Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

D'agowa tai ta kalleshi idanunta suka ciciko tace " rashin yarda dani ne yasa baka sanar dani ba?"

Kai ya girgiza mata alamar a'a yace " Duk duniya kece mace ta farko dana yarda da ita 100% banaji dar a kanki, sai dai ina tsoron abinda ke zuciya."

Kallan mamaki tamai tace " kamar ya?"

Yace " in har kikasan ba da gaske nake ba, bazaki taba nuna jin haushin ki da kishinki ba yanda zasu aminta ba."

Ta dan maka mai harara tace " shine nima kai using da feelings dina?"

Sumbatar lebenta yai fuskarsa da daf da tata yace " do u think it's easy?"

Murmushi tai, tace " amma duk da haka ka wahalar dani."

Sumbatar idanunta yai yace "am sry Baby, na wahalar dake ni kaina na sani, shi yasa nace zan amshi punishment dina."
Ta sake murmushi tace " maganar tafiya fa?"

Yace " Yanzu it's eye for eye, thooth for thooth, we are in a war ni da kawu i am afraid kar wani abu ya samarmin ke ta dalilin revenge dina."

Baki ta turo tace " Amma......"

Hannu yasa ya toshe mata bakinta yace " Baby please."

Idanunta ta rufe sannan a hankalu ta bude jiki a sayaye ta daga kai alamar to."

Mikewa yai ya dauketa yai toilet da ita.

Sai daya cika musu bahon wankan sannan ya sa kayan kamshi na ruwa sannan ya sata a ciki shima ya shiga.


Ta kalleshi tace " Allah baiyi zan tsaya bikin Jibiya, thanks to someone."

Idanu ya kankance yace "someone? Do u mean me?"

Ta dan murguda baki tace " nidai ban fadi suna ba."

Kallanta ya tsaya yi, ta debi ruwa a hannunra ta watsa mai tace " yallabai kallan fa?"

Dariya yai yace " fada kikeso?"

Ta tsuke baki, shima hannu yasa duka biyu ya riga watsa mata ruwa, nan itama ta dage tana watsa mai, dariya sosai suke yi wanda kana ganinsu kasan suna cikin tsananin kaunar juna.

Bayan sun gama wanka, ta jawo towel d'aya ta rufa sannan tace " na fita."

Kallanta yai yace " nifa?"

Tamai gwallo tace " ka dauka da kanka."

Tai d'akinsa tare da zama kan gado tana dariya.


Ashraf ya fito yana zuwa ya sa hannu a gugunta ya matse da karfi, wanda ya sa ta saku kara yace " ni kika ki daukoma towel?"

Tana ihu da dariya tace " sry Yayana na tuba na daina."

Yace " inaa baki dainaba sai na hukuntaki tukun na."

Ganin yaki saketa yasa tace " Yaya Nisa?"

D'agowa yai da sauri ta mike da gudu tana dariya.

Murmushi yai sannan ya mike sambal akan gado tare da rufe idansa.

Ahhh na kosa in gama wannan case din in ganni tare da matata kullum.

Abinda yake fada kenan a ransa.




*#ASHRAFEENAH TEAM*
[8/28, 19:57] Umar Dalha: *ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

*Gareku yan gro din World of Hausa Novel, Mumbari M.Jabo, Maryam mai dala grp na gode kwarai da yanda kuke san littafin nan. ILYSM😍*

*81*


Washegari da safe bayan Kawu ya fita, Dan Litti yazo ya dauki Mumy da Nafi yai abuja dasu dan tacan zasu tashi gobe.

Little kam taji takaici sai dai Nafi tace mata ai ita saboda makaranta, tunda su sai nan da 1mnt akace list dinsu ma zai fito.


Ashraf sai dayaga tafiyarsu sannan ya kira Kb yace " a ina kace an samu Dan Siyasan?"

Kb yace " yana nan asibitin Murtala ashe bashida lafiya ne shiyasa akaita nemansa aka rasa."
Ashraf yai murmushi sannan yace " ganinan zuwa ka turon ward din da yake da number d'akinsa."

Nan take Kb yamai Text Ashraf yaja mota yai gaba.

Bayan ya isa asibitin ne ya tafi ward din masu cancer sannan ya duba number d'akin.

Knocking yai nan akace ya shiga, a hankali ya tura kofar d'akin, wani ne a kwance jikin nan duk ya rame kamar me kanjamau sannan ga wani matashi a kusa dashi a zaune.

