Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taba hirarsu data shafi kasuwanci da kuma kasar gaba daya. Tare suma kalli labaran suna sharhi akai.

Bayan sun gama Alh Ahmad ya kalle shi ya ce .



"" ya labarin deeni kuwa ? Duk da dai muna waya da shi amma mun kwana biyu bamuyi waya ba ,yana lafia ko ?

Alhaji yayi murmushi yace ,lafia kalau,ya maida hankali yana karatu yadda ya kamata. Ina kara maka godia bisa taimako da hadin kai da ka bani ""

Alh.Ahmad ya yi daria ya ce ,"Ai deeni ya dana ne,kamar yadda ku ka riki farida kamar 'yarku haka nima na riki deeni""

Ya kara kallon sa da kyau yace,,"yanzu ma maganar yaran nan ce ta kawo ni,kan maganar da mukayi kwanaki ,kaga tsahon wata tara kenab da tafiar deeni,komai ya mike masa ya soma fuskantar karatunsa da gaske,haka nutsuwa tana kara shigar sa,din haka inaga lokaci yayi da zamu fito mu bayyanawa yaran nan da iyayensu mata manufar mu da kuma dalilinmu ,kaga watan sha biyu nakeson auren yaran nan ,kuma har da farida ciki,kaga yanzun wata biyu ya saura ,gara mu sanar dasu su shiryawa maganar auren tun wuri;""

Alh. Umar ya sauke ajiyar zuciya ,yace.

" kayi gaskia tamkar ka shiga cikin zuciyata ne,inada shirin maka maganar sai ka rigani ,inaga yanzu abinda za'ayi ,ka kira farida da mahaifiyarta kayi musu bayani,haka nima nan zan kira nawa iyalin nayi musu magana. Abinda nakeso da kai shi ne,mu tabbatar musu da maganar da muke fada UMARNI ne muke basu ,maganar mu doka ce a gare su ,dole su bita ba wai ra'ayin su muke nema ba. In munyi haka zai zo mana da sauki,amma in muku nuna ra'ayinsu muke nema zai sa mu sami matsala ,zai zamana tamkar mun vasu damar kin bin abinda muke so ne "

Alh Ahmad yayi dariya,yace,,kayi gaskia ,maganarka abin dubawa ce. Inaga gobe in Allah y kaimu zan kirasu muyi maganar,zaka ji yadda mukayi da su"

Alh. Umar ya amsa da,nima in Allah ya yarda goben zanyi magana dasu,sai mu duba ranar da ta dace mu tsayar da ranar biki"

" To shikenn ,Allah ya kaimu goben "

Da wannan. Maganar suka yi sallama ,tare da yiwa juna sai da safe akan zasu hadu washe gari bayan tashi daga harkokin su da yamma za su hadu..........





SHIN IYAYEN SU SUN YARDA ZAA AURAWA DEENI FARIDA NE KAFIN YA DAWO ????



WANI IRIN FARIN CIKI DEENI ZAI YI IDAN YA SAMU LABARIN AN DAURA AURENSHI DA FARIDA?

MUJE ZUWA 😜😜😜



.

sumy luv😍😍😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬



Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE



Cpoied by SUMAYYA SA'AD❀❀







18





Kamr yadda ta kasance da su shamsu haka ta faru tsakanin farida da mahaifinra da mahaifiyarta. Tunda ya fara musu bayanin manufar sa bai kai ga karasawa ba ma farida ta mike ta tare shi da fadin .

"Abba ba zan taba airen wani namiji a duniya ba inba deeni ba ,nayiwa deeni alkawarin kaona da zuciyata,zuciyata deeni take matukar so,don haka Abba kabar wannan maganar ta yaudara. So kike inci amanar deeni ? Kuma Abba bazan iya rayuwa da wani ba in ba deenni ba ,Abba ka taimakeni ,gara min mutiwa ta daa rasa deeni"

Mikewa yayi ya sharara mata mari sai data ga taurari.

" yarinyar banza mara kunya" ya fada yana huci.

