Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

me son zama cikin dabbobi,tsuntsaye da son kiwon su.

Deeni yana son (spat) yana son (swimming),yana matukar son MISBAH da labaransa"

Ras! Ras!! Ras!!! Bahijja taji gabanta ya fadi,ta maimata

**MISBAH**

Ta tambaya cikin mamaki.

Farida ta girgiza mata kai ,'Kwarai MISBAH (the author )wannan marubuci Deeni yana sonsa da labaransa. (Ideologies ) dinsa suna matukar burge Deeni,a kullum in munyi fada da Deeni to akan littafin MISHAB ne ,har na dauki littattafansa kishiyoyina saboda ba abinda ke dauke hankalinsa daga gareni sai takardun MISBAH.

Tana maganar tana bude mata wani drowar dake cike da takardun MISHAB,gaba daya ba wanda bashi da shi,daga na hausa har na turanci,daga na labari har na addini.

Shuru tayi tana jnjina soyayyar da yakewa takardunta,ko ita bata da wasu copies na takardunta sai dai original dake cikin computer dinta.....

Lafiya Doctor ??;

Farida ta katse mata tunani.

Ta girgiza kai,,"Ba komai""

Farida taci gaba ,"Deeni yana son rayuwa mai sauki,haka nan yana son ganin ya taimaki marasa karfi. Deeni bai dauki rayuwa da zafi ba""

Magode kwarai da wannan bayanai naki da hadin kai da kika bani."

Farida ta kalleta ,(please ) likita ki taimake shi""

Bahijja ta girgiza kai,"Nsha Allah.

Bahijja bata bar gidansu farida ba wanda ainihin cikin gidan su Deeni suka dawo tunda zuka koma lagos,sai da ta sa Bahijja taci abinci tayi wanda da sallah sannan suka rabu.

Bahijja ta gama abinda take a garin kaduna ,washegari ta hau jirgi ta koma lagos,tare da sake sabon shiri wa yadda zata tafiyar da Deeni.



Asslamu Alaikum"

Ta fada lokacin da take kutsa kai cikin dakin .

Yana tsaye bakin window bai juyo ba,ta karasa dab da shi.

" Deeni sallama nake "

Nan ya juyo ya kalleta a yatsine ya watsar , sannan ya amsa ciki -ciki .

Tayi murmushi,yau ce rana ta farki da ya amsa sallamarra.

Tayi murmushi ,a ranta tace,"Wanann akwai son nunawa mutane isa."

Gado ya nufa ya kwanta,ya juya mata baya. Ta matsa kusa da gadon.

Deeni abokina ba gaisuwa ? Ko fishi kake dani ne ? Sorry "

Ta kama kunne,"Na tafi na bar abokina ,to ai ba laifina ba ne,in na zo baka kula ni,baka jinm maganata,ba ka taya ni aiki,shi yasa na dai na zuwa. Ina zaune yau a gida sai mind dina ya dinga fada mun Deeni abokina yana missing dina ,kuma gashi na zo ka juya mun baya..""

Duk surutun nab da takeyi bai ce mata kala bahar ta gaji ta kyale shi,can ta canja salo.

Naji labarin abokina ma'abocin son karance-karance ne,ko zaka iya fada min waye (favourite author ) dinka?

Har yanzun bai kulata ba,nan ta mike ta bar inda yake ta zauna kan kujerar dakr dakin,ta jawo jakar data zo da shi tafara ciro littattafan da ke ciki tans dubawa,har yanzun ya juya mata baya. Waya ta dauko tayi kamar tana magana.

'"Naga kun samin sabbin littattafai har wanda bana karantawa,wa ya ce kusa min littafin MISHAB? Ni bana son karanta labarinsa,yabi ya ishe mu da labaran rikicin rayuwa ,duk labaransa na bakin ciki shi kullum sai wahalar da mutane ,kullum yana hada mutane da matsaloli.

