Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna zaune a kan wani katuwar bishiya marsiyya tace "wallahi aunty ni gabana ma faduwa yake tsoro nake Al ameen ya nufi gidan su yasmeen biko', "habawa ai nasan halinsa akwai zuciya da girman kai a tare da shi. dan haka bazai je wani biko ba kuma na gaya miki. akwai wani terget da nake yi a kansa na domin kuwa bazan taba bari ya auri Zainab ba sanin kankii ne idan ta shigo gidan to karyar mu ta kare dan haka dole a wargaza auren. yanzu abunda nake so dake shine anjima zaki canza suffarki zuwa Zainab ni kuma zan koma wani saurayin daban a yau zamu wargaza komai. marsiyya tayi dariya irin tasu ta mugayen aljanu hahahahaha. gaskiya aunty na kin hadu kinga kuwa sai mu wargaza komai a cikin tsari... Dan haka yanzu ma kawo kunnanki kiji marsiyya ta mika kunne ta fada mata wani abu can sai naga sun kyalkyale da dariya

Al ameen bayan sun gagaisa da duk yan gidan yasmeen ce kadai bai gani ba. bayan an kawo mishi kayan makulashe da lemo aka ce ya dakata ayi wa dady magana. yace to umma ta shiga ta gayawa dadyn cikin farin ciki ya ce gashi nan zuwa. Nuratu ce ta fito a daki ta nufo gurin al ameen. kallanta kawai yake bai mata magana ba har saida tazo gabansa tukun tayi tsaye ta wani murtuke.



Wani irin kalan uku biyar bakwai goma ta dinga yi mishi hakan yasa yace. " Nuratu lafiya ki kuwa Zo mu gaisa mana kin wani tsaya kina kallona."
kai! ina wasa da kai ko ni sa'arka ce da zaka ce inzo mu gaisa. cikin tsiwa da masifa take fadar haka gashi wata iriyar katuwar murya ce ta mace kuma ke maganar. wato kai har ka isa ka saki aunty na ko yanzu kazo da niyar ka maida ta ne kenan ko me? to bazata taba komawa ba dan haka ka tashi ka tafi abunka tun kafin abba ya fito dan in ya iske ka anan to ka shiga uku sai ka gwamma ci da baka zo bama.



Al ameen duk tsoro ya kama shi domin lokaci daya yaga nuratu ta canza kama duk wani bakin gashi ya rufe fuskanta. cikin tsiwa da masifa tace '"ka tashi ka fita daga gidan nan nace. da karfi ta fada kuma maganar na fitowa biyu-biyu Al ameen jikinsa yaji ya kama bari ga wani mugun tsoro daya ziyarce shi lokaci guda. tashi yayi ya nufi kofar fita a guje. ya kama kofa kenan zai bude maganar abba tasa ya dakata.



cikin karfin hali ya juyo. mamaki ne ya kamashi domin can ya hangi Nuratu a kan sofa tana wasa abunta. ta juyo tace yaya Al ameen tafiyq zakayi?. Murmushi yayi yace a'a tym din har zufa ta keto mushi. abba yace "bismillah mana zauna kayi hakuri fa na bata maka lokaci." al ameen ya zube kan kapet '"ba komai ai abba ina wuni. ( suka gaisa)



Al ameen cike da kunya yace to dama abba.. dama.. dama...abba da yaji in"inar taki karewa yace kaga ba sai kayi min bayani ba domin kuwa ta fada min komai kuma ita nabawa Rashin gaskiya kuma nayi mata fada naja mata kunne. sannan kuma yanxu kai ya kamata da mu baka hakuri.



