Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

biyayya ,ta manta baya. Ya kara sa mata albaek na biyayyar da tayi masa,tare da mata alkawarin cewa zai mata duk abinda take so a duniya muddin bai fi karfinsa ba .

Bayan angama iyauenta mata ma suka bita da tasu kalar nasihohin,sannan Abban da kansa ya rike hannunta tare da kishiyar mahaifiyarta suka kawo ta har gidansu deeni.

Falon baba sukayi da ita,inda mama da Baban tare da shamsu da kuma wasu 'yan uwan suke jiran zuwan su,nan kuwa suka mike suka tarbe su cikin murna da farin ciki,inda mama ta jawo hannun farida dake ta rusar kuka tace.

" Bari ni dai in amshi 'yata da ke ta rusa kuka,an rabaki da mama bayan kina tare da daya maman naki ,me zai dame ki?

Nan suka yi daria duka,amma ban da farida da shamsu. Nan dai akayi gaishe gaishe tare da barkwanci ,yayin da aka gabatar musi da abinci da sha ana hira. Sannan Abba ya bada amanar farida ga Alh umar da mama da kuma shamsu.

Sun karba hannu biyu tare da nishi alkawarin farida ba zata taba fuskantar wata matsala ko damuwa ba ,zasu riketa tamkae yar cikinsu . Haka shamsu ma yayi alkawarin riketa amana da kula da ita ,tare da yin hakuri da duk wani abu dazata masa.

Abba yaji dadin maganar sa kwarrai ,nan aka ta saka musu albarka ,yayin da suka hadu duka suka yi musu nasiha sannan suka kara jaddadawa juna yanzu zumunci ya kullu,an zama yan uwan juna .



Bayan tafiarsu baba yasa shamsu a gaba yana gargadin sa da ya rike farida hannu bibbiyu ,ko da wasa kada ya musguba mata . Anan shamsu ya masa alkawarin rikera da gaskia .

Mama kuwa alfarma ta nema abarta tayi rikon farida na tsawon sati biyu a wurinta kafin su tafi gidansu da shamsu.

Baba yace wannan tsakaninki da ita da mijinta ,in sun amincen to,in kuwa ba su amince b babu dole,.."

Nan farida tayi saurin mannuwa a jikin mama tace ,"na amince"

Mama tayi murmushi tace ,"yawwa yar mama "

Shamsu ya kalle su yana daria ,ya ce

Nima na amince"

Baban shima ya kallesu yace ," To nima na amince ."

Nan suka sa daria duka,sun jima suna hira a wajen kafin suyi sallama. Shamsu ya nufi dakinsa na gidan ,baba ya yi bangarensa,mama ta ja farida suka yi nasu bangarwn. Ta sa mata ruwan zafi tayi wanka saboda tasan tana tattare da gajiya ,ta bata gashasshiyar kaza mai zafi tare da tea me zafi. Bata so haka ta sa ta ci sosai,sannan ta ce to maza ta haye gado ta shige bargo tayi bacci don ta samu hutu.

Bata musa mata ba saboda ita dai farida ko ummanta bata sakewa da ita kamar yadda take sakewa da mama tun tana kankanuwa.



Washegari kuwa 'yan biki suka watse kowa ya kama gabansa,gida ya saura daga mama sai farida ,shamsu,lukman da masu aiki. A wannan lokacin mama ta samu damar yiwa farida gyara ba musammana wanda ta san mahaifiyarta bata samu damar mata wannan ba ,sboda wai kunya da kuma ba wani shakuwa tsakanin su. Dan haka mama ta daukarwa kanta nauyin farida da kula da ita.



A hankalin ta dinga mata nasiha akan aure,da kuma tadda rayuwar aure take. Ra dinga fahimtar da ita abubuwa da yawa wanda bata sani ba ,ta wani bangaren tana shiga da ita kicin tana koya mata girke girke kala-kala saboda ita mama Allah ya bata baiwar iya girki. Ba anan tsaya ba,hatta kwalliya da iya dressing kamar ba dattijiwa ba ,,sai da ra koya mata tana nuna mata wani......





