Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wasa yana cilla sama shi kuma yana daria.

Nana ya bude akwatin ya ciro masa sabbin toys din da ya siyo masabya bashi,anan wurin deeni ya zauna yana ta wasa da Deeni. Shi dai megadi ya tafi ya barsu don Deeni ya hana ya musu magana ,ya ce suprise zai basu.



Tsawon minti goma yana da Deeni har ya soma mamakin me yasa yaji tsit ba wanda ya fito duba Deeni karami shi daya?

Nan ya daga shi ya nufi falon ciki yana fadin...

" zanci tarar iyayenka ,sun barka kai kadai na tsawon lokaci ba wanda ya leko ka,kar ka damu ga uncle Deeni ta dawo ,zai dauke ka ya tafi da kai su kuma suyi ta zaman su a ciki...."""

Deenibdai sai dariya yake masa tare da fadin mommy ko daddy.

Ya ce "uncle zaka ce,uncle Deeni "

Nana ya yi kokarin kwaikwayon sa ya fada cikin maganar yara 'yan koyo. Shekararsa biyu amma ba baki sosai,sai girma da yayi kamar dan shekara uku.yaro ne lafiyayye mai ki da karfi. Da alama ya samj kyakkyawan raino da kula daga iyayensa.

" Salamu Alaikum ,mutanen gidan suna nan kuwa ko sai na tafi muku da yaro za ku fito?

Deeni ya fada yana kokarin kutsawa cikin daya falon tare da daga labule.

Wani abu idonsa ya gane masa me kama da mafarki ko almara,,wani abu da kwakwalwa ko hankalinsa ba zai iya dauka ba.

Farida ya hango kwance jikin shamsu ,shi kuma ya rungumota yana ta kokarin massaging kanta,yana matsa mata kai alamar yana mata ciwo ,tana ta zuba shagwaba.

" Daddy kaina zai tsage,daddyyn deeni inajin murda;;""

Yi hakuri mommyn Deeni,zai bari,kwanta ina ci gaba da matsa miki tunda kin sha magani zaki samu bacci yanzu,kiyi shiru kar ciwon kan ya karu"

" Daddy deeni fa ? Ta fada cikin shagwaba da kuma ciwo .

Yana can yana wasa ,ki samu bacci zan fita da shi in kaishi gun mama tunda ka kya jin dadi. Wannan babyn namu dai da yazo yanzu yana wahalar min da farida na,sai mun masa bulala in yazo.

Tayi murmshi ta ce , Ya shamsu macw zamu haifa mai sunan mama,kaga kuwa ba a yiwa mama bulala ba,in kuwa ka mata sai hannunka ya nade"

Dariya sukayi duka,sam basu kula da Deeni da ke tsaye a kansu ba,wabda tsananin firgita da kaduqa da abinda ya gani sai da ya saki deeni ya sha kasa ,bai ma san yayi hakan na. Gaba daya hankalin sa ya bar jikin sa,baya hayyacin sa.

Ihun deeni ya jawo hankalinsu ,shamsu ya mike a firgice gabansa ya mummunan faduwa,yayin da farida ta ji wani irin hajijiya ,sabon zazzabi ya lullubeta ,tsananin firgita da ganin Deeni bata san lokacin da taji mararta ta juya ba ,wani azabar ciwo taji ya kamata,tuni jini ya soma bin kafarta yna gudu ,alama ne na cewa cikin jikinta wanda bai wuce wata biyu ba ya bare saboda tsabar tsorota da tashin hankali data shiga. Haka nan shamsu duk kokarinsa ya kasa ko da motsi a wurin ,kansa sunkuye ya kasa hada ido da Deeni,ya kasa ko da motsawa balle yaje ya daga deeni dake ta kwala ihu a wurin

Farida dai dakyar ta samu ta zauna bisa kujerar da suke da sabida hajijiya da wani abu da taji yana yawo a tsakiyar kanta ,ki ciwon marar ma bata lura da shi ba sai dai tabbas tasan abu na bin kafarta wanda bat san menene ba.

Tsawon minti biyar suna cikin wannan halin,duk wani farin ciku da murnar da jin dadin da ya dawo da shi nigeria sai da ya neme shi ya rasa,kunci ,bakin ciki ,takaici, da bacin rai ya maye gurbin su.

