Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

itama sai ta fara canza suffarta. Itama ta koma wata dudanniya. Mai ban tsoro.




turaren mayu kuma saboda mu. To waye zai aikata haka. Ko dai boka suka dauko. Hmm ai kuwa da yaci ubansa indai boka ne. Kinga taso mu shiga cikin gidan.


Bacewa sukayi sai gasu sun bullo a cikin parlo. Nan ma sukaga kaskon wutar. Dakin yasmeen suka bullo. Nan suka iske su yasmeen tuni sunyi barci. Marsiyya tace inaga fa ba wani abu sune da haukansu kawai suka kunna wancan hayakin..............................................................................


Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks





โœ๐ŸผAutan marubuta โœ๐Ÿผ



๐Ÿ‘‘King boy๐Ÿ‘‘














๐Ÿ™Ž๐Ÿฟโ˜  MIJIN ALJANAH โ˜ ๐Ÿ™Ž๐Ÿฟ


page 103 - 104


|
|
na king boy isah๐Ÿ‘‘
|
|
__________________________
๐ŸŒŸ5STAR APR 2017 ๐ŸŒŸ
|_________________________|




***** 5 star *****
๐ŸŒŸ5โƒฃSTAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION ๐ŸŒŸ ยฉ5SWA
***** 5 star *****











Dakin umma suka nufa. Dakin a kulle suka ratsa ta jikin bango suka wuce. Mamaki ne ya mugun kamasu. Ganin kasumu mashe-mashe sai barci yake a kan gadan kursiyya. A gefan sa kuwa wannan yan guntayen aljannun ne. Suna gadinsa. Marsiyya ce ta daka musu tsawa kaii! Me kuke yi a nan. Wata muguwar zabura sukayi. Bama da suka juyo suka ga marsiyya ce. Sunsanta sarai. Yar sarkinsu ce. Gaisuwa suka fara kwasa suna tuba. Dai-dai lokacin boka ya farka yana jinsu amma ya lumshe ido kamar me barci. Koma yaki yarda yayi motsi ko kadan.


Kursiyya tace. Wannan kuma da kuke tsaro shi din wayene?. Daya daga cikinsu yace shi din uban gidan mu ne a karkashin sa muke aiki. To me ya kawo shi gidan nan?. Eh zuwa akayi aka dauko shi wai domin yazo ya fitar da aljannun gidan nan. Hahahahahahaha. Marsiyya tayi dariya tukukun ta murtuke fuska. Ta harari boka dake kwance. Da jajayen idanta tace. Au wai shi wannan dan bashi da kunya mu yazo ya kora. To bari in shekaka lahira kafin ka fitar damu. Din. Karkarwa boka ya farayi a cikin bargo kamar ya kwalla ihoo. Dan tsoro.



Hannu ta dan mika sama. Sai ga wata sharbebiyar wuka sai kyalli take ta bayyana a hannun. Dagawa tayi da niyar ta cakawa boka a makogwaro. Cikin hanzari ya mike yana nishi day-daya ya daga hannu biyu yana rokonsu. Dan allah kuyi min rai ni ba bokan gaskiya bane.ni makaryaci ne. Kawai kasuwanci na mayarda abun. Yana maganar kamar wanda zaiyi kuka. Dariya sukayi su biyun gaba daya. Hahahaha-hahahah saida sukayi mai isarsu. Tukun. Shidai kallansu kawai yakeyi.




Marsiyya ta kara bakinta gurin kunnusa ta dade tana gaya mishi wani abu. Saidai duk yanda na matsa domin inji me take fada. Banji ba. Dole sai hakura nayi. Bayan ta gama gaya mishi maganar naga boka yayi likis. Zuwa can kuma ya dago kai yace idan akayi haka zadai ku barni in tafi ai ko?. Kursiyya tace karkaji komai zamu barka ka tafi. Kaida yan komatsan ka. Yanzu dai sauko daga kan gadan nan. Hawa kan gadan ma da kayi sai nayi maka hukunci. Miko min hannunka. Da sauri ya mika. Dogon farcin ta mai tsini tasa ta dan yanke sa. Jini ya fara fita. Da sauri ya matse gurin. Maza ka koma falo. Da sauri boka ya tashi ya fita a dakin falo ya dawo yana ajiyar zuciya. Sannan kuma sai tunane-tunane yake yi na maganar da marsiyya ta gaya mishi.




