Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaga Anisa na tahowa, hade rai yai jakarsa ya dauka yai kamar bai ganta ba, Anisa ta karaso da saurinta ta rike rigarsa ta baya.

Dole hakan yasa ya tsaya, juyowa yai ya kalleta yace " ya akai?"

Idanunta ne suka ciciko tace " yaya."

Kallanta yai yace " ya akai?"

Ta share kwallarta tace " jikin Umma ba dadi, ga ya Asim har yanzu shiru."

Kallanta yai kawai baice komai ba.

Anisa ta rike hannunsa tace " yaya muje dan Allag ka duba Umma, itama tun dazu take nemanka."

Bai musa ba nan suka nufi bangaren Umma.

Tana kwance a d'aki tana ganin Ashraf ta shiga kokarin mekewa zaune.

Ashraf ya kalleta sannan ya kalli Anisa yace "dan bamu guri ko?"

Anisa ta juya ta fita.

Umma ta karasa zama sannan ta kalli Ashraf tace " Ashraf ya maganar Asim?"

Kallanta yai sannan yace " Asim? Ina zan sani in har ku iyayensa baku sani ba?"

Mamaki ne ya kamata tace " Ashraf na rokeka dan Alla......."

Ka tseta yai yace " duniyarnan al'amuranta na bani mamaki, har kasan zuciyarki daga ke har dan naki banaji akwai daidai da kwayar zarra da san 'yan uwantaka da kukemin, banda neman halakani da kukeyi, amma wai ko kunya ni kike cewa in taimaki danki?"

Umma jikinta yai sanyi dana sani suka ziyarceta tace " Ashraf na sani sai dai......"

Katseta ya sake yi yace " ni a wannan lokacin ba abinda zaki fada da zan aminta dashi, abu d'aya nazo fada miki yanzu, in har kinason danki ya fito, sannan kinasan farincikin 'yarki to inaso nima kimin abu d'aya."

Da sauri tace " zan maka shi ko menene."

Ya kalleta yace "inaso idan na nemi shedarki akan mutuwar mahaifina ki bada shaida yanda kika sani tsakaninki da Allah."


Cikin tsoro ta kalleshi tace " Ashraf me kake fada haka?"

Yace " wannan ba damuwa ta bace, iya abinda zance da ke kenan, in kuwa har kikaki bada shaida kamar yadda nace to ki jira abu biyu, na farko danki dolene ya ziyarci gidan yari, na biyu kuwa ki jira takardar mutuwar auren 'yarki kinsani sarai yanda Anisa take sona, na tabbata bazata taba yafe miki ba inhar taji kece sanadiyar mutuwar aurenta."


Hankalin Umma ne yai mugun tashi,Ashraf yace " sai ki zab'a da mijin da bai taba sanki ba, bai kuma damu da ke ba da 'ya'yan da kika haifa kike sansu kamar ranku suma haka, sai ki duba kiga wanene zai fi miki amfani nan gaba."

Yana kaiwa nan yai waje.

Hawaye ne ya biyo kuncin Umma lalai yau tana ganin tashin hankali ina zata sa kanta da rayuwarta???????


************


Dady zaune a d'aki kusa da matarsa cikin kunar rai yake sanar da ita komai, hankalinta yayi tsananin tashi da jin abinda ya faru sai dai abinda basu sani ba, Habib wanda ya taho d'akin, cak ya tsaya jin zancen da sukeyi.


Hankalinsa yayi mugun tashi da jin abinda ya faru, muryar mahaifiyarsa yaji tace " Dadyn Habib yanzu ya zamuyi da hakkin maraya da kuma wanda ya rasu?"

Dady cikin mamaki ya kalli matarsa yace " dama kin sani?"

Kallansa tai cikin kulawa tace " najiku a ranar da abin ya faru da safe kuna zancen, wanda hakan yasa nai saurin kiran Ruma na sanar da ita sai dai bakin alkalami ya riga ya bushe dan alokacin Abbas ma yana cikin mota."


Jikin Habib ne ya shiga rawa, muryar Dady yaji yana cewa " Na shiga uku, tunda nake a rayuwata ban taba tunanin zan hada kai in kashe wani ba sai gashi nayi akan mijin kanwata wlh kinji na rantse miki tun bayan faruwar wannan abun duk sanda na kwanta sai nayi mafarkin Abbas yana min murmushi wanda hakab ke kara karyamin zuciya sai dai san abin duniya yasa na kasa yin nadama sai ma tunanin yanda zan kara mallakar wata dukiyar tasa da nakeyi."


