Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yarima yazid
ya numfasa yace nayi hakane saboda na nunawa
duniya cewa tafarkin da kuke kai ba shine tafarkin
gaskiya ba,tabbas kuna cikin bata mabayyani
yanzu gashi ka kamu da cutar da kowa yake
ganin cewa babu yadda za'ayi ka warke harka
tsira da rayuwarka,kwana da kwanaki kana
kwance
kamar gawa ba ci ba sha,ba magana,ba motsi da
bude ido saboda bakin sihirin dake jikinka amma
gashi yanzu farat daya da taimakon ubangijina na
tasheka zaune harma ka iya budar baki kayi
magana alhalin kana jiran mutuwarka ne nan da
cikar kwanaki kadan.
Shin wannan bai isa yasa kayi imani cewa babu
abin bautawa da gaskiya ba face ubangijin
musulunci?
Koda yarima yazid yazo nan a jawabinsa sai
sarki Aiyuba ya bushe da dariya.
Al'amarin daya baiwa su gimbiya nauwara
tsananin mamaki kenan,sarki Aiyuba ya sake
yunkurawa da kyar ya mike zaune batare da an
taimaka masa ba sannan ya dubi yarima yazid
yace,kai yazid yanzu kai kana ganin cewa zaka
iya kareni daga kaddarar da ababan bautarmu
suka shirya a kaina,kabar ganin cewa ka tasheni
a yanzu har na iya magana da motsi,ina mai
tabbatar maka da cewa ruhina yana can a dajin
Hajrul Aswad a hannun ababan bautarmu,kuma
ajikin wasikar jini,idan har kanason ka ceci
rayuwata to saidai kaje ka yaki dukkan allolinmu
dake cikin kogon dajin hajrul aswad ka kashe su
su dari tara da casa'in da
tara,sannan kuma ka kone WASIKAR JINI yadda
har abada ba zata sake yin tasiri ba.
Ina mai tabbatar maka da cewa idan ka nufi dajin
hajrul Aswad da wannan manufa saika hadu da
mugayen masifun da zasu shallake
tunaninka,kuma babu yadda za'ayi ka iya tsira
daga wannan masifu bare har ka iya isa kogon
Hajrul Aswad ka kashe allolinmu ka kone
wasikar jini.
Baya ga wannan kayi sani cewa ko masifar da
zaka fuskanta daga dan uwana waziri Ridwan
wanda yake son ya gaje wannan karagar mulki
tawa ta isheka domin bazai taba bari ka sami
nasara ba.
Lokacin da sarki Aiyuba yazo nan a
jawabinsa sai yarima yazid yayi murmushi a karo
na biyu sannan yace,naji yarka tace kabar mata
wasiyar zainur yayi amfani da duk shawarar dana
bashi me yasa kayi imani da hakan alhalin kuma
yanzu gashi ka kasayin imani da abinda zan iya
aikatawa?
Koda jin wannan tambaya sai jikin sarki Aiyuba
yayi sanyi ya sunkui da kansa kas sannan yace
nayi hakane
saboda ni na fison na mutu akan tafarkin da
iyayena da kakannina suka mutu amma ina
sha'awar 'yata ta mutu akan naka tafarkin.
Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa
gimbiya Nauwara ta dubi sarki Aiyuba tace haba
yakai Abbana ashe yanzu baka so
ka cigaba da rayuwa tare da ni hat kaga
'ya'yanka da jikokinka?
Koda jin haka sai hawaye ya zubowa sarki Aiyuba
yace yake 'yata kiyi sani cewa na dade da cire
wannan buri daga cikin rayuwata saboda tuni na
bayar da jini na ga ababen bautarmu kuma nasan
cewa bazan kai lokacin da zakiyi aure ba.
Koda jin haka sai Yarima Yazid ya tari numfashin
sarki aiyuba yace yanzu idan na tafi izuwa dajin
hajrul aswad na tsallake duk masifun dake kan
hanyar naje na hallaka ababan dogaronku kuma
na kone wasikar jini na dawo nan gareka a raye
cikin koshin lafiya
kuma kaima na iske ka araye zaka karbi addinina
kayi imani da ubangijin musulunci?
Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa
sarki aiyuba yace,yakai wannan dan sarki kayi
sani cewa a zuri'ar mu babu abinda yafi alkawari
muhimmanci don
iyayena shekaru arba'in da uku da suka shude
abinda nake nufi shine tun ina da shekara bakwai
a
duniya na yiwa mahaifina alkawarin cewa zan rike
addininsu da al'adarsu,kuma zan mutu akan
tafarkinsu,ko a yanzu a cikin zuciyata nasan cewa
addininka shine addinin gaskia,kuma koda kaje ka
samo wannan nasara ka dawo ka riskeni a raye
cikin
koshin lafiya bazan karbi addininka ba.
