Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mishi duk abinda yakeso matukwar yaci jarrabawarsa. Haka nan deeni ya dage domin a zahiri ba abinda deeni yakeso kamar farida,,zai yi dukkan iyawarsa dan mahaifinshi ya bashi farida ,ya aura masa ita .

Soyayyar farida da deeni da shakuwarsu ya samo asali,tun suna yara ,tare suka tashi suna girma,saboda zumuncin da iyayensu mata sukeyi.... Deeni ya girmewa farida da shekara hudu ,tun suna wasan yara har takai ga suka fara girma da abota,har ta juye soyayya da shakuwa me tsanani,,wanda mutum bazai gane wayafi son wani ba a cikinsu. Iyaye da yan uwansu duka ba wanda beson maganar soyayyarsu ba . Mahaifiyar deeni na matukar son farida sabida kaunar da sukewa juna,da kuma irin tarbiyyarya da nutsuwarta . Ta fita daban da yan uwanta.

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬



Writting by SA'ADATU WAZIRI





COPIED BY SUMAYYA SA'AD(sumy luv❀)





06



Tunda deeni yadawo daya masallaci bayan sallar isha ya zubawa wannan littafin na MISBAH ido,wanda faruda tayi wurgi dashi ,labarin ya taba zuciyar sa da tunaninsa,yanason sanin ya aka kare amma kuma alkwari yayi ,haka nan farida na gava da wannan labarin .

Yasa hannu ya dauki littafin yasa shaida a inda ya tsaya ,ya rufe yana kallon littafin har yasa shi cikin wata karamar drower ya rufe ,yana tunanin kalmar nan ta sauyin SHAUKI anya kuwa ?change of emotions gaskia hakan bai yiwuwa ba,gashi shi yakan gasgata duk wani labaran MISBAH ,yana da yakinin duk wani abinda ya fada yana iya faruwa,infact yana ma faruwa gana gani ,to amma wannan karon yana da ja ,sabida bai taba yadda shauki yana canjawa ba ,musamman ma shauki irin nasa,shauki na gaske ,shaukin da ya jima yana gina shi gini me karfi da tushe ,rushe shi abune da bazai taba yiwuwa ba balle a akai ga canji ..

Nan ya yi saurin canja tunani ya dakko littafin sa yana karantawa ,amma fa karatun babu abinda yake tunawa sai littafin . Tuni haushin kansa ya kama shi , ya ma zaayi ya bari haka ta faru dashi ,?

Zuciyarsh yaji tana zafi ,,deeni akwai dan banzan zuciya,tuni yaji tana hawa. Rufe ido yayi yana addua cikin zuciyarshi,sannan yayi saurin mikewa yabar study room din ,ya nufi cikin dakinsa ya dakko laptop dinsa yana kallon hotunan farida yana murmushi,,wasu hotunan nata tun tana jairirya,wasu kuwa tana yarinya ,,wasu kuwa suna tare tun suna yara har zuwa girmansu..

Waya ya dauko ya buga mata ta dauka tana murmushj tare da kashe murya tana mishi kalaman soyayyar da yake so,wanda suke kara haukata zuciyar sa da soyayyarta.

Lumshe ido kawai yayi yanajin kaunarta na bin jikinsa,yana ratsawa tare da hango su suna gudanar da wata aurw ne tattare da tsananin so da kauna,,tarw da farin ciki mara iyaka.

Bayan sun gama wayar ne ya tirawa MISBAH labarinsa kamar yadda ya saba ta email dinsa,yana yawan sharing feelings dinsa da kuma experience dinsa akan soyayyarsa da rayuwarsa ,da tarin tunaninsa da kuma hangensa, harma yayi challengn sabon labarin sa da ya rubutu na CHANGE OF EMOTIONS .