Halin da ya gansu ya ganar da shi dukkan abinda yake faruw ,ya fahimci cin amana da. yaudarar da farida da shamsu suka masa.wani abu da bai taba zata ba balle tsammanj ,ko a mafarki ko. A tunaninsa bai taba giftawa ba.

Wani abu yaji ya tokare shi a zuciyarsa,haka ya dinga jin wani azabar radadi a kansa,wani irin azabar ciwo da bai taba jin makamancin sa ba . Amma duk da halin da yake ciki sai ya sa hannu ya dauki Deeni ya nufi gabansu ya mika musu shi,sai dai dukkansu ba wanda ya iua motsawa balle ya sa hannu ya karbe shi. Hakan yasa ya ajjye shi. Akan cinyar farida ya juya ya fita.

Yana shirin barin falon ya ci karo da su umma tare da baba ,da kuma Abba da umma ,wato mahaifiyar farida.

Ashe Alh Umar ya yi waya can America aka ce masa ai tun tuni Deeni ya taho nigeria,tun daga nan hankalin sa ya tashi ya aina tsawon lokacin da aka ce masa ya taho yasan tabbas ya iso,haaka nan tunda bai je gida ba ko gidansu farida ,to tabbas yasan gidan shamsu zai nufa. Ranar da suke gudun zuwanta ne dai ta zo.

Tunda mama ta sami labari hankalinta yai mummunan tashi,Alh ya tattaro su duka don su yiwa Deeni bayani,su fahimtar da shi ,wanda a zatonsu zai fahimta,(hmmmm atunaninsu akwai wani bayani da deeni zai fahimta neπŸ€”),to amma mama tasan dama za'a rina.....

Mama na ganinsa da yanayin da ya shiga hankalinta ya kara tashi,ta jawo shi ta rike gam tana fadin .

Deeni addu'a zaka yi kaji,ka dinga maimaita hasbunallahu wa niimal wakil,ko la'ilaha illah anta subhanaka inn kunti minazzalimin""

Gaba daya kansu suka yi kowa da irin abinda yake fada masa ,da irin bayanin da suke masa . Sai dai deeni ya dawo kamar zararre,tamkar mara hankali,kallon su kawai yake bakinsa na motsi amma baya ma jin me suke fadi balle ya gane.

Ya kalli mahaifiyarsa yace,,Mama kinada kudi ki bani in biya me mota lr da ya kawo ni ?

Deeni na biya shi,har mun sa ya sauke maka kaya ya sa a motar mu,zo mutafi gida""

Deeni ya kalleta,"Mama farida ,jini na zuba a jikinta ku kaita asibiti"

Sai a lokacin suka mai da hankalin su kanta,umma ce da mama sukayi kanta,suka dagota hankalinsu a tashe suna salati,sukai mota da ita. Tare da Abba suka tafi,yayin da baba ya tsaya tare da shamsu da deeni,ya jawo su duka.

Bayani ya fara da nasiha ,da kuma fadin ba laifin shamsu da farida bane ,su suka yi hadin nn saboda wani dalili nasu,su kuma suka musu biyayya.

Bana son ji Baba ,duk wani abu da zaka fadamin ko wani dalili bana son ji,ka rike dalilinka,duk abinda zaka fada ba zai cire min ciwon da nakeji yanzu a zuciyata ba. Kasan me nakeji Baba ? Da kasani da baka tsaya yi mun wani magana ba ...

Baba ka sama mun magani ,ciwon da nakeji a kwalkwata da zuciyata yanzu za su iya kashe ni,Baba yanzu ina jurewa amma anjima ba zan iya jurewa ba. Baba zai kashe ni ka kaini asibiti ko ka min addu"a ,kamin duk abinda zaka iya mun ko zan samu saukin ciwon da nakeji .....

Kai Babana nw ,ME SONA ,me yanke dukkan wani hukunci na rayuwa saboda ka kawo ni duniya ,ka bani ci da sha, ka kula da lafiyata da karatuna ,ya zamar min dole in maka biyayya.

Nayi biyayya baba da abinda kayi ,sai dai baba ka taimake ni wannan abinda nakeji baba ban taba jn irinsa ba,baba bana ganinka sosai ,duhu na rufe mun ido,ina jin duniyar na zagawa dani ....

Kama kansa yayi da karfi,basu ankara ba sai ganinsa sukayi ya fadi ,ya zube kasa a sumeeee.............



