Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsaya. Fitowa tayi ta shiga sashen wasu wakokin. Abun haushi abun takaici dana leka wayar folder wakokin inya murai ne kala kala irin su davido. WizKid. P.square. d'ja nick minaj. Kai tarkace dai wanda wasu ma bata san abunda suke cewa ba. Abun haushi ba ko wakar hausa a wayar ta balle ayi maganar wa'azi.




(Na kalle nasmat nace lalai wannan tayi nisa ace mutun ba ruwansa da wa'azi ma a waya balle ayi maganar karatu. Nace wai ma in tambaye ki a gidan nan akwai al qurani. Nasmat tayi Murmushi tace to cikin su wa zai karanta ni fa tunda muka shigo gidan nan ma sau daya naga yasmeen tayi sallah karatu kuma ko aya daya. Nace tabb lalai dole su kursiyya susha shagalin su. )




Cikin wata irin jagulalar murya taji ana wakar dorobucci din kuma ba kida jimawa kadan kuma taji an kara sauyawa an kara chanza muryar. Iyafiss din ta cire da sauri a kunnanta tana kallansa. Can kuma sai ta fara jin motsi a parllo. Wanke-wanke ta dakata daya ta nufo parloo dan ganin abunda keyin motsi. Kamar munahika haka take tafiya. Lokacin da tazo parllan ne ta duduba sai can ta hangi labule na motsi shi kadai. A tsorace take amma tace sai fa tajw ta gani ko miye a ciki. (Kmr in ce karta je nidai)





Gafda da labilan window din tajw ta mika hannu tana karkarwa duk a tsorace tana finciko labilan ta daka wani uban ihoo sakamakon jin wani abu da ya daki fuskanta ya wuce. Da sauri ta juya dan ganin miye. Wata bakar mage ce mai ido jawur. Ta tsare yasmeen din da kallo. Yasmeen ta danyi ajiyar zuciya ganin ashe mage ce ma.


Yun kurin korar magen ta farayi tana nuna mata hannu. Tana fadin shitt! Tafi! Wace daga nan! Mage kuwa sai ma kara matsowa tayi taku biyu. Yasmeen ta cire takalmin kafanta tadinga shunawa magen nufinta ta tsorata ta. Magen kuwa fur taki ta ko motsa kamar wace take a gidan ubanta sai ma zama tayi a gun. Tana lasar gashin jikinta.


Yasmeen tace yau naga jaraba wannan wace irin mage ce haka da jaraba gata ba kyan gani um! Bari dai in rabu dake inje inyi aiki na. Yasmeen ta juya ta fara tafiya. Tana tafiya magen nabinta a baya bata lura ba. Saida ta kusan zuwa kitchen tq juyo. Mage ta gani biye da ita. Kan uba! Wai bazaki bar gun nan ba. Shitt! Wuce! Mage kuwa sai ta kara zama kmr dazu.



Yasmeen Takalmin dake hannunta ta wullawa mage da niyar ta same ta habawa cikin zafin nama magen ta kauce. Dayan takalmin ta cirw ta kara wullawa abun mamaki magen da baki ta cafee shi. Al amarin da ya tsorata yasmeen kenan ta ruga da gudu cikin kitchen ta kullo kofar ta fara maida nunfashi. Tsoran maida aifis din tayi shi yasa yanzu ta kunna waka kawai ta budw volume na wayan taci gaba da wanke wanke.



Can anjima ta fara jin wani kalan dariya kamar na dan jariri sai dai kuma marar dadin ji. Yana fitowa daga gefen damanta. Karan dariyan har ma ya wuce na wakar da take ji. Ta hantsar ido ta dinga hangen wani bakin abu suman tsaye tayi tukun ta fara juyawa kamar mai sankarau. A hankali takw juyawa da kan nata. Idanunta ne sukayi tozali da jajayen idanun magen nan kuma ita ce ke dariya ga bakin ta da wasu shegun hakora dogaye ne amma duk a rube suke. Kara ta saki ahhhhhh! Ta warci wayanta tayi out a million.





