Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daya kasance ba haka ba."
Nafi tad'an juya kai sannan tace " Amma yaya daga ina kake a daren nan?"
Yace " Ko Mumy inta ganni na dawo a wannan time din banaji zatamin wannan tambayar."

Baki ta d'an turo batace komai ba.

Ya kalleta yace " ki wuce ki kwanta gobe kizo da safe muyi maganar makarantar."

Ta jinjijina kai alamar to, sannan ta juya.

Kallanta ya tsaya yi baisan sanda ya saki murmushi ba can yace " me aka mata? Wata zuciyar tace kasan su ai."
Tsaki yaja sannan yai 'yar kwafa.


B'angarensa ya nufa yana shiga ya shirya tare da kwanciya ya d'auko diary din Abbansa shafin tsakiya ya bud'e.

" Ashraf ban taba tunanin abinda naji da kunena ba har kuma a wannan lokacin ina fatan abinda naji ya zama karya ba gaskiya ba, don't ever trust anyone except ur self."

Ajiyar zuciya yai yace " Abba me kaji? Me yasa baka rubuta ba?"

Idanu ya lumshe zuciyarsa na zafi, a haka bacci yai gaba dashi.......

*Fatan Alkairi gareku Masoyana, Allah ubangiji ya barmu tare (Ameen)*


*THE INNOCENT TEAM*


*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

  *Wannan shafin sadaukarwace gareki yar uwar arziki Lubbabatu Maitafsir, Allah ubangiji ya kareki daga sharrin mutane, yasa ki gama da duniya lafiya....Ameen suma Ameen*

  *43*

    Da safe bayan nafi ta tashi daga bacci tai wanka sannan ta fita zuwa kitchen, da kanta ta shiryama Ashraf abinci sannan ta d'auka tai b'angarensa.

   Tsayawa tai tana mamakin ganin taje kwankwasawa taga kofar a bud'e, shiga tai tare da sallama sai dai jin shiru ba'a amsa mata ba yasa tai tunanin ko wanka yakeyi.

  Shiga tai ta ajiye tiren a kan dinning sannan ta karasa cikin falon da niyyar zama, a kwance ta ganshi akan duguwar kujera yana bacci, ta saki murmushi sannan ta karasa gun.

   Tsugunnawa tai a saitin fuskarsa ta kuramai ido bacci yakeyi sosai, a hankali tace "Handsome." sannan ta kalli kirjinsa littafine wanda bangonsa ke da kauri kana gani kasan ba irin littafan yanzu bane, hannu tasa ta d'aga littafin, jitai an rike hannunta.

  Da sauri ta kalleshi har a lokacin idanunsa a rufe suke, ta sake littafin tare da neman tashi, jawo ta yai wanda hakan yasa ta fad'a kan kirjinsa, idanu ta shiga kiftawa tana kallansa, idanunsa a rufe yace " ina zaki?"

   Kallan mamaki tamai ya akai yasan itace? Ko ya d'auka matarsa ce? Katseta yai da cewa " kin gama kallan nawa? Me kika gano?"

  D'agashi tai kad'an sannan tace " yaushe na kalleka?"

 Murmushi yai sannan ya bud'e idansa a hankali ta d'auka zaiyi mamakin ganinta sai taji yace " kin tabbatar ba kallona kike ba?"

 Kai ta d'aga tare da d'an juya kai, ya d'an had'e rai yace " to amma ya akai nakeji kamar anata kallona?"

  Ta kalleshi cikin shagwaba tace " dama ba bacci kake ba?"

  Ya sakar mata hannu sannan ya d'auke littafinsa tare da mikewa zaune yace " wayacemiki ba bacci nake ba?"

 Ta kalleshi idanunsa kuma sun nuna bacci yakeyi, tace " to ya akai kasan ina kallanka bayan bacci kake??"

  Ya sa diary din a gefensa sannan yace " ke zan tambaya."

Mamaki ya kamata ta kalleshi sannan ta nuna kanta da yatsa tace " ni kuma?"

