Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawo mn ziyara. Cikin murya irin ta mata yayi maganar.




Asiya sulalewa tayi a gurin sumamiya. Daga ganin hakq yasmeen ta taso tana dariya. Tace maganinki kenan. Ai gobe ma ki kawo mn ziyara. Asiya da ta tashi falkawa sai kawai ta tsinci kanta a kan gadan ta. Cikin dakinta. Abun ya daure mata kai...


***********

Yan kwanan nakin nan da al ameen yayi a S.A. duk ya rame ya wani lalace kallo daya zaka mishi ka gane hakan indai ka sanshi can dama. Ba wani abu bane yasa shi cikin wannan halin illa barazanar da dursum keta yi mishi da kuma kashedi ga yawan bashi tsoro da ake. Sai yaji shi duk ya tsani kasar ma ba abunda yake so illah ya sauka a gida Nigeria. Kamar kullum. Yauma yanq chat a imo sai yaga an kirashi video call. Da watq bakuwar number. Bayi wata-wata ba ya daga kira don ganin waye ke mgn. Gabansa ne yayi mumunan faduwa ...............................................




















๐Ÿ™Ž๐Ÿฟโ˜  MIJIN ALJANAH โ˜ ๐Ÿ™Ž๐Ÿฟ


page 112 - 113


|
|
na king boy isah๐Ÿ‘‘
|
|
__________________________
๐ŸŒŸZAMANI APR 2017 ๐ŸŒŸ
|_________________________|




***** zamani *****
๐ŸŒŸZAMANI WRITER'S ASSOCIATION ๐ŸŒŸ ยฉZ.W.A
***** zamani *****







Zainab tace yaya dama.. Dama me?. Fada inaji. Dama ba... Al ameen da yagano zainab bata so ta fadi maganar ne yace kaga malam kawar matata ce. Shi yasa na santa. Da sauri Zainab tace aa yaya al ameen. Gwara kawai mu fada mishi gaskiya domin ramin karya kasan kurare ne. Duk zurfin sa kuwa. Inji husaini. Zainab tace yaya hussaini kayi hakura. A chat muka hadu. What a chating ya fada zainab har saida ta zabura sakamakon mgnr da yayi a wani razane. Al ameen yace of course a whatsapp ma muka hadu. Amma karka yi mata mumunan zata domin a wani group na Whatsapp mai suna hayatul islam muka hadu. Nima garin biye biyen Link dina na shige sa a ciki na ganta kuma kasan dai halin mutumin naka da... Husaini a lokacin ya saki fuska yayi Murmushi idasa mana. Ka fara magana ka tsaya. Karasa mn kowa yaji. A daidai lokacin wayar husaini tayi kara yana duba screen din yaga mai call din sai ya tashi da sauri ya nufi dakinsa yana waya. Nan aka bar al ameen da Zainab a parllo. Hira suka hau yi suna dariya. Can al ameen yace wai ni kam laifin me nayi miki ne kikayi block dina. Ni sai kwanaki ma na lura da haka da na dauka ba kya hawane ashe blockdina kikayi.