Sumy luv😍😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬





Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE





=================== GIDAN NOVELS ====================================





22





Wani lokacin haka zata ta dinga mata fada da nasiha akan ta rungumi abinda Allah ya bata hannu bibbiyu ,idan ta nuna halayya na kin amincewa hakan ya nuna bata yarda da abinda Allah ya bata ba,don haka ta hore ta da tayi hakuri ,tayi juriya ta saka soyayyar shamsu a zuciyarta,saboda shine mijinta yanzu,don haka ba karamin zunubi bane ta mayar da tunanin wani namiji da sunan so balle har taji sha'awar sa. Ya zame mata dole ta danne son zuciyarta,ta fi karfin zuciyaeta ta rungumi abinda Allah ya bata hannu bibbiyu ,ta gode masa.

Nan ta girgiza kai tare da fadin , naji mama,nagode ,insha Allah zanyi duk yadda kika ce.."

Mama tace ,"Akwai wani aiki a gabanki ,nasan bakya son shaamsu,haka shima baya sonki,amma fa yanzu ya zame miki dole ki so shi,kuma dole ki ja hankalinsa ya so ki a matsayin ki na matarsa. Yana da kyau ki kama zuciyarsa,ki jefa soyayyar ki a zuciyar sa kafin ku kai ga fara zaman aure.

Sunkuyar da kai tayi kinyar mama ta kama ta ,hakan yasa mama ta mike tace.

To zan fita amma ga kaya nan ki ahirya kiyi kwalliya ki fito ,shamsu na falo yana jiranki ,na hada muku dinner zakuyi tare.

" To mama "

Ta amsa murya kasa-kasa .

Bayan fitar mama ta mike ta kalli kayan,,wani jan material ne mai kyau da tsadar gaske ,sai kamshi yake. Ta sa a jikinta,doguwae riga ce mai sharpe ,dinkin ya kamaa jikinta tamkar don ita akayi material din ,fatarta mai haske tayi matukar karbar kayan.

Nan ta tsaya tana kallon kanta a mudubi,ta tuno yadda take bata lokaci da tana kwalliya don ta burge Deeni,amma in ya zo sai dai ya yi ta mata daria da gwalo yana cewa bata yi kyau ba . Da kanshi yake tayata ta gyara yana koya mata yadda zata yj kwalliya,in yaga ya kalleta ya mata murmushi yacs,,

". Kinyk kyau mrs Nuruddeen duk duniyar nan ba macen xa ta kai matata farida kyau a wurina_

Ta kanyi murmushi ta boye fuska ,amma yau da ikon Alkah tana kwalliya don ta burge wani ba deeni ba,wani namijin da bata taba noticing dinsa ba a matsayin namiji ,bata taba kula da shi ko ta bashi muhimmanci ba ,asali ma ita yaya shamsu tamkar bako ne a gareta ,shi ne yau ya zamo mijinta. Lallai Allah shi ya barwa kansa sanin abinda ya lullube .

Tana cikin wannan tunanin mama ta dawo ta ce.

"Har yanzu farida,ina ji dai sai na sa miki hannu . Farida sarkin tunani ,na ce miki ki rage tunani amma ba kya ji ko ?

Murmushi kawai tayi ta sunkuyar da kai. Ta ce ' kinyi kyau kuwa,kayan sun karbe ki. Bari in miki daurin tunda naga ke bakya son yi..""

Nan kuwa ta ajiyeta ta mata daurin da ya kara fito da kyan fuskarta,ta taimaka mata wurin sa dan kunne da abin wuya da dai sauran kayan karau. Ta bata takalmin da ya dace da kayan ,sannan ta fesa mata turare mai kamshin da dadin gaske.

Ta ce ,yauwa ,yanzu 'yata ta fito a amarya sak,sai gun ango ko ?

Kanta sunkuye tayi saurin rufe fuska.

Mana tace to na rafi tunda kunyata akeji ,amma fa ina fita ki fita ,kinga tun dazu yana jiranki.."

" To mama " ta amsa murya a kasa.

Bayan ta fita itama ta bi bayanta ,tana tafiya cikin nutsuwa da hankali tamkar mai tsoron kasar ko taisayinta.

Tun kafin ta iso turarenta ya rigata isowa,hakan yasa ya dago kai a zatonsa ta iso falon. Hango ta yayi tana tahowa ,ta zuba kyau,tana wani taku tamkar wacce take filin gasar sarauniyar kyau. Yarintarta da cikarta ,budurcinta ya bayyana a zahiri,nan ya tsinci kansa da kallonta ya kasa kau da kai daga garera . Sai sheki take tana kamshi,bai ankara ba har ta iiso dab da shi. Nan yayi saurin kau da kai.