 Ya juya kai sannan yace " amma da alama in babanki ya ganki yanzu banaji zai yarda kece 'yarsa."
 "Why?"ta fad'a tana kallansa, yace " komanki ya canza kinsan me ake nufi da komai?" ya karasa maganar yana neman kare mata kallo, mikewa tai da sauri tace " ni bansan wani komai ba sannan me yasa kabar kofarka a bud'e?"
  Yace " baki nake jira sai dai nayi mamaki danaji basuzo ba."

  Baki? Da safe?
 Kai ya d'aga sannan yace " bakin da ba'a sanin zuwansu bare tafiyarsu."

   "B'arayi??" tafad'a cikin tsoro, wani murmushi ya saki sannan yace " just 4get,kikace me jiya?"
  Tace " cewa nai zankoma skul yau saboda karatu, na saba bana dawowa gida shiyasa yanzu nakejina daban."

  Dinning ya kalla ganin breakfast yasa ya mike ba tare da ya bata amsa ba ya d'au diary djn nan ya shiga d'akinsa, toilet ya fad'a yai wanka sannan yai brush ya fito ya shirya.

  Nafi kam haushi duk ya isheta taya za'ai suna magana ya tashi ya barta agun ba tare Da yace mata komai ba, ta d'an harari kofarsa kad'an sanna tace " badai bacci ya koka ba? Wata zuciyar tace zai iya kuwa dan kinsan ya tab'a tsaidake yai bacci, ta dan cije leb'e sannan ta mike da niyyar yin zuciya ta fita, har taje bakin kofa ta tuna so take fa ashe tabar gidan nan, komawa tai a hankali tana tafe tana zumbure zumbure, har ta shiga falon zata zauna sai kuma ta kara kallan kofar ta kalli hotonsu da Anisa ta makama hoton harara sannan ta tab'e baki tace " da alama kai kadai kake santa, dan da tana sanka da bazata yarda da sharrin da akama ba wani ni karu.....Tsaki taja sannan ta kara hararar hoton tace " ko meye ma nasa hoto a falo? Sai kace ba'a sansu ba?"

   Ta had'e rai tare da kara hararar kofar tace " san maso wani kaima dai kakeyi kamar ni." tana cikin murg'udawa kofar baki Ashraf ya fito, idanu ta zaro ganin ya ganta yanda ta karkace baki, juya baya tai da sauri tare da rufe bakinta da hannu.

  Har ya karaso gunta bata sani ba sai kamshin turarensa kawai da takeji yana ratsata,har wani lumshe ido takeyi, saitin kunnenta ya kai bakinsa yace " badai bayan murgud'a bakinba harda zagi?"

 Daidai inda yai maganar ta juyo da fuskarta da sauri cikin tsautsayi bakinta ya tab'a nashi, jikinta ne ya hau rawa da sauri ta matsa ta fara ja da baya ta rufe bakinta da hannu tai waje da gudu.

  Shi kansa a kame ta barshi ganin yanda ta fita da gudu baisan sanda ya saki wani murmushi ba, da sauri ya girgiza kai yace " me ke damuna? Rainane ya kamata ya b'aci fa ganin abinda ya faru meyasa nake murmushi???"

   Kan dinning ya karasa ya bud'e babbar kular dankali ne na turawa sai dai an sarrafashi da nikaken nama dasu vegetables, kamshi ne kawai ke tashi, murmushi yai sannan ya bud'e d'ayar karamar kular awara ce a ido sai dai dayakai bakinsa sai yaji kamar cuscus, ya sake murmushi sannan ya had'a tea yana cin abinci yana santi, a ransa yace " nasan Nafisa ce tai lalai mijinta ya......." kasa karasa wa yai sakamakon jin dayai maganar tamai banbarakwai.
 

  Nafi kam da gudu ta fad'a d'aki a zaune taga little tana waya da alama da ya Habib ne ganin yanda take wani rage murya, Nafi ta fad'a gado sannan taja bargo ta rufe kanta ruf, tanaj Little na cewa " Yaya to ai kaine jiya ka tafi ba sallama, daga fitarmu."

