Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

leda tace kashh! Ga turare amma ba garwashi ko dan ai akwai na ruwa.wata yar kwalbar turare naga ta fiddo sannan ta mike ta koma dakin. Da shigarta ta bude kwalbar turaren tafara bin kusurwoyin dakin tana zubawa sannan tazo ta kara zubawa a kan gadon. Su marsiyya ido kawai suke binta da shi.



Sanda ta gama tukun ta haye gadon tace ai nayi maganin ku kuma inma mayu ne in fatalwa ce kai inma aljanu ne sai mu gani. Yace ko layin nan nasan basu isa su ketaro ba balle ma ace sun zo gidan nan ba har su shigo dakinan domin na riga na daure su tsaff.


_na kalli nasmat nace bata san akwai wasu ma a cikin dakin ba_πŸ˜€


Bayan ta gama surutanta taja blanket dinta ta rufa. _Marsiyya tace ai kuwa bake ba barci_ Ba'a dade ba taji an fara kwankwasa kofa. Tace yasmeen! yasmeen! Shiru. Can an dan jima kuma sai ta dinga jin ana taba bargon ana dan ja sama kadan. Da sauri ta bude ta duba bataga komai ba.




Ta kara jan bargo ta rufa _kachau!- kachau!_ ta dinga ji a saman dakin Kamar ana kada karau-rawa. Tashi tayi zaune abun ya fara bata tsoro fa miye haka bayan kuwa kawu yace mata idan ta fesa turaren nan ba aljani ba zuwa ko kusa da inda aka fesa turaren nan. To ya akayi hk ko dai jabu ya bani ne.




Shiru taji an daina kada karau-rawar can jimawa kadan tana zaune kuma taji kara a ban daki kamar ana wanka. _*Shaaaa!* Karin zubar ruwa_


πŸ™„ shiru ta zubawa kofar ban dakin ido tana sake-sake a xuciyarta ta tashi ta leko ko kuwa ta kudun dune abunta a gado.


_(ni kuwa nace wllh dama kin kwanta abunki domin abun yafi karfin ki keda kawun naki)_


Kwantawa tayi taja bargo ta kudundune Tayi shiru ko motsin kirki bata yadda tayi. Shiru taji anyi. Kuma sai ta fara jin kukan jarirai da yawa ma ba daya ba.

_*inyarrr-inyarr* kukan jarirai_

Ya cika mata kunne saida ta toshe kunnuwanta da yatsa. a hankali ta cire hannun. Dariyar garada taji anayi a gaba dayan dakin.

_*hahahuhuhoho* dariyar garada_

Wani mugun tsoro ne ya shige ta domin an kure iya saninta layar da ke jikinta da kuma turarikan dama ita su take takama dasu karkarwa ta farayi. Domin tsoratatan da ake yi yayi yawa.

_(nasmat tace irin su kursiyya ai basa jin tsafin boka domin suma shedanun ne. Qur'an kadai zai fatatake su)_



Wani lokacin ma ji take yi kamar ana jan bargon sai ta ririke. Ji tayi ana girgiza kofar dakin kamar za'a ballata. Itadai batayi magana ba kuma bata dago kai ba. Can jimawa kuma ta fara jin wani iska mai karfi na busawa.

_*Fuuhhhh* karar fitar iskan mai kama da guguwa_ hade da wata dariya a cikinsa.




Da sauri ta tashi ta yace bargon. Ihuu ta kwalla sakamakon abunda ta gani. Gadan da take a kwance ne a sama wata rabe yake da kasa. Ga kuma wata guguwa da ke zaza gaya ta.




Kamar wacce aka ce ta kalli gefan ta na hagun.
_Wohuhu_

Wata muguwar hallita ce ta gani mai kawuna uku ko wanne kai kuma yana da idanu sunkai biyar. Da tana ganin nisan wajen saman da gadan yayi. Amma bata san lokacin da ta duro ba. A zaune tazo kamar ba ita ta fado ba. Ta tashi ta zungura a guje. Ta bude kofar ta nufi.dakin yasmeen.



