Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a cikin wannan halin da yanayin ta gama takabar,sai dai duk da hakan ba tayi yunkurin fita fara wani aiki ba....









Sumy luv😍😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬









Written by SA'ADATU WAZIRI GOMBE







Copied by SUMAYYA SA'AD❀❀









36



Bayan rasuwar Mislihu Alh. Umay ya samu labari don haka ya zo ya dauki Deeni bayan ya farfado ya samu sauki na jiki amma fa kwakwalwarsa tamkar ya farka da sabon abu ,kullum yana cikin firgita da yin wasu abubuwa tamkar yana tsorace.

Haka mahaifinsa yasa ana yi masa addua su ma suna masa ,har ya dan samu sauki,amma kam har yanzu da matsala . Yayin da kotu ta yankewa Dr. Yasir da sauran ma'aikatan asibitin hukuncin daurin rai da rai. Allah ka tsare mu da son zuciya..





Asibitin ya tsaya na dan wani lokaci saboda abunda ya faru da gidan da asibitin duk sun shia gado ,sai dai dama asibitin nasu ne su biyu da shi,sannan itama tana da gadonsa. A takaice dai wurin ya dawo nata da danta Muhammad ,wanda tayi alkawarin kula masa da shi ta damka masa kayansa wataran in tana da rai. Don haka ta shirya komai a rubuce saboda mutuwa ta kuma nemi lawyer na musulunci da Alkali suka zama shaida.



Watanni shida da rasuwar Doctor Mislihu bayan gama takabarta ta hau shirye-shiryen yadda zata farfado da asibitin yafara aiki,ya dawo kamar da,a niyyarta ma har yafida,saboda tsaro da tantance ma'aikata sai yafi nada.

Bahijja kenan mace mai kamar maza,haka ta dage tana ta shige da fita ba zama ,tana neman taimako da yadda zaayi komai ya farfado ,wanda gudun tunani da bacin rai yasa ta dage da zama(busy) yau bata nan gobe bata can har sai da ta tabbatar komai ya dai daita mata kamar yadda takeso ,komai ya farfado ya soma aiki,sannan ta samu nutsuwa kadan.



A kullum ta zauna maganar Deeni ke fado mata,da sakon da amanar taimakonsa da mijinta ya damka mata.

"Ya zama dole in nemo shi inji ya ya kare ? Sannan in sake duba (case) dinsa inga wane irin (treatment) ya kamata a masa."

Bata bata lokaci ba ta fara binciken file din Deeni wanda ta riga da dama tasan wannan case din,sai kari akan (wrong treatment ) din da aka yi ta masa.

Nan ta bincika address dinsa,sannan ta sake zuwa asibitin da aka kwantar dashi tare da Doctor ta sake bincike akan treatment dinsa ,sannan ta sake tabbatar da address dinsa. Daga nan ta daura damarar niyyar taimakon sa har sai inda karfinta ya kare,in ta tabbatar ya samu lafia zata samu kwanciyar hankali ,burinta da na mijinta ya cika,daga nan zata ci gaba da cika burin mijinta da nata har ta Allah ta kasan ce akanta,idan kuwa Muhammad ya girmata damka masa dukiyarsa,ta ci gaba da masa addu'a da shi da mahaifinsa. Wannan shi ne burin Doctor Bahijja da kuma kudurinta ,bayan shi ba komai a zuciyarta da tuaninta ,daga aikinta sai rubuce rubucenta.....