Lallai saina mutu akan addinina don cika alkawari
ga mahaifina da kakannina,amma ina mai umartar
'yata gimbiya nauwara data karbi addininka
saboda a kawo karsehn wannan bakin addinin
namu da kuma bakar
al'ada.
Kayi sani cewa ban san iyakar rayukan dana
dauka ba don cika umarnin allolinmu da biyan
bukatunsu,bansan iya adadin jama'ar dana
zalunta ba,ko don saboda wannan babban dalili
dana
dauka a doron kasa,lallai inason na mutu akan
tafarkina domin shine kadai horon daya dace
dani.
Yake 'yata na sani cewa daga kuruciyarki kawo i
yanzu baki taba kashe koda kwaro ba da
hannunki,baki taba zaluntar wani bil'adam ba don
haka ne nayi miki
sha'awar shiga wannan addini mai adalci saboda
ya dace dake kuma inason anan gaba keda
zuri'arki
kuyi rayuwa mai inganci wacce zaku amfaneta
duniya da lahira.Koda gama fadin hakan sai sarki
aiyuba ya kamo hannun yarima yazid sannan ya
kamo na gimbiya nauwara ya hada waje guda ya
dubi yazid yace daga yau na sauke nauyin dana
dorawa dan'uwan nauwara wato zainur na
dorashi
akanka yakai yazid Bin Arsanal,na bar maka
amanar 'yata,lallai ka shigar da ita cikin
addininka mai tsari kuma ka shafe addinina da
makiyana daga doron kasa,wannan ce kadai
hanyar da zaka iyabi ka yada naka addinin a
wannan nahiya gaba daya.Wannan
shine kalamaina na karshe a gareku ina maiyi
muku fatan sa'a da nasara amma tabbas ni kam
tawa ta kare,lallai bazaku dawo ku riskeni a raye
ba.
Koda gama fadin hakan sai gimbiya nauwara ta
rungume sarki aiyuba ta fashe da matsanancin
kuka,shima saiya kama kukan a lokacin da
tausayinsu ya turnuke yazid,zainur da sauran
hadimai suma suka kama zubar da hawaye.
Bayan sarki aiyuba da gimbiya nauwara sun dan
jima a kankame da juna sai ya cire jikinsa daga
cikin nata sannan ya dubeta a lokacin da hawaye
ya zubo masa yace,daga yau gidan nan ya
haramta a gareni har sai bayan kun
dawo daga dajin Hajrul Aswad a cikin nasara.A
sannan zaki iya hawa karagar mulki.Koda gama
fadin hakan sai sarki Aiyuba ya koma kan
gadonsa ya kwanta yana mai yiwa Gimbiya
Nauwara kallon
karshe a lokacin data kura masa idanu tana zubar
da hawaye.Nan Yarima Zainur ya kamo hannunta
ya jata suka fice daga cikin turakar sarki tana
waigensa shima yana zubar da hawaye.
SHIN SU YARIMA YAZID ZASU ISA KOGON DAJIN
HAJRUL ASWAD A RAYE SU DAUKO WASIKAR
JINI?
WANE IRIN MUGAYEN MASIFU ZASU HADU DASU
AKAN HANYA KAFIN SU ISA CAN?
TSAKANIN WAZIRI RIDWAN DA YARIMA ZAINUR
WAYE ZAI GAJI SARAUTAR?
INA LABARIN SARAUNIYA LAZWARA?
SHIN ITAMA ZA'AYI WANNAN TAFIYA NE TARE
DA ITA?
MENENE DALILIN DA YASA LOKACIN DA GIMBIYA
NAUWARA DA YARIMA YAZID SUNA GANIN JUNA
SAI ZUCIYOYINSU SUKA BUGA DA KARFI?
INA LABARIN ARDADU KUWA?
WAISHIN KUWA INA SARKI MARWATU?
Mu Hadu A Wasikar Jini Littafi Na Shida domin
jin cigaban wannan kasaitaccen labari.
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Shida (6)
Part A
.
