Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake tambaya. Aunty hajara tace kasan niger? ya zaro ido yace niger kuma ba niger ba akace maka 9ja. yace nasan niger mn nama taba zuwa sau daya. Anty hajara tace to yau zakayi zuwa na biyu can zamu je.



Idi yace hajaya motar fa ba mai domin man ciki bazai isa ko kano ya kaimu ba. Yasmeen tace kaga baka da matsala muje a hanya masha man. Nan fa suka duru cikin motar. Suka dau hanya.



********-----**
Basmah Zaune take tayi zugun sai tunane-tunane takeyi. Abubuwa sunyi mata yawa ita dai gaskiya bata ga anfanin zuwa bordingscl ba ba abun da ya kara mata a rayuwa sai masifa da bala'i.




Sallamar dataji ne ya katseda a duniyar tunanin da ta afka. Da gudu naga ta tashi ta nufi kofa fuskarta cike da farin ciki.ganin mai sallamar. Taje ta rungume ta. Su zee manya ashe ana ma duniyar. Shine ko leko mu ba'ayi. ..




Zainab tayi murmushi tace a'a basmah ba haka bane kinsan fa mai harda. Dole sai ya maida hankali. Domin karatun al qur'ani baya haduwa da shiririta. Basmah tace gaskiya kam haka ne. Ta kama hannun zee tace muje ciki.



Dakin ta suka shiga suka zauna a kan dan tsoho gadon ta. Bayan sun gaisa zee take tambayar ina ummi. Basmah tace wllh ta danje anguwa ne bata dade da fita bama. Zee tace kawata kinga yanda kika rame kuwa kika wani kode wllh gaba daya kin canza daga basmah dinki ta asali. Basmah tace hmm kedai bari zee ai allah ma ne ya sawake.




Zainab tace naji lbrn duk abunda ya faru dake zee amma ke kuwa me ya kaiki aikata wannan danyan aiki bayan basmah tare mukayi karatu ajin mu daya kinsan fa illar aikata lesbian.
.

Hawaye ne suka gangaro daga fuskan basmah tace zee nima ba a san raina na aikata ba sharrin shaidan ne da kuma hadin bakin wata macuciyar malamar mu. Sanin kanki ne ummi bata da wani guri da ya wuce in kamala karatun boko. In sama aiki tukun inyi aure. Wai a ganinta a nan gida bana maida hankali shi yasa ta maidani boarding to kinga abunda ya jawo. Yanzu gashi. Ibrahim dinma ya janye yace ya fasa aure na domin lbr ya kai gare shi. Ta karashe zancen da fashewa da kuka.






Zainab ce ta fara lalashinta tana cewa." Kiyi hakuri kawata komai yayi farko ai zaiyi karshe kuma komai yayi zafi maganinsa allah. Mai hakuri yana tare da allah kuma kinsan cewa abunda hakuri yayi rashin hakuri bai isa yayi sa ba. To anma ni abun da yafi bani mamaki shine wai da akace aljanu sun shiga jikin ki shin ina duk addu'in da ake koya mana tare dake a makaranta.?




Da alamu dai watsar da su kikayi shi yasa har aljani ya kusance ki. To yanzu dai abunda nake so dake shine ki kula. Sosai ki dage da karanta suratul baqara. Ayatul qursiyya. Aminarrasullu. Domin malam ya gaya muna cewa wadanan suna karya aljani.




Basmah tace na gode kawata zan dinga kula sosai. Daidai lokacin ummi ta shigo da sallamah. Suka amsa. Saida ta nema guri ta zauna tana cewa a'ah manyan baki yau su zainab ne a gidan namu. Wato sai kawarki tana nan zaki zo gidan ko.?



Zainab cike da kunya. Domin ta dade bata zo gidan ba. Tace aa wllh ummi karatu ne kawai baya barin na in leko yanzu ma mun dan sama hutu ne ana bikin wani malami daga cikin malaman mu.




Ummi tace to allah ya kyauta. Ya maman naku. Lafiyar su lau wllh tana cewa ma in gaida ki da yake na gaya mata nan zanzo. Ummi tace to madallah ina amsawa.





