Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zafi sai dai ba zafin dazai kona mutun ba.

Yar kara tai sakamakon zafin dataji a gabanta, Ashraf ya sunkuyo tare da zama a gefen gun yace " raguwa kawai."

Kallansa tai tace " yaya mai kake kai kuma anan?"

Yai murmushi yace " baki gani ba? Matata zan taimakama tai wanka."

Idanu ta dan zaro tace " zan iya da kaina."

Yace " na sani sai dai banaji zan iya tafiya na barki."

Kanta ta kawar gefe batai auni ba kawai taji soso a bayanta da sauri ta juyo ta kalleshi sai dai ta kasa magana.

Gira ya d'aga mata yace " kina farin ciki ko? Allah ya baki namiji mai kulawa ko?"

Ta d'an yi murmushi kadan a ranta tace " dama yaya....."

Bata karasa fadar abinda zata fada a ranta ba taji hannunsa yana wanke mata wuyanta.

Kallansa tai a hankali tasa hannu ta rike masa hannunsa,wani irin kallo ya mata mai sagar da gababuwan jiki, a hankali ta zare hannunta.

Da kashi ya cud'ata sai daya gama sannan ya mike ya ce kiyi wankan tsarki.

Ya juya ya fita.

Kallo ta bishi dashi, a hankali murmushi ya bayyana a fuskarta.
Shikansa yana fita ya saki murmushi sannan ya kalli kansa a madubin d'akin yace " wai da gaske nine kuwa???"

Zama yai a bakin gado sai a lokacin tunanin Dadyn Habib ya fado mai, idanu ya runtse cikin kunar zuci yace " wani kuma abin mamakin zan gani nan gaba??? Ya Allah gani gareka."

Motsin Nafi dayajine yasa ya mike ya sa hannu a kugunta ganin tana d'an dingisa kafa kadan, yana kallanta tai sallah bayan ta idar ta dade tana addu'oi sai dai gaba d'aya addu'oin ta akan mijinta takeyi bayan ta shafa ne ta juyo ta kalleshi cikin shagwaba tace " Yaya mai zancema Little?"

Cikin rashin kulawa da abin yace " akan me kenan?"

Tace " na kwana anan mana."

Kallanta yai yace " kice mata kin kwana a gun mijinki, menene a ciki? Ni inaji ma kin dawo nan kenan."

Idanu ta zaro tace "bangane na dawo nan kenan ba?"
Ya hade rai tamau yace " kwarai, nima inasan matata a kusa dani."

Kallansa tai cikin mamaki tace " Sai muzo mu zauna nida yaya nisa ko me?"

Yace " Nisa?" sam yama sha'afa da ita.

Kallan Nafi yai yace " to sai me?"
Baki dan turo tace " ni dai ban yarda ba kabarni a can gaskiya."

Ya mike yace " shikenan da alama zanje bikon matata."

Gani tai ya mike, da sauri ta riko shi.
Juyowa yai ya kalleta ta shagwabe mai fuska ba tare da tace komai ba.

Kallanta yai shima fuska a hade bai ce komai ba, sun dade a haka kafin tace " ni fa ba haka nake nufi ba."

Ya kunshe dariyarsa yace " then?"


Fuskar ta tadan sosa tana kallansa, ya zauna a kusa da ita tarecda jawota jikinsa yace " what are u afraid of?"

A hankali tace " Yaya Mumy ba ta....."

Yace " wannan ba uzuri bane a guna."

Tace " 'yan gidan nan duk......"

Yace shima ba uzuri bane a guna."

Tace " amma...."


Katseta ya sakeyi yace " we have already become one, ya kamata ko menene yanzu mu ajiyeshi a gefe."


Kara kwantawa tai a jikinsa tare da d'agamai kai...


Tare suka koma bacci lokacin tashinsa nayi ya mike ya shiga wanka, farkawa tai a hankali take tafiya ta shiga kitchen, tayi mamaki ganin ba komai a ciki na kayan abinci sai kawai kayan shayi.

Tace " 'yan gidan nan sun saba da a aiko musu da abinci kawai."

Ruwan zafi ta hada tayi tunanin fita taje kitchen sai dai tana tsoron kartaje kafin ta dawo Ashraf ya fita.

Nan ta jera kayan shayin akan dinning yana fitowa ya ganta a falo.

Yai murmushi ya tuna sanda Anisa nanan har ya fitama bata sani ba tana baccinta.

