Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

waccan juma'ar da taje gidan su wata kawarta ta wasa. Mota suka hau suka nufo gida tafiya ake fatima sai waige-waige take yi ta kalli can ta kalli can. Tana kallan shaguna. Dady tsaya-dady tsaya. Bai shirya ba ya take birki. Ya fara tambayarta miye. Dady danyi baya. Yi baya dady. Baiyi gardama ba yayi baya da motar. Saida suka zo saitin wani shago tace ya tsaya. Da gudu ta sauko taje tana kokarin dauko wata yar baby. Wacce suke a jere duk na sayarwa ne.


Mai shagon ne ya fito yana neman dukanta alhj ya dakatarda shi. Yace mamana miye hk kika zo zaki daukar musu abu na sayarwa ne fa ko baki sani ba?. Na sani dady wannan nake so ka saya min ina santa. Dan Murmushi yayi kadan yace ke kuwa me zakiyi da wannan katuwar diyar robber ai tayi girma duba karama mn. Wannan tafa kusan kaiki tsayi. Aa baba ni wannan nake so. Alhj ya kalli mai shagon ya tambayi kudin diyar robar. Mai shago yace dubu bakwai. Alhj yace ina zuwa. Mota ya koma ya dauko kudi kash! Ashr na baro kudin a gida. Saura dubu uku ne a hannunsa. Ya dawo cikin yanayin damuwa gashi mutumin baisan shi ba. Balle yace in ya fito zai kawo mishi. Ita kuwa fatima rike take da yar robar har ta fara wasa da ita.



Ya dawo yace malam na manta kudina ne a gida kaga saura dubu uku canjina kayi hakuri ka rike wannan ka bamu yar robar in yaso idan na fito zan kawo maka. Mai shagon yace ai ina ban sanka ba bazan taba yarda ba. Kaga kawai in bazaka saya bane to.



Alhj ya kalli yar tasa yace fatima kinga yanzu bani da canji zo muje gida in dauko kudi sai mu dawo in saya miki. Fatima ta saka kuka wai ai ita baza'a rabata da yar babyn ta ba. Alhj yayi-yayi da ita ta bari ya dawo amma taki. Ba yanda ya iya dole wayarsa ya bawa mai shagon ya rike ya basu yar babyn kafin ya dauko mishi kudin. Haka kuwa akayi. Mai shago ya karba yaje shago ya ajiye tukun ya dauko musu wata yar karamar akwati. Ta kayan yar babyn ce. Suka karba fatima sai murna take ta dauki yar babyn wacce ta kusa tsayinta tasa a mota suka tafi gida............................................... . .........











????☠ MIJIN ALJANAH ☠????


page 118 - 119


|
|
na king boy isah??
|
|
__________________________
??ZAMANI MAY 2017 ??
|_________________________|




***** zamani *****
??ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION ?? ©Z.W.A
***** zamani *****




IN DEDICATED TO YOU SMART SANAH ALLAH YA ALBARKACI RAYUWARKI. yan uwa muna yi muka tallar litaffin shaharariyar marubuciyar nan wato SANAH SHAHADA mai suna *FANSAR KAI* labari ne mai nishadan tarwa fadakarwa soyewa kai uwa uba ma daukar fansa. maza-maza ka garzaya *OKADA BOOK* Domin ka mallaki naka. okada book wani app ne na wayar andriod dake bada damar saye da sayarwa na littafai a saukake. maza-maza ka/ki garzaya kar a baki/ ka labari. ku nemi okada book app a playstore





