Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah yasa ba inda yake tunani zasu ba.

Tsoronshi ya kara daduwa ne sanda yaga anyi kwanar gidan, idanu ya runtse cikin tsananin tsoro, Dan litti yai Parking sannan ya kalli Ashraf yace " Mun Iso."

A hankali Ashraf ya bud'e idanunsa gabansa ne ya yanke ya fadi, da sauri ya fito daga mota yana girgiza kai alamar ba haka bane, ya kalli Dan litti yace " ka tabbatar nan yazo?"

Kai dan litti ya d'aga alamar haka ne, Ashraf ya dafa kansa cikin tsananin tsoro can wata zuciyar tace " mayb baiga sakonka ba."

Jiyai ance " Buddy."

Da sauri ya juya Habib ya gani ya fito daga gidan da saurinshi, yana karasowa ya rungumeshi yace " Ayya Aminina da alama jikinka ne ya baka na dawo ko?"

Ashraf ya d'an yi yake yace " lalai kasha hanya."

Habib yace "sosai ma, dan ma naje naga gimbiya."

Kallan mamaki Ashraf yamai,Habib ya katseshi da cewa " muje ciki ku gaisa da Dady kasan yace sam baka zuwa gunsa, gashi kullum sai ya tambayeni kai."

Ashraf yai murmushi sannan yace " muje to."

Jikin Ashraf kamar wanda aka zubama ruwa haka yake tafiya, sunje shiga ya kalli Habib yace " dama Dady da Kawu suna shiri??"

Habib ya dafashi yace " me kake fada, ka manta Dady baya shiri da Kawu har bayan auren Mumy."

Ashraf a ransa yace "then y??????"


Jansa Habib yai suka shiga ciki.

Dady na zaune yana karanta jarida yana ganin Ashraf ya mike cikin tsananin farin ciki yace " wa nake gani kamar d'ana da baya nemana???"

Ashraf yai murmushi ya karasa gunsa yace " Dady na sameku lafiya?"

Dady ya zauna tare da nuna ma Ashraf kusa dashi ya zauna, Ashraf ya girgiza kai sannan ya zauna a kasa wajen kafarsa yace " Dady ina wuni?"

Dady ya dafashi yace " Ashraf nida d'ana amma ganinsa ya min wuya?"

Ashraf yai murmushi sai dai a ransa yana kara kallan Dady da tunani kala kala dake yawo a ransa, can yace " Dady kasan aikin namu ne sai a slow."

Dady yai murmushi yace " to ya za'ayi dama komai sai hakuri."

Habib dake zaune yace " wato Dady kaga Ashraf ka manta dani ko? Dama kullum tambayar ka ya Ashraf yake? Wani aiki yakeyi yanzu? Me yakeyi? Wa da wa ya hadu da d......."

Da sauri Dady ya katseshi da dariya yace " kai kuwa ba dole inji halin da dana yake ciki ba?"
Ashraf yai murmushi a ransa yace " shiyasa kake barin Habib ke zuwa kwana akai akai saboda kasan me nakeyi???sai dai akan me? "


Nima nace lalai fa akan me kenan? Soyayyace ta 'yan uwa ko akwai wani b'oyayyen al'amari a kasa????



Hmmmmmmm



*#ASHRAFEENAH TEAM*
💞

*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡




*My Kawa Bilyn Abdul wannan shafin sadaukarwa ce gareki, Allah ya kara kareki a duk inda kike* Ameen.





*60*


Nan Dady yai ta jansa da hira shima yana biyemai kafin daga bisani yamai sallama, Habib yace "muje ka gaida Mum."

Ashraf ya dafashi yace " next time kanina."

Murmushi sukai a tare Ashraf ya kira Dan Litti suka dau hanya, suna hawa kan titi dan litti ya kalli Ashraf yace " Ashe ma kasan 'yan gidan."

Ashraf yai murmushin takaici yace " Gidan yayan mahaifiyata ne "

Dan litti yasa dariya yace " ohh shiyasa yazo nan?"

Murmushi kawai Ashraf yai ya bud'e window tare da kurama titi ido, suna isa gida ya fito jiki a sanyaye yai b'angarensa.

Nafi kam harta gaji da jiran dawowarsa gashi ta mai abinci, ganin anyi sallar isha'i yasa tai tunanin dubawa ko ya dawo.