In soyayya ce ma yayi ta wahalar da su,mutm ba zai samu wanda yakeso ba." Tana maganar tana satar kallonsa.

Gani tayi ya juyo ya mai da hankalin sa kanta gaba daya,ganin ya mai da hankalinsa gareta tasa ta ajiye wayar ta juyo da sauri suka hada ido,ya yi saurin kau da kai.

Tayi dariya ta mike ta matso kusa da shi hannunta rike da littafin .

"Kasan labaran marubucin nan kuwa ?

Ya dago idanunsa ya tsareta dasu,"kar ki sake""

Ya fada yana kallonta har ta so ta rikice,akwai wani abu a muryar sa mai sa a saurare shi,kuma ayi yadda yake so. Zai iya controlling mutum da muryar sa kawai wanda za mu iya cewa baiwa ne da Allah ya yiwa Deeni.....

Tayi saurin cire idanunta cikin nasa,tace.

" Kar in dake me ?

*Zangin (best author ) dina MISHAB . Dazu kin tambayame ni waye beat writer na,to MISBAH NE"

Ta dan yi murmushi tace,"Ai ba zaginsa nayi ba,gaskia na fada"

Ba gaskiya bane,me kika sani akan rubutun MISBHA ?

"Fadamun ina son sani."

Haka nan yaji yana son biye mata,yace.

"Ba zan fadi ba sai dai in kina so mu zama abokai kamar yadda kika nema ki dauko sabon littafin da kika ce ya yi sabo ki karanta mun,saboda yanzu ina da ciwon kai ba zan iya karatun ba. Kinga kema in kin karanta za kiji wani darasi ne dabirin (logic )hikimar da ke cikin rubutun sa."

Tayi murmushi,"Me zai hana ? Zan karanta maka ,amma ba don mu zama abokai ba,,saboda na riga na zama abokiyarka tun tuni. Sharadin karanta maka labarin MISBAH shi ne,zaka dinga jin maganata,zaka dinga fada min damuwarka,sannan zaka yarda in dinga duba lafiyar ka"""

Lafiya ta ? Ya tambaya yana kallonta.

"Ban fada maka abokiyarka Bahijja likita bace? Kuma na lura abokina baya cikin koshin lafiya,kamar ciwon kanka,inka bani hadin kai cikin kankanin lokaci zamu yi maganin sa. Sannan kana fada min damuwarka in baka shawara ,kaga riba biyu ,yi sauri ka amince ,yi sauri ka yarda..."""

Kallonta yake yana mamakin ta,ita ko wace iri ce ? Bata fushi bata gajiya da magana,duk da baya kukata ba ta gajiya da duj halin da ya nuna mata,gashi har ta koya masa ya saba da ita da halayyarta.

Zura masa ido tayi tana kallon sa,'Ina sauraron amsar ka""

Bai bata masa ba sai jan pillow da tayi ya hadasu waje daya yayi matashi dasu,ya dago kansa tare da dora kafs daya kan daya. Ya kalleta yace.

"Ina jin ki"

Tayi murmushi,'inason (style ) dinka da (attitude ) dinka ""

Tayi saurin ciro wani card da biro a jakarta.

". Samin hannu mana (autograph)in zama mutum ta farko saboda nan gaba in ka fita kana yiwa 'yan mata wannan halin zasu haukaxe akan ka,kasan "yan mata na son namiji mai aji (classic tall ,handsome) sannan ga (attitude);yana musu jun kai yana shan kamshi,maganaa ma tsada take masa,yanzu zan zo ince in suna son zuwa kusa da kai to su zo ta wajena,saboda ni abokiyarka ce,ta hannun damarka,har (Autograph )dinka ina dashi. A lokacin ni zan zaba maka irin matar da ta dace da (personality ) dinka ,wacce za ku dace,zata haifa maka (cute cute little angels)"

Tsayawa yayi yana kallonta kamar wata t.v,yana mamakin ra.