Ta ja kujerar dake kallon sa ta zauna itama ta kasa dago ido ta kalle shi,kanta a sunkuye ta ce .

Yaya shamsu ina wuni?

Muryarta me dadi da sanyi ta daki dodon kunnensa ,yaji ya taba zuciyarsa.

Ya amsa," lafia farida ,ya kike? Ya fada cikin kau da kai .

Ta amsa kai sunkuye ,"lafia "

Mama ta shigo tace ,To ko waye ake kawar wa da kai da sunkuyar da kai ban sani ba. Shamsu ,farida halal dinka ce fa,farida shamsu mijinki ne,kina da damar kallonsa ko mene abin sunkuyar da kai ban sanj ba . Ni zan wuce bangaren babanku,ki tashi ki zubawa mijinki abinci, kuma ina so ku saki jiki da juna kuyi hira,"

To mama" suka amsa a tare.

Bayan fitar mama farida ta kasa daga kai,yayin da shamsu ya yi karfin halin dago kai yana kallonta kanta sunkuye tana wasa da yan yatsunta.

Nan y yi kokarin kawar da shirun ta hanyar cewa.

Tunda bazaki zuba min abincin ba bari ni in zuba miki,"

Nan ya bude kular abincin fried liver with potatos ne,ya zuba mata ta hade da juice ya mika mata .

Ta dan kau da kai ," Da ka barshi zan diba da kaina "

Ya yi murmushi yace,"Naki ba barshi".

Ya fada cikin muryar tsokana da kwaikqayonta ,hakan yasa t dago kai ta kalleshi. Gabanta ne yayi mummunan faduwa saboda yadda ya yi sai taga ya bala"in yi mata kama da Deeni,yadda yake murmushin sa da yadda yake zolayarta. Bata san yaushe ta saki murmushi ba ,murmushin da yasa shamsu yaji ya tsaaya masa a zuciya,ya tsinci kansa da kasa dage idanunsa daga gareta har sai da ya ga ta dago.

Ya yi saurin mikewa," Ni zan wuce naga dare yayi "

Cikin sanyin murya tace,ya shamsu kaci abincin mana,kar ka kwanta da yunwa"=

Ya tsinci kansa da kasa musa mata.

Sun ci abinci tare ,sai dai sunyi zaman kurame,dukkansu sun kasa sakeqa da juna yayin da suke kallon juna a sace,,har mama ta dawo ta same su a haka. Ita ta zauna a wurin ta kau da shirun tana kokarin jansu da hira tare da sa su yin magana da juna . Da Shamsu ya zo tafiya mama ta sa farida tayi masa rakiya har kofar dakinsa da ke gidan ,suka yiwa juna murmushi tare da fadin " sai da safe " ta juya.

Shamsu ya bita da kallo yana jinjina takunta da yaba halittar da bai taba mai da hankali ya lura ba,yayin da farida taji hankalinta ya tashi da ta hango kofar dakin Deeni wanda suka kallo juna da na shamsu . Ta sawa kofar dakin ido,hawaye suka zubo mata,soyayyar sa da kewar sa taji yana ratsa ta.

Shamsu ya tsinci kanshi da zuwa inda take,ya lura da yanayin da take ciki idonta lumshe hawaye na zuba ,bai san yaushe ya jawota jikinsa ba ya mannata da jikinsa gami da shafarta yana lallashi.

" kiyi hakuri farida ,nasan ba abu ne mai sauki ba ,sai dai tuna baya ba abinda zai baki sai bacin rai."

Nan ta fashe masa da kuka ,ya zanyi ya shamsu? Ya zanyi da soyayyar Deeni da ke cina yana azalzalar zuciyata? Ya shamsu ina son Deeni ,ina cikin tsananin kewar sa. Ina son kasan cewa da Deeni"

Nan ta dada kankame shi tana kuka,tun yana lallaahi har ya daina ,ahi kadai yansan me yakeji a jiki da zuciyarsa.

Tabbas abinda bai so ba abin da bai zata ko ya tsammani bane ya faru da shi,wato ya tsinci kansa da jin kishin dan uwansa,hakan yana nufin soyayyar farida ta shiga zuciyarsa kenn ? Ya ci amanar dan uwansa da tushe ,ya bari zuciyar sa ta kamu da son farida lokaci guda.