Karasowa yai gunta yace " Me yasa kika tashi bayan jikinki ba kwari?"

Hannunta tasa cikin nasa sannan ta mike tace " muje kasha ko tea ne naga ba kayan abinci a kitchen din."

Yai murmushi sannan suka karasa.

Tea ta hadamai mai kauri a hankali yake kurba idanunsa na kanta.

Bayan ya gama ne, ya sunkuyo ya sumbaceta sannan ya dau jakarsa yai waje.

Kallo ta bishi dashi harya fita.


Ashraf yana fita suka hadu da Dan litti nan sukai gun mota.

A tsaye sukaga Asim yana ta danna waya da alamar wani yake nema bai sameshi ba.

Ashraf ya dauke kai kamar bai ganshi ba, Asim yace " Lala Ashraf wuyanka ya isa yanka dan an karama matsayi shine har zaka iya ganina ka wuce ni?"

Kallansa Ashraf yai ya saki murmushi yace " Ai ban kula da mutum anan ba, ya dafatan ka fara sabawa da inda aka maida ka Assistant director."

Asim ya kumburo fuska yace " kana tunanin zan yarda da wannan karamin office din?"

Ashraf ya kalli Kawu wanda ya taho ta bayan Asim yai murmushi sannan yace " Ayya gashi banaji Kawu zai daukeka daga nan yanzu."

Asim cikin masifa yace " kana tunanin Abban ya isa ya barni anan?"

Ashraf ya kalli Kawu wanda kalaman Asim suka dakarmai kunne.

Asim ya cigaba " in ma kana tunanin Abban ya isa ne to gwara......."

"ni kake fadama haka Asim? Kawu yai maganar cikin zafin rai.

A tsorace Asim ya juya yace " Abba!"

Ashraf ya saki wani murmushin ya hade hannayensa biyu yace " Nabarku lafiya da alama akwai maganar da zakuyi."

Yana kaiwa nan ya wuce mota Dan litti yana dariya shima ya shiga sukai gaba.




Kawu ya kalli Asim cikin kunar rai, da sauri Asim ya matso yace " Abba abinda ya faru shine....."

Wuceshi kawu yai ya shiga mota shima yai gaba.

Asim a zuciye ya naushi iska da hannunsa.....



*#ASHRAFEENAH TEAM*
💞
*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡




*My Kawa Bilyn Abdul wannan shafin sadaukarwa ce gareki, Allah ya kara kareki a duk inda kike* Ameen.





*62

Ashraf ne a mota ya kalli Dan liti yace wai meyasa fans din Zuciya sunqi yin zuciyane 🤔🤔 Dan liti have nima abin naban mamaki dan jiya Ummu Khausar Sai 12:00 tayi barci Sabo da jira

Ashraf ya dafashi yace " next time kanina."

Murmushi sukai a tare Ashraf ya kira Dan Litti suka dau hanya, suna hawa kan titi dan litti ya kalli Ashraf yace " Ashe ma kasan 'yan gidan."

Ashraf yai murmushin takaici yace " Gidan yayan mahaifiyata ne "

Dan litti yasa dariya yace " ohh shiyasa yazo nan?"

Murmushi kawai Ashraf yai ya bud'e window tare da kurama titi ido, suna isa gida ya fito jiki a sanyaye yai b'angarensa.

Nafi kam harta gaji da jiran dawowarsa gashi ta mai abinci, ganin anyi sallar isha'i yasa tai tunanin dubawa ko ya dawo.

Da yake yanzu tanada makulli bayan ta kwankwasa taji shiru sai ta bud'e kofar, duk wutan bangaren a kashe yake da alama ba mutum a ciki, ta d'an d'aga gira tare da yin ajiyar zuciya tace " bai dawo ba."

Tayi nufin juyawa sai taji ringing din waya, ita kuma ba tata bace dan tata na gida, cikin tsoro ta fara yin sanda tana bin inda takejin karar gashi a bin mamaki ba'a d'aga wayar ba.

D'akinsa taji karar na fitowa a hankali ta murd'a tare da yin addu'oi a ranta, kwan wuta ta kuna da sauri tana tsoron kafin a maketa gwara taga waye.


A binda ta gani ne yasa gaba d'aya jikinta ya mutu, tsayawa tai cak tana kallan Ashraf wanda ke zaune a kasa ya hada kai da gwiwa, ga kuma wayarsa nan a hanunsa yanaji ana kira bai dauka ba, sai dai ta kula ba wayarsa bace da yake amfani da ita.