Dan murmushi al ameen yayi yace aa abba ai ba komai nine ya kamata in bada hakuri sannan kuma ina so mu koma gida na maida ta dakinta tunda bata gama i'ddah ba. "To alhmdulilah naji dadin wannan abu bari a kirawo ta waya ya dauka ya kira hajiya kuma yace suzo tare da yasmeen din.


bayan sunzo sun zauna yasmeen itama a kan karpet ta zauna. abba ya gaya musu abunda yq kawo Al ameen kuma yace Yasmeen ta bashi hakuri sannan taje ta shirya su koma gida. ba gardamq yasmeen ta juya tabawa Al ameen hakuri hade da cewq hakan bazai kuma faruwq ba. Al ameen yayi mamaki matuka da Yasmeen tayi laushi har haka duka kwanantq daya fa a gidan amma da alamu tq gaji da gidan yace a zuciyarsa da nasan haka ne ai dana bartq tayi sati muga watakil ta kara hankali. nqn dai yace "ba komai komqi ya wuce. yasmeen ta tashi ta shiga ciki domin ta shirya ba'q dade ba ta fito suka kama hanya suka taho su umma har kofa suka rako su. umma tace wa abba " ah alhaji kagafa diyan zamani wai da kansa yazo biko. alhj yace ai ya birge ni ba gashi ba salin ali ya dauki matarsa yq mayar ba tare da wani yaji ba. ai da duk mutane zasu gane da duk sun watsar da al adunan na kakanni yanzu ai an waye. umma tace " uhm allah dai ya kyauta.




Kursiyya da marsiyya na gani a saman iska suna bin bayan motar su Al ameen Ran kursiyya duk ya baci ta canza fuska. Marsiyya tace kiyi hakuri aunty ban zata alhj zai fito da wuri bane shi yasa na jinkirta. "Ni rufe min baki mai zaki gayq min bayan kinsan ga ysnda muka tsara abu. yanzu a lokacin da ace kin fito a matsayin abba kinyi mishi Rashin mutunci da ba shikenan ba. auren ya mukenan amma gashi kinyi mana asara wannan tsinannar shikenan ta dawo. Marsiyya tace haba ai dan ta wannan mai sauki ne. ana babbakar giwa wqke jin kaurin bera. kursiyya tace ban gane ba. "Auntu ta Zainab zamuyi ba wannan ba. dole mu hana zainab shigowa gidan nan. kursiyya tace " kuma fa haka ne domin ita wannan sai yanda mukayi da ita.




Su al ameen tunda Aka taho ba wanda yayi wa wani magana a tsakaninsu har aka zo gida. Sai bayan sun zauna a Parllo ne. ya tashi yaji ya kwantq a jikinta yake cewq "haba Yasmeen miye abun daga hankali wai dan nace zan kara aure nake ga ai karin aure ba haram bane tunda an hallatq mana yin hakan kumq Zainqb yarinya ce mai hankali bazatq taba yin wani abu wanda ba haka ba. nasan dai ku mata duk abunda kuka fi tsoro shine aje wajen boka da malam a kwace muku miji ko. to ita zainab ba haka take ba yarinya ce mai kirki da kuma sanin ya kamata.




Yasmeen kanta Taji yana juyawa jiri ya fara dibanta dakyar ta samu ta iya control din kanta. tasa yatsa a kunne ta goge wai ta kara saurarawa dakyau taji wai da gaske ne abunda kunnanta ke jiye mata ko kuwa. in kuwa da gaskr ne hakane to me Al ameen yake nufi kenan cin mutunci ne wato abun ka dawo dani yau kuma ka dinga min zancen karin aure chabb zakuwq ayita.......................................................
ni kuwq nace bari in wullar da kayan rubutun in gudu kar a hada dani.lolz





Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks





โœ๐ŸผAutan marubuta โœ๐Ÿผ



๐Ÿ‘‘King boy๐Ÿ‘‘



Bigboy ISAH FANS
๐Ÿ™Ž๐Ÿฟโ˜  MIJIN ALJANAH โ˜ ๐Ÿ™Ž๐Ÿฟ
page 130 - 131
|
|
na king boy isah๐Ÿ‘‘
|
|
__________________________
๐ŸŒŸZAMANI APR 2017 ๐ŸŒŸ
|_________________________|
***** zamani *****
๐ŸŒŸZAMANI WRITER'S ASSOCIATION ๐ŸŒŸ ยฉZ.W.A
***** zamani *****
. _*DEDICATED TO UR|โ€ž> AUNTY NA FATIMA USMAN (MMN ALI)*_ ๐Ÿ‘๐Ÿฝ THANKS d like and support me. allah yayi albarka
Yasmeen ta kalle shi tace Dr. me kake fada? "Abundai da kikaji din tabbas haka yake kuma tunda dai su abba suka bani hadin kai to ba wani mahaluki da ya isa ya hanani kara auren nan. zata yi magana ya tari lumfashinta da cewa.
" Idan fa kika takura to abunda ya faru a baya shine zai kara faruwa."
ba yanda ta iya dole taja bakinta tayi shiru amma tsabar tunane-tunane harma kanta ya fara mata ciwo.
acikin satin nan manyan Al ameen suka je gidan su zainab aka tsaida magana ba'a saka auren a lokaci mai tsayi ba kawai asabar mai zuwa. kuma yau laraba. .
su zainab kam ansha murna. Basmah ce babbar kawarta komai tare suke a shirye-shiryen auren nan.
Yasmeen har yanzu bata tabbatar da Al ameen da gaske yake ba sai Yau da ya kawo mata kayan fada da kishi ๐Ÿ™Š
( karfa kuji nace kayan fada da kishiya ku zata ko su wuka ๐Ÿ”ช katako tabarya Guduma ๐Ÿ”จ da bindiga๐Ÿ”ซ Da dai sauran kayan Shekewa ๐Ÿ˜…๐Ÿ˜‚ a'a ina nufin sababin zannuwa wasu daga cikin kayan daki da dai sauran tarkace)
sannan ya hada mata da dubu dari idan wani abu baiyi mata ba ta canza cike da mamaki Yasmeen ta karba. tana san yi mishi wata tsiwa sai dai kuma tana tsoran abunda zai faru domin tasan idan ya fada sai ya aikata.
*To alhmdulilah* Ansha shagali taro yayi taro kuma y watse an kawo amarya Zainab a dakin Umma aka sakata dakin yasha kayan gadan ma chanxa shi akayi. bayan duk yan biki sun watse daga tsakar gida daga ni sai nasmat da mukaga haka nace ke zo mu shiga ciki muga me ke faruwa ne? da sauri ta biyo ni.
Yasmeen ce zaune a kan armchair tayi tagumi sai wani hararen daki umma take nama rasa me take harara agun ashe tsabar kishi ne. gefe daya na parllon kuma dana juya Marsiyya da Kursiyya na gani a kan kujera sofa suma sunyi zuru-zuru ko wacce zai a bace.
Marsiyya tace lalai gaskiyarki aunty munyi babban kuskure na barin Zainab ta shigo gidan nan. kina ji fa shigowarta ma sai da tayi addu'a a kofa. Kursiyya tace "um ke dai bari ni yanzu bamma san ya zanyi ba wato a nufin ta dai ta kwace min daki ko?. amma Ba komai Itama Zamuyi maganinta. yanzu duko min wayata in hau online inga ko yana on. inyi mishi magana ko naji dan sauki- sauki
" ya za'ayi ya hau on a daidai wannan lokacin ai nasan ko kiransa kikayi ba lalai ya dauka ba. yau fa daren amarcinsa.kuma kina dai kallo a gabanki ya shiga dakin da leda a hannu". a cewar marsiyya
kursiyya tace kinga ni dai dauko min ko kiransa ne nayi inji ko karya zaiyi min irin na da. marsiyya ta mika hannuta sama sai kawai ga wayar ta bayyana. kursiyya ta kar'ba ta kira but no answer har hajen sau 5 amma anki pick call nata. haushi ya karq dabaibaye ta.
Dakin amarya kuwa Zainab ce zaune a kan gadan fuskarta rufe da mayafi. Al ameen ya shigo "'Amarsu ta ango amarya bakya laifi, abunda ya shigo dashi kenan a matsayin sallama. sai faman wage baki yake.
bayan ya ajiye Ledodijn hannunsa nanma ya hau wata wakar. "ahyyee mamah. "ahyee mamah mamah yeehi yeeh ayee mamah labolabo mamah yeeh iyeeh"..
Zainab murmushi kawai tayi domin abun yq bata dariya. Al ameen yaje ya hau kan gadon suka yi gaba-da-gaba yace,
"to amarya bude min wannan Kyakyawar fuskar mana tunda yanzu na zama mamalakiyarta". ba gardqma kuwa ta bude fuskan.
"wow kinga yanda kika kara wani irin kyau gashi sai kyalli kike kuwa"
