Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matakin Kare Tenkwai daga sharrin sa kin San ba abunda ze Hana wnn Abu duk da ba lokacin yin sa bane sunce sai sunyi





Ina tsoron fushin badu akan wannan auren idan karshen shekara tazo nasan hukuncin raba shi ze dauka Amma ba komai zan dage bangarena ze sata Dan nadinga kula da ita bazan Bari wani Abu ya same ta ba bazan Bari ya lalata Miki itaba kiyi hakuri lamunde




Lamunde sharar kwalla kawai take cike da tashin hankali batasan yaza siyiba basu da kowa basu da komai basu da me Hana wannan lamari tanata Sharar kwalla




Yanzu Dan isa da mallaka da wulakanci auren Yar tawa ma sai Ana kwana biyu masu zuwa za a sanar Dani wannan wulakanci har Ina dame zamuji gaba dayansu basa cikin farin ciki yaran Nan haka zata tafi tabar mun su ga Mara lafiya danma kince ze koma wajen ki shima sai kuka




Ihu suka jiyo a waje anata koke koke suka fita da gudu mezasu gani tenkwai ce a sume yayin da su Rama keta rabzar kuka lafiya meya faru Suma sai sukaji Ana shela daga waje ta daurin auren Tenkwai da Ja'e kwana biyu masu zuwa Wanda ya kama ranar bikin cin jariran garin


Tofa muje zuwa



AKWAI LITATTAFAI NA WANDA ZAN MUKU BAYAN NAGAMA ARNAN DAJI SUNAN ZUWA GAREKU BA DA DADEWA BA


*AKAN RABON GADO*
*FACCALATA*
*MATAN AUREN KO YAMMATA*
*DAN ISKAN NAMIJI*
*GIDAN MARAYU*

WANDA KUKA ZABA SHIZAN FARA YO MUKU BAYAN MUN GAMA ARNAN DAJI SABODA YADDA NAKE KAUNARKU FANS??AMMA SAI NAGA COMMENT DINKU
[9/11, 22:29] +234 810 679 5647: *?ARNAN DAJI?*


*NA*


*FAREEDA ABDULLAHI*




*_?KAINUWA WRITERS?? ASSOCIATION_*??
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation





*GAISUWA ME TARIN YAWA GA MASOYANA DAFATAN KOWA NA CIKIN KOSHIN LAFIYA INA BARAR ADDU ARKU INADA WATA BUKATA A WAJEN ALLAH DAN ALLAH KUTAYANI ADDU A ALLAH YABIYAMUN ITA NAGODE MASOYANA*




WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA MAHAIFIYATA ALLAH YAJA KWANA



*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JIN KAI*




65-70




Hankali tashe iyar Ja'e ta leka tace suje anji sun sani ay sukan su abun ya basu mamaki na ganin iyar Ja'e meya kawo ta oho ita da Sam Bata shiga wasu abubuwan dasuka shafi gidan sarautar koda yake ita dazata aurar da danta komeye namu ma oho suka wuce suna ta shelarsu hankalin su kwance cike da farinciki





A guje Rama ta debo ruwa ta zuba Mata ta farfado kuce mafarki nake kar kuce a gaske naji wannan batu tabbas badu be chanchanta da zama abun bautaba tunda ya kasa temakona akan wannan hali kullum sai na Kai Masa kuka na amma be taba amsa mun ba kullum susuke nasara akan kowa da komai Tai shiru tana ta sheshsheka





Aduke ta taso da kyar ta dafa ta karki damu Yar uwa kiyi hakuri ki aure shi kodan ki daukar Mana fansar abunda yai Mana bazan taba yafewa Ja'e ba kobayan Raina karku kyale shi ku daukar mun fansa keda rama iyar Ja'e ta dago fuska jage jage da hawaye dama shine shi yai Miki wannan abun Dana sameki cikin lalura meyai Miki tana girgizata kigaymun mana kuka kowa yake anrasa me magana a cikin su





Tabbas nayarda akwai wani ubangiji bayan badu Wanda shike bamu ruwan sama Amma bamu San shi ba kullum addu ata haske yazo wannan gari inga Wanda ze kawo karshen mijina da Dana bana kaunarsu ko kadan basu kasance masu tausayin na kasa dasuba su kansu kawai suka sani basa tausayin kowa Banda burin dayafi Naga karshensu





