Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Waya nace masa Baba zan yi aure ,ya ce in kawo duk mayar da nakr so a duniya zai aura min ita,na ce masa na samu mata,na samu uwar 'ya'yana ,Doctor Bahijja,Abokiyata kuma likita ta. Ya taya ni murna ,ya min alkwarin mallaka myn abinda nake so ko menene shi indai bai fi karfinsa ba.

Na ce masa bana son komai sai Bahijja 'yarsa ce,shi babanta ne,'yarsa nake so ya aura min. Na masa alkawarin rike masa ita da amana,don haka yau mamanki da babanki zasu tambayeki wa kikeso? Ina fata zaki fito musu da gwaninki..

Kalamansa sun ratsata,kuma sun mata dadin gaske,wanda bata san yaishe ta fara hawaye ba. Tun tana 'yar karama take buri da sha'awar ta ga soyayyar uwa da uba,ta ga kauna da gata daga iyaye kamar kwacce yarinya ,amma ta san wannan burin nata ba zai taba cika ba. Muslihu ya so ya cika mata wannan burin ,sai dai hakan bai samu ba...

Bata san yaushe ta kifa kanta bisa hannayensa ba tana kuka..

"" Deeni ka gama min komai a rayuwa"""

""Burina kenan Bahijja in faranta miki,inga na cika kowanne irin buri naki karami ko babba,duk da ke din ba mai buri bace."

""Burina guda in mallaki Deeni da zuciyarsa "

Yayi mata murmushi,"Burinki ya cika my dear,ina jin dadin yadda kike sona Bahijja ,yadda kike nuna damuwarki da kulawarki a gareni.. Ina bukatar wannan har karshen rayuwarta..""

" kasamu Deeni,soyayyata da kulawata naka ne"

Yayi murmushi ,"Nagode ,anjima Mama zata zo ta tafi da diyarta gida don mata shirye-shiryen aure,saura kadan Abokiyata ta zama amaryata..""

Murmushi tayi tare da boye fuska saboda kinya ,musamman da ta ga irin kallon da yake mata.......





**** **** ****



Da yamma Mama ta zo ta tafi da Bahijja tare da Baba Andi can gidansu Deeni,duk da tana jin wani iri da nauyin Mama amma ta daure sabodaDeeni..

Mama ta lura da haka,don haka tayi kokarin kawar mata da nauyin da take ji,ta ce.

"Bahijja ke diyata ce,soyayyar da kike wa Deeni shima yake miki ya sani sonki da kaunarki kamar 'yata. Ina godiya ga Allah da ya kawo ki rayuwar Deeni,don haka saki jikinki nan gidanku ne,zan miki duk wani abinda uwa zata yiwa diyarta ko shakar haka kar kiyi..""

Alhaji ya shigo yana jinsu ,shima ya matso ya ce.

Haka zan miki duk abinda amahifi zai yiwa 'yarsa Nsha Allah""

"" Na gode Baba "

Ta fada kai sunkuye yayin da taji hawaye na kokarin ciko idonta,wani feelings ne da bata taba jin irinsa ba,wani irin farin ciki na daban taji yana ratsa ta..

Allah abin godiya ,Allah mai kyauta da kari,ya bata miji da iyaye lokacin da bata zata ba balle tsammami....

Alhaji ya zauna gefen Mama ,ya ce,"Bahijja wane lokaci kika ga ya dace mu tsaida ranar aurenku?

Kanta sunkuye tace,"Baba ai ku iyayena ne,duk ranar da kuka ga ya dace ku ka tsayar dai dai ne.." Alhaji yace ,"To Allah ya miki albarka,ina so zan hada airen ku tare da lukman ,shima ya samu matar sa,sai mu hada muyi nan da sati biyu masu zuwa. In mun hada ku mun hutar da 'yan uwa masu zuwa daga nesa sau biyu,tunda mun shirya sai mu hada""

To Baba ,tafada kai sunkuye.

"To Allah ya miki albarka."

Nan ya mike ya fice,mama ta kalleta ta ce,

"To diyata zata zama amarya sai an bawa asibiti hutu ko saboda a bawa jiki hutu da nutsuwa""

Tsananin kunya yasa Bahijja kife kai,Mama na dariya ta ce.

"Na fada miki ni mahaifiyarki ce.."