Gaba d'aya jikin Habib ne ya shiga rawa, da kyar ya iya saukowa daga saman dakin, d'akinsa ya nufa ya zube a kasa sam kwakwalwarsa ta dauke ya rasa ma tunanin mai zai fara abu d'aya kawai yake mai yawo a zuciya mahaifinsa da mahaifin Little sune suka hadu suka kashe mahaifin Ashraf wannan wani irin mugun al'amari ne?????




************


Kawu ne a d'aki sai safa da marwa yakeyi dole yasan matakin dazai dauka akan wannan yaron, dan kuwa baiga mai rabashi da Ruma ba baiga kuma bai rabashi da dukiyarsa ba.

Akwatinsa ya dauko na karkashin gado, sai dai ya zaro takardar wasikar da Abbas yamai yaga tagardar ba komai, hankalinsa ya tashi matuka ya fito daga d'akin ya nufi bangaren Umma.

Anisa ce kadai zaune a falo, ya shigo kallansa tai tace "Abba kazo duba Umma ne?"


Fuskarsa a hade yace " ke kika bud'emin akwatin kasan gado na?"

Gabanta ne ya fadi cikin i-ina tace " ba ni bace."

Tsawa ya daka mata yace " tun bayan shigarki d'akina ba wanda ya kuma shiga bazaki fadamin gaskiya ba."

Shiru tai sai gabanta dake faduwa, jitai yace " Ashraf kika ba?"

D'agowa tai ta kalleshi a tsorace tace " wlh ba ruwan yaya ni......"


Lebensa ya ciza da karfi yai waje a zuciye.

Bangaren Ashraf ya nufa wanda rabansa da bangaren har ya manta.

Jin kwankwasa kofa yasa Ashraf ya mike dan dama yana zaune ne tun dazu yana neman wayar Nafi tunda yasa layin Mumy shi ya amsa da kansa to na Nafin kuma sam ya ki shiga.


Yana bud'e kofa yaga kawu a tsaye.

Ashraf cikin mamaki yace " lafiya?"

Hannu kawu ya mikamai yace " bani wasikar daka dauka a d'akina."

Ashraf ya mai kallan mamaki yace "wasika?"

Kawu yace " wanda kasa Anisa tadaukoma."

Ashraf yace " ohhh wannan? Nikaina bansan inda yake ba."

Kawu yace " mene?"

Ashraf yace " kunya kakeji kayi karya ka b'oye akan Mahaifiya yace karna auri 'yarka?ko kuwa kunyar mai illa dakai kakeyi?"

Kawu ya juya bai kara magana ba cikin takaici lalai dole ya dau mataki akan yaron nan dan kuwa da alama ya gama sanin komai.




*#ASHRAFEENAH TEAM*


*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡



*84*



Rayuwa tayima mutane 4 zafi, na farko Kawu wanda yake tunanin yanda zaiyi ya halaka Ashraf ba tare da sanin kowa ba.

Na biyu Habib wanda kunnensa ya jiyomai tashin hankalin dayafi karfinsa.

Na uku Umma wacce ta rasa ina zata sa kanta, 'ya'yanta zata ceta ko kuwa mijinta.

Sai na karshe Hisham wanda nadamada danasani suka taru suka mai yawa.


Yau kwanan su Nafi 4, da barin gari, jikinta dai haryanzu ba wani sauki sai dai ba kamar da ba, yanzu tana dan cin kayan itace (Fruit)

Mumy kam ta kasa daurewa ranar suna zaune a d'aki ta kalleta tace " Nafisa anya ba ciki gareki ba?


Nafi cikin tsananin mamaki ta kalli Mumy gabanta ya fadi.

Mumy ta matso kusa da ita tace " bakida kowa a garin nan da ya wuce ni, shiyasa nima na cire kunyar surukantaka na tambayeki, Nafi a matsayin 'ya na daukeki ba sirika ba, nayi dana sani sosai na kin amincewa dake danai tun farko har nake nuna miki cewa mace mai ilimi itace ta dace da Ashraf."

Kan Nafi na kasa ta kasa dagowa.
Mumy ta dafata tace "muje asibiti."

Da sauri Nafi tace " a'a Mumy."

Dariya Mumy tai tace " me? Kunya kikeji?"

Nafi tai kasa dakai.

Haka Mumy ta matsa mata dole da yamma suka nufi asibiti.