Yasmeen na barci taji ana kwankwasa mata kofa. Hakan yasa ta tashi cikin barci ta fara tambayar waye?. Waye ne?



Cikin wata murya dake nuna mutun a razane yake anty hajara ke magana. Nice yi sauri ki bude pls yasmeen yi sauri ki taimaka kiyi sauri ki bude. Tana maganar tana waiga baya tana kallan dakin.



Yasmeen ta taso tazo kofar dakin ta kuma tambaya kece. Wa?. Daidai lokacin ne anty hajara ta hangi wani baki kirin din abu ya durfafo inda take.





Habawa kara rikicewa tayi ta ke bugwan kyauran nace miki nice hajara ke dawaye a cikin gidan in ba niba. Yasmeen bata bude ba tace au aunty hajara me kika taso yi a cikin daran nan yanzu around 2:30 o'clock fa πŸ™†πŸ½




Anty hajara ta kara juyawa taga abun gadan gadan ita ya nufo. "Na shiga uku ta fadi kmr mai shirin yin kuka yasmeen yanzu ba lokacin tambayoyi bane pls bude min kofa pls yasmeen. Yasmeen tace to anty key din ne ya makale yaki murduwa.



Hajara tace kash! Ta juya domin ganin nisan inda abun yake. Ashe ma bata ga abun tsoro ba saida abun ya kara matsowa gare ta. Taga fuskan nan fa ta fara buga kafa tana wani makewa jikin kyauran tana bugawa kamar ta fashe da kuka 😫 wata irin haliita ce sanye da bakaken kasa ga kusunbi a baya. Idanunta jawur hakoran dogaye sunfi tsayin babban dan yatsa ga wani irin hanci kmr na alade🐽 saidai shi baki ne.



Abun tafiyar fatalwa yake hannu a waware ga yatsotsin wasu mugayan farata ne zako-zako . anty hajara kamar ta sΓ ki ihuu sai dai kuma tana tsoran yasmeen ta rainata.badan abun na tafiya a hankali ba da tuni ya iso gare ta.


Kara tsurewa tayi ganin abun ya kara sauri yana tahowa wani tagal-tagal zai kamata kiris ya rage saura baifi taku biyu ba ya karaso taji kofa ta bude. Ta wani fada kan yasmeen yasmeen da sauri ta mayarda kofar ta rufe tana tambayar lafiya kuwa anty. Ya na ganki ma duk wani iri kamar a tsorace kike.




Aunty hajara da ta tabbatar ta tsira kuma taga alamu yasmeen bata ga abunda ta gani ba. " tace wllh cikinane ya murda. Ta dafe cikin tana yamutse fuska. Shine nazo in dan shiga toilet.



Yasmeen ta kalle ta tace " sannu aunty ya cikin fatan dai da sauki kash! Gashi ba maganin ciwan ciki a guna. Amma anty toilet ai akwai toilet a cikin dakin da kike. Jubi ne ya fara ketowa hajara domin ta rasa karyar da zatayi.............................................................
πŸ˜‚ *nace nasmat rike bairon nan da paper kici gaba da rubutun domin ni dariya taci karfina. Su yar gado an sambado kar......*😜


Little of writer's



King boy












πŸ™ŽπŸΏβ˜  MIJIN ALJANAH β˜ πŸ™ŽπŸΏ


page 83 - 84


|
|
na king boy isahπŸ‘‘
|
|
__________________________
🌟5STAR APR 2017 🌟
|_________________________|




***** 5 star *****
🌟5⃣STAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION 🌟 Β©5SWA
***** 5 star *****







_*NOTE* kawayen yasmeen ina so kuyi hakuri ku barni in cigaba da rubutuna hankali kwance kmr yanda na tsaraπŸ˜‡ ko dan tun farko laifi nane da ban fadi muku asalin yasmeen ba kuma ban fadi muku yanda suke da hajara ba. Da kuma yanda sukayi facali da addinin su muje zuwa dai in kukayi hkr zaku ji komaiπŸ˜€_ *luv u all fans wanda na sani dama wanda allah bai sada mu ni da shi ba.ina muku fatan alkhairi kamar yanda kuke min*









Anty hajara tace ni ai nama manta da cewa a kwai bandaki a cikine. Bata jira yasmeen tayi magana ba ta nufi ban dakin da sauri tana yan noke-noke yasmeen kallo kawai ta bita dashi bata kawo komai a zuciyarta ba ta hau gado abunta ta kwanta.




