Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai yawaye yana kallona ya wuce bai gaisheni ba,baka isa ba ."

Jin hakan yasa deeni ya juyo ya kalleshi fuska ba walwala ya ce .

" Ina kwana ? Da fatan ka wayi gari lafia ""?

Bai saurari amsar mahaifin nasa ba yasakai ya fita ,mahaifin nashi ya bishi da kallo. Baiyi mamakin hakan ba,sabida yasan halin deeni ,sai dai fa duk abinda zaiyi yi dan baazaiyi aure yanzu ba da bai san ciwon kansa ba ,yayi haukansa ya gama .



""Ina kaunarka dana ,,shiyasa nake son yiwa rayuwarka gata kafin in kai ga maka aure,,sai na maidaka mutum sosai,,mace kowa zaka sani kowacce iri kakeso a rayuwa "

Mahaifiyar deeni ce ta shigo tare da matsowa inda yake , ta tsake masa tunanin da fadin "

Alhaji bazaka sake duva maganata ba kuwa ?

Ka auna irin soyayyar da rayan nan suke yiwa juna , karfa ka illata rayuwarsu sabida wani dalili naka na daban . Sannan yarinuar nan ya kakeso tayi ? Dukkna tsawon rayuwarta bata da wani wanda take saurara in ba deeni ba ,kanaso ace deeni ya yaudareta ya rabata dawasu mazan kuma shi be aure ta ba ?

Ya dago udo ya kalleta yace ,

In bazaki gaji da maganar nan ba ,to nima bazan gaji da fada miki a'a ba ,sabida bazan biye miki inbata rayuwar dana ba . Inshi bashi da hankali yakamata ace ke kina dashi .

" Alhaji a duba yarinyar nan,ita kuma meye laifinta a ciki don taso danmu,jininmu ,sai mu hukuntata akanshi ? So kake mahaifinta ya hadata da duk wanda ya samu ? Farida kamar diyarmu ce,bazamuso ta shiga gidan wani can da bata san halinsa ba ..""

" wannan ne damuwarki ?

," duka"" ta amsa masa .

" Saboda deeni yanason yarinyar nan fiye da tunaninka ,haka ba jima da saka burin farida tazama surikata ,uwar jikoki na . Na tabbatar da zanyi alfahati da ita ,duk inda akeson mace ta gari ,yarinyar nan ta kai ""

"". To shikenn naji ,karki damu indai wannan ne damuwarki ""

Ta kalleshi cukin murna sa doki tace ,,kana nufin ka amince ?

" ki saurara ,ki sa ido kiga hukuncin da zanyj ,,ba zan bata rayuwar kowa ba "

Yana gama fadi ya mike ya nufi dining table ,ta bishi da kallo tana nazarin kalamansa.

Kawarai hakan ya mata dadi ,saboda akwai alamun nasara . Da murna ta mike ta bishi tana murmushi ba tare da takara ce mishi komai ba ,sai kokarin masa hidima .



Denni na fita kai tsaye ya wuce gidansu farida ,a kofar gida suka hadu dukkansu hankalinsu a tashe ,,farida idanunta jawur tana ta zabgar kuka tamkar wadda akace iyayenta syn rasu. Hakan ya mummunan daga hankalin deeni ,soyayyarta ya dinga ji yana ratsa shi,yaji tankar ya jawota jikinsa ya rumgumeta ,sai dai bashi da ikon yin hakan ,don hakan sai yayi abinda yasan zai iya ya hau lallashinta tare da bata karfin gwiwa cewa ba gudu ba ja da baya yana tare da ita ,alkawarin da ya mata na aure ba fashi ,yana tare da ita.

Ta kalleshi idanu jawur sun kimbura ,ta ce

""Deeni ina zan saka raina in na rasa ka ?

" ya zanyi rayuwar da batare da Deeni ba ?yaya zan soma rayuwa da wanj namiji a rayuwa matsayin miji ba Deeni ba ??

Nan yayi saurin rufe mata baki ,idanunsa suka kada,ya dinga jin wani irin zafi da radadi a zuciyarsa.