Washe gari tunda sasafe. Su Yasmeen suka tashi sukayi wanka sannan suka fito suka nufi kitchen domin hada dinner. Sunsha mamaki da suka tarar da kawu a daki. Da sauri hajara ta karasa. Gurinsa ta tashe she shi tana tambaya lafiya kuwa kawu muka ganka a falo.? Boka ya tashi yana yan waige-waige tukun yace uhmm da kinsan uban artabun da mukasha da aljanu jiya da dare. Da sai kin jinjina min.



Ashe dai aljanun gidan nan naku sun wuce adadi.kuma ni ban taba ganin tsagerun aljanu masu taurin kai ba sai jiya. Kinsan ance sarkin yawa yafi sarkin karfi. To jiya sarki yayi iya bakin kokarin sa na yaga ya fitarda su daga gidan nan amma abun yaci tura. Har saida ya gaji ya barni dasu. Nan fa na nuna musu cewa ni dan gado ne. Kinga wannan ciwan kadai suka sama nasarar yi min. Da sauri hajara ta kamma hannun tana dubawa ayya sannu kawu. Nake ganin ma wannan ai kamar sawun farce ne?.



Eh mn farcen wata yar.... Bai karasa ba yaga marsiyya ta bullo a bango tana hararen shi. Hakan yasa yayi kwana. Yace farcen wata yar sarkin aljanu ce. Lokacin Yasmeen tace to kawu fatan dai anyi nasara? An kore su?. Yayi murmushi yace ai ynz gidan nan ba aljani ko daya. Domin gabaki daya na kore su jiya. Dan haka ku kwantar da hankalinku. Kuma zan tsaya inyi kwana biyu a nan dan tabbatar da tsaro. Yasmeen cike da murna harda dan tsalle na jin dadi. Tace mun gode-mun gode kawu. Bari mu shiga mu hado kayan kari..



Misalin karfe biyu naga motar al ameen. Ta shawo kwana a guje. Yazo daidai gate. Yayi oda. Da sauri M. Lawal ya zo ya bude. Bayan ya bude ne. al ameen ya shigo yayi park. Yace kai M.lawal zo nan. Da sauri m.lawal yaje ya duka yanayi mishi sannu da dawowa. Tsawa al ameen din ya daka mishi. Cikin tsiwa kuma ya haushi da fada. Wai yana jin mutun nayin hurn amma yaki zuwa ya bude kofa da wuri. Saida yayi mishi fada sosai shidai M.lawal hakuri yake ta faman badawa. Yana kuma tunanin yanda mai gidan nasu ya canza haka. Domin bai taba yi mishi abu makamancin wannan ba.



Al ameen ya juya a fusace ya shiga cikin gida. A falo ya tarar da . Yasmeen ita kadai zaune take tana chat tayi wanka. Tasa ka wata hadadiyar yellow atampa mai kwaliyar flaws. Dinkin riga da sket sunyi mata kyau sosai sun kama jikinta. Tsayawa yayi a bakin kofar yana kallanta yana murmushi. Ita kuwa hankalinta yana kan waya sai murmushi take ita kadai. .


Da dai yaga bata da alamar tasowa. Sai yayi gyran murya. A'ehhm! Da sauri ta dago kai. Idanunta basu sauka a kan kowa ba sai al'ameen. Wulli tayi da wayar ta saka yar kara ta nufo kanshi tana oyoyo-oyoyo taje ta wani rungume shi. Kamar wacce data shige jikinsa. Nan fa ta shiga. Kukan shagwaba. Um! uhm! um! A shagwabance take magana shine zaka tafi ka barni har na tsawon kwana biyu ko?. Jin yayi shiru kuma ya kame kamar gunki. yasa ta dago ta kalle sa domin taga me ke faruwa.




Lokacin data kallesa ta lura da wani waje ne ya zubawa ido hakan yasa ta juya baya domin taga me ke faruwa. Gabanta ne yayi mumunar faduwa. Kawu ne a zigidir daga shi sai gajeran wando yana yan matse-matse irin na muna hicci. Kuma shi al ameen yake kallo............. ....... . ........................ . .............................................



Turkashi!!!!!!! Me yake faruwa ne. Na tambayi nasmat??????



Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks





โœ๐ŸผAutan marubuta โœ๐Ÿผ



๐Ÿ‘‘King boy๐Ÿ‘‘





๐Ÿ™Ž๐Ÿฟโ˜  MIJIN ALJANAH โ˜ ๐Ÿ™Ž๐Ÿฟ


page 105 - 106


|
|
na king boy isah๐Ÿ‘‘
|
|
__________________________
๐ŸŒŸ5STAR APR 2017 ๐ŸŒŸ
|_________________________|




***** 5 star *****
๐ŸŒŸ5โƒฃSTAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION ๐ŸŒŸ ยฉ5SWA
***** 5 star *****






allah ya baki lafiya sister *๐Ÿ˜ซibrahim Fatima*๐Ÿ˜ซ ku taya ta da addu'a yan uwa






al ameen ya nunasa da yatsa yace yasmeen waye wannan. zatayi magana ya daga mata hannu hade da yi mata tsawa. dakata yasmeen dama cin amanata kike yi idan bananan kin cuce ni yasmeen. Yasmeen me kika nema a gurina kika rasa?. kuka ta fara tana so tayi mishi magana amma ina kuka yaci karfinta.



.daidai lokacin anty hajara ta shigo falo din. tsayawa tayi cik ganin abunda yake faruwa. ta kalli. kawu dake faman raba ido.tace kawu miye haka kake yi lafiyan ka lau kuwa?. Sannan ta juya da murmushi ah al ameen yanzu ka dawo?. Yasmeen me ke faruwq ne. Naga kina kuka! Wani abu ne ya faru. .


Al ameen bai saurare ta ba. Karasawa yayi gaf da kawu. Boka kuwa sai wani makyarkyata yake yi. Waye kai me ya kawoka gidana. Tambayar da ta fito daga bakin al ameen din kenan.


Kawu ya tsaya inda-inda ganin hakan yasa al ameen ya daga hannu ya sharara mishi mari. Hade da cewa fada min kai waye.. Zan fada zan fada. Su Yasmeen kuwa kallo ne kawai nasu. Boka yace ni sunana tasi kuma ni tsohon saurayin Yasmeen ne. Tana sona ina santa hakan yasa duk lokacin da baka gida. Take gayyato ni domin har ynz tana sona. Idan nazo wuni nake a gidan nan muna soyewa.



Wani marin al ameen ya kara kai mishi hade da cewa tsohon banza kawai kai ko kunya baka ji ba?. Wannan yarinyar baka haifeta ba?. Su hajara kuwa mamaki ne ya cika su. Shin me ya samu kawu anya kuwa lafiyarsa. Yasan abunda yake shirin aikatawa kuwa?. Yasmeen. Kasa ta zube da gwiwoyinta. Tana kuka tana fadin wllh karya yake. Al ameen. Wllh kawun hajara ne. Kuma magani yake bayarwa mun dauko sa ne domin ya fitar mn da aljanun dake cikin gidan nan. Kum...... Bata idasaba ya daka mata tsawa me zaki gaya min.



Kin dai riga kinci amanata ban taba tunanin zaki min haka ba Yasmeen kin dade ashe kina cin amanata ke da wannan.ya kamo kwalar rigar kawu ya jijiga. Yace amma sai yau allah ya toni asirin ki dama ance rana dubu ta barawo daya tall ta mai kaya. Kuma shi ramin karya kurare ne. Dan haka yasmeen kije na sakeki saki 1 ki tatara kayanki ki bar min gida yanzun nan.



Juyawa yayi ya kalli bokaTukun yace me kaka jira a nan bazaka bace ba ko so kake in hadaka da hukuma ne? Da sauri boka ya tatara nashi ya nashi ya fita a guje. Har yana tuntube. Yasmeen kuwa ita da anty hajara magiya suka shiga yiwa al ameen yayi hakuri ya saurare su amma ina banxa yayi dasu. Dadai suka ga abun nashi ba alamar zai yi hakuri sai suka tashi. Yasmeen ta dauko kayanta.



Tana tafiya tana waigowa tana kallansa tana zubda hawaye. Shi kuwa gogan naku ko kula ma baiba.