Jiki a sanyaye Ashraf ya shiga tare da karasawa bakin gadon.

Matashin wanda baifi shi ba yace " ban gane ba?"

Ashraf yai murmushi sannan ya dauko complimentary card dinsa ya mika mai yace " sunana Ashraf."

Kallansa yai, wanda hakan yasa Ashraf yace " ba Dan siyasan dayai House of rep bane da?"

Matashin yace " shine."

Ashraf ya kalli mara lafiyan yace " Alhaji Uba ka san Mansir?"

Kallan Ashraf yai fuskarsa dauke da alamar tambaya, Ashraf yace, " Mansir kanin Abbas marigayi mai A&A Food. Ltd?"

Haryanzu dai bai fahimta ba sai dai ya maimaita kalmar A&A?"

Ashraf yace " eh wanda yake auren kanwar Hisham."

Jin sunan Hisham yasa ya fara kokarin mekewa zaune, hakan yasa d'ansa ya taimakamai ya zauna, kallan Ashraf yai yace " ina Hisham? Ka taimaka ka kiramin shi."


Ashraf yace " baya kasar ne yanzu haka ma shiya turoni nadubaka, baisan baka da lafiya ba."


Hannun Ashraf ya kama guda d'aya wanda Ashraf ya dana start da d'ayan hannunsa a wayarsa dake aljihunsa.

Mutumin yace " Yaro ka ba Hisham hakuri, a zahirin gaskiya nayi laifuka da dama a rayuwata ta duniyar nan, wasu na nemi yafiya wasu kuma banma san inda mutanen dana cuta suke ba, na hau mulki, dadinta yasa na manta da Allah na kwashi dukiyar jama'a sannan na cuci jama'a Hisham na d'aya daga cikin mutanen da bazan taba mantawa ba saboda nine sanadin talaucewarsa."

Ashraf yai shiru tausayin mutumin ya kamashi, ita dama rayuwa haka ne, yau in kaine gove ba kai bane.

Mutumin ya cigaba, ka san kanin mijin kanwarsa?"

Ashraf ya ce "eh shine Mansir din ai.",

Mutumin yai ajiyar zuciya yace " kacema Hisham wlh wannan mutumin shine ya sani komai, shawara yazomin da ita ta neman kudi, nikuma alokacin idona ya rufe, zuciyata ta zarme ina ganin zan samu kudi mai yawa da xai sa inyi campaign ba tare da matsala ba, shi yasa na dauki shawararsa, sai dai dalilina yasa aka kama dukiyarsu mai yawa har hakan yakai ga ajalin mahaifinsa, wanda tsoro yasa nakasa fadar abinda ya faru a lokacin, ina tsoron kar nima azal ta fadamin."



Kuka ne yaci karfin mutumin ya shiga yin tari a hankali,yace " yanzu gashinan kowa ya gujeni, wannan yaron shi kadai ke taimaka ta, shi kuma ba jinina bane rikonsa nai, nawa 'yayan duk sun gudu sun barni."

Idanun Ashraf ne ya ciciko, yasa stop sannan yace "amma wace irin cancer ce ke damunka?"

Murmushin yake yai yace " blood, anyi maganin har an gaji shiyasa nace shima yaron nan ya barni kawai a gida in kwanana yazo in tafi."

Ashraf ya kalli matashin, hawaye yaga yana gogewa, tausayi ya kara kamashi, ya kalleshi yace " ya sunanka?"

"Abdulmalik."
Ya fada
Ashraf yace " wani aiki kake?"

Yace " kasuwanci nake a kwari, inada karamin shago."

Ashraf ya kara tausaya mai, yace " aure fa?"

Yace " shekarar Alhaji 5 kenan ba lafiya ina ni ina tunanin aure?"

Ashraf yai shiru kafin daga baya yace " ka zo ka sameni a address din dake jikin katin, inada sha'awar kasuwanci inyaso sai in bude ma babban shago sai ka dinga mana."

Kallan mamaki Abdulmalik yama Ashraf, shikam Uba kuka kawai ya saka yana godiya kamar me, Ashraf yace ba komai, sannan ya ajiye musu kudi dubu 30 ya fita.

Yana fita ya runtse ido cikin tsananin tausayi yace " Rayuwa kenan."



**********


Kawu ne zaune kusa da Asim ya kalleshi yace " wlh kaji na rantsema yau itace rana ta karshe da zaka ganni anan, in har baka fadamin inda ka samu takardun nan ba."


