Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya bar kursiyya datake da sifar Yasmeen yana fita ta kama wata shu'umar dariya hahahaha wanda yasa gabaki daya fallan amsawa. bacewa tayi taje ta dauko yasmeen da take ta sharar barcin ta har ynx.









kan sofa ta kwantar da ita kamar yanda take da. a hankali fuskan kursiyya ta fara sauyawa ta koma kamanin ta. yasmeen bata tashi ba sai karfe uku harda mint 6 tana tashi ta dubi agogo tayi mamaki sosai saidai ba wannan ya bata mamaki ba dinner da ta hanga alamun ance abinci.







da sauri ta mike zumbur ta nufi dinner din. bata rai tayi tukun tayi tsaki mtseeww wai ni al ameen me yasa yake min hk da safe yaci abincin sa bai tayar dani ba kuma ynz ma haka. ta nufi daki da niyar ta dauko waya ta kira shi taji dalili.









al ameen bayan ya koma office yaga ba aiki hakan yasa shi bude data. nan fa massage suka fara shigowa. al ameen ya shiga dubawa. al ameen ya kasance mutun ne mayaudari amma fa na yan matan whatsapp domin a halin ynz yan matansa sunfi a kirga wasu ma har mantawq yake da su.






massage din wata number mai suna yar wahala naga ya bude massages ne kamar haka"







Β° bayan salama da fatan alkhairi masoyina ina so kasani cewa jiya banyi barci ba kwata kwata dan rashin ganin reply dinka kwana nayi a online amma baka zo ba why.

srry my sweet karki damu kaina ne ke dan yi min ciwo shi isa na dan kwanta.


bai karanta sauran ba yayi tsaki ya fito daga massage din lokacin husaini ya shigo.office din. yayi mai sallama. ah sai ustaz ya akayi ne.






lokacin usaini ya karaso wato kaidai har ynz bazaka canza halin ka ba na kin amsa sallama ko ynz kayi asarar lada goma fa.






al ameen dan sosa keya yayi yace au srry fa wslm. gidan ku ne wslm din baraka amsa min sallama cikaka ba wato chat ya bata ka baki daya ko al ameen. dariya al ameen yayi.




kuma nace ma ka daina cemin ustaz din nan karma mutani suji su zata ni din wani malami ne ku dama mutanan nan daga fadin gaskiya sai ku fara cewa mutun ustaz shehu miye da miye.






al ameen yace ynz dai ba wannan ba dama ina so in baka wani labari baka san nayi saban kamu ba ko. usaini ya kalle shi cikin rashin fahimta yace ban gane ba me kake nufi.





al ameen yace bazaka gane ba kai kam ai shekaran jiya nayi sabuwar budurwa galeliya har a ledan ta. usaini yace hmm budurwa kuma ai ni har nagaji da ji indai a gunka ne domin kusan kullum idan muka hadu sai ka fadan kayi sabuwa.






kai wannan fa ta daban ce karkaso kaga yanda ta damu dani al ameen yayi murmishi yace wai kasan wani abu irin auren whatsapp din nan mukayi amma da ango take kirana.




usaini yace uhm lalai tsageran cin yayi yawa wato har wasa da aure kuka a whatsapp din ko to wllh zai iya dauruwa da gaske indai kunbi ka'ida


kai dallah share duk shirme ne ba wani gaske ba. messages din photos yagani a number kursiyya yauwa yar albarka ashe ma ta turo pics din ya kalle usaini yace matso kusa ka ga matan manya domin nadan babbar yarinya ce.






usaini ya matsa yana murmushi. me zasu gani kuwa inba photan................................. kuyi hkr fa sis nasmat nace ta leko min pics din taki amma bari in leka da kaina.

shiga nan kayi like din page din mu domin karanta sauran labarin

https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarks

king boy












πŸ™ŽπŸΏβ˜  MIJIN ALJANAH β˜ πŸ™ŽπŸΏ


page 23 - 24


|
|
na king boy isahπŸ‘‘
|
|
__________________________
🌟5STAR MAR 2017 🌟
|_________________________|




***** 5 star *****
🌟5⃣STAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION 🌟 Β©5SWA
***** 5 star *****

...
.