Deeni dake tsaye yana kallon su ya tsinci kansa cikin wani irin tsananin farin ciki da jin dadi ,son mahaifan sa da kaunatsu yaji yana kara kardi a zuciyarsa.

""Zan mallaki Misbah na nan da sati biyu Nsha Allah."



A sati biyun nan mama tayi hayar masu gyaran amarya na musamman suka sa Bahijja gaba da gyara baji ba gani..

Mama ta fahimci nauyinta da Bahijja ke ji,wanann yasa ta damkata a hannun masu gyara da kuma aminiyarta Haj. Amina da tazo bikin da kanwarta...

Ya zame mata dole tayiwa matar Deeni gyara,Deeni gudan zuciyarta ne,zata iya komai don farin vikinsa,tunda Bahijja ce farin cikin Deeni ba zata yi wasa da ita ba...

Lokaci guda Bahijja ta canja,rayi wani irin kyau da haske me ban mamaki ,ta dawo tamkar wata Balarabita,duk inda ta wulga sai kaga tamkar anyi walkiya saboda tsabar haske da kyau da daukar ido da take ...

Deeni ya kasa daga ido akanta duk inda tabi yana binta da idanunsa,yana jin alfahari da samun mace irinta. Tabbas Bahijja ta ishe shi har iya karshen rayuwarsa,bashi da bukatar wata mace ......



Ana saira kwana uku biki 'yan uwa da abokan arziki suka cika gidan wanda musamman Alhaji ya tura ticket na jirgi wa mutanen gombe da kaduna don zuwa bikin dan gatansa.

Daya bangaren na gidan aka warewa baki,yayin da bangaren su Hajiya sai aminiyarta da kanwarta tare da su farida da mahaifiuarta.

Dakin Deeni shi ua koma dakin Bahijja shi kuma ya koma gidansa na farm house sai dai kullum yana makale tsakanin idonsa kan Bahijja ,bai iya jure rashinta ko na kankanin lokaci...

Bahijja ta kasa gasgatawa kanta sabuwar duniyar da ta tsinci kanta,gata da kauna da take gani gun mahaifiyar Deeni da 'yan uwansa kadai ya isheta farin ciki,ballantaan kuma uwa uba Deeni..



Bayan sallar juma'a jama'a da dama suka shaida daurin aurwn Deeni da Bahijja ,aure yayi albarka,dumbin jama'a ne suka cika a daurin auren. Bayan nasu aka daura na lukman da Amaryarsa Abida,duk a masallacin juma'ar unguwarsu aka daura...

Bayan daurin aure Mama ta shirya walima ta musamman ,abinci ba irin kalar da babu tun daga gargajiya har turawa. Wajen ya tsaru soaai,an gayyaci malamai mata masana da kuma 'yan uwa da kowa in ya ci abinci ya tofa albarkacin bakinsa.....







Ina kuke FANS din Dr Deeni Da Dr Bahijja πŸ—£πŸ—£πŸ—£πŸ—£ranar da kuketa jira yau gata ta zo.......











SUMY LUV😍😍😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬









Written by SA'ADATU WAZIRI GOMBE









Copied by SUMAYYA SA'AD❀❀







48





Haka a wajen Alhaji ya shirya nasa da maza abokai da yan uwa a waje,kowa ya ga Deeni wannan rana yasan yana cikin tsananin farin ciki. Wannan ya kara kayatar da kyan fuskar sa.



Cikin gida a daki Bahijja ta sha kwalliya da gayu sosai,duk da shiga mai sauki tayi,doguwar riga mai tsadar gaske ta sa wanda Mama tayi mata order daga Dubai. Blue ce ammata kwalliya mai sauki da fararen duwatsu,ya matukar karbar fatarta mai haske ,haka ya dad fito da kwalliya fuskarta. Ta tufke gashinta baki mai tsayi da sheki tare da lulluba gyalen rigar ,ta sa cover shoe masu tsadar gaske da ya yis shige da irin dressing dinta,ta sa bracelet mai saukin kwalliya tare da zobuna guda biyu wanda suka yi matukar kayatar da dogayen yatsunta.

Bahijja macece doguwa mai kyakkyawar kira,shigar da tayi tai matukar kyau da bata taba ganin tayi ba ,sai kamshi take.

Mama ta shigo ta ganta ita kanta tayi bala'in mata kyau,ta dinga ganin duk yawan taron nan ba kamar surukarta Bahijja ,tabbas ta amsa sunanta matar Deeni.