" karki kara furta haka farida ,karki sake ambatun rayuwa da wani namiji a rayuwarki. Kinajin zan iya numfashi in ganki kina rayuwa da wani ? Farida duk runtsi,duk wuya ,duk dadi ,munabtare da junan mu. Ni ne mijinki abokin rayuwarki,in Allah ya yarda zan mutu in na budi ido naga kin auri wani namiji """

Hawayene ya gangaro mishi na tausayin kansu duka .





Sumy luv❀❀

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½



Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE





COPIED BY SUMAYYA SA'AD❀❀







11



Deeni ,farida ,ku ne da sassafe haka? Lafia kike ta kuka inata magana tun dazu baku.ma san ina gurin ba ?



A tare suka mai da kallonsu kansa,shamsu ne yayan deeni. Tuni deeni ya fada jikinsa yana kuka.

" ya shamsu kaji abin da Abba ya mun ko? Wai bazan auri farida ba ,ya shamsu kasan irin son da nakewa farida,ta yaya zan iya rayuwa babu ita ?

Itama faridan tayashi tayi tana kukan tace .

" ya shamsu ka taimakemu ,bazan iya auren wani namiji ba sai deeni,ya shamsu zan mutu inba deeni ,"

Kawai ta durkushe har kasa ta rushe musu da wani irin kuka deeni na tayata . Gaba daya suka zamewa shamsu hoto,ya bude baki yana kallonsu,yana mamaki duk da yasan irin soyayyar datake tsakaninsu ganin su cikin wannan tashin hankalin ya bashi mamaki tare da tausaya musu.

" yi hakuri farida " ya fada cikin muryar lallashi.

"" ba mai rabaki da deeni insha Allah ,zan taimaka muku , dake da deeni duk kanne na ne ,share hawayenki,mike muyi magaana."

Haya ya dunga sharewa deeni hawayenshi ,yana lallashinsu duka har suka dab fara samun nutsuwa ,anan ya tambayi deeni ya bashi labarin yadda sukayi da mahaifinsu,farida ma ta fada mishi yadda tayi da nata mahaifin ,ta kare zancen da kuka tana cewa "

Ya shamsu in deeni bai fito ba wlh Abba auramun duk wanda yakeso zaiyi,ni kuma ya shamsu deeni nake so " ta fashe da kuka .

" ya isa farida,naji "

Ya fada cikin muryar lallashi da tausayawa , a ransa yace ,"soyayya me zafi ta kama zuciyar yan yara."



Ya tausaya musu kwarai,musamman a wannan shekarun irin na su da dukkansu ba mai tunani dai dai,,haka nan duk yadda zaa musu bazasu taba fahimta ba ,sabida sun haifi soyayyarsu tun suna yara suka tashi da ita ,sukayi ta rainonta ,don haka ravasu da juna ba karamin tashin hankali bane a gare su. Don haka ya kudiri aniyar taimaka musu,sabida a halin yanzu bazasu taba fahimta ba ,abu daya zasu fahimta a aura musu juna,kafin haka ya faru kuwa sai iyayensu sun canja ra'ayinsu ,ko dai baba ya hakura yayiwa deeni aure yanzu,ko kuwa Abban farida ya hakura tabar farida har deeni ya gama karatunshi. Sai dai fa wannan abin yafi komai wahala,don kuwa in duk duniya da abinda ke cikinta zasu taru basu isa su canjawa iyayensu ra'ayi ba.

A nan ya shamsudden suka yanke shawara da deeni da farida. Cewa zasuje can Gombe su sami Bappan su suyi mishi bayani ,haka zai nemi wani yayanta ya rakashi katsina itama su sami wani yayan mahaifinta wanda in abbanta yaki amincewa shi sai ya daura mata aure da deeni,shima deeni se kanin mahaifinshi ya masa waliyyi, in yaso wurin zama gida da komai zai dauki nauyinsu akansa.



Nan take murna ta cika zuciyar deeni da farida,har ma suka haskowa juna murmushi,suna yiwa shamsuddenen godiya .

Kwarai yaji dadin ganinsu cikun farin ciki ,saboda shi dai daga deeni har farida kannen sa ne .

Bayan sun sami butsuwar ne ya tambayeta ko Abbanra ya tashi ? Don dana baba ne ya aikeshi ya ce ya fada masa yau da yamma inbaya komai yana so su hadu,akwai maganar da zasuyi .

Nab deeni da farida suka kalli juna jikinsu yayi sanyi,deeni ya ce " maganar rabamu zasuyi ko ?