Addu'a ya dinga yi a zuciyarsa,tare da kokarin sharewa farida hawaye.ya ja hannunta ya kaita har kofar dakin mama tare da kara bata baki,har sai da ya ga ta saki ranta tayi murmushi tare da masa godiya.

Ta shige ciki ta samu mama suka dan yi hira kadan sannan tayi shirin bacci. Duk yawanci hirar tasu ta kare ne a nasiha da misalai da mama ke bata game da yanayin irin mata da t ahiga ne ..............







Gaskia yau nayi typing da yawa 😑😑se kuma ankwana biyu😜😜





Sumy luv😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬





Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE





Copied by SUMAYYA SA"AD❀❀





24





Kwanci tashi ba wuya a gurin ubangiji,sai ga ciki ya bayyana jikin farida,iyaye da 'yan uwa kowa ya yi mirna musamman iyayensu maza da mta. Suna shan addua da albarka a kowanne kwanann duniya.



Shamsu dai kamar zai cinye farida,da yanada iko da numfashi ma sai ya mata. Baya bari tayi komai , ya bata kulaqa ta musamman tare da kokarin ganin kullum tana xikin farin ciki . Kullum ana kan binciken lafiaeta data baby.



Tun daga wannan lokacin mama ta kara tsinkewa da al'amarin auren farida da shamsu,ta kara tabbatarwa aurensu wani hukunci ne na ubangiji,rabon shamsu ne a jikin farida bana Deeni ba,wani baya haifar dan wani,haka wani baya auren matar wanj



Nan ta kara dukufa da yiwa deeni addu'a. Allah ya bashi ikon hakuri da juriya,ya kuma kawo masa nasa rabon ta wani wurin.



Farida ta haifo danta santalele namiji mai matukar kama da shamsu,tamkar an tsaga kara. Nan zuciya ta cika da murna ,iyayensu sunyi matukar murnar samun zuri'a da akayi tsakaninsu . Wannan ya kara karfin zumuncin su da kara tabbatarwa sun zama daya.



Farida da baby sun sha kaya da gata kala-kala. Sun zama abin so a dangi,kowa son su yake da sha'awar su.



Shamsu ya fadawa iyayensa cewa ya yiwa yaro huduba da sunan kaninsa deeni,wato NURADDEEN . Sun yi murna kwarai,musammaman mahaifin deeni da mama.

Tabbas deeni ya cancanci haka daga gare su,saboda dukkan su masoyan Deeni ne,daga shamsu har farida,haka nan shi masoyin su ne.



Alh Umar ne ya bugawa deeni waya ya yi masa albishir da zuwan baby da kuma takwara da aka masa ,wato mai suna da shamsu ya masa.

Kwarai Deeni ya ji dadi yayi murna soaai har ya cewa babansa zai zo in sunyi hutu,sai dai mahaifin nasa ya taka masa birki,ya nuna masa zuwa gida zai mai da masa hannun agogo baya ,ya daure dai ya karasa,sauran sa shekara biyu ya gama ,in yaso zuwa ya sayo wa mai sunan sa duk irin abinda yakeso.

Ba don yaso ba haka ya hakura ,ta wani bangaren yana ganin gaskiyar mahaifinsa ne. Tabbas inya dawo gida yaga farida sake tafiya ya barta zai yi wuya,don haka hakurin dai shi yafi masa.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya musu,shamsu da farida da dansu Deeni karami,suna rayuwa tare da rainon dansu cikin so da kukawa da juna ,tare da kulawa da juna ,tare da mahaifansu,yayin da deeni ya dage ya ci gaba da karatun sa.





* * * * * * * * * *



Tunda ya sauka kasar sa nigeria yake cike da farin ciki da wani irin dokin zuwa ya ga yan uwansa,lumshe ido yayi yana shakar iskar kasar sa mai albarka,kasar mama da baba,kasar masoyiyar sa farida.

Sanye yake da red t.shirt hade da blue jeans ,idanunsa boye cikin fararen glass ,ya yi wani irin haske da kyau ,saboda samun hutu da canjin yanayi da ya samu.fuskar sa kunshe da murmushi,kana ganinsa kaga wanda yake cike da farin ciki.



Hayar taxi yayi a nan cikin airport din,ya sa kayansa a boot sai gida.