Juyowa tayi baya tana cikin gudun jin dariyar nan a bayanta magen ta gani har ta kusan kamota. hakan yasa kara warewa ta nufi dakinta a million. Tana shiga ta turo kofan kuma ta saka key ta morda bayan nan ta danne kofan. Magen na ganin hakan sai ta rikide ta dawo marsiyya. Dariya na hange kursiyya dake zaune a sofa tana ta kyalkyalawa. Marsiyya ma ta fara dariya tace aunty kinga an fara wasan ko ai yau kam bazan barta tayi sakat ba duk da dai naga kmr kin huce. Kursiyya tace sis ai ko haka kika barta ma ya ishe ta ga tsoro ga jan fada kenan. Marsiyya tace wai hk suke daman sai faman iho ba addu'a. Kursiyya tace eh mn ai mu gwara hkn domin gaba ta kai mu..



Al ameen bayan ya gama duba patients dinsa yabawa wasu kuma magani sai ya dawo office ya zauna ya fara sana'ar tasa. Yauma yayi sabowar budurwa a wani group shi yasa ya kirata. Idan kaji yanda suke waya sai ka rantse kace sun dade suna soyayya wato dama can masoy ne bayan kuma haduwar jiya ne. Kursiyya haushi da kishine suka kule ta me wannan yake nufi ne wai wama yake waya da ita ne. Batt ta bace sai a wani kasaitacen daki dan karami madaidai ci ta bayyana can gefe kuma wata hadadiyar yarinya ce a kan bed ga dukan alamu da ita ne al amin ke waya.



Wata rudadiyar dariya dakin ya dauka hahahahaha ke karamar marar kunya ki fita daga harkar mijina baiyi kama dake ba kinji ina gaya miki yafi karfinki dan kima sani hahahahaha.....


اعو ذ بكلمت الله التا ما ت التي لا يجا وز هن بر ولا فا جر من شر ما خلق وبر ا وذرا ومن شر ما ينز ل من السما ع ومن شر ما يعر ج قيها ومن شر ما ذرا في الا رض ومن شر ما يخر ج منها ومن شر فتن الليل والنهار ومن شر كل طا ر ق الا طارقا يطر ق بخير يا رحمننژو ″


A'uzu bi kalimatil laahi tammaatil latii laa yujaawiZuhunna barrun walaa faajirun min sharrin maa khalaka, wabara'a wa zara'a, wamin sharrin maa yanzilu minas samaa'i wamin sharrin maa ya'ariju fiihaa, wamin maa zara'a fil ardhi wamin sharrin maa yakhruju minhaa, wamin sharrin fitanil laili wannahaari wamin sharrin kulli daarikin illa daarikan yadruku bi khairin ya rahman”.



Wannan addu'a zainab ta fara karantawa nan take naji kursiyya ta kwalla uban ihu tayi waje. Zainab tayi ajiyar zuciya tukun ta kara da ayyatul kursiyya ta tofa a ko'ina na dakin.






( na kalli nasmat nace su kursiyya fa yau ba'azo a sa'a ba. Tace eh mn ai dama su al ameen ta raina su yasmeen su da yake ba ruwan su da Addu'a wannan addu'ar fa da kaji ta karanta to duk wanda ya karanta ta allah zai kare shi ya kuma tsare shi ga duk wani shaidani ko sharri sai dai alkhairi ya same shi a ranar amma fa in yayi iklasi wato ya dogara ga allah idan yayi addu'ar ya kawo a zuciyarsa ta karbu. Nace kai kai wannan garabasa haka ai kuwa zanyi kokarin hardacewa ko saboda marsiyya karta kawo min farmaki wataran)




Xainab da suke waya da al ameen bata ce mishi komai ba sai dai tasan tabbas rayuwarsa na cikin hadari wato aljana ta aure sa. Kursiyya a galabaice ta kuma gida marsiyya ta tare ta lafiya kursiyya ta kwashe labarin ta gayawa marsiyya komai marsiyya tayi Murmushi tace aunty ki bar komai a hannuna idan tasan wata ai bata san wata ba idan kuma tana takama ita ta iya addu'a ai al ameen din bai iya ba. Dan hk bari inje in magance matsalan.



Marsiyya direct gidan su zainab ta nufa da farko tun daga nesa take jin wni masifafan zafi karuwa yake ita kuma tana nufarsa. Wato abunda na lura dai karfin addu'ar zainab ne. Marsiyya ta hangi gidan zagaye da wuta ba hanyar shiga (wato dai allah ya sa musu guards na wuta a gidan ya ba shedanin da ya isa ya kusanci gidan sanadin addu'ar nan. Hkn yasa ta ta juya ta kona office din al ameen.