Ganin haske ya kewaye d'akin ne yasa ya d'ago ya kalleta da idanunsa wadanda sukai jaa, a hankali yace " Nafisa can u please get out?"

Kallansa tai cikin tsananin mamakin halin data ganshi cikin rawar murya tace " Ya Ashraf?"

Idanu ya runtse yace " please can u get out, banasan ki ganni cikin wannan halin....." ya karasa maganar cikin wata irin murya, sakon da aka turo mai yana kokarin bud'e kofa ne yasashi cikin wannan halin.

Kawu ne yai reply kamar haka "Max na d'auka kunyi da Yaya akan bazaka kara nemana ba? To shi yace kaje yana nemanka." wannan sako ya d'agama Ashraf hankali, a iya saninsa Kawu mahaifin Habib kawai yake cema Yaya, sai dai tayaya za'ace da hannun yayan mahaifiyarsa?????

Ganin bai maida reply ba yasa Kawu ke ta kiransa.

Kashe wutar Nafi tai sannan a hankali ta taka zuwa inda yake, ta tsugunna tare da rungumoshi jikinta, idanunta sun cika taf da kwalla tun da take bata taba ganin Ashraf a irin wannan yanayin ba, hawaye ne ya ziraro mata a hankali tace " taya zan iya tafiya na barka cikin wannan yanayin?"

Ashraf ya d'an zare jikinsa kadan yace " Nafisa please......"

Hannu tasa ta rufe bakinsa sannan ta kara kankameshi hawaye suka fara zirya a idanunta cikin kuka tace " Yaya can u please share ur burden with me? Zuciyata tana zafi idan na duba naga bansan abinda ke faruwa dakai ba, bansan a wani hali kake ciki ba, Yaya ka taimaka ka sanar dani damuwar ka dan Allah...."

Kuka take sosai wanda yasa jikinsa yin sanyi, kankameta yai sosai a hankali yaji hawaye ya gangaro ta idanunsa, yace " Nafisa ya zanyi? Ya zanyi da rayuwata, duk wanda nake tunanin yana sona sai na duba sai inga makiyi na ne, duk wanda nake tunanin yadamu dani sai in duba inga ashe amfani yake dani a b'oye, na d'auka i am smart sai dai yanzu na tabbatar i am the biggest foolish in the world, me yasa Allah ya d'auke Abbana ya barni? Meyasa....."

Kuka take sosai ta sa hannu ta toshe bakinsa tana girgiza mai kai" Yaya ka daina fadar haka, Allah na tare da kai sannan duk wanda ya zalunceka Allah bazai barshi ba ko shi wanene."

Idanu Ashraf ya runtse wasu zafafan hawaye suka zubo mai yace " me ya kaini binciken abinda ya riga ya shud'e, why???"

Nafi ta kankameshi tana girgiza kai tace " laifinane yaya ko ma menene laifina ne, please ka yafemin, da ban sanar dakai ba banaji zakai binciken nan, yaya ka yafemin Laifinane, nice na ja maka shiga wannan halin."

Ashraf ya sa hannu ya shafi bayanta yace " ba laifinki bane, na dade ina bincikena, iya kace ke taimakamin kikai, karki sake cewa laifinki ne."

Nafi shasheka kawai takeyi, bata san me ya jiyo ba amma ta tabbata abin ya shafi danginsa.

Sunyi shiru suna manne da juna cikin duhu, Ashraf can cikin wata sansanyar murya taji yace " Thank u Nafisa."

D'agowa tai cikin mamaki duk da ba haske ba ganinsa take ba sai dai mamaki karara ya bayyana a fuskarta, wannan itace rana ta farko data tabajin Ashraf yayi godiya bama ga ita ba, a'a bata tabajin yace ma wani bama.

Murmushi taji yayi ya d'an ja numfashi kadan yace " kina mamaki ko? Ni kaina rabon danaji na fadi wannan kalma ba naji zan iya tunawa."

Hannayenta tasa akan fuskarsa sannan ta hada goshinsu tace " Yaya in kamin godiya akan me kenan? Ni kuma ince me kenan, yarinyar datake yar kauye ka..........."


