Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata baya samunta to shine na samu labarinka a gurin kawata. Zulai cewa aikin ka ko sarkin malamai ne yana kama wa. Dan haka nazo a taimaka min kai ni koma kashe tane ayi in huta dan gabaki daya ta kwace min miji. Sai wani iyayi da take yi. Ni kuwa nasan ba sune zasu sa mijina ya juya min ba kawai dai asirce sa tayi.




Boka yayi dariya hahahah! Wannan ai karamin aiki ne q gurin mu. Sai dai akwai sharadi. Dole kibi dokoki da ka'idoji dan haka maganar da zamuyi tana bukatar sirri tashi mu dan zagaya nan baya amma karki ji komai aikinki kamar yankan wuka kafin ki koma gida ne.




Murja ta tashi ta bishi ko me yace da ita oho. Nima ban bisu ba. Nandai suka dawo tare murja din na daiga sai bata rai take boka kuma yana wata irin dariya. Boka ya sallame su suka tafi yace kafin suje gida ne an gama aiki. A hanya zulai take tambayar murja dan me take ta wani babata rai.?
Murja tace wllh wancan mutumin kawai dan iska ne kika kawo ni gunsa. Zulai tace me ya faru wata maganar ya gaya miki wacce bata dace ba.




Murja tace aa. Zulai tace to miye. To ni in gaya miki gaskiya tunda muka zagaya bayan kukar nan ba wata magana ko wani magani da ya bane. Illa cewa da yayi in cire kayana. Saida yasa nayi zigidir. Yana hadiye miyau ya kama shashafa ni Sai kace wata amaryar sa duk dade war nan fa da kika ga nayi wllh jikina ne yake ta mamatsawa. Kamar wanda xai ciri mangwaro yana neman mai laushi.




Zulai ta kwashe da dariya. Harda rike ciki๐Ÿ˜‚. Ita kuwa murja sai ma ta dada bata rai. Saida zulai tayi dariyar mai isarta tukun tace haba sis to miye aciki bayan shashafawa da mamatsawa ne kawai yayi.ynz mudai muyi rokon bukata ta biya shine. Murja tace to allah yasa amma fa yau na matsu kamar gyada. Tare suka kara fashewa da dariya. Suka ci gaba da tafiya.




Boka kuwa suna tafiya ya bi bayansu da wani shu'umin kallo har suka bace. Saida suka bace tukun yayi. Tafi da hannuwa.
_*raf raf* karan tafi_ wasu bakaken aljanu ne guda biyu naga sun bayyana. Munana da su...............................................




Little of writer's

King boy













๐Ÿ™Ž๐Ÿฟโ˜  MIJIN ALJANAH โ˜ ๐Ÿ™Ž๐Ÿฟ


page 89 - 90


|
|
na king boy isah๐Ÿ‘‘
|
|
__________________________
๐ŸŒŸ5STAR APR 2017 ๐ŸŒŸ
|_________________________|




***** 5 star *****
๐ŸŒŸ5โƒฃSTAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION ๐ŸŒŸ ยฉ5SWA
***** 5 star *****


assalamu alaikum. ina baku hakuri readers bisa rashin post dina a kan lokaci. wannan nan bada jimawa ba komai zai dai-daita isha'allah. love you all ma friends


Gasu wasu yan gajeru bakake. Yan lukutaye.Kasumu ya kalle su yayi wata irin dariya ta shedanu tukun ya umarce su da suje su kashe kishiyar matar can. Kai tsaye suka ce baza suje ba. Ya tambaye su dalili. Suka ce ai a sharudan da muka gindaya maka mun hanaka sha'awar mace balle harma ka taba jikinta. Nan fa ya shiga raraba idanu. Domin yasan yayi kuskure.




Afuwa ya fara nema suka ce sam ba wannan zancen. To dai tun daga ranar suka sama sabani da aljanun nasa. Ita kuwa murjah aiki baiyi ba ta dawo yafi a kirga saidai yace mata taje zai sake kokartawa. Harma dai ta gaji ta daina zuwa.




Shekarar su mujabir 1 a garin daura ramma ta haihu ta haifi yarinya wace itace hajara. Bayan wata shekarar daya da rabi kuma ta sake haifar yaro. Haka suke ci gaba da rayuwarsu cikin annashuwa dake mujabir ya sama sana'ar sa da yaro yake yi wato barance amma yanzu ya mallaki shago nashi na kansa.