An mata gwaje gwaje nan aka tabbatar musu tana da ciki na sati bakwai, farin ciki agun Mumy baya misaltuwa, ta kalli Nafi cikin zumudi tace " kinsanar da Ashraf?"

Kanta ta girgiza alamar a'a tace " ni ai ko waya bamuyi ba tunda muka taho."

Mamaki ya kama mumy tace " akan me?"

Nafi tace " wlh bakomai, kawai dai nasan yanada al'amuran dake gabansa ne dayawa."

Mumy tai shiru, jikinta yai sanyi ba shakka kam yanada su dayawa.

Nafi ta kalleta tace " Mumy karmu fadamai harsai ya gama."

Kai Mumy ta daga alamar amincewa.


************


Ashraf na zaune gidan Uncle Salim dashi dasu Auwal Max.

Ashraf ya kalli Auwal yace " kayi hakuri kaga haryanzu bamu maidakai ba."

Auwal ya girgiza kai yace " ba komai, acan din ma me nakeyi banda wahala, matata ta rabu dani ko ince tunda taga banida komai ta fitineni sai dana bata takardarta, 'ya'yan da muke dasu guda biyu ta kwashesu, ni ba sana'ar arziki ba sai dai inyi can inyi can."

Ashraf ya kalleshi cikin tausayawa, Auwal yai murmushi yace " na sani alhakin Abbas ne ke bina, mai gida ya kula dani sosai amma naci amanarsa."

Ashraf ya mike jin idanunsa na rawa ba shakka an zalunci mahaifinsa dayawa, shiyasa akullum in ya tuna akwai ranar hisabi sai yaji zuciyarsa tayi wani dadi.

Sako ne yashigo wayarsa daga Little.

Cikin mamaki ya bude _Yaya dan Allah kazo gidan gona na Mumy dake bayan gari akwai matsala._

Abinda aka rubuta kenan a sakon, shiru yai yana kara kallan sakon.

Kb ya kalleshi yace " ya akai?"

Ashraf ya mika masu wayar, sannan yace Auwal ya shiga ciki.


Kb ya karanta yaba Salim shima ya karanta, Ashraf ya kalli Kb yace " bari inje."

Uncle salim ya kalleshi yace " anya Ashraf baka tunanin da matsala kuwa?"

Ashraf yai murmushi ya kalli Dan Litti yace " Mutumin muje?"

Dan Litti ya mike, Kb ne ya dafa Ashraf yace " Ashraf."

Ashraf yai murmushi yace " karka damu, kawai dai nan da 20mins ka kira 'yan sanda kuzo gurin."

Kb ya kalleshi cikin kulawa, Ashraf ya kalleshi sannan ya kalli Uncle yace " cikin abu biyu akwai d'aya, ko dai da gaske wani abun ne ya samu Little kaga kuwa in naki zuwa ko me ya sameta daga baya bazan iya yafema kaina ba, ko kuma trap ne Kawu ya shirya min."

Salim yai shiru tabbas ya gamsu da bayanin Ashraf, ya mike yace to muje tare.

Ashraf ya girgiza kai yace " A'a Uncle karka damu ba abinda zai faru."


Sun fito dashi da Dan litti suka shiga mota sukai gaba.


A hanya ya turama Little sako akan gashinan zuwa.

Sun isa can waje gari inda gidan gonar Mumy yake, da sauri ya fito ya shiga ciki.

Yana shiga cikin gun yaji daga baya ta waje an datseshi.


Tsayawa yai cak ya kurama kofar kallo.

Sannan ya kalli cikin gun, ba komai agun, kajin ma babu ga kajinan nan wayam.


Dan Litti daya taho yazo yin kwana yaji an kwadamai wani katako.

Nan ya fadi kasa a sume.

Ashraf kam da sauri ya koma bakin kofar ya fara jijiga.

Wayarsa ce tai kara, nan ya zarota.

Ganin number Little yasa ya daga da sauri.

Jiyai an sheke da dariya, da sauri ya danna record a jikin wayar sannan yace " Kawu ina Little?"

Kawu ya sake dariya yace " kai da Little sai dai ranar tashin kiyama, dan kuwa kai daga nan sai kabarinka."

Ashraf cikin mamaki yace " me kake shirin yi?"

Kawu ya sake dariya yace " me? Are u scared?"

Ashraf yai shiru.