Tayi murmushi,"Tabbas diyata tayi kyau"

Tace,"Bari inje zan turo wacce zata zo ku tafi tare wurin walimar,duk an gama taruwa""

Ita dai Bahijja kanta sunkuye har mama ta fita,shuru taji gidan yayi alamar duk an fits wurin walima. Tana nan zaune shiru zuciyarta cike da tunani kala kala taji motsin shogowa. Kamshin turarensa ya tabbatar mata da Deeni ne ya shigo dakin,nan tayi saurin daga kai suka yi ido biyu,yana mata wannan murmushin..

Ya zuba mata idanu,itama ta kasa dauke idonta a kansa,yayi mata kyau sosai. Sanye yake da blue shadda kalar nata kayan ya sha aiki,shigar ta matukar masa kyau. Hular da ya kafa a kansa ta kara fiddo da kyan fuskarsa,gashin kansa kwance irin na fulani sak,ga sajen da ya karawa fuskarsa kwarjini da annuri...

Ji tayi tamkar ta je ta fada kirjinsa ta kwanta,amma sai ta kasa saboda kunya duk da yana mijinta. Shi yasa hannu ya jawo hannunta yana wasa da 'yan yatsunta,tsigar jikinta taji tana tashi tana jin sonsa da shaukinsa yana ratsa jijiyoyinta,yana bin jikinta.

" Haba MISBAH na ,ya zaki kawar min da fuska,amaryata ki tuna fa ke halal dina ce yanzu,baki san irin jin dadi da tsananin farin ciki da fuskarki ke sauke mini bane da baki kawar da kai gare ni ba . A yau sai naji soyayyarki ta zama sabuwa ,ta zama danya sharaf a zuciyata. Toho gareni,please Bahijja ko zan samu nutsuwa.."

A hankali cikin nutsuwa ta matso gare shi ya jawota jikinsa tare da bata kyakkyawar runguma,tuni ta bace a cikin jikinsa,suna manne da juna tare da jin irin son juna da sha'awar juna..

Cikin muryar rada yake mata wasu irin kalaman soyayya masu ta da hankali da tsuma zuciya da ruhinta.

Nagode Bahijja da soyayyarki,wannan shi ne (the most beatiful moment of my life)..

Rufe ido tayi jin kalaman sa na ratsa ruhinta,tana shakar kamshin sonta tare da fadin.."Deeni ina sonka ,kai nawa ne ni daya,mallakina ni daya.."

Haka ne Bahijja ni naki ne ke daya kamar yadda kike ke tawa ce ni daya,bana taba hada ki da kowacce mace a duniya,haka ba zan taba hada soyayyarki da kowa ba""

Sun jima a cikin wannan halin na tsananin shauku da son juna..



A hankali ta turo kofat tayi sallama amma shuru,hakan yasa ta kutsa kai,Farida kenn..

Gabanta yayi mummunan faduwa ,ya dinga bugawa da karfi ganin Deeni da Bahijja a hakan ya mummunan daga hankalinta.

Wani irin masifaffen kishi taji yana turniketa,masifaffen kyan da ta ga sunyi da Deeni da Bahijja ya razana ta tamkar dama an halicce su don juna ne. Tsohuwar soyayyar sa taji ta taso mata ta kasa gani da jure soyayyar da taga Deeni yana yiwa Bahijja wanda ita duk tsananin soyayyar da suka yi a baya ta dinga gani kamar wancan soyayyar wasa ce..

''Ya za'ayi Deeni yaso wata mace a duniya fiye da ita? Ya za ayi Deeni ya ci amanar kauna? (Readers kuji fa karfin ) Na zata Deeni zai yi aure ne ba don soyayya ba sai don raya sunnah kamar yadda nayi,ya za'ayi Deeni yaso wata fiye da ni ? Har yau ban taba son wani fiye da shi ba ,duk da nayi aure na zama uwa amma soyayyarsa bai taba barin zuciyata ba ko na second daya. Ya zanyi in rayu da wannan bakun ciki da bacin ran da na gani yanzu. ???(To jama'a farida na tambaya)....

Nan ta sake daga kai ta kalle su,har yanzu suna wata duniyar . Ta kalli kanta ta kalli Bahijja sai taga ta mata nisa,ta mata fintinkau nesa ba kusa ba...