: Amma duk da haka uban gidan sa kuma amininsa wato mr mubarak yana taimaka mishi sosai.





Ranar wata laraba ne boka kasumu ya kawo musu ziyara sunyi matukar mamaki ganin ya gane gidansu wato inda suke. Mutumin da ko garinda suke bai sani ba amma gashi tsullum a gida kamar wanda yasan gidan dama.




Bayan sun gaisa mujabir ya nunawa kasumu yaransa lokacin Hajara ta dan fara wayo. Kasumu yaji dadi kuma ya nuna farincikin sa sosai. Nan ya nemi da abashi yaro daya. Wato tsakanin hajara da kuma Walid yake so a bashi daya. Mujabir ya nuna rashin amincewarsa amma daga bisanj ya yarda ko ba komi ai dan uwansa ne bazai cutar mishi da d'a ba.




Ramma kuwa ta rikice tace kwata kwata ita ba haka ba. Ganin ba yanda zatayi dole yasa ta hakura. Bata kara tada hankalinta bama saida taji cewa hajara za'a bawa boka masha jini. Ai kuwa da kyar aka rabasu kowa yana kuka.



Kasumu ya tafi da hajara can garinsu. Tsawan shekaru saidai ya kawo ta taga gida ya koma da ita. Walid kuwa ya girma yama kusan shekara 10 allah yayi masa rasuwa. Hakan yasa ramma ta tada jijiyar wuya ita ala dole sai an dawo mata da yarta ( wato hajara) mujabir ya tuntubi boka da maganar amma boka yace hakan bazai yuyuba ala dole shi xaiyi mata aure.




Mujabir ba yanda ya iya dole yaja girma ya hakura ya bar mishi ita. Bisa wasu maganganu da boka ya fadi mishi wanda suka kashe mishi jiki.



( haka ake san babba da juriya da hakuri da maida komai ba komai ba kaci girma)



Ya dawo ya sama ramma ya bata hakuri. Yace tayi hakuri idan aka amshe hajara a gun kasumu ba'ayi mishi adalci ba domin shi ya raine ta har ta girma kuma shima babanta ne sannan kinga mu allah yaga dama ya bamu wata yar to amma shi fa. Harkar bokancin shi ya hana shi yin aure.


Ramma ba yanda ta iya hakan yasa ta hakura. A can naija delta akawa hajara aure. Hakz ta kasance ba arabi ba boko. Sai tarin jahilci da boka yake tusa mata. Domin kadan ta hana itama ya kafurtata ta zama bokanya. Amma allah baiyi ba da taimakon wata kawarta.



A shekarar mujabir ya mutu sakamakon hadarin mota. Ramma taci kuka sosai ta zama abun tausayi. Domin bata da gata mijinta shine kominta shine uwarta shine ubanta kuma shine danginta. Dr mubarak ne ya aure ta wanda can dama shine amini mijinta wato mujabir.



Dr Mubarak auren sa daya tal a duniya duk da manyanta da yayi. Matarsa ya' daya ta haifa garin haihuwar na biyun ta rasu. Tun daga nan bai sake aure ba wai aiki ya hana. Sai a wannan karun.



Yasmeen itace y'a daya dillo a gurin Dr mubarak a hannunsa ta girma. Haka ta tashi ba tarbiya ba ilimin addini sai boko. Gata tantiriya ce. Kuma gwanar rawa. Domin a abuja ansha saka gasar rawa tana lashe kofin.

Dr mubarak ya dauke Ramma suka koma abuja inda suke da zama shida yasmeen. Sannan shi Dr Mubarak. kasurgumin dan boko ne kuma babban likita hakan yasa ba ruwansa ya watsarda addini baki daya ba ruwansa.


Mubarak ya kasance dan boko ne. Domin dan boko daban kuma mai karatun boko daban. Dan boko shine boko akidah ba ruwansa da Qur'an hadisa. Balle a tafi shashin sauran litattafai irin na fiqhu. Domin shi gani yake musuluncin ma a yanzu kauyanci ne. Shi kam ya waye. Haka itama kuma yarsa wato yasmeen.