Zee tace ummi ashe haka al'amarin ya kasance ga basmah. Ummi tace eh wllh kindai gani zainab. Haka allah yaso. Zainab tace amna aljanun sun fita ko ummi." Eh ashe ma aljana dayace kuma an fitar da ita. " to ummi dama akwai wasu shawarwari da malamin mu na islamiyya ya bamu game da irin wannan.

.



Yace ba'a barin mai aljani ya dinga kwana shi kadai a daki kuma ba'a barin sa ya ja ruwa ko yaje kusa da wuta domin aljanin zai iya hankadashi cikin rijiyar ko kuma ya toya shi in kusa da wuta ne. Kuma ba'a barin mai aljani a gida shi kadai domin aljanun zasu iya fitar dashi. Sau dayawa ana samun wannan akasin wani idan aljanun suka kadashi wani gurin shikenan. Baku bashi. Sannan malam yace ana so a dinga karantawa mai aljanu suratul baqara gabaki dayanta. Idan mutu bai iya ba kuma sai ya dinga karantawa mai aljanun ayatul qursiyyu da amunnarrasullu.......



Basmah tace ke miye haka an gaya miki an fidda aljanar kinzo sai zuba kike to waye mai aljanin? A nan. Ummi ta dankwashi kan basmah tace ja'ira lokacin da ake ririke ki za'a sakoki daki ai da a lokacin ne bazaki fadi haka ba ko. Zainab na gode kwarai da gaske kuma zanyi afmani da wannan shawarwarin naki.




Kuma basmah cikin satin nan zata koma islamiyya domin ni gabaki daya ma bokon ta fita a raina. Zainab tace a'a ummi ai bokon ba laifi bane indai zaka dinga kula karka watsar da addinin ka da addu'in da manzo ya koyar na neman tsari ka dinga yi.





****

Marsiyya da kursiyya gudu suke cikin iska a sararin samaniya suna dariya ta fitar hankali. Marsiyya ta dakata tace aunty amma naso ace kin koya musu hankali wllh wai waye ne ya shigo da karatun ne?.





Kursiyya tace nima ban sani ba.amma dana san ko waye ne da sak nayi maganinsa Shima. Domin ya wargaxa min damata.




Marsiyya tace nifa yau mugunta nake ji. Zuwa can kuma tace yauwa na tuno mu tafi gidan su basmah...................................................






_Muguwa ko me zakiyi a gidan su basmah kuma?_ maman hisham ce ta fada bani ba.lolz


Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks





โœ๐ŸผAutan marubuta โœ๐Ÿผ



๐Ÿ‘‘King boy๐Ÿ‘‘







๐Ÿ™Ž๐Ÿฟโ˜  MIJIN ALJANAH โ˜ ๐Ÿ™Ž๐Ÿฟ


page 97 - 98


|
|
na king boy isah๐Ÿ‘‘
|
|
__________________________
๐ŸŒŸ5STAR APR 2017 ๐ŸŒŸ
|_________________________|




***** 5 star *****
๐ŸŒŸ5โƒฃSTAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION ๐ŸŒŸ ยฉ5SWA
***** 5 star *****


๐Ÿค” BAZAN GAJIYA BA BAZAN KUMA DAINA MIKA GODIYATA A GARE KI BA๐Ÿ‘๐Ÿผ HAKIKA KE MASOYIYAR GASKIYA CE MAI SAN CI GABANA A RAYUWA. ONE LOVE ๐Ÿ˜˜
๐ŸŒนZAINAB YUSUF๐ŸŒน





Kursiyya tace muje daman ina so in ganta nima din. Tashi sukayi furrr!!! Da masifafan gudu irin nasu na aljany Suka nufo gidan su basmah.

Daidai lokacin kuwa su basmah sun fito kofar daki suna bankwana da zainab zata koma gida. Wani mugun iskan guguwa ne ya fara zagaye tsakar gidan.basmah ta wani makalkale zainab. Ita kuwa zainab ayyatul qursiyya da li'ilafi take ta faman yi tana tofawa a saitin gurin.


Ba'a jimaba naga kurar ta bace iskan ya daina. Zainab ta kalli basmah tace haba basmah kina ganin guguwa haka anma kin wani kudun dune kin shige jikina bayan kinsan addu'in da aka koyar damu na in guguwa ta taso.


