Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kara cewa ci gaba da dariyarka mana. wato bazaka barni da abunda ke damuna bama sai kazo ka kuma dasa min wani bakin ciki? mai makwan ka min jaje ka kuma Rarashe ni ka tayani daukar Fansa sai dai kazo ka cika ni da surutai ka kuma kara tunzura Zuciyata shin haka Salon son naka yake? Idan kayi wasa a yanzu zan batar da kai daga fadin duniyar nan".



Dursum kam idanunsa sunyi jajur har baya iya magana domin sarkar ta shake shi Sosai. tari ya Fara kamar Wanda zai mutu marsiyya na ganin haka ta fara rokon aunty nata ta Sake shi Zai mutu fa in bata Sake shi ba. sakinsa tayi ya fada ruwa Tunjum! Ya lume Zuwa can naga ya fito a suffar wani dodo mai ban Tsoro gashi kato Jikinsa Duk Sulbi ne Idanunsa hancinsa baki da kunne Wasu kwaruka ne ke fita yan kananu bakake. magana ya fara wacce muryar in mutun yaji kamar Dodon kunnansa zai fashe. " Kursiyya ni kikawa haka? Ni kike nema ki kashe domin kawai na fada miki gaskiya. Lalai yau badan ina Sanki ba kuma inq jin kunyar babanki Da sai na koya miki hankali na nuna miki banbancin Mace da Namiji. Kinci Darajar Mahaifinku da kuma San da nake miki. kuma sako yaje wa mahaifinki daga wajena Dan haka yace yana nemanku Daga ke har kanwarku Maza-Maza kuje gida.



"Tabbas zan koma Gida amma sai na dauki Fansa ta tukun nan" cewar kursiyya


"Allah ya bada Sa'a amma ina baku shawara kuyi gagawar dawowa gida Domin Fushin mai Martaba ba kyau ina jiye muku Tsoran afkawa cikin Fushinsa"


Batt dursumm ya bace. Su Kursiyya kuwa suka dawo gidan Al ameen. yau kam su al ameen sun shakata haka suka wuni suna kai kawo tsakanin daki da parllo da kuma kitchen suna wassanni suna farantawa juna Rai. Yasmeen tana daki tana jinsu amma taki Budewa wai ita tayi fushi. duk yau bata ci wani abu ba Sai lacasera dake cikin dan fridge dinta da kuma cincin su kadai take ci in ta ji yunwa ta matsa mata.


Gaba dayan gidan suka ji yana girgiza duhu ya mamaye ko'ina Al ameen da Zainab ma da suka Rike wa juna hannu basa ganin junansa. Yasmeen na daki a tsorace ta mike ta nufi kofa da lalubr ta bude ko far ta fito a guje tana ihoo tana kiran sunan Al ameen karo taci da kujera hakan ya tabbatar mata data iso Parllon. Su Al ameen kuwa kara makalkale junansu Sukayi Zainab kuwa ta fara jawo Suratul Baqara.


Dariya suka ji anayi Ta ko wane bangare na gidan suka jin dariyar na fitowq. gidan kuma yaci gaba da girgiza kamar da. Haka itama Zainab a tsorace take karatun da karfi.


"Ke!! kimin shiru ki tsaya da karatun nan bada ke nake yi ba idan kuwa kina so abun yq shafe ki ne to bismillah ci gaba". Kursiyya ce ke maganar Cikin wata irin murya wacce ita kanta ta isa ta tsorata dan adam uku-uku take fitowa. jikin Zainab Ya hau bari Ta fara karkarwa Amma taki daina karatun Sai dai ta Rage ba kamar dazu ba da take yi da karfi.



kursiyya ce ta bayyana A jikin bango da wata irin hallita mai Firgitarwa wacce idan ka ganta ko kai waye sai ka firgita
"Keeeeeeeee!! kina cika min kunne fa da karatun nan naki ki dakata ko kici na jaki yanzun nan." Shiru Zainab tayi domin ta kadu bata taba ganin wata hallitaba irin wannan. sulalewa tayi daga jikin al ameen ta fadi a kasa sumama. yasmeen tana ganin halittar itama ta kwada kara ta rufe idanunta da karfi. Al ameen Rudewa yayi gaba daya ya fita hayyacinsa yama Rasa dame Zaiji................................................................