Dr Mubarak Jarida itace Qur'anin sa labaran safe na bbc shine hadisin shi. (Wa'iyazubillaah allah ya kare mu)

Ramma ta rike yasmeen da hannu bibiyu. Kamar ita ta haife ta. Saidai ba yanda batayi ba a kan Yasmeen ta koyi karatun al qura'ni da kuma addu'a amma taki. Har aka daura musu aure ita da Dr al ameen wanda shima dan abokin Dr Mubarak ne kuma a hospital din Dr din yake aiki. Gabaki dayan su yan boko ne. Akidarsu daya. Basu kula da addini ba.


: Hajara bayan anyi mata aure da shekara daya ta haihu diya mace wacce yarinya kyakyawa nuratu suke kiranta. Ana nan ana nan kuma ranar sai aka wayi gari kasa ko sama aka rasa mai gidanta. Bayan tare suka kwanta a gado daya. Nan taci gaba da zama har kusan wata uku amma shiru ba labari. Gashi yanzu na girma harda ya' gaskiya ni bazan iya zama gurin boka ba.




Haka kuwa ta gaya mishi tace tana san ta dawo gurin umma wato Ramma haka kuwa akayi ya bata kudi mota zuwa lagos to a nan ne ma ya hada mata da wannan layoyin da turaren.




Da taje lagos Dr Mubarak ya karbe ta hannu bibiyu haka itama yasmeen taji dadi sosai na ganin hajara kuma gata yar umma ce hakan yasa take kiranta da aunty hajara. Ita dai jininsu ya hadu da aunty hajara...

Kursiyya tace kinji dai takaitace tarihin su:

Marsiyya tace haba nifa ince dama daga gani a cikin su ba wanda yayi islamiya. Wato sun watsar da addinin su basu san shine maganin mu ba dama maganin duk wani bala'i


Kursiyya tace.................................................



Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks





โœ๐ŸผAutan marubuta โœ๐Ÿผ



๐Ÿ‘‘King boy๐Ÿ‘‘










๐Ÿ™Ž๐Ÿฟโ˜  MIJIN ALJANAH โ˜ ๐Ÿ™Ž๐Ÿฟ


page 91 - 92


|
|
na king boy isah๐Ÿ‘‘
|
|
__________________________
๐ŸŒŸ5STAR APR 2017 ๐ŸŒŸ
|_________________________|




***** 5 star *****
๐ŸŒŸ5โƒฃSTAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION ๐ŸŒŸ ยฉ5SWA
***** 5 star *****




๐Ÿ˜ฐ assalamu alaikum. fatan alkhairi a gare ku masoyan masu kira da masu massages duk ina sane daku kuma ina baku hakuri bisa rashin post da nake yi kamar da๐Ÿ˜๐Ÿ˜

๐Ÿ‘๐Ÿผ
Jinjina da gaisuwar ban girma a gare ki.
Aunty na kuma mai kaunata. mai san ci gabana. a kullum a koda yaushe ina godiya da shawar warin ki๐Ÿ‘๐Ÿผ
๐ŸŒธFATIMA MMN ALI๐ŸŒธ
Allah ya bar zumunci kuma ya raya mana ali๐Ÿ‘๐Ÿผ




Kursiyya tace sis wllh nayi missing din al ameen anya kuwa bazan bishi garin da suka tafi din ba domin ni ji nake bazan iya kwana dayq ba ba tare da na sa shi a idona ba.


Marsiyya tayi dariya tace aunty bafa wannan kasar suka tafi ba domin naji lokacin da yake gayawa yasmeen wai saudiarabia dasuje. Kursiyya tace to ai ku can din ma sai in bisa kinsan fa garin masoyi. Marssy tace aunty baga Facebook nan ba kuma ga whatsapp. Ai sai kisa ya tura miki pics dinsa masu mugun kya.


Kursiyya tace kwarai kuwa haka za'ayi.

********

Al ameen suna tafiya a cikin mota yaji gabansa nata faman faduwa yarasa dalili yace ko gidane ba lafiya hkn yasa shi fiddo waya ya kira yasmeen yaji ba wata matsala haka can gidansu ma ba wata matsala. A nan ne hankalin sa ya dan kwanta.