Shamsu yace kwantar da hankalinka ,in ma magnar zasuyi ai mun samo mafita ko ? Kasan ko baba beji maganar bappa ba amma dai bappah zai saurare mu ,kuma ya daura maka aure ko ?

Farida ma tace ,Abban mu dai najin maganar Bappan mu,amma fa zai yi wuya ya canja masa ra'ayi , sai dai nima zai iya daura min aure "

Shamsu yace to kun gani ,karku damu,kuyi murmushi"

Nan suka masa murmushi duka,shima ya musu sannan ya shige ciki ya barsu a gurin a tsaye.

Deeni ya kalli farida yace, " Nsha Allah sai na mallake ki masoyiyata ,matsayin matata ta sunnah".

Allah ya tabbatar mana deeni,tafada tana kallon sa.

Yace , farida in yaya shamsu ya fito zamu wuce,inaso ki tuna ki sani ,duk wuya duk rintsi muna tare,farida ke tawa ce kimun alkawari.""

"" ni taka ce har abada ,ni amanarka ce""

""Farida nima naki ne har abada ""

" Mu tafi " muryar shamsu sukaji ya fito.

Nan ya dinga zolayar farida yana cewa.

" mata zankadediyar zan masa a Gombe ,sai ku zama ku biyu ;"

Ai kuwa bai ankara ba ya ga tasa masa kuka ,ba shiri ya hau lallashi har ya samu tayi shuru. Yana jinjina soyayyar da suke yiwa juna . Nan ya shige ciki ya fadawa baba sakonsa ,sannan ya ciro motar sa suka kama hanyar Gombe ,farida na tsaye tana kallon su har suka bace .









Sumy luv😍😍😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬



Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE



Copied by SUMAYYA SA'AD❀❀







12



Dab da magriba Alh.Umar ,wato mahaifin deeni ya dawo daga office dinsa,kai tsaye ya wuce gudansu farida,ya samu mahaifinta a falon sa ,suka gaisa ,suka hau tattaunawa akan kasuwanci sannan matsalolin kasarmu da muke ciki na yau da kullum har aka kira magriba,sukayi alwala suka nufi masallaci tare.

Abinci da komai tare sukaci a gidan Alh. Ahmad,wato mahaifin farida. Suna nan tare har bayan isha'i,sukayi sallah suna hira har Alh. Umar ya yi masa maganar da ainihin ta kawoshi. Sun jima suna tattaunawa akan maganar wanda ya dauke su tsawon lokaci,har kusan karfe goma na dare ,sannan suka kai ga matsaya ,suka yanke hukunci, da alama kuwa dukkan su sun amnince da hukuncin da suka yanke.

Goma da rabj sukayi sallama ya nufi gida wanda ya yi dai dai da lokacin da su deeni suka dawo daga gombe.

Alhji yayi mamakin ganinsu a wannan lokacin.

" shamsu ,deeni, daga ina haka "?

Deeni bai saurareshi ba ya kama hanyar shiga cikin gida,ya daka masa tsaqa.

" Wai bada ku nake magana bane zaka kama hanya ka shiga ciki?

Bai saurare shi ba ya cigaba da tafiya,hakan yasa Alhaji shan gabansa ya ce,,,,

"" kai saurara ,gidana kake ,magana nake maka,wa zaka gwadawa danyen kai ? Me kake ji dashi ne ? Kana tsaye a gidan nawa.............""

Deeni ya katse shi ,ya ce, " ina tsaye a gidan mahaifina ne ,bandmga kuma wanda ya isa ya hanani shuga gidan nahaifina ba ,randa na shiga gidan mahaifinka sai ka kore ni ;;""

"" Deeni !!! Shamsu ya daka masa tsawa .

"" Bakada hankaki ne ? Baban kake yiwa wannan maganar? Ban fa sanka da rashin da' a da kadabi ba , meye ya haifae da wannan rashin da'ar ?

