka basu form da sauran abubuwa.

Ba musu take yin komai, sai dai tana bukatar amsar tambayoyinta daga bakin Ashraf.

Sun dade sosai sai bayan magrib suka fito, akan sai zuwa gobe azo a amsa.

Gida suka wuce, ta kalleshi tace " kana zuwa gida kuwa?"

Yace " nadaije kwanakin can da dadewa."

Tai shiru kafin tace " Baffa fa?"

Shiri yai shima kafin ya daure yace " yayi aure sannan ya bata labarin zuwansu da kamashi da akai."

Tayi dariya sosai jin turancinsa abinda ya ja mai.

Suna isa gida sukai sallama sannan tai bangarensu, duk da tana san magana da Ashraf sai dai tana tsoron zuwa bangaren tagansu da Anisa.


**********

Washe gari da safe, Ashraf yai wanka ya fito, bangaren Umma ya fara zuwa, tana kwance ba lafiya dan hawan jininta ya tashi, Anisa na zaune kusa da ita.

Ya gaishesu sannan yace zaije station yaji ya ake ciki, Umma tamai godiya tare da rokon ya taimaka ma Asim.

Ashraf yana fitowa ya kira Habib yace " mutumin kana ina?"

Yace " ina gida."

Yace " Dady fa?"

Yace " wlh dazun nan ya fita wai banki zaije, nace zan rakashi ma yaki."

Ashraf yai murmushi dan dama jikinshi ya bashi za'ai haka.

Mota ya fada Dan Litti yace mu tafi?

Ashraf ya girgiza kai yace " yanzu kawu zai fito so nake kabi bayansa ka sanar dani inda zaije."

Dan litti ya amsa da to, sannan yai waje shikuma Ashraf ya ja motar yai gaba.

Wayarsa ta jaka ya dauka ya kara turama Kawu sakob Auwal.

Kawu wanda ke ta zirga zirga a falon, hankalinsa duk ya gama dugunzuma bacci ma kasa samu yai jiya, yanajin sakon Auwal hankalinsa ya kara tashi ainun, da sauri ya kira number Dady.

Dadu ya dauka yace " Ya akai Mansir?"

Kawu yace " ya ya? Ka ciro kudin?"

Dady yace " ganinan na fito daga bankin yanzu sai dai ina za'a kawoma kudin? Sannan kana tunanin inkaba Auwal zai kyalemu kaga wlh duk na tattare kudina na sa a jakar nan."

Kawu yace " ni zansan yanda za'ai, sannan karka damu nace zan san yanda za'ai wasu kudin su shigo."

Dady yai ajiyar zuciya sannan ya kashe.

Kawu ya runtse ido yace " yanzu na samu kudin da zan taimaki Asim, in na gama dashi sai in dawo kan Auwal."


(Azahiri gaskiya Ashraf dama ya sani sarai, yasab duk yanda kawu yaso ga san Dansa bazai tava yadda ya tattare arzikin daya tara dakyar ba ya taimaki Asim ba, ya kuma san kawu zaiyi amfani da sakon magana na Auwal dayake turamai yai blackmailing din dady akan Auwal ne yake bukatar wannan uban kudi ko kuwa ya toba musu asiri.)

_Wannan kenan_

Kawu ya fito da sauri ya fada mota sannan ya turama Dady sako akan inda yake so su hadu.

Dan litti kam yana biye dasu har suka isa Mariri gun da gidaje ma kwayanune a gun.

Nan ya kira Ashraf wanda ke zaune a office hankalinsa a kwance yanashan tea, jin inda kawu yai yasa ya kira Kabir ya sanar dashi inda suke tare da cewa " ku tabbatar kun kwace."

Kb yace " karka damu abokina yaran danasa bazasu baka kunya ba."

Nan ya kashe wayar ya cigaba da shan shayinsa cikin annashuwa.

Kawu kam ya isa wani kango ya kira Dady yace " ya ya? Ka taho?"

Yace " ganinan na gangaro."

Daf da gun kadan Dady na tuka mota ga gun hanyar duk batada kyau wasu mutane ya gani a gabansa sanyi da kyalle baki sun rufe daga hancinsu, tsoro yasa ya taka burki tare da kallansu.


Nan suka zo suka bud'e motar d'aya yasamai bindiga d'ayan kuna ya d'auke jakar kudin, suka hau mashin sukai gaba.


Dady kam hannu kawai ya dora akai sam ya kasa komai.

Wayarsa ce tai kara ya duba ganin kawu ne yasa ya daga cikin tsananin tashin hankali yace " Mansir na mutu, na shiga uku, million 80 din dana dauko an kwacesu."

Yana kainan ya kasa magana.

Kawu ya fito a rikice, nan ya hangoshi ya isa inda yake cikin tsananin tashin hankali.