Al ameen bayan sun kamala waya da zainab yayi Murmushi yana kallan pic dinta data turo mishi. yace yarinya kenan ai kema kin kusan shigowa hannu ke bazan yaudare ki da wuri ba domin fuskan ki nada kyau hk ma muryarki akwai zaki dan hk zamu dan dade maybe mu kai wata. Ya dora ma pic din kiss ya ajiye wayar. ( nace tabb wannan babban mayaudari ne wato wata shine dade wa)




Yan dube dube yake yi a takardu wani daga cikin abokan aikinsa ya shigo cikin hanzari yake yi mai magana al ameen kayi sauri taso taso. Al ameen da shima ya dan daga hankalin sa jin irin wannan kira haka. Ya fara tambaya lafiya lafiya. Mutumin yace ba lokacin bata wa taso dan allah. A kidime ya tashi yabi bayan abokin nasa gudu gudu sauri sauri suka nufi wani bangare dake cikin general hospital din.



Marsiyya a daidai lokacin ta bullo a office din ganin wayar al ameen da tayi yasata tayi tace da kyau. Wayar ta dauka ta lalubo number zainab ta kira before ta canza murya. dawo da muryarta ta al ameen. Zainab taji wayarta ta hau Ring da sauri ta dauka dan ganin waye. Al ameen ta gani shi yasa tayi Murmushi tace wato baka gaji da jin muryata ba ashe. Ta dauka ta makala a kunne hello Darling.




Daga can marsiyya tayi magana cikin muryar al ameen ba banbanci ko kiris tace hello zeeluv dina. Zainab tace ya naga ka sake kira ko mantuwa kayi ne? Marsiyya tace ko kadan dama kiranki nayi in gaya miki magan mai muhimmanci zainab tace to ina jinka babyna..........................................

Good morning happy juma'a al mubarak

Little of writer's

King boy











🙎🏿☠ MIJIN ALJANAH ☠🙎🏿


page 69 - 70


|
|
na king boy isah👑
|
|
__________________________
🌟5STAR APR 2017 🌟
|_________________________|




***** 5 star *****
🌟5⃣STAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION 🌟 ©5SWA
***** 5 star *****


🌹🌹 dedicated to u zainab yusuf ina godiya da addu'a ki na alkhairi a gare ni ☺


👺👺 sako daga nasmat to readers nasmat tace duk wanda ya karanta wannan page din da rana wuta balbal 😂 ni dai ba ruwana👺👺






Wato a gaskiya dama abunda nake so in gaya miki shini ki fita daga harkata don a gaskiya ba sanki nake ba koda kuwa munci gaba da soyayya to dan in faranta miki kawai zanyi ba wai dan ina sanki ba. Gaban zainab ne ya fadi jin abunda al ameen din ke fada. Koma sai tayi ajiyar zuciya tace.




Naji na gode kuma da ka sanar dani tun yanzu baka bari sanka ya mamaye ko'ina na jikina ba bisa wannan godiya zanyi maka. Amma ina so in shaida maka cewa yaudara ba abu ce mai kyau ba idan kayi wa yayan wasu kaima sai anyi wa naka. Kuma al ameen bana sanka na rabu da kai har abada baza ka sake jina ba. Mtsewwww.ta katse wayen tini ta sankama shi a block wanda ko massage dinsa bazai shigo ba haka ma a whatsapp din tayi block dinsa.





Marsiyya nan take itama tayi block din number zainab wata shu'umar dariya tayi tukun tace shikenan an wuce gun aunty kisha kurumin ki al ameen naki ne ke kadai bari mu koma ga yasmeen itama.



Ba'a dade ba sai naga al ameen ya dawo cikin hanzari ya dauki wayansa da ya manta a lokacin ya kira yasmeen yake shaida mata da cewa tafiya ta kama shi kuma yana tunanin zai fi kwana biyu a can inda zasu din. Gaban yasmeen ne ya fadi ta dafe kirji al ameen me kake fada haka wannan wane irin tafiya ne ni gaskiya ban amince ba.



Kiyi hakuri yasmeen nasan bazamu kai sati ba kuma nasan cewa ban kyauta miki ba amma ba yanda zamuyi domin wannan umarnine daga sama kuma tafiyar nada mahimmanci. Ke dai kawai ki kula.



Al ameen ni gaskiya bazan iya zama a gidan nan ni kadai ba mu biyun ma idan ka tafi aiki karka ga yanda ake tsorata ni balle kuma ace baka nan.




hb yasmeen ba abunda zai kama ki bafa ke kadai bace a gidan ga mai gadi kuma ga driver ni dai dan allah kawai kiyi min fatan alkhairi kinji. Yana fadin haka ya katse wayan domin shi kadai ake jira har ma an fara kwalla mai kira.