*wannan page din naku ne yan samari facebook luv kursiyya tace in gaida ku. lolz*







(ina lekawa nayo baya da gudu. nasmat tayi dariya tace
me zan gani hk kaifa namiji ne. kardai ace duk abunda kake fada cika baki ne. hararenta nayi nace da kinga pic din ba kyan gani abun tsoro bari dai in dawo in baki lbr na juya na koma )






al ameen da husaini kallo daya sukawa pic din suma basu yarda sun kara ba.


pic din wata halita ce mace amma bakikirin da ita kamar gawayi ba abunda kake gani a jikinta sai wasu jajayen idanu chaka-chaka a jikinta tana da bindi ( hutsiya) bakin ta wani wakeke ne idan kasa jariri zai shige. kafafun doki ne da ita hannuwa ma kofato ne.







kana iya ganin abubuwan cikin kanta su kwalwa ne da sauran su. bayan al ameen ya goge pic din yayi tsaki mwtseew data tsorata mutane hk kurum.







husaini da shima kansa ya tsorata sai kuma abun ya bashi dariya ganin yadda al ameen din ya tsorata. dariya yake kyakyala masa. hada rike ciki al ameen ya harare shi. malam ya isa haka.




husaini ya dan sasauta dariyar yana mgn cikin dariya- dariya toh toh shikenan. kallan al ameen yayi yace _MIJIN ALJANAH_ ya kuma kyalkyale wa da sabuwar dariya. husaini kaga ni fa bana san wannan abun miye kuma na dariya hada ce min wani _MIJIN ALJANAH_ toh ni allah ma ya shiga tsakanina da su ni fa ka sani duk gidan mu ma aljanu tsoran su suke because ba wanda aljani ya taba shiga. aha.








to naji usaini ya fada lokacin ds ya dakata da dariyar yace ba wanda aljani ya taba shiga amma inaga ai kai ka kwaso ta domin ni ko a fim din horror ban taba ganin kalan hallita mai ban tsoro irin wannan ba.





al ameen yayi yar dariya yace kaji matsoraci kawai inaga tayi ne dan ta tsorata ni kuma gashin ban tsorata ba sai kai.





hmm muka tsorata dai in baka tsorata ba kai miye yasa ka gogewa kaji mutun. al amern wllh ina gayama ka kula domin ynz al jannun ma chat suke sosai sai su shigo cikin mutane atayin harka da su kuma bazaka taba ganewa ba.






al ameen dariya yayi sosai yace amma gaye ban san kai mugun matsoraci ne ba sai yau wato dan kaji ana cewa wai aljanu na chat har ka wani dauka to ya za'ayi ma aljani yayi amfani da waya bayan ba ganin su ake yi ba kuma su iska ne.







husaini yayi murmushi yace to naji amma kasan cewa aljani yana iya rikidewa ya zama mutun ko wata hallitar ko. al ameen zaiyi wata mgnr husain ya daga mai hannu kaga bani amsa eh ko aa.





eh hk aka ce amma ni sam ban yarda ba. husain yayi murmushi yace to kar allah yasa ka yarda amma tunda suke iya zama mutun kuma suna ci suna sha to kaga kuwa dan su sayi waya suyi chat ba wani abu bane kadai kawai ka kula ka rage yaudarar yaran mutane .






al ameen yayi dariya yace ai gaye ba abunda za'a fasa kaga wannan yarinyar. ya nuna mai number da aka rubuta yar wahala. husai ni yace ai yar wahala aka rubuta.




eh sunanta fauziya tun da na tura mata pic dina ta rikice ni kuma wllh yarinyar bata min ba ko kadan dan karka so ka ganta wata black.





husaini yaja tsaki mtseeww to uban wa yasa kace kana santa da farko ai dai nasan ba ita ce zata fara cewa tana sanka ba dan hkn abu mai wuya ne.





al ameen yace gaye karka so kaji muryar yarinyar it ix very sweet but her face ix bad 4 me.




allah ya sawake ma yasa ka gane kuma. al ameen yace ba amin ba domin ina nishadi sosai inga budurwoyina 5 ko sama da hk a online ko wacce kuma bana bari tayi chat da wani ko wata sai ni in dai ina on gaye ka shigo harkar nan fa zan baka number yarinya 20 domin ni sunyi expired a gare ni dan ni delet dinsu ma zqnyi.





allah ya kiyaye min wllh ba dani ba kaga bari in koma office dina nima naga ba aiki ne nayo nan. husai ya juya yayi hanyar fita. al ameen yace to matsoraci sai ka dawo husaini yace matsorata dai ya fita yana dariya.


husaini bai dade da fita ba wayar Yasmeen ta shigo. dauka yayi yace hello my dear gaskiya abincin ki na yauma yayi min dadi sosai.