Anty hajara ta shiga toilet ta zauna kamar wacce datayi kashin da gaske. Sake-sake kawai take a zuciyarta wai kawu ya bata laya marar kyau. Ta dan jima a toilet din shiru tana zaune tana tsoran ta fito da wuri yasmeen ta gane ba kashin tayi ba hakan yasata yanke hukuncin tsayawa a ciki har sai ta dai-daici lokacin da yasmeen din tayi barci tukun sai ta fito.






A wannan shawarar ta kafu. Tana nan zaune ita kadai kan toilet kamar wace akasa dole sai raba ido take. Wani kyankyaso ne ya fado daga sama. _*diff*karar fadowar kyankyasan a kan tias_


Wata irin zabura tayi hade da yar kara bamai yawa ba. Saida ta lura da kadangaran ne kuma ta waiwaiga bataga komai ba tukun ta dan sama natsuwa.



Ji tayi ana shafar gashin kanta dake daure da ribon dake kan nata ba dan kwali dama hulace kuma ta baro ta a dakin umma. Da sauri ta waiga. Shiru bata ga komai ba. Juyowarta keda wuya wasu kyankyasan guda biyu suka fado _*tim*_ da masifan gudu tayo waje ko pant dinta bata ja sama ba. Sai a wajen. Allah yasa lokacin yasmeen barci ya fara debanta.



Anty hajara tayi ajiyan zuciya taje ta haye kan gadan yasmeen.nan ta dan tabo yasmeen lokacin ta tashi taga anty hajara na niyan kwanciya. Yasmeen tace ah aunty hajara ai dama saida nace miki tun farko ki dawo nan mu kwanta kika ki yan......


"Bata karasa maganar ba" aunty hajara tace ai ni badan komai na dawo nan ba sai dan zafin da ya dame ni amma da acan zan koma in kwana ai.

("ni kuwa nace in ba tsoro ba a koma mana. Lolz)



Yasmeen tace ai akwai ac. Eh naji akwai ac ai wutar dakin ce ta dauke baki daya. Kinga yanzu dai ba wannan ba ni barci nake ji. Ta juya baya ta rufe idanu.



Yasmeen tace ayi barci lafiya itama ta juya ta kama barcinta.


Su kursiyya parloo suka dawo suka cika shi da dariya irin tasu ta shedanu.

_*Hahahahuhuhhehehehekyalkyalkyalkyalkyakyakyakya* dariyar su kursiyya.lolz_


Kursiyya tace sister naji dadin zuwan ki gidan nan gaskiya gashi yanzu kinyi maganin wannan hajarar. Marsiyya tace wai ni waye kawunta ne boka ne kenan.

Kursiyta tace kwarai kawunta boka ne amma karamin boka. Dan Karya tafi yawa a lamarinsa.



Marsiyya tace ba kawunsu daya da yasmeen ba kenan?




Kwarai kuwa. Domin nasan asalinsu nayi bincike a kan yasmeen kwanaki domin in gano asalinta dan naga rashin addu'ar ta yayi yawa ba ruwanta da sallah balle xikiri yanzu dai bari in gaya miki yanda suke.



_maman yasmeen wato ramma wace suke kirada umma a baya ta taba aure kafin ta auri baban yasmeen Auren ta na farko wanda a shine ta haifi hajara din mahaifin hajara garinsu daya da umma can wani kauye ne a 9ja duk da garin musulmai ne amma tsafin su yayi yawa gasu da rashin imani_




Boka mai tabargaza baban boka ne a kauyen yanada yara biyu maza. Yayinda yaga mutuwa ta fara kusanto shi sai ya fara koya musu harkokinsa na bokanci. Babban dansa wato mujabir yafi dan uwansa kasumu ilimi da kwakwalwa. Domin shi yana daukar abubuwan da ake koya musu din sosai ba kamar kasumu ba da shi abun bai dame shi.