Duhun yayi yawa gashi da rana ne hakan yasa na fito a guje fada da Aljani ba dadi fa. ba dan hk ba da na shigar musu ๐Ÿ˜…๐Ÿ˜ฐ๐Ÿ˜ฐ๐Ÿ˜ฐ๐Ÿ˜ฐ๐Ÿ˜‚ .lolz


Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks





โœ๐ŸผAutan marubuta โœ๐Ÿผ



๐Ÿ‘‘King boy๐Ÿ‘‘















๐Ÿ™Ž๐Ÿฟโ˜  MIJIN ALJANAH โ˜ ๐Ÿ™Ž๐Ÿฟ


page 136 - 137


|
|
na king boy isah๐Ÿ‘‘
|
|
__________________________
๐ŸŒŸZAMANI APR 2017 ๐ŸŒŸ
|_________________________|




***** zamani *****
๐ŸŒŸZAMANI WRITER'S ASSOCIATION ๐ŸŒŸ ยฉZ.W.A
***** zamani *****








. _*DEDICATED TO UR|โ€ž> AUNTY NA FATIMA USMAN (MMN ALI)*_ ๐Ÿ‘๐Ÿฝ *Na gaida ki kyauta na gode da kulawar da kike bani hakika kece lamba daya a fagen kaunar wannan littafin.๐Ÿ‘๐Ÿฝ๐Ÿ˜‰

๐Ÿค” BAN MANTA DAKU BA๐Ÿ˜˜

๐ŸŒนUSAINI 80K๐ŸŒน

๐ŸŒนUMAR D UMAR๐ŸŒน

๐ŸŒนAbdul King Article๐ŸŒน

๐ŸŒนMUFEEDAT๐ŸŒน

๐ŸŒนSAJEEDA BATULA๐ŸŒน


๐ŸŒน Mmn islam๐ŸŒน

๐Ÿ‘๐Ÿฝ๐Ÿ˜€ I love u oll my friends ๐Ÿ˜ ONE LOVE






"Keeeeeeeee!! kina cika min kunne fa da karatun nan naki ki dakata ko kici na jaki yanzun nan." Shiru Zainab tayi domin ta kadu bata taba ganin wata hallitaba irin wannan. sulalewa tayi daga jikin al ameen ta fadi a kasa sumama. yasmeen tana ganin halittar itama ta kwada kara ta rufe idanunta da karfi. Al ameen Rudewa yayi gaba daya ya fita hayyacinsa yama Rasa dame Zaiji.


Ana cikin haka sai kawai al qmeen yaji an shaki wuyansa ta baya an daga shi sama. kan iska. kokarin kwacewa ya hau yi nan ya fahimci da sarka ce aka dauro wuyan nashi. Dariya aka ci gaba dayi hahahahaha ๐Ÿคฃ kamar bangwayen dakin zasu tsage dan karar dariyar. abunda ya kara dugunzuma hankalin Al ameen kenan Tsoro ya sake mamaye shi ga dakin har yanzu masifar duhu,



Kursiyya ce ta bayyana tana dariya ta cikin wani haske ita kadai ake gani a duk dakin sai kuma al ameen dake makale a sama wanda lunfashin sa har ya fara daukewa dalilin daurin da aka mishi sai wuntsile-wuntsile yake da kafafu.

wata Rudadar murya Kursiyya ke magana da ita " hahaha Al ameen ka tafka babban kuskure na yaudarana da kayi. ka saba yaudara a net ka yaudari mata da yawa naga wannan a bincike na da niyi wasu sun tsani maza ta dalilinka sau da yawa wanda basu taba soyayya kake yaudara. wannan yake karya musu zuciys suji sun tsani soyayya bama ta net ba har ta face to face.


Garin kwashe-kwashrn ka kuma ka debo ruwan dafa kanka ks ballo mayunwaciyar Zakanya kuma dole ta cinye ka. hahahaha Al ameen wato yanzu da mutun ce kawa abun da kamin shikenan kaci bullus ko. to wannan ba mutum bace kursiyya kenan yar gata gurin sarkin aljanu. daga kaina baza ka sake Yaudarar wata mace ba mutun ko Aljan domin yanzu zan kashe ka na batar dakai haka kuma suma wannan matan naks bazan barsu ba bayan na kashe ka suma kashe su zanyi ka sani yanzu ba ko birbishin Sanka a cikin zuciyata.