Asim jiki a sanyaye cikin tsoro yake kallan Mahaifinsa.

Kawu yace " to shikenan, ka karashi rayuwarka anan ni dakai kuma......"


Da sauri Asim yace " Sata nai a d'akin Ashraf."


Idanu kawu ya zare cikin tsananin mamaki yace "mene?"

Nan Asim ya bashi labarin abinda ya faru.

Hannu kawu yasa cikin takaici ya wankama Asim wani wawan mari yace " bakada hankali ne? Me yasa ne nikam kwakwalwar kifi Allah ya d'orama? Kana tunanin Ashraf Shine zai ajiye takardunsa a fili? Yaron da nafi shekara 10 ina sawa a min bincike akan ma yawan dukiyar Abbas daya barmai amma sam hakab ya faskar saboda tsananin wayau da takatsantsan irin na yaron, shine kakeso kacemin ya ajiye takardu a d'akinsa?"

Asim yai shiru, Kawu ya naushi iska cikin takaici yace " kana xaune sokon banza ya kamaka cikin ruwan sanyi, kai wannan yaro nikam bansan jakantarka ba."

Waje yai da sauri cikin takaici, yana fitowa Anisa ta kirashi tace "Abba nikam Mumy tayi tafiya ne?"

Cikin fada yace " kamar ya?"

Tace " a'a naga bangarenta ansa kwado ne sannan su Afra sun koma bangaren Little shine dazu da Afra tazo tacemin ai Mumy tayi tafiya."


Cikin tashin hankali yace " ina Ruma zataje ba da sanina ba? Sannan d'azun nan fa na barta a gida."

Kashe wayae yai a zuciye ya kira wayar Mumy a kashe ya jeta, nan fa idanunsa suka kada.

Ya na kokarin saukowa daga steps din gun sai ga Ashraf.

Kallansa ya dingayi harya iso, Kawu ya kalleshi yace " ina Uwarka?"

Ashraf yai dariya yace " haba kawu wannan ai wayan zagine, kace ina matarka dai?"

Kawu ya fara huccin takaici, Ashraf yai murmushi tare da girgizamai dan yatsa yace " no no no ai bai kamata ka nuna tashin hankalinka tun yanzu ba, inkai haka u will spoil the game, it won't be fun."

Ya sake murmushi sannan yai ciki.


Wani irin ihu kawu yasa na takaici, Ashraf ya wani murmushi sannan yai ciki😏




*#ASHRAFEENAH TEAM*

💞

*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡



*82*


Kawu cikin tashin hankali yai gida, b'angaren Mumy ya nufa ko mota ma bai rufe ba, yana zuwa kuwa yaga kwado a kofar da zata sada ka da b'angaren, Ruma! Ruma! Ruma! Abinda kawai yake fada kenan cikin tsananin tashin hankali, kofar ya taba tare da rike kwadan.

Ya dade a haka kafin ya koma na sa bangaren cikin takaici, ba shakka dolene ya nemo Ruma dan kuwa in har bai ganta na kwana biyu ba bayaji hankalinsa zai kwanta, a iya saninsa mutane kan ce in har ka auri mutum ka zauna dashi na shekaru to fa soyayya na gushewa sai dai zaman hakuri da na 'ya'ya, shikam a yanda yakejin zuciyarsa gaskiya bai yarda da hakan ba, kaunar Ruma da yakeyi bayaji ko tsufa yai da ita zai daina santa.


Ashraf kam gun Kb ya shiga Kb yace " kaje kuwa?"

Ashraf yace " naje sai dai abin ba dadi."

Ganin bayasan maganar yasa Kb yace " yanzu mutuminka ya fita."

Ashraf yadan yi tsaki kadan yace " na ganshi, ya waccan fa?"

Ya fada yana kallan inda aka killace Asim."

Kb yace " yanacan."

Ashraf ya kalli Kb yace " bari inje inada abinyi."

Nan ya fito, baiga kawu ba hakan yasa yai murmushin mugunta yace " ko kaifa, dan banaso ka badani."

"**********

Kawu kuwa gida ya taho da gudun gaske yana zuwa ya ajiye mota ya fito, ko kofar bai rufe ba saboda tsananin firgici, bangaren Mumy ya nufa, kwado kuwa ya gani daga kofar da zata sadaka da bangarenta, kofar ya shiga jijigawa cikin wani irin kunar rai, ba shakka bazai taba yarda a dauke mai Rumansa ba, shifa a iya saninsa yaji ance in har mace da namiji sukai aure na wasu dan shekaru to fa soyayyarsu na tafiya sai dai kimma da hakuri yasa zama ya d'ore, sai dai shikam abin ba haka yake ba, yanaji dole ne ya zauna da Ruma ko ya samu nutsuwa, kofar ya dinga jijigawa, ganin ba yanda zaiyi yasa yai b'angarensa cikin tashin hankali.