Yasmeen tace ai mun bata da kai yau fushi nake da kai.




cikin wata irin murya yace haba my sweet wife me kuma nayi da za'a bata dani laifin me nayi?






Yasmeen tace ai laifi ba daya kayi ba har biyu ma .






na shiga uku na. ya fada cikin zolaya ni din ?


Yasmeen ta danyi gungunin kuka cikin shagwaba tace. " shine zaka ci abinci kai kadai kuma kana gani na ina barci kakk ka tada ni ko laifi na farko kuma da safe ma hk kamin why.?





al ameen yayi jim kadan ya rasa me xaice mata can kuma sai ya basar yace maybe wasa take yi bari nima in mayar mata da martani.







" shima cikin shagwaba kmn yadda tayi yace to sarauniyata ayi hakuri aiki ne yamin yawa gashi nan tuli a office but baran kara ba.





Yasmeen tace. uhhm uhhm baran kyale kaba sai nayi maka hukunci zaka dawo gidan ai ka same ni.





al amin yayi dariya yace wow i want wllh indai irin na jiya ne. zan dawo ma da wuri me zan kawo miki.





yasmeen duk da ba tare suke ba saida ta rufe ido tace uhm ka taho min da kankana mai zaki. yace shi kadai. tace da buhu uku na kiss.... ta katse wayan.




dariya al ameen yayi cike da farin ciki ya fada a fili buhun kiss ko to ai hikenan yarinya kin samu.




kursiyya dake zaune a kan wata kujera dake office din nasa ta zuro mai jajayen ido zumbur ta mike jin abunda ya fada. a zuciya tace duk kuwa yanda za'ayi ni zakawa kiss din nan.........................,.........

*sis nasmat tace a gayawa kursiyya bata isa ba ita za'awa kiss din to nidai ba ruwa na. ke da ita ne in kuma a kwai wacce itama zata ja da kursiyya to.lolz*




shiga nan kayi like din page din mu domin karanta sauran labarin

https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarks

king boy



dan autan writer's king boy
















πŸ™ŽπŸΏβ˜  MIJIN ALJANAH β˜ πŸ™ŽπŸΏ


page 25 - 26


|
|
na king boy isahπŸ‘‘
|
|
__________________________
🌟5STAR MAR 2017 🌟
|_________________________|




***** 5 star *****
🌟5⃣STAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION 🌟 Β©5SWA
***** 5 star *****

...
.



wannan page din naku ne yan group din 3star hausa novels thanks an ur Pray to me aci gaba da gashi kursiyya na gaishe ku. luv uhy ol
.
.
.
.
.


Yasmeen zaune take tana chat a facebook hankalin ta kwance ynz zargin da take ya lafa rudanin da ta shiga domin taji al ameen yace mata aiki ne yayi masa yawa shi yasa bai tada ita ba sabanin da da take zargin wani abu.




magana suke da wata frnd dinta da sukayi school tare wayarta ce ta tsaya cikk tayi lock amma taki ta dauke ta yi hold na switch amma ina wayan tayi wani huking taki ta matsa battery ta cire abun mamaki wayar na nan yadda take.





tsayawa tayi tana kallan wayar ga battery a hannunta amma kuma waya a kunne magana taji anayi hakan ya bata damar juyo wayar. wani kwarangwal ne skeleton ke mata magana.







Yasmeen idan kina san kanki da arziki ki rabu da miji na idan kuma ba haka ba zaki jawowa kanki bala'i da matsifa. Yasmeen ta dan tsorata hakan yasa ta saki wayar ta tashi ta ruga a guje dakin ta ta kulle dan kwarangwal din nan kuwa dariya ya kamayi kamar na dan jariri hahahahaha.