Al'amarin Ardadu kuwa lokacin daya isa wannan
gida inda su barde Uraidu suke dauke da taswirar
zuwa dajin Hajrul Aswad cikin tsananin farin ciki
bisa sanin cewa shi kam ya gama arziki na
duniya bashi ba talauci,sai aka bude masa kofar
gidan ya shige ya isa har can ciki inda barde
Uraidu ke
zaune.Koda barde Uraidu yaga Ardadu ya shigo
fuskarsa cike da annuri sai shima farin ciki ya
lullubeshu saboda ya san cewa ya samu nasara.
Cikin zakuwa Uraidu ya taso daga kan kujerar da
yake zaune ya tari Ardadu yace ina abindana
umarceka da samowa,shin ka dace?
Koda jin wannan tambaya sai Ardadu yayi
murmushi sannan kuma ya murtuke fuska yace ta
yaya zan mika maka wannan abu mai daraja
alhalin banga cikon alkawarinmu ba.
Koda jin haka sai barde Uraidu ya bushe da
dariya sannan ya dubi wadansu dakaru nasa.Nan
take dakarun suka shiga cikin wani daki suka fito
da wadansu manyan akwatuna guda hudu na
karfe.Koda aka bude akwatunan saigasu cike taf
da lu'u lu'u,koda ganin wannan dukiya sai Ardadu
ya zaro taswirar daga cikin aljihunsa ya nunawa
barde Uraidu,sannan yayi wuf ya dauko wata
fililar wuta ya rike ya dubi Uraidu yace idan
kukayi wani yunkuri na yaudarata zan kone
wannan taswira yanzu take,abinda
nakeso daku shine yanzu mu fita waje a dora
wadannan akwatuna bisa keken doki a bani
sannan na danka muku wannan taswirar.
Koda Ardadu yazo nan a zancensa sai Barde
Uraidu ya bushe da dariya sannan ya dubi Ardadu
yace hakika ka burgeni domin ka nuna mana
cewa kai tsohon macucine wanda yasan kan
tuggu,ka sani cewa saboda muhimmancin
wannan taswira dake hannunka ko kuda banson
ya sauka a kanta saboda haka a shirye nake nabi
dukkan umarninka.
Nan take Uraidu yasa aka dauko wadannan
akwatuna na kudade aka lodasu akan keken dokin
saida Ardadu yaga ya hau kan keken dokin ya
zauna sannan ya wurgawa Uraidu wannan
taswira ya cafe shi kuma ya zaburi keken dokin
da gudu ya tafi a cikin dimbin farin ciki.
Tafiyarsa keda wuya sai barde Uraidu ya bushe
da dariyar mugunta yace shasha kawai ai hanyar
kashe makahon kare yawa gareta.
Ka dauki ajalinka ka tafi dashi baka sani
ba.Gama fadin hakan keda wuya sai uraidu ya
koma cikin wannan gida yayi shiga ta badda
kama sannan ya fito aka kawo masa doki yahau
ya zabureshi da gudu ya nufi gidan waziri ridwan.
Ta cikin wata barauniyar hanya Uraidu yabi ya
nufi gidan waziri ridwan,hanya ce ta bayan gari
inda babu mutane kuma babu wanda yasan da
wannan hanya face shi kansa Waziri Ridwan sai
kuma wanda ya yarjewa.
Waziri Ridwan ya kirkiri wannan hanya ne saboda
aiwatar da al'amarunsa na sirri ba tare da wani
ya gani ba.
Ta cikin wani bututun karfe dake cikin karkashin
kasa Uraidu yabi da dokinsa sai gashi ya fito
tsakiyar gidan waziri ridwan bisa dokinsa.Da
fitowarsa sai wani hadiminsa ya ruga gareshi ya
ruke masa dokin ya sauka sannan ya durfafi
turakar waziri ridwan tamkar cikin gidansa yake
shiga.
Waziri Ridwan na zaune a cikin kuryar turakarsa
yana nazari a cikin madubin tsafinsa saiga Uraidu
ya shigo fuskarsa cike da annuri koda waziri ya
hangoshi sai shima ya mike tsaye zumbur ya
tareshi cikin murna,
Take Uraidu ya zube kasa bisa guiwoyinsa yayi
gaisuwa sannan yasa hannu a cikin aljihunsa ya
dauko wannan taswira wacce aka zanata a kan
fatar damisa ya mika masa.Cikin tsananin farin
ciki Ridwan ya karbi taswirar ya dubata da kyau
kawai sai ya bushe da dariyar farinciki sannan ya
dubi
Uraidu yace tabbas ka cika aikinka daidai don
haka yanzu zan cika alkawarina a gareka,kaje ga
sarkin
gida akwai rijiya guda goma a cikin gidan nan
wadanda ke cike da zinare da lu'u lu'u kaje kaida
yaranka ku yashe wannan rijiyoyi kuyi gaba da
abin ciki rabonku ne.Koda jin wannan bishara sai
barde Uraidu ya kamu da tsananin farin ciki ya
sake zubewa kasa yana godiya sannan ya mike
tsaye zumbur ya ruga waje da gudu.