Basmah tace sorry kawa na manta ne. Da sauri zainab ta rike baki. Kin manta me din? Addu'o'in mana. zainab tace tabb amma lalai yarinyar nan kin cika sakaci wllh. Sai na gayawa malam idan kika je ya zane ki tunda dai ance zaki koma.



Basmah dariya tayi tace kinga ni ba wani iskanci zaki tsaya yimin ba idan zaki tuna min ki tina min. Zainab tace to mamal nura yace duk lokacin da iska ya taso mai karfi ko guguwa mutun yace

) *ุงู„ู„ู‡ู… ุงู†ูŠ ุงุณุง ู„ูƒ ุฎูŠุฑ ู‡ุง.ูˆุงุนูˆ ุฐ ุจูƒ ู…ู† ุดุฑ ู‡ุช*(

Basmah tace au na tuna ma.

โ€œALLAAHUMMA. INNI. AS'ALUKA. KHAIRAHAA. WA A'UZU BIKA. MIN SHARRI SHARRIHAAโ€



Zainab tayi murmushi tace ni zan koma fa. Nan sukayi bankwana. Ta rako Zainab har kofa zainab na kara jadada mata ta ringa yawan karatun al Qur'an ta. Sukayi bankwana. Zee tafi gida.




Can na hangi su kursiyya a kan bishiyar wata tsamiya da alamu dai duk a jikice suke sunji jiki. Ashe wai sune suka je a ta ciki guguwa. Addu'ar zainab ce ta fatatake su suka bar wajen. A guje.




Marsiyya tace me yake faruwa haka ne.? Bayan nasan basmah ta riga ta watsar da karatun ta. Amma nayi matukar mamaki da tayi addu'ar nan ni banyi tunanib hk ba wllh.


Kursiyya ta wani bata rai hayaki na fita ta saman kanta. Fuskarta ta wani canxa kala.tace ba basmah bace. Wannan yar iskar yarinyar ce wacce suke chat da al'ameen. Wacce kikayi block dinta din nan.to ita ce tabbas na ganta da idona.





Marsiyya tace kam buhu... Dama itace ashe. Lalai wannan tana so tajawa kanta masifa da bala'i domin idan ta yarda ta fada tarkona. Hmm ko dan kyale ta in kyaro na yawo zabo na yawo to wataran za'a hade. Zan nuna mata ita ba komai bace. Nasan takamarta addu'a to wataran ai zata manta taki yi.




Kursiyya tace barta zata hadu damu. Ai fada da aljani ba dadi...




Karfe 3:00 na rana su yasmeen suka karasa kauyen ai kuwa a gajiye suka firfito sunsha tafiya. Ga motar su da ta basu matsala. Saida anty hajara ta biya gidaje masu muhimmanci suka dan gagaisa ta tambayi lbrn mijinta aka ce ai har ynz ba labari. Tukun suka wucd can fadar boka. Masha jini.




Boka yayi farin ciki sosai da ganin su. Anty hajara ta gabatar mishi da yasmeen sannan take gaya mishi matsalar data kawo su. Cewa aljanune suke takurawa yasmeen a gida. Shi yasa suka zo gurinsa domin yayi wani abu a kai.




Dariyarsa yayi irin wacce ya saba tukun yace yar baba ina layoyin dana baki ko baki yi aiki dasu bane da turarukan dana baki. Idan kika turara turaren nan aljani ko anguwar bai isa ya shigo ba balle gidan.




Anty hajara tace wannan aljanun gaskiya masu mugun taurin kai ne domin ba yanda banyi musu ba duk wani abu da ka koya min na jaraba a kansu amma abun yaci tura!!
.

Boka ya sake dariya yace. Yace to yanzu me kuke so ayi muku ne. Domin in na fahimci zancen ki to bakaken aljanu ne kuka hadu dasu. Amma idan kuna so sai in hadaku da kibru-da-kibsu suje su fatataki su su dawo.