Hmmmmm ,,Doctor MISBAH KENAN





Please kuyi hakuri aiki ne yamun yawa πŸ™πŸΌπŸ™πŸΌπŸ™πŸΌ







SUMY LUV 😍😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬









Written by. SA'ADATU WAZIRI GOMBE











Copied by. SUMAYYA SA'AD❀❀





37





Haj. A'i na zaune a falo ita daya tayi nisa sosai a tunani,tana tuna yadda rayuwarsu take da da ta yanzu,lokaci guda rayuwarsu ta canja ,sun baro yankin su cikin 'yan uwa da abokan arziki,inda suka saba da rayuwarsu da komai ,sunyi nesa da dansu da 'yan jikokinta guda biyu da duk da suna zuwa lokaci-lokaci,ga rayuwar Deeni ta canja gaba daya . Duk kokarin da suke yi akan Deeni ba wani canji,yadda Deeni yake rayuwa yana matukar kona mata rai. Lukman ne take dan gani taji dama- dama,shima tunda ya kammmala katarunsa na jami'a kullum yana tare da mahaifinsa wurin harkar kasuwancin sa,rayuwar su na cike da kewa da wani walwala.

Mai musu aiki ce ta katse mata tunanin,'"Hajiya kna da bakuwa".

""Wacece haka ? Daga ina take ?

Gata nan ." Ta bata amsa,sannan ta juya.

Bahijja tayi sallama tare da karasowa cikin falon, Hajiya ta amsa tana mata maraba tare da mta kallon rashin sani.

Bayan sun gaisa Bahijja ta kalleta,ta ce.

"Nasan zaki yi mamakin ganina,saboda baki sanni ba. Sunana Doctor Bahijja ,ni likita ce a asibitin da aka kai Deeni kwanakin baya,asibitin doctor Mislihu . Ni matarsa ce da muke aiki tare ,bayan rasuwarsa ni na ci gaba da kula da asibitin.

Kafin ya rasu burinsa ne ya ga ya taimaki Deeni,sai dai burin nasa bai kai ga cika ba ta Allah ta kasance akan sa. Ina fatan cika masa wannan burin don haka nake son taimakon Deeni da dukkan kokarina har dai naga ya samu lafiya.

Bama bukatar taimakon ki""""".

Sukaji muryar Alh. Kamar daga sama .

Dukkansu suka mai da kallon su kan Alhaji,ya ci gaba da fada.

"Yau ce rana ta karshe da zaki sake tako gidan nan ,kowa yasan irin yadda ku ka kara dagula rayuwar Deeni,ku ka yi wasa da lafiyar sa. Ku godewa Allah da banyi kararku ba.

Cikin sadda kai da girmamawa Bahijja ta ce.

"Alhaji dukkan mu ba wanda yaso abinda ya faru,kuma bamu yi haka da ganganba sai don wata kaddara da ta fada mana. Burin mu ne daga ni har marigayi maigidana mu ga muna taimakon mutane,haka taimakon danka yana daya daga cikin burin,don haka nake me rokon ka da ka kara bamu dama ,insha Allah zamu yi kokarin mu akan danka ya samu lafiya.

Alhaji dai ya dage Bahijja ma ta dage da kyar da kyar ta sha kansa ya yarda ,sai dai ta dinga zuwa duba shi har gida . Bata musa masa ba saboda tana son taimaka masa,don tasan an musu laifi ,sannan zata karasa abinda mijinta ya fara kamar yadda ya UMARCE ta.









Hajiya ce tayi mata jagora har zuwa bangaren Deeni,ta nuna mata kofar dakinsa. Nan ta cewa hajiya ta koma ita zata shiga. Hajiya bata musa mata ba ta juya,ita dai addu'ar ta Allah ya bawa danta lafiya.

Tura kofar dakin tayi wanda yake mamaye da duhu,duk da rana ce amma ya rife ko ina kif. Yanayin garin kuma dama inba a kunna wuta ko bude windo ba babu ta inda haske zai shigo. Hakan yasa ta kara bude kofar don taga haske,nan ma ta hango window din dakin.

Kai tsaye ta nufi window din ta sa hannu ta zuge labulen tare da bude (windows) din daki duka ,tuni haske da wani irin iska mai sanyi ya dinga ratso dakin,nan ta maida kallonta gare shi ,yana zaune tsakiyar gado kamar kullum ya hade kai da gwiwa yana kife wuri daya.