A cikin taxi din Deeni yana ta sake sake tare da tunanin shin wa zai fara zuwa ya gani?masoyiyarsa farida ko kuma iyayensa ko yaya shamsu da matar sa? Yaba son basu surprise ne shi yasa ko baba bai fadiwa yana zuwa ba ,yafi so sai dai su ganshi kawai,mahaifinsa ya zata sai wani watan zai gama ya dawo.

Ya yi murmushi,"Farida zata ganni bazata,zanga ni da ita wa zai fi farin ciki da ganin dan uwansa?

Yana wannan sake saken har suka iso cikin unguwarsu,a nan ya tsaya yana tunanin ina zai fara shiga gidnsu ko na su farida ,ko kuma gidan ya shamsu..............??



To masu karatu ku bawa deeni shawarar inda zai fara shiga........

Sai munji shawararku wadda zan bawa deeni😜😜😜😜😜





Sumy luv😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬





Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE





Copied by SUMAYYA SA'AD❀❀





23



A wannan sati biyu mama tayi dukkan iyawarta da dagewarta akan Shamsu da farida,taga sun saki jiki da juna ,da kokarin nuna musu su rungumi kaddara suyi ibadar aure,su manta komai. In sunyi haka tabbas basu yiwa Allah butulci ba ,kumansun yarda da kaddara kamar yadda ake so kowane musulmi na kwarai ya yi. In sun haka kuwa Allah zai sa albarka a rayuwar su,ya daga darajar su a duniya da lahira.

Da irin wannan maganganun na mama yasa suka saki zuciyar su,musamman ma dai farida ta riga ta saduda,ta daura damarar manta baya,ta kuma cusa soyayyar mijinta da Allah ya kaddara mata a zuciyar sa.

A satin biyin ta koyi abubuwa da yawa ,don haka tayiwa mama godiya sosai,dami da mata alkawarin zama mace ta gari,saliha ga Shamsu,zata yi kokarin kawo farin ciki da kwanciyar hankali tare da nutsuwa a rayuwar Shamsu ,ta riga da ta amince,ta karbe shi matsayin mijinta.

Wannan magaba tayiwa mama dadi matuka da zancen farida ,tayi ta saka mata albarka.



Shamsu shima bai yi kasa agwiwa ba ya kara jaddadawa mama rikon da zai yiwa farida bisa gaskiya da amana da kuma soyayya.

Mama tayi ta sa musu albarka ,ta raka su har mota tare da hadawa farida guzuri iri-iri.



Farida taji kewar mama sosai ,saboda shakuwa da sukayi a yan wadannan kwanakin da sukayi tare.

Kauna da soyayya tare da kulawa da shamsu ya dinga nunawa farida. Ya tabbatar mata da soyyayr ta na tare dashi ,don haka itama ta saki jikinta da shi,ta mika wuya gareshi. Da kanta ta kai kanta garw shi har dakinsa,mutuncin mama kadai da girmanta da take gani ya isa ya hnata cutar da shamsu.

Ta lura yana sonta da bukatarta ,amma ya kau da kai,bai taba nuna mata hakan ba ,don haka da kanta ta yanke shawarar mika kanta da rayuwarta gaba daya ga mijinta. Bazata iya raba kanta da son Deeni ba ,amma zata iya raba kanta da tunaninsa ta cusa na mijinta a zuciyarta.

Wanka tayi fes ta feshe jikinta da kamshi ,tare da saka sexy dress ,ita kanta ta yaba kanta,ta zurawa kanta ido a mudubi .

" Yau ce ranar da zan ci gaba da rayuwata,ranar da zan mallakawa wani kaina,zuciyata da gangar jikina,wani ba deeni ba.

Ina fata zaka yafe mun ,ka manta dani a rayuwarka Deeni,na yankewa kaina hukuncin rungumar aurena da mijina hannu bibbiyu don nemar yardar Allah.

Da wannan tunanin ta nufi dakinsa,tayi sallama ,yana zaune bisa gado sanye da kayan bacci,hannunsa rike da ipad yana danne dannen sa alamar wani aiki na office yake yi.

Sallamarta yasa shi daga kai yare da amsawa,ganinta a yanayin da bai zata ba yasa shi kasa karasa sallamar. Ya yi saurin kau da kai zuciyar sa na bugawa,tuni ya ji ya rude musamman da ya jita dab da shi.