Hannu yasa ya d'an turo kanta bakinsa yakai cikin nata, wani irin salon soyayya suke ma juna wanda kana gani kasan son da sukema junansu lalai a bayyana yake, sun dade suna sumbatar juna kafin a hankali bakin Ashraf ya sauko kan wuyanta, wani irin yarr taji a jikinta wanda yasata yin numfashi, Ashraf sam ya manta da zancen sai ta aminta dashi, sarafata ya shiga yi sai dai itama duk da batasan kan abun ba haka kawai taji lalai tabbas tanasan ba Ashraf dinta farin cikin da yake nema.


Soyayya mai karfi suke nuna ma juna sam bata san sanda ya zuge zip din rigarta ba sai jitai yabrabata da rigarta, ba shakka tsoro da fargaba ne ke damunta sai dai bataji duk wani wahala da ake fada zata iya bijirema Ashraf.


Ya gama fita daga hayyacinsa haka itama a daidai wannan lokacin mai afkuwa ta amfku............Nikam ganin haka yasa na fito ga duhu wanda yasa ni yin tuntube da kujera😭





************



A kauye kuwa Datti yau ya dawo ya taradda matarsa Mairo ta yimasa tuwo miyar kubewa bushashiya sai dai da zabuwa akai miyar, mamaki ya kamashi ya kalleta yace "mairo badai da zab......"

Katseshi tai cikin salonta na jan hankali tace " Haba Datti bada zabuwarka bane, zabuwa ta ce data kasa na yanka mana ita."

Baki taga ya washe yace " kai Mairo Allah ya miki albarka kinsan darajar dan adam."

Nan ya yanko malmalar tuwo ya zuba nama sosai da miya ya hau ci, sai uban santi yake zubawa.

Itakam sai murmushi takemai.


Yaci yai hani'an ya tauna kasusuwa sannan ya kalleta yace " kai Mairo Allah ya barmin ke "

Tace " Amin Datti."


Ya kara washe baki yace "rabon dana kai nama bakina har na manta sai dai in gani a kwanon wani."

Tai dan fari tace " ai banga laifinka ba, yanzu ba gashinan kafi kowa dukiyar dabobi ba duk yankin nan."

Ya sake washe baki yace " Zabina guda 20 ne kaji guda 30 banda raguna, saniyoyi da akuya."

Ta matso kusa dashi tace " yaushe za ka nunamin ne nima in gansu."

Dariya ya kwashe dashi yace " karki damu gobe da kaina zan kaiki ki gansu."

Tace to Datti Allah yabarmu tare.

Yace Amin Mairoro ta....


Nace inma Maikoko ce...Lol masu suna Mairo tuba nake🤢



*#ASHRAFEENAH*

💞

*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com


*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡




_*MY INTIMATE FRIEND AISHA MUHD UMAR*_💞
*As it's a special day for My Intimate Friend, i just can't express how happie i am today, It's ur wedding day, the day 5th August have become a memorial day for us.*
*Allah ubangiji ya baku zaman Lafiya da zuri'a dayiba Ameen suma Ameen*




*63*


Ashraf yana fita ya wuce gidan su Ferry, yayi sa'a kuwa a lokacin Mahaifin su Ferry ya dawo.

Tare suka shiga gidan bayan sun gaisa Isma'il ya kalli Ashraf yace " banyi tsammanin ganinka da wuri haka ba."

Ashraf ya dago cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa yace " Kasan komai ko kuwa kaima bincike kakeyi??"

Isma'il yai murmushi yace " Bansan komai ba sai dan abinda ba'a rasa ba."

Ashraf yai dan huci kadan yace " Auwal Max a ina zan sameshi??"

Kai ya girgiza yace " bansan inda yake ba, tun wannan ranar, in fact banmasan ko yana raye ba ko ya mutu, sai dai nasan abu d'aya tabbas shine wanda yaja Alhaji a wannan ranar sai dai abin zargi shine sun fita daga gida tare amma daga baya danai bincike sai naji Alhaji ne kawai a cikin motar sannan a bincike nane na gano Auwal Max mai gadi yana kallansa sanda ya shiga kasan mota, hasashe na ne yasa nasan yayi wani abu bawai proof gareni ba."

Ashraf ya matse hannunsa da karfi, tare da runtse ido yace " Shi Abban a ina ya san Auwal max din?"