Uraidu na fita kuwa sai yayi kicibus da sarkin
gida kawai sai sarkin gida ya kama hannunsa ya
jashi izuwa wani daki ya nuna masa wadannan
rijiyoyi na zinare da
lu'u lu'u.Koda ganin wannan dukiya sai Uraidu ya
dimauce ya kama kyalkyala dariyar farin ciki
tamkar mahaukaci sabon shiga kuma ya kama
sintiri a tsakanin rijiyoyin yana lekasu.
Daman masu iya magana sunce zama waje daya
tsautsayi ne kuma a bari ya huce shi ke kawo
asara ko
rabon wani.Lokacin da barde uraidu ya tsaya
bata lokaci a can dakin da rijiyoyin dukiya suke
shi
kuma waziri ridwan na ruke da taswirar nan yana
kara nazarinta a hankali cikin nutsuwa kawai sai
yaga ashe babu inda ya nuna ainihin kogon Hajrul
Aswad,daya sake nazarin taswirar da kyau
saiyaga ashe taswirar ta wani dajin daban ce
wanda ba a cikin nahiyar yake ba.
Nan take zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata
kone kawai saiya mike tsaye zumbur ya ruga
waje ya nufi dakin da wannan rijiyoyi
suke.Adaidai wannan lokaci ne barde Uraidu ya
fito daga cikin dakin a guje domin yaje ya kirawo
yaransa su jide dukiyar kawai sai yayi karo da
waziri ridwan,cikin bakin zafin nama waziri
ridwan ya zaro wata sharbebiyar wuka ya
lumawa Uraidu a ciki.
Take wukar ta bullo ta gadon bayansa amma
saboda jarumtaka sai barde Uraidu ya bangaje
waziri Ridwan ya fadi,jini yayi tsartuwa a
lokacin da jiri ya debeshi ya juya ya dubi ridwan
ya bude baki da kyar yace,ya shugabana saboda
me zaka kasheni alhalin na cika aikinka kamar
yadda kake bukata?
Koda jin wannan tambaya sai waziri ridwan ya
mike a fusace yace kai shashasha aikinka bai
cika ba.Kawai sai waziri ya cillawa
uraidu wannan taswira yace duba da kyau kagani
sarkin yaki yaudararka yayi bai baka taswirar ta
gaskiya ba wannan jabuce.An gaya maka
™Abbas Abdulkadir Hada Hada™
ana cin dukiyata ne a saukake?
Ka sani nayi asarar miliyoyin dinare akan wannan
aiki tun daga
farkonshi kuma a yanzu kana son nayi asara
ninkin ta farko?
Koda jin wannan batu sai barde Uraidu ya bushe
da dariya cikin karfin hali,al'amarin dayai matukar
baiwa waziri ridwan mamaki kenan.
Uraidu ya fadi kasa yana kakarin mutuwa amma
duk da haka saiya bude baki da kyar yace yakai
waziri
Ridwan shin ka mantane da dimbin dukiyar da
kashe a baya a kokarin karbe wannan karagar
mulki daga hannun dan uwanka saboda
hassadarka da zaluncinka har izuwa yanzu ka
kasa samun wannan nasara kuma baka daina
asarar miliyoyin kudade ba.
To kasani mutum yana mutuwa da burinsa,nafi
shekara talatin ina fashi da sata,ina kashe
mutane don kawai na tara dukiyar da zata isheni
iya rayuwata amma saboda haramtacciyar hanya
nakebi ta tara dukiyar batayi mini albarka ba bare
burina ya cika.
Tabbas hanyar da kabi don cika burinka ka ninka
tawa sau dubu a
rashin tsafta don haka ba zaka taba samun
nasara ba,lallai da wannan bakin burin naka zaka
mutu.