  Nafi kam haryanzu bakinta a rufe yake duk da tana cikin bargo, me ta aikata??idanu ta runtse tace " me yasa ya kawo kanshi nan to?" iho ta d'anyi tare da kara dukunkunewa ganin haka yasa Little tai sallama da Habib ta matso tace " Feena meye hakan?" ta fad'a tana kokarin yaye bargon, Nafi kam ta kara kankame bargon ta daddane,Little tace " feenah meye hakan? Wani abun aka miki?ko su umma ne?"

 Nafi kam ba magana sai kara kudun dunewa take hakan yasa Little ta mike tai waje, a falo ta tsaya ta kira Ashraf,  shi kuma a lokacin yayi shiru sai abinci da yakeci yana mamakin meya hanash karasa maganarsa wayar Little ta shigo.

 Yana d'agawa tace " yaya inaji fa su Umma sun ma Feenah wani abun kaganta ta dawo ta shige bargo ko magana ta kimin.

 " karki damu bari nazo sai inji." tace to amma ni Mumy na kirana, zan bwrdai d'akin a bud'e.
 Ya amsa da to.

  Sai daya gama cin abinci sannan ya d'au key din mota ya fita, b'angarensu ya nufa, kamar yanda tace kofar kuwa nanan a bud'e hakan yasa ya shiga, tare da sallama.

 Nafi tanajin sallamarsa ta kara kudundunewa, Ashraf ya karasa tare da tsayuwa a gefen gadon yace " Malama tashi ko? Ko kin fasa tafiyar?"
 Nafi ta kara shigewa, ya d'aga kafad'a yace " bari kawai in fadama little mai kikai inaji hakan zai sa ki tashi."

 Gaban Nafi ne ya fad'i batai auni ba taji yace " Little kinsan mai yarinyar nan tamin??????"

 Ai batasan sanda tai wani irin mikewa va ta rufe mai baki da hannunta duka biyu ba tana faman girgiza mai kai Alamar kar ya fad'a.

  Kallanta yai duk ta sake karfinta akansa, wuyansa har kasa yai ya d'an sa hannu ya fara known karin zare mata nata hannun ita kuma ta kankame bakinsa, juyowa tai da niyyar yima Little magana sai taga ba kowa.
  Mamaki ya kamata ta juyo ta kallesh.

 Hannu yasa ya zare nata hannun da karfi yace " me? Kunya kikeji?"


*THE INNOCENT TEAM*
 
*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

  *44*

   Nafi fuskarta d'auke da mamaki ta ke kallansa, ya kalleta shima yace " What?" murmushi tai sannan tace " dama ka iya tsokana? This is the first time i......"
  Katsets yai tare da had'e fuska yace " yaushe kika dawo da kike tunanin komawa?"
 Tai murmushi sannan tace " Yaya S3 zamu shiga so nake kafin lokacin waec a karamin lesson sosai."
Ashraf bai san sanda yace " ai kina kokari sosai, bakiyi primary ba amma gaski kin iya speaking sannan ko a class result dinki ba mai muni bane." a zahirin gaskiya shi ya d'auka a ransa yake fad'a sai dai gani yai Nafi tayi kasa dakai cikin farin ciki tace " Yaya a koda yaushe tsoro nake kar exam ta fito inga banyi abin arziki ba banaso kayi tunanin rashin amfanin kaini makarantar dakai."

   Kallanta yai na wasu 'yan dakiku duk da kanta na kasa sai dai yaji dadin kalamanta, yace " yanzu kin daina san kiga Mahaifinki?"

  D'agowa tai ta kalleshi idanunta suka ciciko sai dai hawayen basu zuba ba, Ashraf ya sake had'e rai yace " Naga alama haryanzu ke raguwa ce." ya juya zai fita, hannu tasa da sauri ta riko rigarsa, ya tsaya cak sai dai bai juya ba.

  A hankali ta fara magana " Yaya ba wai dan kayi zancen Baffa bane yasa kaga nayi haka, kuma yanzu ko ni bazance zanje ba harsai na gama karatuna, sai dai naji dadi ta yadda baka manta da komai ba."