""Shin ni ya akayi na kasa hada Deeni da kowanne irin namiji a duniya ? Tabbas saboda Allah bai taba hadani da namijin da ya kaishi bane,yayin da Allah ya hada Deeni da macen da ta fini."

Kau da kai tayi taji hawaye na zuba mata,tsananin kishi da son Deeni taji yana shigarta,ta macen da abinda ya kawota,ta mance da cewa ita matar wani ce,uwar wasu ce....

Karar wayarta ce ta dawo da su hayyacinsu duka,nan tayi saurin share hawayen yayin da Deeni da Bahijja suka ganta bazata a gabansu..

Ras !!! Bahijja taji gabanta ya fadi,ita ma din kishin farida taji ya shigeta,har yau in ta tuno irin soyayyar da Deeni da Farida sukayi sai taji hankalinta ya tashi...



Deeni ganin Farida a gabansa bazata tana kallonsa tamkar ta hadiyeshi yasa ya ji ya shiga dan rudani,musamman da ya san yadda Bahijja take da kishin Farida a zuciyarta,duk da ya sha nuna mata cewa Farida ba ta gabansa yanzu,amma ta kasa fahimta. Sam ko kadan babu ita a ransa,amma ya rasa dalilin da yasa yaji ya wani irin rudewa a wannan lokacin...

Bahijja na kallon irin rudewar da yayi yasa taji ranta ya mummunan baci,hankalinta ya tashi .

Dukkan su idon su ya rufe da wani irin kishi,musamman irin kallon da Bahijja ta ga Farida na yiwa Deeni. Yayin da Farida ta dinga jin kishin irin kallon da Deeni ke yiwa Bahijja...

Nan faridan ta daure,tayi dariyar yake ,ta ce....

""Ango da Amarya ,ina tayaku murna,Allah ya bada zaman lafiya.."

Bahijja bata iya ta amsa ba,sai Deeni ne ya amsa a takaicw,yasa kai ya fita..

Farida ta kalli Bahijja tace,"Amarya,Mama tace in fito da kee ana jiranki wurin walima""

Girgiza kai tayi dakyar ta cije tayi dariyar yake,ta fito suka jera tare..



Tunda ta fito idon kowa ya koma kanta ta fito ta haska wajen gaba daya kowa sai albarkacin bakinsa yake fadi,Mama kanta ta kasa hakuri ,ta taso da fara'arta ta zo ta kama hannun Bahijja ta jata gun zamanta. Wannan ya kara bakanta ran Farida,har agun mama ma Bahijja ta ture gwamnatin ta ...

Wani hawayen bakin ciki taji yana zubo mata ,wurin walimar da bata zauna ba kenan,ta juya ta koma ciki,har aka tashi daga walimae bata dawo ba....



Ranar lahadi jamaar biki kowa ya watse ,yayin da ranar lukman ya tare da amaryar sa a gidansa da mahaifin su ya bashi,yayin da Shamsuddeen ya koma saboda aikin da ya bari a kamfaninsu na kaduna. Farida kuwa da yake ana hutu da yaara za su zauna su yiwa mama hutu...

Mama ta shiryawa Bahijja da Deeni kayansu,siyayyar da ta musu na kayan sawa da sauran su ta sa a mota ta tura tare da baba andi taje ta shirya musu....



Gidan yayi tsit ba kowa daga Farida da yaranta,sai Deeni da Bahijja wanda suma suna shirin tafiya nasu gidan....



Alhaji ne ya kira Deeni da Bahijja falo suka same shi yana zaune shi da mama ,nan suka nemi wuri suka zauna.

Alhaji yayi musu nasiha da fada sosai tarw da musu fatan alkhairi haka mama ta kara damka musu amanar juna tare da musu nasiha da cewa siyi hakuri da juna,zo mu zauna zo mu saba..

Alhaji ya mika masa key na gida.

ya yi murmushi ,"Nagode Baba,mallaka min Bahijja da kayi matsayin nata ta kadai ya ishe ni babbar kyauta. Ka mata waliyyanci,ka zama mahaifinta,yayin da Bappah ya min waliyyanci. Na gode da amanar yarka da ka bani Baba,ina da gidana nallakina na godan gona wanda ka taimaka min na kafa shi,haka Bahijja tana da gida,zamu zauna a duk wanda muke so. A halin yanzu rayuwar mu soyayyarmu ,ayyukanmu,gidajen mu da dukiyoyinmu suna hake ne. Baba,Mama,mun gode ,kuyi ta mana addu'a,muma zamuyi ta muku.."