Tenkwai ta dago ido cike da tausayinta tabbas batai sa a ba a rayuwarta baga miji ba Baga da ba duk mugaye masu munanan dabi u azzalumai masu danne hakkin kowa nice zan kawo karshen Ja'e nizan auri Ja'e nayarda zan aure shi zan kawo karshen shi zan koya Masa darasi a wannan duniyar tamu




Cike da mamaki lamunde ta kalleta kin amince zaki zauna da azzalumi bashi da imani sam kema kashemun ke zeyi shike Nan kema zan rasaki tamkar yadda na rasa Dan uwanki na rasa mahaifin ki sai kuka dama inada Dan uwa meyasa baki taba gayan ba yana Ina Ina ya shiga





Lokaci na zuwa da zan baki tarihin rayuwar mu a wannan gari zakisan matsayin mu awannan gari na kuguru na Miki alkawari ranar bikin shekara na abun bauta badu zan sanar dake komai da duk abun da ya faru a Rana me kamar ta wannan zansanar dake koma wace ke a garin Nan




Gaba daya lamunde tasa kowa a cikin rudani gashi duk Wanda yay magana a cikin su sai ta daga Masa hannu Bana bukatar tambayar kowa a yanzu Amma kamar yadda nai alkawari gaba dayanku ku taru ranar zan Baku tarihin mu Nan da wata biyu masu zuwa kowa yai shiru an rasa me magana





Nayarda ki auri Ja'e Amma kamar yadda iyar sa ta fada Ina bukatar zamanki a sashen ta Dan nasan baza ta taba Bari ya cutar min dake ba kuta shi kuje kuduba Mara lafiya suka mike suka koma dakin da Mara lafiyar yake duk yana jin meke faruwa a waje ya Kura musu ido yana binsu da kallo daya bayan daya




Iyar Ja'e ce ta shigo dakin mado kowa yay shiru ta karasa kusa da shi sunan ka mado kasamu rashin lafiya ne Amma Kai bawana ne a gidan sarki Ni matar sarki ce Babar dansa Ja'e magajin garin Nan a sashina kake Dan haka ka shirya komawa bakin aikin ka zan sanar wa da matarka da danka rashin lafiyar ka bansan inda kasamo wannan kayan ba ba irin namu bane Dan haka yadda kaga shigar mu take Kai ma taka zata koma haka kana da kyan jiki da wuri zaka warke




Yai Mata shiru yana ta tunani tabbas yanada Mata da da Amma kamar ba a Nan suke ba ba irin wannan kayan suke sawaba Amma baze iya tunawa ba Tom shikenan Ina Mata ta da Dan nawa inaso zan gansu zan koma wajen su har na warke Inasan su zan zauna dasu




Ranta kal tace suna gida kabari kaji kwari Nan da kwana biyu saika koma Amma zan dawo gobe na dubaka naga ya jikin naka yake sai na taho ma da kayan naka kasa a jikin ka muba ma amfani da wannan inda kasamu lalurar ne suka sama Amma mu da wannan mike amfani bana so kasanarwa da kowa kowa ya tambayeka kar kace komai Koda ko matar kace kar kace nice nasa aka Fara dubaka




Gaba dayan su mutuwar zaune sukai jin wannan batu kamar almara me take nufi zata tafi dashi su cinye kenan hankali tashe tenkwai ta bude baki zata Fara magana ta daga Mata hannu muje Inasan magana daku ta fice suka bi bayanta suka shiga dakin lamunde har da aduke data ke takawa da kyar ta dinga basu hakuri su rufa Mata asiri su rufe wannan sirrin ta zayyane musu duk Shirin ta jikin su yai sanyi da wannan tunani nata tabbas suna Kama da mado ba me ganewa idan aka turashi tunda Suma wasu na tirin baza a ganeba Kuma wannan ce kawai hanya daza a tseratar da rayuwarsa





Rama tace iyar Ja'e na Miki alkawarin zan tira shi kafin ranar daze koma wajen ki nayi alkawarin kula da lafiyarsa har ya warke kafin tunanin sa ya dawo bazan janye ba ki dauke Ni matsayin me kula dashi yadda matar mado bazata zargi wani Abu ba bare har asirin ki ya tonu




Cike da farinciki iyar Ja'e tace tabbas kinyi gaskiya naji Dadi da kuka fahimceni kinga kema baze Miki nisa ba ta dubi tenkwai duk San da kike son ganin sa zaki gan shi tunda bayina Ni a bangarena suke banasan siyi nisa dani a Daren yau mado Dole ze bar gari duk da hatsarin dake tattare da tafiyar say Amma Dole yase da ransa bamu San me wannan mutum yazo dashi ba bamusan alherin dake tare dashi ba sai ya warke