Haka suka fita. Basu hau motar gidan ba napep suka tara suka hau cikinsu kowacce da abunda take tunani. Can Yasmeen tace aunty hajara kinga abunda kika jawo mn ko. Kinga abunda kawu yayi mn ko.? Laifin me nayi wa kawu ne. Ta fada cikin kuka. Cike da tausayi hajara ta juya ta dafata. Kiyi hakuri Yasmeen haka allah ya tsara amma koni nayi mamaki sosai abunda kawu ya aikata mn kamar wanda aka sashi dai wannan sharrin ai yayi yawq. Gaskiya al amarin nan abun a duba ne.


Dai-dai lokacin suka karasa kofar gidansu. Bayan sun biya mai napep suka shige ciki. Yasmeen na hada ido da umma ta fashe da kuka ta ruga da gudu ta fada jikinta. Umma ta fara tambaya lafiya?. Lafiya?. Lokacin hajara ta karaso gurin jiki ba kwari kamar kazarda kwai ya macewa a ciki. Umma da taga dai Yasmeen bata da niyar yi mata magana. Sai ta juya ga hajara tana tambaya minene?. Lafiya ku fadamin mana. Duk ta wani rikice. Anty hajara tafiddo farar takardar ta mika mata. Gabanta ne ya fadi. Hajara ta miye kuma wannan takardar miye. Yasmeen cikin kuka tace umma ya sake ni. Dumm!" Gaban umma ya fadi ta dafe kirji saki saki fa kika ce?.



To me kika mishi da ya sake ki bayan baku taba ko samun sabani a tsakanin ku ba to taya zai sake ki. Me kika yi mishi?. Yasmeen tace ban mishi komai ba. Aa ba wannan zancen shi mahaukaci ne da zai sakeki ba laifin fari balle baki? Kudai fadi min gaskiya. Su Yasmeen raba ido suka shiga yi.


Tayi tayi dasu amma fur! Suka ki su gaya mata abunda ya faru. Tace to shikenan bari babanku ya dawo tunda kun rainani ai shi kwa gaya mai...............................


FRIENDS KUYI HAKURI DA WANNAN DAN KARAMIN PAGE DIN GOOD NIGHT.
*SHIN ME KUKA FAHIMTA A CIKIN AL'AMARIN NAN?*









๐Ÿ™Ž๐Ÿฟโ˜  MIJIN ALJANAH โ˜ ๐Ÿ™Ž๐Ÿฟ


page 107 - 108


|
|
na king boy isah๐Ÿ‘‘
|
|
__________________________
๐ŸŒŸZAMANI APR 2017 ๐ŸŒŸ
|_________________________|




***** zamani *****
๐ŸŒŸZAMANI WRITER'S ASSOCIATION ๐ŸŒŸ ยฉZ.W.A
***** zamani *****










su yasmeen na fita daga gidan al ameen ya fashr da wata mahaukaciyar dariya. hahahahah- hahahahaha- hahahahaha. nan take naga kursiyya ta bullo. itama dariyar take. zuwa tayi ta rungumi al ameen din. cikin murna da farinciki. tace sis tsarin ki yayi ina ji dake ina sanki ina kaunarki miye tsari na gaba?.



fatar al ameen din naga tana banbarewa. abun mamaki jikin marsiyya ke bayyana. ( kadan ta hana in sume. a gun. har sai bayan one week in farfado.lolz) bayan ta gama juyewa ta dawo asalin marsiyyarta tace. yanzu gida ya dawo hannunki aunty ke zaki dinga tafiyarda komai. yanzu Yasmeen zaki dawo. bata rufe baki ba naga kursiyya tayi juyi ta dawo Yasmeen sak ba wani banbanci. good aunty yanzu sai musha shagalin mu a gidan nan kafin al ameen ya dawo. ko ya kika ce. kursiyya tace haka ne fa kuma hegiyan yarinya akwai kwanya hiyasa nake sanki.





kasumu zaune yake yayi tagumi duk abun duniya ya ishe shi. wannan wace irin rayuwa ce. haka shidai tunda ya taso har yanxu bai aikata wani aikin alheri ba.abunda ya aikata yau yake tunawa. tabbas ya aikata babban kuskure. amma ya zaiyi. yasan idan baiyi hakan ba tabbas sai sun haukata shi tunda suka umarceshi da yayi din. to amma da wane ido zan kalli Yasmeen da hajara?.
wasu zafafan hawaye ne suka kwaranyo a fuskarsa.