😭😭😭😭😭😭😭😭



Allah ya bamu alkairi jama'a ,,dan wlh nima hannu na rawa yake kar ayo biyu,,ga deeni a sumee nima wayata karta fadi......







Sumy luv😍😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€





writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE







Copied by SUMAYYA SA'AD❀❀



ASSALAMU ALAIKUM



Yan uwa!! Mata ce ta cewa mijinta ya saketa,shi kuma yaki ,hakan yasa ta dakko wuya wai idan be saketa ba zata kashe kanta.

Shi kuma ganin haka yasashi sakinta. SHIN YAYA HUKUNCIN WANNAN SAKIN DA YAMATA ? TA SAKU KO BATA SAKU BA πŸ€”πŸ€”?

Sai naji daga gareku....nagode







27





Wasa gaske al'amarin Deeni ya tsananta,wani lokaci ka ganshi lafiya wani lokaci ya haukace musu,gana daya baya hayyacinsa,bai san me yake yi ba,hankalin iyayensa da masoyansa ya kai kokuluwar tashi. Daga karshe Alh ya fita dashi kasar india ,anan aka ci gaba da duba lafiyar kwakwalwar sa,saboda abin yamatukar raba masa kwakwalwa,kwakwalwarsa ta kasa dauka da jurewa wannan damuwar.



Ana duba lafiarsa a asibiti kuma ana masa rokon Allah,tare da sauke masa Alkur'ank ,da haka da taimakon ubangiji Deeni ua soma dawowa hayyacin sa. Sai ya zamana ya daina surutu tunda suka dawo gida,ba ya kula kowa ,baya cewa kowa komai. Kullum yana zaune a dakinsa,baya fita sai dai wani ya tafi masallaci ya dawo. In an kai masa abinci wani lokaci zai ci ,wani lokaci kuma haka abincin zai kwana wani ya tarar da wani.



Lokaci guda rayuwar Deeni ta canja ,ya yi baki,ya rame ,kuma baya aikin komai sai kwanciya da zaman gida. Ya dawo rayuwar sa sam bata da wani manufa.



A duk lokacin da Deeni zai kwanta bacci,to yakan rufo ido ya hango shi da farida,lokacin da hoton farida da shamsu zai bayyana a fuskar sa yakan yi saurin bude ido wanda a nan za su rine suyi ja,yaji kansa ya fara sarawa ,ya kama kai da kirji . Wani lokaci sai dai a shigo a same shi a sume.



Halin da Deeni ya shiga ya daga hankalin kowa a zuri'ar su,musamman iyayensa da kuma shamsu da farida. Wani lokacin mahaifin sa sai ya zubar da hawaye saboda bakin cikin halin da dansa ya shiga. Rayuwarsa ta dawo useless bata sa wani amfani ,ya yi da na sani tare da jin bakin cikin abinda ya yi.

Kulum yana binciken asibiti ko masu maganin gida da za su dawo da shi dai dai,sai dai abu guda yake ji kullum,shi ne abin ya mugun taba masa kwakwalwa da zucya,wanda fitar sa a wannan hali sai a hankali . Sai dai dayawa masu magani ko likitoci na bashi shawarar cewa ya canja masu wuri,wato ko dai ba ya bar garin ko kasar ,ko dai wani wurin da zai nesanta deeni da rayuwar da yayi ta baya.



Wannan yasa Alh Umar ya tattara nasa ya nasa da kasuwancinsa ya raba su biyu ya koma lagos ,ya yin da ya barwa Shamsu sauran kasuwancin sa a kaduna .



Alh Umar ya tattara iyalinsa,wato hajia A'i da Deenj da lukman suka koma garin lagos ,ya bar Arewa gaba daya. Saboda ya san Deeni yana da sha'awar zama a garin ,sannan yana ga zai ji dadin tafiyar da kasuwancin sa. Haka Deeni zai samu kyakkyawan canjin yanayi ,yayin da ya bar Shamsu da Farida a kaduna.



Tabbas Alh.Ahmad ya yi bakin cikin rabuwa da abokinsa,makwabcinsa,wanda yake kamar dan uwansa Alh. Umar . Ya daukar masa manar dansa da kuma hakkin kula da shi da kasuwancin da ya bar masa,da ya dinga kokarin sa ido inda yaga ya karkace ya yi masa gyara.

Farida da mama sun rabu cikin kuma tare da bakin cikin rabuwa da juna.





*** *** *** **** **



""ALHAJI ! ALHAJI !!