Kamar ance ya duba right glass din motar hantar cikinsa ce ta kada. A tsorace ya rufe idanu. Awaki ne sak a jiki amma kan na mutane ne. Gasu da dama kuma. Dan akuyan na gaba mai kan wani mumunan bakin mutun. Shine keta faman wullowa al ameen harara.





Al ameen ya dade idansa a rufe tukun jimawa ya bude. A nufinsa ai gudu suke a mota yanzu sun wuce abun. Habawa Can ya hange su suna cin tsanwar ciyawa๐Ÿ˜ฐ




Nan ya fara nunawa abokinsa husaini. Nuna mishi gun kawai yake yi da yatsa amma bakinsa ya rufe ya kasa magana. Shi kuwa hussaini sai faman tambaya yake yana ce mishi miye? Miyene? Domin shi ya duba gun baiga komai ba sai falwaya da bishiyoyi da ake wucewa a bakin titi.




Al ameen kuwa gashi yana so yayi magana amma abun ya ci tura! Dan dole ya hakura ya bar nunawa kuma shima ya rufe ido.



Ana cikin tafiya husaini ya cewa driver idan yanada suratul baqara ya saka musu domin yana bukatar ya dan saurari karatu akwai gurin da yaji yayi mishi tauri a hardarsa. Ba gardama kuwa driver ya sa musu suratul baqara. Nan take husaini ya fara bin karatun. Daidai kokacin al ameen ya bude ido. Yasha mamaki ganin ya daina ganin abubuwan nan.



Wayar husaini ce tayi kara ( ringing)Da sauri ya fiddo wayar yana kallan (screen ) din yayi Murmushi yace allah sarki sister na. Yace wa driver ya dan rage volume zaiyi waya. Wayar ya kara a kunne.
" assalamu alaiki sisterna"

Ta amsa tare da cewa.
" broz wai yaushe zaku dawo ne nifa wannan tafiyar gaskiya bata yi min dadi ba. Zaka tafi ka barni ni kadai,


" sister ban san shagwaba fa duk ba gasu umma nan ba shine zaki ce na barki ke kadai. Kinga in wani abu kike so to ki fada naga wannan kame-kamen naki akwai magana.


" Murmushi tayi tace to yaya dama... "Dama me fada inaji ai daman nasan ba banza ba.

"Broz dama sub dinane ya kare kuma nacewa mum ta bani kudi insai kati take. Wai tace shiririta ne.

Husaini yace " karki damu to bari in turo miki. 2k zai isheki. Wata yar kara tayi hade da tsalle. Masha'allah na gode yayana. Na kaina. Eh zai isama sosai.



" ok to abunda nake so in gaya miki shine banda shiririta banda biyewa samari da kawaye. Zumunci kawai na baki damar yi a duk social net kinji ko?.
" naji yaya. Kuma ai ni dama ba abunda nake yi sai zumunci sai gaishe-gaishen dangi.
" to kinji dai na gaya miki yanzu bari in turo miki sai kiyi sub din, tayi godiya sukayi bankwana,


Al ameen ya kalli husaini yace malam gaskiya baka da kirki. Yanzu saboda allah kana da kanwa mai yin whatsapp amma shine kaki ka bani number ta. Ya fada yana dariya.


" husaini yace kull! Ka kula wannan tafi karfin ka yarinya ce mai kamun kai da natsuwa. Ita ba wai yaudarar samari take yi irin naka ba a whatsapp. ita sada zumunci da wa"azantarwa su yake kaita whatsapp.


Dariya al ameen yayi sosai har yana dafe ciki. Yace wa husaini. " kuma kai ka yarda da bata soyayya kenan.?


" dole kuwa in yarda domin nasan halinta bata min karya. Shiru al ameen yayi jin wata irin murya na cewa....







Ba kai ba zaman lafiya tunda ka yarda ka auri min budurwq al ameen ka jawowa kanka. Ka shiga shirgin da banaka ba. Hahahahaha.


Al ameen dafe kai yayi domin jin kan nasa na wuni juyawa. Husaini yace " al ameen lafiya kuwa naga ka wani dafe kai. Lfy kuwa. Ganin ya dafe kai ya sunkuyar da kai kasa yaki magana. Yasa husaini yace wa driver ya kunna musu karatun su suci gaba da ji.