  Juyowa yai da niyyar yi mata magana idanunsa suka sauka akan wayar da saurayinta ya bata a gabansa, ji yai ransa ya b'aci ya kurama wayar ido ba tare da ya d'auke idansa ba yace " ki shirya ki sameni a bakin mota."
 Yana kai nan ya juya, da sauri itama ta juya dan ganin inda ya kalla, waya ta gani da sauri ta dafa kai cikin takaici ta d'au wayar har tana kokarin jefata cikin drawer sai tace " wait a moment..... Me yasa yaji haushi dan yaga wayar?"
  Ferry ce ta fad'o matavda sauri ta kuna wayar ta danna number ferry, sai data kusa katsewa ta d'aga cikin muryar iyayi tace " Hello! "
  Nafi tai dariya tace " to uwar jan ra'ayin maza nice."

 Muryarta  ta sake sannan tace " Feenah amma kin kwafsa."
  Nafi tai murmushi sannan tace " Ferry tambaya zan miki."
 Tace "me? Akan yayan naki?"
 Nafi ta d'aga kai kamar tana ganinta sannan tace " yanzu yaga wayar da wani ya bani sai naga ya had'e rai sosai, me kenan?"

  Ferry tai dariya sannan tace " cikin d'ayan biyu ko ya fara kishinki ko kuma kice kika fasara abun haka."
  Nafi cikin masifa tace " Nafassara kamar ya?"

  Ferry ta sake dariya sannan tace " saboda kinaso yai kishinki mana yasa kikai tunanin haka."

  A zuciye Nafi ta katse wayar ta ja dogon tsaki sannan tace " na fassara? A gabana fa naga ya had'e rai."

   Wayarce taji tayi kara tana dubawa taga ansa My Number, Alamin ne tai d'am tsaki ba tare da ta d'auka ba ta mike ta hau shiryawa.

   Ashraf kam yana fita yai b'angaren Umma, a zaune ya samesu suna breakfast ya karasa ciki bayan anmai izinin shigowa, Anisa dai kawai cakular abincin takeyi ganin Ashraf yasa ta kuramai ido tanaji kamar taje ta rungumeshi, sai dai abin haushi ko kallanta bataga yayi ba, ya karasa ciki ya kalli Asim wanda ya had'e rai yana zubamai harara.
  Kowa a falon ya d'auka biko yazo yi, bayan ya gaida Umma ta amsa sai ta d'ora da cewa " Ashraf yanzu meye amfanin fad'an da kukai bayan kowa yasan yanda kuke san junan ku yanzu
......"

  Katseta yai tare da kallan Anisa yace " ina kikasamin takarduna na rannan?"

  Kowa yayi mamakin wannan kalaman nasa sannan ran kowa ya b'aci, Ashraf ya cigaba " na kira wayarki a kashe, fad'amin inda suke dan inada abinyi." ya karasa maganar tare da mikewa tsaye, Anisa cikin tsantsan kuluwa da takaici tace " Suna drawer d'akinka."

  Bai sake cewa komai ba ya juya ya fita, Asim ya daki kirjinsa da karfi cikin takaici yace " Umma yaron nan zai samin hawan jini in har ba'a kawar dashi daga gabana ba."

   Ashraf yana fita har zai wuce sai yai tunanin gaida mumy hakan yasa ya shiga, tana zaune itama kusa da Kawu ta zubamai abinci yana ci ita kuma tana zaune kusa dashi, ransa yakai kololuwar b'aci a duniya ba A binda ya tsana irin ya shigo yaga mahaifiyarsa da kanin babansa a zaune suna soyayya duk sai yaji komai yamai zafi, juyawa yai ba tare da ya musu magana ba yai waje, Little dake gyara falon Mumy ta kalleshi tace " har ka fito?"
  Kallanta yai da jajayen idanu wanda hakan ya bata mamaki taga yanzu ya shiga lafiya kalau, yace " karkice mata nazo."