Cike da farinciki ta baro gidan tana zuwa kofar shiga gidan wazata gani sarki kaho fuskar Nan a tamke daga Ina kike munafika kinje wargaza auren gudan jinina ko to baki isaba in Banda kece mahaifiyar sa da tuni nasa anbatar dake Dan nasan bakya kaunar mu nida shi zan iya kashe ki akan Ja'e





Ta sheke da dariya kaho kenan da bakin ka kace nice mahaifiyar sa Dan haka baka Isa Kai min shamaki da Dana ba ba tsoron kasa a kasheni nake ba zan dai gayama ne kawai Dan ra ayina shawo kan yarinyar naje yi abun da ka kasa sai nuna Isa da iko akan Wanda ba danka ba ko danka baka iya tankwara shi bare Dan wani kuma sai gashi Ni makiyarsa na Samo Masa farinciki sabanin Kai masoyinsa daka kasa yarinya ta amince saboda Ni zata auri Dana Dan haka kaga karshen kiyayya kenan




Gashi dai magana tagaya Masa Amma kamar ta sashi a aljanna Dan farin ciki tabbas ta bashi farinciki be taba tunanin zata iya nemar wa Ja'e aure ba sai gashi ta fada karya ba dabi arta bace balle yace ita tayi ransa Kal ya kalleta




In dai ko hakane ki Fadi duk abunda kikeso zan Miki bansan kina San gudan jinina ba sai yau me kike bukata ai miki kinyi abunda mu muka kasayi Dole kema a faran ta Miki





Bana bukatar komai sai yarinyar ta zauna a sashena Dan haka take da bukata Ni Kuma farinciki shine namu Dan ta Mana halacci yarinyar





Hhhhhh in dai wannan ne an Miki Ankara muku bayi Mata guda goma sannan anhada muku da kyautar shanaye guda goma hhhhhh kin kyauta muna godiya masoyi yata a shirya yau a bangaren ki zan kwana





Tai tsaki a ranta base kazo ba badu yaja da ranka shanu Kuma mu bazami komai dasu ba gwara bayi kodan ita amarya Dan haka kabar shi karya kike Dole dake zan kwana yau Kuma baki ISA nayi kyauta ki dawon da itaba





Har zatai magana ya juya ya tafi fadawan sa suka rufa masa baya wata zuciyar tace karshema tun nakune suke ta albarka ki karba kici gaba da kula dasu harsuyi yawa kidawo da yawan shanunku ta share kwallar data zubo Mata saboda tunawa da iyayenta tabbas sai ta dau fansa akan sarki kaho ta juya ta nufi sashen ta






Ummata albishirin ki bukata fa ta biya suka rungume juna sunata ta murna umma harda guda afra Bata San wainar da suke toyawa ba batasan akan me ake maganar ba tace wai farin cikin me kuke ne abani Nima Nasha adara Dani ba a barni abaya ba Yar uwa




Cike da farinciki tace wallahi sis nayi babban kamu wannan dakika ganmu tare suhail ne Dan gidan alhaji ibrahim gadon kudi shine ze aure Ni Nan bada dadewa ba sai ki Fara shiri daga yau




Ido waje aure Jeddah aure yanzu kinsan a tsarinmu ba aure yanzu yaushema har kukai maganar aure dashi baki gayan ba a Ina kuka hadu baki taba gayan ba dama bazaman Amana kike Dani ba Ni bana iya boye Miki sirrina kece ke boyen naki




Mtsww kina da matsala wlh jiya muka hadu Kuma yace yana San aurena sai anjima zezo zami tsaida magana kinsan ba Wanda ze Fara ji sama dake Kece zaki gayawa wasu ma kece fa Babar kawa sai yadda Kika yi Sai abunda kikace a wajen bikin Nan





Hmmm shikenan yanzu naji zance Amma aranta Bata so ba Bata so Jeddah zatai aure ta barta ba tafiso siyi ta gantalinsu tare Dan Jeddah ita tabude Mata ido sosai gashi zata tafi tabar ta gaskiya bata ji dadin hakan ba ita kuma gsky yanzu karatu ma takeso ta koma Dan gayen jiya yy Mata alkawarin daukar nauyin ta





Cike da murmushi tace Tom kawata Allah yasan ya alkhairi yakaimu ranar Amma fa Dole mu jijjige zamu jajige muja magana wannan ranar ai Dole ne kawata kema aikin ce kinyi babban kamu jiya kema kawai ki aure shi ki huta kayya karatu zan koma gsky ayke kina da kwakwalwar karatu sai ki ta fama Amma Ni ko London ze kaini banaso Dan kin San yanzu ba kasar daba zan zaga ba a duniya suka sheke da dariya suka tafa