yanzu kam cike yake da nadama. shi harkar bokan cin ma ji yayi kwata-kwata ya tsane ta. kallo daya zakayi mishi kasan yana cikin damu. wani shago dake kusa dashi yaje ya sayo ashana yazo ya cinnawa. kayan bokan cin nasa. ya koma gefe yana kuka domin shi yanzu baisan abunda zaiyi bama allah ya yafe mishi. domin ya kashe mutun yafi a kirga ya haukata wasu kuma yayi zina da matan aure ma. banda yan matan da yayi dasu masu zuwa gurinsa neman wata bukatar. durkushewa yayi a gurin yana kuka.





hahahaha-hahahaha. mahaukaciyar dariya yaji a saman kansa. daga kai sama yayi. wani makeken dodone. kamar video haka ya cika fadin saman. a tsorace ya dinga jan gindi yana neman wajen labewa.kasumu kenan bazaka taba samun damar fita a bokancin nan ba tunda ka yarda ka shigo ka shiga kenan. hahahaha. hahaha. cikin wata katuwar murya ake maganar mai fitowa da karfi hakan yasa saida ya toshe kunnuwa. kasumu! kasumu! ka dawo sana'ar ka indai mata ne ko dukiya ke tsone ma ido ta zamu baka su. muddin zaka dinga yi mana sujjada kamar yanda ake yiwa allah. (wa'iyazubillah) kasumu har ya fara amijcewa da zancen da yaji shedanin nan ya ambaci sujjada. a fusace ya daga kai sama ya kalle sa yace.



" na tuba bazan kuma yiwa wani aljani ko shedani sujjada ba. Wanda nayi muku a bayama. Allah zan roka ya yafe min. Shedanu kawai mugaye azzalumai. Allah yafi karfin ku ai kuma na fita daga bokancin inga wanda ya isa ya mayardani. Wani alh. Da ke wucewa a hanya. Naga ya tsaya sai kallan kasumu yake dake duk maganar da yakeyi a bayyane take. Ana ji. Mutumin kuma yaji duk abunda kasumun ya fada. Da sauri alhj. ya karasa gurin. Ya fara tambaya bawan allah lafiya. Lafiya kuwa. Kasumu kuwa sai huci yake kamar wanda yasha dan karan gudu. Abun mamaki mutumin na zuwa wajen kasumu ya bar ganin aljanin.




Alhj ya tambaye shi lfy kuwa. Bai boye mishi ko mai ba saida ya gaya mishi duk abunda ke faruwa da yake yana bukatar taimako. Alhj yace. Ba damuwa ka iya ayyatul qursiyya? Kasumu yace miye haka din? Alhj. Ya kama baki yace dan kari! Ah dole aljanu su takura maka. To da yake dai tana da dan tsawo baza ka iya rike ta duk a yanzu ba. Abun da nake so dakai yanzu shine kata fadar ุงุณุชุบูุฑู„ู„ู‡ ูˆุงุนุชุจ ุนู„ูƒ sanda aka sha fama tukun ya iya istigfarin. Mutumin yace yanzu ina zaka?.




Kasumu yace shi kam yanzu baima san ina ya nufa ba. Domin bazai taba komawq kauyen can ba. Idan ya koma yasan kara fadawa cikin kafurci zaiyi. Alhj yace tashi biyo ni muje gidana. Ba gardama ya bishi. Har a lokacin kasumu na fadar astag'firullah.



Karfe hudu na yamma abba ya dawo daga gun aiki yayi mamaki da ya ga su yasmeen a gidan amma bai nuna ba. Bayan su gaishe shi hade dayi mishi sannu da zuwa. Umma ce ta karfi jakan ta shiga gaba ya bita baya har suka kai dakin sa. Da suka shiga yake tambayar umma.me ya kawo yasmeen gida. In ma ziyara ne ai ynz dare ya farayi. Umma ta fiddo takarda ta mika mishi. Ya karanta ( what ya sake ta) cos o what? A kan me al ameen zai sake ta. Umma tace nima dai ban sani ba kuma nasan al ameen bazai aikata wannan mumunan aiki a hakanan ba. Domin yaran peace-loving ne kaima ka sani kaga dai tun da akayi auran nan har ynz ba' wata matsala data taba shigowa a tsakaninsu.