Yasmeen tace aa kawo in san samu ne mudai muna bukatar mu tafi dakai.ina ganin hakan zai fi domin aljanun shakiyyai ne. *Hahahahaha.* boka yayi dariya da wata irin murya tukun yace hakika kinyi tunani yarinya. Domin kuwa. Zuwa dakai yafi sako. To yanzu abunda za'ayi ina so ku tashi ku tafi zaku iske ni a can. Yasmeen da antyhajara suka zaro ido. Zamu iske ka acan kuma kawu.





Yace af kuna kwokwanto ne.? Suka ce a"ah nan suka barshi.suka ce bari suje nan baya su dawo. Anan suka bar har idi driver. Bayan yan mintuna sai gasu sun dawo. Mota suka shiga a nan suka bar kawu kasumu ba ko alamun ya fara shirye shiryen tahowa. Su kuwa suka hayo hanya. Motar bata basu dadi ba domin saida ta basu matsala kusan sau biyar a hanya tana tsaida su..



: Karfe 7:21pm suka shigo garin daura. Bayan m. Lawal ya bude musu gate. Yake fada musu cewa sunyi bako tunda la'asar yaxo yana jiranki.


Yasmeen tace bako kuma ina yake. M. Lawal ya nuna mata saitin mutumin. Ba wani bane illah kawu kasumu boka. Zaune yake ya wani harde kafafu. Ya rufe. Ido a kan wani dan dakali. Dake kofaran falon.



Yasmeen da anty hajara rike baki sukayi cike da mamakin ganin kawu kasumu. Ashe da gaske yake gashi har yazo. Cikin zumudi. Hajara ta sauko ta nufi gurinsa. Yasmeen ma ta bita a baya. Kawu!, kawu! Hajara ke fadi. Ashe har kazo taso mu shiga ciki mana........................................................


(Na kalli aunty fatima nace wai wannan kawun kodai bokan gaskiya ne.? Tace gashi nan dai)


















๐Ÿ™Ž๐Ÿฟโ˜  MIJIN ALJANAH โ˜ ๐Ÿ™Ž๐Ÿฟ


page 99 - 100


|
|
na king boy isah๐Ÿ‘‘
|
|
__________________________
๐ŸŒŸ5STAR APR 2017 ๐ŸŒŸ
|_________________________|




***** 5 star *****
๐ŸŒŸ5โƒฃSTAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION ๐ŸŒŸ ยฉ5SWA
***** 5 star *****





Lokacin boka ya bude jajayen idanunsa. Yace sai yanxu kuka karaso ashe.ai ni na dade ina jiranku a nan gurin. Hajara tace eh mai gadi ya fada mana taso mu shiga ciki. Tashi yayi ya dauki yan komatsen shi. Na bokanci da wata jaka kmr ta wanzamai. Yabi bayansu.



Idi bayan yayi parking din mota ya fito ya nufi wajen M. Lawal yana dariya.



Yana karasawa yace M lawal wai ni kai nawa mutumin ya baka ne. Ka sheko wannan uwar karyar wace. Ba wanda zaiyi zatan karya ne.




M.Lawal yayi mutukar mamaki taya idi yasan karya yake yi. Ba da la'asar mutumin yazo ba.murmushi M.lawal yayi yace kai kuwa waya gaya maka karya nayi.



Idi yace kaga malam ai kafin a hadu da d'ah aka hadu da uba. M.lawal yace ban gane wannan karin maganar ba kana nufin kafin mu hadu dashi kun hadu kenan.๐Ÿ˜ณ






Idi yace kwarai kuwa ai ni tafiyar nan tayi min dadi ai 20k ba wasa ba. M. Lawal yace shine ya baka kudi har 20k to me kayi mishi. Idi yace ai ni babban aiki nayi mishi gwara kai karya ce yasa ka amma kai fa nawa ya baka?.




Nan fa M. Lawal ya fahimci cewa idiris fa yasan komai. Kalansa yayi ya kwashe da dariya yace shege kasn komai. Bani labari ya kukayi dashi.




Idi yayi Murmushi yace. Ai in gaya maka. Ban taba zatan karyar boka ta kai har haka ba sai yau.