Aini saudiyya zaki Fara kaini Yar albarka in dawo inzama hajiya ai ban haifi tsiyaba arziki na Haifa Kuma shi zan ta karba har abada kema ki dage kisamo irin na Jeddah Dan Ina alfahari daku yayana nakai na sai umman mu suka fada cike da dariya suka mike suka koma dakin jeddah Bari inyi bacci kafin yamma tayi Dan nayi karya a gida nace anan zan kwana nagayawa baba kinsan kallon wata muguwar nutsatstsiya yake Miki kece kin iya badda Kama





Hhhhhh ba Dole ba ay indai ka goge da bariki Dole kasan hannunka saboda tsaro ba yadda za'ai ka Bari manya su ganoka ai sai kasamu matsala yanzu kinga Koda anzo bincike na hankali kwance Dan inawa tsofaffin layi ihsani





Suka Kuma kecewa da dariya shegiya Jeddah kinsan ta kan tsiya Dole a Sara Miki danga kyau ga fari komai zam zam diri dai sai dai agani a jikin ki shape kamar ke Kika kera kanki Dole maza sudinga ridewa Amma Dole zamuci uwar sabada a bikin ki kamar a mafarki Dan gidan gadon kudi zaki aura chab wai garin Yaya har Kika yarda da wuri haka tagama fasa Mata kai Nan ta zayyane Mata yadda akai tun daga farkon haduwar su har zuwansu wajen malamin





Suhail kasa tabuka komai yai faruk ne yajasu suka koma gida Dan yakasa control din kansa a hanya Dole faruk ya karbi kan motar suna zuwa gida ya wuce yabar faruk shi Kuma ya fice da motar ya tafi gantalinsa y a zube a daki ba abunda yake tunani sai ita surarta Amma tabbas ba Santa yake ba to meye shibe taba yaba kyan wata ba ko surarta sai Yar jaririyar sa haleema





Tunaninta ya cika Masa kwanya Dole yaje ya ganta koya huta da wannan tunanin Kobe ce Mata komai ba ya ganta tome ma zece Mata shida besa ba Hira da mata barkatai ba shi duk tarin masu zuwa wajensa da masu Kiran sa basa gabansa Amma wannan ta tsaya Masa arai Dole yaje yaganta ba shiri ya Mike ya zari wani key din motar kirar anaconda Fara Kal Tasha tintac ya dau hanya be tsaya ko inaba sai Dan gwauro





Yama rasa mezece yajeyi shiba number dinta ce dashi ba ya dai yi shahada ya Kira wani almajiri Dan Allah shiga kace Jeddah tazo suhail nasan ganinta zebata wani sako to wane sako zebata shi kansa be saniba yaron ya fito tace tana zuwa ya zaro dubu guda ya bashi yaran tsorata ya ki karba ya falfala da gudu sai yasa dariya abunma dariya ya bashi




ANAN ZAN DAKATA GASKIYA COMMENT YAI SANYI YANZU KO YADENA DADINE BOOK DIN NICE TAKU






*FEEDYN BASH*
[9/11, 22:29] +234 810 679 5647: *?ARNAN DAJI?*


*NA*


*FAREEDA ABDULLAHI*




*_?KAINUWA WRITERS?? ASSOCIATION_*??
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA MAHAIFIYATA ALLAH YAJA KWANA YA RAYA ZURI A*





*NASADAUKAR DA WANNAN PAGE DIN GA DUMBUN MASOYANA WANDA NASANSU DA WANDA BANSANSUBA AKO INA SUKE INA MUSU FATAN ALKHAIRI DAFATAN UBANGIJI YATEMAKEMU GABA DAYA YA BIYAMANA BUKATUNMU NIDA KU*



*JINJINA GA KAINUWA WRITERS ALLAH YA KARA WA ZUMA ZAKI DAN MASU SAI DA SUGA SUSHA HAUSHI????*


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JIN KAI*






70-75



Jeddah ta dalawa afra duka tashi kawata yazo wallahi yana waje narasama wane irin kwalliya zanyi wane irin kaya zan sa Dan na burge shi na tafi da zuciyarsa gaba daya tabbas malam yayi gaskiya suhail yazama nawa Ni kadai