Duk da MISBAH bai taba bashi amsar emails dinsa ba bai sa ya fasa rubuta masa ba ,,saboda yasan ba dole ne saya karanta ba,kuma in ya karanta din ma ba dole ne yabashi amsa ba. Irin su misbah dole za suyi jin kai da miskilanci,duk littattafansa yana nuna illar girman kai,,don kuwa Allah ke bada daukakar da mutum zai yi takama dashi,in yaga dana zai iya kwacewa darw daya,wanda a wannan lokacin muamalarshi da mutane zai iya taimakonsa,sai Allah sai dai yasan akwai mutane dayawa da suke da bambanci a rubutunsu.

Rashin amsar da misbah baya bashi be damshi ko ya bashi mamaki ba ,saboda dama ya zaci haka daga gareshi. Yasha masa tambayoyi amma shuru ,dan haka ma wannan karan yana gama tura masa email din ma ya rufe . Da da jyar yasamu karatun ya fara shiga yana fahimta kadan kadan har bacci ya dauke shi ..



Deen matashin saurayi ne dogo ba baki,kyakkyawan gaske . Ba kyanshi zai sa kasoshi ba se halayyarshi ,yana da shiga zuciya . Matashi ne da yake da kula da addininsa sosai,ya yarda cewa Allah zai taimakeshi a rayuwa,zai cika masa burinsa na samun mace saliha,kamila ta gari...



Bayan bautar ubangiji da biyayya ma iyaye deeni bashi da wani buri da wuce yayi aure ,rayuwar cikin aurw da yadda ya tsara zai yi shi,rayuwa ce me cike da soyayya da kuma ibada irin wadda annabin mu (SAW )ya yi da matansa,dan haka kullum adduarshi Allah ya cika masa wannan burin nasa tarw da farida.

Duk wani abu dayake fata da so da tunani a mace to farida na da shi,ga kuma soyayyar da sukewa juna mai tsanani wanda wannan shi zai taimaka su gina rayuwar auren da suke da buri. Saboda idan akwai so da kauna ana iya jure dukkan wani tsanani da jarrabawar rayuwa.

Duk da karancin shekaru irin na deeni shi da auren nan yakeso,bashi da wani dogon buri illa ya kara girma yayi dogon karatu da kudi,ya mallaki abin duniya kafin yayi aure,saboda a fadinsa rayuwar sa ba a hannunsa take ba ,bai so ta Allah ta kasance akansa batare da ya cika burinsa ba .

Haka nan ta bangaren farida ,tunda tayi wayo,ta girma tasan kanta ,to deeni shine abokinta ,kuma masoyinta ,bata sauraron wani namjij balle ta bashi fuskar soyayya. Asali ma dai tun kafin wani ya tunkareta labarin ta da shakuwar su da deeni zai riske shi.

Gata mace me kyau da tsari ,ga tarbiyya ,abin so da sha'awa ga kowanne namijj,sai di fa nan gani nan bari ,saboda ita jinta take tamtar matar deeni,bambancin ta da matar aure kadan ne a cewarta.saboda a tunaninta tsayawa da ma ta yi magana da wani namiji tamkar tayi cin amana ne ga deeni ...



Wannan kenanπŸ€”





Copied by sumayya sa'ad

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬



Writting by SA'ADATU WAZIRI



COPIED BY SUMAYYA SA'AD(sumy luv❀)





07



Kwani tashi deeni ya tattara ya koma zaria,suka fara jarrabawa. Haka nan ra bangarwn farida ma suka fara jarrabawar kammala secondry,hakan yasa sukayi besa da juna . Haka nan yawan mu'amalar su ya ragu sabida karatu da kuma karancin lokaci,sai dai duk da haka rana bata fitowa ta fadi batarw da sunyi magana da juna ba na tsawon lokaci tare da mafarkin tsara rayuwarsu tare..

Deeni ya rigata gama jarrabawa dan haka ya tattaro ya dawo gida tare da shiri da tsare tsaren yadda aurensu zai kasance .yana karati sannan wani lokacin yana zuwa gidansu farida suna karatun tare ,,yana koya mata abinda bata gane ba . Haka nan yana matsawa mahaifiyarsa akan tafara yiwa mahaifinsa maganar auren sa da farida .