Yasmeen jinta tayi jikinta duk ba kwari yanzu gidan nan za'a barta ita kadai gaskiya idan aka cika bata tsoro bazata iya zama ba. Ta gaji da zaman dakin hakan yasata tasowa kamar muna hika take bude kofan sai da ta leko taga magen bata nan tukun ta fito. Fridge ta nufa ta dauko coca cola da dan kofi ta dawo ta zauna gaban katuwar tv din ta kunna kallo.


Arewa 24 ta ke kallo suna wani shiri na addini tsaki tayi ta fito ta fara chanza channel mbc action ta shiga da shigarta da fitowar wani mugun kara duk daya. Nan take ta done kunnuwa. Ta dago kai ta tv da alamu dai film din horror ne domin idanuwanta ne suka yi arba da wata mumunan halita wacce daga ka ganta ma ba sai ance maka zatayi mugunta ba abun wani tsanwa tsanwa ne idanuwansa jajaye hakoransa kuwa wasu zakozako ne dogaye wanda a gabanta ya raba wani mutun gida biyu da hakora.




Tsayawa tayi tana kallan nan ma tana waige waige ita ko me yasa take san kallan horror film ba. Daga cikin dakinta take jin irin karan dabar dake cikin tv abun sai karuwa yake. Zuwa can kuma sai wutar dakin






Dakin yayi duhu baki kirin gabaki daya ko tafin hannunta bata iya gani lalube ta shiga yi ko zata ci sa'a ta iske window ta bude labule domin yanzu rana ce tsaka tunda ynz dudu 12 ne. Kamar makwainiya haka take ta lalube a daki. Garin lalube taji taci karo da wani abu lalubawa tayi taji jikinsa duk gashi ne. Ita kam ta rasa miye wannan domin aduk parllon ta ba abu makamancin haka.





Ci gaba tayi da laluba abun domin ta tabbatr da ko miye nan ta nufi tataba. Saman abun taji kaho a kai. Bata dadare ba tayo kasa da hannu wajen fuska taji ido lafiya lau da baki da hanci duk irin na motane. Ihoo ta kwala taa waaaaahh!! Ta fara ja da baya-baya tana fadin waye mutun ko aljan waye👺 ido abun ya bude taga hasken idanun kamar danja.





Kara tsalla iho tayi a cikin duhun ta fara gudu duk da bata san inda take nufa ba. Wani gun taci karo da kujera wani lokacin taci karo da bango haka tata xagaye parllo tana iho. Ji tayi wata mahaukaciyar dariya ta barke hahahahaha! , hahahahaha!



" ke yasmeen ki natsu cikk ta tsaya tana karkarwa cikin duhu tana dube-dube. yanzu ne lokacin da ya kamata in bayyana miki kaina koma ina umartarki da kisa al ameen ya sake ki domim nice nan kursiyya matar al ameen idan kuma ba haka ba zaki hadu da bala'i da masifu daban daban irin wanda baki taba tsammani ba a cikin gidan nan sannan daga karshe dole ne ki bar gidan wannan zabi ne na baki ki fita da laluma ko ki fita ta tsiya.








Yasmeen wani karfin hali ne da kuma rashin tsoro suka zo mata a lokaci guda. Tace " karya kike ko ke wacece baki isa ki rabani da al ameen ba karyarki tasha karya al ameen nawa ne ni kadai ba wata ya macen da ta isa ta mallaki al ameen a matsayin miji cikin mutun ko aljan bayan ni nan yasmeen kuma in ma kina mafarkin hakan ne to ki daina domin wannan tsafe tsafen naki da kike yi dan ki tsorata ni ki sani daga yau na daina tsorata kuma zan nuna miki ko ni wacece zaki san kin taba yar gado.






Dakin ne gabadaya ya rude da wata irin mahaukaciyar dariya mai fita biyu biyu hahahe hehehehe hhhhh 👹👺 ke yasmeen kinyi kuskure na fada min wannan maganganun yanzu dai kina nufin wato dani zaki ja ko? To mu zuba ni dake. Yasmeen karkarwa tsoro ta fara yi domin tasan cika baki ne take.




