Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

juya suka fice tare
daga cikin dakin girkin ya kaishi inda suka saba
zama suci abinci kan wani madaidaicin
tebur.Bayan sun
zauna sai Haiman ya zubawa zainur abinci kuma
ya zuba masa ruwa a kofi yayi masa nuni dayaci
abinci ba tare da gardamar komai ba kuwa zainur
ya kama cin abincin hannu baka hannu kwarya
har saida yaci ya koshi yayi gyatsa sannan
Haiman ya dubeshi cikin nutsuwa yace,menene
ya faru gareka jiya a daji sa'adda ka fita farauta?
Koda jin wannan tambaya sai Yarima Zainur ya
kawo gwauron numfashi ya ajiye ya kwashe
labarin duk abinda ya faru gareshi a daji ya
labarta masa tun daga lokacin daya harbo
wannan tsuntsu ya gasa domin yaci kawo izuwan
wadannan arnan daji suka wulakanta masa
namansa har yakai su gayin yaki ya korasu har
cikin birninsu inda sarauniya Lazara ta taka masa
birki har sukayi wadannan maganganu shi da
ita.Koda zaiyanu ya gama bashi wannan labari
sai hankalin Sarki yaki Haiman ya dugunzuma
ainun yayi shiru yana mai sunkui da kansa
kas,al'amarin daya firgita jarumi zainur kenan
kuma ya jefashi cikin rudani da wasi-wasi daga
can sai Haiman ya daga kai ya dubi zainur cikin
alamun tausayawa da damuwa yace,ya
shugabana kayi sani cewa kasar nan nan gaba
zata iya shiga cikin rudani da rikici na siyasa
kuma ba
kowane zai haddasa suba face mahaifinka waziri
ridwan tabbas za'a zubar da jini mai yawa kuma
za'ayi asarar miliyoyin rayuka da dukiya amma
kai kadaine zaka iya hana faruwar hakan.Koda jin
wannan batu sai idanun zainur suka zazzaro ya
dubi haiman cikin alamun mamaki da firgici yace
ya yaya zan iya tsayar da mahaifina akan
kudirinsa alhalin yafini sanin tuggun duniya kuma
yasan hanyar da zaibi ya yi maganin duk wanda
yake ganin cewa zai iya kawo masa matsala.
Sarkin Yaki Haiman ya gyada kai yace tabbas
abinda ka fada gaskiya ne domin a duk fadin
kasar nan ma sarki ne kadai baya shakkar waziri
ridwan saboda ya fishi duk abinda
yake takama dashi inason ka sani cewa waziri ya
kasance kasaitaccen matsafi kuma gawurtaccen
mayaki amma kuma a fagen yaki ko farcen kafar
sarki bai kai ba ni kaina da nake kan wannan
matsayi na sarkin yakin kasar nan waziri ridwan
yafini karfin damtse da iya yaki idan har sarki
aiyuba ya riga waziri ridwan mutuwa sai kowa ya
shiga uku
a kasar nan muddin baka yiwa tufkar hanci
ba,hanyar da zaka yiwa tufkar hanci kuwa dayace
dole ne ka cigaba da koyon yaki domin ka zamo
zarton jarumin da babu kamarsa a wannan nahiya
kamar yadda sarauniya lazwara ta baka shawara
idan har kanason kakai kan wannan matsayi tofa
saidai kaje ka koyi yakin a wajen sarauniya
lazwara ko wajen sarki marwatu domin sune
kadai suke da
horon yaki na ban al'ajabi wanda suka samu a
wajen iyayensu.Bayan kahau wannan matsayi na
zarton
jarumin da babu kamarsa dole ne kuma ka zamo
mai tsaron lafiyar gimbiya nauwara domin taci
gaba
da zama akan matsayi
+Abbas Abdulikadir hada hada+
na gadalimar wannan masarauta tamu donta
haka ne kadai zaka iya kare kasar nan da
jama'armu daga
sarrin mahaifinka idan har kuma ba zaka iya
zama mai tsaron lafiyar gimbiya ba dole ne ka
nemi
karagar mulkin kamar yadda mahaifinka ke
nemanta ruwa a jallo domin ka tserar da komai
da kowa na kasarnan.