Mahaifin nasu ya kalle shi ,"dakata shamsu,kyale ni dashi ," ya kalle deeni ya yi murmushi tare da shafa kansa ya ce ,

"" kayi gaskia dana ,nan gudan mahaifinka ne ,ba wanda ya isa ya hanaka shiga ko da kuwa mahaifin ne da kansa. Ina alfahari da hakan,da fatan kai ma zaka yi kokarin tsayawa kan kafafuwanka ka samu naka gidan na kanka ka ajiyeqa naka yaran yadda watarana zasuyi alfahari da cewa nan gidan ubansu ne ,don kuwa kai zan iya kyale k saboda kace nan gidan ubanka ne,kuma ba yadda na iya da kai tunda ni nakawo ka duniya. Amma kasani bazan bar dan ko yarka a gidana ba ,sabida kai ka kawosu duniya ,dan haka kayi kokarin nema musu muhalli kafin suzo,in ba haka ba karkayi kuka dani duj randa ba kori naka yaran a gidana na bar nawa dan,tunda gidan ubansa ne ..?

Nan deeni ya dinga jin zuciyarshi kamar wuta ,ransa bace ya shige ciki ba tare da ya sake tankawa ba . Ya fahimci sarai me mahaifin nasu ke nufi.

Alhajin ya bishi da ido yana masa daria ,zuciyarsa cike da tsananin kaunar sa. Sannan ya mai da hankalinsa kan shamsu,ya kalleshi yace .

" In shi yaro ne kai babba ne a kansa,ka dunga kula dashi kana bashi shawara me kyau,ka dai na biye masa. Karku manta ku ya'ya na ne ,ni mahaifinku ne "

Yana gama fadi ya juya ya yafi batare da ya saurari me zai ce ba ,nan shamsu ya wuce daki yana nazarin maganganun mahaifinsa tare da juya su a kwakwalwarsa.

Bayan fitar Alh. Umar daga daga gidansu farida bai jira sai da safe ba ya nufi bangaren su farida don yana da bukatar yin magana da ita a wannan daren. Ga mamakin sa kuwa ,da ya buga kofar bangarensu ita tazo ta bude masa kofa,ya lura tana cikin damuwa wanda shi ya hanata baccin ma.

Hannunta ya ja har zuwa falonshi ya zaunar da ita suna fuskantar juna ,idonta jawur ,fuskarta cike da tashin hankali. Tausayin 'yarsa da kaunarta ya shige shi,tana cikin rudani a lokacin da take da shekaru masu rauni.

" farida "" ya kira sunanta.

Ta dago kai ta kalle shi.

Menene damuwarki ?=

Menene matsalarki ? Ni mahaifinki ne ,zan miki duk wani abu da kikeso a rayuwa muddin ba cutarwa ne a gareki ba ""

Hawaye ne kawai ya fara zubo mata,don haka ya kyaleta da maganar tambaya,ya ce ,,,,

"" share hawayenki,ki kwantar da hankalinki,ki kuma sani duk wani abu da zan miki ,ko wani hukunci da zan yanke akanki ba cutarwa ba ne a gareki.

Dazu mahaifin deeni yazo gidan nan,wato Alh umar,"

Kanta a sunkuye ,sai a lokacin ta dago kai ta kalleshi ,ya ce;;;

" ya dafa mun duk abinda ke faruwa,kinsan irin mutuncin da dangantaka me karfi da ke tsakaninmu ,duk da bamu da wata dangantaka ta jini sai nakwabtaka . Sai dai fa mun dauki wannan makwabtakar da matukar muhimmancin gaske fiye da komai,ko dan uwana na jini bamu da kusanci da su kamar Alh umar . Mun daukaki juna ,kuma mun rike juna da mutunci da amanar makwavtaka. Don haka mun yanke hukuncin daura auren yaranmu ,dansa da ke 'yata ,ina fata ba zaki ban kunya ba ,za ki ban hadin kai ki min biyayya.............









Sumy luv😍😍😍😍😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬





Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE





Copied by SUMAYYA SA'AD❀❀





13





Wani irin farin ciki taji ya lullubeta ,bata san lokacin da tasaki dariya ba tana fadin.

" Nagode Abba "

Kafin ma yace wani abu tayi ciki da gudu tana tsananin murna.

Binta ya yu da kallo yana murmushi tare dabkadankai.

Tana shiga daki ,ta fada kan gado ta zari wayarta tana kiran deeni,amma layinsa yaki shiga ,ta kira har a gaji hakan ya tabbatar mata wayar sa na kashe. Amma duk da haka bata hakura ba ,haka ta dinga danna wayar har bacci ya dauke ta.