Isma'il ya kara girgiza kai yace " bansani ba, sai dai tun da nasanshi tare nake ganinsu, sai dai a koda yaushe inaji kamar bawai zuciya daya yake zaune da Abbas ba ganin duk wani plan indai mukai kafin mu aiwatar sai muji shi a gari ance Muktar yayi, shi kuma Abbas ba ya kara tada zancen."

Ashraf yace " Daga bangaren mahaifiyata akwai wani abu da kasani na gaba ko wani abun a tsakaninsu??"

Isma'il ya dan shafi goshinsa sannan yace " akwai case daya faru wanda ya jawo asarar dukiya mai yawa daga bangaren matar Abbas."

Idanu Ashraf ya zaro yace " case?? Wani iri kenan?"

Isma'il ya girgiza kai yace " i can't tell u, sai dai kai ka nemo menene."

Ashraf yai shiru yana tunani, sun danyi shiru kafin daga bisani Ashraf yamai sallama.

Yana fita ya shiga mota tare da sa kansa a sitiyari wani irin zafi yakeji zuciyarsa namai.
Ya dade kafin ya daure ya tada mota yai gida.



**********


Nafi kam yau sam bata fita ba tana kwance a d'aki gani take kamar in ta fita za'a gane abinda ya faru daren jiya.

Bayan magrib tai sallah tana zaune ita da Little sukaji ana knocking.

Little ta tashi ta bud'e, Mumy ce ta shigo fuskarnan tata a b'ace.

Little tace " Mumy ya akai?"

Bata kulata ba ta karasa gun Nafi wacce cikinta har ya duri ruwa, Mumy tace " Ki shirya gobe zansa a maidake garinku."

Nafi ta zaro ido cikin tsananin mamaki ta kalli Mumy, Little ta matso tace "Mumy wai meyasa kike haka ne? Matar yaya ce fa....."

Tsawa mumy ta mata tace " fita."

Little mamaki ya kamata ta fita da sauri, bangaren Ashraf ta nufa tana zuwa tahau bugawa, shiru da alama bai dawo ba gashi ta bar wayarta, jiki a sanyaye ta dawo nan ta hangoshi daga nesa.

Da gudunta ta karasa gunsa, Ashraf ya kalleta yace " Little!"

Cikin haki tace " Yaya Mumy ce."

Yace "Mumy?"

Ta daga kai tace "Nafisa...."

Ai bai jira ta gama ba yai bangarensu da saurinsa.

Yana zuwa bakin kofar dayake a bud'e yake yaji Mumy na cewa " Me zaki iyama Ashraf da har kike tunanin zamq matarsa? Ban yarda da wannan auren ba dan haka dole ne gobe ki koma kauyenku."


Nafi kam hawaye ne kawai ke zubo mata.

Muryar Ashraf ce ta daki kunnuwansu yace " Inji wa kenan?"

Mumy ta juyo har zuciyarta sai dataji dan tsoro sai dai ta dake tace " injini ni mahaifiyarka."

Ashraf ya karaso ciki yace " Do you hate us that much? Ni da Mahaifina nake nufi?"

Idanu Mumy ta zaro cikin mamaki tace " me kake fada haka?"

Yai murmushi yace " me? Ba tsantsar tsana bace yasa kike bakin cikin ganin farinciki na? Na sanar dake matatace, na dauka uwa mai san danta zataso farin cikinsa."

Ya girgiza kai cikin takaici yace " sai dai me? Ban taba gani kinso abinda nakeso ba tun da na mallaki hankali na, in har nace gabas nake san yi to burinki kice kekuma yamma kikeso nai."

Cikin murya mai zafi ya karasa maganar da cewa " inkinsan da haka meyasa kika auri Abba har kika haifine??"


Nafi da sauri ta taso tazo kusa dashi ta dan turashi baya, idanunta na zubar da hawaye tace " Yaya me kakeyi hakan?"

Mumy kam gaba daya jikinta ya gama mutuwa kamar wacce aka kwarama ruwan sanyi, Nafi ta cigaba da turashi zuwa waje tanacewa " please Yaya ka bari, kar kai fada da Mumy saboda ni dan Allah."

Ashraf ya rike hannunta idanunsa suka kada sukai jajawur kamar jan gauta, ya kalli Mumy yace " na tabbata sanda mahaifina ya rasu kina daya daga cikin masu farin cikin faruwar hakan."

Nafi kai kawai take girgizawa tana kuka, Ashraf na gama fadar haka ya fara jan hannun Nafi, har sunje bakin kofa ya juyo yace " in har baso kike nabar gidan nan ba kar ki kara shiga harkar matata."