Wai dan tsabar karya haka yace wa su hajiya wai suje zasu iske shi a gida wato nan. Suka ta mamaki Nima lokacin da ya fada nayi mamaki. Wai saida suka dan zagaya zasu je su gaida wata tsohuwa shine ya jani gefe. Ya ce yana neman in taimaka mishi
.



Na kalle shi nace taimako kuma wane iri?.




Nan yake gayamin wai karya yake yi. Bashi da tsafin da zai kawo shi nan kuma ma baisan address din ba kawai karya yayi motar haya zaihau shi yasa yake so wai in taimaka mishi ko nawa ne zai bane. Ni kuwa nace af! Dama ta samu. Nan nace ya bada 20kbaiyi gardama ba ya bani na bashi full address sannan muka tsara cewa xan dinga tsayawar karya a kan hanya saida nayi tsayaw biyar ina ce musu motar ce ta sama matsala. ๐Ÿ˜ƒ๐Ÿ˜‚






To kaji yanda akayi shi kuma sai yaje ya hau motar kudi mai gudu. Dariya M.lawal yayi sosai harda dafe ciki yace kai! Amma mutumin nan yakai dan iska kuma kasurgumin makaryaci. Nima nan da ya zo abun da ya nema kenan. Da yazo ya tambaya na tabbatar mishi da nane gidan sai yace yauwa to dan allah zai bani wani aiki na dubu biyar.




Nace wane aiki ne. Ba bata lokaci yace kawai in su Yasmeen sunzo ince tun dazu yazo ya ma gaji da zuwa. Nace dan wannan ai ba matsala bane. Nan take ya zaro 5k ya damka min kama ganta..


(Nan dai na barsu suna hira. nayi cikin gidan da gudu don kar a bani lbr)



Su anty hajara na shiga falo kawu kasumu ya fara daga kai sama yana kallan silin yana wani zazaro ido. Zuwa can kuma yace tabbas kunyi dabara da kuka ce inzo da kaina domin abun yafi karfin kibru-dA -kibsu. A dan tsorace Yasmeen ta kalle shi tace kawu me ke faruwa aljanu ne a gidan ko fatalwa?..




Ya wani murtuke fuska yana hararen wani bangare a falo. Yace kingan su can kinga irinsu can. Da sauri duk suka waiga amma basu ga komai ba wayam gurin. Boka yace ai dole a dinga tsorataki da yawa. Domin a gidan nan naki babu abunda babu.



A shigowata Na kirga fatalwa fiye da talatin. Aljannu kuma. Bansan iya adadin wanda muka ci karo dasu ba. Amma daga mun hada ido sai su tsere.
Yasmeen ta dafe kirji tace haba nifa ince wannan abun yayi yawa dama.nasan ba aljani daya ne bq ko biyu. To kawu yanzu ya za'ayi?.




Kuje ciki kawai ku bar min komai a hanuna. Kafin safe duk sai na kori aljanun gidan nan. Anty hajara tace yauwa kawo a nuna musu kwarewa da iya aikin bari muje mu hada abinci domin dare ya farayi.



Nan suka bar boka ya zauna a sofa ya rufe ido. Tunanin karyar yakin da ya zuga yake yi. Bayan kuwa baiga aljani ko daya ba. Kuma koma yaga aljani to ba yanda zaiyi da shi sai ta allah dai barawo hannun mata. Shi kudinsa ma yake tunanin ya za'ayi su fito. Domin kar suce aikin gida ne aki salamarsa bayan ya kashe kusan 30k. Ko ya zaiyi ya fito da kudinsa. Abunda yake tunani kenan. Zuwa can kuma sai yayi murmushin mugunta.





bai dade a gurin ba sai ga hajara ta fito da plat din abinci dake taliya ce har sun gama. nan ta kawo mishi ta ajiye mai a gabansa. boka ya dinga wani waige-waige inda ita kuma ta bishi da kallo tana tambayar lafiya?.





can sai taji yana magana shi kadai. eh eh angama to za'ayi hakan.karkuji komai. ba damuwa. dubu 40.to za'a sanar da ita. to na gode. tukun ya juyo ga hajara da ita tsoro nema ya fara kamata. yacr da ita kinji maganar da muke yi ne. kai ta girgiza tace aa. nadai ji taka maganar. yayi dariya hahahahahaha. hajara tun farko shi yasa naso in koya miki wannan abun amma fur! kika ki. yanzu kinga da kin koya da kinji maganar da muke yi ni da sarkin aljanu.