Da yake yanzu tanada makulli bayan ta kwankwasa taji shiru sai ta bud'e kofar, duk wutan bangaren a kashe yake da alama ba mutum a ciki, ta d'an d'aga gira tare da yin ajiyar zuciya tace " bai dawo ba."

Tayi nufin juyawa sai taji ringing din waya, ita kuma ba tata bace dan tata na gida, cikin tsoro ta fara yin sanda tana bin inda takejin karar gashi a bin mamaki ba'a d'aga wayar ba.

D'akinsa taji karar na fitowa a hankali ta murd'a tare da yin addu'oi a ranta, kwan wuta ta kuna da sauri tana tsoron kafin a maketa gwara taga waye.


A binda ta gani ne yasa gaba d'aya jikinta ya mutu, tsayawa tai cak tana kallan Ashraf wanda ke zaune a kasa ya hada kai da gwiwa, ga kuma wayarsa nan a hanunsa yanaji ana kira bai dauka ba, sai dai ta kula ba wayarsa bace da yake amfani da ita.

Ganin haske ya kewaye d'akin ne yasa ya d'ago ya kalleta da idanunsa wadanda sukai jaa, a hankali yace " Nafisa can u please get out?"

Kallansa tai cikin tsananin mamakin halin data ganshi cikin rawar murya tace " Ya Ashraf?"

Idanu ya runtse yace " please can u get out, banasan ki ganni cikin wannan halin....." ya karasa maganar cikin wata irin murya, sakon da aka turo mai yana kokarin bud'e kofa ne yasashi cikin wannan halin.

Kawu ne yai reply kamar haka "Max na d'auka kunyi da Yaya akan bazaka kara nemana ba? To shi yace kaje yana nemanka." wannan sako ya d'agama Ashraf hankali, a iya saninsa Kawu mahaifin Habib kawai yake cema Yaya, sai dai tayaya za'ace da hannun yayan mahaifiyarsa?????

Ganin bai maida reply ba yasa Kawu ke ta kiransa.

Kashe wutar Nafi tai sannan a hankali ta taka zuwa inda yake, ta tsugunna tare da rungumoshi jikinta, idanunta sun cika taf da kwalla tun da take bata taba ganin Ashraf a irin wannan yanayin ba, hawaye ne ya ziraro mata a hankali tace " taya zan iya tafiya na barka cikin wannan yanayin?"

Ashraf ya d'an zare jikinsa kadan yace " Nafisa please......"

Hannu tasa ta rufe bakinsa sannan ta kara kankameshi hawaye suka fara zirya a idanunta cikin kuka tace " Yaya can u please share ur burden with me? Zuciyata tana zafi idan na duba naga bansan abinda ke faruwa dakai ba, bansan a wani hali kake ciki ba, Yaya ka taimaka ka sanar dani damuwar ka dan Allah...."

Kuka take sosai wanda yasa jikinsa yin sanyi, kankameta yai sosai a hankali yaji hawaye ya gangaro ta idanunsa, yace " Nafisa ya zanyi? Ya zanyi da rayuwata, duk wanda nake tunanin yana sona sai na duba sai inga makiyi na ne, duk wanda nake tunanin yadamu dani sai in duba inga ashe amfani yake dani a b'oye, na d'auka i am smart sai dai yanzu na tabbatar i am the biggest foolish in the world, me yasa Allah ya d'auke Abbana ya barni? Meyasa....."

Kuka take sosai ta sa hannu ta toshe bakinsa tana girgiza mai kai" Yaya ka daina fadar haka, Allah na tare da kai sannan duk wanda ya zalunceka Allah bazai barshi ba ko shi wanene."

Idanu Ashraf ya runtse wasu zafafan hawaye suka zubo mai yace " me ya kaini binciken abinda ya riga ya shud'e, why???"

Nafi ta kankameshi tana girgiza kai tace " laifinane yaya ko ma menene laifina ne, please ka yafemin, da ban sanar dakai ba banaji zakai binciken nan, yaya ka yafemin Laifinane, nice na ja maka shiga wannan halin."

Ashraf ya sa hannu ya shafi bayanta yace " ba laifinki bane, na dade ina bincikena, iya kace ke taimakamin kikai, karki sake cewa laifinki ne."

Nafi shasheka kawai takeyi, bata san me ya jiyo ba amma ta tabbata abin ya shafi danginsa.

Sunyi shiru suna manne da juna cikin duhu, Ashraf can cikin wata sansanyar murya taji yace " Thank u Nafisa."