Dariya sukayi yayin da yace,"Allah ya muku albarka Deeni"

""'Ameen """.

Suka amsa a tare ,sannan sukayi sallama da su mama ta raka su har bakin mota ita da Bahijja kamar ba zasu rabu ba.

Wannan soyayya da shakuwa na Bahijja da Mama ba karamin dagawa Farida hankali yake ba,sai tana ji kamar ta zama ita bata da mihimmanci..

Tabbas daga Farida har Bahijja suna fama da kishin juna da ke tsananin cin su a zuciya..

Kai tsaye suka wuce gidan Deeni ,wanda ya ra tsara musu shi sosai,kana shiga gidan zaka fahimci gida ne na masu ilimi daga bokin har addini...



Tun a mota Deeni ya lura da Bahijja bata magana,duk kokarin da yayi don ya takaleta amma bata kula shi ha,shima sai ya nuna mata halinsa,ya dage kai ya kyaleta..

Addu'a tayi sannan ta sa kafarta a gidan ,wani irin kamshi taji yana tashi mai kwantar da zuciya.. Ta lumshe ido tana shaka,nan take taji hankalinta na kwanciya ,fushin nan da take taji yana sauka. A hankali ta dinga bi tana zaga gidan ,Deeni ya bita danido zuciyarsa cike da sonta da sha'awar ta.

Ko ina ta gama zagawa yana biye da ita,ta dawo falo ta zauna,nan ya jawo kujera ya zauna a gabanta yana kokarin su hada ido amma taki. Ya yi murmushi ,yace..

Haka kawai Amarya taji bata son sakar min fuska a daren mu na farko a gidan mu ?

Zuba mata ido ya yi yaji kamar yanzu ma ya fara sonta..

Ina sonki Bahijja soyayyar da ban san irinta ba,komai kika yi a rayuwa sai inga ya miki kyau. Wannan kamshin da ake sha min ma sai naga ya miki kyau,kin kara burgeni"".

Nan ya sauko yasa kanshi bisa cinyoyinta ,ya jawo hannayenta kansa.

MISBAH na meye ya dame ki ?

Ta kwantar da kanta akan nasa suna manne da juna ,ta ce.

(My dear nice house)".

Ya yi murmushi ,yace. Na tabbatar u will be a good home maker?"

Nsha Allah"Ta amsa.

"Deeni ina sonka"

Ta fada tamkar meyin rada a kunnen sa,yana jin muryarta na ratsa shi,yana jin tsigar jikinsa na tashi ,tsantsar sha'awarta cike fal zuciyar sa.

""Bahijja ki kasance dani har abada karki kyale ni,ki cika min gida da irinki da alnarkar ki,ki cika min gida da yaranki,zaki sani farin ciki sosan gaske""..

"" Komai kake so zan maka Deeni,,Allah ya bani yaran da zan cika masu. Nima ina addu'ar Allah ya bani irin Deeni,Allah ya bani ikon sanya ka farin ciki da kyautata maka,Allah ya bani juriya akan ka Deeni..

Ina maka wani so Deeni,gashi dai ka zama nawa amma zuciyata na cike da tsoro da fargaba."

"" Kar kiyi fargaba Bahijja,ni naki ne ""

Bai ankara ba sai jin hawaye na zuba masa yayi Saurin dago ta hankalinsa a tashe..

My deae mene ne ??

Idonta jawur ta kalle shi,"ko zaka iya fassara min rudewar da kayi lokacin da kaga Farida ??? Na mene ne ?? Don kaji tsoro masoyiyarka ta gannu a manne da juna ko kuma ka rude ne saboda ka ga tsohuwar masoyiyarka ???













Tofaa!!!! Ango kaka-kara kaka.........









SUMY LUV😍😍😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬











Written by SA'ADATU WAZIRI GOMBE









=================== GIDAN NOVELS ====================================







Assalamu Alaikum

Yan uwa a wannan page din nake tunanin zan kammala littafin nan part 2 wato kashi na biyu insha Allah...

Wanda kuma a nan nake tunanin dakatawa zuwa bayan sallah in Allah ya kaimu.......