". Ke har kin isa kiyi jayayya dani ? Yaushe kika koyi rashin kunya ? Kin san me kike fada kuwa ? Har kina fadan mutuwa da iliminki da hankalinki ,kin san meye mutuwa da har kike ikirarin gara miki mutuwa ? Me aka miki me zafi a duniyar nan haka ? Kuma ko me ya miki zafi babban sabo ne kice kin gwammaci mutuwa . Miji dai nike da hakkin zaba miki shi ko ? Ba ke ba ,don haka na zaba miki shamsu ,inkin isa in na daira miki aure da shi ki ki zama a gidansa ,sai in san ke cikakkiyar mara kunya ce "

Ta durkusa har kasa tana kuka ,baba kayi hakuri don Allah kar ka rabani da masoyi na deeni,Abba deeni shi ne rayuwata ,ban taba tunanin wani a matsayin mijina in ba deeni ba,Abba ba zan iya biyayyar aure ga kowanne namiji ba sai Deeni "

Ki daina bata yawun bakin fa, shamsu dai kin aurwshi kin gama "

Ta miki , Abba bazan auri shamsu ba sai dai ka kashe ni "

Ya kalleta cikin bacin rai ,ya ce

Baki isa ba ,idan kinason zama a gidan nan matsayin diyata ,idan kinaso mahaifiyarki ya cigana da zaman aure a gidan nan kar ki sake musu dani akan maganar auren ki da shamsu""

Maganarshi ta karshe ya mugun girgizata ,tabbas bazataso auren uwarta ya kare akanta ba . Ya kalleta,kina da zabi ,ko naki auren ko na uwarki,ina saurarwnki"

Cikin tsananin kuka da bakin ciki tace ,Abba na amince ba don inaso ba ,sai don umma,"

Ro banason sake jin komai ko wani musu akan maganar nan,munyi mun gama . Haka ko da wasa ban yarda idan kunyi waya da deeni ki sanar masa ba ,balle ya dawo ya daga mana hankali. Sai ki soma shirye shiryen biki"

Ya kalli mahaifiyarta da ta bude baki tana sauraron su cikin tsananin mamaki ,ta rasa abin fadi. Tabbas namiji halinshi sai shi .

Yace ,ki rubuto mun duk abinda ku ke bukata na bikin farida za'a siyo shi,cikin december za'ayi auren "

Yana gama fadi ya juya ya fita ba tarw da ya saurarwsu ba,haka farida ta zauna a wajen ta sa hannu akai tana ta rusar ihu tamkar wacce aka cirewa ido ko ta easa uwarta ko ubanta.

Mahaifiyarta dai bata da yadda zatayi sai lallashi da nasiha ,sai dai tabbas dole ta taya 'yar ta kukan rashin babban masoyinta . Sannan karin tashin hankalin ma wai ta auri dan uwansa?

Nan ta rungumo ta a jiki tana lallashi ,tana mata addu'a.

'Farida Allah zabi mafi alkairi"" tana fadi tana hawaye ,basu ankara ba sukaga jama'ar gidan duk sun cika falon kowa na tambayar meya faru ? Duk wanda yaji abinda ya faru sai ya tausayawa farida gami da juyayin wannan alamari,saboda kowa yasan karfin soyayyar dake tsakanin Deeni da Farida.

Haka farida ta wuni kuka ,ba ci ba sha,bakin ciki da takaici ya cika mata zuciya,tsananin kewar deeni da kaunarsa taji yana ratsa ta. Hankalinta ya mummunan tashi ,taji kwakwalqarta na juyawa tabdinga jin kamar zata yi hauka saboda kwakwalwarta ta kasa amince mata da hukuncin da mahaifinta ua yanke akanta,ta dawo tamkar wata mai jinni.

Ta mike da gudu ko dan kwali babu akanta ta nufi gidansu deeni,kai tsaye ta wuce dakin shamsu tana kwala masa kira.

". Ya shamsu"" ya shamsu ka taimake ni "

Ta sameshi ya kasa tsaye ya kasa zaune yanata zagaya dakin ,shima abin duniya ya masa zafi. Bai ankara ba ya ganta a dakinsa ba zata tamkar an jehota ,ta sunkuya ta kama kafafunsa.



Ya shamsu ka taimake ni kace baka sona,kace ba zaka aure ni ba . Yaya shamsu kaima ka sani ko ? Kasan deeni nake so,kasan ba zan iya rayuwa da wani namiji ba in ba deeni ba . Ya shamsu ina son Deeni ,ka taimake ni ya shamsu ,bazan iya aurenka ba ""

Kaka take tana ta surutai kamar mahaukaciya ,sai da shamsu ya rikota suka fuskanci juna. Kiyi hakuri farida ,an fada miki ba dole akayi min ba ne kamar yadda aka miki ? Bani da yadda zanyi sai dai bin umarnin mahaifina,bani da yadda na iya,ya zame min dole zan ci amanar dan uwana .