Sa'adda sarkin yaki haiman yazo nan a zancensa
sai ran yarima zainur ya baci har idanunsa suka
ciko da kwalla ya dubi sarki yaki yace,yanzu kana
nufin kace dani na daura damar yin gaba kenan
da mahaifina mu zama makiyan juna?
Haiman ya gyada kai yace tabbas abinda nake
nufi kenan kodai ka zabi kasarka da jama'arka ko
kuma ka zabi mahaifinka ka sani cewa a yanzu
babu abinda mahaifinka zai iyayi amma kasani
cewa duk ranar da babu sarki aiyuba komai zai
iya faruwa ina mai tabbatar maka da cewa
wannan shawarar da nazo
maka da ita yanzu itace babban burin sarki kuma
komai dadewa da kansa zai kirawoka ya baiyana
maka ita.
Koda gama fadin hakan sai sarki yaki Haiman ya
mike tsaye ya koma cikin turakarsa ya janyo kofa
shi kuwa zainur a kan wannan tebur nacin abincin
asuba ta riskeshi saboda kasa yin barci yayi
saboda fargaba,mamaki da tunanin
abubuwan da haiman ya gaya masa,tabbas
hankalinsa ya dugunzuma ainun kuma har saida
hawaye ya zubo masa.
*******************************
Acan birnin Hairan kuwa lokacin da manzon ya
dawo daga birnin Latus Harus tare da abinci mai
yawa da kuma dinare niki niki a cikin buhunhuna
sai farin ciki ya baibaye sarki marwatu da gaba
dayan jama'ar kasar bisa ganin wannan waraka
datazo musu ta fita daga talauci saboda tsananin
farin ciki ma tun kafin tawagar manzo ta iso cikin
garin sarki marwatu da manyan fadawansa
sukayi hawa sukaje suka taro su kuma suka
rakasu aka dawo izuwa cikin fada,nanfa gari ya
rude da shewa,kade kade da bushe bushe na farin
ciki.Bayan sarki Marwatu ya zauna akan karagar
mulkinsa fadawansa sun zauna kowa ya nutsu
sai
sarki marwatu ya bayar da umarni a karanta
amsar wasikar da sarki aiyuba ya aiko masa da
ita.Nan
take kuwa magatakarda ya cika aikinsa tun kafin
a gama karanta wasikar ran sarki marwatu ya
baci
jikinsa ya kama karkarwa kuma zuciyarsa ta fara
tafarfasa kamar zata kone nan take yaji kamar
yasa
amayarwa da sarki aiyuba gaba dayan dukiyarsa
amma daya tuna da halin da kasarsa ke ciki na
fatara,yunwa da talauci sai ya kasa.Nan take
sarki Marwatu ya dubi manzon yace gaya mini
duk abinda
ya faru a lokacin da kajewa da sarki aiyuba
wasikata fadarsa.
Nan take kuwa manzo yayi cikakken bayani
kamar yadda abinda ya wakana,koda sarki
marwatu yaji irin shawarar da gimbiya nauwara
ta baiwa
mahaifinta sai yaji nan take ya tsaneta ainun
kamar yadda ya tsani mutuwarsa kuma ya kudire
a ransa cewa komai daren dadewa sai ya hallaka
gimbiya nauwara saboda ya fuskanci cewar itace
zata iya gadon mahaifinta taci gaba da samun
fifiko akan
gaba dayan sarakunan dake nahiyar amma abin
tambaya anan shine ta yaya zai iya kasheta a
sirrance ba tare da mahaifinta ya san cewa shine
ya kasheta ba?