Idan da me korafi nasan dayawa sunada contact dina,,,so se yayi pinging dina.....tnks









49







Zura mata ido yayi cike da mamaki,"Haba Bahijja,ban zaci haka daga gareki ba,wannan halin na zace shi ne daga halin wata me kasa da shekarunki, (me matured)"

Ranta taji ya mummunan baci,ta ce.

I will not be ,me kake nufi? Me yasa kake avoiding tambayata ? Ka fada min wane irin rudewa kayi don kaga Farida. ??

Ranshi yaji ya baci,amma sai ya daure ya ce.

Ke kinga ya dace mu zauna muna bata lokacinmu a irin wannan lokacin akan wannan maganar marabtushe ko kan gado ? Me ya kawo maganar Farida tsakanin mu a yanzu ?

"Akwai abinda ya kawo,ka ban amsa,me yasa mijina zai rude don yaga tsohiwar budurwarsa ?

For God sake!!Farida matar wani ce,uwar wasu ce,saboda mene ne zaki ta da min rigima yanzu ? Har sau nawa zan fada miki cewa bana son farida,na manta da farida. In ada baya can na so farida laifina ne da za ki dinga daga min hankali akan farida? Haba Bajijja ,a yau zamu fara sabuwar rayuwa,ya zaki bari wani dalili mara tushe ya nemi kawo mana matsala ?

To naji ya ishe ni haka, kiji kiyi tunanin duk yadda ki ka ga dama ,na ganta na rude sai yaya ?""

Cikin zafin rai da bacin rai yake maganar wanda ya kara tunzura Bahijja,ya kona mata zuciya. Ta fashe da kuka ta nufi daki ta rufe ....

Bai yi yunkurin binta ba don shima yana cikin zafi,ya zurawa abubuwan da ya shigo musu dashi na ci da sha ,duk ta daga musu hankali har ya ji bashi da sauran sha'awar cin wani abu.

Kukanta yaji yana matukar daga masa hankali,ga sonta dake kara ruruwa a cikin zuciyarsa,amma zafin zuciya ya hana ya bita dakin balle yayi lallashi. Haka ya dinga kaiwa da kawowa cikin dare,ya rasa me ke masa dadi,haka suka kwana baran-baran a darwnnsu na farki..



Ankira sallar asuba yayi alwala ya murda kofar dakinta,ga mamakinsa bata sa key ba ya sameta zaune kan sallaya. Bai ce mata komai ba ya fice zuwa masallaci,ya dawo ya nufi nasa dakin ,duk da ya kwanta ba bacci kirki amma haka baccin ya gagare shi..

Karfe takwas na safe ya fito falo,anan suka yi kicibis sanye da hijabinta...

""Ina kwana?"" Ta fafa tare da kau da kai

Bai amsa mata ba ya sha gabanta ,tayi saurin kaucewa ta kama hanyar fita..

"Ina zakije ? Ya fada cikin daga mirya.

Gidana zan tafi".ta bashi amsa a takaice.

Da izinin wa ? Da yardar wa ? Karki manta baki da gidan da ya wuce wannan,sannan fita a gidan nan ba da izinina ba,kar ki sake wanann kuskuren....

Ya fada cikin tsare gida ,fuskar sa ba alamar wasa,ya juya..

Wani iein bacin rai da takaici taji ya turnike ta,ta juya ta nufi kicin ranta bace ta dinga kaiwa da kawowa ,gata ba gwana ba wurin girki,da kyar ta samu ta hada masa patatos da source tare da yanka fruit da fresh juice da kuma ruwan tea a flask tare da sauran kayan tea ta jera kan dining table..



Yayin da Deeni yake kaiwa da kawowa ,sam baiji dadin yadda ya mata ba,to amma yana da matukar muhimmanci tasan cewa shi mijinta ne,aure sukayi ,ba zata yi yadda take so ba. Haka nan zafin zuciya da jin kai ya hana shi zuwa ya lallasheta,don shi gani yake bai mata laifi ba..

Bahijja na shiga daki ta fashe da kuka,nan ta dauko diary din nan cikin jakarta ta rungume tana kuka...

Hankalinsa ya kasa kwanciya har sai da ya bita dakin ganunta rungume da diary din tana kuka sosai ya taba zuciyarsa. Abu biyu ne suka hadu masa,tsananun sonta da tausayinta da

Please Login or Register in order to submit comment