Yasmeen najin anyi batun kashe su Tayi Zumbur ta mike ta nufi dakinta da gudu da niyar tserewa. kafin ta kai kofa. Yasmeen ta aiko mata da wata Sarka ta nanade ta tajata Sama itama tana lilo sai iho take kwadawa.



Al ameen yana ganin haka Ya kara Rudewa cikin karfin hali yace.' "Naji na kuma amince ki kashe ni ni nayi miki laifi na cancanci hakam amma ina hadaki da allanki ki bar matan domin kuwa Su basuyi miki komai ba."


"Al ameen ka kyale ta marar mutunci ta kashe mu din ai itama Allah bazai kyale taba banza kawai Shedaniya macuciya kawai. in ba dan Zalinci da Fin karfi ba kije ki nema jinsinki kuyi Aure mn mu me Ruwan mu dake."


Maganar yasmeen tayi masifar batawa Marsiyya Rai har itama kursiyyar. Kursiyya ta kara matse matse mata ciki da Sarkar. Wani uban ihuuu! yasmeen tayi wanda bata yi kalansa ko a baya ba. Tace "Yah Al ameen ka taimake ni Ta matse min ciki kuma ina Dauke da juna biyu." A takure ta Fadi maganar tana kara


Al ameen kara Rikicewa yayi ya fara kokarin kubcewa daga shake war da sarkar tayi mishi. amma ina Sarkar ko dan motsi batayi. da ya kalli yasmeen yaga halin da take ciki hawaye ke Zuba a idanunsa Ya fara Rokon Kursiyya yana mata magiya a kan ta sakar mishi matarshi kuma karta kashe mishi da'.



Kursiyya wata mahaukaciyar dariya ta sake yi wacce ko ina na dakin yake amsawa. Ohh! Al ameen me da ashe kasan ciwan da' to bari kaga. jikin bango ta gwara Yasmeen kanta ya bugu ta Fado kasa sumama.


Wani ihuu! na takaici Al ameen yayi Tukun ya fara fadi mata bakaken magan ganu wanda yasa taji mugun haushi wata muguwar wukace ta bayana a hannun kursiyya wacce takobi ce takai tsawan mutun kallo daya zaka mata kasan duk inda aka bugata a jikin mutun sai ta wuce wato Zata Raba mutum biyu ba tare da ta tsaya wani gargada ba. Kursiyya a fusace ta daga takobin da niyar ta Raba Al ameen gida biyu.



Wani mahaukacin kara su kursiyya sukayi Inda lokaci daya naga komai ya Canza Al ameen ya fado kasa tum! duhun Dake cikin dakin ya washe Sama da kasa na nemi Su marsiyya na Rasa. Gefe na juya Ashe Zainab ce ta farfado ta tuno da Ayatul Qursiyyu Ta fara Karantowa shi yasa suka Gudu.



Dakatawa tayi da karatun da Gudu ta tashi ta nufi Yasmeen da ta hanga can gefe kanta Jini na Zuba. Al amern Kuwa wani Masifafan ciwon kai ne ya zo mishi a lokacin A wahale ya tashi kanshi a dafe jiri na debansa ya tashi ya nufi Gurin su Yasmeen din. Da sauri Zainab ta cire Dan kwalinta ta daurewa Yasmeen kanta. A haka al ameen ya kama Ma Zee Suka taho da ita waje. Da sauri su idiris driver suka taso suka taimaka da bude motar aka saka Yasmeen suma suka shiga driver yaja mota Sai G . N . H . hospital.



Nan suka bar M. lawal a gurin Yana tunanin me ya faru a gidan domin shi kanshi Ya daure yasan dai idan fadan kishi ne akayi To Zainab bazata taimaka a fito Da yasmeen din ba.