Deeni ya bani amanr kula da ke kafin ya dawo,zai dawo ya samu naci amanarsa ,na auri macen da yake matukar so. Farida ba abu ne me sauki ba a gareni,duk kuka da rokona da zakiyi bani da ikon canja ra'ayin mahaifina ,yadda bazaki iya kin bin umarnin mahaifinki ba haka ba zan iya kin bin umarnin mahaifi na ba ;""

Ta fashe da kuka, to ya kakeso nayi?

Kasan dai deeni nakeso ,Deeni ne rayuwata,please ka taimake ni ya shamsu ka taimake ni.

Mama ce taji hayaniyarta ,ta fito ta zo ta janyeta, yayin da shamsu ya lumshe ido hawayen bacin rai na zuba masa,yana jin kukanta na ratsa kunnuwansa,yana kuntata masa zuciya

.....







Kuyi hakuri bacci yazo yasin πŸ˜€πŸ˜€





Sumy luv😍😍😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬





Writting bySA'ADATU WAZIRI GOMBE





Copied by SUMAYYA SA'AD❀❀





Salam !!yan uwa ayi mun afuwa na rashin posting two daysπŸ™πŸΌπŸ™πŸ€Š

􏁫uma sannan naga sakonninku,kuma naji dadi sosai Allah ya bar zumunci

Ameen ..





19



A daki mama tayi ta lallashi amma inaaa!! Farida kuma take ,bata ji bata gani,bata saurare,daga karshe ta tashi ta tafi dakin deeni,ta hau bisa gadonsa tana shakar kamshinsa,tana kuka tana fada masa irin tsananin son da take masa.

Farida taba gushe ba a gurin har sai data shide ta suma a wajen,mama da shamsu sukayi asibiti da ita a rude. Da kyar likita ya samu ta karfado,,sai dai zazzabi mai zafi ya lullubeta,haka nan bata nar kukan da take ba har sai da akayi mata allurar bacci,bacci me nauyin gaske ya dauke ta .

Mama ta zuba mata ido tana kallonta,tana matukar tausaya mata tare da mata addu'a a ranta ,tana maganar zuci.

" Yarinya karama ta hadu da kaddarar da ta kasa jurewa,ta kasa tawakkali,haka nan mahaifanta sun kasa ganewa.""

Nan ta mike don zuwa tayiwa mahaifiyar farida waya ,,nan shamsu ya zauna ya zura mata ido,sai ya daina jin tausayin kansa se farida.. halin da ta shiga ya firgita shi,ya san suna matukar son juna da Deeni amma bai zaci farida na haukan son deeni haka ba. Shin taya zai rayu da macen da take matukar haukan son wani bata ji bata gani ? Taya zai iya rike amanar da mahaifinsa ya damka masa bayaan cin amanar dan uwansa da ya yi ?

Yana cikin wannan hali mahaifiyar farida da yan uwanta suka shigo,hakan yasa ya fita .

Kowa dai bashi da ikon mata wani abu sai addu'a har kusan magriba ,mahaifansu maza sukazo. Tabbas sun tausaya mata,amma hakan bai sa dayansu yaji yana da niyyar canja ra'ayi ba.

Har faridan ta farka tana kuka tana rokon mahaifinta,amma sai ya kau da kai gareta,yace,intaga bata auri shamsu ba to dayan su ba ya numfashi ne ko ita ko shi mahaifinta,ko kuma shi shamsu din . Yana gama fadi ya fice abinsa.

Daga nana farida tasawa kanta dangana,sai dai ita tasan tabbas mutuwa zatayi in tta auri wani da ba Deeni ba ,don haka ta soma shirin bankwana da duniya tana jiran ta Allah ta kasance akanta.



* * * * * * * * * * *



Tun lokaci da aka kulla maganar auren shamsu da farida duk iyayen su suka hau shirye shiryeb biki ,duk wanda yaji magnar aurwnsu sai yayi mamaki saboda kowa dai yasan farida da Deeni take soyayya ba da yayansa ba .