bata ce mishi komai ba kanta ma a kasa yake taki yarda su hada ido. Gashi sai faban zubq yake kamar Dan gidan Redio da akawa gorin magana Sai daga baya ya fahimci Duk surutun da yake ko kalma daya fa bata furta ba. hakan yasa yace, "Zainab ina ce Abokaina sun riga da sun saya baki ko kuma wani ake so in kara Saya yanzun?."
Kai ta girgiza mishi kuma sai ta hau dobe-dobe da alamun wani abu take nema. can naga ta lalibo wayarta ta rubuta kamar haka;
[Da Zaka shigo baka min Sallama ba dama waka ka shigo min. kuma A addinin mu duk wanda ya zo gurin ka baima sallama ba to Karka yi mishi magana Har sai ya koma da baya ya dawo yayi maka sallamar]
Tana gama rubutawa ta mika mishi ya karba ya karanta Yace au Na sha'afa ne Amaryata Da sauri ya tashi ya fita. Su kursiyya suna kallansa su yasmeen Domin har yanzu suna parllon sun sun sha ma fitowa yayi sai kuma Sukaga ya koma yayi Cikakkiyar sallama:
"ASSALAMU ALAIKI, WARAHMATULLAHI WABARKATU HU"..
Zainab Cikin Zazakar Muryarta ta amsa mishi:.
"AMEEM WA'ALAIKA SALLAM WARAHMATULLAHI WA BARKATU HU",
Al ameen yayi murmushi yace, "uhm da wannqn shine ya hana ayi min magana. tace " kwarai kuwa",
"To yanzu dai sakko muci abinci tukun mu kwanta ko?". Tace "aa ba haka za'ayi ba muci kaza dai Sannan muyi Sallah muyi addu'o'i na godewq allah daya Nuna mana wannan Rana". Al ameen a zuciya yace. "wai ni me yasa na cika kwafsawa ne Karfa yarinyar nan ta fahimci ban ma Damu da sallah ba. " oh ai manta wa nayi ne ban fada ba amma addu'ar ma tana Raina ai".
Zai ta sakko suka Zauna a kasa ya jawo ledojin gasasar kaza ce guda daya katuwa sai kuma madara da fruits A cikin dayar ledar. Banyan sun ci abincin Suka Tashi suka Shiga bathroom Suka yo Alwala a gun alwalar sa ma Zainab tayi mishi gyara Sosai ta kuma kara nuna mishi yanda akr yi.
Gaba ya shiga Ya jata Sallah bai iya ko fatiha Ba domin guri uku tana cin sa gyara haka dai akayi aka gama Sallahr ma Raka'a uku yayi shida zaiyi biyu yayi sallahma amma sai yayi uku kuma yayi sallamah. Zee kam har dariya ta kamata amma sai kuma ta matse dariyar Domin tasan Rashin Ilimi babbar matsala ne.
Tahi tayi Ta sake wata Sallah inda tace ya lura da yanda Zatayi har karatun. ba gardama Kuwa ya zubq mata na mujiya. Shima kansa yaga gyararaki sosai a cikin Sallarh sa dayaga tata.
Bayan ta Gama sukayi Addu'a na godewa Allah tukun zee ta cire dan kwali ta miko mishi kai yayi mata addu'a zuru yayi Yana kallanta can taji shiru ta dago tace lafiya. "Yace a gaskiya ni ban wani iya duk wannan ba. ko auren Yasmeen ma muna gama nafila ko addu'a bamuyi ba muka fara wasa da juna." zee tace. "Subhanallah to kaga rike gashin kaina duk abunda nace kaima ka dinga fada." ba gardama ya rike. ta fara Kamar hakka, ''Baarakallahu laka, wa baaraka alaika wa jama'a
bainakumaa fi khairan'' haka ya fada dai-dai ta kuma cewa kace,
"Allahuma inni as aluka min khairu haa"
"Allahuma inni as aluka min khairu haa"
"Wa'auzubika min sharriha"
"Wa'auzubika min sharriha"
Tace "To alhmadulilah wannan sune masu mahimmanci ga mai sabon aure sauran kuma zaka iya rokon allah ko da da hausa ne. kallan Al ameen din tayi taga tuni yama fara fita hayyacinsa domin sai bin jikinta yake da kallo. bazato ba tsammani sai ji tayi ya hade bakinsa da nata ya fara tsotsa. ba yanda ta iya dole itama ta fara mayar masa da Martani domin itama ta dade tana jiran wannan rana kuma tasa guruka da yawa na farantawa angonta Rai a wannan daren. Abun naga Yafi karfina Nayo waje ina dariya Domin Al ameen naga ya fara kokari cire mata Riga.............................................................
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
โœ๐ŸผAutan marubuta โœ๐Ÿผ
๐Ÿ‘‘King boy๐Ÿ‘‘