Cikin tsawa da daga murya yace ,"Zaki karanta ne ko a'a ? Na rasa wane irin tunani ne dake"

Ta harare shi,kai ,karfa kaga na ce ni abokiyarka ce ka nemi ka raina ni,ni yayarka ce,na girmeka (at least respect my age) ka daina min tsawa ""

Juya mata baya yayi ya kyaleta,dariya ma ta bashi,ya hau murmushi shi daya...........







RAF. RAF. RAF

πŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌ

A tafawa MISBAHA ,tasa deeni murmushi wanda ya rasa shi tsawon shekaru har ya fidda tsammani da kuma yin sa...









Sumy luv 😍😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬









Written by SA'ADATU WAZIRI GOMBE









Copied by SUMAYYA SA'AD❀❀







40



Juya mata baya yayi ya kyaleta, dariyq ma ta bashi, ya hau murmushi shi daya.

Lekashi tayi tace, "laa ! murmushi nake gani a fuskarka ? Amma shan kamshin nan yafi maka kyau, gaskiya zaka daina murmushi kar ya bata maka kwatancen ka na (Mr. Attitude).

Karamin pillow dake gabansa ya dauka ya wurgeta dashi, tai saurin cafkewa tana dariya tace: "to tsokanar ya isa lokacin karatu yayi". Nan ta dauko wasu littattafanta ta fara karanta masa. Ya juyo ya kalleta, "sabon littafin MISBAH".

Nan tahau 'yan kame-kame tana zare ido, ka bari wannan sai gobe, bari in fara maka da wani. Ban so, ya fada kai tsaye sai kin fara wannan. Sai tace naji (Mr. attitude).

Nan ta dauko wani littafin da tayi BALLE ta karanta masa, don haka kawai ta juya masa baya ta fara kirkiro masa sabon labari a lokacin, saboda duk littafin da zata karanta masa nata ya sani, kuma ba yadda za'ayi ta karanta masa labarun wasu tace nata ne, don haka tai dabarar kirkira ta hada masa labari a lokacin.

A hankali yaji labarin na ratsa shi yana taba zuciyarsa, yaji yana sashi nishadi, baisan yaushe ya juyo ba ya samata ido, dukda ta bashi baya, ya lumshe ido yana sauraronta. Dr. bahijja na ta kokarin hada labari kiran Sallah ya katsesu, tayi godiya ga Allah ta juya ta kalleshi. Lokacin Sallah yayi. Ya bude ido kinyi alkawarin ci gaba ? Ta girgiza kai, amma bayan ka dawo daga masallaci.

Mikewa yayi ya fita daga dakin ya nufi masallaci, sabanin da da yake sallah a daki.

Fitar sa ya bata damar gyara gadon, da kade kurar da take gadon, ta tattara dakin sannan ta fita ciki tayibdakin am don yin sallah.

Mama tasa aka kai masa abincinsa dakinsa, yayin d suka zaunanda Bahijja sunanhira wanda duk ya kare akan rashin lafiyar Deeni ne da irin canjin da aka samu sosai a tare da shi.

Deeni ya dunga kaiwa da kawowa cik8n dakinyqnq jiran dawowar Bahijja a haka ta same shi.

" kaci abincin kuwa ?

"sai kin karasa mun'"

Ta nade hannu, sai ka ci abinci"

" Banzan ci ba.. "

"Nima bazan karasa ba "

Nan ta bude abincin ta zuba nasa ta mika masa, karba yayi da karfi yana ci.

"Bi a hankali, karka kware, bakasan cewa akwai (manners) na cin abinci ba ma ? "

"Ban sani ba mana na, sai kin fada mun".

Ta girgiza kai,"za dai ka iya kirana yayarka amma banda mamanka".

Murmushi yayi ya girgiza kai, ya kyaleta har ya gama cin abincin ya mika mata.