Cikin nutsuwa ta matso gare shi ta tsaya tana kallon sa tare da nazarin halin da yake ciki . Kamshin turarenta tare da iska mai sanyi ne suka soma ziyartar sa,wannan ya dawo da shi daga wata duniya da ya fada.



Assalamu Alaikum Nuraddeen ". Ta fada cikin sassanyar murya.

Jin murya da bakon yanayi yasa shi dago kai suka hada ido,tayi masa murmushi ,shi dai kallonta yake.

Ta sake kiran sunansa,"Nuraddeen ,na maka sallama baka amsa ba,kasan kuwa shaidanun mutane ne kawai ba sa amsa sallama ? Kai kuma nasan ba ka daya daga cikin su,kai salihi ne,bawan Allah(you re a gentleman) nasan nan gaba in na shigo zaka amsa sallamata. Ni sunana Doctor Bahijja,amma zaka iya kirana da Bahijja . Ni sabuwar kawarka ce,abokiyar ka,naji baka da aboki haka kake rayuwa kai daya,nima bani da kawa don haka na cewa hajia me zai hana mu zama abokan juna ni da kai,? Ka fadamun damuwarka ,in fada maka nawa,mu bawa juna shawara. Ina fata zaka amshi abota ta ?

Kallonta yake fuskarsa daure,sannan da alamar mamakin ganinta duk da yana jinta amma bai kulata ba ,daga karshe ma ya kau da kai daga gareta saboda Allah Allah yake ta fita ta bashi wuri,saboda ba abinda yafi kauna irin ya zauna shi daya ya fada wata duniya daban wacce take da bambanci da wacce mutane ke rayuwa.

Ganin ya juya kai yasa ta sake zagayawa ta fuskance shi,ta ce.

" Hakan na nufin baka amince da abota ta ba? Duk da baka amince da ni ba ni dai ba zan fasa zama abokiyarka ba,saboda Niraddeen shj kadai ne abokin da nake so nayi a duniya,saboda daga ji da ganin Nuradden (is special) .

Zan fara aikina daga yanzu kafin ka amince,shawara ta farko ka dunfa barin ( freash air ) yana ratsowa cikin dakinka,zai baka (good company) kuma zai kara maka lafiya ( it will keep u healthy nd cheer you up).

Na biyu,ni bana abota da kazamai,wannan dakin da kake zaune cikin kura ga kayanka a zube (,toilet )dinka datti,kai baka gyara ba,sannan ka hana a gyara maka. To in kanaso mu zama abokai sai ka koyi tsabta,kasan mu likitoci bama shiri da kazamai,din haka ka tuna kai abokin likita ne." Tana maganar tana tattara dakin.

Ba shiri ya dazo kai yana kallonta,da ta ishe shi,yaji ranshi ya baci,ya mike a zuciye ya fisgi hijab dinta,yaja ta har kofar ya cillar ,fuska murtuk yace.

"" Waye abokin ki ? Bana son kowa,bana bukatar kowa arayuwata ,bana son kowa,ina so in rayu ni kadai,in kika sake zuwa nda nake zan kashe ki.

Bata yu mamaki ba ,dama ta zaci haka daga gare shi...

Murmushi ta masa,tace," Shi yasa nake son ka zama abokna,zan dawo gobe in Allah ya kaimu sai ka fada min damuwarka (and yes ) bana so in dawo in same ka da kazanta,ka tabbatar da kayi wanka."

Rufe kofar ya yi da kardi ,ta jima tana tsaye tana kallon kofar,yayin da kwakwalwarta ta shiga zarya tana tunanin ta hanyar da zata bullo masa har taja ra'ayinsa.

Alama ta farko ta nuna mata yana cikin fushi da zafi ,na biyu kuma kamar yana cikin wani fargaba. Na uku ,alama ya nuna ya yanke kauna daga dukkan wani farin ciki da rayuwar duniya. Wannan ya nuna rauninsa akan addini a zahiri.