D'agowa tai cikin mamaki duk da ba haske ba ganinsa take ba sai dai mamaki karara ya bayyana a fuskarta, wannan itace rana ta farko data tabajin Ashraf yayi godiya bama ga ita ba, a'a bata tabajin yace ma wani bama.

Murmushi taji yayi ya d'an ja numfashi kadan yace " kina mamaki ko? Ni kaina rabon danaji na fadi wannan kalma ba naji zan iya tunawa."

Hannayenta tasa akan fuskarsa sannan ta hada goshinsu tace " Yaya in kamin godiya akan me kenan? Ni kuma ince me kenan, yarinyar datake yar kauye ka..........."


Hannu yasa ya d'an turo kanta bakinsa yakai cikin nata, wani irin salon soyayya suke ma juna wanda kana gani kasan son da sukema junansu lalai a bayyana yake, sun dade suna sumbatar juna kafin a hankali bakin Ashraf ya sauko kan wuyanta, wani irin yarr taji a jikinta wanda yasata yin numfashi, Ashraf sam ya manta da zancen sai ta aminta dashi, sarafata ya shiga yi sai dai itama duk da batasan kan abun ba haka kawai taji lalai tabbas tanasan ba Ashraf dinta farin cikin da yake nema.


Soyayya mai karfi suke nuna ma juna sam bata san sanda ya zuge zip din rigarta ba sai jitai yabrabata da rigarta, ba shakka tsoro da fargaba ne ke damunta sai dai bataji duk wani wahala da ake fada zata iya bijirema Ashraf.


Ya gama fita daga hayyacinsa haka itama a daidai wannan lokacin mai afkuwa ta amfku............Nikam ganin haka yasa na fito ga duhu wanda yasa ni yin tuntube da kujera😭





************



A kauye kuwa Datti yau ya dawo ya taradda matarsa Mairo ta yimasa tuwo miyar kubewa bushashiya sai dai da zabuwa akai miyar, mamaki ya kamashi ya kalleta yace "mairo badai da zab......"

Katseshi tai cikin salonta na jan hankali tace " Haba Datti bada zabuwarka bane, zabuwa ta ce data kasa na yanka mana ita."

Baki taga ya washe yace " kai Mairo Allah ya miki albarka kinsan darajar dan adam."

Nan ya yanko malmalar tuwo ya zuba nama sosai da miya ya hau ci, sai uban santi yake zubawa.

Itakam sai murmushi takemai.


Yaci yai hani'an ya tauna kasusuwa sannan ya kalleta yace " kai Mairo Allah ya barmin ke "

Tace " Amin Datti."


Ya kara washe baki yace "rabon dana kai nama bakina har na manta sai dai in gani a kwanon wani."

Tai dan fari tace " ai banga laifinka ba, yanzu ba gashinan kafi kowa dukiyar dabobi ba duk yankin nan."

Ya sake washe baki yace " Zabina guda 20 ne kaji guda 30 banda raguna, saniyoyi da akuya."

Ta matso kusa dashi tace " yaushe za ka nunamin ne nima in gansu."

Dariya ya kwashe dashi yace " karki damu gobe da kaina zan kaiki ki gansu."

Tace to Datti Allah yabarmu tare.

Yace Amin Mairoro ta....


Nace inma Maikoko ce...Lol masu suna Mairo tuba nake🤢



*#ASHRAFEENAH*

💞

*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡




*61*


Ashraf yana fita daga gidan ya wuce gidan Uncle Salim, bayan sun gaisa ya kalli Uncle yace " Uncle tambaya nazo da ita."

Uncle yace " ina jinka, sai fatan Allah yasa na san amsarta."

Numfashi Ashraf yaja sannan yace " Kasan Auwal Max?"

Kallan mamaki Uncle yamai yace " kwarai kuwa dan driver din mahaifinka ne koda yaushe suna tare."

Ashraf yai shiru hakan yasa Uncle yace " menene?"

Ashraf yad'an numfasa sannan yace " Yana ina yanzu?"

Kai Uncle ya girgiza yace " Allahu a'alam, tun bayan hatsarin mahaifinka ban sake sashi a idona ba."

Ashraf ya kalli Uncle cikin mamaki sannan yace " shima yana cikin motar sanda abin ya faru?"

Uncle yace " kwarai kuwa, a iya sanina tare suka fita sai dai bansan ya akai ba naga mahaifinka kadai a asibiti, sai dai inaji ko shi wani asibitin aka kaishi."

Ashraf yai shiru yana tunani kafin ya mike yace " sai da safe na gode."