  Ya juya ya fita, kallo ta bishi dashi sannan itama ta leka wajen dinning din, yanda ta gansu a kasa suna cikin fara'a gasu daf da juna yasa ta fahimci abinda ya sa yayan nata haka.
  Ashraf kam yana fita yai bakin mota, tun daga nesa ya hangota zuciyarshi tai haske duk da bai fito kan fuskarsa ba amma ya rasa dalilin dayasa yaji kashi 60 na bakin cikinsa ya yaye.

 Cikin atamfa riga da siket take sun zauna a jikinta kalar atamfar akwai orange hakan yasa ta sa mayafi orange tayi kyau sosai.
  Yana karasawa ya bud'e mota ya shiga itama ta shiga, Anisa kam da bayan fitar Ashraf ta d'an tsaya kad'an can ganin zata cuci kanta yasa ta fito da gudu ko d'ankwali babu a kanta tana yin kwanar inda ake ajiye motoci ta hangosu sun shiga mota tare.

   Wani irin kishi ne ya lulub'eta ta saki kukan takaici da tsana da take musu duka su biyun, a haka ta koma ta sanar dasu Umma nan  suka samu abinda sukeso sukaita zugata yau kam zugar tayi tasiri dan ta d'au alwashin amso zuciyar mijinta da dukiyarsa sannan ta kora wannan kucakar kauyensu.

  Suna shiga mota ya kalleta zaiyi magana ringing ya katsesu, jin ba irin ringing d'insa bane yasa ya kalleta, itama cikin nata salon dan da saninta ta d'auko wayar tanasan tabbatar da abinda zuciyarta ke so, kallansa tai cikin shakka sannan ta kalli wayar, ta canzama Alamin suna daga My Number zuwa My Alamin, ganin sunan daya fito kan wayar yasa ransa ya sake b'aci dama gashi bai gama warewa ba a zuciye ya fizgi motar sukai waje.

  Nafi kam bata d'auki wayar ba sai tai kamar irin tsoron Ashraf takeyi,sunyi nisa akan titi ba wanda ya kula wani, Nafi ganin haka yasa ta d'aure tace " yaya baka tsaida magana ba akan tafiya..."
 Bata karasa ba taji yace " gobe ki shirya ko driver din mumy ne ya kaiki."

  She really feel disappointed ganin yanda ya bata amsa ba wani damuwa ko kulawa, wata zuciyar tace " dan kawai ya sake miki fuska yau kin dauka sanki yake? Stop dreaming Feenah."

  Kanta ta juya ta kurama titi ido, a cikim ginin Ado bayaro mall yai parking sannan ya fito, a hankali itama ta fito tare da kallan garin, hadari ne ya fara had'uwa.
 Ta juyo ta kalleshi taga yayi gaba, tsayawa tai cak ranta inyayi dubu ya b'aci ta bi bayansa da kallo ba tare da ta je inda yake ba, sai dayai nisa sannan ya juyo mamaki ya kamashi ganin bata taho ba tana tsaye a jikin mota sai idanu da ta kafeshi dashi.

  Shima tsayawa yai yana kallanta me takeyi acan?"
  Nafi ta juya tare da kifa kanta a saman mota ji take kamar tai kuka ko zataji dadi wannan dizgi har ina? Suzo tare amma ba magana sai kawai yai gaba ya barta, so yake ya nunama kowa bashida hadi da ita ko me?

  Jitai ance " in bazaki jeba shiga mota in maidake gida ko ki hau adaidaita ki tafi, kina tunanin banda abinyi ne?"

  Ta juyo ta kalleshi yana tsaye ya had'e fuska sosai, d'azu ta tuno sanda ya sakar mata fuska wannan wani irin mutum ne?"
  Ran Ashraf ya kara b'aci ganin wayar a hannunta, ta d'aure tace " yaya kasan ban taba zuwa ba amma kana ajiyeni kai gaba kabar ni, ya kakeso inyi?"
  Ranshi ya sake b'aci yace " bakida kafa ne ko kuwa jaririya ce ke?"