Kawu yace " Kasan dai Maryam 'ya tace, 'yata kuma wacce na haifa da Ruma, kana tunanin zan iya halakata ne? Na dauka u are smart ashe kaima kan baya jaaa."

Ashraf cikin fada yace " me kake tunanin yi?"

Kawu yasa dariya yace " kanada sako gun tsohuwarka ne?"

Ji yai alamar kauri hakan yasa ya jujuya mai zai gani?

Wuta ne ya fara ci ta waje.

Kawu yace " ina jiranka."

Ashraf yace " ka kashe mahaifina yanzu ni zaka kashe? Sannan kacigaba da zama da mahaifiyata?"

Kawu yai murmushi yace " it's unfair ko? To amma ya zakai, wannan itace kaddararka Abbas na kasheshi ne saboda ya kwace komai da nakeso a rayuwa, kai kuma zan kasheka ne saboda kana neman rabani da abinda ya zama mallakina."

Ashraf zai sake magana kawu yace " kaje kai lokacinka yayi mu ba yanzu ba."

Yana kaiwa nan ya kashe wayar.

Dariya ya karayi sannan ya fito daga bangarensa ya goge last call din dayai ya kaima little yace " Little wayar Nafin ma shiru, na kasa samunsu duka."

Little tace " insun kira zan kawoma Abba."

Yace "yauwa my Little sannan yai gaba."

***********


Ashraf kam suna gama waya da kawo ya kalli wayarsa sannan yai wani murmushi tare da kiran Kb, yace "kuyi sauri."

Nan kb ya amsa da to.

Ashraf nan ya shiga tuno abinda ya faru.

A safiyar yau ne ya samu Little da kansa har bangarensu.

Ya kalleta yace " duk sanda Kawu yace ki bashi wayarki karkiyi musu ki mikamai sannan karki tambayeshi me zaiyi dashi."

Ta amsa da to.

Sannan ya fito ya tafi shida Dan litti sukai gidab Salim.

A hanya ya kallu Dan Litti yace " mutumin nasan baka da tsoro sai dai abinda nake shirin yi har lafiyarmu zai taba."

Dan Litti yace " karka damu yallabai ai komenene indai har bai sabawa shari'a ba to bazan taba yima musu bama bare inkiyi."


Bayan sunga wannan sakon Ashraf ya mai murmushi kafin ya mikamai, dama Kb ya san komai.


Murmushi ya sakeyi yace " abinda nakeso kayi ka taimaken kayi cikin gaggawa Alhaji Mansir, dama burina shine kayi nufin kasheni wanda hakan zai kaimu gun 'yan sanda daga nan kuma komai zai fara fitowa dala dala."

Zafin wutar ne ya fara damunsa gashi har ya fara shigowa ciki.

Tari ya shiga yi dan hayaki sai shigamai hanci yakeyi duk ya dameshi.

Tari yake sosai wanda hakan ya kaishi ga suma.

Dakyar su Kb suka iya b'alla kofa, nan suka ciroshi akai asibiti dashi.

'yan kwana kwana dama suka kira.



Dan Litti kam ana samai ruwa a hanya ya farka, sai dai gefen kansa sai jini yake yi.

Sun isa asibiti da sauri akai emergency dasu.

Dan litti aka mai dinki shi kuma Ashraf har drip aka samai.


Nan Kb ya kira shugabansu na gun aiki ya sanar dashi ga report nan ankawo musu anyi anyi attempting din kashe wani.

Nan shugaban yace "yanzu zai turo Team dinsa su dau case din."


*#ASHRAFEENAH TEAM*


*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡



*85*



Bayan Ashraf ya farfado 'yan sanda suka zagayeshi aka fara mai tambayoyi, hankalinsa akwance yake amsawa nan ya sanar dasu akan sako kanwarsa tamai ya kuma nuna musu sakon.

Nan suka bukaci anuna musu kanwar.

Ya sanar dasu tana gida.

Kb ya jasu suka nufi gidan.

********

A bangaren Kawu kam tunda wadanda yasa aiki suka sanar dashi cewa 'yan sanda sunzo hankalinsa yai kololuwa gun tashi, ya kasa zaune ya kasa tsaye tsoro da fargaba duk sun dameshi.

'yan sanda sun shigo nan suka tsaya daga waje suka umarci a kira musu Little.

Ba'a dade ba sai gatannan, tsoro duk ya kamata, me zaisa 'yan sanda su nemeta.