Takanyi murmushi tace karka damu mahaifinka zai yi kama komai ,,farin cikinka shine namu duka "

Hakan yasa hankalinsa kwanciya tare da alkawarin dagewa yayi duk abinda mahaifinsa yakeso,donya faranta masa ko da zaiyi abin da ransa bai so,don ya yadda farin cikin mahaifinsa shi ne samun nutsuwar sa da kwanciyar hanklainsa



* * **************

Farida !farida!!farida !!! Taji muryar kaninta na kwala mata kira.

Hararsa tayi ,"meye ne ?

Tana kwance kan gado rungume da hoton deeni,yayin da take magana dashi ta waya,kuma ko minti goma basuyi cikakke da rabuwa ba . Ba abinda ta tsana irin tana magana dashi a katse ta .

Ganin harar datayi masa yasa kanin nata me suna yusuf shima ya turo baki .

"Meye kikke hararata ? Ai nima Abba ne ya aiko ni in kiraki ,in ba zaki zo ba sai inje in fada masa kina waya baki da lokacin amsa kiransa;""

A'a'a ,zo yusuf,tsaya,yi hakuri bazan sake harararka ba ,kace masa ina zuwa""

Harararta yayi yace kinci sa"a da kinga sharri :"

Nan ya fice ,ita kuma ta mike da sauri ,ta bangarwn deeni a waya kuma yanata tsokanarta.

"Kicewa Abba kina biyayya wa mijinki ne ,kina faranta masa rai ,kina masa hira me dadi ,yana jin miryarki me dadi yana ratsa masa jikinsa,kina samun lada,""

""Eh sosai zan fada masa,in yazo mun fada sai in tattaro har da kai ya hada-"

"Bakomai ya bata amsa"

"Ai dama dadi da wuya munyi alkawarin rabashi ni dake "

Tayk murmushi zan dauki wuyar ka dau dadin .

"A'a ni zan dauki wuyae ke ki dau dadin " ni dai a'a . Ta fada xikin muryar shagwaba .

Kin gankk ko ? Kin fara kashemun jiki da shagwabar kin nan ko ? Yanzu tunaninki sai ya fitine ni ya hanani sakat "

Tayi daria , ai haka nake so ,tunani na ni kadai ya fitini zuciyarka ""

Farida !

Ta sake jin murtar mahaifiyarta ,da sauri ta katse wayar ta fita da gudu ,ta ce

Gani nan zuwa umma ,ina bayj ne ." To maza kiyi ki fito Abbanku nasan magana dake tun dazu " to umma "

Nan fa tayk falon nashi zuciyarta cike da tunanin kiran me yake mata haka?

Ganin sauran yayunta mata yasa gabanta faduwa ,dole akwai maganar da Abba zai mata .

Nan ta nemi guri ra zauna ta gaishe shi tare da fadin "Abba gani "

Ya kalleta yace naki ra yan uwanki nayi musu maganar aure ,kamar yadda kika san aladar gidan nan kuna gama sexondry nake auren ku . To Alhamdullilah ,lokaci yayj yan uwanki kowacce ta fada mun zabinta ,kuma nace su turo iyayensu ,sannan zanyi bincike in mun dai daita sai aure,don haka kema nakeso ki fadamun zabinki ,in baki dashi to sai ni in zabar miki ."

Kanta sunkuye zuciyarta taji tana harbawa ,ga Abba yasa mata ido alamar ita yake saurare . Bata dago kai ba ta ce ."Abba Deeni ne mukayi maganar aure dashi ""

Dama dai hakan ya zaci ji ,,sai dai saboda sanin su tare da kuma mahaifiyarta ta fada masa,sai dai yana son jin hakan daga bakinta . Ya gyara zama ya kalleta ya ce " deeni dan gidan makwabcin mu ko ?"

Ta amsa da eh "

"Yace to kamar yadda na fadawa yan uwanki ,kema ki fada masa ya turo mahaifinsa inhar aurwnki zai yi da gaske ,yaro ne da aka haifeshi a ido na nasan iyayensa,nasan halayyar sa,don haka bani da bukatar bincike akansa illa maganar aure. Ku tashi kuje dama maganar kenn""

Nan suma mike duka suka fita.