Babu irin binciken da sarki marwatu baiyi ba a
cikin hallarar tsafi akan yadda zai murkushe
kasar latul harus ya mallake arzikin da suke dashi
kuma ya kawar da sarki aiyuba ya mallake irin
sihirin tsafinsa amma abu ya gagara
saboda duk sa'adda yayi irin wannan binciken
babu abinda yake gani face mutuwarsa.Bayan
sarki
marwatu yayi dogon tunani da nazari akan
wannan sharadi da sarki aiyuba ya gindaya masa
akan
dukiyar da aka bashi aro saiya bushe da dariyar
mugunta,nan take yasa aka shiga rarraba kayan
abincin da aka kawo izuwa birane da kauyukan
kasar sannan kuma ya aika aka gaiyato masa
masana kasa da noma sukazo suka kama aiki
gadan-gadan sannan kuma aka bude hanyar
ruwa daga teku ya ratso izuwa dukkanin
garuruwan kasar don gabatar da noman rani aka
baiwa manoma rance jar
da iri mai kyau suma suka kama aiki baji ba
gani,aikuwa kafin shekara ta zagayo sai gashi
birnin
Hairan ya bunkasa akan harkokin noma da
kasuwanci,arziki ya yalwata a hannun
jama'a,fatara
da talauci sukayi kaura tamkar ba'a taba shiga
cikin yanayi mara kyau ba,kai saidai takai cewa a
gaba nahiyar ma in banda birnin latul harus babu
wani birnin da yafi birnin hairan girman kasuwa
da
daukakarta da kuma karfin arziki nanfa sarki
marwatu ya shagala a cikin wadata da
dukiya,hatta
fadarsa ta mulki sai da aka rusheta aka gina irin
ta sarki aiyuba aka kashe mata dukiya mai
dumbin
yawa.A ranar da shekara ta zagayo ne wasikar
sarki aiyuba ta dawo ga sarki marwatu a karo na
biyu
wacce ta kunshi bukatar kudin da aka rantawa
kasar hairan da kuma dakaso daya cikin kaso
ukun ribar
da aka samu acikin harkokin noman da akayi.
Koda sarki marwatu yaji abinda wasikar ta kunsa
saiya bushe da dariya nan take yasa aka rubu
amsar wasikar inda ya bukaci ayi masa alfarmar
karin lokaci na wata shida.Sa'adda aka kawowa
sarki
aiyuba amsar wasikar yaji alfarmar da sarki
marwatu ya nema sai shima ya kyalkyale da
dariya,a wannan lokaci fadar ta cika
makil,gimbiya nauwara na zaune daf dashi a
damansa a can gefe daya kuma sauran
fadawansa ne su waziri ridwab a zazzaune sai
muzurai sukeyi domin suji hukuncin da sarki zai
yanke.
Kwatsam sai sukaga sarki ya dubi gimbiya
nauwara cikin murmushi yace masu iya magana
sunce ta inda aka hau tanan ake sauka saboda
haka yanzu wacce shwara zaki bani kamar yadda
kika
shawarceni a lokacin dana amince na bashi
wannan taimako?
Maimakon gimbiya nauwara ta bude baki tace
wani abu sai ta mike tsam daga kan kujerarta
taje har daf da sarki aiyuba tayi masa rada a
kunne,take sarki aiyuba ya tuntsire da dariya yayi
ta
kyakyatawa kamar bazai daina ba,al'amarin daya
razana kowa kenan a fadar banda ita kanta
nauwara da kuma sarkin yaki Haiman....
Nima dai ganin wannan dariya tasa na razana na
tsaya.
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Biyu (2)
Part B
.
Banda ita kanta Nauwara da kuma sarkin yaki
haiman.
Daga wannan rana sarki aiyuba bai sakeyin batun
dukiyar daya aikawa sarki marwatu ba har
watanni shidan daya diba suka cika kai har ma
wata shekarar ma ta sake zagayowa bai aiko
masa ba kuma baice kala ba,al'amarin da yasa
sarki marwatu ya saki jikinsa kenan saboda
zatonsa sarki aiyuba ya hakura gaba daya da
wannan dukiyar tasa yabar masa ita.
Nanfa sarki marwatu yacigaba da bushasha
abinsa ya rinka facaka da dukiya son ransa kai
kace rijiyoyin dinare ne dashi.