Nima hkn na gani domin al ameen is fair minded. But kirawo min ita. Umma ta fita ta kirawo yasmeen yare suka shigo. Dady ne ya zare mata ido yace gaya min me kika yi mishi ya sake ki. Dady wllh ba abunda nayi masa. No! Hakan bazai yoyu ba. Dole akwai abunda kika yi masa. Yayi yayi da ita taki fada. Hajara ce kamar wacce aka wullo daga sama ta shigo dakin. Haba yasmeen ki fada musu gaskiyar abun da ya faru mn. Tunda kinsan baki da laifi kuma nima shaida ce. Nan hajara ta fara basu labarin duk abunda ya faru tun daga kiranta da yasmeen tayi har kawo yau.



Abba yayi ajiyar zuciya. Yace to kinji ba. Ga gaskiya ai. To waye zaiga kato a gidan sa. Kuma baya nan kuma yaki zarginki. Ai ni abunda yayi yamin daidai kuma ko nine hakan zanyi. Kuka yasmeen ta farayi. Yace kukan me kuma kike tashi ki bani guri ni. Kuma ki sani nidai bazan dauki kafata inje in basa hakuri ba. Da wane ido zan kalle sa?. Ga gidan nan sai kita zama idan yaga dama yaxo ya nemi ki koma dakin ki to babu laifi idan kuma baizo ba to nidai bazan je bada hkr ba domin tsuntsun da ya jawo ruwa?.



Gida ya zama na su kursiyya kwana biyun nan sharholiyarsu kawai suka sha. Ga mugun kazamta cikin su ba mai shara ko goge..................................................................
โ™ฅ HAPPY โ™ฅ
JUMA'AH MUBARAK
โ™ฅ โ™ฅ




Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks





โœ๐ŸผAutan marubuta โœ๐Ÿผ



๐Ÿ‘‘King boy๐Ÿ‘‘
















๐Ÿ™Ž๐Ÿฟโ˜  MIJIN ALJANAH โ˜ ๐Ÿ™Ž๐Ÿฟ


page 109 - 110


|
|
na king boy isah๐Ÿ‘‘
|
|
__________________________
๐ŸŒŸZAMANI APR 2017 ๐ŸŒŸ
|_________________________|




***** zamani *****
๐ŸŒŸZAMANI WRITER'S ASSOCIATION ๐ŸŒŸ ยฉZ.W.A
***** zamani *****




๐Ÿ˜‡ ASSALAM.BARKANKU DA SAFIYA TO ALHAMDULILAH NA SAMA LAFIYA TUN KWANA BIYU DA SUKA WUCE JIKINA YA WARWARE. INAYIWA DUK MASOYANA MASU KIRANA DA MASU AIKA TEXT GODIYA. KUMA ISHA"ALLAH KAMAR YANDA NAYI ALKAWARI TO ZAN KWATANTA HAKAN WATO POSTS UKU A RANA. MUJE ZUWA. LOVE YOU ALL MY FANS โ™ฅ




๐ŸŒท๐ŸŒทIN DEDICATED TO UR MY BEST AUNTY. MMN ALI.

bakina bazai iya burta godiya a gare ki ba. Badan komai ba sai dan ya rasa kalar wacce zaiyi din a gare ki ๐Ÿ‘๐Ÿผ na gode da kulawa allah ya baki abunda kike so duniya wa lakhirah โ˜บ na gode da kulawa. Love u too much my aunty



(_*After 3days. Da sakin yasmeen*_)


Zaune suke a falo kursiyya ce cikin shigar Yasmeen ba banbanci ko kadan. Marsiyya kuwa na zaune a kusa da ita suna hira.



Salamar da sukaji ne yasa marsiyya ta bace da sauri. Kursiyya kuwa ta tashi ta nufi kofa tana tambaya waye. Cikin wata murya a shagwabe take maganar. Yasmyy nice.
.


Ke wa? Hmm kina so kice kin manta da muryana ko yasmeyy?. Kursiyya tama rasa yanda zatayi domin kuwa idan ta bude matar zata gane ba Yasmeen bace. Muddin in bata san sunanta ba. Matar ta dade a kofa tana bin kan Yasmeen ta bude kofar amma taki. Yasmeen tayi rantsuwa tace wllh indai baki fadi sunanki ba to saidai ki koma ni kuwa bazan bude ba.