Waya ya dauka ya dinga kiran layinta sai dai duk a kashe, tashin hankali kam ya shigeshi a wannan ranar.

********

A can bangarensu Nafi kuwa, sun isa Abuja lafiya, sai dai tun da suka sauka Nafi ke kwara amai, gashi sam ta kasa cin komai, Mumy cikin damuwa tace " Nafi anya kuwa ayi tafiyarnan dubifa yanda kiketa amai."

Murmushin yake Nafi tai tace " Mumy karki damu, tafiyar mota ce kawai ta sani haka, kinsan mu filanuwa akwai mu da hararwar mota."

Mumy ta gamsu da zancen Nafi, a haka har suka kwanta bacci.

Da safe kuwa jirginsu ya d'aga.

Sai kasa mai tsarki.



***********


Shikam Ashraf da safe bayan ya tashi ya fito daga gidan shi da Dan Litti, wata envelope ya mikama Dan Litti yace " yaje gidan Dady kawai ya ba mai gadi yace a bashi, ya juyo karya bari Habib ko wani daga cikin gidan ya ganshi."

Dan Litti ya amsa da to, sannan ya ja mota yai gaba, yana zuwa kofar gidan kuwa yai sa'a ba kowa a gun sai mai gadi, hakan yasa ya mai horn, mai gadi ya taso da sauri, Dan Litti ya kwama sunglasses tare da kallansa ya mikamai envelope din nan yace " kaga mai gidan."

Mai gadi ya amsa yana kokarin tambayarsa inji wa, yaga Dan litti ya ja mota yai gaba.

Cikin rashin kulawa ya koma ciki ya nufi ban garen Dady, Dady lokacin yana kishingide a falo abin duniya duk ya taru yamai yawa yaji kwankwasa kofa, nan yace a Shigo.

Mai gadi ya shiga a hankali ya gaidashi tare da mikamai sakon, Dady yace " inji wa kenan?"

Mai gadi ya dan sosa keya yace " wlh ni kaina ban sani ba."

Dady ya sallameshi sannan ya bude wannan envelope din wata karamar Mp3 ce ta fado tare da yar karamai takarda.

Fuskarsa dauke da mamaki ya sa earphone din a kunnensa tare da danna play.

Kallo d'aya zakamai kasan yana cikin tsananin tashin hankali da jin abinda ake fada, mikewa yai tsaye cikin tashin hankali idanunsa suka kada sukai jaa, mamaki tare da firgice ne suka kamashi, takardar ya sunkuya ya dauka a kasa bayan ya gamajin sharhi daga bakin Alhaji Uba, address ne kawai rubuce a jiki na asibiti tare da number d'aki.

Makullin mota kawai ya dauka ya fito da sauri tare da fadawa cikin motarsa, ya ja ta da gudu yai waje.


Bai tsaya a ko ina ba sai asibitin Nassarawa.

Nan yabi address har zuwa inda ya isa number d'akin, jikinsa ne yai sanyi ya kasa bude dakin, ba shakka in har abinda yaji gaskiya ne shikam rayuwarsa ta kare, kenan ya zalinci Abbas akan hakkin da ba ruwansa, kenan duk yanda ya dauki Mansir ashe shi ne babban soko yana zaune ana amfani dashi.

Dashi Mansir yai amfani yai achieving din duk abinda yakeso a duniya.


Yana tsaye rike da kofar yaji an bude kofar daga ciki, wata nurse ce ta fito, kallansa tai ta gaisheshi sannan tai gaba.

Kofar a bude take hakan yasa daga waje yana kallan Uba wanda ke kwance duk ya tsome, shikanshi Uban kallansa yake dan tabbas bazai iya manta fuskar Hisham ba.


A hankali Hisham ya fara takawa zuwa ciki har ya isa kusa da gadon ya kalli Uba zaiyi magana Uba yai saurin katseshi da cewa " Hisham na gode da ka ziyarceni kafin rayuwata ta kare, ka yafemin abinda ya faru."
Dady kallansa yai cikin wani yanayi yace " me nakeji game da Mansir....."