Boka mai tabargaza yana yawan gaya musu cewa su rike wannan harkar karsu bari ta kubuce musu. Sannan ya gaya musu cewa basu ba aure ba kuma kusantar mace yin hakan kuskure ne domin ko ku kafin in fara harkar nan na hafe ku. Nan dai suka kasance cikin daukar training a kullum.



Ranar wata asabar boka mai tabargaza ya mutu hakan yasa mujabir ya hau karagar mahaifinsa ta bokanci. Wata rana da yamma ya tafi neman wasu ganyayaki da kasar tururuwa a cikin daji.




Yana cikin tafiya can ya hangi wata kyakyawar yarinya ta nufo shi tana iho. Hakan yasa ya tsaya cik inda yake. Tana zuwa ta wani shige bayansa ta makalkale shi tana fadin ka taimake ni ka taimaka min macijine.




Shiru yayi ya dage kai sama wani dadi da dimin jikinta yana ratsa shi. Yace a zuciyarsa au ashe haka abun yake haka ake ji ashe in aka taba mace. Ashe dai mata da baba ya hanamu taba su haka ake jin dadi idan aka taba su.





Nan fa ya kudurci niyar sai yayi aure saidai in duk ya watsar da harkokin nan domin shi tun can farko dama mutun ne mai san yara nashi na kansa. Sai kuma gashi babansa ya sa musu iyaka da mata.




Yarinyar da take makalkale da shi wacce duk a tsorace take. A tunaninta macijin ya iso gare su har yayi wa mutumin illah.jin shiru yayi yawa yasa ta dago da kanta hade da sakin mujabir din.




Shi kuwa abunda bai so ba kenan domin bai ki su kwana a haka ba tana rungume da shi.



Yarinyar ta fara tambayars baiga maciji ba ina macijinda ya biyo ni.? Kyakyawar fuskarta kawai yake kallo yana Murmushi wai shin wannan Yarinyar yar nan garin ce.? Yake tambayar kansa.



Ke yar nan garin ce? Ya tambaye ta. Eh ni yar nan ce mana a nan aka haife ni. Ya sunanki.? Sunana ramma. Kaifa. Ni sunana mujabir ya fada lokacin da yake Murmushi.




Mujabir? mujabir? Ni kuwa ina ma nasan mujabir ta dan sa yatsa a kumatu ta alamun tunani. Au mujabir sarkin bakaye na garin nan ko. Murmushi yayi yace kwarai kuwa nine mujabir dan boka mai tabargaza. Ramma tace bakaga macijin da ya biyu ne bane?



Yace na ganshi mana gashi can. Ya nuna mata wani bangare a gefe. Macijin ne a saman iska shi ba sama ba shi ba a kasa ba. Yana ci da wuta.ramma sai da tayi yar kara. Taja da baya Tana fadin bana so bana so. Ya kalle ta miye bakya so.?



A nutse ta kalle shi tace kwata-kwata bana san tsafi shine abunda nafi tsana ma a rayuwata.

✍🏼Little of writer's✍🏼



πŸ‘‘King boyπŸ‘‘

From comment
08096831009
Number marsyyy 😜












πŸ™ŽπŸΏβ˜  MIJIN ALJANAH β˜ πŸ™ŽπŸΏ


page 85 - 86


|
|
na king boy isahπŸ‘‘
|
|
__________________________
🌟5STAR APR 2017 🌟
|_________________________|




***** 5 star *****
🌟5⃣STAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION 🌟 Β©5SWA
***** 5 star *****





🌷🌷ASSALAMU ALAIKUM BARKAKU DA SAFIYA FATAN KOWA YA TASHI LAFIYA KUYI HAKURI DA PAGE NAN DAI DOMIN IT'S VERY SHORT
😘😘 love u all my fans









Mujabir yayi shiru na yan wasu lokutan tukun ya dago kai ya kalle ta yace ina ne gidan ku?. Nan tayi mai kwatance wanda zai gane. Yace to shikenan sai kin ganni. Sukayi ban kwana tayi mishi godiya bisa taimakonta da yayi.