Ta jima tana nazari kafin ta juya ta samu Hajiya tana kaiwa da kawowa alamar jiran fitowar ta kenn,tana ganinta kuwa ta nufi wurinta da sauri. "

""Likita yaya kika ganshi :?

Bahijja tace,"kwantar da hankalinki Hajiya ,zauna zan miki bayani"".



Ta ce,"Insha Allah Deeni zai samu lafiya,zai samu sauki. Sai dai sai na danyi fama da shi,saboda na lura mutum ne me zafin zuciya da zafin rai,sannan yana tattare da wani fishi da bacin rai a tare dashi...

Sannan akwai wani (memories)* a kwakwalwar sa da yake son shafe su,ya mance da su. Yana so ya shafe wani bangare na rayuwar sa a baya wanda suke masa ciwon gaske. A kokarinsa na wannan yasa kwakwalwarsa ta kamu da ciwo ,rashin lafiya. Ba wai hauka yayi ba,kamar yadda Kai, ko zuciya ,ko ciki suke yyiwa mutum ciwo a jikinsa, haka kwakwalwa ma tana ciwo wanda dole sai ya sha magani zai samu waraka da yardar Allah. Sannan kuma ya kaucewa wannan tunanin.

Na biyu ,matsayinsa na musulmi ya samu rauni,na uku, na lura yana da matsala da duk wata dangantaka a duniya wanda ya jawo yasa ya tsani kowacce irin dangantaka ,har yasa baya kaunar kulla dangantaka kowacce iri ce da kowa ,yafi so yayi ta rayuwa shi daya.

Don haka Hajiya deeni na bukatar taimako kwarai wanda zan yi iya kokarin nayi,sai dai ba mai sauki bane. Mutum ne mai taurin kai da zafin zuciya ,tankwara shi ko juya shi abu ne mai wahala. Ina son jin tarihin deeni kakaf da ainihin shigar sa wannan halin ,saboda in san ta ina zan soma bi in taimaka masa..

Hajiya ta ja dogon numfashi ta kalleta ido cike da tsammani ,tace.

"Zan fada miki komai,tabbas Deeni danmu ne amma bamu kyauta masa ba ,bamu masa adalci ba. Zan baki dukkan wani hadin kai da kike nema domin inga dana cikin walwala............











Please nagaji wlh ,,kuyi hakuri se da safe............













Sumy luv😍😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬









Written by SA'ADATU WAZIRI GOMBE









Copied by SUMAYYA SA'AD❀❀







38





Deeni mutum ne wanda yake (full of life)kullum yana cikin dariya da zolaya gami da kyautatawa kowa,duk da yana fmda zafin rai yana da zuciya da fushi da kuma ra'ayi amma yana wuyar gaske ka fahimci haka,saboda kullum yana cikin wasa da dariya.

Duk wani abu da deeni yake so mu ba shi muke so masa ba,don haka muka sa shi yin abinda muke so musamman mahaifinsa ya danne abinda yake so yana yin abinda muke so saboda biyayya. Sun sha samun sabani da mahaifinsaakan abu da yawa ,amma daga karshe zai hakura yayi abinda mahaifinsa ke so.

Deeni bashi da rauni a addini,asali ma sanin addini yasa shi yi mana biyayya duk da mun fi ba da karfinmu ga neman ilimin duniya shi da kanss ya dage da neman lahira,don haka anan mu muke da rauni ba shi ba.

Ya yi amfani da iya ilimun da ya nemawa kansa na addini ,yana kokarin neman ilimin ne kuma muka raba masa hankali tare ds daga masa hankali akan karatun jami'a ,din haka ya qatsar ya koma bokon.

Raunin Deeni guda daya ne a rayuwa FARIDA."

Sai a lokacin Dr. Bahijja ta ce wani abu tunda ta fara magana ,ta ce.

"Farida ?""