tun a mota yar babyn ta fara magana. a cikin wata irin karamar murya. sufuratu. ina tayaki murna da sayana da kikayi. fatima ta juya domin ganin mai magana bataga kowa ba. tace abba kaine kayi magana ynz. yace aa mgn kikaji nayi. tace mgn naji ko yar babyna ce. alhj murmushi yayi yace yar baby kuma ai ba irin mai magana bace. Zan dinga saki dariys zan dinga baki labarai amma ni fa ba'a barina da yunwa kuma ni kullum sai anyi min wanka an canza min kaya..... alhj tsurewa yayi domin yaji tabbas yar babyn ce ke magana a tsorace ya fige yar robar yana dudubata wai ko zaiga speaker a jikinta amma bai gani ba. ita kuwa fatima murna kawai take da jindadi yar babynta na magana. alhj yace fatima yar babynki ce fa mai maganar nan to amma ni banga speaker a jikinta ba. fatima ta karbe abunta tace baba ai itama da baki take yi kamar mu baka gani bane?.




yace eh ni ban gani ba. hk dai yaci gaba da tuki cike da mamaki har suka karasa gida. fatima ta sauka da gudu tana murna ta nufi cikin gida rungume da yar babynta a parlo ta iske duk yan gidan yara nata rashin ji masu wasa nayi masu rigima ma hk. ai kuwa yan yaran na ganin yar babyn suka yo kan fatima wannan ya karba wannan ya figa wai ko wane yaro sai ya je gurin uwarsa ya kama kuka wai a kwace a bashi. can wasu yara marar ji guda biyu daya ya kama wajen kan yar babyn daya kuma ya kama kafafun sai jayaya suke wannan yana so ya karbe wannan ma yana so ya karbe fatima kuma sai kuka take zasu karya mata yar baby gashi ba dama tayi mgn.



lokacin alhj ya shigo. kai! kai! ku wane irin mararsa jin magana ne. zaku balla mata abu bata kayanta maza. mika mata sukayi. ta karba ta nufi dakinta asiya ta harare ta tace a zuciyarta munahika ai alhajin zai tafi zaki ci ubanki. alhj yace yanzu ku kuna gani a gabanku zasu batawq yarinya abu a gabanku amma ko kuyi magana. haba asiya kece babba fa ko sauran basuyi magana ba ai ya kamata ke kiyi mawa yaran magana. uhm ai ni kullun a wajenka marar adalci ce to amma yanzu kai ga adalci nan a fili ka nuna mana tunda ga yara nan da yawa a gida kuma duk yayanka ne amma ace ka ware fatima ita kadai ka saya mata abu. wannan shine adalci ko. Ran alhj ya bace har zaiyi mgn kuma sai ya fasa ya wuce up stairs. yaje dakinsa ya dauko kudi yq fito yayi tafiyarsa.



su ikilima sukayi dariya sukace aunty asiya kin min daidai ke kadai ce maganin alhj a gidan nan. asiya tace hmm ku kyale sa ai yau saina toya yar babyn nan muga ta tsiya sai inga me zaiyi haba ya zai dinga fifita wacce kudabukar yarinyar a kan sauran yara bari inje gurinta. su Ikilima binta kawai sukayi da kallo. ta tashi buzun-buzun ta ta nufi dakin yara. fatima zaune take a kan gadanta ta zaunar da yar babyn tana cin bisket itama tana tura mata a baki. tana ci ci diyata daga bakin. kawai sai taga bakin ya bude. bata wani firgita ba sai ma dadi da taji. ta tura mata bisket din tace kin koshi.?



lokacin asiya ta karaso gurin ta kama yar babyn da hannu daya ta wullata jikin bango ta fado tim! ta kuma wanke fatima da mari shegiya yarinya me kike a nan tun dazu ina can ina jiranki zan aike ki kin wani shigo daki kin zauna. dama nasan wannan yar babyn da kika samu ita zata dinga hanaki aiki amma bari ynz in dauke tq in yayankata in toya muga ta tsiya. fatima ta fashe da kuka tana bawa asiya hakuri karta yanka mata ya' abun mamaki fatima na fara kukan suka jiyo kuka a baya. asiya ta juya baya. yar babyn ya gani a zaune tana kuka harda ruwan hawaye.************** *(_dililili lin dilililin_ karar mutuwar tecno* lolz