Deeni kuwa a wannan dare kwana yayi yana safa da marwa,kansa ya dauki zafi,yana tunanin yadda bappansa zai kaya da babansa,in yaji zai daura masa aure. To amma duk da haka Bappansu ya tabbatar musu da in har baba yaki yarda shi zai shige masa gaba a al'amarin aurensa. Saboda Bappan sa mutum ne me addini da sanin ilimin sanin yakamata,duk zafin mahaifinsa ba zai hana shi fadar gaskia ba da yin abinda ya kamata.

" farida insha Allah sai na mallake ki matsayin mata,sai kin zama abokiyar rayuwata,uwar 'ya'yana ,soyayyar sa mukwyiwa juna ba zai tafi a banza ba ,burinmu da mafarkin mu bzai rushe ba "b

Da wannan tunanin a ransa da zuciyarsa har asuba .

Bayan dawowarsa daga masallaci ne ya dauko wayarsa , anan ya lura ashe ma tana kashe ne. Nan yayi saurin kunnata ,don yana son jin muryar farida kafin kowa,muryarta na bashi nutsuqa da duk wani gwarin gwiwa. Dan haka ya danna sunanta,shiga daya kuwa yaji ta dauka da sauri tana haki,tamkar wacce tayu gudu.

"" farida lafia kuwa ? Ya fada a firgice.

"" haba deeni ""

Ta fada cikin muryar haki da sauke ajiyar zuciya, ra cigaba.

,"" me yasa ka boye min gaskia baka fada mun ba tsawon dare ,ka sa na kwana cikin tunani da dokin wayewar gari ?

Farida me kike fadi? Me na boye miki ?

Ban fahimta ba "

' deeni ashe baba da Abba sun amince su daura mana aure ?"

"WHAT " ya fada da karfi .

" me kike nufi ? Wa ya fada miki ? Ina kikaji ?

A jere ya mata wadannan tambayoyin .

"Hey deeni relax,kana nufin baka sani ba ?

" Ni ban san komai ba ,ba wanda ya fadamun .

Farida tace ,to nida jiya da daddare abba ya kirani ya fadamun ,yace jiya babanku yazo sunyi magana,kuma sun yanke hukuncin daura mana aure " ALHAMDULILLAH "

Ya fada da karfi tare da ajiyar zuciya ,ya ce .

_" farida wannan albishir din naki wani irin tukuici kike so na baki ? Da yardar ubangiji farida zata zamo mallaki na,uwar 'ya'yana ?

Ban san ma wacce irin murna da farin cikin zan nunawa abba ba,ya gama min komai a duniya farida ina zuwa ........"



Nan ya kashe wayar ya nufi falon babansa da gudun sa ,zuciyarsa cike da tsananin farin ciki da jin dadi mara misaltuwa. Ya same shi zaune a terrance na falon sa,hannunsa rike da jarida yana karantawa yana shan tea. Da Murnar sa ya iso yana daria tare da fadin .

""Baba ina kwana ? Baba dama na san kana so na ,ba zaka so gani na cikin damuwa ba ,you re d best father in d world nagode baba ,Allah ya kara girma da daukaka. Baba na maka alkawari i"ll do my best to prove myself,,zan yi karatu ,in tsaya da kafafuna ,zanyi duk wani abinda kakeso ,daga yau bani da wani buri ko mafarki sai na faranta maka ya babana.

Na gode da wannan gata da ka min na aura min abinda nakeso ,ka tsareni daga fadawa sharri iri iri,kamin babban gata ,ka min abinda kowani uba mai hali zai yiwa dansa. Allah ya. Kara arziki ,Allah ya barni da kai ya babana,nagode".

Kawai sai ya rungumeshi ,abin da bai taba masa ba da girmansa.

Wani irin sanyi da farin ciku yaji a zuciyar sa,tabbas yana matukar kaunar dansa Deeni fiye da komai ,ganinsa haka a jikinsa tamkar yadda yake masa tun yana dan karaminsa yawanci da yake yaro in ya masa wani abu da yake so,irin wannan rungumar yake masa,yana nuna masa yaji dadi soaai da abinda ya masa.

Tuni shauki ya dibesa ,har yaji hawaye sun cika masa ido. Shima ya dada rungumar sa tare da sa hannu yana shafa bayansa,ya ce.