Haj. A'i ta shigo falonsa tana kwada masa kira .

Ya kalleta a firgice ," lafiya cikin daren nan ?

Ta mika masa wani farin takarda ,ya kalleta cike da mamaki.

"Menene wannan ?

Tace ,Address ne na samu,inda zamu kai Deeni,yanzu na kasa bacci na kunna tv kenan naga suna tallen wurin nan. Na lura masu matsala irinta Deeni sun samu waraka..""

Ya kalleta ransa bace ,ya ce,"Dana ba mahauci bane ,kuma ba dan shaye shaye bane da za a kaishi REHABILITATION CENTER

Cikin nuna damuwa Haji. A'i tace. Alhaji ka duba ka bincika ,wannan wurin ba mahaukata ko 'yan shaye-shaye bane,kafin in baka sai da nayi bincike naji komai akan su. Abinda yafi jan hankalina gare su ahi ne,sun hada da Addini da kuma magungunan musulunci . Deeni yana bukatar taimako na Addini da na asibiti duka,wanda duk sun hada.

Dakyar ta samu ta shawo kansa ya yarda zai binciko,in ya masa yadda hankalin sa zai dauka to zai yi tunanin tura Deeni wurin.....







Gaya nan ayi breakfast😜😜😜



Sumy luv😍😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬





Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE







=================== GIDAN NOVELS ====================================





26





Alh Umar ya mugun rudewa ,rabon sa da ya zubar da hawaye har ya manta,amma a wannan lokacin sai da ya zubar da hawaye,hankalin sa ya mugun tashi.ya tsorata da lamarin Deeni,haka shamsu duk jikinsa ya mutu,ya rasa me ke masa dadi,ga halin da Deeni ke ciki ,ga na farida.

Tare suka nufi asibiti dashi,in da faridan take nan suka je,sai dai ita an dace an shawo kan alamarin ,sai dai tayi barin cikin har an mata wankin ciki tare da bata magunguna da allurai.

Tana kwance tana hawaye ,mama rungume da ita tana bata baki da nuna mata ta ci gaba da dauriya da cijewa kamar yadda tayi a baya,,zai wuce.

Umma rike da Deeni karami tana kallonsu,ta kasa fadin komai sai tsabar tausayin 'yarta da ya kamata,ta ahiga halin tsaka mai wuya.

Nan ta matsa itama tayi mata nata nasihar ,sannan ta ce zata wuce gida da Deeni,sannan zata shirya musu abinda za su ci ta aiko asibitin. Mama kuwa tacw zata zauna da ita.



A nan ta samu damar kwaniciya a cinyar mama tayi kukanta sosai,mama bata hanata ba sai dai bata fasa lallashi da bata baki ba.

Suna cikin wanann halun shamsu ya iso yana rude ,mama ta kalle shi tace,,,,

Ka dauki abin nan a hankali,komai ta yi zafi magninsa Allah."

"Mama Deeni yana kwance a emergency tun dazu muna can likitoci a kansa sai yanzu muka samu ya farfado,"

Hawaye ne ya gangaro masa,ya ce,"Mama Deeni yana cikin wani hali wanda mu ne dalili."

Da sauri mama ta mike ba tare da ta karasa jin me yake fadi ba ta fita wurinsa,Shamsu ya matsa gaban farid yana fadin . "Ban baki kulawa ba lokacin da kike bukata,saboda Deeni yana bukatar kulawata fiye sa ke. Farida ban kaea sanin cewa bamu kyautawa Deenj ba sai yau da naga halin da yake ciki ,halin da ya shiga yana cikin tsanani da firgita tare da zafin zuciya da kwakwalwa""

Ta fashe da kuka ,"Ya shamsu ba abinda zai samu Deeni ko? Ya shamsu munci amana.."

Ta fada a lokaxin da ta kara fashewa da kuka .

'Ya Shamsu ba zan iya fuskantar Deenj ba har abada,fatana Allah ya bashi lafia,yasa kuma ya manta sa ni da wannan cin amana da muka masa."

" Ba mao sauki banw farida ,tabbas bamu kyauta masa ba ,har ga Allah bamu kyautawa Deeni ba "

Nan suka lallashi juna ,daga karshe Shamsu ya kama ta suka nufi gurin Deeni a emergency.

Tana hango shj ko daga nesa ne,hango shi tayi yana kwance idonsa biyu sai dai ya kau da kai hawaye kawai ke zuba masa,ransa a mugun bace,hankalinsa a tashe.