Zainab tace kaine fa ka kirani kace gaskiya zaka fada min ba sona kake ba yaudarana zakayi miye-da-miye kace inyi block dinka da kanka kai ka fada min haka. Al ameen yayi shiru yana tunani. Shidai yasan bai taba aikata haka ba domin shi inma ya gaji dake saidai yayi block dinki badai yace kiyi nasa ba. Yace aa kin manta dai tuno dai wata kila wani ne zai gaya miki haka ke kuma sai ki saba layi kiyi block dina. Zainab har zata musa kuma sai ta tuno zuwan kursiyya. A zuciyarta tace tabbas wannan itace zatayi wannan aiki ba wani ba. Nan tayi yanda zata basar da zancen tace wai kana aminin yayana amma ace baka taba zuwa gidan nan ba. Gaskiya badan badan ba da nace baka da. Murmushi yayi yace karasa mana nasan cewa zakiyi bani da kirki ko?. Kuma ba haka bane duk laifin yayanki ne... Sun dade suna hira daga karshe dai ya karbi wayarta da kansa yayi unblock din kansa. Tukun ya bata wayar. Lokacin husaini ya fito yace kai uban surutu tashi mu tafi in rakaka gida ko in barks a nan ne.? Al ameen yace ai hakan ma yayi jeka abunka ka bamu waje muna hira ni da kanwata. Husaini ya rike baki yace au allah. Kai dallah malam tashi mu tafi. Juyawa yayi ya sai surutu al ameen yake ta zubawa zainab. Dadai yaga al ameen bayada niyar tasowa hannunsa yaje ya kama yace kaga malam taso mu tafi karka koyawa kanwata wannan shegen surutun irin naka. Al ameen ya mike badan yaso ba yace kanwata kinga wannan yayan naki korata yake a gidan naku ko. Wannan shi zai tabbatar miki da cewa baya so in zo gidan. Zainab tayi Murmushi tace aa ba haka bane wata kila baya so in kaje gida madam ta maka fada ne shi yasa. a'ah wato dai kema goyan bayansa kike ko tare dake ake korata. Lokacin umma ta fito tana Murmushi ganin su da tayi a tsai-tsaye tace ah har zaku tafi. Al ameen a kunyace ya sadda kai eh wllh umma zan tafi.




To madallah a gaida yan gidan. Yace to zasuji. Umma tace kuma sai yaushe?. Al ameen yace umma ai yanzu tunda nasan gidan zan dinga lekowa muna gaisawa. Ko ni daya ne. Dama can baya rashin sanin gidan yajawo haka. Nan sukayi bankwana da umma. Zainab kuwa har mota ta rakosu sukayi bankwana tukun ta juya su kuma suka tada muta suka tafi.

Su kursiyya a parllo sun tada sautin kida har daga waje ana jiyowa. Su mai gadi kam abun yafi karfinsu karar tayi yawa hakan yasa suka dawo kofar gidan suna ta masifa. Wacce bata da amfani. gidan sai wari da tsami yake tashi. Ba yanda za'ayi mai tsantsani ya iya zama na 10mints a ciki. kaya kaca-kaca ko'ina duk sun warwatsa. Su kuwa sai rawar su suke tikawa. Ita da marsiyya. Su al ameen suka karyo kwana suma tun a farkon layin suke jin kida kamar casu ake a layin. Husaini yace al ameen wai biki ake yi ne a layin naku. Shi kuwa al ameen dake yasan halin kayansa yace. Aa wllh ba biki bane Yasmeen ce. Yarinyar bata jin magana ne wllh na hanata- na hanata amma taki ta bari. Nace matq in ma waka take san ji ta dinga sasauta volume din amma a haka ai volume yayi yawa tana takurawa yan anguwa.





Husaini yace ah lalai wato ma da daurin gindinka take yi bama ka hanata ba saidai kace ta rage volume ko. To yayi kyau amma kasan irin wannan ba kyau ko. To ai ko ba komai ma kasani duk gidan da irin wannan sautin wakar ke tashi kai koma baikai haka kara ba to mala'ikun rahama baxa su sauka a gidan ba. Kuma bayan haka yana janyo aljanu. Shedanun aljanu suna san kade-kade da wak'e-wak'e kaga kenan gidan ka ne club din aljanu kenan kaga kenan yanzu haka ma suna can sun cika maka gida sai tikar rawa suke.

(Nayi dariya nace ka canka daidai ml husaini)

Al ameen ya dan bata rai yace ni fa kaji matsalana da kai kenan wllh. Kai baka waye ba abu kadan sai ka jawo wa mutun aya ko hadisi to ni bana san haka gaskiya. Idan zakayi wa'azi to ga masalaci can ko kuma kaje kasuwa i no need. Kaji mutun to shikenan sai in hanata ta shakata. Bayan kuma kasan ita din babbar yarinyar ce. Husaini ya jinjina kai yace ah lalai. Bazan hanata ba.allah ya baka hakuri kaji muje. Al ameen yace ameen yaja mota sukayi gaba. A kofar gida suka iske su idi da lawal mai gadi. Da sauri lawal ya tashi ya bude musu gate. Nan al ameen yake tambayar idi me yasa baije dauko saba a airport. Idi yace wllh motar ce ta dan sama matsala saida aka gyara kuma wayata ba charji. Al amee yace ok ba matsla. Ya shige.