Uba ya kamo hannunsa hakan yasa Dady ya zauna kusa dashi, Uba ya kara zayyanamai komai daya faru tare da doramai " nayi babban laifi, sai dai ba'a maida hannun agogo baya, Ka yafemin Hisham."


Hankalin Dady yayi mugun tashi, ya mike jiki a sanyaye ba tare da yace komai ba yai waje.

Tafiya yake kamar mara laka a jiki, har ya isa motarsa, ya shiga ciki ya zauna tare da dora kansa akan sityarin motar, me na aikata?

Abinda zuciyarsa ke tambayarsa kenan, waya ya dauka dan kiran kanwarsa, sai dai a kashe ya jita, haka nan ya tada mota cikin karyewar zuciya yai gidansa.

Yanzu kam ya gane komai daya faru dama trap ne da Mansir ya shirya.


*********



Ashraf bayan ya ga Dady ya koma gida dan yana biye dashi shima ya nufi gun aiki."


Bayan azahar suka shiga meeting, sai 4 suka fito, sun fito dukansu Kawu na tsakiyar mutane suka dan tattaunawa, Hisham ya karaso gun.

Hisham nada tsananin zuciya wanda duk itace tasashi yin abubuwan da suka faru a baya, sam ransa ya gama b'aci baima kula da mutanen dake tsatsaye a gun ba, ya karaso gun Kawu.

Cikin tsananin mamaki kawu ya kalleshi yace " Yaya ya......."


Mari yaji an tsinkamai nan fa kowa ya kallesu, kawu mamaki ya kamashi, ya rike gun yace " Hisham ba kada hankali ne?"

Dady yai wani murmushin takaici yace " au yanzu dakaji mari ka manta da yayan?"

Kawu ya kalli mutanen dake gun ciki kuwa harda Ashraf wanda takaici ya kara kamashi, ya daure yace " yaya muje office dina da alama ranka ne a b'ace."

Dady sai a lokacin ya kula da mutanen gun, suka hada ido da Ashraf, nan sukai office din Kawu.

Ashraf yai murmushi yace " Whoa lalai Dady ba sauki."

Nan yai nashi office din hankalinsa a kwance.

Kawu kam suna shiga yasa key ya kalli Dady yace " Yaya meye hakan.....?"

Idanun Hisham sunyi jaa na takaici yace meye hakan?

Dady yace " wai me......"

Jiyai Hisham ya karamai wani marin, dady ya fusata yace " malam meye hakan?"

Dady yace " waccan marin na farko na rainamin hankali dakai ne, wannan kuma na takaicin hada zuri'ata dakai danai ne."

Kawu ya hada rai yace " wannan wani irin banzan zance kake? Mu bayara ba ba komai ba?"

Hisham ya nuna Kawu da dan yatsa cikin kunar rai yace " wlh kaji na rantse maka bazan yafe ma rainin hankalin daka min ba, ba zan yafema sanadin mahaifina dakai ba, bakuma zan yafema amfani dani dakai ba ka auri kanwata, ba kuma zan yafema na amfani dani dakai ba wajan kashe Abbas ba."

Kawu kallan Hisham kawai yake, sai yanzu ya fara gane inda zancensa ya nufa, cikin rashin damuwa Kawu yace " ni ban fahimceka ba."

Hisham yace " naji komai daga Alhaji Uba, munafikin banza da wofi, wlh Mansir nayi danasanin saninka a rayuwa, kai kani ne ga Abbas sai dai ko kadan halayenku ba iri daya bane, shiyasa a koda yaushe kake losing akansa, dukiyar da kake takama da ita ficika ba kai ne kai wahalarta ba, tarawa akai ka kwaceta karfi da yaji, matar da kake takama da ita, ba sanka take ba, ita ma karfi da yaji ka kwace ta, ko da wasa bazaka taba zama Abbas ba duk wannan abun daka kwata kuwa."

Idanun Kawu suka rikide babban takaicinsa a duniya ace mai daga dukiyarsa har matarsa ba nash bane, wani irin abu ya fara da fuskarsa, hannu yasa ya shake Dady.

Cikin wani mugun yanayi yace " karyane, komai nawane, uban waye ya isa yace dukiya da Ruma ba nawa bane?"

Hisham da kyar ya fizge hannun Mansir, cikin tsananin mamaki ya kalleshi yace " kana tunanin wannan abun da kakeyi shi zai sa su zama naka? Ruma da kake tunanin wai hakan santa kakeyi yanzu na fahimci obsession ne ke damunka, lalai kana cikin gararin rayuwa, kuma wlh ka gaggauta ba kanwata takardarta."