  Nafi ma cikin b'acin rai tace " duk da ni ba d'aya daga cikin abinda ka lissafa bace amma ai nima inasan kulawa, taya zamu taho tare ace kana can gaba ni kuma ina can baya?"
 Ashraf ya kalleta zaiyi magana yaji tace " so kake ka nunama kowa bakada alaka dani?na sani kafi karfin ajina balle har ka jera dani sai dai na rasa me yasa nakeji zafin hakan aduk lokacin da kamin, nasan da hakan har kasan zuciya ta to why nakejin zafi?"
 Ta fad'a tare da juyawa tana neman maida kwallarta, jikinsa ne yai sanyi sam matsalarshi kenan bayasan yaga ya sa mace kuka, kallanta yai sannan yace " zaki iya tahowa yanzu?"

  Kallansa tai sannan ta fara takawa a hankali, Yana gaba kad'an tana binshi a baya, har suka isa cikin shop right  nan ya nuna mata babban cart ita kuma ta jawo suka fara zagawa, ita take nunamai abin bukatar makaranta inta sa d'aya sai ya kara biyu a ciki su zama uku, haka suka sai kaya sosai, ita har tsoro take nawa za ace musu in akazo gun biyan kud'i?

  Bai bari taji ba ana fad'an nawa ne yai saurin mika Atm card dinsa nam aka cira sannan akasa wani ya kai musu mota.

  Suna fitowa sukaga gari ya turnuke sosai, nan sukai sauri suka shiga mota, ko fita daga mall din basuyi ba aka fara yayyafi, kafin kace me? Ruwa ya tsuge sosai ruwa mai karfin gaske wanda ko gaban mutum baka gani.

  Nan Ashraf ya gangara gefen titi yai parking, sunyi shiru sai kallan yanda ruwa yake sauka kawai sukeyi, Nafi batai auni ba taji muryar Ashraf cikin sanyi yace " karki sake cemin nafi karfinki wai ko na tafi saboda bazan iya jera wa dake ba."

  Kallansa tai cikin wani irin yanayi mai wuyan fassarawa ya juyo shima ya kalleta, ganin yanda take kallansa yasa yaji wani abu na ratsamai jiki, kansa ya d'auke da sauri, ya had'e rai sosai, Nafi ta matso sannan tace " Yaya ni..."
 Wayarta ce ta sake katseta ya juyo ya kalleta tare da kallan wayar, number d'azu ce, ta kalleshi cikin tsoro kafada ya d'aga mata sannan ya mata alama akan ta amsa wayarta.

  Jiki a sanyaye Nafi ta d'aga tare da sallama, Alamin yai ajiyar zuciya yace " At last kin d'au wayata."
 Nafi idanunta nakan Ashraf tace " sry d'azun ma wani abu nakeyi."
 Ashraf kam wayarsa ce a hannunsa yana dannawa sai dai hankalinsa na kan wayar da take.
  Alamin ya saki murmushi sannan yace " Feenah plz ki daina jamin rai wlh zuciyata zata iya kamuwa da ciwo in har baki tausaya kin amince da ita ba."

  Har yanzu idanta nakan Ashraf sai dai jin kalaman Alamin sun sa ta d'an sassauta murya kamar mai rad'a tace " Alamin ya kake so inyi wai?"

  Yace " ki amince dani na zama saurayinki ni kadai."
  Tace " bangane ka zama saurayina kai kadai ba??"

  Ashraf ne ya juyo ya buga mata wani mugun kallo wanda batasan sanda ta sauke wayar ba daga kunnenta hannubya bata akan ta bashi wayar ba musu kuwa ta mikamai ya sa hannu ya amsa tare da kashe wayar gaba d'aya, mamaki ya kamata a ranta tace ko kishin ne??
 Jitai yace " ku mata wani sa'in me yasa bakuda tunani ne?"

  Nafi ta zaro ido cikin mamaki tace name fa?