Ta glass din window marsiyya ta hangi su al ameen na fitowa daga kofar mota. Da sauri ta juya ta sanarwa kursiyyya. Kursiyya ta juya baya ta kalli dakin kaca-kaca kuma ga wari. Da sauri tace marsiyya ta gyara parllo kafin su shigo ita kuma zata kwashe kayan wanke -wanke ta wanke. Kafin kace me marsiyya ta fara kimtsa dakin tana shashare ko'ina. Ita kuma kursiyya tuni ta kwashe kayan ta shiga kitchen tana wankewa a cikin sauri irin nasu na aljanu shaf-shaf ta gama ta shirya su. ta fito ta tarar da marsiyya ma ta gama. Kursiyya naga ta bace bat. Kafin kace me sai gata ta dawo hannunta dauke da kaskon turaren kamshi. Bullowarta keda wuya su al ameen suka fara kwankwasa kofa.marsiyya najin haka tq bace. Ita kuma kursiyya ta koma Yasmeen cikin wata kafurar shiga. Yar guntuwar riga figil kadan ta wuce cibiyarta.sai kuma jeans wanda ya dame jikinta ya tsuketa sosai komai na jikinta a bayyane yake.




Tafiya take tana karye-karye irin na wanda kunya bata ishesu ba. Tana bude kofar taga su al ameen ne. Rungume shi tayi. Tana oyoyo-oyoyo babyna shi kuma duk kunya ce ta rufe shi kokarin ture tama yake yi. Husaini kuwa tunda yayi mata kallo daya ya kauda kai bai sake kallan inda take ba domin mumunar shiga ce tayi wacce ko wasu arnan ma basa yin irinta........................................................


King boy


















๐Ÿ™Ž๐Ÿฟโ˜  MIJIN ALJANAH โ˜ ๐Ÿ™Ž๐Ÿฟ


page 114 - 115


|
|
na king boy isah๐Ÿ‘‘
|
|
__________________________
๐ŸŒŸZAMANI APR 2017 ๐ŸŒŸ
|_________________________|




***** zamani *****
๐ŸŒŸZAMANI WRITER'S ASSOCIATION ๐ŸŒŸ ยฉZ.W.A
*** ** zamani *****




GOOD NIGHT TO ALL MY FANS. YAUDAI NA CIKA ALKAWARI KO? 3POST


Da kyar al ameen ya samu ya rabata da jikinsa. A hakan ma ta kama hannunsa suka shiga ciki. Tana ta yi mishi shagwaba da karye-karye wai ya tafi ya barta a gida ita kadai. Al amern yace srry dear tafiyar ce tazo muna a bazata muma amma ai bamuyi zatan zamu dade haka ba.



Kuma gida ai ba ke kadai bane a ciki tunda gasu lawal nan. A shagwabance tace aa dr suda suke a waje ni ai kawai aunty hajarq na kirawo tare muke ynz ta shiga daki ma. Al ameen yace hmm lalai kin cika matsoraciya Yasmeen. Wani kiss take kokarin manna mishi yayi saurin dakatar da ita. yace kina so kice baki ga bakon namu bama ko.



Sai lokacin ta dan waiwayo baya. Manyan gari ina yini?. Abunda ta fada kenan domin ita bata san sunansa ba. Husaini ya amsa yana kallan wani wajen ba tare da ya kalle taba yace wato angon ya dauke miki hankali ko ganina ma bakiyi ba ko?. Yasmeen tace kayi hakuri yaya nayi missing dinsa ne sosai shi yasa. Da sauri al ameen ya kalleta yace.