Har ta bace yana binta kallo wanda itama wasu lokutan tana juyowa in sun hada ido kuwa sai suwa juna Murmushi. To bayan mujabir ya cire abubuwan da yake so ya koma gida. Ya kira kaninsa wato kasumu yace mishi to shifa zai bar wannan harka domin kuwa aure zaiyi kuma baban su yace ba dama mutun ya rike mukami nan kuma yayi aure dan haka nidai ajiye wa zanyi idan zaka iya to.



Kasumu baiji haushi ba sai ma farin ciki da ya lulube shi domin dama yanzu yana san abun sosai.yace to yaya ba komai zanci gaba da yi ni. Nan mujabir yaci gaba da koya mishi surukan tsafi da wasu abubuwan na bokan ci. Bayan sati daya mujabir ya damka kambun sarautar bokanci a hannun dan uwansa wato kasumu.



A ranar yaje gidan su ramma inda ta kwatanta mishi tabbas ba karya yayi ba. Dake su al adar su lokacin idan kaje hira gun budurwa sai dai kawai ka shiga gidan. Haka yayi yana zuwa ya fada gidan kai tsaye kamar gidan su.



Da shigarsa ya iske su a tsakar gida ramma sai kuka take faman yi da alamu dai tsohon nata ne ba lafiya. Da sauri ya karasa gurin yana tambayar lafiya. Lafiya?.




Ramma ta kalle shi a lokacin ta kara fashewa da wani saban kukan wanda shi ya kara tabbatar mishi da mahaifintan baya da lafiya. Nan take ya kare mishi kallo yace ina da maganin wannan cutar a gida in kun amince inje in kawo.



Dan tsohon da yake a gangarar mutuwa ya dago yace aa yaro bana so domin ramma ta bani labarin ka cewa kai boka ne. To ka sani cewa indai kana san ramma tsakani da allah tafa dole ka ajiye bokancin nan kuma kabar hulda da aljanu. Wannan sune dokokin auren ta.




Mujabir ya kalle sa yacr baba in dan wannan ne karkaji komai domin ni tuni na bar wannan aiki yanzu dan uwana ne keyi. Domin tunda muka hadu da ramma naji ba wata ya da nake so kuma ba abunda nake gurin mallaka sama da ita. To kuma a lokacin nayi wani dan tsafi da ta nuna bata so sai nima naji kwata kwata abun ya fita a raina. Zuwa yanzu dai banzo nan gidan ba saida na tabbatar da na ajiye duk wani sihiri da harkan bokanci. Yanzu ni mutun Ne sak kamar kowa.



Da tsohon yaji haka yace to alhamdulilah ramma zo nan. Ta matso kusa. Yace bani hannunki yana kwance ta mika mishi hannun dama. Ya juya dubanshi ga Mujabir yace kaima bani hannunka. Mujabir ba gardama shima yaa mika mishi hqannu.




Nan Take tsohon ya damka wa mujabir hannun ramma yace na baka ramma amana ka riketa ammana bata da kowa bata da komai sai ni kadai ni kuwa nasan cewq wannan ciwan nawa ba na tashi bane dan haka ina rokonka da ka kular min da yata karka cuttar da ita.kuma ni in san samu ne ma ina rokon ka da ku tashi ku bar garin nan domin garin nan cike yake da matsafa miyagu marar tsoran allah.