Tayi daria, (good boy) ,"Karbi magani kasha"

Bai musa mata ba saboda burinsa taci gaba masa da labarin da ya tsaya masa a rai, yayinda Bahijja ke tunanin ta ina zata fara karasa masa ? Haka dai ta zauna tana hado labarin tana jan ransa har bacci mai karfi ya fizge shi alamarmaganu da yasha ya fara aiki ,ta kimtsa dakin ta tattara jakarta (box) din maganunsa ta adana waje guda, tazo fita ta tsaya tana kallonsa.

"Ina tayaka murna da sabon canji da ka soma samu a rayuwarka, na fahimci kai mutum ne mai kirkin gaske da saukin kai duk da zafin zuciyarka".

Sau da dama Bahijja kan debewa kanta kewa ta hanyar hidimar Dini da asibiti wanda ta lura suna taimakon juna ne ta sami abuda ke debe mata kewa, ta mance damuwarta da kuncin da take tsintar kanta na dan wani lokaci, yayin da inta koma gida da dare ne komai ya zam a mata sabo, soyayyar mujinta da danta ya dawo mata sabo.

A haka kullum Bahijja ke yi da Dini, har timetable na karatu ta sa musu, in sukayi karatu na addini kamar Alqur'ani da sauran takardu, sai tai ta kokarin hada masa labarin da take kirkira, daga nan sai shawarawri ya biyo baya. Cikin dabara da hikima da kwarewa irin nata ta ringa masa (brain therapy), tana bashi addu'o'i da magani na asibiti da Islamic medicine kamar su habbtis sauda da zaitun da makamantan su, tana bashi shawarwari masu amfani da misali kalakala.

Haka nan cikin dabara ta dinga dangana labarin da take masa na kirkira da labarin rayuwar sa, a hankali ta dinga saita tunaninsa har ya soma manta damuwarsa da bacin ransa. Ya tsinci kansa da rungumara sabuwar rayuwar da ya tsinci kansa, wacce yake jin dadinta. Kana ganinsa za kaga alamar sauki atre dashi, saidai a duk lokacin da yaga mahaifinsa ko yaji sunan dan'uwansa Shamsu yakan tsinci kansa cikin bakin ciki da damuwa.



Kamar kullum yau da ta shigo ta samu yayi kaca-kaca da jakar takardunta da suke karatu yana ta bincike..

" Meye haka Deeni? Me kake nema?

"Naji sauki ne nake neman littafin da kike karanta mun na MISBAH in karanta,meye sunan labarin ma ?

Ras !! Taji gabanta ya fadi.

Ya tsare ta da ido,"Ina littafin ?

Tayi saurin kau da kai ,xBan sani ba,don kawai kana neman littafu sai ka wargaza mun kaya? To sai ka tattara."

"Bazan tattara ba." Ya bata amsa kai tsaye.

Ba zan tattara ba ,kuma sai kin bani littafin nan."

In naki fa ?

'In kinki yau bazaki fita a dakin nan ba".

Hannu yasa ya daddanna (password) din kofar.

"Ba zaki fita ba sai kin bani"

*Deeni ""Ta fada cikin zare ido.

"Baka da hankali ne ?

"Bani dashi "

"Please ka bude "

" In kina son tafiya ki bani.

Ya juyo ya kalleta ,"Kar ki damu ba abinda zan miki ,ni kanunki ne."

Nan ya dare gado ya hau ya juya mata baya tana ta masa masifa amma bai sairareta ba.

Nan tayi ta kokarin daddanna numbers din tana kokarin canka,yace.

In kika yi sau uku ba dai dai ba to ko ansa na dai dai din ma bazai bude ba,kinga zama daram ni dake (my sweet)yaya." Ya fada cikun zolaya.

Nan ta hau masa magiya har yamma ,tace masa ta tafi da littafin gida ta manta ,gibe zata kawo masa.