Au wato yau ba'a kiransa da bokan turai din da aka saba kenan.ya koma ma yaya?. Yasmeen tace eh yau a yayah yake. Lokacin suka zazauna ita kuma ta shiga kicin ta kawo musu abinci ta jajare a dinner room.



( ni dai kam banga kursiyya tayi girki ba shi yasa ma nace abincin nan duk inda ya fito na sata ne.)


Sun fara cin abinci al ameen yace wai me aunty hajara tqke yi ne a daki ta dade haka. Ko zuwa zakiyi ki kirawo ta kice mun dawo taxo mu gaisa. Ba gardama ta tafi . a jikin bango ta iske marsiyya kmr wata faster sai lilo take. Kursiyya tace sis yi sauri kizo mu fita ana neman anty hajara. Bullut! Ta bace ta kuma bullo a sufar hajara komai da komai. Suka jero a tare.



Suka isa dinner din. Hajara tana Murmushi tace kanena ashe ka dawo saukar yaushe ya hanya?.


Ya juya komai nml wllh aunty ashe wannan matsoraciyar ta gayyato ki. Dan allah aunty in ba dan abunta ba me zai kama mutun a wannan gidan. Hajara tace kyale ta dai dama can na gano ta salan tasani wahala ne kaga ai ko ba komai ina tayata aiki ko. Yace hk ne kam. Husaini lokaci ya juyo suka gaisa da aunty hajara shima.


Waje ta samu ta zauna sun dade suna hira tukun husaini yace shifa tafiya zaiyi gashi yamma ta fara yi kuma yana bukatar hutu. Nan sukayi sallama da su yasmeen tare suka fita da al ameen din zai raka shi..

********

Real Yasmeen ce zaune a parllo wasu hawayen bakin ciki na kwararo mata a fuska. Wai ni al ameen ya saka ba tare da ya tsaya yayi bincike ba a kan lamarin. Banyi tunanin al ameen zaka min haka ba. Ban tsanmaci wannan hukuncin daga gare kaba al ameen. Ko dan ma ba laifinka bane kawo ne mai laifi. Duniyar tunani ta fada shin wai me tayi wa kawu kasumu ne.


Ta dade tana tunani amma ta kasa gano laifi ko wani kuskure wanda ta taba aikatawa kawu kasumu. Wasu hawayen ne suka kara kwaranyowa a fuskarta. Daidai lokacin kuwa nuratu ta shigo. Da gudu ta karaso ta fada kan yasmeen. Tana dariya.



Yasmeen da sauri ta hadiye fishinta kuma ta share hawayen dake fuskarta dan kar nuratu ta gani. Tace nuratu wa kika tsokalo ne kuma kika rugo da gudu haka. Nuratu tace wayar mama na sato bata sani ba kin ganta ma. Riga ta daga ta fiddo wayar. Datake rike a hannunta ta boye da riga. Yasmeen ta fige wayar tace ke kuwa in banda abunki me yasa zaki dauko mata waya me zakiyi da ita.




Nuratu tace aunty game zanyi. Aa Nuratu kina ganin bamu da wuta. Ai sai ki cinye mata charji. Kuka Nuratu ta farayi hada buga kafa. Yasmeen tayi lalabun tayi-tayi amma taki yin shiru. Yasmeen tace to yi shiru in baki wani labari mai dadi.



Nuratu ta dan sasauta kukan. Yasmeen kuwa rasa labarin da zata bata tayk ma hakan yasa tayi sauri ta shiga facebook. Tayi search na page din bigboy isah fans. Like tayi tukun ta fara binciken posts nan tayi karu da wani saban littafin sa mai suna aljanar fatima. Ta kalli Nuratu tace kina san in baki labarin aljana.


Gyada kai tayi sannan ta share hawayen ta matso jikin yasmeen. Yasmeen ta bi posts din page 1 tukun ta fara karantawa nuratu kmr haka.:



A cikin garin bauchi gidan kamal S.O babban gida ne dake cike da iyalai. Yana da yara da dama. da yake matansa hudu Asiya uwar gida sai mai bi mata ikilima da kubra tukun hindu wacce itace amarya. Saidai amaryarsa ta mutu wato hindatu.