Tausayinsa da tsohuwar soyayyar sa taji sun taso mata suna tsuma zuciyarta,tayi saurin dafe kirji tana hawaye,ta lura ya kara girma da haske hade da wani irin kyau duk da yana cikin tashin hankali.

Ta lumshw ido tana jin wani abu mai ciwo da radadi yna ratsata.

"Ka yafe min Deeni na ci amanar kauna ,sam ko kadan ban yi fighting wa soyayyar mu ba,nayi saurin mika wuya . Na cika makiyarka da nayi sanadin jefa ka a cikin wannan halin,nasa ka dandani wannan zafin zuciyar. Allah ya baka wacce ta fini,ni kam ban dace da kai da rayuwar ka ba da soyayyarka,tunda can ma kila shiyasa Allah ya rabaka danj. Na tabbatar Allah zai baka wacce tafi dacewa da kai,sai dai ka sani Deeni ba zan daina sonka ba ,hae abada soyayyar ka zata kasance a cikin karkashin zuciyata. Sai dai zan danne ta in ci gaba da rayuwa ta da mijina gami da faranta masa iyakar iyawa ta..""



Muryar mama ce ta katse mata maganar zucin da take yi,ta mai da hankalinta kansu.

Mama ke masa magana cikin kwantar da murya,tana shafar kansa kamar karamin yaro tace,,"" Deeni kayi hakuri ,bani da abinda zan iya baka sai hakuri ,ba wani bayani ko kokarin kare kanmu da zan maka. Magana guda ce ,mun maka laifi duk da muna manya kai kana karami ,amma min maka laifi,mun zalunce ka,kayi hakuri ka yake mana,kar kayi fushi damu."

Deeni yayi murmishin kardin hali yace,"Fushi "" ? Da wa zanyi fushi ? Kima ni waye da zan yafe muku ? Ku iyayen mu ne,kuna da damar yin yadda ku ka so. Da mahaifin farida zanyi fushi don ya zabawa 'yarsa miji ? Ai bani da hujja.

Da farida zanyi fushi ,masoyiyata ,wacce ta min alkawarin soyayyarta da kanta ,wacce tun muna yan kanana muke wa juna son da bamu san irinsa ba ? Ko da yayana da na bawa amanar masoyiyata ,wanda yasan duk wani sirri da tarihin son da nake wa farida ? Ko da nahaifina da ya yaudare ni ya min karya? Ko da mutumin da na dauke shi tamkar mahaifina yace min ya mun alkawarin bani yarsa har inje in dawo ? Ko da mamana mahaifiyata da ta boye min gaskiyar magana?

Mama da wa zanyi fushi a cikinku ? Kuma meye riba ta in nayi fushi da ku ? Abinda ya faru zai canja ne ?

Ya mike cikin zabura da zafin zuciya ,ya ce.

"Damuwata shine yadda zan share wannan mummunan al'amarin daga kwakwalwata da zuciyata ..""

Ya kalli likita dake tsaye a kansa tare da mahaifansa ,ya ce

" Doctor ,kaga nima doctor ne ,likita ne cikakke,sai dai ban kware ba,ni ba professional bane,hala likiminka ya kai inda za'a iya yiwa mutum wankin kwakwalwa?ka bude mun kwakwalwata da zuciyata ka wanke mun su tas ,ina son manta dukkan mutanen nan a rayuwata,bana son tuna su balle in tuna abinda ya faru. Kaga wannan painful memories din abinda ya faru dani ,ina so ka bude ka wanke mun su duka saboda ba zan iya rayuwa da su ba,suna min ciwo sosai ,baza su barni in rayu ba ,ni kuma inaso in rayu. Please Doctor ka taimake ni..""

Tun yanayi a hankali har ya fara da tsawa,lokaci guda ya haukace musu,da kyar ak samu aka masa allurar bacci ya kwashe shi.

Ba mama ba har baba ya shiga cikin mummunan tashin hankali da Abba ,har suka yi nadamar abinda suka aikata masa.

Mama tana kuka tana tofa masa addu'a haka daga farida har shamsu kuka suke bamai lallashin wani..............