Bayan ta iso ogan cikinsu ya kalleta fuskarnan a hade rike da littafi yace "Ke kika turama Yayanki sako akan kina san ganinsa?"

Cikin mamaki tace " a'a."

Yace " ina wayarki?"

Hankalinta a kwance ta mikamai, ya duba wayar babu sakon, ya kalleta yace " ki tuna sosai ina kika ajiye wayarki? Ko kuma wa kika ba?"

Tace " ni ban ajiyeta a ko ina ba, mahaifina dai ya amsh wayar dazu."

Kallan juna sukai, yace " mahaifin naki yana nan?"

Tace " eh."

Yace " kira mana shi."

Nan ta tafi bangaren Abba.

Yana zaune duk hankalinsa a tashe yaji kwankwasa kofa.

Hankali a tashe ya bud'e kofar.

Little ta kalleshi tace " Abba ana nemanka."

Yace " su waye?"

Tace " yan sanda ne, ni kaina bansan me ke faruwa ba."

Cikin tashin hankali yace " me kika ce musu?"

Tace " tambaya ta sukai a ina na ajiye wayata ko wa naba shine nace kai naba kawai."

Hankali Kawu ya kara tashi cikin fada ya kalleta yace " bakida hankaline??me yasa zakice ni kika ba? Ko kema kin hada baki da yayanki ne???"

Cikin mamaki tace " me ya faru?"

Tureta yai ya wuce cikin takaici yana tunanin me zaice? In ya gudu kuma tabbas yasan zasuyi zargin wani abu.


Fitowa yai ya isa gunsu, tare da mikamusu hannu alamar gaisawa.

Bayan sun gaisa wannan officer din na dazu ya kalli Mansir yace " bincike mukazo yi."

Mansir ya kalleshi, Officer yace " kaine ka amsh wayar 'yarka wato Maryam dazu?"

Kawu ya danne tsoro yace " nine, amma menene dan uba ya amshi wayar 'yarsa?"

Officer ya kuramai ido kafin yace " kaine ka turama Ashraf sako ta wayar?"

Kawu yai alamar mamaki yace " ban gane in turama Ashraf sako ba? Akan me zanyi hakan?"

Officer yace " zaka biyomin office da kai da 'yarka dan tsananta bincike."

Kawu zai yi magana officer din yace " in har kana san kar a zargeka kenan, in kuma har da abinda kake b'oyewa to."

Kawu yace " muje, bari na canza kaya."

Nan ya koma bangarensa, ya canza kaya cikin tsananin firgice, tsoro ne fal a cikin zuciyarsa, nan suka taho da Little suka shiga mota suka bisu a baya.


Ashraf kam ya ware sai dai yaki yarda a sallameshi, sun hada baki da likitan akan yace har yanzu bashida lafiya.

Su Little zaune a station duk tayi tsuru tsuru, shikansa Officer din yasan ba ita bace dan dai ya zama dole ne ayi tambayar nan da ita.

Wayarta ta karba ta kira Habib.

Ta dade tana ringing kafin ya daga, tace " yaya kana ina?"

Yace " ina gida ya akai?"

Tace " dan Allah kazo ina police station tsoro nakeji."

Mikewa yai daga kwanciyar da yake cikin rikecewa yace " ban gane ba me kikeyi acan?"

Alama aka mata akan ta miko wayar hakan yasa tai saurin mai kwatance ta mika musu.

Kan kace me sai ga habib ya danno mota a guje da gudu ya shigo cikin station din, sam bai kula da Kawu ba gunta ya nufa da saurinsa ya rike hannayenta yace " Little are u alright?"

Kai ta girgiza mai hawaye suka zubo mata tace " yaya ka kira ya Ashraf kaji ko yana lafiya naji ance yana asibiti."

Cikin mamaki yace " asibiti kuma?"

Kai ta d'aga mai, zaiyi magana suka hada ido da Kawu, wani irin kalli yamai cikin takaici baisan sanda yace " ka gama lalata rayuwar wasu yanzu ta 'yarka kake san lalatawa?"

Cikin mamaki Little ta kalleshi, kawu ma kallan mamaki yake mai.

Habib ya dauke kai sannan ya matsa gun officer dan jin abinda ke faruwa.

Sosai officer yamai bayani, ran Habib ya baci cikin fada yace " Ai ba sai kunyi wani bincike akan wannan baiwar Allahr ba tayayya ma yarinya karama zatai tunanin yin haka? Sannan yayanta ne fa ubansu d'aya banda yanda suke tsananin san juna, shi kuma waccan mahaifinta ne sai dai im shine."

