Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake,gudun maganarsu yake ko jin labarinsu. Wanda Bahijja kuma ta dage sai ya fuskanci abin ya wuce ya huya,sai dai duk kokarinta ya kauce....



Bai taba tambayarta ta tarihinta ba ,haka bai taba fada mata nasa ba,a haka suke zaune ,haka nan har yanzu bai fasa binciko labarin MISBAHA ba.........











Yaseen ya nagaji zan je hutun satiπŸ€”πŸ€”bayana ya rike😑😑











Sumy luv😍😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬









Written by SA'ADATU WAZIRI GOMBE







Copied by SUMAYYA

SA'AD❀❀❀







Assalamu Alaikum

Masha Allah!!! Bisa ga hutun zango da muka dauka ,yau Allah ya dawo damu...Nagode da kulawarku a gareni ,Allah ya kara zumunci. Masu cewa ko lafia aka jini shuru ,,,wlh lafia lau sai dai Dan Adam da baa rasa shi da wasu yan hidimomi nashi na daban ...

Sannan dan Allah ina fatan baza'a kuma samun miskila kamar yadda aka samu a baya ba ,,wannan abu nina sa kaina pls nd pls abarni murabu lafia da kowa kamar yadda aka fara tun farko....



Ina godia ga big Aunty Allah ya barmun ke bisa ga jajircewarki wajen ganin nacigaba da wannan rubutu(Aunty zee )maman nawal❀❀❀❀love u wujiga wujigaπŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜„πŸ˜„









42





Wata safiya Bahijja da Deeni bayan sunyi aiki sun gama da marasa lafia,suna zaune a (free time )dinsu ,Bahijja ta kalleshi .

''Deeni, me yasa ka ke gudun mahaifinka ? Me yasa baza fuskanci gaskia ba da abinda ya faru ? Abinda ya faru ya wuce,kayi hakuri ka yafewa dan uwanka,wannan kaddara ce,bashi da laifi . Farida taci gaba da rayuwa,tana rayuwarta da mijinta da yaranta,me yasa zaka yi ta kuntatawa kanka ?

Idanunsa ne suka kada sukayi jaa,ranshi ya mummunan baci,duk da haka bata fasa maganar ba.

Deeni (you have to let go of ur past )ba zai yiwu ka rike su a zuciyarka ba kana wahalar da kanka,please ka yafe musu....

Nan kuwa taga ya haukace mata yana zazzafa mata bala'i....

Bazan yafe ba,saboda me zan yafe ? In ma na yafe nusu kina nufin zan iya mantawa da abinda suka mun in zauna lafia da su ? Ko na yafe musu bani ba su,bana son jin maganar su a ratuwata,na tsane su,zan iya kisa idan na ganus gabana...

Ta kalleshi cikin fuskar damuwa ta tsiyaya masa ruwa mai sanyi a cup ta mika masa,tace..

Please Deeni zauna... Ya zauna amma bai karbi ruwan ba

Saurare ni Deeni,in har ka dauke wannan zafin a ranka ba zaka iya yafe musu ba ,ko tsana ne ko so je ka sake shi a ranka,ka fiddashi a zuciyarka akansu. Ganun su ko maganarsu dole ne ,dan uwanka ne uwa daya uba daya,zumunci dole kayi,Allah ne ya ce kayi.. Gaba ma ba zakayi da musulmi dan uwanka ba balle dan uwa na jini.

Farida kuwa akwai lokacin da kyakkyawar dangantaka ta hada ku,yamzu kuwa matar yayanka ce,dole ka yarda da wannan....

Mahaifinka kuwa in kayi fada da shi baka da riba ,duk kai zaka sha wuya kaita wahalar da kanka...

Kayi hakuri Deeni,Allah zai baka ladan hakurin da kayi,ya kuma baka sakamako mai kyau a duniya da lahira....

Tana maganar kamar zata zubar da hawaye....

""kamar kani kake a gareni ,ba zan so ganin kanina cikin wannan halin ba...