Farida ta tsinci kanta cikin wani yanayi dabata taba shiga ba ,,ta rasa wani irin abu takeji a zuciyarta da jikinta ? Fargaba ne ? Farin ciki ne ? Doki ne ko tunanin aurwn ne ? Ta rasa me takeji ,sai dai tabbas jikinta ya mutu murus.

Jiki ba kwari ta dau waya ta latsa sunan deeni ta sa a kunne, sai dai wayar tayi ringing har ta gaji ba amsa.



A dai dai wannan lokacin deeni na zaune gaban mahaifinsa eansa bace yana masa fada saboda sake faduwa jarrabawar sa da yayi wannan karon . Ya jima baiga mahaifinshi cikin bacin rai haka ba,shi dai kansa sunkuye yana bashi hakuri,saboda shima baiji dadin hakan ba .

"" Baba kayo hakuri ,nayi iya kokarin iyakacin iyawata amma har yanzj Allah bai sa na kai ga masara ba ""

Wannan kake kira kokri " baban ya fada a fusace.

" ai mai kokari ba ya gazawa,kar ka dauka zamu shirya muddin kana wasa da karatu,in har baka min yadda nakeso ba kar ka zata zan taba maka yadda kake so ""

Nan ya mike ya fita ya barshi a wurn .

Hankalinsa ya tashi matuka ,haka ran sa ya mummunan baci ,yaji wanj irinzuciya da bacin rai na taso masa. Rufe ido yayi yana addu'a saboda samun saukin abinda yakeji. .

Wai har yaushe za su dunga samun rashin fahimta da mahaifinsa ? Sam ya kasa fahimtar sa ;ya kasa ganin kokarinsa. Ya makale a aji biyu ya kasa gaba ya kasa baya ,tabbas in ya sake faduwa korar sa za'ayi.

Zuciyar sa da kwakwalwarsa suka cushe da tunani iri iri ,ya rase meke masa dadi .

Mahaifiyarsa ce ta shigo tana bashi baki da lallashi tarw da kalamai masu kwantar da hankali har ya samu zuciyarsa tayi sanyi kadan ,,sannan ya mata godia ya samu ya mike ya shiga ciki . A nan yaci karo da tarin kiran farida a wayarshi,bai bata lokaci ba ya kirata ta dauka cikin muryar shagwaba tace "

" nayi fushi "

". Afuwan my dear ". Ya fada cikin mueyar lallashi.

"". Deeni meke damunka naji muryarka kana cikin damuwa?

"Akwai farida ,yau ma kamar kullum ban sami nasara a jarrabawata ba ,banji dadi ba ,haka na batawa baba rai , dukkan wani tsammani na yanaga jarrabawata""

Murya kasa kasa tacw nina banji dadi ba deeni ,,wannan karon naji ciwon abun diue da kai da Baba "

""Farida kalamanki sun razana ni ,yau ce rana ta farko danaga kin nuna damuwarki akan rashin nasarata , na zata kin fahimce ni ,kinsan matsala ta na rashin fahimtar karatun da nake amma duk da haka ina dagiya don ganin na cimma burin baba da kuma burin kasancewarmu tare da ke "" na sani deeni " ta bashi amsa .

Murya kasa kasa tace "kamun rashin fahimta nima,na nuna damuwata ne badan gazawarka ba ,sai dan son kasancewarmu tare ,tunda da bakin ka kace idan ka ci wannan jarrabawar babanku yayi alkwarin maka duk abinda ka nema ko kake bukata ,tabbas da ka samu nasara da yazo dai dai lokacin da muke da neman biyan bukata .......



Bye



Copied sumayya sa'ad❀

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬



Writting by SA'ADATU WAZIRU GOMBE





COPIED BY SUMAYYA SA'AD❀❀









09



Muryar deeni sukaji tsaye daga kofa.