Koda jin wannan batu sai waziri ridwan ya zare
takobinsa ya nufo uraidu ya fusace shi kuwa
Uraidu sai yacigaba da kyalkyala masa dariya har
saida yazo daf dashi ya daga takobin sama ya
fille masa kai,take kan Uraidu yayi sama ya fado
kasa tum amma kuma dariyace akan fuskar har a
sannan,
cikin tsananin fushi waziri ridwan ya kwalawa
wadansu dakarun sojan haya kira su dari biyu da
ashirin a cikin shiga ta bakaken tufafi suka fito da
gudu daga cikin wani babban daki na gidan
suka zo suka zube a gabansa su suka suna masu
sunkuyar da kawunansu kas.
Sudai wadannan dakarun sojan haya sun ninka
dakarun uraidu sau biyu a girma,kwarjini da iya
yaki kuma suna dauke da muggan makaman yaki
irin wanda ma ba a
saba gani ba.
Take waziri ridwan ya dubi wadannan dakaru
yace na umarceku dakuje gidan sarkin yaki
haiman a daren yau ku kashe duk mai numfashi
dake gidan,sannan ku nemo wannan taswirar ta
dajin Hajrul Aswad ku kawo mini.Koda jin wannan
batu sai gaba dayan dakarun suka amsa cikin
hada
murya sukace an gama ya shugaba.
Wannan shine abinda ya faru a gidan waziri
ridwan bayan barde
Uraidu yakai masa jabun taswirar dajin Hajrul
Aswad
*
Al'amarin Barde Ardadu kuwa lokacin daya tafi da
dukiya a cikin keken dokin yana mai matukar farin
ciki sai yayi ta kyalkyala dariya domin ji yake
kamar yafi kowa a duniya samun sa'a da
nasara,kai tsaye ya nufi gidan sarki kasuwa
domin karbar waccan dukiya ta farko wacce ya
bayar da ita ajiya.Yana zuwa kuwa aka bude
masa kofar gidan ya kunna kai ciki,bisa sa'a
kuwa sai ya iske sarkin kasuwa zaune a harabar
gidan bisa
shimfida,jama'a sun kewayeshi ana tattaunawa
akan harkokin kasuwanci mafi akasarin jama'ar
dake wajen fatake ne.Koda sarkin kasuwa yaga
Ardadu ya shigo sai ya mike tsaye daga kan
shimfidarsa ya tareshi suka gaisa.Sarkin kasuwa
ya juya ya dubi wadansu hadimansa dake tsaye a
gefe guda yace dasu suje su dauko jakar mai kala
kaza a cikin daki kaza.Nan take hadiman suka
ruga
izuwa cikin gidan don cika umarnin cikin mamaki
da farin ciki Ardadu ya dubi sarkin kasuwa yace
nawa zan biyaka bisa wannan ajiya da kayi mini?
Koda jin wannan tambaya sai sarkin kasuwa yayi
murmushi yace ai duk abinda kayi niya shi zaka
bayar idan ma kaga zaka takura to zaka iya bari
sai wani lokacin.
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kara
turnuke Ardadu ya gane cewa lallai sarkin kasuwa
bai bude ajiyar daya kawo masa ba yaga
abinda ke ciki,kawai sai ya tambayi kansa a cikin
zuciya yace dama ashe akwai irin wadannan
mutane a duniya masu amana haka?
Kafin ya baiwa kansa amsa sai ga wadannan
hadiman sun fito dauke da ajiyar Ardadu.Take
aka sanya jakar cikin keken dokin bisa wadannan
akwatunan dinare-
dinare.
Ardadu ya shafa dukkan aljihun jikinsa yaji ko sisi
don haka sai yasa hannun ya bude wannan jakar
kudi kadan ya zura hannunsa cikin domin ya
dauko dinare guda uku kacal ya baiwa sarkin
kasuwa a matsayin ladan ajiyarsa.
Kash rashin sani yafi dare duhu,
inda Ardadu yasan abinda zai biyo baya da bai
cusa hannunsa a cikin wannan jakar kudi ba.Ashe
tun ranar da uraidu ya bashi wannan
jakar acan kasanta akwai wani karamin bakin
maciji mai mugun dafi,macijin najin hannun
Ardadu ya shure shi saiya dankara masa sara bai
san sa'adda ya kurma uban ihu ba,shida jakar
kudin suka fado kasa,kudin suka tarwatse macijin
ya yunkura zai gusa sai wani daga cikin dakarun
sarkin kasuwa ya dankara masa sara ya baje a
kasa matacce,shi kuwa Ardadu saiya kama
karkarwa kamar wanda aka tsoma a cikin ruwan
kankara,idanunsa suka wurkila kuma saiga farar
da dafara na fitowa ta cikin bakinsa,kafin sarkin
kasuwa da yaransa su baiwa Ardadu wani
taimako tuni rai yayi halinsa ya zama gawa.