carji ya kara a wayar ta dauke. gashi ba wuta. nuratu tace aunty ya naji kinyi shiru kuma gashi labarin ya fara min dadin. yasmeen tace kinga wayarce ta dauke nima naso inji wai ko yar babyn ce aljanar idan itace kuwa zan so inji karshen labarin domin zai dadi gaskiya. gashi nima wayata ba charji. kuka nuratu ta fara wuyy-wuyy hajara da sauri ta fito tana tambaya miye. yasmeen tace kinga wayarki ta dauko ta kawo min ina karanta mata wani labari shine charji ya kare kuma lbr ya fara dadi kinji dalilin kukan. hajara tace na shiga uku yanzu kun shanye min charji kenan bayan kunsan bama wani samun nepa. yasmeen tace wato mu muna ta labari ke ta charjin ki kike ma ko?.

********************


al ameen ne kwance rungume da kursiyya dake a matsayin yasmeen ita tuni har ta fara barci shi kuwa ina barcin ya gagara Zainab kawai yake tunani domin duk yau wunivl yayi yana murmushi a duk lokacin da ya tuno ta. haka ita ma can bangaranta rike take da wayarta ta hau online ta shiga cikin inbox din al amen jira take kawai ya hau. amma shiru gashi har wajen karfe 11:30 yanzu jin shiru-shiru din yayi yawa yasa ta hakura ta kashe data. ta tashi taje tayo alwala. tazo ta fara nafilar dare kamar yanda ta saba yi kullum.




al ameen abun ya takura mishi sosai tunanin Zainab ya hanashi sakat. a hankali ya fara zame jikinsa yana raba yasmeen da jikinsa. a hankali yanda baxata farka ba. ya kuwa ci nasara har ya tashi ko motsawa batayi ba. shi kuwa ya nufi parllo tun a hanya ya fara kiran number Zainab amma shiru anki dagawa wajen kira uku yayi yaji shiru tana ringing amna ba'a dagawa yace hmm wannan inaga tayi barci bari in leka whatsapp inga ko ta aiko min da wani sakon. ita kuwa Zainab tana sallah taji kiransa gashi raka'ar farko ce ba yand ta iya dole ta kyale wayar tata ring.




al ameen ya bude data massages suka fara shigowa, daidao lokacin kursiyya ta farka taga al ameen baya nan. bacewq tayi. tukun ta tashi ta duba ban daki baya nan ta nufo parllo. a zaune ta hange shi ya tsurawa wayar idanu. sai da tazo saitin kansa ta leka taga a kan whatsapp yake tace au inaga kursiyyarsa yake san gani cike da farin ciki ta koma kujerar da ke facen dinsa ta zauna dake shi baya ganinta baima dan tazo ba, tana mika hannu sama naga wata makekiyar waya ta bayyana a hannunta bude data tayi itama,




al ameen ya duba last seen din Zainab yaga baifi 10 mints ba da saukarta nan yaji wani bakin ciki ya cika shi. kursiyya daure fuska tayi ganin al ameen ko bude massages din data aika mishi dazun baiba. wayar al ameen ce ta hau ruri gani tayi ya kalli wayar alamun ya ga wanda ke kira lokaci daya taga ya kama murmushi fuskarsa cike da farinciki har karkarwa yake wajen daga wa. tunani take yi a ranta shin waye wannan da yake kiran al ameen a dai-,dai wannan lokaci.?.........................................................



uhm nan fa ake yinta.lolz



Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks





✍??Autan marubuta ✍??



??King boy??