Ya karaso cikin falon hankalinsa a tashe. In akwai abinda take dagawa deeni hankali be wuce ace zai rasa farida ba ,ya durkusa a gaban mahaifinsa idanunsa jawur ,hanakalinsa baya jikinsa,,ya ce ,

"Baba addini be hanani aure ba ,hasali ma ya halattamun yin aure a wannan lokacin. Baba addini bece dan bakaci jarabawar makarantar duniya ta boko karkayi aure ba ,,addini bece dole sai kanada gida da mota da abun duniya sannan kayi aure ba . Baba ka fadamun hujja da addini ba da abin duniya ba .

" ina zaka ajiye matar?

"Dame zaka ciyar da matar?:

Mahaifinsa ya jefa masa tambaya fuskarsa a daure,saboda koda wasa bai shirya yiwa deeni aure a yanzu ba .

Baba inada mahaifina wanda yake da arzikin da zai iya rikeni nida mata ta,har zuwa lokacin da zan gina kaina incigaba da rike kaina da matata har da iyayena da kuma sauran 'yan uwana. Baba ba zama zanyi kaita ciyar dani kana rike ni ba ,zan tashi in nema ,zanyi karatu,komai zanyi dan in kafa kaina . Baba ka taimaka mun matsayinka na mahaifina ka dafa mun .

Baba ni dan gatan ka ne ,na roke ka don Allah kayimun wannan gatan ka auramun farida, baba idan na rasa farida na rasa komai,baba farida macece ta gari,yarinya ce kamila ,ga nutsuwa da addini,macece danake yiwa yayana kwadayin samun uwa kamar ta.

Na jima ina gina soyayyata da rayuwata da zanyi da farida,baba banj da wata rayuwa in har ka rusa min wannan rayuwar na rasa ta............

Tausayinsa ya kama hajia don haka itama tasa baki tana taya deeni rokonsa.

Alhaji yaji ransa na baci ,,sai dai deeni yayi abinda zai yi ,amma bai isa yace zaiyi aure yanzu ba ,hasali ma ya dauki abin nasa a yarinta ,dan haka ya mike yabar musu falon ransa a bace batare da yace musu kala ba . Sai dai hakan ya tabbatar musu dacewa bai yiwa deeni abinda yakeso ba ,lokuta da dama daga yanayinsa suke gane eh ko a'a dinsa.

Hakan ya kara rikita deeni ,yabishi yana rokinsa.



Ransa na matukar kaunar deeni ,,komai zai iya masa amma fa banda maganar aure yana dan karaminsa. Bashida wani dalilin da zai sa yaki aurawa deeni farida,sai don kawai ba yanzu bane lokacin da yakamata deeni yayi aure ba . Don haka ya dauka kai garesu yayi tafiarsa.

Bangarensa ya nufa batare da damuwa da halin da deeni yake ciki ba,dan yasan yarinta ce ke damunsa,rashin sanin ciwon kansa ne yasa yake cewa zaiyi aure yanzu.

Deeni yakasancwe cikin halin dimuwa da tashin hankali,lokaci guda yaji duniyar tana juye mishi sama da kasa ,rayuwa ba farida wani abune da bai taba tunani ba ,don haka da sake .

Ganinsa cikin tashin hankali yasa mama itama hamkalinta ya matukar tashi,ta hau lallashi da bashi baki cewa zata cigaba da lallaba mahaifinsa har ya amince. Da kyar tasamu ya saurareta ,sabida idonsa ya rufe ,bai san ma me yake fadi ba .

Yace ,, ba wanda ya isa ya hanani auren farida ,ko mahaifinsa bai yadda ba shi zai aureta a haka".



A wannan dare deeni yayi kwanan tashin hankali da bakin ciki tare da tsoron rasa farida a rayuwar sa,a duk lokacin da yatuna zai iya rasa farida idan har nahaifinsa bai amince masa ba sai yaji ya tsinci kansa cikin gigita da dimauta. Haka ya kwana abin a ransa,ya kuma tashi dashi ,yayin da hajia ta kwana magana daya da mahaifinsa tana nuna masa tsakanin deeni da farida in an raba su ba karamin illata rayuwar su za'ayi ba.amma fir Alhaji ya kafe ba wanda ya isa ya canja mishi ra'ayi.