Tuni Alh umar ya siyawa shamsu da farida tsalelen gida na gani na fada,ba abinda bai sa musu ba na zamanj mai tsadar gaske.

Hatta kayam daki bai bukaci Alh Ahmad da yayi ba,b dakin da bai sa kaya a ciki ba ,duk wani kayan l

Kyalw kyale an sakwa farida da shamsu.

Ganin kara da kawaici da Alh umar ya masa yasa shima ya ce to ya bar wani maganar hada kayan aure ,haka nan shi ya dauki nauyin biya masa kudin sadaki. Alh umar baiki tayi sa ba ,saboda a fadinta shamsu dansa ne.

Ansa bikinsu a juma'ar farki na watan karshe.



Ranar da Deeni ya bugowa mama waya gaba xaya rudewa tayi har ya so ya fahimci akwai matsala ,amma sai ta nuna masa ba komai,tana fama da hayaniya ne ana shirin auren yayun farida wani satin ,sannann shamsu ma zai yi aure.

Ihu yasa mata na murna da mamaki ,ya ce

Mama ya shamsu zaiyi aure ? Mama kinsan ban taba ganin ya shmsu da budurwa ba sai kace me tsoron mata,amma nayi mamaki . A ina matar da zai aura take ? Unguwar mu ?

Mama tayi masa dariar da bata kai zuci ba ,tace.

Deeni kenan ,wannan tambayoyi haka,ro koma dai yana nema ko baya nema ya samu ,yarinyar unguwarmu take ,"

Ayya mama,ina farida? Tna zuwa kuwa ? Kinsan nayi ta neman wayar ta a kashe,haka layin ummanta ma baya shiga ,ina jin dai hidimar bikin suke mama,yanzu da ina nan da har dani za a hada da auren yayun ta da yaya shamsu ayi,amma ba komai mu namu mu biyu zaayi mana special one ....

Tuni mama taji t rude ,ganin shamsu ya shigo tayi saurin mika mishi wayar.

Ga dan uwanka nan kuyi magana ""

Jiki ba kwari shamsu ya karbi wayar yayi da mama ta koma gefe tana hawaye,tsananin taisayin danta ya ratsa ta ,tana tunanin ranar da deeni zai samu labarin auren farida shamsu da halin da zai shiga ,bacin rai da tashin hankalin da zai shiga ne babban fargabarta . Tasan halin Deeni da zuciyar sa,in ta kule shi ba me kyau bane ......

Oh Allah !!! Kayi mana maganin abinda ba zamu iya yiwa kanmu ba ""

Tunda shamsu ya karbi wayar Deeni ke ta masa surutu yana zolayar sa,yana masa tsiya amma yayi tsit kamae ruwa ya ci shi. Deeni na tambayar sa yarinya da zai aura yar wanj gida ce? Kuma meye sunanta?

Tuni yaji kansa ya sara,tambayar tayi masa kunci , y rasa inda zai sa kansa.ya hau masa kame kame,yayin da deeni ya dauka zafin kan aure ne ya debe shi,don hka ya kyale shi,nan ya kawo masa zancen da yafi kowanne kunci.

Ina amanata da na baka ,farida ? Ina fata kana kulamun da ita ,ya take ,a wane hali take ? Kullum sonta da shi nake kwana ina tashi ,bani da burin da ya wuce in gama karatu in dawo in auri farida............

Kafin ya kai ga ida maganar sa shamsu ya yi saurin katse wayar tare da kashewa ,saboda ba zai iya jurewa ba . Dum kunyar deeni ta ishe shi hauahin kansa da tsanar kansa ya kama shi , bai san yaushe ya sa kuka ba.............



Nace wai dan ma ba ido da ido suke magana da deenj ba kennπŸ€”





ASUBA TA GARI YAN UWA





SUMY LUV😍😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬



Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE





Copied by SUMAYYA SA'AD❀❀





20



Kwanci tashi ba wuya,bikin su farida ya matso,an gama shirin komai ,'yan uwa da abokan arziki sun gama cika gidagen duka biyu cike yake da jama'a.

Duk wanda ya kalli fuskar shamsu da farida yasan suna cikin dmuwa da tashin hankali,kowa kuwa yasan dalili ,don haka dai aka dinga binsu da fatan alkhairi.