🙎🏿☠ MIJIN ALJANAH ☠🙎🏿


page 120 - 121


|
|
na king boy isah👑
|
|
__________________________
🌟ZAMANI APR 2017 🌟
|_________________________|




***** zamani *****
🌟ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION 🌟 ©Z.W.A
***** zamani *****









😟 _*DEDICATED TO UR|„> AUNTY FATIMA MMN ALI*_ 👍🏽 THANKS d like and support me 😜 allah yayi albarka


_kufa ya y hakuri dani kunsan ance kana taka allah na tashi. abunda ka tsara ba a ko wane lokaci bane yake zuwa dai yanda kaso domin har ga allah nma ina so inyi sauri kafin azumi in idasa mijin aljananan amma I'm very busy_😰





al ameen ya danyi gyaran murya tukun ya dauki wayar mamaki ne ya cikata da taji kalan maganar da al ameen yake yi.



ya wani make murya da yayi yake maganar cikin salo. ita bata ma taba ji yana yi wa ko yasmeen magana a haka ba.




" sister har wannan lokacin bakiyi barci ba. me kike yi ne?.


Zee tace " eh wllh na danyi nafila ne. dan allah kayi hakuri dazun ina jin kiranka to lokacin ina sallah ne ba yanda na iya. shi yasa kaga ban dauka ba.



"ba komai sister na fatan dai ana taya mu da addu'a.


" addu'a ai dole ayi muku idan ban yi maka ba to wa zanwa. Al ameen ji yaya maganar nayi mishi yawo a kwakwalwa. a Zuciya tace " tabbas wannan ta kamu.



kursiyya na gefe ta wani daure fuska ranta ya baci wani bakin hayaki naga ke tashi daga kan nata. kishi ne ya cika ta. wato shi wannan dan mutumin kwashe-kwashe yayi mishi yawa kenan. wannan kuma ko wacece oho!




tashi tayi ta zagaya ta bayanshi domin ta duba taga wacece wannan. *MY ZEE ZAINAB*




haka taga an saka a jikin number, tace "tabb lalai za'ayi dan guntun bala'i a gidan nan wannan mayyar ce ashe.
maganar da taji ya kwaso ne ya dakatar da ita daga zancen zucin da take.



"Sister na in tambaye ki mana. kina da saurayi kuwa?.


"Eh mana inada samari har guda uku ma sai dai duk a ciki nafi san daya.



" guda uku fa kika ce?. ya fada a cikin mamaki



" eh yaya guda uku ko sunyi yawa ne?.


Al ameen yayi ajiyar zuciya yace" aa sister ai kinsan abun rabo ne...? kuma ai ke din a yanzu kamar kwarar hatsen da zakaru hudu suka zagaye tana sai mai rabo zai samu nasarar daukarta.



Zainab murmushi tayi domin kuwa ta gane me yake nufi. wato ya sako kansa a ciki kenan. cewa tayi " to ai a cikinsu ma ba wanda yake zuwa yanzu domin yah husini duk ya kore su wai yan iska ne. zasu bata min tarbiya.
al ameen yace " yauwa yayi min daidai wllh irin wannan samarin sai sun sama kamilar yarinya sannan suke zuwa su juya mata tunani su lalata mata tarbiya.




hira suka sha sosai al ameen na kara shigar da kansa. basu rabu da juna ba sai karfe 1 da wani abu. duk maganar da suke yi kuwa kursiyya na tsaye tana ji. sai chanza halita take tana wani huci kishi ya cika ta. tace




"Al ameen kenan bazan taba bari ka auro Zainab cikin gidan nan ba domin kuwa bana santa ko kadan.




bayan al ameen ya gama waya cikin farin ciki ya tashi ya nufi daki. kafin ya shiga tuni kursiyya ta koma kan gado. a yanda ya bar yasmeen haka ya iske ta tana ta sharar barcinta.




sai tin kanta yaje yana shafa gashin kanta a hankali yake maganar. " kiyi hakuri yasmeen nasan munyi alkawari dake bazan kara aure ba.domin a lokacin banyi tunanin Zanga wata wace ta kaiki kyau bà.
a yanzu kuwa kwatsam sai ga Zainab ta fado rayuwata. kuma ina jinta sosai a cikin raina. tana da kyau ga ilimi ladabi da biyaya gata kuma da kunya. yasmeen kin min afuwa zan auri Zainab.