Hawaye ya kwaranyo a fuskan ramma haka shima mujabir sai da ya share kwalla a fuskansa. Tukun yace to baba naji na karba kuma zan rike ramma a mana baza cutar da itaba zamuyi zama na amana zamu zama _*DANGIN JUNA* asmeey b ali_ 😘
Bazan bari hawayen ta ya sauka kasaba zan riketa kamar itace yar kawuna _*MAIRO*khadija candy_😘
Yana cikin magana sukaji hannun baba ya fadi kasa _*sharr* alamun dai rai yayi halinsa_




Gaba daya sai suka rude suka rikice nan fa ramma ta kwalla uban ihuuu wai kukaπŸ˜’πŸ˜‘

( _*pls yan uwana mata kukan mutuwa ba abune mai kyauba bama kamar wannan zamanin da muka maida abun kamar wani addini idan ma bakiyi ba sai ace ai baki damu bane ko kuma ace farin ciki kike da mutuwar ke.no! Ba haka bane kukan mutuwa ba abune mai kyau ba ku tuna. Lokacin da shugaban mu. Wato annabi Muhammadu S.A.W lokacin da zaiyi wafata da yarsa sayadda fatimatu zata zubar da hawaye. Yayi mata kashedi mai ban tsoro. Wanda yake nuna mana rashin dacewar abun. Sannan wasu matan ma abun kamar biki suka dauke shi domin kuwa in ban manta ba wani labari da ya taba zuwa min. It's true. Wasu matane su uku anyi mutuwa to shine suka taho gidan mutuwar. Sun kusan zuwa sai wata take cewa mu fara daga nan. Dayar tace aa ku bari sai munsha kwana. Ta tsakiyar kuwa cewa tayi ni wllh mura nake allah yasa muryar tawa ma tayi karfiπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜…. Wai kunsan me za'a fara kuka mutuwa wai irin naku mata wanda wai sai a dora hannu akai akama ihuu da borin karya ana fadin na mutu na lalace to kika sani ko a rubuta hakan daga kince kin mutu kin lalace kin shiga uku. Allah yaga dama yace mala'ika rubuta ta mutu ta shiga uku ta lalace. To kinga wa gari ya waya kenan. Tabbas akwai ciwo amma kiyi kukan ki na hankali kwance ba ki dinga ihuu kina harbe harbe kamar yar bori ba allah ya kyautayasa masu yi su gane su daina*_πŸ˜€)



Little of writer's


King boy















[6:36PM, 4/13/2017] ✍🏼KING BOY ISAHπŸ‘‘: πŸ™ŽπŸΏβ˜  MIJIN ALJANAH β˜ πŸ™ŽπŸΏ


page 87 - 88


|
|
na king boy isahπŸ‘‘
|
|
__________________________
🌟5STAR APR 2017 🌟
|_________________________|




***** 5 star *****
🌟5⃣STAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION 🌟 Β©5SWA
***** 5 star *****




Good night frinds have peaceful night




Ramma na kwala ihun kuka kafin kace me mutane rututu sun cika gidan nan akayi mishi jana'ixa mutane da yawa na yaban abban ramma mutun ne na gari domin duk fadin garin ma ba wanda ya kaishi kula da addini
Bayan sati biyu da mutuwar abban ramma aka daura musu aure ramna da mujabir sun dan yi zama a garin basu fi wata daya ba suka kwashe yan kayansu suka dawo dauraπŸ™Š




Al amarin kasumu kuwa. Ya zama kasurgumin boka nacuci azzalumi wanda har ya zamana cewa ya sama wasu shedanun aljanu guda biyu idan aka kawo mishi aiki na kisa su yake sawa su shanye jinin wanda za'a kashe. Idan ka kawo mishi aiki kafin ka koma gida tuni ya shanye jinin wanda kasa a kashe.
Kasumu dai ya zama _*hatsabibin boka* gentle lady_😘

Shanye jinin mutanen da yake sawa anayi hakan yasa suke kiransa da boka masha jini. Kamar kullum yauma yana zaune a _*karagar tsafi* zainudeen zain_

gindin wata katuwar itaciyar kuka ce. A nan yake xama shi ya baro cikin gari baya komawa cikin gari sai lokaci zuwa lokaci. Wasu mata ne. Guda biyu naga sun nufi inda yake din kamar muna fukai suke tafiyar.