Tsura mata ido yayi yana kallonta,maganarta na ratsa shi,haka nan ya dinga jin maganganunta na masa tasiri a zuciyar sa ,yaji zuciyar sa ta sauka ,tayi sanyi..

Ya dauki ruwan sanyin yasha ,ya kalleta ya mata murmushi tare da mika mata tissue.

"" Gashi ,share hawayen da ke shirin zubo miki,kar su zubo in miki tsiya nan gaba.......

Murmushi tayi ta amsa,"Deeni ba zaka canja ba,tashi yau kaine best student koyarwar da na maka ya shiga kwakwalwarka da zuciyarka,don haka yau da kai zamuje outing..

Yayi daria ,"yau ta ina rana ta fito Abokiyata DoctorBahijja zata fita dani yawo ??

Murmushi tayi bata kulashi ba ,taje ta dauko mota ya shiga suka fita...

Kai tsaye suka wuce asibitin gwamnati na garin suka dinga bi tana nuna masa marasa lafiya,wasu gasu nan kwance cikin azabar ciwo ba lafiya wasu ga ciwo ba kudin magani,wasu na son yin ibada da sauran ayyuka ba lafiya. Abin tausayi kala-kala da ya fara sa jikin Deeni mutuwa,daga nan suka wuce sauran asibiti na masu kudi su kuma ga kudin ga komai amma lafiya da saukin Allah bai nufa ba...

Daga nan suka zarce gidan marayu,marasa galihu ,masu neman taimako basu da kowa bansu da komai sai Allah, sai abinda gwamnati taga dama ta san musu,suna watse basu da mai tallafa musu,ba uwa ,ba uba da zasu lallashe su,basubda wanda suka damu da su da rayuwarsu. Anan Deeni ya ga abun tausayi sai da ya zubar da kwalla...

A mota duk jikinsa yayi sanyi ,Bahijja ta kalle shi tace,

"" Yaya bakin cikinka da dacin ranka yake da na wadannan bayin Allah ? Baka ganin ni'imar da Allah ya maka,kana da lafita da karfinka da gatanka da iyayen da suka damu da kai...

Anta baka ganin matsayin iyaye ya kai suyi mana yadda suke so ko da bata mana rai ne suna da hakki?? Deeni rayuwar nan tayi kadan mutsaya muna bata lokacin mu akan wani bacin rai ko tsana,gaba ko wata kiyayya...

Ka godewa Allah da ni'imomin da ya maka,in ya jarrabe ka sai kayi kokarin ka ci jarrabawar . Ka yarda da kaddara,ka saki ranka kayi hakuri Allah yana tare da masu hakuri(innallaha ma'assabirin😭)...

Yayi murmushi idon shi jawur,hawaye ya gangaro masa,ya ce.

"Nagode Bahijja ,tabbas kin cika abokiya tagari,likitan da tasan hakkin patient dinta,sannan ke mutumiyar kirki ce,Allah ya miki sakayya da abinda kika mun. A yau kinsa naji wani kunci da nauyi ya bar zuciyata ,duk wani fushi da kiyayya da nake ji a raina ya tafi .......

Tabbas nayi nadamar bata lokacina da nayi,sai dai insha Allah zan gyara gaba ,daga yau,daga yanzun nan Deeni ya zama sabon mutum wanda ba ya rike da kowa a zuciyar sa,ba ya fushi da kowa. Ina jin zuciyata fara , zanyi kokarin gyara rayuwata da tsakanina da iyayena da 'yan uwa na...



Yau ce rana ta farko da nakeji da son fuskantar yaya Shamsu da Farida ba tare da wani bacin rai ko tsanar su ba, na yarda na amince haka Allah ya hukunta mun. Na gode Bahijja ...