Mama ta girgiza kai ,tacd ,"kwarai farida,in akwai abinda Deeni yake so a rayuwa da muradi a rayuwarsa to farida ce. Dukkan ZURI'AR mu ba wanda bai san da haka ba,tun yana yaro har ya girma ya mallaki hankalin kansa,abinda yake so daya ne Farida,ita ce rauninsa..........



A hankali Hajiya ta labarta komai tun daga farko har karshen abinda ya faru.

Bahijja taji jikinta ya yi sanyi,ta matukar tausaya masa sosan gaske.

"Allah sarki bawan Allah." Ta fada tana kallon mama .

" Tabbas ba ku kyauta masa ba ,mahaifansa ,dan uwansa da masoyiyyarsa,tabbas wannan cin amana ne mai girma,dole ya ji dukkan wata dangantaka ta fita ransa.

Tabbas ya yi kokari ma da ya tsaya a haka,Deeni jarumi ne,na jinjna masa,kuma Nsha Allah zan taimaka masa ya fito daga cikin wannan kejin ya zo yayi rayuwar sa kamar kowa.

Kila da mutuwa farida tayi,zai iya daukar kaddara ya jure, da farida ce masa tayi Deeni bana sonka wani zan aura zai jure ya hakura,amma wannan abinda ku ka masa ya masa ciwo wanda ciwon da cin amanar shi yafi zama a zuciya da kwakwalwar sa fiye da Farida.

Yana jin cewa iyayensa basa son sa,ba sa kaunar sa,sun ci amanar sa. To in iyauenka za suki ka su ci amanarka zaka dinga jin to kai ina zaka shiga ? Ya zaka yi da rayuwarka ?

Abinda ciwo matuka,zaka iya jure tsana da kiyayyar kowa amma ban da mahaifanka,saboda mahaifanka ,'yan uwanka su ne kai,su ne rayuwarka.

Abinda Deeni yakeji, ciwon da ke cikin cikinsa da ni daku duk ba zamu iya sani ko fahimta ba sai shi sai Allahnsa. Ina fata Allah Ubangiji ya bashi lafiya,ya bani iko da taimakon iya taimaka masa,ya cire masa wannann ciwon da ke zuciyar sa."



Ta mike ,'Ni zan wuce ,zan dawo gobe in Allah ya kaimu . Sannan zan ci gaba da bincike akansa daga gare ku,da fatan zaku bani hadin kaii""

Mama dake sharar kwalla ta ce,"insha Allah za muyi duk abinda ya kamata ,mun gode "

Nan sukayi sallama ta tafi.



Alhaji dake tsaye yana jinsu hankalinsa ya matukar tashi,tsananinnadama ya kara shigarsa,tausayin dansa ya kama shi. Ya iso falon hankalinsa a tashe ,ya kalli hajiya.

" Ki yafe mun abinda na miki ,abinda na yiwa danmu ban kara fahimtar illar da na yiwa yara na ba sai yanzu.

Hajiya tsayawa tayi tana kallonsa,don kuwa a tsawon shekarun da sukayi na aure bai taba budar baki ya bata hakuri ba komai girman laifin da ya mata,haka bai taba nadama akan wani abu daya zartar don ra'ayinsa ba ....



***** ***** *****



Washegari karfe sha daya ta nufo gidan,bayan ta gama zagaye marasa lafiya a asibiti.

Kamar yadda ta same shi jiya haka ta sake samun sa a yau,hannunta rike da tray.

" Asslamu Alaikum Nuraddin"

Dago kai yayi ya kallera ya watsar,ta kalle shi ta girgiza kai..

*Ka.manta me nafada maka jiya? Ka dinga bude (window) ,kaga yau ka kara min aiki,dole in dinga zuwa bude maka (window ) tunda ina son abokina ya shaki iskar duniya.""

Nan ta zage komai kamar jiya ,sannan ta zo ta hada (coffee) ta mika masa. Ko kallonta bai yi ba balle ya karba,ya dage kai...