Cikin tsananin mamaki sarkin kusuwa ya dubi
gawar Ardadu sannan ya dubi makudan kudaden
da suka tarwatse a kasa daga cikin wannan jaka
ya dubi yaransa yace yanzu dama ashe kudi ne
haka a
cikin wannan jaka wannan mutumin ya kawo mini
ajiya ban sani ba.
Koda jin wannan batu sai babban
hadimin sarkin kasuwa yayi ajiyar zuciya ya
shugabana ai bana fidda tsammani cewa
wadannan akwatunan guda hudu ma dake cikin
keken doki kudi ne a ciki,shin baka san ko
wanene wannan mutum bane?
To ba wani bane face mashahurim danfashin nan
daya gagari fatake wato Ardadu.
Koda jin haka sai tsoro ya kama sarkin kasuwa
yasa aka bude wadannan akwatuna gudu hudu
sai gasu cike da dinare da lu'u lu'u,nanfa kowa
ya dada firgita ainun a wajen.
Babu abinda ma yafi firgita sarkin kasuwa face
ganin tambarin waziri ridwan daga cikin
akwatunan kudin.Nan fa sarkin kasuwa ya sake
dimaucewa fiye da ko yaushe jikinsa ya
™Abbas Abdulkadir hada hada™
kama tsuma ya dubi babban hadiminsa cikin
alamun tsoro da firgici yace,tabbas muna cikin
mummunan hadari wannan dukiyar dai ga dukkan
alamu ta waziri ridwan ce kuma ina ganin cewa
satota akayi saboda nasa halin waziri ridwan
babu mutumin dazai iya amincewa ya bashi
wannan dimbin dukiya domin a juya masa ita.
Yanzu me ya kamata muyi?
Shin zamu dauki wannan dukiya ne
mu mayar da ita ga waziri ko kuwa zamu ajiye
tane har sai anyi cigiyarta?
Koda jin wannan tambaya sai babban hadimin ya
numfasa yace ba zamu mayar da wannan dukiya
baga waziri ba kuma ba zamu ajiyeta ba anan
gidan shawarar da
zan bayar itace mu kwashe wannan dukiya mu
kaita gidan sarki mu dankata a hannun gimbiya
nauwara tunda a halin yanzu itace mai kula da
harkokin kudade na kasar nan.
Koda jin wannan shawara sai hankalin sarkin
kasuwa ya kwanta nan take ya bada umarni aka
tafi da dukiyar izuwa gidan sarki,
gawar Ardadu kuwa sai aka dauketa a sirrance
akaje aka boye saida dare ya raba sannan aka je
aka jefata a ruwan teku kifaye da sauran halittun
ruwa suka sami rabonsu.
Ohh Allah ka kiyashemu da yin mummunan
karshe,
hakika duk mutumin da yasa kwadayin duniya a
ransa gami da cin zali da cuta to da wuya
karshensa yayi kyau,wannan shine yanda karshen
munafuki Ardadu ya kasance,saidai kuma ya
mutu musulmi don haka babu wanda yasan
sakamakonsa a wajen Allah duk da cewa kuwa ya
karbi musulinci ne da zuciya biyu,
*
Al'amarin su Yarima zainur kuwa lokacin dasuka
baro gidan sarki tare da gimbiya nauwara bisa
dawakai da nufin su koma gidan sarkin yaki
haiman sai sukayi kicibus da sarkin yaki a cikin
keken doki tare da dukkan hadimansa da kuma
dakarun dake tsaron gidansa.
Cikin kaduwa da alamun tsananin mamaki yarima
zainur ya sauko daga kan dokinsa yazo gaban
keken dokin ya dubi haiman yace yakai abbana
ina dalilin fitowarka
daga gida alhalin kana bukatar ka kwanta kayi
jinyar raunikan dake jikinka,kuma ina ka nufa
daga nan?
Kafin haiman ya budi baki yace komai saiya dubi
gimbiya nauwara da yarima yazid ya yafuto su da
hannu.
Take suma suka sauko daga kan dawakansu
sukazo gareshi a sannanne haiman ya dubesu su
ukun yace dani daku duk rayuwarmu na cikin
mummunan hadari.Nan take ya kwashe labarin
duk abinda ya faru tsakaninsa da Ardadu bayan
fitarsu ya zaiyane sannan yace dole ne daganan
mubar cikin garin nan kuma mu nemi inda zan
buya nayi jinyar jikina,kema gimbiya ba zaki bi su
yarima izuwa wannan tafiya mai mugun hadari ba
dole ne ki zauna tare dani har izuwa lokacin da
zasu dawo.