Nan ma bai kulata ba ,nan fa ta hau lallaba shi tana lallashi,duk wannan bai yi aiki ba.

Ta ce,"Deeni in na tafi fa ba zan sake zuwa ba,ka manta sharadin mu zaka dinga jin magana ta ??"

Ya juyo ya kalleta,"Maganar ki wanne ne banji ba ? Na sha magani,na ci abinci irin wanda kike so,na sa kaya irin wanda kike so,na saurari shawarwarinki ,kullum muna karatu tare sannan yanzu mu abokai ne ,surutun da banayi kinsa na fara magana ,tun banaso har na fara so,menene baki sani nayi ba Doctor Bahijja...........Oops Abokiyata Bahijja?

Ta daka masa harara ,"Akwai abinda ya saura baka yi ba,shi ne kunce abotar mu,daga yau na daina abotar ,kuma ta window zan fita kaje ka nemi wata abokiyar ta karanta maka labarun ,don ba zan baka littafin ba ,kuma ko ina zaka shiga ba zaka samu ba.""

"Me yasa?

Ya bata amsa,,"saboda ke ce MISBAH da zaki hana ni ko kuma zaki boye mun labarin. Sannan batun neman wata abokiyar bazan iya ba,saboda ko bakomai a tare da ke akwai muryar da take taba min zuciya in kina karanta min labarin, don kuwa ko shi MISBAH da ya rubuta labarin in yaji yadda kike karantata shi da dukkan (feelins) dinki da (emotions )dinki zai ji kamar ba shi ua rubuta ba.

Sannan batun fita ta window kuwa Bismillah,iyakaci kugunki da kafarki daya ta karye,iyaka ta in sai miki ayaba da lemo"".

Harara ta galla masa,ta kuwa nufi window gadan-gadan zata fita ,ya yi saurin fisgota fa rigarta.

Ta daure fuska ,"Ka kyale ni""

Zuwa yayi ya bide mata kofar ,"Fita,kin kira kanki da abokiyata amma ba zaki iya daukar wasa da nake miki ba.""

" Eh bana son irin wanan wasan. ""

Nan ta sa kai ta fice ,ya lura ranta ya baci,sam baiji dadi ba.



Kwana uku Bahijja bata zo ba,Deenj ya rasa me ke masa dadi? Ya samu sabuwar rayuwa tare da ita da (company) dinta.

Hankalin sa ya matukar tashi da rashin ganin Bahijja ,ya kasa hakuri har sai da ya tamvayi mama ina ne gidansu ne ? A wanne asibiti take aiki ?

Mama ta kalle shi,Deeni kenan yanzu duk zuwan da Bahijja yake gidan nan baka taba tambayarta ita wacece ko daga ina take ba ?

"Mama ki ban amsa."

""Nima ban sani ba ,sai na bincika. Zan tambayi mahaifinka""

Ranshi ya baci,ya juya ya koma ciki. Wanan ya bata damar yowa Bahijja waya ta fada mata halin da yake ciku.

Bahijja tace,""Mama ina ga lokaci yayi da Deeni zai soma zuwa asibiti yana shiga cikin ajin da muke musu (lecture da ba da shawarwari,ya kamata ya fara shiga mutane. Munyi mai wuyar,kiris ya ragewa Deeni. Kafin ya samu waraka sai ya dai na kebe kansa a gefe......









Wannan kenan





Sumy luv ce dai har kullum😍😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬











Written by SA'ADATU WAZIRI GOMBE











Copied by SUMAYYA SA'AD❀❀













Assalamu Alaikum

Gaskiya ina matukar jin dadin yadda jama'a da dama ke binmu da nuna jin dadin wannan labari,hade da qara min kwarin gwiwa,da addu'o'i da nake samu,duk da wasu sun san cewa bani na rubuta ainahin labarin ba..........πŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌ









42





Bahijja tayi kokarin janye kanta daga gidansu Deenj saboda tana gani lokaci yayi da zata janye daga gareshi,yanzu ya sona dawowa hayyacin sa. Abu kalilan ne ya rage masa yawan nasiha da masa tuni akai-akai, don haka ta bada shawarar in yana zuwa daukan darasi a (couselin center ) dinsu zai mike.