๐Ÿ™Ž๐Ÿฟโ˜  MIJIN ALJANAH โ˜ ๐Ÿ™Ž๐Ÿฟ


page 134 - 135


|
|
na king boy isah๐Ÿ‘‘
|
|
__________________________
๐ŸŒŸZAMANI APR 2017 ๐ŸŒŸ
|_________________________|




***** zamani *****
๐ŸŒŸZAMANI WRITER'S ASSOCIATION ๐ŸŒŸ ยฉZ.W.A
***** zamani *****







. _*DEDICATED TO UR|โ€ž> AUNTY NA FATIMA USMAN (MMN ALI)*_ ๐Ÿ‘๐Ÿฝ *Na gaida ki kyauta na gode da kulawar da kike bani hakika kece lamba daya a fagen kaunar wannan littafin. Mmn hisham bazan manta dake ba.*๐Ÿ‘๐Ÿฝ๐Ÿ˜‰







washe gari da safe:
Zainab tare suka shiga ban daki da al ameen wankan janaba din ma bai iya ba duk sai da gyagyara misha ta kuma kara koya mishi karatun. Zainab tayi wanka ta saka kaya ta feshe duk jikinta da turare tukun ta fito ta nufi kitchen a parllo ta iske yasmeen a kan sofa a nan ta kwana. bata tayar da itaba kitchen din ta wuce ta hada musu kayan breakfast ta kawo ta jera a kan dineeetabal.


Wajen yasmeen ta koma ta tada ta a hankali bayan yasmeen ta tashi tace "ke malam a name mutun na barcinsa zaki tashe shi."
Zee tace. "aunty ki tashi kin kusan makara fa yanzu har karfe 7 ta kusa naga bakiyi sallah ba shi yasa na tashe ki"
"Yasmeen tace to naji na kuma gode amma daga yanzu karki sake cemin aunty Dallah dube ki to anan me al ameen ya gani ma da har ya auro ki in ba dan jarabarsu irib ta maza ba"
"Haba aunty me yayi zafi haka Ni a tunani na ai duk wacce ka iske a gida dole ka kirata aunty kuma kishi ba abunyi bane domin kishiya yar uwa ce. kuma bazan daina ce miki aunty ba tunda ke na iske a cikin gidan nan."
yar dariya Yasmeen tayi tukun tawa zee kallan sama da kasa. "Wato ke a tunaninki har kin sama wajen zama ne a gidan nan da har kike tunanin kishi nake dake. Ai ni banga abunda Zanwa kishi a nan ba. Domin idan naga dama a yau-yau zaki bar gidan nan. marar aikin yi kawai mtsewwwo taja wani dogon Tsaki hade da mikewa ta nufi hanyar dakinta. Maganar da Zee take ne yasa ta dan rage Sauri domin jin me take Fada.
"Ba Damuwa aunty ni bazan daina yi miki biyaya ba domin ko zaman aure bai hadamu ba ni ina girmama na gaba dani kuma karki Raina mutum koda yaya yake domin ta iya yuyuwa yafi ki a gurin Allah. Kuma Da kike maganar Fitar dani daga gida wannan bazai dameni ba domin ni na yarda da Allah kuma komai na Rayuwar mu a rubucr yake duk abunda zai faru dani nasan can dama haka Allah ya tsara." Yasmeen najin haka ta sake yin wani tsakin da niyar ta wuce cikin dakin. "Aunty kiy sauri ki fito ga Breakfast nan na shirya mn ke muke jira".