Lumshe ido tayi hawaye na gangara wanda bata san yaushe suka zo ba ,tana fadin..Alhamdulillah "".. A ranta..ya tsura mata ido yana kallonta,kamar wata bakuwa ko sabon halitta,kaunarta yaji ta shiga ransa,haka yana bata wani girma na musamman. Ta mike,"Yau ranar farin ciki ce garemu da ni da kai,sai godiyar Allah .yanzu saura guri guda zan kaika,ina fatan zaka ji dadin zuwa wurin ""

" Me zai hana ?" ya bata amsa ..

""Musamman inda ke a wurin..

murmushi tayi ta girgiza masa kai suka tafi..

wani tafkeken farm house ta kaishi na (lagos state government )ba abinda babu ciki,kaji ne,dabbobi ne ,shuke-shuke ne,tsuntsaye ne,kala kala a wurin ..

Wani farin ciki da jin dadi ta gani ya bayyana a fuskarsa,ya dinga ratsa cikin gonar yana bin kan dabbobin dabtsutsayen yana shuke-shuken dake wurin sun matukar burge shi, bai san lokacin da ya fara dariya shi daya ba. Irin abin da yake so yaga ya yi,ya kafa a rayuwar sa. Ga bishiyoyi,ga shuke-shuken 'ya'yan itace kala daban -daban ...

lumshe ido yayi ya ware hannun yana shakar iskar wurin yana jin yana ratsa shi,yana jin wani irin tsananin dadi a ransa irin wanda ya jima bai ji ba.

Zuwa tayi gabansa ta harde hannu tana kallonsa tana murmushi,tana jin dadin yadda ta ga tayi sanadin kawo farin ciki a rayuwar sa. Nan ta dinga jin wani irin farin ciki a ranta ,wannan dama shi je burinta a rayuwa ta ga tana sanya dariya da farin ciki a rayuwar mutane ,anan take samun nata farin cikin da nutsuwa da jin karfin gwiwar cigaba da rayuwa.......





sry nasan zaku iya samun mistake ko typng erro ,,wlh typing din dare nayi kuma ban kuma bi nayi editing ba kawai nayi posting,,wlh nagaji ne kuma burina kawai nima inga yau nasaku farin cikii (kamar dr da patient dintaπŸ˜›πŸ˜›)

Tnks









Sumy luv😍😍😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬









Written by SA'ADATU WAZIRI GOMBE







Copied by SUMAYYA SA'AD❀❀







43



Kamshin turarenta yaji iska ta debo yana sauka kan fuskar sa yana shaka yana ratsa jiki da zuciyarsa,yana shiga yana ratsa shi. Soyayyar tace mai zafi da sanyi tare da dadin gaske yaji yana shiga yana kama zuciyarsa da dukkan ilahirin jikinsa yana ratsa shi tare da saukar masa ds wani irin farin ciki da ni'ima mai dadin gaske.....

"Alhamdullah",Allah na gode maka."

Ya bude ido yaci karo da fuskarta tana masa murmushi,shima ya hau mata murmushin Suka kyalkyale da daria duka,tace. "Wow! In kayi dariya kana cikin farin ciki (u rilly look great)"".

Ya kalleta,"(thanks to u )Bahijja."

Ta girgiza kai,"Mun godewa Allah,don haka Mr. Deeni daga yau kasan inda ka kama,kasan inda kasa gaba,(u belong here)...... Ta nuna masa gonar.

Ba gidan magani da allura ba,duk da likita kake amma kafi kyau da dacewa da nan gidan gonar,inda farin cikinka,jin dadinka da passion dinka yake,to me zaka jira? Ko ka nemi aiki anan ko kayi kokarin bude naka,duk wanda kakeso zaka iya""...

Yayi dariya," Na gode da shawararki ,tabbas a nan passion dina yake ,(thank u so much)Bahijja . Daga yau din nan na miki alkawarin bude sabon rayuwa ,kuma zan fara yin wani abu me ma'ana da rayuwata insha Allah.

Amma ina so ki min wani alkawari, ki zama abokiyata mai ban shawara ,yayata kuma mai guiding dina...""

Tayi murmushi ,"Insha Allah ,Allah ya yi mana jagora duka".

Ameen "Ya amsa tare da fadin .