Mama ta same shi a daki ta mika masa (address)din su Bahijja,ta lura yana cikin damuwar rashin zuwanta,tabbas Bahijja tayi tasiri a rayuwar Deeni.



Tunda ya karbi (address) din yake tunanin yaje ko a'a ? Haka zuciyar sa da kwakwalwarsa suka dunga tun zura shi da ya je.

Washegari ya shirya ya fita,tunda ya shiga wurin kwakwalwar sa ta dinga tunano masa da abunda ya faru. Hankalinsa yaji yana tashi, yaji kamar ya koma,ya tsaya shi dai bai shiga ba shi bai fita ba.

Wani ma'aikacin wurin ne ya masa magana.

"Malam wa kake nema ? Ba a tsayawa a nan,ko shiga ko fita"".

Deeni ya kalle shi ya mika masa hannu suka gaisa,sannan yace.

"Ina tambayar Doctor Bahijja ne ""

Mutumin ya kalle shi yace,"Madam tana can bangaren koyarwa ,tana cikin aiki amma ka jira in ta gama zan mata magana,in kuma kana sauri sai ka dawo gobe da wuri kafin ta fara aiki.

Deeni yace ,"In ba zaka damu ba ka raka ni zuwa inda take sai in jirata a can"".

Tare suka jera da mutumin zuwa ciki,suna fatiya yana kalle-kallen yadda wurin yake,da irin jama'ar da ke zarya a wurin.



(Hall) ne dan madaidaici cike da majinyata kuma dalibai,Bahijja tsaye gaban su tana ta bayani,tana ilmantar da su tare da wayar musu da kai,su kuma suna mata tambayoyi tana basu amsa,yayin da ta dinga binsu daddaya tana tambayarsu matsalolinsu suna fada mata tare dsmusu misalai da mutane daban-daban. Wani lokaci takan koma tarihin Annabawa,Sahabbai da manyan bayin Allah da irin gwagwarmayar da suka sha a rayuwa. Don haka ba wani bakin ciki ko bacin rai da zai saka tsayawa da rayuwarka bayan kana da Allah da addini,kuma Allah ya baka yadda zakayi in ka koma ga Alkur'anj ,sannan zaka ga kai baka da matsala ma kan tasu ko na wasu.

Allah ya mana kyautar rai da lafiya ne don mu bauta masa,don samun rabo duniya da lahira,ba zamu samu wannan babban rabon ba sai mun kula da kanmu da lafiyarmu,sannan muji dadin kyautata idar mu.

Nan ta basu addu'o'in da za suyi na cikin Hisnul muslim,wanda yake cike da azkar din da Annabin mu yayi,kuma ya yi umarni da a yishi.



Deeni ya harde hannu a kirji yana tsaye ya kwanyar da kai yana jin ta da saurarenta,maganganunta na ratsa shi. Hikimar ta na iya zance da iya fahimtar da mutane ya burge shi,iliminta da fahimtar ta yasa shi jin wani sauyi.

Ya zura mata ido yana kallonta yana murmushi,wai da wa wannan likitar ke masa kama ? Yanayinta,koyarwarta,hikimarta akwai inda ya sansu.

Kamar da wasa ta juyo sukayi ido biyu,ta hango shi tsaye gabanta. Nan ta dage kai kamar bata ganshi ba.

Murmushi yayi ya kutsa kai ajin ,ya wuce kai tsaye gabanta ya kama kunne.

"Sorry"

Bata kula shi ba,ya juya ya kalli ajin ,"Sannun ku 'yan uwana dalibai majinyata,wannan. Malamar ta ku kuma likitar ku nima malamata ce kuma likita ta,na mata laifi na zo bata hakuri kuma nima daga yau zan fara zuwa ajinku,ku tayi ni bawa malama hakuri na dawo dan uwanku kuma abokin ku."""