Shekarar hindatu uku a gidan ta rasu sai dai ta mutu ta bar wata yar jaririyar yarinya mai suna fatima. Yarinyar fara kyakyawa a duk gidan tafi kowa kyau domin ita ta dara mahaifiyarta ma kyau. Alhj kamal kuwa ya dauki duk san duniyar nan ya dora a kan fatima domin yana jin tausayinta sosai kasan cewarta karama kuma maraya.


Irin san da yake nuna mata shi ya jawo mata ta zama kamar jaba a gidan maza da mata yara da manya baki daya ba mai ragawa fatima a gidan bata samun sauki da farin ciki sai abbanta na gida.


Hakan yasa ma in baya nan sai ta shiga daki abunta wani lokacin tata barci wani tym din kuma tata kuka abunta idan ta tuno mahaifiyarta. A labarin da nake baku yanzu fatima takai shekara 9 da rabi a duniya ta iya yiwa kanta komai. Domin har ta saba da wahalar da yan uwan nata suke bata.



(One day!) Fatima ce ta tashi daga barci ta kalli dan agogon dake ajiye a kan mirror dakin nasu firgigit ta zabura ganin karfe 6:10 bata yi sallah ba. Sauran yan uwan nata mata da suke tare a dakin ta kalla.akwai Manya a cikinsu harda wacce ko yau za'a iya kaita gidan mijinta. Ni dai har ynz ban tantance yawan su ba amma kowa da gadanta.fatima ita ba abun ta tashe su ba tasha fada in bataci sa'a bama har duka. Tashi tayi ta nufi ban daki a guje. Tayi alwala ta dawo ta tayar da sallah. Naji muku haushi sosai da baku ji karatun yarinyar nan ba.



A hankali bayan tayi fatiha take jan suratul ุงู„ุบุง ุดูŠุฉ ghaashiya. Muryarta na fitowa a hankali. Kamar kar karatun ya kare. Tayi zaman tahiya kafin ta karasa ta sallame. Tun kafin matar ta karaso take kwalla uban kira. Fatu! Fatutu! Da karfi. Fatima najin haka ta kama sauri allah! Allah take ta idar da sallah kafin matar ta shigo.



domin tasan halin mama asiya kwarai bata bata dadi kuma tafi kowa musguna mata a gidan. Asiya ita ce uwargida. Banko dakin tayi.


Kamar wacce zata karya shi. Ta tsaya a gurin ta kama baki. Iyye yar banza wato sai yanzu ma kike sallah baki tashi da asuba kinyi ba ko.? inji mama asiya. A zuciya kuwa tace yarinya kina kokari domin kuwa ni banma yi ba tukun. Daidai lokacin fatima ta idar da sallah ta juyo ta dan risina tace mama asiya ina kwana. Munafuka. Kaganta kamar wata salaha. To da ban kwana ba zaki ganni ne. Maza-maza ki iske ni a kitchen.



Yau dake zamu hada kayan kari. Saura kuma ki ki zuwa da wuri ta kama kunnan fatima ta murda. Kinga kunnan nan to sai na cira shi. Ko in babalaki in yaso in bada kudin dori.



Faima sai da tayi dan kara domin zafin da taji na murda kunnan gashi har yanzu taki sakinta. Asiya tace. Bazaki bar yiwa mutane ihu ba sai kin tada mana yara. Maza ki iske ni a kitchen kinji ko? Gyda kai fatima tayi tace naji gani nan zuwa mama. Mari ta wanka mata. Wacece mamarki din?. Allah ya suttura in haifi yarinya kamarki. Ta nuna wasu yan mata dake gefe a gado suna ta sharar barci tace kinga yarana can ba kamarki ba. Mtseww Ta ja tsaki ta fice.