Dadai taga lalai Yasmeen da gaske take bazata bude ba tace. Haba yasmeen asiya ce fa. Kawarki wace kuka karasa makaranta tare. Ohh asiya wa? Hmm asiya Muhammad(Reality) da sauri kursiyya ta fuske ta bude kofar tace yar rainin wayo ai naso ace kinyi min gardama da sai na bari kin juya tukun in bude. Amma tun farko ina sane na kuma gane ki. Kawai dai yau tsokala nake ji. Asiya ta wani murgude baki. Tace ni kuwa wllh har nayi fushi da tafiya ma zanyi abuna.





Ohh! Srry sister wasa fa nake miki. Ta jawo hannunta shigo mn. A shagwabance ta shigo tana kunbure baki tana tatokarewa. Marsiyya kuwa tana gefe sai hararen ta take. Dake ita bata ganin Marsiyya.

( ni kuwa nace indai su Marsiyya ne ai da gudu zaki fita a gidan๐Ÿ˜€)

Bayan ta zauna Yasmeen ta tafi domin hado mata juice๐Ÿท ita kadai a falo sai raba ido take. Ji tayi anja gashin kanta da dan karfi daga baya. Tace haba Yasmeen miye hk ko so kike ki tsinka min gashi. Shiru din dataji yasa ta waiga bata ga komai ba wajen wayam. Bata damuba ta juyo abunta.




Taci gaba da harkokin gabanta. Ba'a jimaba wani katan kadangare ya dilko a gabanta tim!! Ta saman kujera tabi a tsoraci. Ta kwalla ihuu. Tabi yasmeen har kitchen. Tana haki. Yasmeen ta tambaya lafiya? Me ya faru ne asia?. Kadan gare. Yasmeen din dariya ta hau yi mata. Wai wannan uban ihun duk sbd kadan gare ne.



Asiya tace ahh. Kiji yar rainin wayo dama ace kema din bansan ki da mugun tsoran kadan garen bane. To amma dadin abun da duk mota daya ce ta kwaso mu. Lokacin yasmeen ta gama hada lemon a kofi biyu ta zuba. Tace muje parllo. To uwar tsoro. Bayan sunzo sun zauna Yasmeen ta mikawa asiya kofi daya na juice din wanda aka zubawa kankarq yayi sanyi. Asiya ta karba ta dan kurba tukun ta ajiye. Tace yauwa dama nazo ne a kan maganar nan da mukayi ranar. Yasmeen tace wace magana fa? Na manta tuna min. Asiya ta harare ta. Ji yar air ko kina mance komqi ai baza ki manta wannan ba. Kawai dai raina min wayo zakiyi. Kuma kin san dai halina sarai bana daukar raini . ehhy!




Kursiyya ta rasa ya zatayi domin bata san maganar da sukayi da Yasmeen din ba. Da taga dai ba mafiyata. Sai ta juya ta kalli marsiyya cikin magana irin tasu wacce ko bakinta ba'a ganin motsawarsa. Tace sister kiyi wani abu mana. Marsiyya kuwa dama kamar haka take jira ayi. Tufe bakin Yasmeen keda wuya Marsiyya ta bace. Asiya tace ke kiyi dani kin wani tsaya kina jamin aji. Ina sauraren ki miye abunyi?. Yasmeen tace kedai sha lemo tukun. Rufe bakin ta keda wuya suka dinga jin wani irin kararaki na fitowa daga dakin umma can kuma suka dinga ganin hayaki na fitowa tururu. ..


.asiya a tsorace take tambaya Yasmeen miye wannan?. Miye wannan Yasmeen. Kafin Yasmeen tayi magana. Kofar suka ji an buga ta balle ta fadi a kasa tum! Saida yan hanjin cikin asiya ya kada sakamakon idanunta da sukayi tozali da wani narkeken aljani mumuna a tsaye a kofa. Duk jikinsa a yayanke yake jini na futa kamar ankunna famfo. Fuskarsa kuwa ba kyan gani. Ihu asiyya tayi hade da makalkale Yasmeen ita ma din ihun take. Asiya da taga abun bazai yuyuba. Yashi tayi cikin rudu da gudu ta nufi kofar fita ko jakarta bata tsaya dauka ba da niyar ta fita ta tsere. Habawa. Kafin ta karasa Kofar wani jaki ne marar kai ya bayyan. A gabanta. Yace asiya yan mata ina zaki ne keda kika

Please Login or Register in order to submit comment