hajara ta dan ja da baya a tsorace kawu sarkin aljanu kuma. eh sarkin aljanu. abun da yaks gaya min shine. wai wannan gidan na aljanu ne can asalinsa ma shi yasa yanzu sukayi yawa. amma yace a bashi cin hancin ko na 40k ne shi kuma yasan yanda zaiyi da su ya kore su gaba daya......................................................................





wannan karyar da naji an zungura yasa na dakata a nan domin tafi karfin kwanyata.lolz

GOOD MORNING TO ALL MY FRIENDS

little of writers


king boy










๐Ÿ™Ž๐Ÿฟโ˜  MIJIN ALJANAH โ˜ ๐Ÿ™Ž๐Ÿฟ


page 101 - 102


|
|
na king boy isah๐Ÿ‘‘
|
|
__________________________
๐ŸŒŸ5STAR APR 2017 ๐ŸŒŸ
|_________________________|




***** 5 star *****
๐ŸŒŸ5โƒฃSTAR ONLINE WRITER'S ASSOCIATION ๐ŸŒŸ ยฉ5SWA
***** 5 star *****



๐ŸŒค๐ŸŒคAssalamu alaikum.Barkanku da safiya. Ina rokon Allah ya sada mu da alkhairin dake cikin wannan rana ya kuma tsare mu sharrin dake cikinta. Love u oll my friends๐Ÿ˜˜ godiya da fatan alkhairi.





Hajara tace dubu arba'in kadai kawu? Yace eh dubu 40 kuma nasan daga an bashi kudin nan shikenan matsalarku tazo karshe.

A daidai lokacin yasmeen ta fito daga daki. Nan ta same su.hajara tace yauwa sis karaso.bayan yasmeen ta sama waje ta zauna ne. Anty hajara take gaya mata yanda sukayi da boka.



Yasmeen tace ai dan wannan ba matsala bane yanxu ake san kudin ko sai anjima. Da sauri kawu yace aa zaifi dacewa a dauko yanzu. Duk da dai ya tafi amma sai in kai mishi yanzu. Yasmeen tace ti kawu bari in tashi in dauko maka ta mike ta nufi. Daki.



Ba'a dade ba sai gata ta dawo da kudi yan dubu-dubu mikaku a hannunta. Ta mikawa kawu tace gashi dubu hamsin ne a bashi ace ya rike sauran. Mudai dan allah ya taimaka yace su tashi msna daga gida. Pls kawu. Kawu ya amsa yana murmushi. Karkiji komai ai baya da wasa.




Nan da gobe nasan bazai bar aljani ko daya ba. A gidan nan. Yanzu bari in tashi in shiga daki sai in kirasa in bashi. Yace wanne daki aka tanada domin ni?. Yasmeen ta nuna mishi dakin umma tace ga dakin can kawu. Da sauri hajara tace. Aa can dakin fa yanada hadari sosai. Aljanun sunfi yawa a can.



Kawu yayi Murmushi yace karki damu ya' ta ko kin manta kawun naki ne. Ai ni aljani ba abunda ya isa yayi min aljannu tsoran mu suke yi ba mu ke tsoransu ba. Bari ma dai in fara aiki na. Zan samu kasko na wuta guda biyar? Yasmeen tace kawu bani da kasko har biyar biyu ne kadai dani.sai dai ko in murfin langa.




Yauwa to maza jeki dauko su yi sauri ki hado har murfin langar. Yasmeen ta tashi taje ta dauko mishi. Yace to abunda nake so yanzu kuma garwashi a ina za'a samu. Yasmeen tace ba matsala.bari in je makwabta baza'a rasa ba. Tashi tayi ta dauki gyalen ta ta nufi makwabta. Kafin ta dawo naga kawu ya bude jakarsa yana fiddo wasu. Garin magunguna a daure da tsumma.