Yana kaiwa nan yai waje.

Wani irin ihu Kawu ya saki yana cewa " waye ya isa yace ba nawa bane?"

Ya dade a haka kafin hankalinsa ya dawo jikinsa, nan fa ya shiga tunani uban waye ya sanarma Dady abinda yake a b'oye?"

Fitowa yai ya nufi office din Ashraf.



*#ASHRAFEENAH TEAM*

💞


*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡



*83*


Kofar ya bude ba tare da kwankwasawa ko sallama ba, a zaune yaga Ashraf yana aiki yana kuma kurban tea dake gefensa, kana ganinsa kasan hankalinsa a kwance yake, jin yanda aka bude kofar ne yasa ya kalli gun, ganin kawu ne yasa ya sakar mai murmushi tare da dagamai hannu yace " Hi!"

Ran Kawu ya kara b'aci matsowa yai gunsa ya kuramai ido.

Ashraf ya kalleshi cikin rainin hankali yace "ya akai? Ko shayin zan hada ma?"

Kawu yanasan ya tambayeshi ko shine ya fadama Hisham sai dai yana tsoron karya buloma kansa aiki, yaje haka kawai Ashraf din bai san komai ba ya sanar dashi.

Daurewa yai ya juya, har ya kai tsakiyar gun yaji Ashraf yace " Ba tambaya kazo kayi ba?"

Kawu ya tsaya cak tare da juyowa ya kalleshi, Ashraf ya mike tare da matsowa inda kawu yake cikin gadara, ya dan tafa hannayensa biyu a hankali yace " Ohhhh kana tsoron kar inji?"

Kawu ya buga mai wani kallo, Ashraf ya dan rike kunne yace " sry kanin Abba, sai dai ya zamuyi? Da alama Dady fa yasan komai."

Idanu kawu ya zaro cikin rawar murya yace " kai kai ne ka....."


Dariya Ashraf yasa yace "kawu meye hakan? Kar ka badani mana, ya muryarka zatai rawa daga nan?"

Kawu ya daure ya nuna Ashraf da yatsa yace " Ashraf wannan shine last warning dina akanka, ka shiga hankalinka dani, kada kai tunanin komai yana tafiya yanda kakeso kai tunani kaci riba akaina, wlh kayi min kadan, tsohon ka ma bai isa yaja dani ba bare kai da aka haifeka a gabana."


Hannu Ashraf yasa ya kankame jikinsa yace " Ahh so Scary!!"

Kawu ransa ya kara baci yace " ina tausaya ma dan wlh......."

Ashraf ya hade hannayensa biyu yace " plzz na rokeka kar ka tausayamin dan Allah, Dan Allah na rokeka kana kwafsamin in naji zancen tausaya war nan."


Zuciyar kawu ta cika taf da takaici, a zuciye yai hanyar fita, Ashraf yace " ka tabbatar kanacin abinci mai kyau kafin ka shiga prison dan naji labarin abincin can ba dadi."

A zuciye kawu ya bankade kofa yai waje.

Yana fita ya kara kallan kofar cikin takaici yai kwafa yace " in ni banje ba kai ka ziyarci kabarin ka ai."


Daga ciki kuwa yana fita Ashraf ya furzar da wata iska tare da zama akan kujera Ya kira Uncle Salim.


**********


Su Nafi an isa kasa mai tsarki sai dai Nafi kam jiki yaki dadi sam, haka suka shiga d'akin da aka basu a kasar madina ita kam duk ta gama fadawa.

Mumy cikin kulawa tace " Nafi ya kamata muje asibiti nikam naga hararwan nan ta isa ga ba abinci kike ci ba."

Nafi ta dago tace " Mumy Allah in na huta nasan komai zai tafi."

Kallanta Mumy tai tace "kinga yanda kika rame kuwa?"

Nafi tai murmushi tace " Allah ba komai Mumy."

Shiru Mumy tai jikinta yai sanyi.

Nafi kam gata dai a kasa mai tsarki garin da take masifar san gani amma gashi tazo a kwance ba lafiya.



**************


Da yamma Ashraf ya koma gida, yana fitowa daga mota

2 Comments On ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA
avatar
sadiyayunusa

1 year ago

Reply

Inaso sosai

avatar
khadija-murtala

17 days ago

Reply

Yayi dadi sosae

Please Login or Register in order to submit comment