( Ni kuwa nace. wannan Fadan na kishi ne amma fa da Aljana. lolz)


Su husaini ne suka karbi Yasmeen da Sauri aka nufi Emergency da ita. Dake ba bangaran shi bane ya fito ya bar Sauran likitocin a ciki domin huruminsu ne. Wajen su zee ya dawo a rikice yana tambaya me ya faru domin Shima abun ya Daure mishi kai. Zee tace yah yanzu dai a kirawo iyayen ta ya kamata a sheda musu halin da yarsu ke ciki shi yafi mahimmanci.


Husaini ya juya ga Al ameen wanda tunda aka zo ya sama waje ya zauna kanshi rike sai Zufa yake. Domin kanshi yake ji kamar Zai tsage. Husaini yace. "kai lafiya kuwa kazo ka sama waje ka zauna Kira wo iyayen Yasmeen mana a sheda musu."

"wllh kaina ne ke masifar ciwo kamar Zai tsage nake ji. ga wayar kira su". ya mikawa Usaini wayar. Husaini ya lalubo number Hajara ya sheda mata halin da Yasmeen din ciki. A Rude itama ta nufi gurin umma ta gaya mata.



Lokaci Daya naga idanun Al ameen sun wani canza kala Tsaye ya mike yake magana irin ta mata. Al ameen bazan taba Rabuwa da kai ba tunda na samu nasarar Shiga jikinka duk rintsi Duk wuyi bazan fita ba sai na dandana maka azaba.........................................................


๐Ÿ™†๐Ÿป๐Ÿ™†๐ŸปAL AMEEN YA SHIGA UKU ASHE TANA JIKINSA๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™‚๐Ÿ™†๐Ÿปโ€โ™‚๐Ÿ˜ฐ



Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks





โœ๐ŸผAutan marubuta โœ๐Ÿผ



๐Ÿ‘‘King boy๐Ÿ‘‘









๐Ÿ™Ž๐Ÿฟโ˜  MIJIN ALJANAH โ˜ ๐Ÿ™Ž๐Ÿฟ


page 138 - 139


|
|
na king boy isah๐Ÿ‘‘
|
|
__________________________
๐ŸŒŸZAMANI APR 2017 ๐ŸŒŸ
|_________________________|




***** zamani *****
๐ŸŒŸZAMANI WRITER'S ASSOCIATION ๐ŸŒŸ ยฉZ.W.A
***** zamani *****








. _*DEDICATED TO UR|โ€ž> AUNTY NA FATIMA USMAN (MMN ALI)*_ ๐Ÿ‘๐Ÿฝ *Na gaida ki kyauta na gode da kulawar da kike bani hakika kece lamba daya a fagen kaunar wannan littafin*.๐Ÿ‘๐Ÿฝ๐Ÿ˜‰





๐Ÿ˜ณ Husaini da zee hada ido sukayi a tare domin sunji al ameen na magana saidai basu ji ko me yake cewa ba hakan yasa husaini yace,
"me kaki cewa wai?" cikin 1 second tuni kursiyya ta bar jikinsa Al ameen yaji tambayar tazo mishi wani banbarakwai. " Yace ni me kuwa nace nace nayi kawai kaina ke ciwo."



A lokacin ne hajara da su mmn yasmeen har dady suka karaso duk a Rikice suke cikin tashin hankali suka fara Tambayar Al ameen me ya faru da yar su.



Al ameen in'ina ya kamayi Domin ya rasa ma abunda Zai gaya musu Shin wace amsa ma Zai basu yace Aljana ta Raunata ta kenan?. kai gaskiya bazan fada ba mmn yasmeen ta rikice sai tambaya take ina Yasmeen lokacin wani doctor ya fito da Sauri su husaini suka tarye shi suna Tambayar ya jikin nata.



yace Jikin nata alhmdulilah da sauki tama dan Sama barci ne nan da Rabin awa zata iya farkawa in yaso lokacin Dazu iya shiga ku ganta. Su al ameen suka ce Alhamdulilah" gaba daya. Al ameen ya biyo doctor yana Tambayarsa ko sun duba cikin da ke jikinta bai samu matsala ba. Doctor yace, "Eh gaskiya ba wani matsala a ta nan bangaran ma. godiya Al ameen yawa allah ya koma gurin su abba wanda duk sun Sama waje sun zauna umma da hajara har yanzu hankalin su bai kwanta ba sun matsu suji me ya sama yasmeen.
Bayan al ameen ya isa gurin ne Dady yace, "Al ameen gaya mana me ke faruwa ne i hope dai ba fada bane Tsakaninta da amaryarka Domin naji an ce min kayi aure.