Karatun na farawa al ameen ya fara jin kan nashi ya rage ciwan da yake yi mishi.



Haka suka ci gaba da tafiya zuwa airport โœˆ



Ana tafiya Al ameen ya fiddo wayarsa ya bude data. Ya fara dube-dube massages domin duk safiyar yau bai bude data ba.



Mamaki ya kama shi ganin massages din Zainab basu shigo ba. Hakan yasa ya lalubo no ta abun mamaki tayi block dinsa. Nan ya fara tunanin ko dai ta gano shi mayaudari ne shi yasa tayi block dinsa.





Da yayi niyar kiranta kuma sai ya fasa. yace to ni miye ma damuwana bayan nasan idan nayi niya sai na sama goma irinta a yau......................................................



Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks





โœ๐ŸผAutan marubuta โœ๐Ÿผ



๐Ÿ‘‘King boy๐Ÿ‘‘














๐Ÿ™Ž๐Ÿฟโ˜  MIJIN ALJANAH โ˜ ๐Ÿ™Ž๐Ÿฟ


page 93 - 94


|
|
na king boy isah๐Ÿ‘‘
|
|
__________________________
๐ŸŒŸ5STAR APR 2017 ๐ŸŒŸ
|_________________________|




***** 5 star *****
๐ŸŒŸ5โƒฃSTAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION ๐ŸŒŸ ยฉ5SWA
***** 5 star *****









๐ŸŒทMANTAWA DA KU ABUNE MAI WUYA A GUNA.TAMKAR UWA CE TA MANTA DA DANTA๐Ÿ‘ผ๐ŸปWANNAN ABU NE MAI WUYA DAN HAKA BAZAN MANTA DA KU BA. MASOYAN GASKIYA.
๐ŸŒนHADIZA HADI๐ŸŒน
๐Ÿ‘ฐ๐ŸปMAMAN HISHAM๐Ÿ‘ฐ๐Ÿป

NA GODE DA IRIN ADDU'IN KU A GARE NI.๐Ÿ˜‡ allah ya bar zumunci ya kuma kara hada kan mu duk yan group din
โœ๐ŸปBIGBOY ISAH NOVELS๐Ÿ‘‘
Ina ji daku ina kaunarku๐Ÿ˜˜





Nan fa ya juya gurin kursiyya suka fara chat dinsu irin na masoya. Abun kamar suna ganin junan su.





: *******

Al amarin su Yasmeen kuwa bayan sun tashi hajara ta shiga wanka. kafin ta fito yasmeen ta hada musu abun kari ta kai dinner ta shirya.


Anty hajara na fitowa ita ma ta shiga. Wankan abunta. Anty hajara kuwa duk a tsorace take. Domin abunda ya faru jiya. Ita kadai a dakin yasmeen tana kwaliya amma ta dinga tsorata. Daga taji motsi sai ta waiga da sauri. Allah- allah take yasmeen ta fito. Domin ita kadai din nan tsoro take ji.




Bayan 30mints yasmeen ta fito. A gefan gado ta iske anty hajara. Sai zare idanu take kamar kace arr! Ta ruga. Yasmeen Tace wa aunty hajara "gafa kayan break din can na shirya a dinner kije ki fara kari kafin in fito mana.



Anty hajara tace aa babu komai ai bana wani jin yunwa sosai gama kawai mu tafi tare. Yasmeen zuwa yanxu ta fara gane cewa aunty hajara na jin tsoro. Amma gudun kar ta fada tasan halin antyn nata yanzu sai ta karyatata. Hakan yasa tayi shiru taki ta bayyana.






Anty Hajara na zaune tana raba ido. Har Yasmeen ta gama kwaliyya tasa kaya tukun suka fito tare. Farlo suka je suka zauna suka fara breakfast.anty hajara kuwa sai wani satar kallan dakin umma take yi.



Suna cikin cin abinci. Al ameen ya kira Yasmeen ya sanar da ita cewa. Yanzu zasu tashi. Fatan alkhairi tayi mishi tare da a sauka lafiya. Allah ya bada sa'a yasa a samo abunda akaje nema. Sannan ta gaya mishi ta kirawo aunty hajara ta tayata zama kafin ya dawo. Nan har yace abawa anty hajara. Din su gaisa.