Bayan ya fito ya shiga mota ya jingina kansa da kujera, yana nazarin kalaman Uncle, mai zai sa Alhaji Isma'il ya fadamai sunan driver din mahaifinsa????


Ya dade yana tunani kafin yaja mota yai gaba.

Nafi kam Little ta kawo mata kaya tare da mata kallan zargi, Nafi ta harareta tace " me kike tunani?"

Little tai dariya tace "ah to abin naku dai ba kunya da alama daga ke har yaya."

Nafi tai saurin fizgar kayanta tace " me mukai?"

Little ta girgiza kai tace "hmm ko sai nazo nayi gashi? Ko kuwa ba tun yau ba aka bud'e?"

Idanu Nafi ta zaro sannan ta d'au kayanta ta dan bigama Little tace "lalai wannan kanwar batada kunya, to wlh mu ba ruwanmu salahaine."

Little ta rufe baki tace " hmm da alama kam."

Nafi ta harareta sannan ta zura kaya suka fita tana kokarin kare kanta agun Little, ita kuma sai tunzurata takeyi.


Ashraf yana dawowa gida yai sallah sannan ya kwanta akan kujera yana tunani, can wata idea ta fadomai hakan yasa yai bacci tare da tunani da fatan Allah ya taimakeshi gobe.

Da safe ya shirya sun fita shida Dan litti, a hanyarsu ta office ya zaro wayar nan dake cikin jala ya saka number kawu sannan ya turamai sako kamar haka " Yallabai ina bukatar taimakon ka, kudin hanuna sun yanke. daga Auwal Max."

Ya dade yana tunani kafin yai shahadar turamai, suna isa office ya kalli Dan Litti yace " ka tabbatar kabi Kawu duk inda zaije, jikina yana ban zai fito yanzu ka bishi duk inda yai."

Dan Litti ya amsa da to, sannan Ashraf ya sauka, a hanyarsa ta shiga yaga kawu wanda yake kokarin saukowa daga beni, kallan mamaki yamai ganin yana cikin hanzari.

Da sauri yasha gabansa, yace " Kawu sai ina haka?"

Kawu ya dan yi murmushin yake yace " akwai aikin dazan je dubawa ne a construction site."

Ashraf yamai kallan zargi yace " Hmm naga ne ka fito ba tare da Secretary dinka ba."

Kawu yad'an juya kai sannan yace " yana mota yana jirana."

Ashraf ya jinjina kai tare da cewa " shekanan a dawo lafiya."

Nan yai gaba, kawu ya kalla yaga yana sauri, waya ya daga ya kira Dan Litti yace mai ya tabbatar yabi kawu gashinan ya fito.

Ashraf office din kawu ya wuce yai knocking, kamar yanda yai zargi Secretary dinsa ne zaune yana rubuce rubuce, Ashraf yai murmushi sannan yace " Cigaba da aiki dama gun Kawu nazo."

Ya mike tare da cemai, bayannan yanzu ya fita, Ashraf ya jinjina kai sannan yace " amma ya akai ya fita shi kadai? Kana aikin ka kuwa?"

Da sauri yai kasa dakai alamun ban hakuri yace " wlh nace zan bishi yace in zauna ba dadewa zaiyi ba."

Ashraf ya juya ya fita batare da ya amsa ba.

Ajiyar zuciya yai sannan yace " ya ga sakon?"

Kawu kam yana fita duk ya rikice ganin tun bayan faruwar abun nan bai kara ma tunawa da wani Auwal Max ba bare yasa ran haduwa dashi, menene nashi namai sako yanzu? Rashin kudi?

Unguwar Nasarawa ya shigaz yai parking a wani tangamemen gida sannan ya fito da sauri yai cikin gidan yana waya, Dan litti na ganin haka ya kira Ashraf ya sanar dashi ya shiga wani gida.

Ashraf yai murmushi tabbas gun wanda suka hada abun yaje daga ganin sako, yai murmushin ganin abun yazo mai da sauki yace " zaka gane gidan?"

Dan litti yace " Yes Ma!"

Ashraf yai dariya yace " nine Ma?"

Dan litti shima yai dariya yace " ganinai tun da ka tashi yau bakai dariya ba shiyasa na saka."

A tare sukai dariya kafin Ashraf yace " bayan La'asar kazo mu tafi."