Bata hakura ba ,"kayi kokarin sha (I'am a very good coffee marker ).oh na gane ,ko sai na sa maka a baki ne ?

Nan tayi kokarin kai cup din bakinsa,ya yi saurin doke hannunta sai da cup din ya fadi kan tiles ya kashe har ruwan coffee din ya dan kona ta.

""Auchhhh!!! Tayi kara.

'"" In ba zaka sha ba meye na bigewa ? Kaga yanzu ka kona ni, ( u re such a bad friend ) ""

Har yanzu bai kulata ba,nan ta hau tattara glass di. Da ya fashe,bata ankara ba kuwa ya yanke ta. Ga mamakinta ta ga ya mike ya dauko (first aid box ) yayi dressing wurin ..

Ra jima tana kallonsa tana mamaki ,saboda bata zaci hakab ba.

Ya kalleta fuska a murtuke ," Wai me kike so ne gare ni ? Na ce miki bana son ganin kowa a inda nake,bana bukatar wata DANGANTAKA !!!!

ya fada cikin tsawa da huci..

Kinji ciwo saboda ni,ban so,don haka kar ki sake kuskuren zuwa inda nake.""

Da karfi ya fisgeta zai yi waje da ita ,sai yaji kansa yana wanj irin sarawa ,yana masa azabar ciwo . Nan ya saketa ya rike kai yana nishin azaba tamkar mai shirin barin duniyar....

Hankalinta ya tashi ,tayi saurin ciro wasu allurai guda uku a cikin jakarta tayi masa a hannu,ta taimaka masa zuwa gado ya kwanta,bacci mai karfin gaske ya dauke shi. Ta jima tana zaune tana kallon sa cikin damuwa da tausayawa,sannan ta mike ta karasa abinda take yi a dakin ,sannan ta fita.



Haka Bahijja ta kasance kullum sai ta zo gidan du Deeni duk da baya son hakan,baya kulata,haka zata yi ta masa surutu tana masa hira,har ya soma sabawa da hakan.wataran cikin dabara zata dinga jefa masa magani cikin (juice) ko abinci.

Ganin har yanzu bata samu yadda take so ba tsawon qata uku amma Deeni ba shi da niyyar canjawa,don haka tayi niyyar sake canja salo,ta cewa hajiya tana son zuwa har kaduna gidansu Deeni inda ya zauna da inda ya yi rayuwa ,sannan tana son ganin farida don mata wasu tambayoyi akan deeni.

Hajiya tace,'Da zai yiwu da na rakaki,to amma ba inda zan iya rafita in bar Deeni,don haka zan yi waya in sanar da su Shamsu zuwanki,zan baki cikakken (address) ba zaki fuskanci matsala ba insha Allah ".

Ta mike ,"Na gode Hajiya da yarda da kuma hadin kai da kike bani."

Hajiya tayi murmushi tace ," Nice da godiya,ba abinda zan miki sai addua,Allah ya ska miki da lakhairi"".

Sn rabu akan zata yi kwana biyu kafin ta dawo...



**** ***** ****



Kwance yake yana ta juye-juye a gado ,ya rasa me ke masa dadi,tun dazu yake sauraron zuwanta amma shuru. Ya riga ya saba da tana zuwa kullum dai dai wannan lokacin,amma yau har yamma shuru..

Nan ya mike ya zuge labulen dakin kamar yadda ta saba masa,nan ya dinga kaiwa da komowa . Can ya bude kofar dakin ya fita abinda ya jima bai yi ba tunda ya dawo daga asibitin yana nan a cikin dakinsa.

Hajiya na tare da Alhaki a falon kawai sukaga Deeni bazata yana leke-leke ,a tare suka mike cikin mamaki ...

" DEENI"

Suka kira sunansa a tare.

Ya kalli Hajiya yace ,"Mama ba wadda ta zo gidan nan yau?"

Kallon sa take da mamaki ,ta jima sosai rabon da taji Deeni ya kirata balle.magana,kuka zatayi ko dariya? Ta rasa.