""Sannan zaki bani littafin nan na MISBAH ,kuma zaki zama ABOKIYAR RAYUWATA...""""

Ta dalla masa harara ,"Abokiyar rayuwarka kadai? Ka manta har ABOKIYAR MUTUWARKA ma zan zama .."

Ya yi dariya ,"yauwa my Bahijja'"..

Wucewa tayi ta fita ta wuce mota ,har ta saba da halinsa na zolaya. Ya bita har ya shiga suka tafi yana zolayarta.

Har gida ta kaishi ta ajiyeshi,ba yadda bai yi ba ta shiga ta ki,ta ce ya gaida hajiya. Anan ya karbi numbern wayarta sukayi sallama.



Kai tsaya ya wuce falon mahaifinsa,anan ya same su duka har lukman kaninsa,yana dariya ya gaishe su. Kallo daya zaka masa kasan yana cike da tsantsar farin ciki.

Ya zauna kusa da mahaifinsa tare da kwantar da kansa a cinyarsa.

"Baba ka yafe mun"

Alhaji Umar ya dinga ji da ganin Deeni kamar a mafarki,sai da hawayen farin ciki ya zubo masa bayan shekara takwas zuwa tara Deeni ya fito daga kejin da ya shiga...

Mahaifinsa ya kalleshi,Deeni Alhamdulillah ,tsantsar farin cikin da nake ciki bnsan iyakarsa ba. Nima ka yafe mun.

Mama dai ta kasa jurewa sai da tayi kuka,farin ciki da jin dadin da suka tsinci kansu a ciki,sai godiyar Allah. A nan Deeni ya tabbatar musu da ba zai taba sake daga musu hankali ba.

"Zan yi biyayya a gare ku insha Allah"".

Alhaji ya kalleshi,ya ce,"Allah ya maka albarka Deeni,nima na muku alkawari dukkan ku 'ya'yana ba zan sake shiga rayuwarku ba,kowa yayi abinda yakeso duk da nasan nayi latti duk kun gama karatu..

""Baiyi latti ba Baba ."Deeni ya katsae shi.

Ko a yanzu zaka iya yin abinda nake so,ina fatan zaka taimake ni kasa mun albarka."

Insha Allah Deeni sai inda karfina ya kare..""

Yace,"Wannan yarinya likita Bahijja Allah ya mata albarka ..

Mama ta kalli Deeni ,"Zaka kaini jar gida insa mata albarka.

Yayi dariya ,"To mama ko yanzu ma in kin shirya".

Tayi dariya ,*ba yanzu ba sai gobe "

Alhaji yace,"Nma ba za a barni a baya ba""







Washegari bayan sallar isha Deeni ya tuka su zuwa asibiti wanda anan gidan Bahijja yake,suka yi tambaya don kuwa Deeni bai taba zuwa gidanta ba.

Sun samu baba andi ta ce bari ta shiga ciki ta mata magana,anan Deeni ya mike yana zagaye falon nata dabyadda ta tsara shi yana murmushi yana jin sonta na kara tasiri a zuciyarsa,soyayyar Bahijja na shigarsa yare da saka masa wani irin tsananin farin ciki da jin dadi.

Yana tafiya yana zagaye wurin har ya hango gurin da ta kebe mai kama da (libry)anan ya hango hotunanta da mijinta da danta suna rumgume da juna,ya zurawa hoton ido yana tuno Dr. Mislihu . Sai a lokacin ya fahimci mijinta ne.

Wani dan madaidaicin (diary)ya gani da biro a hade alamar bata jima da yin rubutu ciki ba,haka zuciyarsa ta dinga azalzalarsa ya bude ,yana kwadayin sanin komai game da Bahijja. Nan ya yi karfin halin budewa duk da yasan hakan ba dai dai bane.

Abu na farko da ya fara gani yaji zuciyarsa tayi mummunan tsinkewa shi ne,(To my dearest wife MISBAH).

""MISBAH ? Ya maimaita a ransa ..