Yasmeen dan lumshe idanun da tayi bude warta ke da wuya idanunta sukayi arba da wata irin halita a gabanta daf da ita. Wani irin abu ne kanshi sumul sai gashi da baifi a irga ba. Idanu kwala kwala ba irin na mutane ba. Ga hancin wani dogo da shi. Kunnuwan budewa suke suna rufewa abun ban tsoro. Daga baki abun yayi yasmeen tana ganin hk ta sulale kasa sumamiya domin daga bakin abun ya kara mishi muni da ban tsoro hakoran a rube suke ga wasu bakaken tsutsotsi yan kanana cike da bakin suna ta motsi a ciki.




Kursiyya dake gefe tace sis me yasa kikayi haka ai naso ace kin kyale ta muga abunda zatayi nidai nasan ba . Tunda nasan ba addu'a datayi ba kinga kuwa ko me zatayi bayan wannan ba tsoranta damuji ba.



Wannan halittar ta taho tana dariya ba kyan gani tsutsotsi na zubowa daga bakin ta nan na fahimci cewa ba wata bace marsiyya ce ta zama hannan halittar👹........................................................,.....



😀 GOOD NIGHT muga wacce datayi mafarkin marsiyya yau 😀




Little of writer's ✍🏼


👑king boy 👑















🙎🏿☠ MIJIN ALJANAH ☠🙎🏿


page 71 - 72


|
|
na king boy isah👑
|
|
__________________________
🌟5STAR APR 2017 🌟
|_________________________|




***** 5 star *****
🌟5⃣STAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION 🌟 ©5SWA
***** 5 star *****
















Aunty kyale ta ai gwara ayi mata hk kina ji fa abunda take gaya. Kursiyya tace kinsan me yanxu abunda nake bukata shine kafin ta farka mu gyara komai na parllon nan. Marsiyya ta dawo yanda take tace na gane kafin 5minutes tuni har sun gyara komai aka dau yasmeen aka kaita dakinta kan gado.



Yasmeen ta dade a kwance tukun ta farka ji tayi kanta nayi mata ciwo-ciwo nan ta fara tuno abunda ya faru kuma mamaki ya cikata data tashi ta ganta a kan gado ta rasa waya kawo ta. Yasmeen ta taso ta nufi kitchen domin ta girka abinci domin yanzu karfe 1 tayi. Tunani take me zatayi Murmushi tayi domin tinawa da tayi da barjajiyar shinkafarta wace datayi dambun shinkafa ranar al ameen ya hana. Shi yasa tace to bari kawai tayi yanzu.


Bayan ta wanke barzzazar shinkafarta tsaff ta zuba a madam baci ta rufe da leda tukun ta dora wata tukun yar ta zuba ruwa madaidaici ta dora a wuta ta dora madambacin ta rufe ruff. Ta dawo ta tafasa karas dinta da koren wakenta tukun ta yayanka su tare da kabeji da albasa da attaruguzu ta yayanka su gutsin gutsin. Bayan garin yayi laushi ta sauke ta zuba mai ya kama garin shinkafar sosai tukun ta dauki kayan lambun nan ta zuba ta cakude ya gaurayu tukun ta zuba magi da gishiri.




Ta dauko tafasashiyar hanta ta yaya itama ta zuba a ciki ta chakude tukun ta sake kunna wuta ta dora. Dan lokaci kadan ta bashi misalin 5mint taji ya fara kamshi hakan ya tabbatar mata da ya daho takin ta ta nufa domin ta dauko wayarta. Bayan ta dawo kitchen tsaye tayi ganin abunda ya faru an sauke tukunyar an deba abincin duk ga dai wani a plat nan an bari. Karasawa tayi ta duba taga dai tabbas hkn ne ta duduba kitchen din gaba daya bata ga komai ba tace ko dai bera ne ko kuma mage. Murmushi tayi tace haba ai wata dabar bazata iya yin wannan aikin ba kawai matsafiyar matan nan ce wace ke san al ameen. Tace amma ba komai taso zaman lafiya tunda ta bar min nawa abincin. Na cikin plat din ta dauka ta nufi dinner




Abun mamaki a dinner tebur ta iske plats biyu anci abinci a gurin. Kai kai wllh na gaji baxan iya zama ni kadai a gidan nan ba wannan bala'i har ina bari in gama cin abincin nan in kira anty hajara. Gwara tazo asan matakin da za'a dauka.