Hmmmmmmmmmm😭😭







Sumy luv😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬





Writting buSAADATU WAZIRI GOMBE









Copied by SUMAYYA SA'AD❀❀





28





Ruwan sama ake tsugawa sosai ruwa irin na lagos,wanda idan ya fara sai anga tsawarsa. Iska ce me hade da feshin ruwa ya shigo ta windo ya wanke mata fuska,hakan yasa tayi saurin bude ido hade da addu'a.

Ta mike ta nufi jikin window din ta lumshe ido tana shakar daddadar iskar da ke dukan fuskarta tana jin yana ratsa ta ,yanayin da tfi so fiye da kowanne yanayi kenn.tuni taji zuciyarta tayi mata fari,ta tsinci kanta cikin wani nishadi.



Karar door bell ne da aka danna ya ja hankalinta zuwa kofa,Doctor Bahijja kenan tayi saurin zarar hijabinta ta nufi kofar falon , a nan mai gadi ke fada mata suna da baki da ke son ganinsu,sunje cikin asibiti aka ce basu iso ba ,shi ne suka biyo su gida,sun ce wai yana da matukar muhimmanci suga likita.

Tayi mirmuahin da tasaba wanda kullm yana makale a fuskarta ,ta ce

" Kaisu falon baki,kace su jira ko ?

To madam

Ya amsa tare da juyawa ,duka cikin harshen turanci suke maganar..

Nan ta juya ta nufi dakin barcinsu,kai tsaye ta same shi har yanzu bacci yake duk da iska mai sanyi da ke ratsa dakin ,yana ratsa fuskar shi bai sa shi farkawa ba .

A hankali ta sa hannu tana jan bargon da yake lullube tana murmushi ,amma sai ta ga ya dunkule guri guda ya ci gaba da baccin sa tamkar wani baby.

Ta kalli kyaykkyawar fuskar sa me kunshe da annuri da lafiya ,tare da kwanciyar hankali . Soyayyar sa taji ya kara tasiri a zuciyarta ,cikin muryar shagwaba tace.

""Please my dear" ka tashi mna,kana da baki "

Bai saurareta ba sai kokarin jawota jikinsa da yayi yana narke mata a jiki,ya cigaba da kwanciyarsa a jikin ta,yana jin sonta na karawa baccin nasa dadi.

Girgiza kai tayi tana murmushita kwace jikinta tare da sa hannu tana jan hancinsa,tana wasa da shi .

My dear please ka tashi ka duba time fa karfe sha daya na safe ,baccin ya isa haka. Ba don ruwan sama ba da fa ka fita tun karfe takwas."

Cikin muryar bacci ya ce,"shiyasa nake son damuna ,yana bani hutu ,ina samun nutsuwa da Bahijja na,amma ina!! Wannan likitar ba zata bar wannan likitan ya huta ba.

In barka ka huta daga baya kace me yasa ban tashe ka ba ? Ka fa tuna me kace mun "

," Komai bacci me dadi da nake ki tashe ni ko da kamshin jikinki"

Rungumota ya sake yi ya cigaba da kwanciyar shi"

Bata kulashi ba ta mike ta nufi gadon Muhammad da taji alamar ya tashi yana ta ciccilla kafa yana wasa tare da surutai irin na yara. Yana ganinta kuwa ya wangale baki yana mata daria,yana sanye da body suit dinsa masu kyan gaske da ban sha'awa .(hmm, kaga dan likitoci ,πŸ˜€)kaunar dan nata taji ya kara shiga zuciyarta ,dariyar da yake mata ya sa taji kaunar danta har cikin zuciyarta tare da godewa Allah da ya azurta ta da kyakkyawa kuma lafiyayyen da son kowa.( dama ahalin likita na cuta ne 😜😜ciwon ma tsoran gidan likita yake)

Tasa hannu ta daga shi,yaro ne da bai wuce wata shida ba ,ta rungumo shi a jikin ta ,ta ce.

Ni dai na kasa tashin Abbanka ,amma ni da kai zamu tashe shi tare.

Nan taje ta ajiye shi a kansa,nan da nan ya wangale baki har da tsalle saboda ya ga abokin wasansa. Nan ya hau sukuwa a kansa yana jansa tare da masa yaren su na yara ,dolensa ya bude ido yace.

" Ta nan mommyn ka ta bullo ko ? Ta hada ni dambe da kai,to bari in mike muyi.

Nana ya tashi ya biyeshi suna wasa yana cilla shi sama ,shi kuwa yana ta dariya,itama ta taya su.

Please Login or Register in order to submit comment