Bai bata amsa ba ya koma ciki ya tuea kofa ya kwanta,kwanciyar da yaji bata masa dadi ba ,ya mike ya nufi bakin window ya tsaya yana kallon motoci dake wucewa bisa titi..........





Se anjima jama'a



Taku har kullum...





Sumy luv 😍😍😍😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬









Written by SAADATU WAZIRI GOMBE









Copied by SUMAYYA SA'AD❀❀







ASTAGHFIRULLAH WA'ATUBU ILAIK

Allah kayafe mana kura-kuranmu,,,,Ameen





39



Zaune take a falo tana jiran isowar masu gidan,yayin da take kallon yadda aka tsara ginin gidan da yadda aka tsara falon.

Farida ta iso tare da 'yan yaranta guda biyu suna ta tsalle-tsalle Deeni karami da Aisha,ta tarbi Bahijja cikin fara'a ,itama ta amsa tana daria ,suka gaisa.

Deeni karami ne ya gaisheta,ta amsa tare da jawo su tana musu wasa da dariya ,tana tambayarsu makaranta suna bata amsa.

Farida ce tace,to maza a je ciki ayi wasa a barni zanyi magana da Aunty ko?

Nan sukayi ciki sannan ta maida kallon ta ga Bahijja tace,

"Hajiya tamun bayanin zaki zo,sai dai bata fada mana ko mene ne ba "

Bahujja tayi murmushi tace," Abu me muhimmanci ke tafe dani,sunana Doctor Bahijja,kamar yadda na fada miki ni likitar Deeni ce.

Jin sunan Deeni yasa fatida taji zuciyarta ta tsinke,hankalinta ya tashi. Nan da nan Bahijja tayi mata murmushi.

Keantar da hankalinki,ba wani abu me wahala yake tafe dani ba,illa iyaka inaso ki tainake ni in taimaki Deeni. Inaga wannan shi ne iya abinda zaki iya masa ki taimake shi shima yaci gaba da rayuwa kamar yadda kika ci gaba da naki rayuwar.."

Kanta sunkuye jiki ba kwari tace,"A shirye nake da in baki ko wani irin taimako ,zanyi farun ciki in har akwai taimakon da zan iya wa Deeni."

Bahijja tace ,"Naji dadin hakan ,ina so ne ki fada min komai akan Deeni ,ina nufin ,halayyarsa,me yake so ? Meye baya so ? Banda wanda nasani ,a ganina kece mutum mafi kusa da Deeni,wacce tasan kananan abubuwa akansa wanda wasu ba za su sani ba. Komai ina son sani,me yafi sashi farin ciki,? Ya yake rayuwar sa? Kamar ( hobbies ) dinsa ,wane abinci yafi so ? Wanne yanayi yafi so? Me yafi sa shi nishadi da farin ciki ?

Farida tayi shuru ta fada duniyar tunani ,rufe ido tayi tana tuno komai a game da shi,tana tuno wasu yanayi da suka yi tare a da.

Ta bude ido jikinta a sanyaye tace,tashi mu shiga ciki"

Nan ta ja ta sama zuwa bangaren da Deeni yake ,ta bude mata dakinsa,ta kunna wuta haske ya bayyana ,ta ce.

Ga dakin Deeni wanda ya shirya shi da hannunsa,ina ga ganin wannan ko ban fadi ba zai fahimtar dake ko wanene Deeni.

Bahijja tayi murmushi tace,"Kwarai ddakinsa ta bayyana shi a zahiri,daga (study room) dinsa na fahimci Deeni mutum ne me son karance-karance."

Farida tayi dariya,"Kwarai yana son karance-karance da binciken takardu tin daga kan na Addini har na boko.

Deeni ma'abocin ilimi ne ,ma'abocin soyayya. Yana samun farin ciki a kananan abubuwa,mutum ne

Please Login or Register in order to submit comment