Nan ta bar fatima tana kuka. Ta zubda hawaye sosai tukun ta tashi taje da sauri ta shiga bedroom tayi brush tukun ta canza kaya ta fito. Dugi dugi ta nufi kitchen. Fatima tasha wuya sosai a kitchen din dake gaba daya ake haduwa ayi girki a gidan. ba mai tausaya mata a cikin matan baban nata duk su ukun miko wancan kulkula wannan wanke can gyara can. Ba mai tausaya mata ko ganin kankantarta a cikin matan. Bayan an kamala ita suka dinga dorawa kulolin abincin tana kaiwa dinner. Saida aka kamala komai tukun suka korata daki kuma suka ce in ta shiga ta kwanta kmr mai barci kar ta yarda alhj ya gane cewa ta tashi balle ma ya gano tayi aiki. Haka ta tafi tayi yanda sukace ta hau gadanta tayi shiru. Tana ajiyar zuciya. Su kuwa kowacce. Sai ta shigo dakin ta tada ya nata-ya nata duk suka yi wanka sukayi brush tukun aka nufi dinner. A nan kwance suka bar fatima. Tana jinsu duk abunda suke.
...................................................











๐Ÿ™Ž๐Ÿฟโ˜  MIJIN ALJANAH โ˜ ๐Ÿ™Ž๐Ÿฟ


page 116 - 117


|
|
na king boy isah๐Ÿ‘‘
|
|
__________________________
๐ŸŒŸZAMANI APR 2017 ๐ŸŒŸ
|_________________________|




***** zamani *****
๐ŸŒŸZAMANI WRITER'S ASSOCIATION ๐ŸŒŸ ยฉZ.W.A
***** zamani *****










Wajen cin abincin bangare bangare ne wajen yara mata daban haka maza ma daban.ban karasa tabbatar da yawan yan gidan nan ba saida naga maza. kowq dai sai harakar gabansa yake yara masu rigima nayi. Masu dan wayan cikin su kuwa na sasanci. Bangaren uwaye kuma sunsa abincin gaba an zubawa kowa nasa saidai ba damar ci. Sai alhj ya fito. Asiya tayi tsaki tace wai ace abincin ma sai an sawq mutane doka a kan.ji dallah yanda ya bar mutane najin yunwa yaje yayi zamansa... Shiru tayi sakamakon jin yara sun bar hayaniya alamun shigowar alhj kenan. Idan ya shigo duk rashin jin yaro sai ya natsu. Bayan yaje ya zauna. Uwayan wato matansa. Suka fara gaishe sa tukun suma yaran maxa da mata masu dan wayo suka biyo layi daya bayan daya suna gaida shi. Yayi mamaki da baiga fatima ba a cikin yan zuwa gaishe shi din. Da zai tambaya kuma sai ya kyale.



Shi ya fara yin bismillah ya fara kai abincin baki tukun kowa ya fara ci. Dokar cin abincin kenan sai ya fara cin indai yana gida tukun kow zaice. Fatima kuwa tana daki ga gajiya ga yunwa kuma sun sata barcin dole. Saidai kwata-kwata barcin yaki zuwa domin yunwar dake kwakwalar ta. Tana jin kwaram niyarsu ana cin abinci kamar ta fito sai dai kuma tana tsoran tayi laifi. Domin tasan in ta saba musu to yau ta shiga uku ko abincin rana baza su bata ba. Haka suke mata idan tayi musu wani laifin. Su sakata aiki mai tsanani kuma su sata azumin dole horo da yunwa. Haka dai ta hakura ta kwanta tana kuka.



Bayan an gama cin abinci kowa ya kama gabansa dake yau weekend ba makaranta. Alhj ya koma dakinsa amma sai ya kasa natsuwa da ya tino baigs fatima ba. Hakan yasa ya fito ya tambayi matan wai ina fatima ni ban ganta ba. Asiya tayi farat! Tace uhmm alhj kai da kasan halin yarinyar nan da shegiyar lalata. Tana can dakin yara nayi nayi in tashe ta tayi sallama amma taki tashi.