Maza tashi ki shirya kina shegen zance sai ya tafi kinsan ba karamin mutum bane cewar umma data ke sawo Kai umma wanka zanyi ke banasan shashanci wankan ubanki zira Kaya ki gyara fuskar ki fita afra ko ta kasa magana kawai binsu take da ido ta rasa wannan San zuciya na umma da Jeddah ita dai Bata burin auren asiri tafi San na soyayyar gaskiya Dan shine ginshikin rayuwa Allah ya kyauta tafada a ranta




Cikin hanzari tasa wani less me kalar ja da ratsin ash dinkin Riga da siket ya karbeta duk halittun ta ba inda be fito ba tayi kyau na mamaki batayi wata muguwar kwalliya ba ta daura Dan kwalinta ta fito tashiga dakin umma Nan da Nan jiki na rawa tahau bulbula Mata turaren ita kanta jitai yana hawa Mata Kai ya isa Dan Allah umma wannan turaren ba Dadi kamar na Yan bori Dan Allah barshi haka karya kadani




To uwar kinibibi koma na meye shige ki tafi karki Mana asara ba malam ne yace yana shakar Saba sai dai wani bashi ba Kuma kinsan irin tsadar maganin nan maza ki wuce Yar albarka ki shigo dashi mu gaisa ta balla Mata harara ke kin cika rawar jiki wallahi daga zuwan farko zezo wani ki gaisa ko kunya bakya ji jibi fa yadda kike mtsww tayi ficewar ta




Ai tana dosar wajen sa yai mutuwar tsaye wani masifar kyau yaga ta kara fiye da dazu tana zuwa kusa dashi wani kamshi ya dake shi ya dafe kansa yafi minti biyar be dago ba itama Bata tanka ba gabanta yanata faduwa kodai zaton ya yahau Masa Kai sai taga yadago idanunsa sunyi jajur ya kalleta tadan firgita ita kanta dataga yadda idanuwansa suka Sanja kala suka rune Nan da Nan





Cike da kasala ya Fara magana Jeddah inasanki sai da tsigar jikin ta tashi Ina kaunarki zan aure ki a lokaci kankani Nan kusa zan aureki ki amince min zuciyata zata fashe bazan iya jurar kallon kiba batare da kinzama mallakina ba banasan auren mu ya wuce wata daya kiyi magana Dan Allah kar na mutu kirjina




Kamar zata zuba ruwa a kasa Tasha Dan murna zuciyarta Kal bukatarta ta biya me Kuma zata nema a duniya yanzu ta Gama samun duniya amma sai ta basar aure suhail aure kace fa bayan kasan faruk ke sona Kuma cikin wata guda Ni marainiyace Banda mahaifi sai mahaifiya mu masu karamin karfine kafi karfina kanemi dai dai dakai kawai nasan iyayenka nazasu yarda ka auren ba




Ambatar sunan faruk datai kamar ta watsa Masa ruwan dalma a zuciyarsa saboda masifar kishin daya yunkuro Masa Amma ya danne bakinsa har daci yake faruk ba aurene a gabansa ba yanzu ki bani dama na nuna Miki nafi kowa sanki a duniya zan aureki cikin lokaci kankani iyayena basu da matsa ba dukiya nakeso ba ke nakeso zaman lafiya nafi bukata sama da kudi wane irin kudine bamu mallaka ba daza a karbe duk abunda na mallaka abani ke nafi bukatar hakan akan komai ya wani marairaice Mata




Itako dake tasan komai ta wani basar chan tayi shiru kamar bazata Kara maganaba shikenan suhail nizan koma ciki Amma kaje Kai shawara da iyayenka Nima zanyi danawa Amma kagaya musu mu bamu da komai talakawane mu masu rangwamen gata Banda mahaifi sai danginsa a adamawa ta shiga matsar kwallar farinciki shi Kuma yadauka tunawa da mahaifin tane ko Kuma talaucin dasuke ciki ya kudiri aniyar ciresu daga kangin talaucin




Yakara narkewa a tausayin ta shike Nan zan gaya musu insha Allah cikin satin Nan za a Gama komai atsaida Rana kigayawa mamanku tasanar da danginku zan turo ga wannan ba yawa ya zaro rafar dubu dari ya Bata sai na dawo gobe ko kabar shi Dan Allah wallahi sai kin karba harda rantsuwa Tom nagode besan sutafi bukataba shikenan shiga gida dama sakon kenan yanata murmushi tashiga gida shi Kuma ya tada motar ya bar wajen