Washe gari a haka suka tashi gidan cikin rashin kwanciyar hankali ......





Sumy luv❀❀❀

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬



Writting by SAADATU WAZIRI GOMBE



COPIED BY SUMAYYA SA'AD❀❀





08



Deeni ,abba na yamana maganar aure yau,kariga da kasan hakain abba,muna gama secondry sch yake aurar damu,kuma kasan tsattsauran raayi irin nasa,ba mai canja masa,wannan akidar gidanmi ne ,ni ban isa incanja ba . Kuma deeni kasan kaine rayuwata,baza iya ko tunanin rayiwa da wani da namiji ba ,inba deeni ba . Abba yace katuro,in baba yaki fa ?

" bazai ki ba farida ,saboda baba naso na,kuma zan nuna masa idan bayason rasa kai na to ya auramun farida "

Tuni muryarshi ta canja ,"Farida kimun alkawari duk runtsi bazaki rabu dani ba ki auri wani ba. Farida bansan ya zan rayu bake ba ."

" Deeni nima ba zan iya rayuwa dawani ba in ba kai ba ,,nutsuwata da lafiata sai in ina tare da kai deeni"

Cikin muryar damuwa yace ,farida muna tare duk rintsi bazamu rabu ba ,zan fadawa abba zai zo nema mun aurenki gurin abbanki"

" kayimun alkawari deeni?? Nayi miki alkawari farida " ya bata amsa.



Nan sukaita bawa juna kwarin gwiwa tare da kaunar juna,,sannan sukayi sallama.



Wannnan tsoron dashi deeni yake kwana yake tashi ,wato tsoron rasa farida. Yana firgitashi sosai,sabida sanin halin mahaifinshi dana farida,dukkansu suna tafia ne akan ra'ayinsu da tsarinsu,ba wanda ya isa ya canja musu ,,sai dai yakan danji sanyi idan ya tuna irin soyayyar da mahaifinsa ke masa,zai iya aura masa farida don farin cikin sa.sannan a tunaninsa daga shi har farida basu da wani dogo buri,,dakinshi zai ishesu rayuwa kafin su kai ga inda zasu.



Suna gama waya bai bata lokaci ba ya nufi dakin mahaifiyar sa,kai tsaye ya labarta mata abinda ake ciki. Kansa sunkuye gaban ta yana sauraron amsar ta,yayin da ita kuma tayi jugum tana juya maganar a ranta.



Tabbas tasaan abu ne me wuyar gaske,sai dai kuma tasan irin tarin soyayyar farida da deenikarfin soyayyarsu ya wuce a rabasu,,ya wuce tsattsauran ra'ayi da akida irinta iyayensu ,dole ne daya zai sakko ko mahaifinsa ko nata,raba deeni da farida sai Allah .



""Mama""deeni ya katse mata tunani.

Ya kalketa,tunanin me kike ? Ko akwai matsala ne ?

Tayi masa murmushi tarw da girgiza Kai , ta ce .

""" Bawani matsala insha Allah ,anjima idan ya shigo zanyk masa maganar ,karka damu "

Ya sake kallonta cikin fuskar damuwa ya ce ;;

" mama ba ' a samj matsala ba ko ?

Tayi masa daria ,deeni kenan ,baza'a samu ba insha Allah ,komai zai tafi dai dai .ba kai kadai keson farida ba,nima ina sonta "

Murmushi yayi ya sunkuyar da kai,, ya fiya zuciyarahi cike da murna.

Tun fitarsa mama tashiga cikin damuwa da maganar zuci,tasan dole akwai rigima tsakanin deeni da mahaifinsa. Nan tacigaba da addua Allah ya kawo abun cikin sauki.

Daga deeni har mahaifiyarsa sun kasance cikin zulumi da tunanin me zai faru ?

Jin dawowar mahaifin nasa yasa yaji bugun zuciyar sa ya karu ,ya dunga safa da marwa a tsakar dakinsa. Baiyi yunkurin fita ba ,yana jira har sai an bukaci yaje.