  Ya kalli wayar yace " ke kina ganin burgewa ne saurayi yaba budurwa waya ba wata magana mai karfi a kasa?"
  Nafi ta turo baki batare da ta amsa ba, yace darajarta take ragewa agunsa alama kuke nunawa na abin hannunsa kuke so.

  Nafi cikin takaici tace " ai ba ni nace ya bani ba sannan magana mai karfi ai za'ayita in na gama makaranta."

  Dariya taga yayi sannan taji yace " kin manta me nace miki kenan ko? Randa zakizo garin nan."
 Kallan mamaki tamai yace " cewa nai sai na yarda da yaron sannan zan baki takardarki."

  Kallan sa tai sai dai zuciyarta taji ba dadi haryanzu wato yana tunanin bata takarda ko??????

*THE INNOCENT TEAM*

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

  *45*

  Ranta yakai koluluwa gun b'aci Ashraf bai tsamani ba kawai yaga ta bud'e motar ta fita, ga ruwa ake sosai, da sauri shima ya bud'e kofa ya fita, tafiya kawai take tsabar ruwa batama san ina take sa kafarta ba, Ashraf ya hanzarta ya riko hannunta.

   Kallansa tai sannan ta fizge hannunta da karfe ta nemi ci gaba da tafiya, hannayensa biyu yasa ya rike kafad'arta ya juyo da ita saitinsa yace " Nafisa!!" ya fad'a tare da jijiga mata kafad'a, Nafi ta shiga neman kwace jikinta ganin yanda ruwa ke dukansu gashi da alama taurin kai take nemanyi yasa kawai ya d'agata cak yai mota da ita ahakan ma saj wutsul wutsul take, ya bud'e mota ya sata sannan ya zaga  da sauri ya shiga tare da sama motar lock.

  Nafi ta juya kanta gefe, hannunta ya kamo yace " menene wai?kanki d'aya kuwa?"
  Ta kalleshi da idanunta da suka ciciko cikin wani irin murya ta kalleshi tare da cewa " yaya ni nace ka aureni?"
 Kallan mamaki ya mata, ta share hawayenta duk da tasan abanza dan kuwa hawayen sai ma kara zubowa takeyi, ta kalleshi sannan ta cigaba " Yaya ni bw mutum bace?dutse ce ni ko kuwa?"
 Kallanta kawai yake sam ya kasa magana, hawayen da takeyi da kalamanta sune kawai ke ratsa shi, ta kara share wasu kwallan sannan ta cigaba " ka tab'a ganin inda mace a ranar da aka daura mata aure miji yake mata zancen saki? Ka taba tunanin yanda wannan matar zataji duk da yarintar dake damunta a lokacin??"

   Ashraf jikinsa ya mutu sosai, Nafi ta sake goge kwallar sannan tace " ka bani takarda ta yanzu inaji shine kawai abinda ya kamata, a gun iyaye da mutanen garinmu ne kawai kake mijina waya san abinda ke tsakanin mu? Ni kaina mantawa nake da auren ka akaina, baka tunanin halin da zan fad'a idan na fara kula wani?ku kuwa ba zunubi na aikata ba in nai hakan?"

  Ashraf ya kara rike hannunta yace " Nafisa!"

  Hannunta ta kwace ta kalleshi cikin idanunta da suke zubo da kwalla tace " na gode sosai daka taimakeni, ka kula dani ka kuma sani a makaranta sai dai ina ganin lokaci yayi da nima nake bukatar zuciyata ta huta da kokwanton ni matar aurece ko bazawara ko kuwa budurwa?ka bani takardata gobe in koma mahaifata."

   Idanu Ashraf ya runtse sannan ya bud'esu a hankali ganin yanda take kuka bai san sanda ya jawota jikinsa ya rungumeta ba, kokarin kwacewa ta shigayi sai dai ya riketa sosai ganin ta kasa kwacewa yasa ta rikeshi itama tare da cigaba da kuka, jikinsu ya

2 Comments On ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA
avatar
sadiyayunusa

1 year ago

Reply

Inaso sosai

avatar
khadija-murtala

17 days ago

Reply

Yayi dadi sosae

Please Login or Register in order to submit comment