Yana tafiya yana tunanin Anya ma ko shine tayaya za ace yaje wajen wata ba haleema ba harda maganar aure tabbas idan be auri jeddah ze iya mutuwa ita yakeso da ita ze rayu ahaka ya karasa gida ya shiga sashen hajiyarsa yai sallama ya shiga suna tarema da alhaji ko tsoro Babu bare fargaba aransa ya shiga falon




Yauwa naji dadin ganin ku tare hajiya dama magana ce nakeso miyi daku daddy aure nakeso nayi cikin lokaci kankani cike da farinciki hajiya tace to candy Dinma bazaka barta tayi ba takarasa a dakinta saura shekara daya fa tagama kayi hakuri Mana suhail bansan ka da wutar ciki ba alhaji ma yai dariya kabari takarasa mana ko babban mutum ko dai kafara matsuwane ya fada cike da murmushi




Yai shiru ya numfasa hajiya ba haleema bace wata ce daban wannan mun hadu da ita a wajen bikin abokina Inasan ta sosai Amma talakawane shine nake Kara tausaya Mata so nake Nan da wata daya ai auren nan da sati daya nakeso agama komai sai asa bikin sati biyu kitemakamun Dan Allah yai rau rau kamar ze kuka




Hajiya jin abun take tamkar mafarki Kai suhail baka da hankali ko kafara shaye shayen zamani karka maida mu kananan mutane Mana ita haleeman kayi Yaya da ita ko Kuma so kake ka yaudarar musu yarinya wannan wane iskancine haka kaji yaro Dan Allah alhaji ya daga Mata hannu




Ya isa hajiya namiji mijin mace hudu ne Dan haka indai tanada tarbiyya zan aura Masa ita Amma da sharadin idan haleema ta karasa karatun ta ze aure ta wannan Dole ne hankali kwance yace na amince ko a rana days nema a daura hajiya kamar zatai bindiga yanzu suhail ko mahaifinka be zauna da Mata biyu ba sai Kai kana yaron ka dakai me kake nema haka indai wajen Nan ne kake kwadayi wlh saika gaji dayi mtsww




Ya isa hajiya cewar alhaji halitta halitta ce Kika sani ko yanada karfin daze iya jurewa Mata hudu ma Dan haka inbazaki Fadi alheri akan wannan lamarin ba kiyi shiru fatana ya kasance adali karna Kara jin bakin ki indai ba albarka zakisa ba tashi kaje zansa ayi binkice akanta Dan haka karka damu zan sanarwa iyayen haleema kaima kuma kagaya Mata to daddy ya Mike ya fita ransa Kal yanaso ya Kira ta beda number dinta ya manta be karba ba





Tana shiga tafara rawa a tsakar gida Nan uwar ta tayata afra ta fito ya akai ta kwashe komai tasanar musu dan haka kafin dare ma yayi zomu koma wajen malamin Nan afra tunda nagane ki zamanki bama sekinje ba umma wa wallahi Dole muje tare Banga ta zamaba haka suka dauki hanya sai gidan malam suka zayyane Masa komai yai dariya tabashi ragowar kudinsa takara Masa dubu ashirin yai Mata daurin baki saboda ko anzo bincike kowa yakasa aibata ta dama Kuma tana Dan musu ihsani duk da haka dai akara rufe baki saboda wayanda Bata sani ba afra ma tasa akama Mata gayen ta a hannu me suna Jameel yace ba matsala suka dawo gida suka shirya ita ta tafi nata wajen afra tabi Jameel wannan kenan




A ranar da iyar Ja'e ta koma tasa mado ya bar gari adaren ranar washe gari matarsa ta fito tana ta nemansa be kwana a daki ba Dan besaba irin wannan ba iyar Ja'e tace ta kwantar da hankalin ta zatasa ane Moshi labari yazagaye gidan ba aga mado ba hankalin kowa ya tashi Dan mado yanada kirki mutum ne na mutane




Rama ce take cirewa suhail Kaya Tai masa tik haihuwar uwarsa gaskiya wannan sura Tai Mata ga banana Masha Allah tagama kwadai Tuwa Amma Ina tasan ba fuska gaka ta tire Masa jikinsa tsaf fatar sai Tai duhu ya koma sak mado gaskiya tana sansa Amma yaza tayi tariga ta hakura tabarwa tenkwai duk da aure zatai Amma tasan na daukar fansa ne zata dawo wajen abun sonta




Sai ga aike daga iyar Ja'e nakayan sa irin nasu Tenkwai ta karba ta mikawa Rama Dan ita kunya

Please Login or Register in order to submit comment