Yasmeen tana daki amma tana jin dariyar. lalai yanzu ta tabbata akwai aljanu a gidan nan kuma tabbas aljanar macece domin duk mafarkanta da kuma tsorata ta da ake bata ga namiji a ciki ba.





sai da taji an dakata da dariya tukun ta leko parllo taga wayar nan inda ta yadda ita amma ba komai wato ba a kunne take ba. bata dau wayar ba. dakin ta ta koma ta shiga bath room dan ta danyi wanka domin dare ya fara yi.






wanka take abunta shiru gidan ba motsin komai. ba'a jima ba ta fara jin kukan jariri. shiru tayi ta dan dakata da wankan ta saurara. tabbas kukan dan jaririne. to miye ruwana da shi inaga makwabta ne . ci gaba tayi da wanka abunta.



kukan ne ya kara yawa. taji kukan kamar a cikin dakin ta ne hkn yasa ta dakata da wanka a hankali tazo ta kama kofan ta bude. ihoo ta saki mai rikitarwa ta kulle kufan da sauri. wasu yan jarirai ne guda biyu a tsakiyan dakin daya ba kai kan nasa ta gani a hannun dayan yana gurgura da hakori shi kuma marar kan shike kukan.





ban daki ta koma ta kama karkarwa tsoro sai makyarkyata take tana waige waige a bathroom din. fachal fachal taji anayi a cikin bath. ita da bata bar komai a gun ba to miye hkn. a hankali ta nufi gun.


( sis nasmat tana cewa karki je tsoro nake ji amma ina bata ma kula da mu ba)




tana lekawa ta saki wani kara. ahhhhhhhhhhhhh" kawai sai gani mukayi ta zube a gun sumamiya ( ni da nasmat da muke rabe a guri daya mun kakame saboda tsoro an rasa wa zaije ya leko bahon wankan domin ko ni a firgice nake. )



ba wani abu bane bahon ne cike da jini sai wata yar tsohowa a ciki duk kayan cikinta su hanji su miye gasu nan a fili tsutsotsi ne keta yawo a cikin wani katan kaine gare ta hancin wawakeke shima duk tsotsa ce ke fita a ciki ba abunda ya tsorata ni sai da naga kunnuwanta kalan na shanu ne idanta kuma baki ne wul wul ba alamun fari a jiki da gudu nayo baya sis nasmat na tambaya miye nace jeki gani.




karan da tayi yasa su mai gadi da driver suka rugo da gudu cikin gidan bisa mamaki suka iske ta tana dadana waya. hajiya lafiya. me yafaru muka ji ihoon ku.





man lawal kawai ina cikin farin ciki ne shine yasa hakan ba wani abu ba kuje ba komai.






futa sukayi suna tsaki wannan yarinyar fitinana ce wllh kaji fa wannan ihon da tayi ko da rana ne ya balle yanzu takwas ta wuce. hmm kadai bari ai bakaji irin haushin da naji ba lokacin da take fadar wai farin ciki ne inji lawal.



Yasmeen ta mike tana wani shu'umar dariyar mugunta. zeesa tace au dama Yasmeen ta iya dariya ne hk. nace da alamu dai har yanzu zazabin da kike bai sauka ba domin bakya ganewa ita Yasmeen a bandaki muka barta ai)


daidai lokacin sukaji odan al amern da sauri lawal yaje ya bude mar ya shigo saida suka gaisa tukun ya nufi cikin gidan kursiyya kuwa wani dan juyu tayi kawai sai gani nayi kayan jikinta sun canxa sai uban kamshi yake tashi a jikinta.







zaune take kan armchair tana dadana waya sai gashi ya shigo tashi tayi cikin farin ciki ta tarye shi. wow sweetyna kinga yanda kikayi wani masifafan kyau kuwa. wannan kyan duk nawane.







ya fada yana rungume da ita. daka mai kai kawai tayi alamun eh. ajiye kayan dake hannunsa yayi. baisan lokacin da ya fara kissing dinta ba ta ko'ina domin kamshin jikinta da yayi matukar dauke mai hnkli ya kuma bashi sha'awa.







nan fa itqma kursiyya ta shiga mayar mai da martani kissing din juna kawai suke chamak ya dauke ta kamar yar baby yayi dakin Yasmeen da ita wanda har a lokacin bakin su a hade yake.