Al ameen yace. "Aa dady ba tsakanin su ba domin ga Amaryar nan ma tare muke da ita kuma badan itaba da tuni Aljanar Ta kashe mu gaba daya. daga ni har yasmeen din. da sauri Zainab tayi magana. " Wannan bayi na bane yin Allah ne shine ya cece mu daga gare ta kuma ni a tunanina Sakacin da kuke da addu'a ne ya jawo haka domin na lura daga kai har Yasmeen din ba mai ilimin Addini."



dady ne ya dakatar da wannan shafin domin yaji Zainab ta dago shafin Laifinsu
"Al ameen aljana fa kace to miye hadin ka da Al jana ni fa banma wani karasa Yarda da wannan aljanun da ake fada ba. kawai daga mutun ya kamu da Zazabi mai Zafi ya fara surutai sai ace wai aljanune to kuma koma al janine ai bazai taba ya' ta ba ko shi waye dan uban sa aljanin banza.
zee tace dady kayi hakuri amma ai dole mu yarda aljanu domin ga ayoyi nan da dama cikin Al qura'ani mai girma wanda suka bayyana mana ceww tabbas akwai aljanu kuma suma suna Rayuwa ne a doran kasa kamar yanda muke yi. suma cikin su akwai Musulmi akwai kafurai akwai mugu akwai kuma wanda ba mugun ba...."
Maganar wata nurse ce ta dakatar da zee. tace zaku iya shigowa kuganta. Da sauri su umma suka shiga gurin.
"



Yasmeen ji tayi kawai kanta nayi mata wani masifar zafi lalubawa tayi taji Alamun bande ji a gun kokarin tuna abunda ya faru da ita ta fara yi. ai kuwa ta tuno duk abunda ya faru. momy ce ta karaso gun tana mata sannu. ita kuna kofa take kallo cikin masu shigowa ko zataga Al ameen dinta shiru bata Gansa ba.


Tambaya ta farayi ina Al ameen zee tace yana waje Tare muke da shi. wata kallar harara yasmeen ta aikawa da zee.
( wato kishin ne har yanzu) Zee kuwa ko a kanta domin tasan halinsu su mata game da kishi. Cikin kuka Yasmeen din take magana. "momy ina Al ameen ku gaya min mana yana ina Allah yasa dai bata kashe min shi ba."

mum ta dafata. "Yasmeen lafiyanki kuwa wacece zata kashe shi kuma, to al ameen lafiyansa lau kanshi ne ke ciwo shine ya tafi karban magana but yanzu Zai dawo ki kwantar da hankalinki kinji." Gyada kai yasmeen tayi amma har yanzu zuciyarta bata gamsu ba tunaninta Al ameen ya mutu ne shine ake boye mata domin taga kowa a gurin amma babu shi. Sauran mutanan gurin ne suka fara mata sannu ya jiki tana Amsawa amma da zee tace ya jiki banza tayi da ita ko kallanta bataiyi ba. kowa yayi tunanin wani abu a gurin amma ba wanda ya nuna.



'Ana faman dubiya ita kuwa nuratu kokarin hawa kan gadan da Yasmeen take takeyi da gyar ta samu ta hau. ta kalli yasmeen. " aunty nazo ki karasa min Labarin ALJANAR FATIMA domin kullum sai nayi mafarkin fatima da yar babynta shi yasa nake so inji yabayin. yasmeen tace. " To naji zan karasa miki amma ba yanzu ba tukun sai ranar da kika zo gidana Zan miki labarin har karshe amma kinga nan asbiti ne kuma bani da Lafiya... (keeeeeeyy!) karan bude kofa. kofar take kallo ganin waye zai shigo. wani mugun kara Yasmeen din ta saki hade da makalkale umma sosai tana fadin ku boye ni gata nan zata kashe ni momy wallh kashe ni zatayi bana so in mutu yanzu ku boye ni. kowa ya tsorata sosai a gun tambayarta aka shiga yi "wacece wacece" domin su basu ga kowa ya shigo ba bayan Al ameen. juyawa tayi da hannunta take nuna saitin al ameen din tana cewa "gatan nan mum karku bari ta karaso kashe ni zatayi ku ceceni.