Suna tafe suna waige-waige suna sauri-sauri da suka karasa gare shi sai dayar tayi sallama. Assalamu alaikum.
Tsawa ya daka mata ke dakata ba'ayi mana salama a gurin nan. Ya kalli dayar yace ke zulai baki sanar da ita bane. Sunkuyar da kai tayi tace kibru-da-kibsu su taimake ka ayi mata afuwa mantawa tayi.





Matar tace au'uzubillahi minah shaitan nurraj salamar ma ba'ayi? Wata tsawar ya kara daka mata tukun ya fara magana da kakausar murya. "Karki kara korar shedanu a wajen nan domin sune abokan aikin idan basu ki sani komai bazai yi ba.




Zulai tace kawata wai ke me yasa baki waye bane nan fa gurin boka masha jini muke idan karatunki zakiyi ko kuma korar shedanu ki bari sai kin koma gida amma ba a nan ba.wai ni inace bukatarki ce ma ta kawo mu nan. To wllh idan kika sake wani kuskuren ni da kaina zan hana boka yayi miki wannan aiki. Ah kaji min mata an gaya miki shi boka aikin allah yake yi ne.
Ayi hakuri na daina bazan karaba. Matar ta fada. tana fadin haka boka ya wangale baki yana wata irin dariya. _*Hahahahah* dariya_
Tukun yace dadai yafi miki yanzu kafin ki fadi me ke tafe dake muna bokatar ki cire hijab din dake jikinki.hahahaha.




Murja ta kalli zulaihat ta zaro ido hijab kuma. Zulaihat kinfa san ni matar aurece ko. Zulai tace kinga malama ki cire hijab kawai kamar yanda boka ya umarta ke dai ba biyan bukata keke so ba. Inace kece kika ce min ko kunciya zaiyi dake indai bukata zata biya to ke ba matsalan ki bane. ?
Boka yayi fakarai da kunnuwa yana sauraren maganar da suke yi ashe.


Murja zatayi magana. Taji boka ya fashe da dariya wacce har saida tasa su biyun suka dan zabura.cikin wata magana mai hargowa yake fadin cewa. Hahahaha ku tashiku bani guri in dai kunsan baza ki iya bin umarnin boka ba. Hahaha.





Da sauri zulai tace afuwa dai boka kibru- birsu su taimake ka. Xata bi duk umarninka.




Nan take murja ta cire hijab.😧 wooo. Tubarkallah. Nan fa na kara gamsuwa da sirrin hijab hakika allah mai hikima ne. Da ya sa wannan sutura ta tsare mutunci ga matayen mu. Wato hijab.




Domin yanda murja take kyakyawa haka ga na fulani kamar zasu fasa rigar. Su fito dan girmansu . amma hijab ya rufe wannan asirin idan ka ganta da hijab bazaka taba tunanin hk take da girman. Na fulani ba.




Juyawa nayi ga boka dan jin yayi shiru. Mamaki ne ya cika ne ganin yanda ya tsare murja da kallo yana bin duk sasan jikinta da wani mayen kallo bama kamar gabanta wanda yake a ciki kusan rabi a fili.
Boka! boka! boka! Zulai take kiransa. Sai a kira na hudu tukun yayi firgigit ya dawo daga duniyar tunanin da ya fada. Wato tuni surar jikin murja ya tafi da gaba daya imanin sa gaba daya.




Murja tace kace ta cire hijab kuma gashi ta cire baka ce komai ba kuma ka tsaya sai kallanta kake. Boka yace ba haka bane ina dan wani tunani ne. Ina jinki fadi min me ke tafe dake yayin da ya juya ga murja.



Murja tace wato a gaskiya boka abunda yake tafe dani shine kishiyata ce gabaki daya ta kwace min miji na rasa gane kansa nabi bokan nabi malaman amma ko'ina naji shiru domin wai cewa suke ita din mai kula da addini ce tana yawan shayuwar dare kuma wai idan zata kwanta tana karanta.Al falaq...an naas...an nasr wai shiyasa duk abunda aka aika

Please Login or Register in order to submit comment