Bayan sun gaisa ne anty hajara take cewa. "Waka ake yin rayuwa wato ka tafi ka bar mana kanwa a gida ita kadai. Yayi dariya yace " to me zai kamata a gidan dama ai ta saba xama ita kadai. Kuma ba ga masu gadi nan ba ga driver ai ba ita kadai ne a gidan ba su uku ne.




Aunty hajara tace "to naji amma karka kara domin gidan nan naka ni kaina ban yarda dashi ba domin jiya ma.....
Kuma sai tayi shiru.



"Yace jiya me.?

Tace jiya ma tace an tsoratata sosai a gidan nan.




Al amern yace to yanzu dai tunda gaki nan ai shikenan nasan zaki kullar min da ita.
.




Aunty hajara tace " karka damu babu abunda zai same ta tunda ina tare da. Ita.
( a zuciya kuwa tace nima in kula da kaina mana. Lolx)


Bankwana sukayi ta mikawa Yasmeen wayar itama sukayi bankwana. Tayi mishj bye bye.




Anty hajara sai kallan dakin umma take domin wayarta na ciki kuma gaskiya tsoran dakin take ji bazata iya shiga ita kadai ta dauko ba.



Yasmeen sai surutu take ta suburbudawa sai zuwa can ta lura da hankalin aunty hajara ba a gurin ta yake ba. Sai dakin umma take kallo.



Yasmeen tace aunty hajara lafiya kuwa naga sai kallan dakin can kike. Ko da matsala ne. Anty Hajara tace aa wllh ba komai kawai dai wayana ne na rasa inda take a dakin shine nake tunanin inda na sakata.



Yasmeen tace to aunty hajara muje in tayaki dubawa mana. Murmushi aunty hajara tayi domin ita dama abunda take so kenan Yasmeen ta rakata. Tace yauwa to tashi muje ki tayani dubawa.
.


: Tashi sukayi suka nufi dakin kowa a tsorace yake a cikinsu bama kamar anty hajara. Domin jiya da dadare taji jiki a dakin. Yasmeen ce ta tura dakin a hankali kamar muna fuka.



Saida ta lalaka tukun ta kunna kai ta shiga haka itama anty Hajara ta bita baya a bude ta bar kofar sbd tsaro.


Marsiyya na bayan kyaure. Suna shiga ta banka ( door) din. Da sauri su biyun suka kallo kofar basu ga komai ba hakan yasa suka ci gaba da duduba wayar.



A can karkashin pillow Yasmeen ta zaro wayar. Aunty hajara tace. Au ashe nan na sakata. Haka tayi irin abun nan kamar dai bata san inda ta ajiye ba da gaske.




Kofar fita suka nufa da niyar fita. Idone ya raina fata. Lokacin da aunty hajara ta ja kofar taji ta gam ko motsi batayi.

( kaka kara kasa ga akuya ga kura ga Yasmeen da hajara a dakin aljana๐Ÿ˜‚ su aunty maman ali a kawo dauki)


Nan sukayi-sukayi kofar taki buduwa bayan kuma ba'a kulle take bA. Sunkai kusan mintuna sha biyar a gun amma kofa taki buduwa.




Hakan yasa suka hakura suka koma kan gado suna ta sake-saken yaya xasuyi. Dakin ne gaba daya ya dauki wata mahaukaciyar dariya mai firgitarwa.

*hahahahahahaha* _hahahahahahah_
~Hahahahahahahah~

Kankame juna sukayi a tsorace suna raraba ido jira suke kawai suga ikon allah suga abunda zai faru.



Wata murya marar dadi ta fara magana.
~ke Yasmeen me ya kawo ku dakina me kikazo yi a dakina. Ko kinga ina shigar miki daki ne?~




Yasmeen cikin murya mai karkarwa a tsorace ta daga kai tana kalle- kalle. Tace dan allah ki gaya mini ko ke wacece me nayi miki kike azabtar dani me na tsare miki? Me kike so?



.dariyar ce ta kara bayyana.
*Hahahahaha*

Baki da matsayin da zaki san duk wannan yanzu tambayarki nake yi me yasa kuka shigo min daki. Ke waccan yar rainin wayyon wai jiya harda zuwa kika kwanta min a katifa. Ko to yanzu zanyi maganin ku.






Daidai lokacin idiris ya shigo gidan yana bitar tilawarsa. Su kursiyya kamar wuta ta tinkaro su haka sukaji hakan yasa sukayi gagawar barin gidan a million.



Su Yasmeen na kankame da juna. Kofar sukaga ta wangame kuma anyi shiru. hakan yasa sukayo waje a guje. Ana rige-rige. Da kadan sun banke idi drivers.



Sakin baki yayi yana kallansu. Su kam basu ma kula da shi ba. Wajen ya biyo su yana tambaya lafiya-lafiya hajiya.?


Su Yasmeen kuwa sai maida nunfashi ake daya-daya. Da kyar ta iya daga baki tana cewa fatalwa ce a gidan.idi yace fatalwa kuma. Yanzu da safen nan ai ni na dauka fatalwa sai dare take yawo . inaga kawai dai kun tsorata ne.




Maganarsa ta cewa inaga kun tsorata ne ita tabawa anty hajara haushi. Tace kaga malam jeka abunka in ka kawo sakon.


Kayan miyan dake hannunsa ya mikawa Yasmeen yan musu wani irin kallo. Tabbas yaga tsoro a idonsu. Yace to idan ma fatalwar ce da gaske akwai wani malami wanda muke daukar karatu a gunsa idan kin bada izini zanyi mishi magana sai yazo yayi muku karatu. Da yardar allah ko aljana ce sai ta bar gidan.
.



Yasmeen datayi magana... Maganar Anty hajara ya dakatar da ita. Kai dallah malam ka tafi ka bawa mutane waje an gaya maka mu muna harka da wadan nan almajiran ne. Ba abunda suka iya sai san kudi. To anji an gode bama so jeka abunka. Ta bishi da wani mugun harara.





Yasmeen bata ce komai ba. Anty hajara tace sis inada mafita. Da sauri yasmeen ta dago tace aunty miye mafitar?.



Anty hajara tace idan kin yarda da shawara ta muje kauye mu taho da kawu kasumu. Domin shi kadai zai iya yi mana wannan aiki. koma miye a cikin gidan nan zai fitar dashi babu bata lokaci. Domin shi din ma yana hudda da manyan aljannu๐Ÿ‘‰๐Ÿฝ๐Ÿ‘บ๐Ÿ‘น........................................................

๐Ÿ˜‚( ~nace tofa su kursiyya da boka za'a hada su ashe?.~)


Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks





โœ๐ŸผAutan marubuta โœ๐Ÿผ



๐Ÿ‘‘King boy๐Ÿ‘‘











๐Ÿ™Ž๐Ÿฟโ˜  MIJIN ALJANAH โ˜ ๐Ÿ™Ž๐Ÿฟ


page 95 - 96


|
|
na king boy isah๐Ÿ‘‘
|
|
__________________________
๐ŸŒŸ5STAR APR 2017 ๐ŸŒŸ
|_________________________|




***** 5 star *****
๐ŸŒŸ5โƒฃSTAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION ๐ŸŒŸ ยฉ5SWA
***** 5 star *****











Yasmeen ta danyi jum kadan zuwa can kuma sai ta dago kai ta kalli aunty hajara tace kuma fa haka ne. Kinga idan yazo ma sai ya zauna a gidan ya korar muna su gaba daya.


Farin ciki ne ya ziyarci cikin zuciyar anty hajara jin an karbi shawarar da ta bayar. Tace to kinga ba bata lokaci zamuyi ba shiga daki ki dauko mana gyaluluwan mu yanzu mu tafi. Yasmeen tace aunty wllh bazan iya shiga cikin nan ni kadai ba kizo dai muje tare.


Ba yanda aunty hajara batayi ba da yasmeen a kan taje ta dauko musu mayafi amma taki. Dole sai taren suka shiga. Duk a tsorace suna waige-waige. Daga sun danji motsi kadan sai sun waiga gurin. A haka dai suka shiga. A parllo yasmeen ta ajiye kayan miyan sannan taje ta dauko musu gyale da handbag dinta. Suka fito.




Idi suka yiwa magana ya fiddo mota. Ya tambaya anguwa zasu.wace unguwar zai kaisu

Please Login or Register in order to submit comment