.
. yau kam kursiyya tasha kiss iya kiss domin da ace Yasmeen din gaskiya ne to da inaga sai lips din ta sun dan kunbura dan tsabar tsotsa.lolz






tashi yayi ya cire kayan jikinsa da niyar zai shiga ban daki yayi wanka. kursiyya kuwa rasa abunyi tayi domin Yasmeen na bathroom din kuma idan ya shiga tabbas sai ya ganta. ................................


good morning to oll my frnds wanda na sani da wanda ban sani ba have peaceful day


shiga nan kayi like din page din mu

https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarks






king boyn ku ne little of writer's


















πŸ™ŽπŸΏβ˜  MIJIN ALJANAH β˜ πŸ™ŽπŸΏ


page 27 - 28


|
|
na king boy isahπŸ‘‘
|
|
__________________________
🌟5STAR MAR 2017 🌟
|_________________________|




***** 5 star *****
🌟5⃣STAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION 🌟 Β©5SWA
***** 5 star *****









kursiyya tace
dr bari inje in hada maka ruwa kafin ka shigo. da sauri ta tashi ta shiga bandakin ta kullo har ynz yasmeen na yanda take a kwance sume.







kursiyya tazo daidai kanta ta tsuguna ta taba kayan jikin yasmeen nan take suka koma kalan na jikinta har kamshin sannan ta mike ta dan mike hannunta sai ga ruwa yana dakar fuskan yasmeen kuwa sai ta tashi.







kanta taji yayi wani nauyi ya fara ciwo. nan fa ta tuno abunda ya faru da gudu ta fito a ban dakin a dakin ta iske al ameen.







yasmeen lafiya kuwa zaki wani rugo da gudu haka haba ai sai ji ciwo pls ki daina kinji. kin hada ruwan.






ba amsar da ta bashi ba kenan domin a firgice take dr wllh akwai aljanu a gidan nan wllh tun jiya ake firgitani. murmushi yayi yace hmm mata! mata iyayen tsoro to kiji in gaya miki gidan nan ba wani aljani kawai tsoran ki ne.





tafiya yayi zai shiga ban dakin da sauri ta ruko hannunsa pls dr muyi wankan tare domin ni kam tsoran zama ni kadai nake. murmushi yayi tukun a zuciyarsa yace af! to ai ni abunda nake nema kenan. yi sauri ki iske ni a bayin . hk ya shiga ba ko addu'a shiga bandaki



yasmeen ta fara kokarin cire kaya ta iske shi. abun mamaki ai ni ba wannan kayan bane a jikina inji yasmeen to ni wannan kayan ai bani da ko shegen su. to tayayi ma suka kasance a jikina bayan ko wanka banba balle in chanxa kaya. wai me ke faruwa a gidan nan ne bari mu fito in tambaya dr kayan nan. lokacin da ta ajiye su a kan gadan ta daura towel ta bi bayansa.





kursiyya tana ganin Yasmeen ta fita a ban dakin nan ta hada ruwa mai dumi kayan kamshi tasa a ciki da turaren wanka ita a nufinta tunda Yasmeen na waje to ita sai tazo a matsayin ta suyi wanka tare da al ameen din. abun haushi tare taga sun shigo abinda ya kona mata rai kenan ta ciji yatsa ta bacr bat domin bazata iya tsayawa kallan al ameen na wanka da Yasmeen ba dan idan ta tsaya tabbas mumunan abu zai faru domin har ynz bata da niyar cutar yasmeen tsoratatan da takeyi ma duk zafin kishine.







a can kasar bagadad kukar bulokia kuka ce mai dumbun tarihi garin aljanune. wasu bakaken aljanu ne a kanta munanai ko wane da kalar sufar sa wani dogo mai kaho daya a goshi a cikinsu nagani ya murtuke fuska ba alamun fara'a a fuskansa.







haba durmus miye na damuwa karka bamu kunya mana ka zama namiji dan ka rasa kursiyya zaka iya samun wata ai wacce ta fita.




wata irin tsaw ya daka mai mai kama da saukar aradu kaaaaaai! dakata bazan taba samun kwanciyar hankali da natsuwa ba in ban dauki mataki a kan wannan taka dirin dan adam din ba da ya raba ni da kursiyya.



aljanin na 1. wanda ya fara mganar yace to tayaya bayan kasan kursiyya ta riga ta zama mai bodygurd kuma fa kasan cewa a cikin mu ba wanda ya isa ya jada kursiyya ko ba dan karfi da allah ya bata ba kasan cewa sarki bazai barka ba in dai har ka cutar da yarsa.






dursum yace haka ne amma kasani cewa zanci gaba da bibiyar sawun su duk inda suke ina wajen kuma dole sai an sama kuskure wani lokacin kaga sannan ne zan aika ta mai duk abunda naso. kuma ina tabbatar ma ya jama kansa kai bama shi kadai ba gabaki daya yajawa yan adam din baki daya maza da mata.