Bai bata lokaci ba yaci gana da karantawa,sai lokacin ya lura da diary din da marigayi mijunta ya rubuta mata ne,yana fada mata irin muhimmancinta da soyayyar da yake mata gami da yabonta na ayyukan kwarai da take,yana mata addu'a gami da sa mata albarka.

Nan ya rufe ido yana kokarin tuno inda yake ganinta da diary din nan mai kama da littafi,da lokacin da take zuwa gidansu wurinsa,da kuma asibiti,in tana zaune bata da komai takan dauko littafin tana karantawa ...

Sannan wannan shine littafin da ta rike da sunan tana karanta masa sabon littafin MISBAH.

"Wato Bahijja ita ce MISBAH"". Ya maimata.

'Author din da nake so tun ba yau ba ,Author din da na hada (special bond ) da ita tun lokacin da na fara karatun littafin ta a rayuwata,Bahijja abokiyata wacce take yanzu masoyiyata ita ce MISBAH na da na jima ina so ina kauna? Wow ! Bahijja na ita ce MISBAH na ..""

Kaunarta yaji yana dada tsuma shi,yana ratsa shi..



**Ke din daban ce special ce tunda har kika iya min dabara ,ni kika mayar marar wayo ? Ni kika fooling,wato dama wannan labarin kirkirankika yi a lokacin shi yada na nemi lityafin nan sama da kasa na rasa,ashe dama yana boye ne a cikin kwakwalwarki. (I love ur smartness)ina sonki Bahijja 'yar Baiwa,MISBAH na . Sai yanzu na fahimci labarin rayuwata da kikela yi kokarin hada min naji yana shiga ta,naji labarin ya tsaya mun a rai . Na so inji karshen sa ko zan samu in warware nawa matsalat..""

Ya yi murmushi yana kallon hotonta ,""labarin da kika fara ni zan karasa miki,ba ni kika fooling ba ? Jiya kiga yadda zan fooling dinki...""

Nan ya yi ta ganin takardunta a wurin daban-daban da irin article din da tayi ta rubutawa.



MISBAH na 'yar baiwa ce ,Nsha Allah zan zama ABOKIN RAYUWAR ki da MUTUWARKI kamar yadda kika fada,zaki ga yadda zan kawo farin ciki da canji a rayuwarki"

Ya yi murmushi ya ce,""Yayata Bahijja,Abokiyata,masoyiyata MISBAH .""

Nan yasa hannu ya dauki littattafan da yake so,sannan ya dawo gun su mama ya samu Baba Andi ta gabatar musu da abin motsa baki,yasa hannu ya dauki apple yana ci yana lumshe ido ,yana jin kamshin Bahijja ko ta ina a gidan .

Baba Andi tace,"kuyi hakuri na samu ta fara sallah ne .""

Mama tayi murmushi ,""Bakomai"

bata rufe baki ba kuwa Bahijja ta fito da fara'arta lullube da hijab,tunda ta shigo falon idonsa ke binta,ya zurawa fuskarta ido me cike da kamala da annuri ,murmushin dake kan fuskarta ya kara haska fuskarta ,yaga ta masa wani irin kyau da kwarjini......

Wani irin SO me karfi yaji yana shigar sa,Son da bai taba tsammanin akwai irinsa ba ,ashe da wasa yake ba so ba,MISBAH ita ce so,ita ce SHAUKI. kallonta na kara masa son rayuwa,yana kara masa tsammani ,yana sa shi wani irin farin ciki da nishadi............







he's inlove again πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»







πŸ€”πŸ€”πŸ€”πŸ€”amma anya kuwa Deeni baya zurfafawa dayawa a soyayya ??



Shin Bahijja zata karbi Deeni kaninta a matsayin masoyi ???



wani hali Deeni zai kasance idan Bahijja taki amincewa a karo na biyu???



sai munji ra'ayoyinku...







taku har kullum......