'Naji dadin ganinka haka Deeni,wannan farin cikin da jin dadin da na jima inason ganinsa a fuskar ka ban ganshi ba sai yanzu ,nayi missing din wancan deenin nawa da wannan moment din a kokarina na gyara ka in sa ka a hanyar da naga ya dace da kai, kazama mutum mai daraja da kima anan muka samu sabani ,muka yi nesa da juna ,muka zama tamkae bakin juna,""

Ya dada manna shi a jikinsa tare da fadin .

"" Bari inyi enjoying wnnan moment din don ban san yaushe zan sake samun wannnan kauna da kulawa daga gareka ba haka deeni """

A zuciyar sa yake wannnan maganar ,sai dai a zahiri lumshe ido kawai ya yi yana jin kaunar dan nasa cikin farin ciki.

Muryar deeni ya jawo hankalin mama da ya shamsu da lukman zuwa inda suke ,suka tsaya suna kallon su. Mama ce ta ga abin ba na karewa bane tace .

" Deeni lafia ko ?

Nan ya saki baban da sauri ya nufe ta, " Mama "



Ya kalli ya shamsu ,ya kamo hannunsa yace ,,

" kaji baba ya amince zai aura min farida ,mama ku tayani godia wurin baba,ban san irin godiar da zan masa ba sai addu'a""

Dukkansu murna suke suna dariar ganinsa cikin farin ciki.

"" Deeni abinda zai sa ahi farin ciki ba wani abu ne wuya bane ,san shi bai dau duniyar da zafi ba,,,"" mama ta fada a ranta .

"" Dama nasan mahaifinka zai gane cewa abinda yake hanga maka da rayiwar da yake son maka ba shi ne a gabanka ba,farin cikinka yana ga abubuwa masu sauki,rayuwa mai sauki.Allah ya tabbatar da wannan farin cikin a rayuwarka ";;

Ya koma gaban mahaifin nasa tare da zama a daya kujerar dake gefen sa,ya jawo hannunsa ya hada da nasa ya manna,ya ce ,,

" Baba me kakeso in maka a rayuwa ??

Mahaifin ya kalle shi ya yi murmushi , ya ce.

". Karatu nakeso kayi Deeni ,zaka iya barin kasar nan karatu,ba zaka dawo ba sai ka gama ????????????



πŸ€”πŸ€”ANYA BABU LAUJE CIKIN NAKI KUWA A WANNAN TAFIYAR



SHIN A RA'AYI IRIN NA IYAYENSU DEENI ZASU IYA SAKKOWA CIKIN SAUKI HAKA DAMA ??



KUBIYO MU DANJIN ME AKE CIKI



SUMY LUV😍😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬





Wrirting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE





Copied by SUMAYYA SA'AD❀❀





14





Shuru yayi na tsawon lokaci,yana kallon sa ,sannan ya ce.

" Baba ban fahimta ba ""

Ya yi murmushi ya ce ," zan fahimtar da kai ,ba dai farida kakeso ba ??

Ya girgiza masa kai da ,Ehh "

"" kanason farida ,inaso kayi karatu,tunda kuwa ba sama maka farida kai kuma zaka cika min burina na ganka a cikakken likita ko ? Ya girgiza masa kai alamar eh . Yace " to nayi magana da mahaifin farida ya amince zai bar farida ta jiraka,kaje kayi karatunka ka dawo tunda har nasa baki yasan da gaske nake. Sai dai duk da haka zabi biyu na bashi ; ko ya amince sai ka dawo ,ko kuma a daura auren karshen wata baka nan jar se kadawo ta tare,da kanshi ya yanke shawarar se ka dawo din,saboda ba yadda za'ayi ka tafi da ita wata kasa kana karatau ita kuma tana zaune haka a kasar da bata san kowa ba ,haka karatinka nason nutsuwa da mai da hankali,ba gadda za'ayi ka raba hankalinka ya zama baka bata lokaci ba,haka baka bawa karatun ka lokaci ba,kaga za'ayi biyu babu.

Don haka ya amince mana na tsawon shekara biyar din nan ,dan mutinci na da kuma zumuncin da ke tsakaninmu da kuma soyayyar da

Please Login or Register in order to submit comment