Tana cikin cin abincin ta wutsiyar ido ta dinga hango wani abu na lekowa daga dakin umma daga ta juya gurin kuma sai taga ba kowa. Har dakatawa tayi da cin abincin ta maida hankalin ta ga kofa. Daga taga abun ciki hanzari take juyawa. Abun mamaki kuma sai taga kofar a rufe ma. Ta ci gaba da cin abincin. Amma ina kofar aka fara budewa ana rufewa da karfi. Abincin bai sama ciyuwa ba ajiyewa tayi ta tashi ta nufi dakin har yanzu dai budewa ake ana rufewa.





Wata dariya taji tana fitowa daga dakin kmr dai dan jariri ne keyin ta Hhihihihiehehe hakan yasa ta juyawa baya da gudu ta nufi dakinta. Tqna shiga ta bank kyauran wayarta ta dauka tayi calling din anty hajara sai a karo na biyu aunty hajara ta dauka. Cikin muryar wanda yake a firgici takr maganar aunty kizo ba lafiya kiyi sauri dan allah gidan ba lafiya pls aunty. Tambaya take lafiya lafiya yasmeen me ke faruwa ne amma ina bata bata amsa ba ta kashe wayan. Da sauri ta dauko gyalan ta ta yafa. Yar yarinya ce karama a zaune tare suke kallan hajara ta kalle ta tace nuratu idan mum ta fito kice mata naje gidan yasmeen kinji. Nuratu tace to mum me zakiyi a can.



Hajara ta juya ta kalleta tace ni ma ban sani ba sai najr na gani. Mum nima zanje. aa nuratu ba ynz ba xamu je dake wqtaran. To ki gaida min mumy na da uncle al ameen da baba mai gadi da driver da..... Kai nuratu surutun ki yayi yawa naji xan gaida kowa da kowa. Hajara ta juya ta fita. Da sauri ta tsaida napep daidai kofan gidan aka ajiye ta ta biya mai adaidaita tukun ta karasa cikin gidan.



Bayan sun gaisa da mai gadi da deriver take tambayar su me ke faruwa. A cikin gidan domin yasmeen ta kirani tace inzo maza maza. M lawal mai gadi da idi suka kalli juna tukun suka ce wani abu kuma aa mu ba abunda ya faru a gidan na. Hjr tace to shikenan bari in shiga cikin in gani har zata wuce kuma sai ta juyo tace na mantq in gaya muku nuratu na gaishe ku ku duka.




Sukayi Murmushi muna amsawa yau ina take ne. A gida na barota domin tahowar gagawa ce nayi. Lawal yace ayya a gaida ta in an koma hajara tace data ji.



hajara da sauri ta nufi cikin gidan kai tsaye ta shiga ko sallama babu. kira ta fara kwallawa yasmeen! yasmeen kina ina. but shiru taji.



kitchen ta leka bata nan hakan yasa ta ta nufi dakin yasmeen din tana tura kofa ta hangi yasmeen din a kan bed ta wani kudundune.



hajara ta fara tambaya lafiya kuwa yasmeen yayin da ta karasa wajenta. anty hajara wllh ba lafiya gidan nan aljanu gare shi ko aljanu ko kuma fatalwa. hajara tayi Murmushi tace haba dai yasmeen ina ganin ki wayya ashe baki waye ba ai wannan maganar duk shirme ne kawai tsorata dai kike yi. ina al ameen din?




ya al ameen sunyi tafiya yau tafiyar gagawa ce tazo mai domin nima sai ta waya mukayi bankwana. hajara tace ohh wato kice dai so kike inzo in tayaki zama a gidan kafin ya dawo ko. to ai dan wannan da ba sai kinyi karya bama da wai aljanu.




yasmeen tace wllh anty da gaske nake domin yau an tsorata ni sosai wllh. hajara tace ke rabani da zancen nan. yanzu dai ina abinci domin ni yunwa ma nake ji me kika dafa. yasmeen tace dambun shinkafa nayi amma har ya kare aljanu sun cinye



Hajara tayi Murmushi tace wai aljanu sun cinye ke me yasa kin cika karya ne wannan maganar ai ba mai yuyuwa bace kinga nidai tashi kije ki girka min domin nasan babu ne. Yasmeen tayi Murmushi to aunty me kike so in dafa miki ne?




Ta dan yi tunani kadan um! Kawai dafa min indomie dan inta ce mai saurin dahuwa kar in wahalar dake. Aa aunty ai ba komai fadi duk abunda kike san ci.




Kinga kedai dafo indomei din domin wllh da yunwa na taho. Yasmeen tace baki ci abinci banr ko ba'ayi ba a gidan. Anyi mana baidai karasa ba.

Please Login or Register in order to submit comment