Hannu tasa ta karbi ipad din ta ajiye a gefe ,ta dare bisa cinyarsa tare da jawo shi jikinta ta rungume shi . Nan ya bata hadin kai ,shima ya kara mannata a jikinshi sosai yana shakar kamshi tare sauke wani irin ajiyar zuciya yana jin tsananin son ta da sha'awarta suna shigar sa.

Cikin muryar rada idon sa a rufe yana manne a jikinta yace...

Farida kin amince dani,ba kya tunanin dee.....

"" shhhhhh"

Ta fadi gami da saurin rufe masa baki tace ,,

Karkace komai,na mika rayuwata da kaina ga mijina wanda shamsu shine mijina,gaskiyar rayuwata. Ni matarka ce,kanada hakki da damar yin duk abinda kake son yi dani,buri na a yanzun kawai in kyautata maka . Ina neman yardarka ,saboda Allah ya yarda dani.

Nan ya dunga sauke ajiyar zuciya ,shi kadai yasan me yakeji a zuciyar sa da jikinsa.

Bai bata lokaci ba ya dada cusuwa a jikinta ,tuni suka manta komai suka fada wata duniya. Farida ta mallakawa mijinta shamsu kanta ,, yayin da shimanya mallaka kansa da komai nasa ,yana mai sa.mata albarka gami da alfahari da ita .

Tuni suka rungumi auren su suka rike hannu bibbiyu,suna kula da juna tare da tarairayar juna,suka bude sabon shafi na rayuwar su,iyaye na sa musu albarka.

Ba wanda ya kai mama farin ciki da kuma fargaba ,a kullum Deeni ya yi waya sai shamsu da farida sun tsinci kansu cikin sabon tashin hankali . Sai dai a kwana a tashi har sun saba da hakan ,don kuwa mahaifin deeni ya hana ko da wasa a fada masa gaskia ..

Lokacin da karatu yayi wa deeni yawa ma yana dadewa bai yi wayar ba.mahaifinsa yana yawan ziyarar sa,yana ganin yadda ya cigaba sosai a karatunsa,ya yi nisa kuma tana kokari sosai ,ya kwantr da hankalinsa,,saboda ko da wasa bai san me ke faruwa ba. Kullum da burin auren farida yake kwana yake tashi........

Bye



Mu kwan lahia jama'a







Sumy luv 😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬



Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE





Copied by SUMAYYA SA'AD❀❀







25



Can dai deeni ya yanke hukuncin zuwa gidan dan uwansa ,ya cewa direba ya juya. Dama ya riga yasan gidan da mahaifinsu ya bawa shamsu,don haka ya yanke hukuncin wucewa gidan shamsu ya ga mai sunansa Deeni da dan uwansa,ya yi masa murnar aure,ya ga kalar matar da yayansa ya aura...😭



Yana daria ya fito hannunsa dauke da akwati wanda cike yake da kayan sawa da kayan wasa na mai sunansa Deeni karami. Nan ya cewa mai taxi din ya jirashi zai shiga ciki ya amso masa kudinsa. Nan ya yi ciki ya bar sauran kayansa a motar.

Tura gate din gidan ya yi yana jan akwatin da ke hannunsa,yana ratsa tsakiyar gidan,yana kallin ginin da cikin gidan yana murmushi. A ransa yana fadin,kwannan shima zai mallaki nasa gidan tare da farida.

"Anya kuwa in na auri farida ina da wani sauran buri kuwa a rayuwa?

Yana cikin wannan tunanun yaci karo da security na gidan wanda dama ya shiga ciki kai wani sako ne ,ganin Deeni yasa shi washe baki yana dariya saboda dama tsohon mai gadinsu ne Alh ya bawa shamsu shi yana masu gadi.

Nan ya karbi akwatin tare d a bude masa kofar falo,anan ya ci karo da Deeni karami a tsakiyar falon ,an baza masa toys yana wasa .

Da sauri ya isa gare shi yana dariya,yasa hannu ya daga shi, Deeni kuwa kamar ya sanshi ya wangale baki yana dariya.

Deeni yana zura masa ido yana kallon irin kamar da yake yi da shamsu,son yaron da kaunar sa yaji ya shiga zuciyar sa,nan ya dinga masa

Please Login or Register in order to submit comment