Nan suka hada baki suka ce,,'''muna maraba da sabon abokin mu..""

Suka kalleta ,"Malama kiyi hakuri.."

Nan suka sake hada baki suna ta bata hakuri har sai da ta amsa ta hakura,Deeni ya kafa mata ido yana mata dariyar zolaya. Bata kula shi ba har suka tashi ya bita har (office)a nan ya sata gaba yana ta mata naci tayi hakuri.

" Ba zan kyaleki ba kamarnyadda baki kyale ni ba kwanakin baya,kiji ya fitinar take ? Gara ma ki hakura mu shirya."

Ta kalle shi ba alamar wasa,ta ce.

"Mr . Deeni ,nan ba gida bane,wurin aikina ne inda ma'aikata na ke ganin girma na da girmamani ,don haka ban son wasa. In har zaka ginga zuwa daukan darasi to ba wasa,muna da (discipline)da dokokin da zaka kiyaye. Ba latti,ba fashi,kuma ba yin yadda kake so..""

Dauke kai yayi ya bata fuska,"Bana son (classes) din naki.""

Ganin yadda ya juya ya murtuke ,lokaci daya kamanninsa suka canja ya firgita ta,ta mike .

""(Please )mana Deeni ,ka saurare ni"

Damuwa ta bayyana karara a fuskarta.

Nan kuwa ya kwashe mata da dariya yana tsokanar ta.

"Na firgita wata .""

"Deeniii """""

Ta fada tana zare ido.

" Kai ki,zan kama ka ne .

Dariya yayi yabfita yana fadin," Gobe karfe tara na safe (i will be here )ba latti ba karya doka,ba fashi.

Nan ta bishi da kallo taba dariya,har ya tafi ya dawo.

"Zan sami littafin nan ki sunan littafin ??""

Juyawa tayi bata kulashi ba ,ta rufe kofar office din. Don haka Deeni ya dage da zuwa kullum ba fashi,haka kullun yana mata nacin labarin nan ko sunan sa,amma bata saurare shi ba,va irin nacin da bai yi ba har ya hakura. Har (internet )ya shiga yana (searching)sabbin littafan MISBAH amma bai samu ba,tun na karshe da ya sani da ba sunan wani sabo a cikin list din littattafansa.

Abun yana matukar daure masa kai,duk nacinsa da kokarinsa ya kasa samun ko mutum daya da yace ya samu sabon littafinsa.

Haka Deeni ya samu sabuwar rayuwa tare da sabbin mutane da suke tare da Doctor Bahijja,killum takan musu darasi tayi musu tambayoyi,duk wanda ya ci takan fita da su yawo zaga gari,da zuwa ziyarar wuraren tarihi na ilimi. Duk wanda ya warke gaba daya a sallame shi

Anan Deeni ya dunga taimaka mata da wasu ayyukan kasancewarsa likita,duk da kwarewar sa da karatun da bai kai nata ba zama da ita yau da gobe yasa ya fara sabawa da koyon aiki sosai ,daga dalibi ya bige da (praticing)da (training).

Bahijja takan yi mamakin kokari da nuna kware na Deeni gashi da saurin fahimtar aiki,tabbas da ya jima yana aiki da karo karatu da ba karamin taimako zai yi ba ...



A kwana a tashi Deeni ya ya warware ,shakuwa da sabo yana karuwa tsakanin sa da Bahijja ,zukan wuni tare a asibiti suna aiki tare.

Sai dai har yanzu Deeni bai taba fada mata damuwarsa ba wanda ke cinsa,abinda iyayensa da farida suka masa ya kasa mantaws da wannan cin amanar,haka kullum gudun haduwa da su

Please Login or Register in order to submit comment