Tafi Sukaji Raf! Raf! Raf! Al ameen ne ashe yana jin duk Abunda ke Faruwa Tsakaninsu. "Yasmeen dawo ki Zauna zamuyi magana." Al ameen ya fada ko juyowa batayi ba ta shige dakinta. Al ameen yazo ya zauna kusa da Zee ya juya yana kallanta yana murmushi ya dan Shafa gefan kumatunta yace. "A Ina kara godewa allah daya bani ke a matsayin mata. gaki da Tarbiya hakuri da juriya ga natsuwa" Kiss ya manna mata A goshi tukun yace Ina sanki zeena. "Love u too" kawai ta fada cike da kunya ta Rufe idonta Domin tuno abunda Ya faru jiya a tsakaninsu duk sai taji kunya ta Rufe ta. hannuwanta ya kama ya bude idon yace. " Amarya kenan to miye na kunya bayan kuma na... Duka ta kai mishi da sauri ya goce ya tashi yana Tsokalarta suna zagaya Parllon cike da nishadi.

Yasmeen tana jinsu Bakin ciki ne da Kishi ya kara kule ta. Kan gado take A zaune tama Rasa me keyi mata dadi ko wankan ma ta kasa shiga.

Su Al ameen sun dan dade A parllon hat kusan 7:30 amma Yasmeen bata fito ba. hakan yasa yaje ya tura dakin yaji a rufe ya kwankwasa tana jinsa amma tayi Shiru ta kyale sa. har ya gaji ya koma yace wa Zainab.
"Amarya muje mu karya wannan bata da niyar fitowa kuma kinga gun Aiki Zan tafi. Ba gardama zee ta tashi suka nufi dinner din domin karyawa. Shayi mai kauri sai indomie da taji kayan hadi gefe Daya ga soyayen dankali da doya da kwai. ga kuma wainar kwai a gefe. Al ameen tun kafin a zoba mishi kanshi ya isheshi ya fara zumudi. ciyar da juna suka dinga yi Abunda ya kara bawa Kursiyya haushi kenan Batt suka bace suka bayyana a wata katuwar kuka wacce take a tsakiyar wani kogi.

'Al ameen sai zuba uban santi yake Tambaya yake Shin wai wama ya nuna mata kitchen kuma ita da take amarya ai bai kamata ta fara Girki tun yau ba. Zainab murmushi tayi tace angona kaidai ci abinci karfa ince Santi kake.

"To in nayi santin ma ai ba laifi bane. nifa gaskiya nama fasa futa ba inda zanje"

"Ah to nima dan kar inyi maka katsalandan ne angona amma da tun dazu zance maka ka fasa Zuwa gurin aikin nan mu tsaya mu..." kuma sai ta kasa karasa maganar.

Al ameen yace kunya ko. uhm idan "kunya tayi yawa fa tana hana a kyautatawa miji yanda ya kamata kinsan hakan ba"

"Yes na sani kuma zan kiyaye my oga. amma fa kar amarcin mu yasa muci haram ya kamata dai ka sanar da shugaban Hospital din"

"Ai baya da matsala zan sanar da shi kuma zan gayawa brox ya duba patients dina."


*Su kursiyya ne zaune kan kuka duk Sun koma wata irin hallita mai suffa abun Tsoro jikinsu irin na mutun kai na jaki Ga kuma wani wagegen baki da Jini ke kwaranya daga Ciki Wayarta Ta jawo ta kira Al ameen bugo Daya ya dauka domin yarinyar ta fara bashi haushi gwara yayi mata baro-baro ko ta rabu dashi haka yace a zuciyarsa.

ko sallama batayi ba ta fara magana.

"Haba mijina al ameen dina ya zaka min haka kwana biyu baka kirana kama Daina daukan kirana dama haka auren yake?".