**********


Nafi kam ganin Little ta fita skul, yasa taji gidan shiru, dan ma tanata latsa wayarta can ta mike da niyyar zuwa kitchen, a kofar falo suka had'u da Habib, mamaki ya kamata tace " Ya Habib?"


Ya sakar mata murmushi yace " Gimbiya i really miss u."

Kallan mamaki tamai sannan tace " ni?"

Ya d'an hade rai, zai yi magana tai saurin cewa " Little tana makaranta bakuyi waya bane."

Ya hade rai yace " cewa nai gunta nazo?"

Ta zaro ido tace " inba gunta kazo ba,gunwa kazo to? nadai san ba guna kazo ba."

Ya kalletq yace " taya kika san haka?"

Tai murmushi tace " haba ya Habib ina nakai wannan matsayin?"

Yai ajiyar zuciya sannan ya mika mata leda yace " tsarabarki ce ta Abuja."

Ta amshi kayan tana mai kallan mamaki, bata samu tai magana ba taga ya juya yai gaba, ta dan tabe baki tace " Tsarabar Little dai."

D'aki ta maida kayan ba tare da ta bude ba sannan ta fita tai kitchen.


******


Ashraf sai yamma bayan sun tashi Dan litti ya wuce dashi gidan da kawu yaje, tun a kan hanya dayaga sun dau kwanar Nassarawa G.R.A yaji gabansa nafaduwa, addu'a kawai yake yi a ransa Allah yasa ba inda yake tunani zasu ba.

Tsoronshi ya kara daduwa ne sanda yaga anyi kwanar gidan, idanu ya runtse cikin tsananin tsoro, Dan litti yai Parking sannan ya kalli Ashraf yace " Mun Iso."

A hankali Ashraf ya bud'e idanunsa gabansa ne ya yanke ya fadi, da sauri ya fito daga mota yana girgiza kai alamar ba haka bane, ya kalli Dan litti yace " ka tabbatar nan yazo?"

Kai dan litti ya d'aga alamar haka ne, Ashraf ya dafa kansa cikin tsananin tsoro can wata zuciyar tace " mayb baiga sakonka ba."

Jiyai ance " Buddy."

Da sauri ya juya Habib ya gani ya fito daga gidan da saurinshi, yana karasowa ya rungumeshi yace " Ayya Aminina da alama jikinka ne ya baka na dawo ko?"

Ashraf ya d'an yi yake yace " lalai kasha hanya."

Habib yace "sosai ma, dan ma naje naga gimbiya."

Kallan mamaki Ashraf yamai,Habib ya katseshi da cewa " muje ciki ku gaisa da Dady kasan yace sam baka zuwa gunsa, gashi kullum sai ya tambayeni kai."

Ashraf yai murmushi sannan yace " muje to."

Jikin Ashraf kamar wanda aka zubama ruwa haka yake tafiya, sunje shiga ya kalli Habib yace " dama Dady da Kawu suna shiri??"

Habib ya dafashi yace " me kake fada, ka manta Dady baya shiri da Kawu har bayan auren Mumy."

Ashraf a ransa yace "then y??????"


Jansa Habib yai suka shiga ciki.

Dady na zaune yana karanta jarida yana ganin Ashraf ya mike cikin tsananin farin ciki yace " wa nake gani kamar d'ana da baya nemana???"

Ashraf yai murmushi ya karasa gunsa yace " Dady na sameku lafiya?"

Dady ya zauna tare da nuna ma Ashraf kusa dashi ya zauna, Ashraf ya girgiza kai sannan ya zauna a kasa wajen kafarsa yace " Dady ina wuni?"

Dady ya dafashi yace " Ashraf nida d'ana amma ganinsa ya min wuya?"

Ashraf yai murmushi sai dai a ransa yana kara kallan Dady da tunani kala kala dake yawo a ransa, can yace " Dady kasan aikin namu ne sai a slow."

Dady yai murmushi yace " to ya za'ayi dama komai sai hakuri."

Habib dake zaune yace " wato Dady kaga Ashraf ka manta dani ko? Dama kullum tambayar ka ya Ashraf yake? Wani aiki yakeyi yanzu? Me yakeyi? Wa da wa ya hadu da d......."

Da sauri Dady ya katseshi da dariya yace " kai kuwa ba dole inji halin da dana yake ciki ba?"
Ashraf yai murmushi a ransa yace " shiyasa kake barin Habib ke zuwa kwana akai akai saboda kasan me nakeyi???sai dai akan me? "


Nima nace lalai fa akan me kenan? Soyayyace ta 'yan uwa ko akwai wani b'oyayyen al'amari a kasa????