kursiyya najinsa duk abunda yake fada wai kishi ne ke kara ziyarto zuciyarta. ba dan tana tsoran Zainab ba da yau sai taje taga bayanta. ji yayi ta dan motsa kadan da sauri ya dauke hannunsa daga fuskanta ya kwanta.
_washe gari da safe._



_kursiyya ta fara farkawa a barci. zaune tayi a bakin gado tana tunanin matakin da zata dauka a kan Zainab domin tasan indai Zainab ta shigo gidan nan to karyarta ta kare. ko ince karyarsu. tashi tayi taje gefan da al ameen yake a kan gadan ta tsure shi dana mujiya. al ameen din nata a kullum kara kyau yake mata. kara shiga ranta yake._
_hannu tasa tana shafa fuskarsa a hankali. take fadin al ameen bazan taba bari ka auri Zainab ba._


_tunda na rabaka da yasmeen to tabbas itama sai nayi duk iya kokarina na hanata shigowa. domin al ameen kai nawa ne ni kadai mahaifiyar ka ta haifa mawa._



_ji tayi ya dan moskuta kadan da sauri ta kalle shi wani haske ya fito daga idanunta ya shiga jikin al ameen._



_tashi tayi ta nufi parloo a nan ta iske marsiyya. tace "yar kanwata kin ganni sai yanzu ko?._



_marsiyya tace " ai ba damuwa aunty ke da kike tare da mai gidanki dama ai dole kifi war haka ma baki tashi ba. kursiyya tace_




_" uhmm sis akwai gagarumar matsala fa. da sauri marsiyya tace aunty matsala kuma ta me_😳




" _Al ameen aure zai kara. kuma abun damuwar ma shine wai Zainab zai auro yarinyar nan datake takura min._




" 🤔 _aunty aure kuma. hmm lalai al ameen ya debo ruwan dafa kansa. mu zai rainawa wayo ai abunda bazai taba yuyuwa ba kenan. to waima aunty me yasa kike tsoran yarinyar nan sosai ne.? kawai mu gama da ita mana._
_kursiyya tayi Murmushi tukun tace kanwata kenan. ai abunda baki sani ba shine Yarinyar nan ko kusa da gidan su bazaki iya zuwa ba. domin kuwa bata wasa da adduo'in kare kai. Al ameen dinma fa bai sanar dani ba tukun. amma jiya dai naji duk abunda yace. saboda haka ni nasan matakin da zan dauka a kansu ke dai kawai ki zuba ido kiga abunda zai faru. yau wasan zai fara ni da su._



Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks





✍??Autan marubuta ✍??



??King boy??













🙎🏿☠ MIJIN ALJANAH ☠🙎🏿


page 122 - 123


|
|
na king boy isah👑
|
|
__________________________
🌟ZAMANI APR 2017 🌟
|_________________________|




***** zamani *****
🌟ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION 🌟 ©Z.W.A
***** zamani *****









😟 _*DEDICATED TO UR|„> AUNTY FATIMA MMN ALI*_ 👍🏽 THANKS d like and support me. allah yayi albarka




_sai wajen karfe goma tukun al ameen ya farka daga barcin da aljanar ta saka shi. zabura yayi ya tashi zaune sakamakon agogo da ya kalla yaga karfe goma har tayi._



_ya juya baiga yasmeen ba yace " au wato yasmeen ta tashi shine taki tashi na ko.tashi yayi ya shig bathroom ya watsa ruwa yayi brush tukun ya fito. har lokacin yasmeen bata shigo dakin ba._




_hakan yasa ya fara kwada kira. " yasmeen! yasmeen! can yaji ta amsa na'am. ba'a dade ba sai gata ta shigo fuska ba annuri ko kallansa batayi ba. ta zo gabansa tayi zololo! tana kalan gefe gani lafiya?._