Ana gobe daurin auren da safe mahaifin farida yayi kiranta falo,fuskarta a kode kuma a kumbure saboda kullum tana cikin kika. Nan ya sata a gaba yana mata nasiha.me ratsa jiki sosai tare da fada da kuma gargadi na taji tsoron Allah tayi biyayya ga mijinta,ta rungumi kaddarata hannu bibbiyu.

Tana kuka tayi masa godia ,tare da alkawarin zata yi masa biyayya,ya rungumi kaddara ,ta saduuda,Allah ya bata ikin jurewa.

Yaji dadi kalamanta sosai ,ya sa mata albarka sannan ya ce mata Deeni ya kira shi yana son magana da ita saboda duk wayar da zai saneta ya kora a rufe.

" Inaso in ya kiraki ki nutsu ki amsa,kar ki nuna masa komai . Sannan karki fada masa abin da bai sani ba ,kar kiyi yadda zai zargeki. Ki tuna taratu yake yi ,idan yaji wani abu yana iya barin karatun ya dawo,kuma ya samu an daura miki aure,yazo aita rigima dashi ,zhi ya rasa ki kuma zai rasa karatun ,kinga ya yi biyu babu kenn. Ni na tabbar in kina son deeni ba zaki so hka ya faru da shi ba ".

Nan ya mika mata wayar," zai iya kira a kowanne lokaci"".

Gabanta na tsnkewa ta karba tana tunanin me zata ce masa ? Ya zata yi ta fara magana da deni ?

Tana cikin wannnan tunanin kuwa ya bugo ,nan ta zurawa wayar ido da lambobin nasa tana kallo,idonta ya ciko da hawaye ,da kyar ta iya hadiye kukanta ta dauki wyar .

Murya kasa kasa tayi sallama,nan Abba ya mike ya bar falon,don ya basu wuri suyi magana.

Farida na!!!. Deeni ya fada cikin muryar shauki .

Farida I missed u so much,nayi rashinki sosai wayarki da ta umma sam ba a samu,na san dai hidimar biki ne ko ?

Lumshe ido tayi tna jin muryarsa hade da soyayyarsa mai karfi suna ratsa ta .

"Darida kinyi shuru ,kina jina kuwa ?

Ina jinka deeni,ina sauraron daddadar muryar da nayi matukar kewa ne. Deeni kunnuwa na sun jima suna son jin wannan muryar,kasan mun jima bamu yi waya ba ,wayarka ba a kira ,sai dai kai ka kira,in kuwa an kira ma za a ji baya shiga."

Jikinsa ne taji yayi sanyi,ya rasa dalili muryarta duk ya kashe masa jikj.

_" Farida kiyi hakuri ,ki kuma dada hakuri akan wanda kikeyi ,kinga yanzun mun gama jarrabawa har na samu nasarar shiga aji biyu ,kinga kuwa na fito da result me kyau irin wanda ban taba ba . Inasha Allah kamar yau ne zan gama in dawo "".

"Nayi murna matuka deeni,Allah ya baka saa ,Allah ya taimake ka. Ina nan ina maka addu'a.

" na gode farida,shi yasa nake sonki,nake kuma jin kamar duk duniya zai yi wuya a samu mace kamar ki. Ya shirin biki? Naji har da ya shamsu ma zai yi biki,ranar muna magana da shi su mama wayar ya yanke ,da na sake kira kuma bai shiga ba. Ya ce mun a unguwarmu rake ko ? Kin san wacce yarinya ce ?

Nan da nan ta rude ,ta dabarbar ce ,ta rasa inda zata sa kanta ,baki na bari ta ce.

Ban sani ba ".

Tayi saurin cewa ,baka tambayeni karatu na ba""

Haka ne fa faridana ,in na dawo zaki hada matsayi biyu ai ,mata da kuma malamata,don kuwa darasi zan dunga dauka a gurinki. Tabbas farida inna aureki nayi sa'ar mace ,'ya'yana sai sun min godia da sama musu uwa ta gari.

Kuka me karfi taji yazo mata,tayi karfin halin cewa ,

Deeni umma na kirana ,zan mata qani aikin,sai mun sake waya""

To farida na ,ya amsa .

Kullum kina tuna inasonki ,kullum sonki karuwa yake ,ina nan na rike miki amanar kaina kamar yadda kika rike mun amanar kanki".

Ba shiri ta kashe wayar ta kwanta a wurin tayi kukanta ta koshi,ta tuno gove inAllah ya kai mu war haka ta zama mallakin shamsu ,ta rasa deeni har abada.