Ashraf ya gama shan shayinsa ya kwantar da kansa kan kujera tare da lumshe ido yace " Dady taya zaka bari Kawu ya dinga juya ka? Da na dauka kai ne mai wayau akansa sai dai yanzu na gane kai din a ido ne kake da cikar zati amma kawu ya fika nesa ba kusa ba."


Kawu cikin kunci da bakinciki ya isa station shikam Dady dakyar ya karasa gida idanunsa da jikinsa duk sun nuna alamar damuwa Da karayar zuci.


Kawu yana shiga station din wani tunani ya fado mai, ya akai aka kwace kudin da su biyu suka san da shi? Da sauri ya kira Secretary dinsa yace " dubamin ka gani Ashraf yazo?"

Nan yaje ya dubomai aka sanar dashi ai tun safe daya shiga office ma bai fito ba.


Hannunsa ya dunkule ya naushi bango wanda wani radadi da zugi suka ziyarceshi, yace cikin takaici "To waye? In har ba Ashraf bane wanene wannan da yake neman dimautani?yake neman ganin karshena?"

Zufa ce ta karyomai ya karasa cikin station din ya samu kabir yace ya ake ciki?

Kabir yace " yaki fadar inda ya samu wannan filayen, sannan wadanda suka bashi kudi sunce tabbas suna bukatar kudinsu yau zuwa gobe."

Kawu yace "in aka ki fa?"


Kb yai dariya yace " ai dole ne ma abiya dan kuwa kuto za'a shiga dashi wani satin dokene yabiya kudi sannan asan kuma hukuncin da za'amai "


Kawu yace " hukunci?"
Kb yace " kwarai dan in har satarsu yai to fa lalai sai ya ziyarci prison."


Hankalin Kawu ya kara tashi, jiki a sanyaye ya fito ko Asim bai gani ba.


Da yamma Dan Litti ya amso passport din Nafi nan Ashraf ya sa aka musu visa na umara wanda zasu tashi jibi nan, dan dama yafisan su tafi da wuri to sai yai sa'a ya samu International saboda ya tabbata daga Asim ya sanar da kawu a inda ya dauko takardun nan to fa babu makawa yasan shikenan Kawu zai san shine ya shirya komai...



Hmmmmmm😷




*#ASHRAFEENAH TEAM*

💞

[8/28, 19:55] Umar Dalha: *ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡



*80*




Mikewa yai daga zaman da yake tare da furzar da wata iska sannan ya d'au wayarsa yama Nafi da mumy sako akan su shirya saboda tafiyarsu.


Nafi kam kallan sakon take tayi, duk da tana masifar san zuwa kasa mai tsarki sai dai abin ya zo mata a ba zata, na farko ga bikin Jibiya wanda ya matso daf sannan ita a iya saninta Hajj ake fara yi tunda shine farilla.

Sai dai taci alwashin yima Ashraf magana in ya dawo.


*********


Sai Yamma ya fito daga office station ya wuce inda acan ya samu Umma, kana ganinta kasan tana cikin wani halin kusa da ita ya karasa yace " Umma lafiya?"

Hawaye ne ke zubowa a idanta tace " Ashraf banga alama Mansir nada niyyar taimakama Asim ba, na sanshi sarai akan dukiyarsa zai iya hakura da Asim a matsayin d'ansa ni kuma na tattare dukiyata naba Asim ya sa a kudin company din da ya siya."

Ashraf yai shiru tabbas ganin halin da take ciki ya sa ya tausaya mata sai dai bazai taba yin bailing Asim ba dan kuwa shine key dinsa na kama Ubansa.

Umma yaji ta kamo hannunsa tace " Ashraf na sani tun kana karami ba sanka nake ba, ban damu da harkarka ba sai dukiyarka, har rayuwarka na nemi salwantarwa ni da Asim, sai dai a yanzu ina dana sanin hakan, banida wanda zan iya roka akan ya taimaki Asim sama da kai, ka sani iyayena ba masu karfi bane ga girma ta zo musu, ni kuma banida uban kudin da ake bukata, Ashraf ka dubi girman Allah ka taimaki Asim."

Ashraf ya kalleta cikin kulawa zuciyarshi ta farayin sanyi, sai dai tunowa dayai ita kadaice taga Auwal Max a yayin da yake lalata birkin mahaifinsa yasa ya dake.

Yace " Umma karki damu muna tattaunawa da 'yan sandan insha Allah komai zai yi daidai."

Idanu ta runtse tace " Nagode Ashraf ban taba tunanin zan nemi taimako a gunka ba."

Ashraf yai murmushi sannan ya mike.

Gun Kb ya nufa, Kb yace " ya za'ai da kudin nan?"

Ashraf yace " ka kai banki a jiya bayan komai ya kammala zamu maidamai kudinsa."

Kb ya jinjina kai alamar gamsuwa sannan yace " what are u planning to do next?"

Ashraf yace " D'an Siyasan nan fa? Har yanzu shiru?"