Little cikin mamaki ta kalli Habib tace " Yaya ya zaka ce Abba ne? Mai zaisa Abba ya cutar da Yaya?"

Habib bai amsa mata ba ya kalli Officer.

Kawu kam ya ma rasa mai zaice, aransa yace "like father like son dukansu sai zuciya basu iya controlling din fishinsu ba sam.

Sai yamma wanda yaje bincike ya dawo dauke da doguwar takarda, duk abinda ya faru a wayarta ne da wanda aka kira da time din kiran da kuma texts.

Kawu kam yana zaune ne kawai.

Bayan an kawu ne aka ga tabbas an kira Ashraf bayan kuma texts da akamai.

Mamaki ya kama Little duk da Yaya ne yace taba Abbanta wayarta inya tambayeta bata kawo komai a ranta ba.

Officer ya kalli Little yace " me zaki iya cewa gameda sako da kuma waya da akai da layinki?"


Abbanta ta kalla sannan ta daure tace " nidai wlh ban kira Yaya ba."
Officer yace " mahaifinki fa?"

Tace " shima nasan bai kira yaya ba, saboda me zaisa ya kira yaya a wayata bayan ga wayarsa? In ma ya kira wani to sai dai in Nafisa ya kira."

Officer yai murmushi yace " hakane abinda kika fada me zaisa ya kira yayanki a wayarki bayan ga wayarsa? Wannan itace kalma ta farko da take bukatar bincike."

Kawu kam gabansa sai faduwa kawai yakeyi.

Officer yace " kuje gida zamuyi bincike zuwa gobe."

Habib ya jata suka shiga motarsa sukai gaba.

Kawu ya shiga tashi cikin tashin hankali.


*************



Datti kam jiki ba dadi da kanshi yake bi gari gari kauye kauye kauye sai dai ba Nafi ba labarinta ba kuma Dan Litti.

Hankalin Datti ya kara tashi nan ya fara zuwa gun malamai akan amai addu'a akan yarsa ta fito.


Sai dai haryanzu ba labari, Datti duk ya canza magana ma ba damunsa tai ba, ba dukiya, ba 'yarsa dama wadancan sun gudu, duk ya zama abin tausayi.


*#ASHRAFEENAH TEAM*

*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡


*SECOND TO THE LAST PAGE*

*ILYSM MY FANS*


*86*


Yau kwanan Ashraf uku a asibiti, 'yan sanda sune suke tsaron d'akinsa sai dai duk abinda ke faruwa Dan Litti na kawo mai rahoto, Little kam tayi kuka sosau ganin yayanta cikin wannan hali, haka ma Anisa, duk yanda taso akan ya barta ta zauna agunsa yaki sai ce mata yai ai Umma ma ba lafiya gareta ba kuma tana bukatar ta.

Umma kam neman yanda zata fito da Asim kawai takeyi, sai dai duk inda taje ta nemi taimako akaji wannan uban kudin sai kaga kowa yana dauke kai.


Yau da kanta ta shirya tazo gun Ashraf, bayan sun gaisa ta kalleshi tace " Ashraf in har nai abinda kace zakasa a saki d'ana?"

Ashraf yace " zan biya kudin da ake binsa zai kuma yi bailing sa "

Tace " naji yaushe kakeso in fada?"

Murmushi ya mata yace " zan sanae dake lokacin."

Cikin damuwa tace " Yaushe to zaka sa a fito da Asim din?"

Yace " karki damu saboda ankusa a cikin satin nan ne insha Allah."

Nan ta fito tai gida.


Dady shima yazo, kuka sosai yai agaban Ashraf magana d'aya yake cewa "Ashraf ka yafemin, kalmar da kawai yake fada kenan."

Ashraf ya kalleshi yace " karka damu Dady ko ma menene na yafema."


Yau 'yan sanda suka isa company din da Kawu yake, shi kam a wannan lokacin nema yake ya tattara komai na company din ya gudu, bai taba tunanin za'a zagayo kansa da wuri haka ba.

Yana zaune a office suka iso, ID dinsu ogan ya fito dashi yace " u are under arrest."

Kawu ya daure yace " akan me kenan?"

Officer

2 Comments On ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA
avatar
sadiyayunusa

1 year ago

Reply

Inaso sosai

avatar
khadija-murtala

17 days ago

Reply

Yayi dadi sosae

Please Login or Register in order to submit comment