Yadda deeni yake cikin tunani da fargaba haka farida ma ta kasance ,tana sauraron wayar deeni .

Bayan Ahj umar wato mahaifin deeni ya gama duk wani abu daya saba na al'adar sa in ya dawo,yana zaune a falonsa haj A'i ta same shi da maganar deeni .

"Alhaji magana zamuyi" ta fada tana kallon sa ,hakan yasa ya juyo ya maida kallonsa gare ta tare da tattaro hankalin sa akanta yace """ wace irin magana kuwa "? Ta gyara zama tacw ,,nu kabata sanin soyayyar deeni da farida kuwa,,''??

Ya kalleta ban gane ba ,deeni da farida?

"". Ta girgiza kai " kwarai......

Nan ta bashi labarin soyayyarsu,da shakuwarsu, takara da cewa .

"Yanzu lokaci yayi da mahaifin farida yakeson ya aurar da ita tarw da yan uwanta,kamar yadda kasani shi mahaifinsu yaranshi na gama secondry sch yake aurar dasu ,farida kuwa bata da wani saurayain da yawuce deeni ,,dan haka tayi masa magana ya fito,ya tura iyayensa a san da maganar neman aurenta ,shi ne ya min magana ya ce in fada maka""

Alhaji ya kallwra cike da mamaki ,ya ce .

Haba hajia ,ya kikemun irin wannan maganar kamar wata karanar yarinya ? Insu yara ne kema sai ki zama yarinyae ki biye musu ? Yaron da karatu ma ba inda yaje ? Yaron da baisan ciwon kanshi ba shine zaa nemar masa aure? Dan uwansa ma yaushe akayi maganar airen sa wanda ya girme da komai balle shi ? Da maganar shamsu ma kika min sai na saurareki amma DEENI ?ai ko ina da yarinya bazan aurawa kamar deeni ba ,yaron da yaki karatu,ya kasa nai da hankali akan rayuwar sa, yasan me yakeyi,ahekarun deeni nawa wai kike maganar auren sa? Shekarunsa ishirin da daya,yaro ne dabai san ciwon kansa ba balle har a dora masa na wata .

" baba addini ya hana dan shekara ishirin da daya aure ????

Muryar deeni sukaji tsaya daga kofa...................







Copied by sumy luv❀❀

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬



Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE



COPIED BY SUMAYYA SA'AD❀❀







10





Tunda sassafe farida ta bugawa deeni waya,daga jin muryarsa tasan ba lafia ba ,hankalinta yai mummunan tashi,kawai sai ta fashe mishi da kuka ,muryarta na rawa tace .

""Deeni ya zamuyi ? Dama abinda nake tsoro kenn kullum ,kasan babanka ba zai yarda ba ,haka abbana ba mai canja masa ra'ayi,bazai taba bari na in zauna injiraka ba ,hada ni aure zaiyi da koma waye ""

" cikin muryar rauni da matujar tashin hanklai yace

""Saurareni farida, baki da wani miji sai in Nsha Allah,Allah ne ya hadamu ba mai rabamu . Inma baba yaki nizanje in sami yayana babana,Bappah na zaj daura mana aure ,ba dai abbanki zai aura min ke ba ?

Abbanki zai aura min ke ,in har nabturo waliyyi na zai daura mana aure . Anjima kadan ,zan fita,zan wuce gombe ,zan je in sami bappah na ,kafin in wuce inason ganinki,ki fito kofar gida mu hadu"

Nan ra amsa masa da toh,ta ajiye wayar .

Bai bata lokaci ba yayi wanka ya kimtsa,ko breakfast bai tsaya yi ba ,ya cewa mama shi ya fita. Ko kallon mahaifinsa baiyi ba balle ya gaishe shi.

Tsawa ya daka masa tare da kiran sunansa.

Cak deenin ya tsaya ,sai dai ko juyowa bai yi ba balle ya yi niyyar zuwa inda yake.

Alhaji yace ,ban haifi dan da gari

Please Login or Register in order to submit comment