Hmmmmmmm



*#ASHRAFEENAH TEAM*
💞
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡




*61*


Tana kallo Datti washegari ya d'aga rigarsa ya zuge wani zip ya zaro yar karamar wuka sannan yaje kusa da tirken ya d'an barzo wani gini sai ga makulli ya fito, da sauri ta koma jikin bango ta labe, ya kara le lekawa sai daya tabbatar ba kowa sannan ya bud'e turken.

Kwalla mata kira yai sai ga Mairo ta taho hannunta duk gari tace " Datti ya akai? Ina tankade ne banji kiranka ba."

Ya washe baki yace " zo kiga tirken."

Tai murmushi tare da cewa ai har na saduda na dauka ma ka manta ko baxaka nunin ba."

"Ah haba yanzu dai shigo ki gani "

Nanta shiga ciki mamaki ya hanata magana, wannan wani irin arziki gareshi??? Yi tai kamar abin bai bata tsoro ba ganin yawan dukiyarsa tace " Allah ya kara amfa nawa, na gani bari na koma na karasa tankad'en."

Dadi ya kama Datti ganin bata rude da ganin dukiyarsa ba lalai baza ta ci amanarsa ba.


***********


A b'angaren su Nafi kuwa bayan komai ya wakana, itakam bacci ne yai gaba da ita, Ashraf ya mike tare da kunna fitilar gefen gado ya d'auketa ya d'aurata kan gado tare da lulube mata jiki, ya sani dolene tasha wahala tunda na farkon ta ne.

Ya gyara kasan da suka b'ata sannan ya shiga wanka.

Bayan ya fito ya zauna a gefenta tare da kura mata ido, wani irin shaukin santa ne ke kara ratsashi, lalai ba shakka zuciyarsa na tsananin san Nafisa.

Hannu yasa yana shafar gashin kanta a hankali ya sumbaci goshinta cikin tsananin kauna yace " Nagode Nafisa, da kika jure wulakancin da na miki a baya baki takura na baki takardarki ba, lalai da nayi takaicin rayuwata na kuma yi rashi babba."


Kwanciya yai tare da jawota jikinsa ya rungume yanajin dadin dumin jikinta, wannan rana ya manta sam da abinda ya faru dashi domin kuwa farincikin da ya keji ya kawar da waccan damuwar.

Nafi kam bacci take sosai, sai asubahi motsin Ashraf ya farkar da ita.

Tana bud'e ido kuwa suka hada ido da shi da sauri ta rufe idanta yai murmushi sannan yace " ki jirani yanzu zan dawo in taimaka miki sai kiyi sallah.
Bata amsa mai ba wai ita a dole bacci take.

Ya fita yana murmushi.

Ana idar da sallah ya fito ya dawo b'angarensa ta lulube har kanta da bedsheets din daya rufeta dashi.

Yai murmushi sannan ya wuce toilet.

Gurin wanka ya toshe sannan ya kunna ruwan dumi, sai da ya taru sosai sannan ya dawo d'aki ya zauna kusa da ita yace " Hajiya Amarya zaki iya bud'e fuskarki."

Tana jinshi amma kunya ya hanata bud'ewa hannu yasa ya d'agota cak daga ita har bedsheets din yai toilet dasu.

Nafi sai dan motsi takeyi alamar wai bataso.

Shikam yana shiga toilet din ya fara kokarin ajiyeta, ganin za'a ajiyeta a kasa yasa tai saurin bud'ewa dan batasan inda suke ba.

Ashraf yai dariya yace " why? Kina tsoron kar in yarda ke ne?"

Ta juya kanta da sauri, hannu yasa ya kama bedsheets din ya fara kokarin jawota baya tai da sauri wanda hakan yai sanadiyar yayewar zanin gadon sakamakon juyin datai.

Idanu ta zaro ganin ba komai a jikinta da sauri ta fara kokarin komawa ta nade cikin zanin gadon, sai dai kafin nan Ashraf ya fizge zanin gadon da karfinsa.

Nafi tasa hannu ta kankame jikinta.

Kusa da ita ya matso ya d'agata ya sata a cikin wannan ruwan dumi mai dan

2 Comments On ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA
avatar
sadiyayunusa

1 year ago

Reply

Inaso sosai

avatar
khadija-murtala

17 days ago

Reply

Yayi dadi sosae

Please Login or Register in order to submit comment