lokacin Al ameen ya karasa gurin yana cewa "yasmeen lafiya kuwa me ya same ki ya jikin naki" a yayin da ita kuma kursiyya take gani a maimakon shi din ji tayi tana cewa "Yasmeen kin tsalake Rijiya da bayq da kika samu kika tsira da rayuwarki dazun amma yanzu bazan barki a raye ba yar yasmeme kina tunanin wai zan barki ne hahahaha to ki chanza tunani" hannu al ameen ya mika zai taba fuskar Yasmeen din yayin da ita kuma take ganin kursiyya ta miko hunnan wani ihuuu tayi hade da tsillo daga kan gadon Sauran kadan ta fado badan su hajara sun Riketa ba. da sauri su Zee suka kira doctor Allurar barci aka yi mata sannan ta sulale ta kama barci.



har Magariba ta gabato suna asbitin ganin dare ya farayi abba yace to mu tafiya zamuyi ya kalli su al ameen yace suma su tafi gida in yaso sai a bar hajara a nan ta kwana. haka kuwa akayi gaba daya suka tafi sai hajara sai yasmeen dake barci aka bari. karfe 8 su al ameen suka dawo asbitin suka kawo abinci amma har lokacin Yasmeen bata farka ba. sun dade a asbitin sai wajen karfe 11 suka koma gidan da zasu tafi zee ta tofawa Yasmeen addu'a. yau kam ko zee din ta kasa gane wa Al ameen domin gaba daya ya chanza shiru shiru yake kuma bai fiye shiga mutane ba.



ayatul qursiyya ta fara karantawa tana tofawa a dakin kamar yanda ta saba yi ko a gida. Tsawa ya daka mata yace ta daina baya so tace ai addu'a ce domin kariya. karayi tayi ta tofa Ai kuwa da gudu kamar wqnda aka kora ya fito ya bar dakin. abun ya daure mata kai daga baya kuma sai tayi tunanin ko barkwanci ne irin nasa da ya saba yi.



A gidan su Yasmeen jarfe 12:30


Dady ne zaune a parllo duk daren nan amma shi fim yake kallo hannunsa rike da Jarida kuma yana karantawa. umma kam tuni taje ta kwanta. yana zaune ya fara jin kuka a tsakar gidan " kuwwwwwwwwww,wooooooo" haka yata jin kukan na karuwa kuma yana kara kusanto dakin. ta ji yayi gen ya mutu dakin yayi duhu rudum ya lalubo wayarsa ya danna switch ba charji. abun ya bashi mamaki domin a full take. daga waje kasa yaji ana tada gen. bayan kuma yasan ba wanda ya bari a maimakon mai gadin su da yayi tafiya. karan tada gen. yake ji can kuma sai yaji surutu yan-. yan. haya- haya. sai hayaniya ake surutun ba na mutun daya ba bana biyu ba. a hankali ya nufi saitin window da yake dan ganin haske ta wajensa domin duhu yayi yawa kuma gashi yana upstairs a Tsorace yake tafiya cikin sando domin hayaniyar ta yawaita. karasawq yayi ya leka. don Tsoro ji yayi kamar zai fada kasa daga kan benan wasu halitu ne wanda bai taba ganin kalarsu ba sai hidima suke a tsakar gidan kamar dai gidan biki. halittun da yawansu basu karasa girman mutum ba, suna da bindi dogo ko wanne yana da zallakeken hakori a gaba dogo wanda ya fito daga cikin dogon bakin fatar jikinsu dark Green ce mai walkiya. can ya hangi wata Tsohuwa tsohuwa a cikin su tana bugon mai tada generator di tana cewa. "kai kumudu baka jin magana yanzu gashi ka kashe mana inji ga mai gidan baya nan balle ya zo ya tada mana So kake muyi party a cikin duhu ko?." kumudu ne ya dago kai da jajayen idanunsa suka hada ido biyu da abba sai da fitsari ya kusan fitowa abba a wando dan tsorata da yayi na ganin mumunar fuskar aljanin nan. da sauri kumudu yace " lah ga mai gidan can saman shigifa" da wata irin murya marar dadi. gaba daya Aljanun naga sun daga kai suna kallon abb.......................... . ..............................