Ina mai tabbatar muku da cewa dazarar waziri
ridwan ya gano cewa jabun taswira Ardadu ya
bashi zai turo a kashe mu kuma
a caje gidana gaba daya don neman ta gaskiyar.
Ko da gama fadin hakan sai sarkin yaki haiman
ya zura hannunsa a cikin aljihun wandonsa ya
fiddo wannan taswirar ya dankawa yarima zainur
a hannunsa yace ga amanar sarki na dankata a
hannunka kamar yadda ya bukata.Yanzu saimuyi
sauri mubar cikin garin nan tun kafin makiya suzo
su riskemu, koda jin wannan batu sai su yarima
suka juya da baya cikin hanzari suka nufi hanyar
data nufi wajen gari suna masu sakarwa
dawakansu linzami,aikuwa sai dawakan haiman
da jama'arsa ma suka rufa musu baya.
WASIKAR JINI
Littafi Na Shida (6)
Part B
.
Aikuwa sai dawakan Haiman da jama'arsa ma
suka rufa musu baya.
*
A can Gidan Waziri Ridwan kuwa duk da cewa ya
kirawo wadannan dakarun sumame ya basu
umarnin
sukai hari izuwa gidan sarkin yaki da daddare sai
yaji yakasa samun sukuni da kwanciyar hankali
nanfa ya kama kai kawo yana tunani iri iri.
Daga can sai kawai ya shiga can cikin turakarsa
yayi gagarumar shigar yaki cikin batar da kama
sannan ya kirawo wani hadiminsa yace dashi yayi
sauri ya tafi izuwa cikin daji inda dakarunsa na
sumame sukayi kwanton bauna ya gaya musu
cewa su rarrabu kaso kaso a cikin dajin kuma su
zuba ido
sosai domin a koyaushe zasu iya ganin
makiyansu su yarima zainur,da zarar an gansu a
kashe su a dauko masa taswirar dajin hajrul
Aswad.
Koda jin wannan umarni sai badakaren ya risina
yace an gama ya shugabana.Nan take hadimin
ya rugo ya kama doki yahau ya fice daga cikin
gidan da sauri.
*
Acan birnin sarki Marwatu kuwa tuni yan leken
asiri sun kaiwa sarki marwatu labarin cewa sarki
Aiyuba ya kwanta cutar ajali har takai cewa ma
baya ci baya sha,kuma baya iya yin komai da
kansa saidai a kwantar a tayat.
Koda jin wannan labari sai farinciki
ya lullube sarki marwatu take ya aiyana a ransa
cewa batun biyan bashinsa yasha ruwa kuma
lokacin
da zai rama cin fuskar da sarki Aiyuba yayi masa
yayi.
Nan take yasa aka shirya dakarun yaki na mutum
dubu dari uku ya jagorancesu suka kama hanyar
da zata kaisu birnin sarki aiyuba.
Haka dai wannan runduna taci gaba da tafiya ba
sassauci dare da rana har saida suka iso dajin
karshe wanda daga shi sai cikin birnin sarki
aiyuba sannan suka
yada zango.
Bayan sun kafa sansani sai sarki marwatu ya
tashi wani kwararren badakare dan leken asiri ya
turashi izuwa cikin garin domin ya gano halin da
ake ciki.
Dama bokan sarki marwatu ya shaida masa cewa
nan da cikar sati biyu sarki aiyuba zai fadi ya
mutu.Idan har yana son yaci garin
da yaki to lallai ya afkawa garin a ranar da sarki
aiyuba ya mutu kada ya bari a kara koda kwana
daya.
A ranar da bokan ya gayawa sarki marwatu
wannan labari sarki aiyuba ya shafe kwana uku a
kwance yana jinya yanzu kuma sarki marwatu ya
shafe kwana biyar cif yana yin wannan
tafiya,yanzu kenan saura kwana shida sarki
aiyuba ya mutu.
*
Lokacin dasu Yarima Zainur suka durfafi cikin
dajin suka kama tafiya saida suka shafe yan
sa'o'i suna tafiya dama yarima yazid ne akan
gaba,kawai sai akaga yaja linzamin dokinsa ya
tsaya cak.