Kb yace " yau muke sa ran dawowar yaron daya tafi binciken."

Ashraf yace " Allah yasa a sameshi wannan karan."
Kb ya amsa da Amin.

Gun Asim ya shiga, Asim har yayi baki ya rame, dan tunda yazo gun nan ya kasa cin abincinsu.

Ashraf ya kalleshi yace " Asim ance baka cin abinci, kasan dai dole ne kaci abinci ko ma samu mu gama wannan fadan da ya tunkaromu lafiya ko?"



Asim wanda kansa ke kwance kan tabir din ya dago ya kalli Ashraf yace " Nasani ni kuma tawa ta riga ta kare."

Ashraf yace " Haba Asim da hankalinka kuwa?"

Asim yai wata dariya ta tsantsar takaici, yace " rayuwa kenan, mahaifina da na dauka duk duniya yafi damuwa dani sai gashi lokacin da nake bukatar kulawarsa ya nunamin karema ya fini matsayi a gunsa, sannan kai da nake ganin kaine babban makiyina a duniya yau gashi kaine kake kula dani."

Ashraf ya hade rai yace " kai dai ka daina wannan tunanin na shirme ka kula da kanka har Allah ya kawo mana mafita."

Asim yai murmushin takaici baice komai ba.

Ashraf tare suka taho da Umma a motarsa tana sauka shima ya sauka yai bangarensa.

Ya sani Anisa na gun Umma hakan yasa ya fito falo bayan yayi sallar magrib sanyi da singlet da kuma gajeran wando.

Tv ya kunna yana kallan labarai, sai dai ya rasa ke yasa yau yakejin tsananin kewar Nafisansa, gyara kwanciyarsa yai ya koma rufda ciki, duk da yasan ba'asan kwanciyar sai dai yana ganin ita kadaice mafita.

Ganin hakan ma ya kasa kwantar mai da hankali kawau ya mike ya hau exercise, kwankwasa kofa yaji, sam ya manta shigar dake jikinsa ya karasa ya bud'e.

Nafi ya gani a tsaye fuskarta a maze.

Bari kofar yai a bud'e shikuma yai ciki, ta shigo tare da maida kofar ta rufe.

Sai da sukaje tsakiyar falo sannan ya tsaya tare da juyowa ya kalleta, Nafi itama kallansa tai, Ashraf kam wani abu ya dingaji yana taso mai, Nafi ta daure ganin kamar zuciyarta na neman yin rauni da kallan da yake mata, wanda shi kansa bai san yanayi ba.

Ta daure tace " Yaya mai kake nufi da zancen tafiya jibi?"

Ashraf kallanta kawau yake baice komai ba, ta dan motsa baki sannan tace " Yaya ke ka daukeni? Kaza? Tattabara? Ko me? Ba ka damu da ni ba, ka daina shiga harkata sannan kawai sai ka min sako akan inshirya wai jibi zanyi tafiya? In har a matsayin mutum kadaukeni banaji zaka dinga min abu haka, na rasa ya kakeso inyi da raina, ka daina kulani, na dauka na huri zuciyata nima na jure da kulaka, ka daina ko amsa wayata wannan ma na huri zuciyata na jure sai dai inma sako yanda kake min, sai dai banaji duk wannan abun da..........."

Yanda bakinta yake motsi tana magana gashi tasa jambaki light pink kawai yake kallo, kasa jurewa yai ya kai bakinsa cikin nata, wanda ya hanata karasa maganar da takeyi.

Wani irin salo yake mata wanda duk yanda taso taki biyemai ta kasa, kiss suke sosai wanda kana gani kasan lalai masoyan sunyi rashin juna da yawa.

Bakinsa na cikin nata suna mikama junansu sakon ni mai cike da kewa Ashraf kam duk ya rikice, ya saka controlling din kansa kan kace me? Ita kanta ya rabata da kayan jikinta, nan suka fada kan kujera........Hmmmm babban al'amari nikam ina ganin haka nai gaba.


Ashraf ya dade yana kwasar garar da ya dade bai ji ba, sai dai ya rasa dalili yau jinta yake daban ita kanta yau tasan Ashraf yayi missing dinta.

Suna gamawa ya rungumeta tsam a jikinsa, yana fitar da wani numfashi na farinciki, Nafi ma idanunta ta lumshe tanajin kaunarsa na kara ratsata, cikin wata irin murya mai cike da ma'anoni da yawa yace " Baby i really miss u."

Hannu ta runkule ta dan naushi kirjinsa tace " then y?"

Ya kara jawota jikinsa yace " dole ce ta sani hakan, saboda inasan amfani da Anisa."



2 Comments On ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA
avatar
sadiyayunusa

1 year ago

Reply

Inaso sosai

avatar
khadija-murtala

17 days ago

Reply

Yayi dadi sosae

Please Login or Register in order to submit comment