Lalai abba zaisan akwai aljanu ashe daga today.lolz


Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks





โœ๐ŸผAutan marubuta โœ๐Ÿผ



๐Ÿ‘‘King boy๐Ÿ‘‘





๐Ÿ™Ž๐Ÿฟโ˜  MIJIN ALJANAH โ˜ ๐Ÿ™Ž๐Ÿฟ


page 140 - 141


|
|
na king boy isah๐Ÿ‘‘
|
|
__________________________
๐ŸŒŸZAMANI APR 2017 ๐ŸŒŸ
|_________________________|




***** zamani *****
๐ŸŒŸZAMANI WRITER'S ASSOCIATION ๐ŸŒŸ ยฉZ.W.A
***** zamani *****






๐Ÿ˜Kuyi hakuri fa na fiki matsuwa da inga na kamala book dinan amma ayuka ne sunyi over ynz ma bikin abokina ake mune angona ๐Ÿ˜Ž dan haka in kunji shiru kuyi uziri kawai. king na san duk mai sanshi ๐Ÿ˜˜ love u all ma๐Ÿ˜








dady jin an ambaci haka a Rude yayo baya domin ya gudu. juyawarsa keda wuya yayi karo da kalar aljanun nan guda biyu kafin yayi wani yunkur'i suka sunkuce shi sukayi sama da shi yana ihuu! yana wuntsile-wuntsile suka bace da shi basu bullo ko'ina ba sai gurin gen. tsakar gida kenan tsakiyar aljanun abba suma ne kawai baiba dan Tsoro. haka suka ce
ya tayar musu da gen. a tsorace hannun na karkarwa ya fara jan gen. din ja biyu yayi gen. din ya tashi gaba dayan gun ya dau wani kara da shewa na ajlanu sai jin dadi suke suna tafawa. abba kam sai karkarwa yake suma ne kawai baiyi ba. ganin hankalinsu yayi wani gun a hankali ya zame jikinsa ya tsere daki. yana shiga parloon wata dariya yaji anayi dariyar mace. daga jikin bango wata aljana mununa ta bayyana tana yin dariya. tace ba kai ne mai zagin mu ba kana cewa ba aljanu to yanzu ka gane akwai mu ko. mu ba bugo ba zagi kawai shagalin biki ne zamuyi na wata biyu kullum cikin dare kaima dole ka dinga fitowa walima kajj ko?.

ciki kaduwa ya gir-giza kai alamun eh zai yi Dariya ta karayi hahahahaha maza ka wuce. da gudu ya tashi har yana tun-tube ya shiga dakin da gudu kamar an koro shi. can ya fada kan umma baima lua da ita ba shi wajen buya kawai yake nema.
Farkawa tayi tana murje-murje Alhji lafiya kuwa?. cikin Rada yake ce mata "kiyi shiru, kiyi shiru kar suji mu"
"suwa" ta fada da dan karfi, da sauri yasa hannunsa ya toshe mata baki. shiru sai da aka dan dade tukun ya sake ta. shiru yayi cikin blanket ko motsin kirki baya yi. har safe.

tun da sasafe abba ya Rikice wai aje a nemo mishi malamai suzo suyi karatu Aljanu sun cika mishi gida
abun dariyama yabawa umma tace alhj inace kaine kace ba aljani ma jiya. " pls yi shiru karsu ji mu nasan suna nan kasa suna bidirinsu bari ma in leka inga".
a hankali yake tafiyar har ya karasa wajen window ya leka wayam ba komai a gurin kamar ma sam wasu halittu basuyi shagali a gun ba. lokacin itama umma tazo ta leko bata ga komai ba tace. " wai ni alhj me ke faruwa ne ina ce kace ba wani aljani a duniya duk karya ce to ka kwantar da

Please Login or Register in order to submit comment