Nan take kowa ya tsayar da nasa dokin akayi tsit
a lokacin da yarima yazid ya kama raba idanunsa
yana kallon gabas da yamma kudu da
arewa,kawai sai ya juyo ya dubi gaba dayan
abokan tafiyarsa yayi musu inkiya suyi
shiru,kuma kada wanda ya motsa daga inda yake.
Nan take yarima yazid ya shiga karanta wadansu
addu'o'i na musamman,faruwar hakan keda
wuya saiga wata runduna ta mayakan sumame
su da yawa sunzo sun gifta ta gabansu bisa
dawakai a sukwane dauke da muggan makamai
suna ta waige
waige da kalle kalle.
Nanfa su sarkin yaki suka firgita
ainun domin sunsan cewa ko ba'a gwada ba
linzami yafi karfin bakin kaza,tabbas cikin dakiku
kadan idan
wadannan dakarun sumame sukayi musu rufdugu
zasu gama dasu komai irin kokarin da zasuyi
kuwa saboda ido ba mudu bane yasan koma
kuma da ganin kura kasan zata ci mutum.
Ba zato ba tsammani sai su sarkin yaki haiman
sukaga Allah bai baiwa wadannan dakaru ikon
ganinsu ba duk da cewa gasu sunzo daf
dasu,wani lokacin ma har
bangaren su sukeyi amma basu gansu ba.Haka
dai wadannan dakarun sumame suka gaji da
neme neme da dube dube suka gaji sukabar
yankin wajen gaba daya.
A sannan ne yarima yazid ya hango wani kogon
dutse a can gabansu nan take ya bayar da
umarni aka karasa can.
Ba tare da wata gardana ba kuwa daga dayansu
suka durfafi wannan kogon dutse.
Da isarsu sai sukaga yazid ya tsaya a bakin kofar
kogon bayan ya shiga cikinsa ya duba ko ina ya
tabbatar da cewar babu wani abu mai cutarwa a
cikinsa saida kowa ya gama shiga cikin kogon
sannan yarima yazid ya tofa wata addu'a ta
musamman a kofar kogon sannan shima ya
shiga.
Bayan kowa ya zauna ana hutawa kuma an
dauko guzurin abinci anci ansha,sai sarkin yaki
haiman ya yunkura da kyar ya mike tsaye yana
mai dogara sanda ya taho inda yarima yazid ke
zaune ya
zauna kusa dashi suka fuskanci juna sannan yace
yakai wannan dan ssarki kayi sani cewa tabbas
yau naga abin al'ajabi a tare dakai kuma zuciyata
ta karkata izuwa ga wannan addini naka,na sani
cewa
inada karfin sihirin tsafi daidai gwargwado amma
sihirin wadancan dakarun sumamen da suka fito
farautarmu ya ninka nawa sau goma,amma sai
gashi
sunzo har gabanmu kuma sun kasa ganinmu.
Ina ganin haka na gamsu cewa ba kowa bane ya
bamu kariya face ubangijinka saboda naga
lokacin da
kake ta karanta wadansu addu'oi a cikin ranka na
neman tsari.
Sa'adda haiman yazo nan a zancensa sai farin
ciki ya kama yarima yazid yace tabbas nayi
murna da Allah ya nufeka da fahimtar hakan,to ka
sani cewa muddin muna cikin wannan kogon
dutse babu wani mahaluki walau mutum ko aljan
da ya isa ya
shigo har nan ya cutar damu,kai hatta dabbobi
da kwari ma ba zasu iya zuwa kusa da mu ba.
Albarkacin addu'ar dana karanta na tofa a bakin
wannan kogo.
Kafin yarima yazid ya gama rufe bakinsa kuwa
saiga wani AYARI na kuraye kimanin su arba'in
sun fito farautar abinda zasuci,kallo daya
zaka yiwa kurayen ka gane cwa suna cikin
tsananin yunwa domin sai zazzaro harsunansu
suke suna
lasar duwatsu da kasa kuma suna dalalar da
yawu.
Koda kurayen suka hango alamun mutane a cikin
kogon da su yarima yazid ke ciki sai suka ruga
da gudu domin su kawar da yunwar su suna kar
™Abbas Abdulkadir Hada Hada™
tar kasa da faratan kafafunsu tamkar sunci
babu.Koda suka iso daf da bakin kofar kogon
dutsen
sai sukayi turjiya suka kasa shiga ciki suka kama
koke koke sunaja da baya.Ba komai ne ya
haddasa
hakan ba face ji da sukayi

1 Comments On WASIKAR JINI 1 to 8
avatar
abdulrasheed-yusuf

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment