Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankalinka tunda babu" bai karasa jin me umma ke fada ba yaji magana ta kasa ana cewa. "alhji mun gode fa sosai da aran gidan da ka bamu jiya mukayi sarkin aljanu day. gobe waziri day. jibi fadawa day. a haka har sai anzo su hakimi da sauran tarkace sannan azo kan uwayen amarya day. alhji bai ko iya lekawa ba sai karkarwa da yake yi. yana fadin. "kinji ta ko-kinji ko shikenan na kwaso wa kaina bala'i aljanar ce fa wannan ke magana" A cikin kunne yake wa umma Radah.



Umma tace "wai ni miye haka Dr gashi na leka banga komai ba Dr lafiyanka kuwa"....



"A saboda wannan abu da kayi mana zan baka Aljanu guda biyu masu Tsaran lafiyarka. zasu dinga binka ko'ina don tabbatarda Tsaro." da sauri abba ya leka "A'a wllh na yafe bana so na gode kuzo kuyi duk abunda zakuyi amma ki bar tsaron na gode". Ba saitin aljanar yake kallo ba domin tun kallon Farko da yayi mata yaji hantar cikinsa ta kada.
*hahahahaha* dariya tayi. "mun yanke hukunci ba mai ketare wa in na ajiye kara ko cikin aljanu bare kai kace zaka min gardama karya kaka" ta bacce batt!
Dr na juyawa yaga wasu yan kananun halita da basu wuce mage ba sai dai ba magen bace a tsaye suke tafiya idan ka kalle su dan muninsu da ban tsoro baza ka sake kallo ba. Abba yace "Na shiga uku"

"Alhj me ke Faruwa kuma?" bai tsaya bata amsa ba ya nufi daki da gudu yan aljanun kuma suka bishi a guje. har ma sun fishi gudu da kyar ya samu ya Riga shiga dakin ya Rufo kyauran da kadan ya datse kafar wani daga ciki.


umma tazo tana kwankwasawa. "Alhj bude mana me ke faruwa ne" Domin ita bata ganin komai ko maganar aljanar bata ji ba. daga cikin dakin Alhj yace "wai ke bakya ganin su ne. wallahi aljanune gasu nan wai gadina zasuyi dan allah Taimaka ki kirawo malam mujitafa wata kil shi yasan yanda zaiyi ya kore su"

"Hmm alhj kenan yanda ka dauki malam mujitafa ba abakin komai ba yau har kaine kuma kake neman taimakon sa. hmm ruwa baya Tsami banza kenan yanzu sai ka gane ko wane mutun akwai ranarsa Maganar da nake ta faman fada maka kenan amma sai kace bazaka taba neman taimako a gurin su ba To yau ga Ranar sa Allah ya kawo ji dakai da tamakar kai dan boko ne mai.. . "


"ke wai ni zaki tafi ne ko kuma zuba zaki tsaya kina tayi kamar Rariyar Garara." "yi hakuri Alhji bari inje to allah yasa ya Zo.
Ta dau gyalen ta ta zagaya da kyar ta Samu malam ya taho shima dan tace taimako ne. amma da yace bazai je ba "Ai duk mulkin mutum Ba malami ne ya kamata yaje gunsa ba sai dai sarkin in ya matsu yazo gun malam din badan malaman mu yanzu sun zubar da Darajar su ba sun saka kwadayi da san abun duniya a Zuciyoyinsu".


hakuri ta bashi tace matsalar aljanu ne. Ba'a jima ba sai gasu sun dawo tare. Malam yaja ayatul qursiyyu da wasu ayoyin ya totofa a parllon dama Tsakar gidan yace. "bismillah zaka iya fitowa" ta leke ya fara dadai yaga baiga aljanunba sai ya karasa fitowa. godiya sosai yawa malam kuma yace a koya mishi addu'a kariyar kai daga aljanu. malam yace ai ayatul qursiyyu da li'ilafi kadai sun ishe ka a duk lokacin da kaga abunda baka lamunta ba to ka karanta su allah zai shiga tsakanin ka da duk wani mugun abu. " Dr yace amma naji ance aljanu na Rikidewa su canza halitta shin da gaske ne?


SHIN DA GASKE NE ALJANU SUNA IYA RIKIDEWA
(CHANZA KAMANNINSU)??
Eh da gaske ne tabbas Aljanu da Shaitanu sukan
chanza Kamanninsu zuwa duk wata siffar da suka
ga dama.
Tun azamanin Manzon Allah (saww) da
sahabbansa an samu Misalai da dama akan haka.
Misali kamar lokacin da Manzon Allah (saww) ya
sanya Abu Hurairah gadin abincin Zakkah, sai wani
Shaitani ya rikide yazo a Siffar mutum yana satar
abincin.
Sau Uku ajere Abu Hurairah (ra) yana kamashi
akan zai kaishi wajen Manzon Allah (saww) shi
kuma yana yi masa magiyar cewa ba zai dawo ba.
A karo na uku ne yace masa idan ya kyaleshi zai
sanar dashi abinda zai amfaneshi. Shine yace
masa ya rika karanta ayatul kursiyyi duk sanda zai
kwanta barcinsa.
Abu Hurairah yazo ya gaya ma Manzon Allah
(saww) sai yace masa "SHIN KO KASAN DA
WANDA KAKE MAGANA ACIKIN DARARE UKUN
NAN KUWA?"
Yace masa "A'a". Sai yace masa "AI SHAITANI
NE".
Hadisin yana nan acikin Sahihul Bukhariy lamba ta
2,311. ( ZAUREN FIQHU'S POST)


daga
Sayyiduna Ubayyu bn Ka'ab (ra) cewa yana da
wani wajen da yake shanyar dabino sai ya kasance
duk lokacin da yazo ya duba sai yaga dabinon
nasa yana raguwa. Don haka ya fara fako ko zai ga
mai satar masa dabinon.
Yace nazo rannan na leka kawai sai naga wata
dabba mai kamar Yaro saurayi.
Sai nace masa "Kai Aljani ne ko Mutum ne?" Sai
yace mun "A'a Ni Aljani ne".
Sai nace masa "To matso kusa in ganka".
Da ya matso kusa sai ba rike hannayensa, sai naji
su Kamar Qafafun kare.
Sai nace masa "Shin Haka Halittar Aljanu take?"
Sai yace "Kwarai kuwa. Kuma su kansu Aljanu sun
san cewar ina daga cikin Mafiya Qarfun Jiki
acikinsu".
Yace "Ai mun samu labarin cewar Kai mutum ne
mai son yin Sadaqah shi yasa muke son Muci irin
abincinka".
Sai nace masa "Shin wanne abu ne zai Karemu
daga gareku?" Sai yace "Wannan AYATUL
KURSIYYI din nan".
Da Ubayyu din yazo ya gaya Manzon Allah (saww)
labarin yadda sukayi sai yace masa "QAZAMIN
NAN YAYI GASKIYA".
Al-Hafiz Ibnu Hajr Al-Asqalaniy (rah) ya kafa
Hujjah da wadannan hadisan guda biyu cewa
Shaitan ma yakan iya surantuwa ya chanza siffah
zuwa ga wasu kamanni wadanda zai yiwu Mutane
su iya ganinsa.
Hafiz yace ayar nan wacce Allah yake cewa :
"HAKIKA SHI DA QABILARSA SUNA GANINKU NE
TA YADDA KU BAKU GANINSU".
Yace wannan ayar ta kebantu ne da lokacin da Shi
Shaitan din ko Aljanun suke cikin ainahin siffarsu
wacce Allah ya haliccesu akanta. Amma idan suka
rikide, zai yiwu arika ganinsu da siffofi
mabambanta.
Don Qarin bayani aduba cikin FAT'HUL BAARIY
juzu'i na 4, shafi na 489. ( ZAUREN FIQHU'S POST)

Abba yace tabb lalai yana da kyau in fara koyon ayatul qursiyyun yanzunan.......................... .....................

SU ABBA YAN BOKO ANJI MAZA ZA'A FARA KARATU. LOLZ


Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks





โœ๐ŸผAutan marubuta โœ๐Ÿผ



๐Ÿ‘‘King boy๐Ÿ‘‘






๐Ÿ™Ž๐Ÿฟโ˜  MIJIN ALJANAH โ˜ ๐Ÿ™Ž๐Ÿฟ


page 142 - 143


|
|
na king boy isah๐Ÿ‘‘
|
|
__________________________
๐ŸŒŸZAMANI APR 2017 ๐ŸŒŸ
|_________________________|




***** zamani *****
๐ŸŒŸZAMANI WRITER'S ASSOCIATION ๐ŸŒŸ ยฉZ.W.A
***** zamani *****






Abba bai bar malam ya tafi daga gidan nan ba saida ya iya ayatul qursiyyu haka itama umma ta koya. Abba ya bawa malamin nan kyautar kudi da yace bazai karba ba kuma sai ya karba yace tunda kai ka ga dama ks bani ba laifi yayi godiya ya tafi abunsa.


****
a gidan Al ameen kuwa abu ya Rikice domin Al ameen ya dinga abubuwa iri iri kamar mahaukaci zainab ta fahimci aljani ne a jikinsa shi yasa take yun kirin yin karatu sai dai daga ta fara sai Al ameen ya zo ya makure ta wani lokacin kuma yata jubgarta da kyar take iya kwatar kanta. a cikin daren jiya dai tasha wuya domin yanzu tsoran Al ameen din ma take.



bayan ta shirya ta gama abinci ta zuba sunci kuma ta zuba wanda zasu kai asbiti tace Al ameen ya tashi ya kaita daga nan ya dubo yasmeen amma yaki yace taje kawai shi baza shi ba taje driver ya kaita. tayi tayi amma mutumin ya kafi shi ba inda zashi da ta takura mishi. mikewa yayi tsaye lokacin idanunsa suka yi wani jajur.yana mike wa ya wanke ta da mari. "Dauka abincin maza ki tafi driver ya kaiki nace ni ba inda zani" cikin wata murya wacce bata Al ameen din ba ake maganar. a Rude yasmeen ta dauki kular abincin a tsorace ta fice tana tafiya tana juyowa tana kallansa domin ta tabbatar da matsala.



"Driver ya dauke ta Sai hospital. Zainab na fita Al ameen yayi dariya mai karfi da muryar mace yace "Shikenan kunyi bankwana Da al ameen domin yanzu dama ta samu zan dauke shi in kaishi wani gurin in hallaka shi. in batar da shi daga doron kasa. hahahahah ta sake dariya a karo na biyu tukun ta bata Rai. Kitchen ta nufa ta je gaban k.gas ta dora hannunta saiting wajen wutar. tana kunnawa ta fita daga jikin al ameen din al ameen sai ganinsa yayi a gaban gas ga hannunsa wuta zafi da Sauri ya janye yana yarfe hannu domin ya dan kone kadan ta yadda wajen bazai fito bama. ita kuwa tana gefe tana dariya al ameen kuwa Ruwa ya jefa abun yana tunani me ke faruwa kafin ya karasa tunanin ta sake shiga jikinsa bayan tasha dariyarta.



Al ameen ya nufi waje yanayin tafiyarsa ka dai ka gani in dai kasan shi to zaka san da matsala domin ya chanza yanzu haka ya fito a kasa yake tafe yana yan surutai kamar mahaukaci.
****

Basmah na gani sai hauka take ina ririke ta da kyau wai zata fada Rijiya itana tun jiya aljanar ta dawo jikinta. da sauri aka aika a kirawo malam ba'a same shi a gida ba ya tafi wajen wata Ruk-yar dole sai kara saka basmah daki akayi kamaninta duk sun sauya sai surutai take barkatai ga jarabar karfi...



Dady yana zuwa Asbiti ya samu su hajara jikin yasmeen da sauki sai dai ita har yanzu Al ameen take ambato wai a tunaninta ya mutu ne aka ki a sanar da ita. dady yace "Al ameen bai mutu ba kuma ko jiya ya zo nan duba ki amma sai kika nuna tsoransa kike kika ce wai wata mata kike gani bayan kuma shine. Amma wata kil aljanu ne suka shige sa amma ko sune akwai maganinsu bari dai Al ameen din yazo." yasmeen tace. "Abba wane magani kuma" ayatul qursiyyu ya karanto yace kinga wannan to ta isa tayi Raga-Raga da aljani Dan haka ya kamata kema ki harda ce ta.




yana fadi tana fadi har ta dan Fara iyawa dai-dai lokacin Zainab ta shigo Rik da plask da kuma wata yar Kula. Gaban gadon ta Dire su ta durkusa ta Gaida Umma da abba da kuma Su hajara. Yasmeen ciki-ciki ta amsa ya jikinda Zainab tayi mata. Zainab tace. "ga abinci nan.." kafin ta Rufe baki Zaimab tace "Kinga malama bamu san iyayi ina al ameen ki dauki abincinki kuma ki tafi da shi bama so, ta nuna wata kular, ga abinci nan in kina so sai ki kara Domin naga Alamu yunwa ce ta kawo ki gidan Al ameen din" Dady ne ya dakawa Yasmeen tsawa ke Rufe min baki Ba dan ita ba ke da Al ameen din ai da yanzu kun mutu. saboda Tsabar jahilcin ku ko fatiha baku iya ba ita ta cece ku amma shine yanzu zaki dinga yi mata Rashin kunya. to kar in kuma ji" gunguni yasmeen tayi To ai kaine baka sakani makaranta ba. "me kike cewa? ya tambaye ta. "dady ni fa bance komai ba" juyawa yayi ga Zainab yace kiyi hakuri kinji daga yau bazata sake ba kuma ina so dan allah ki dinga koya mata karatu. ki Riketa kamar yar uwarki ku Zauna lafiya. ya juya ga Yasmeen ya mata fada sosai a kan ta kula yaga alamu ita ke tada Tarzoma....


Ana cikin haka gaban Zainab yayi mumunan faduwa Al ameen ya fado mata A Rai da gudu ta mike ta nufi Waje domin tasan akwai matsala. su dady na magana amma ina bata ko saurare su ba. da sauri taje ta Tsaida napep domin driver har ya koma. Husaini lokacin ya karaso asbitin shima ganin Zainab din a Riki ce kuma ta hau napepk yasa ya bisu. 500 tabawa mai napep yana ga canji tace Rike A rude ta shiga Gidan M. lawal ta Tambaya ko yaga Fitar Al ameen.


Yace tabbas ya fita kuma ni naga ma duk ya canza da Zan tambaye shi ko lafiya kuma dai Sai na fasa. "Innalilahi wa'ina ilaihi Raji'u yake tashi daga bakinta ga kuma hawaye da Suke zarya a fuskanta. lokacin Husaini ya shigo tana ganinsa ta Ruga ta fada jikinsa tana kuka. tana fadin. "yaya shikenan sun tafi da shi dama abunda nayi gudu kenan" Tambayarta ya shiga yi me ya faru.? da kyar ta iya Rage kukan Ta fadi mishi duk abunda ya faru jiya da dare da kuma Safiyar yau. Innalilahi. shima ya fada lokacin da Zufa ta fara karyo mishi. M. Lawal ya Tambaya ya dade da fita.M.lawal yace gaskiya yanzu Zaikai Awa biyu da Fita.........................m..................................


GOOD MRNG. FRNDS KUZO MU SHIGA GARI NEMAN AL AMEEN.


Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks





โœ๐ŸผAutan marubuta โœ๐Ÿผ



๐Ÿ‘‘King boy๐Ÿ‘‘









๐Ÿ™Ž๐Ÿฟโ˜  MIJIN ALJANAH โ˜ ๐Ÿ™Ž๐Ÿฟ


page 144 - 145


|
|
na king boy isah๐Ÿ‘‘
|
|
__________________________
๐ŸŒŸZAMANI APR 2017 ๐ŸŒŸ
|_________________________|




***** zamani *****
๐ŸŒŸZAMANI WRITER'S ASSOCIATION ๐ŸŒŸ ยฉZ.W.A
***** zamani *****






"Awa biyu fa to wane waje kaga ya nufa?. " kasan ina ciki so wllh banga in da ya nufa ba" husaini ya dafe kai to yanzu su ina zasu nufa ma. shiga muta muji yace wa zee da sauri ta shiga ya bi hanya banda dube-dube ba abunda suke yi wai ko allah zaisa su ganshi..
****


al ameen hanyar katsina ya nufa tafiya yake amma nisan da yayi bana kadan bane domin tuni ya fita daga garin daura. tafiya yake yana yan surutai kamar mahaukaci daga ka ganshi kaga sabon shiga a hauka illa suturar jikinsa da take da haske. bakin titi ya tsaya kamar mai shirin tsallakawa sai da wata mota ta feso a guje tukun kursiyya ta fita a jikinsa ta tunkuda shi kan kwalta da kudirin motar ta murtsike shi. ๐Ÿš—
Tun daga nesa mai motar ya take birki sanadiyar kuracewa Al ameen da yayi ganin birkin bazai yi ba kiris ta hana ya murtsike Al ameen ya lauye kan da karfi wani ice ๐ŸŒด suka daga gaban motar yayi Ratsa-Ratsa mutanan ciki ba abunda suke in banda ihuu! masu kalmar shahada kuma nayi. wasu sunji ciwo wasu kuma basu ji ba.



kursiyya taji haushin wannan abun sosai komawa tayi ta shiga jikin Al ameen din. kawai tq dau hanya Tasa al ameen din yaYi gaba abunsa ko a kansa.
Motane uku na cikin motar da basu ji Ciwo ko kwarzane ba sune suka fito suka nufi gurin Al ameen. wayam basu gansu ba. daya ya juya can ya hangi Al ameen din ya kada kai yana ta tafiya hankalinsa kwance. kira ya fara kwallawa. "Bawan Allah "bawan allah" amma ina Al ameen yayi kunnan uwar shegu ko waigowa baiba.



ganin haka suka Ruga da gudu kanshi da Niyar su ci ubanshi. Gaban shi daya daga cikin su ya tarya zai kwashe shi da mari sai kuma ya tsaya jin Al ameen din sai surutan iska yake kuma ko alamar tsayawa baiba sai ma gocewa mutumin da yayi yaci gaba da tafiya abunsa.



sauran suka karaso suke Tambaya ya akayi ya barshi ya wuce. dariya yayi yace Ai mahaukaci ne. "mahaukaci kuma cike da mamaki wani yayi wannan tambayar." ya za'ayi kace muna mahaukaci ne bayan gashi Tsaf-tsaf." "Ai gashi nan sai ku Tarye shi ku gani da idanunku.


Da sauri wani yaje ya kamo hannunsa. hade da cewa. " kai malan kana da hankali kuwa?. juyowar Al ameen keda wuya ai kuwa sai ya Shake wuyan wannan matashin ba abunda yake fada illah. "Al ameen sai na kashe ka A yau Al ameen bazaka kara kwana a duniya ba Al ameen." saurayin tsorata yayi jin ana sai an kashe Al ameen gashi kuma da wata kalar murya ake mgnr daga kaji ta kasan bata asalin al ameen di bace. kokarin kwacewa yake yana fadin bani bane Al ameen din wllh bani bane Al ameen. yake fada yana kiki niyar kwatan kansa da kyar yan uwan nasa suka kwace shi daga hannunsa. dake hadi da karfin iska ne.
Ba yanda suka iya da Al ameen din Domin da kyar suka samu suka kwaci kansu.domin a cikinsu duk wanda ya Rika cewa yake Sai na kashe ka al ameen. shi yasa suka kyale shi. shi kuma hankalin nashi ya kada ga tafiyarsa ya hau hanya. Tafiyar awa biyu yayi ya kawo wani gari A bakin gari yaga wani makeken Dam ๐ŸŒŠ
wanda duk mai hankali bazai yarda ya shiga ko baki-bakin ruwan ba. amma sai Al ameen yayi dariya da gudu ya nufi dam din ya fada ciki sai da kursiyya ta kaishi can nesa inda tasan daga ta fita a jikinsa mutuwa kawai Zaiyi. ai kuwa sai ta Fita Al ameen ganinsa yayi A tsakiyar Ruwa lokacin da hankalinsa ya dawo. kasa ya farayi yana sama Ruwa yana wasa da shi. nan take ya fara ihun neman dauki domin ko kadan bai iya ruwa ba.



Ya dade a wannan hali har ya zamana ihuu ma baya fitowa sosai. wata mota 407 dake wuce wa har ta Wuce naga tayo baya Wani mutum naga ya fito da gudu ya nufi dam din lokacin kuwa. Al ameen yasha Ruwa har ya Suma yayi kasa. dattijon na zuwa yayi super๐ŸŠ๐Ÿผโ€โ™€ ya fada Ruwan ya lume ya shiga lalube. yayi kusan mints 10 A kasan Ruwa can naga ya dago da Al ameen a kafada har yazo bakin Rafin Abokin tafiyarsa ne ya kama mai suka fito Da shi.
Sai a lokacin Kasumu ya lura da fuskar Al ameen ne mijin Yasmeen. Ai kuwa da Sauri suka fara danna mishi ciki Ruwa na fitowa ta bakin ๐Ÿ˜ช Tari ya fara a tare suka ce Alhamdulilah lokacin suka kamashi Suka saka shi mota suka yo gida...



Zainab kuwa da Husaini hanyar kano suka nufa su a zatansu can yayi Sunyi nisa Sosai saida sukayi tafiyar da sun tabbata mutun a kasa ko awa uku yayi yana tafiya bazai zo nan ba. amma shiru basu ga Al Ameen din ba kuma sun Cigiya amma ba wanda yace yaga ko mai kama da shi โ˜บ๐Ÿ˜Š ba yanda suka iya dole suka hakura suka dawo cikin gari suna Tambaya amma ba labari.


su kawu kasumu kafin su zo gida a hanya Al ameen ya Farka sai kuma ya tashi da wani irin Salo domin duk abunda ya dauka bugawa kansa yake. ko kuma ya buga kansa jikin mota da dai suka fahimci ba lafiya yake ba. dole kawu kasumu ya dawo baya yana Ririke shi domin Kuwa yawa Kansa mugun Rauni Sanadin buga kanshi da yayi a karfen motar.
Basu dade ba sai gasu a gida. M. lawal ya bude yana ganin kawu kasumu ya fara kiran. "ah boka boka" kawu kasumu ya juyo cikin fushi yace. "Bana san wannan sunan domin na dade da tuba yanzu nima aikin gadi nake a gidan wannan bawan allahn" ya nuna mai motar. mn lawal zai kara wata magana sai ya hangi Al ameen a cikin mota da Sauri ya zo ya kama suka fiddo shi a ririke sai hauka da Sambatu yake. M lawal yake tambaya ina suka samoshi. Kasumu yace" A can kusa da katsina ya fada Ruwa zai hallaka kanshi wai me ke Faruwa da shine naga yana abu kamar mahaukaci" M. lawal yace. "Ina tunanin dai iskokai ne domin matar shi da abokinsa a yanzu haka sun tafi nemansa" Al ameen ne ya kubce daga Rikon da aka mishi yaje ya dauki wata Wuka ๐Ÿ”ช Ta M. lawal Da niyar hallaka kansa ba dan Sunyi Saurin Rike shi ba. su husaini sun gaji da yawan nema a gari suka ce bari su dawo gida. A kofar gida suka hangi mota suka ce lalai akwai wani abu domin basu san mai motar ba da sauri husaini ya karasa tun a kofar gida suke jin hayaniya. da suka shiga Al ameen ne Ake kokowar kwace wuka a hannunsa wai shi sai ya yanka kansa....... .......................................................m









Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks





โœ๐ŸผAutan marubuta โœ๐Ÿผ



๐Ÿ‘‘King boy๐Ÿ‘‘



Last page In Shaaa Allah




๐Ÿ™Ž๐Ÿฟโ˜  MIJIN ALJANAH โ˜ ๐Ÿ™Ž๐Ÿฟ


page 146 - 147 THE LAST PAGE ISHA' ALLAHHH ๐Ÿ‘๐Ÿฝ


|
|
na king boy isah๐Ÿ‘‘
|
|
__________________________
๐ŸŒŸZAMANI APR 2017 ๐ŸŒŸ
|_________________________|




***** zamani *****
๐ŸŒŸZAMANI WRITER'S ASSOCIATION ๐ŸŒŸ ยฉZ.W.A
***** zamani *****









Da sauri su husaini suka karasa cikin gidan husaini ya tofa mishi ayatul qursiyya kawai sai yayi sanyi ya bar haukan da yake.


husaini yaja hanunsa suka shiga mota su kawu kasumu na binsu baya a tasu motar basu Zame a ko'ina ba sai kofar gidan M. Nasiru mai Ruk-yah


kai tsaye husaini ya shiga gidan Rike da hannun Al ameen kasan cewar kawun su ne M. nasir din.


Da suka shiga bayan ya gaida matar gidan ya tambaya ina malam?. matar tace wllh yaje can gidan su basmah wai iskokanta ne suka dawo.


Zainab tace iskokan basmah sun dawo! yayi yi sauri muje can din. ba'a dau lokaci ba suka karaso gidan su basmah din. malam zaune yake sai fama yake da Marsiyya taki ta fita shi har yama Rasa ya zaiyi da ita.


A lokacin suka shigo da Al ameen. Abun mamaki ana shigowa gidan al ameen ya dawo garas wato kursiyya ta tsere. Tambayar husaini yake wai me suka zo yi nan? husaini ma yayi mamaki ganin al ameen din da yake yunkurin kashe kansa amma gashi yanzu garas.



A zuciyarsa ya kawo cewa aljanar ce ta gudu da aka zo shigowa. Malam Al amarin marsiya ya bashi haushi ainun hakan yasa shi cewa a kawo mishi Ruwa a kwano. kafin a kawo da husaini yaga da dan space sai yace amma shima wannan aljana ce,



A jikinsa amma muna shigowa nan kaga ya ware" hannu kawai malam ya daga mishi.da aka kawo Ruwan yayi Ruk-yah a ciki tukun ya dinga karanta suratul baqara kuma yana dibar Ruwan yana watsawa a fuskan basmah din.


Marsiyya ihuu! take kamar wacce za'a cire wa Rai amma dan taurin kai cewa taki bazata Fita ba Sai dai in a kashe ta. lokacin Naga sauran dangi sun karaso su abba da dady har da Yasmeen.



A rude Yasmeen saida taga Al ameen din a zaune ya Natsu tukun itama ta sama nuTsuwa, kawu kasumu ta gani a gefe a zaune a zuciyar ta tace shi kuma wannan me yazo yi nan, lokacin ya waigo ta kuwa galla mishi harara, sunkuyar da kai kawai yayi, hajara ma tayi mamakin ganinsa amma ko kallonsa batayi ba. malam kam baya da Alamu tsayawa,



A karatunsa marsiyya kuwa sai kuka take tana ihuu! kursiyya ta fara kira "aunty ki taimake ni ki cece ni" kursiyya dake gefe Rasa yanda zatayi tayi domin tasa in har ta shiga hannun malam ta banu. Ganin ana neman hallaka kanwarta marsiyya kuma tasan halinta da Taurin kai ko tace ta fita bazata fita ba. haka yasa ta Yankr shawarar bawa malam hakuri. Jikin basmah din itama ta shiga.


A lokacin suka ji murya ta Rabu biyu daya nabawa malam hakuri daya kuma na kara. malam yace,"ke kuma wacece?." "sunana kursiyya kuma ni yayartq ce dan allah kayi hakuri kabar toya ta"



Al ameen Tsuru yayi yana kallan basmah da bakinta ne ke mutsi amma duk wanda yaji yasan ba ita ke magana ba. malam, "au dama kece kursiyyar ke me yasa kika addabi Rayuwar wannan bawan allahn kuma har ta kai ga kina neman halaka shi kina so ki rabashi da Rayuwarsa"



"Malam shi yasan abunda yayi min Aure na yayi ta waya bayan baisan ko ni din wacece ba kuma baiji ko muryata ba balle yaga pic dina a haka ya aure ni ya Rabani da masoyina kuma yamin alkawarin bazan kara aure ba sai gashi nazo gidansa naga yana da mata amma sbd san da nake mishi banyi mishi komai ba a lokacin kuma sai na boye kaina ma idan ma ina san wani abu a gurin shi sai dai inyi suffar matarshi."


Al ameen

Please Login or Register in order to submit comment