Bata dade ba sai gashi ta dawo da rabshi da yawa. Ta kawo mishi. Zubawa yayi a ko wane kasko. Ya bada garin maganin. Ya basu yace ku kai ko wace kusurwa ta gidan nan. Ba gardama suka tashi. Kowa ta dau bibiyu suka raraba a square gidan. Bayan sun dawo yake ce musu to kunga wannan hayakin da nasa kuka kai ko amfaninsa shine nan da wata biyar ma aljani bai isa ya tako kafarsa cikin gidan nan ba.




Zan bar wannan shi kuma a nan fallo shima saboda tsaro. Kuje kuyi harkokin gaban ku kawai baku da matsala. Da Murmushi a fuskarsu suka tashi cike da farin ciki wai anyi maganin aljanu. Kawu ya shiga daki ya ajiye karikitan sa gefe guda. Tukun ya dawo ya kalli yamma yayi tafi! Raf! raf! Sai ga aljanun nan su biyu sun bayyana wato kibru-kibsu. Zubewa kasa yayi ya gaishe su tukun ya mika kokon bararsa a gunsu.wai a kan su taimake shi. A bisa karyar da ya tafka. Su kuwa suka ce sam bazasu sake taimakon sa ba tunda ya karya musu dokoki yake amfani da mata bayan kuma sun hanashi.




Hakuri ya shiga basu yace bazai karaba idan dai har suka taimake shi. Idan kuma ya kara to suyi mishi duk abunda suka ga dama. A haka suka yarda bayan da suka saka shi yayi musu sujada.

(Wa'iyazubillah! Allah yayi mana tsari da bokanci dama zuwa gurin bokan masu zuwa ma allah yasa su gane. Su kuma koyi hakuri da juriya. Domin rashin hakuri ne ke kai mutun ga zuwa wajen boka. Bayan shi boka bai isa yayi abunda allah bai nufa ba. Allah yasa mu dace. Ameen)



Nan ya tambaye su shin da gaske akwai aljanu a gidan nan ku kuwa dai tsoransu ne irin na mata. Aljanun suka ce tabbas akwai aljanu domin nan a dakinsu ma kake sai dai mu bamu san ko suwaye ba tukun sai sunzo. Kuma zamu baka tsaro da kariya kaida duk sauran yan gidan nan. Boka yayi godiya nan suka bace batt. Shi kuma ya tashi ya nufi falo yaci abinci tukun ya dawo dakin kursiyya a gadanta ya bingire sai barci.lolz




Su yasmeen yau an saki jiki sosai domin cqn na hange ta rike da waya sai suburbuda dariya take. Ba wani abu take wa dariya ba. Sai chat din da suke ita da kawayen ta. Haka itama aunty hajara. Sai faman chat ake cikin nishadi da walwala.


Karfe 11:00pm su kursiyya ne suka nufo gidan a kan iska sai dariya take mai karfi irin tasu ta aljanu. Ba wani abu take wa dariya ba. Illah muguntar da marsiyya tayi a yau. Domin yau ta karasa yarda yar uwar tata azzaluma ce. Dan sai suna tafiya. Taje ta tadewa wancan kafa. Tasawa wannan dutse a wanya yayi tuntube. Ta tsorata waccan.




Yau har akwai wanda ta jefa rijiya. Da kyar aka ceto rayuwarsa. Gidan suka nufo.marsiyya tace kai! Aunty a rage dariyar mana. Ke abu baya wucewa a wajenki?. Kursiyya tace kedai bari ai yau nasha dariya. Har na gaji. Daga nesa marsiyya ta hangi hayaki na tashi a gidan. Tace aunty ji wani hayaki. Dake tashi. Kursiyya tace yi sauri muje mu gani. Batt! Suka bace sai gasu sun bullo a cikin gidan. Marsiyya ta duka gaban kaskon tace aunty wannan ai turaren mayu ne. Kuma nasan dai saboda mu aka sashi.



Kursiyya ta kyalkyale da dariya kuma sai ta bata rai. Nan take naga wasu bakaken gashi dogaye na fitowa a jikinta bakinta ya wani koma dogo kamar na alade. Kanta kuwa haka ya koma rusheshe ba ko gashi daya a jiki. Marsiyya na ganin haka

Please Login or Register in order to submit comment