ya juya ya kalle su ya mika wani talbeben hanunsa mai kamada jani talau. lolz yace duk wanda yake goyan bayana kuma ya yarda zai bani hadin kai wajen rama abunda akayi min ga yan adam to ya doro hanunsa nan. nan fa ya dinga binsu da kallo da idanunsa masu kama dana damusa.





baki daya saida suka dora hannunsa yace yauwa naji dadin hk abokaina ynx ku tashi mu watsu gari duk wanda yama laifi kadan kai koma baima ba mace ko namiji ne indai yama kawai ka shiga jikinsa. gargadi but karku shiga jikin mai ruko da addini ko mace mai yawan barin tsiraicin ta a fili muje. dake sun kasance masu fukafukai nr ba bata lokaci sai gasu sun iso garin daura nan fa suka warwatsu ko'ina.





tare sukayi wankan cikin farin ciki yana cuda ta tana cudasa bayan sun gama suka dauro towel suka fito nan aka sake shiga wani saban salon kaunar domin kowa a cikinsu komai sai dai dan uwansa ya masa Yasmeen ita ta shafa mai mai ta feshe shi da turare mai kamshi hatta kaya ita ta saka mishi abun gwanin bansha'awa. ( su mu gwabraye anji haushi. lolz




bayan sun shirya ne tsaf tsaf ta kunna tsintsiyar kamshi mai dadi. nan dai take ta faman shirya dakin nata. kallan ta yakeyi yana lasar harshe yanda yake jin wani irin santa a can kasar zuciyarsa har yama matsu dare ya karasa yi domin ya..... . ba abunda ke kara burge sa a jikin yasmeen kamar kirjinta dake ciki full da na shanu. sai kuma hipa dinta da suke kamar wacce tayi ciko. kai masha'allah domin duk abunda yake bukata ga diya mace Yasmeen tana da shi hakan yasa shi yi mata alkawarin cewa bazai taba kara mata aure ba domin shi kam ba wata diya mace da ta fi mai Yasmeen shi kam ko yaga wata ma mai kyau din idan ya tuno tashi matar sai yayi hamdala. ( nasmat tace ai da wannan karin naka dama mata uku ka karo mata yafi da ace ka karo mata kursiyya.)





bayan ta kamala gyaran dakin ko'ina tsaf tsaf ta gyara sai kamshi yake tashi a dakin . zuwa tayi ta zauna kan cinyarsa ta dan kwantar da kanta a kirjinsa dr wllh na gaji bazan sama damar girki ba ynz. su kam gabaki daya bama ta yin sallah ba suke tukun dan kwananan ba sallah ba salati sukr bare ma kuma addu'a



kallanta yayi ya dago kanta da hannu yace my to ynz zabi na gare ki in tashi in girka miki ne ko mu tafi hotel ne.




cikin sasanyar murya tace aa dr muje hotel din dama na dadw ban fita ba duk gidan ya isheni ga tsoro da ake ta bani kai kuma sam kaki yarda.




hmm kinga tashi mu tafi ko in dauke ki ne kafin tayi magana camak yayi sama da ita. kirjinta ya hadu da nashi. wani laushi da dadi yake jikin nata baiki yayi tafiya daga nan zuwa kano ba yana dauke da ita.lolz...........................



sis nasmat naga ta ruga da gudu kafin su fita ta fita. tambayarta nayi inazuwa.ta juyo tace kursiyya zan kirawo ince gashi nan za'a tafi aci da hakinta tazo ta dau mataki. lolx........ good night to all my frnds


shiga nan kayi like din page din mu domin karanta sauran labarin

https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarks


naku har kullum kingboy little of writer's









πŸ™ŽπŸΏβ˜  MIJIN ALJANAH β˜ πŸ™ŽπŸΏ


page 29 - 30


|
|
na king boy isahπŸ‘‘
|
|
__________________________
🌟5STAR MAR 2017 🌟
|_________________________|




***** 5 star *****
🌟5⃣STAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION 🌟 Β©5SWA
***** 5 star *****






*uhm naga yan nan gidan yau ko cigiyar kursiyya bakuyi ba balle ni kundai ganni yau sai ynz to kuyi hkr wani al amari ne yashigo min ina rokon asakani addu'a oll my friends*





dauke yake da ita har saida suka zo farfajiyar tsakar

Please Login or Register in order to submit comment