SUMY LUV😍😍😍

πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬MISBAHπŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬πŸ‘©πŸ½β€πŸ”¬











Written by SA'ADATU WAZIRI GOMBE









=================== GIDAN NOVELS ====================================





44







Yadda Deeni yaga tana gaisawa da su Mama da Baba suna ta hira cikin kaunar juna da kulawa ya kara masa jin dadi da nutsuwa,haka yake burin ganin matarsa da iyayen..

Bahijja ta mai (a kallonta kansa,ta lura ya tafi wata duniya. Biron dake hannunta ta jefa masa tana dariya ,ta ce.

'"Abokina Deeni,wacce duniyar aka tafi??

Yayi mata murmushi,ya ce,"Duniyar abokiyata Bahijja,gidanki ya mun kyau ,ya birgeni ,musamman (libry)dinki,cike yake da irin littattafan da nake so""

Ta zaro ido tana kallon sa,"Kaji min yaro ,daga zuwa gidan mutane har kasan hanyar (libry)dinsu ??

Ya yi mata muryar tsokana ,yace,"Ba gidan mutane bane ,gidan Abokiyata fa Bahijja ne. Sannan kin manta lokacin da kike zuwa nawa dakin kina mun yadda kike so ? Yanzu lokaci na ne."""

Tace,"" Gidanku gidanmu ne ,ko mama?

Mama ta girgiza kai,"kwarai """.

Ta kalli Deeni tana masa gwalo,ta ce.

"Gidana kuwa gidana ne ni daya,Baba Andi daga yau in yazo kar ki bude masa kofa ..""Baba Andi tayi dariya tace,"Ni na isa in shiga tsakanin yaya da kaninta ?? Deeeni yayi dariya,ya ce ,"Yawwa Baba Andi, daga yau kin zama babbar abokiyata,zan shigo inyi yadda nake so gidan yayata..""

Bahijja tace,"In kuwa kayiwa yayarka barna zaka sha bulala."

Dariya sukayi duka har da Alhaji,Mama ta kalleta tace.

" Allah ya miki albarka 'yar nan "

Ameen Maama."ta fada kanta sunkuye.

Tace,"kuyi ta mna addu'a mama,kuna sa mana albarka,insha Allahu Allah zai taimake mu..

Deeni ya kalleta yana dariyar tsokana,zuciyarsa cike da sonta ,yace.

"Allah ya miki Albarka 'yar nan ......

Ta hararebshi ,"Mama kinga yaron nan ya raina ni."

Alhaji ya kalleta yana murmushi ,ya ce .

Zan baki bulala ki dinga zane shi."

Suka yi dariya duka,tace,'Yauwa Baba,gara in fara zane shi don naga girman jikinsa na yaudararsa...

Deeni yace,"To wata ma tayi girman jijin mana

Mama tace,"Deeni naga alama nima zan fara maka bulalar.."

Nan suka yi ta dariya suna hira har wurin karfe tara sukayi niyyar tafiya,Bahijja ta raka su har mota. Ta lura da wani irin mayataccen kallo da Deeni yake mata,haka ta ganshi cikin tsananin farin ciki. Sai dai bata zurfafa tunani ba ta kau da abin a ranta amma ta rasa me yasa kallon yake yawan fado mata rai(πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»)...





***** ***** ****



Deeni da iyayensa suka ziyarci su Shamsu tare da sauran dangi,Shamsu da Farida kam sunsha mamakin ganin yadda Deeni ya ware har abinci ya zauna suka ci tare da shi da Faridan da yaransu ana wasa da dariya..

Tun Farida najin wani iri ,tana takura har ta ware tana kallonsa tana mamakin ganinsa haka. Ya kuma nuna mata shi dan duniya ne ,ya dinga janta da hira,"Aunty Farida kaza ,Aunty kaza akayi." Tun bata da niyyar sakewa har ta sake..

Deeni kuwa har cikin ransa ya gama da farida da tunaninta ko soyayyarta,a halin yanzu duniyarsa,farin cikinsa da shaukinsa yana ga Bahijja.