cikin fada yace asiya wace irin banzar magana ne kika fada min kina nufin fatima bata tashi ba har yanzu. me yasa kika zama muguwa maciya amana iyee asiya. yarinyar nan fa marainiya ce amanarta na baki. amma yanxu dan allah ace duk kin tashi yaranki sunyi wanka har sun karya amma ita dake ba yarki bace shine zaki barta har wannan lokacin bata karya ba. yanzu karfe 9:30 fa. Ta wani marairaice haba alhj in kuwa kace haka baka kyautaba yanzu duk irin tatalin da nake wa wannan yarinyar kana so kace baka gani alhj. Ni ai a ganina rashin tashin ta din ma da nayi duk a cikin gata ne. Na barta ne ta hutawa rant....


Tsawa ya daka mata. Ke dallah rufe min baki bana san wannan zakin bakin naki. Maza wuce ki kira wo min ita. Murguda baki tayi ta tashi tana gunguni. Wai irin wannan ai sai yaja a rainata a gaban kishiyoyinta ake mata wannan abun. Alhj yace me kikace. Juyowa tayi. Aa ni banyi magana ba. Ta wani gallo mishi harara. Ta nufi dakin yara. Fatima najin turo kofarta tayi maza ta rufe idanunta kamar mai barci.



Asiya kuwa tazo ta kama tikarta fati fati. Tashe muna fuka kinzo kin kwanta wato sai barci kike.maza jeki kiyi brush ki zo wannan masifafan mutumin na kiranki. Fati batq ce komai ba ta sauko taje tayi brush ta dawo. Tazo gaban asiya tace nayi. Rigarta ta gyara mata ta kuma dan go goge mata fuska kamar da gaske. Tace idan kika yarda kika ce kinyi aiki kuma kika gayawa alhj ni nace ki dawo daki ki kwanta to ni dake ne a gidan nan kinsan dai halina sarai.


Fatima tace bazance ba aunty. Dankwashinta tayi a kai. Kinci uwaki. Nice aunty wato bama mama ba ko. Wuce muje. Fatima ta shiga gaba asiya na binta baya. Alhj kallo daya yayi wa fatima ya gane tana jin yunwa. Bata karta ba. Momyna sunanda yake kiranta da shi kenan. Kinci abinci kuwa. Girgiza kai tayi tace aa ynz na tashi a barci. Barxi kuma wato bakiyi sallah ba ko?. Bana ce ki dinga kula da sallah ba ki bar wasa da ita. Dady nayi fa tun da wari nayi sallah sannan na koma barcin. That good haka nake san ji momyna.



Juyawa yayi ga matan nasa wanda duk sun Zuro musu ido ba abunda suke sai hararen fatima. A cikin zuciyqrsu kuma tsanarta na kara fadada. Ina abincinta?. Ya tambaya kubra tace alhj wane abinci kuma ai gidan nan ba wani sauran abinci duk an cinye tana can tana barci. Alhj yace ynz yarinyar bata ci abinci ba shine kukaki ajiye mata. Ko dan kunsan ba yayqnku bane. Wato ita maraya batada uwa ko. Bai tsaya jin abunda zasuce ba yaja hannun fatima yace zo muje in saya miki abinci mamana. Yaja hannunta suka fita.



Nan ya bar mata sai surutai suke yi. Har asiya na cewa wai anya kuwa uwar yarinyar can ba asiri tayiwa alhj ba kuma har yanzu bayan ta mutu yake tasiri a kan yarta ba.nifa abun ya fara bani tsoro. Iklima tace haba aunty barta mn ai gasuwa zatayi a gidan nan domin ko yar aiki sai tafita jin dadi wllh. Yarinya karama sai kini bibin tsiya.



Mota suka hau alhj yaja saida suka je wata rumfar mai shayi tukun ya faka ya fito yajawo hannunta suka shiga suka zauna yasa a soyo mishi indomei da kwai da kuma zallar wainar kwan da kofin shayi biyu. Kudi ya kashe musu dai sosai a gurin. Fatima saida taji cikinta ya cika nat! Domin kuwa rabanta da ta sama isashen abinci tun

Please Login or Register in order to submit comment