Dariyace ta kubce wa Al ameen domin har saida ya rike baki.
"Ke tsaya wai ke wace irin jahila dakikya ce me kike ma kursiyya ko kur.... me ma to wallah bari kiji in gaya miki..................... ......................................
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks





โœ๐ŸผAutan marubuta โœ๐Ÿผ



๐Ÿ‘‘King boy๐Ÿ‘‘







๐Ÿ™Ž๐Ÿฟโ˜  MIJIN ALJANAH โ˜ ๐Ÿ™Ž๐Ÿฟ


page 134 - 135


|
|
na king boy isah๐Ÿ‘‘
|
|
__________________________
๐ŸŒŸZAMANI APR 2017 ๐ŸŒŸ
|_________________________|




***** zamani *****
๐ŸŒŸZAMANI WRITER'S ASSOCIATION ๐ŸŒŸ ยฉZ.W.A
***** zamani *****







. _*DEDICATED TO UR|โ€ž> AUNTY NA FATIMA USMAN (MMN ALI)*_ ๐Ÿ‘๐Ÿฝ *Na gaida ki kyauta na gode da kulawar da kike bani hakika kece lamba daya a fagen kaunar wannan littafin. Mmn hisham bazan manta dake ba.*๐Ÿ‘๐Ÿฝ๐Ÿ˜‰










Dariyace ta kubce wa Al ameen domin har saida ya rike baki.
"Ke tsaya wai ke wace irin jahila dakikya ce me kike ma kursiyya ko kur.... me ma to wallah bari kiji in gaya miki Ba sanki nake ba kuma bazan taba Sanki ba. Wama yasanki da har zaki dinga kiran mutum da mijinki auu! wai dan anyi auren wasan nan a grp to bari in gaya miki gaskiya wannan ma Ni a Matsayin nishadi na dauke shi ba komai ba. kuma Ina so in gaya miki Ki Rabu dani dan allah domin ni magidan ci ne Mata na biyu a halin yanzu.


Cikin kuka Kursiyya tace Ni zakawa haka Al ameen Dama kai mayaudari ne ashe Ban sani ba. Shin kasan ko ni wacece kuwa. Saboda kai na Rabuda ahalina na rabu da Masoyina wanda Zan aura dan uwana. Ba ina fadi maka haka bane domin ka so ni Aa ina fada ne kawai domin takaicin da ke cikin Raina. Wato kai mayaudari ne ko To ka yaudari Wata wacce ita ba'a Yaudara Dan haka ka jira Daukar Fansa bazata zo maka da Kyau ba. Domin ni ba Mutun bace Ni Aljana ce.



"Banza mahaukaciya Da yawa na hadu da irinki masu cewa su aljanune kuma ba abunda ke faruwa daga Karshe dan haka wannan bazai Taba tsorata ni ba." Katse wayar yayi tukun yayi Tsaki yace Shirmamiya kawai. Block din number yayi.



Kursiyya Wulli taya da wayar cikin Ruwan dake kasan kukar Hawayen Jini ne suka fara kwaranya a kan bakaken idanunta masu ban Tsoro. Marsiyya kuwa ta shiga Rarashinta Taba bata Hakuri. Wasu irin Muryoyi na dinga ji Na dariya na tashi a gurin wanda su kansu su kursiyya saida suka Rude suka kama waige-waige Domin ganin mai Dariyar Sai can daga bisani wani dan-kareran Aljani ya bayyana yana Zagaya su Yana dariya Ba kowa bane face Dursum. "Kursiyya! Kursiyya! Cikin wata iriyar murya marar Dadin ji yake maganar.


"Na so Ki So mai tsanani na kula da ke na rike ki amana Amma kika guje ni ta Dalilinsa kuma kika hanani daukar Fansa a kansa To yanzu gashi ke da kanki naji kina maganar Daukar Fansa A kansa Saboda kawai ya iya kalaman soyayya kika guje ni a kansa Bakiyi tunanin komai ba kika Tare a gidansa kika guji iyayenki _hahahahahah_ ya karashe zancen da kwashewq da wata irin dariya.



Nuni tayi da hannuta bangaren sa kawai Sai ga wata irin bakar sarka ta fito daga hannunta da sauri ta nanado wuyan Dursum sama ta daga shi yana Reto " Yi dariyar ta

Please Login or Register in order to submit comment