_mamaki ne ya cikasa yama kasa cewa komai ya tsaya yana kallanta. can da ta gaji da tsayuwar tace "malam ka kirawo ni kuma baka ce dani komai ba ka barni a tsaye._




_al ameen yace " yasmeen lafiyarki kalau kuwa. yanzu kinsan ko karfe nawa karfe goma harda rabi fa. amma shine zaki ki tayar dani bayan kinsan karfe 9 nake fita aiki. wane irin rashin mutunci ne wannan?_



_juya tayi ta kalli agogon dake manne a bangon tace "ohh! srry kayi hakuri mantawa nayi. inace shikenan laifin?_



_" yasmeen kin wani canza lokaci daya lafiya kuwa ko nayi miki wani laifin ne? " laifi ta tabe baki to ai sai ka binciki_ _kanka domin wannan tambayar kane kawai zaka iya bawa kanka amsa amma ba ni ba. tsaki taja ta juya tana yi mishi irin tafiyr yan bariki. al ameen ya saki baki yana kallanta._




_bayan yasa kayansa ya kimtsa ya dau jakarsa ya fito a parllo ya iske ta ta kunna wakar wizkid sai tikar rawa take yi. wace yama rasa a ina ta same ta._




_yasmeen! yasmeen! yasmeen! da karfi yake kiran sunan nata amma bata ji domin karan spekun ya cika dakin. zagayawa yayi ya kashe socket din. da sauri ta juyo._




" _haba malam wane irin wulakanci ne wannan da zaka kashe min waka ina nishadi na?. bai damuba yace "muje muyi breakfast ni fita zanyi idan yaso in mun gama sai ki dawo kiyi abunda kike so. ba mai hanaki._




_dariya tayi mai kama da yak'e tace abincin kari kake tambaya ko. ai sai kaje gurin mai shayi ka saya domin kuwa yau abinci iya naws kadai nayi kuma na cinye aheey!._




_al ameen yace yasmeen wane banzar magana ne haka kike fada?. kin taba gani na fita naje wajen mai shayi break dama tun da kika zo gidan nan?._




_"aa ban taba gani ba amma yau sai ka fara ai. ran al ameen Yayi mugun bace don har ya fara niyar wanka mata mari! wata zuciyar ce ta hana shi aikata hakan. jakarsa ya dauka rai a bace ya fice ya bar gidan._




_Kursiyya ta kwashe da dariya tace yanzu aka fara. Al ameen ne zaun e a office dinsa yama rasa me ke yi masa dadi damuwa duk tabi tayi mishi yawa me yayi wa yasmeen ne ko dai taji maganar da yayi jiya ne?. kai gaskiya bata ji ba wannan kawai shirmanta ne. da taji ai nasan da bala'i sai yafi haka_.



_wayarsa ya fiddo daga aljihu ya bude data ya shiga whatsapp domin yaga massages din Zainab ko zuciyarsa ma tayi sanyi. massages ne keta kwararowa. a jikin number kursiyya kuwa massages ne yafi sha biyar._
"slam"
"ykk"
_"mijina nayi missing dinka kwana biyu"
"yan magana sunyi gaskiya da sukace in so yayi so zuciya buyu ke dunkulewa waje daya. haka zuciyata da taka ta zamto daya. a duk ranar da ban saka a ido ba bana iya barci mijina"
"inata maganq kamin shiru lafiya kuwa"_

_"mijina"_

_"na kiraka ma naga kaki dauka. ko nayi ma wani laifin ne?"_
_"hmm tunda hakq ne nima nayi fushe da kai"_


_al ameen da ya gama karanta sakunan kursiyya abun dariya ma ya bashi. yace mahauka ciya kawai ai ni yanzu kin zama kwantai a gurina. kin tsufa dan haka a sambadi hanya. bama fushi ba block dinki zanyi muga ta tsiya kuma._


_yana gama fadin haka ya antaya ta a block list nashi dake cike da sunayen yan mata. fitowa yayi yaci gaba da duba sauran. daga wacce zai zugawa karya da kalaman shi na love. sai wacce zaiyi banza da ita. sai wacce zaiyi block haka naga ya dinga yi._



_number Zainab ya ga an aiko massages da sauri ya bar abunda yake ya nufi. number ta. da ya bude sako ne kamar haka_.