'yan uwa da abokan arziki kowa ya yi murna da sabon canjin da aka samu daga Deeni. Farida ta masa murna sosai ,amma sai ta tsinci kanta a cikin wani bakon yanayi na rasa soyayyar Deeni da tayi,sai a lokacin ta kara fahimtar abinda yayi,addu'a tai tayi har ta samu saukin abin. Saboda ita har yanzu cikin kasan zuciyarta akwaii Deeni a binne ,sai dai zata ci gaba da jurewa da kuma rungumar rayuwarta da mijinta da 'ya'yanta ,ba zata taba tono shi ba.





A cikun wannan lokacin Deeni da mahaifinsa suka yi ta shiga da fita da buge bugen neman makeken fili a kusa da asibitin Bahijja don ann ya cewa mahaifinsa yake so ya yi gidan gonarshi. Shi dai bai tambayeshi dalili ba,ya biye masa don yanzu duk abinda Deeni ke so shi ake masa,da sauri ma kuwa. Shakuwa da soyayya ta musamman ta shiga tsakaninsa da mahaifinsa,gaba daya Deeni ya dawo sabon mutum..



Abinka da masu gidan rana ,lokaci kankani aka gama ginawa Deeni gidan gonar sa,aka daukar masa ma'aikata masu taimaka masa da komai. Duk wani abinda yake bukata an sa masa ciki,a hankali wurin ya dinga habaka yana yiwa Deeni yadda yake so..



Irin farin ciki da jin dadin da ya tsinci kansa a wannan lokaci ba a magana ,yayin da ya sako Bahijja gaba da nasa salon tsokanar wanda ya samo. Wata number ya samu yana tura mata text message.



Tana zaune office dinta tana karance karance taji wayarta tayi kara alamar shigowar sako,ta dauka ta bude. Gabanta ne ya ba da rass!!

"MISBAH""

Shine abinda taga an rubuta.

Tayi bala'in rudewa saboda duk duniya mutum daya ne yasan ita ce MISBAH ,wanda yanzu baya duniyar.

Kafin ta gama fita daga wannan rikicin ta sake ganin an turo mata wani.

(I knw u re my MISBAH).

Mikewa tayi tana sake maimaita sakon a ranta,mamaki ya bayyana karara a duskarta,nan tayi saurin mai da amsa.

"Waye kai?(wrong number)

ya bata amsa da ,"In wrong number ne me yasa kika tambayeni ?

Nan tayi saurin kiran layin,amma sai taji a kashe ,tayi shuru tana tunanin duk wanda yayi abin nan yasan yadda take tunani,yasan zata kira ,to waye ne ? Ko da wasa bata taba kawo Deeni a zuciyarta ba,asali na ta kasa kawo kowa a ranta. Haka tayi aikin wurin da abin a ranta.

Tana sallama gidanta kuwa wani sakon ya shigo.

"Allah ya hice gajiyarki my MISBAH ""

Yanzun abin ya fara taba mata rai ,wa ce ko wane dan rainin wayon ne ?

Tayi tsaki ,zata wuce ciki taji muryarsa.

"Haba madam Bahijja ,wucewa haka ba kya duba gabanki ? Tun dazu nazo ina jiranki,awa na guda na samu Baba Andi itama har ta gaji ta tashi,amma ni ban gaji da jiranki ba. Haba abokiyata."

Bahijja ta harare shi,"Gama cin abincin ka sha ruwa maza kaje gida kayi wanka ka kwanta kayi bacci,kana da aiki gobe..""

Ya yi saurin mikewa ya sha gabanta ,"Wa kike cewa yaro ? Wai an fada miki shekara talatin wasa ne ?

" Matsa ni kaban wuri,talatin din har wata kayan gabas ce ? Akai na dai talatin dinka na komai bane.."

Har ta soma tafiya ya sake shan gabanta ya harde hannu tare da shan mur ,ya kafa mata idanunsa.

' Waye yaro ?

Muryarsa da irin kallon da yake mata duk suka rikitata ,ta rasa

Please Login or Register in order to submit comment