Ya ja hannun Nafi sukai waje, zubewa Mumy tai a gun ta rike inda zuciyarta take jin tana mata zafi ta saki wani irin kuka mai kuna.


Ashraf kam jan Nafi kawai yake sunje yin kwana sai ga Anisa ta sha gabansu, ya buga mata wani kalli dan yanda yakejin zuciyarsa tayi sa'a ka da bai mareta ba, itama harararsa tai tace "anji kunya wlh kwartanci da ranar Allah, to wlh baku isa ba naga uban da zai maye min gurbina."

Ashraf ya kalleta cikin tsananin bacin rai yace " gurbin inaji nine nake rike da ragamarsa ko? To mai zai faru in na sallami mai gurbin?"

Idanu Anisa ta zaro tace "mai kake nufi Yaya?"

Yace " zaki matsa ko sai na fahimtar dake abinda nake nufi??"



Da sauri ta matsa ya ja hannun Nafi sukai bangarensa, bai saketa ba sai da suka shiga d'akinsa ya kalleta cikin tausayi ya runtse idanunsa, ransa na kara soyuwa, baya ya juya mata yana wani hucci da sauri da sauri.

Nafi da sauri ta matso ta rungumeshi ta baya, tasa kanta a bayansa tana kuka tace " Yaya please cool down, me yasa ranka zai baci akan abinda baikai ya kawo ba??"

Idanu ya runtse yanajin wani abu na tasomai a ransa yace " ina zaki gane bayan wani bangaren na sanar dani harda Mumy a salwantar da mahaifina, tunda nasan abu ya hadasu da danginta."

Nafi ta kara kankameshi ta baya tace " Yaya Mumy fa ba wai tsanar ka tai ba, ka taba ganin inda uwa taki danta? Ni inaji a jikina akwai dalilinta na yin haka."

Idanu ya sake runtsewa, Nafi ta zagayo ta gabansa ta rungumeshi tace "please yaya kadaina fadamata magana mai zafi haka tun balle in akainane."

Hannu yasa ya zareta daga jikinsa yace " Nafisa, kinsan ya nakeji a raina? A duk lokacin da matar nan tamin haka? Tun da nake da ita bata taba san abinda nakeso ba, bata taba yarda da abinda nace ba, bare in nemi kulawarta ko shawararta."


Hawaye ne ya zubo mai, Nafi kam hawayenta sai tsananta gudu suke yi, da sauri Ashraf ya juya dan bayasan taga hawayensa.

Kara rungumeshi tai tace " Yaya fitar da duk abinda ke ranka, inaji kamar abubuwan da kake hadiyewa sunyi yawa, shi hawaye rahama ne in kayishi yanasa bakin cikin mutum ya ragu, sannan maganar Mumy ni dai inaganin da wani abu."

Ashraf ya hadiye hawayensa yabar idanunsa a runtse, Nafi ta dago a hankali ta danyi dage ta sumbaci bakinsa kadan, tace " i am here with u, ka daukeni a matsayin mutum mara ji mara magana, ka fadi duk abinda kake boyewa a ranka ko ka samu sauki cikin ranka, Yaya na kula bacci ma bakayi yanda ya kamata, kuma ni nasan duk saboda abubuwan da kake hadiyewa ne kai kadai."

A hankali ya bud'e idanunsa ya jawota ya rungume tsam, yace " Nafisa I really Luv u."

Dagowa tai cikin mamaki, ya kara kankameta yace " kece mace ta farko ko ince mutum na farko da nake jin tabbas wannan itace, itace wacce takesona tsakani da Allah, itace wacce ta yarda dani, itace wacce zuciyata ta aminta da ita, itace nakeji in har tana tare dani i can endure everything."

Ya dan yi ajiyar zuciya yace " ban taba tunanin zan taba jin mutum haka a raina ba, ban tabaji na aminta da mutum haka ba, Nafisa please don't ever betray me"

Wani hawayen dadi ne ya zubo mata kai kawau take girgizawa tace " How can I! How can I......."

Sam ta kasa karasawa ya dago

2 Comments On ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA
avatar
sadiyayunusa

1 year ago

Reply

Inaso sosai

avatar
khadija-murtala

17 days ago

Reply

Yayi dadi sosae

Please Login or Register in order to submit comment