( _ASSALAMU-ALAIKUM yaya al ameen fatan ka tashi lafiya. ina so ka dauki magana nan da zan fada da muhimmanci. ni na kasance mace ce mai kunya sosai fiye da tunaninka. nayi iya kokari na domin in fadawa yaya mun san junan mu amma ina kunya ta hanani. a saboda haka nake ganin ya dace kai ka fada mishi. karda wankin wula ya kaimu dare. I LOVE YOU YAH AL AMEEN_😘)

_wata iriyar mika naga al ameen yayi wace na rasa dalilinta sai kuma naga ya juya zuwa farin ciki da jin dadi duk damuwarsa ta tsere._



_baiyi wata-wata ya turo mata text_

_"In dai yayanki ne to karki damu ni zan sanar da shi a yau isha'allah. kuma na gode sosai da sake karbana da kikayi. allah ya barmu tare._
_Yana gama tura wannan sai ya fito ya shiga massage na wayarsa ya rubutawa husaini sako.

" aboki fatan ka tashi lafiya kana inane? jarabar yasmeen fa ta kara yawa dan haka ina tunanin kara aure cikin wannan watan. ina fatan zaka sa al barka._



_jimawa kadan sai ga massage ya shigo. komai nml. baka zo office dina ba to a ina zaka ganni. nayi farin ciki sosai da jin wannan zan cen kace zaka dawo mai sim 2 ni kuwa har yanzu ina no sim ko.😀 to shikenan amma gaya min wace ce?"_



_Al ameen yace to fa anzo gurin. da ya yanke shawarar kin gaya mishi. kuma sai ya tuna da cewa barin kashi a ciki baya maganin yunwa. yace gwara in sanar da shi kawai ta fanjama fanjam._




"_Ba wata bace illah kanwarka zee. wato a gaskiyar zance muna san junan mu. tsakanina akwai soyayya mai karfi wacce ada ni da wasa na dauke ta amma ynz ta rikide ta dawo SON GASKIYA_.🔜"


_yana rubuta haka ya tura kuma ya saka wayar a airplane domin ji yayi gabansa na faduwa. baisan wace irin amsa husaini dai dawo da ita ba fitowa yayi ya kulle office din ya koma can wani part na cikon hospital din ya labe domin yasa tabbas husaini sai yazo.
Husaini yana karanta sakon yaji wani iri. me wannan ke nufi?. kanwata Zainab kenan. no bazan taba bari hakan ta faru ba. yarinya mai ilimi kai kuwa da ko fatiha aka turke ka baka iya kawowa_.

_a fusace husaini ya fito ya nufi office din al ameen. a garka me da kwado ya iske_ shi.............................................................................;;



Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks





✍🏼Autan marubuta ✍🏼



👑King boy👑

























🙎🏿☠ MIJIN ALJANAH ☠🙎🏿


page 128 - 129


|
|
na king boy isah👑
|
|
__________________________
🌟ZAMANI APR 2017 🌟
|_________________________|




***** zamani *****
🌟ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION 🌟 ©Z.W.A
***** zamani *****







. _*DEDICATED TO UR|„> AUNTY NA FATIMA USMAN (MMN ALI)*_ 👍🏽 THANKS d like and support me. allah yayi albarka


🤔🤔🤔😰 KUYI HAKURI KUNJI NI SHIRU TO WLLH ALHAJI NETWORK NE YA TSARE NI 😰



Kursiyya

Please Login or Register in order to submit comment