Bayan ta fita ta mikawa Abba wayar sa ta nufi gidansu deeni ,kai tsaye ta wuce dakinsa domin yin bankwana da shi da memories dinsa. Haka ta dinga bi tana tsincs duk wani hotunanta,wasikunta da duk wani tarkacenta da zai tuno masa da ita. Duk wani gift data taba bashi sai da ta tattara . Sai dai tana da tabbacin ba za ta rasa wasu a wurin sa ba,yayin da ta dakko nata gaba daya da ya taba bata ta dawo da su. Duk randa ya dawo yaga haka yasan ehh sun rabu har abada,taci amanar kaunarsu da soyayyar da suje wa juna ,bata rike alkawari ba.

""KAYI HAKURI DEENI "

Nan tayi kuka tayi kuka har ta gode Allah,yayin da take kallon dakin tamkar yana ciki,tana ganin duk wanj shiga da fita nasu da suka raba yi a dakin,fadan su,wasan su,dariyar su da kukansu . Ta tuno da zolaya tare da tsokana irin na Deeni ,sai da tay murmushi.

Ba shiri ta dinga tuno irin ran da ya dinga daukar ta hoto ranar da zai tafi. Bata da yadda ta iya sai hkuri da abinda ya fi kardinta.

Nan ta share hawayenta ta fita,t ja kofar.

Tuni taji zuciyarta ta bushe ,hawayen idanunta ma sun bushe ,bata da sauran abinda zai kara daga mata hnkli ko sa ta kuka ko daria ,ko wani farin ciki tunda ta riga ta rasa DEENI ........





Hmmmmmm.....





Sumy luv😍😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬





Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE







Copied by SUMAYYA SA'AD❀❀





Naji dadin yadda wasu suka fahimci cewa wani baya taba auren matar wani,haka nan wata bata taba haifar dan wata ,,yayinda wasu suke ganin anyiwa Deeni rashin adalci ,,tabbas dan jin dadi kam dole deeni bazai ji dadi ba amma ku duba exactly abinda ke faruwa mana ,wlh nawa ne suke shan soyayya kuma yazama na wadda akayi dashi ba dashi ake murarta ba ......

Gareki MARIAM HASHIM naji dadi yadda kika fi kowa fahimta😍😍i am really appreciated, tnks







21



Washe gari bayan an sauko daga masallacin juma'a aka daura auren Shamsuddeen da farida,dubban jama'a ne suka shaida ,kasancewar daurin auren dana yan uwanta yasa jama'a sukayi yawa,aka cika,manya da kananan ,talakawa da masu kudin duka wannan ranar unguwar ba masaka tsinke,cike take da jama'a 'yan daurin aure,'yan uwa da abokan arziki.



Bayan daurin aure mahaifansu maza suka shirya gagarumar walima wanka aka gayyaci manya manyan malaman sunnah ,suka zo suka gabatar da wa'azi me tsoratarwa da kuma shiga jiki game da aure. Daga shamsu har farida sun sha jinin jikinsu ,wa'azin ya shige su,suka kara tabbatarwa da fa aure ibada ne ba son rai ko zuciya ba,haka nan aikin ibada zasuyi . In kuwa aka samu akasin haka za su iya fadawa ga halaka,ya zame musu dole su ji tsoron Allah ,suyi aikin auren don Allah don tsoron sa da kuma kwadayin samun rahamar sa. Anan dukkuansu suka kara sakankancewa,suka saduda,suka rungumi kaddara.

Da yamma lis aka tashi daga walimar ,jama'a suka watse ,wanda suke nesa kuwa suka koma cikin gidajen da suka zo,sai washegari su tafi ,saboda su Abba dai sunce ba wani sauran taro ko bidi'a ,wannan daurin aire da walima ya isa.



Bayan sallar isha'i Abba da kansa ya raka sauran 'ya'yansa gidajensu,yayin da farida take karshe kasancewarta kusa,nan ya kira farida ta kara jan kunnenta da taji tsorob Allah,kada ta kuskura ra biyewa wani son zuciyarta tace zatayiwa mijinta wani eashun kunya ko saba masa,din kuwa aljannatar na karkashun kafar sa,don haka ta bi a hankali tayi masa

Please Login or Register in order to submit comment