Kwatsam rana daya sai aka wayi gari a birnin
Hairan wannan ruwan kogi da janyo izuwa cikin
birnin ya kafe,fari ya afkowa gonakai ya zamana
cewa kwari sun cinye gaba
dayan amfanin gona duk fataken kasar kuwa sai
suka durkushe basu tsira daga sharrin en fashi
akan
hanyoyinsu ba,bakin fatake kuwa masu kawo
ziyarar ciniki a birnin sai suka dauke kafa nanfa
ungulu ta
koma gidanta na tsamiya ya zamana cewa
mutanen kasar sun fara gudun hijira izuwa
kasashen dake makwabtaka,da masifa takai
masifa saida shi kansa sarki marwatu da iyalinsa
suka fara fuskantar matsalar yunwa ba shiri sarki
marwatu ya debi ragowar yar dukiyar data rage a
hannun sa ta dinare buhu dari uku yayi shiri ya
tunkari birnin latul harus.
Bayan tafiyar kwana goma sha daya ne cif sarki
marwatu ya iso birnin latul harus da safe a
lokacin rana ta dan hudo,a wannan lokacin sarki
aiyuba na zaune a fada gimbiya nauwara na
zaune a
damansa sai ga wani hadiminsa ya shigo da
sauri ya zube kasa yana mai yiwa su sarki
marwatu iso,koda akaji cewar sarki marwatu ne
yazo sai kowa ya cika da tsananin mamaki ba
tare da nuna wata damuwa ba sarki aiyuba ya
bada izini akaje aka shigo da sarki marwatu da
jama'arsa da kuma
yar dukiyar dazo da ita.Kai tsaye sarki marwatu
ya durfafi inda karagar sarki aiyuba take kansa a
sunkuye,koda dakarun sarki aiyuba suka ga sarki
marwatu na kara kusanto sarkin su sai suka
yunkura suka zare takubba zasu tareshi amma
sai sarki aiyuba ya daga musu hannu yana mai
hanasu.
Fuskarsa cike da murmushi dakarun suka mayar
da takubbansu cikin kufe amma sai suka zubawa
sarki marwatu idanu ba tare dasun daga
hannuwansa akan kufen takobinsu ba,kuma sarkin
yaki haiman ne akan gaba daf da sarki aiyuba ya
kurawa sarki marwatu idanu yana jira ya gani
kozai yi wani mugun nufi.Koda ya rage saura
baifi taku biyar ba a tsakanin sarki marwatu da
sarki aiyuba sai sarki marwatu ya tsaya cak
sannan ya durkusa kasa bisa guiwoyinsa biyu a
lokacin da hawayen takaici ya zubo masa sannan
ya budi baki batare da
ya iya daga kansa ya dubi sarki aiyuba ba yace
ya kai sarkin sarakai kuma dodon sarakunan
wannan nahiya kayi mini aikin gafara bisa cin
amanarka danayi da kuma karya alkawarin danayi
maka tsawon shekaru biyu,na tuba na bika kuma
ina mai rokonka alfarma guda daya kuma ta
karshe koda laifin danayi kisane hukuncinsa ina
mai rokonka daka tausayawa jama'ar kasata ka
dawo musu da arzikinsu na noma da
kasuwancinsu kuma ka dauke
musu farin daya addabi gonakinsu ni nasan cewa
kayi amfani ne da karfin sihirinka na tsafi wajen
jefamu a cikin wannan masifar.
Koda sarki marwatu yazo nan a jawabinsa sai
sarki aiyuba ya tuntsire da dariyar mugunta yayi
ta kyakyatawa kamar ba zai
daina ba,daga can kuma sai sarki aiyuba ya
murtuke fuskarsa tamkar an aiko masa da sakon
mutuwa ya dubi sarki marwatu cikin alamun
tsananin takaici har
kwallah ta cika masa idanu yace,yakai wannan
sarki ma'abocin kaskanta a gabanmu kayi sani
cewa laifinka yakai na hallaka ka yanzu take ba
don komai basai saboda nasan cewa a duniya
babu
abinda ka tsana sama dani da kuma 'yata
gimbiya nauwara kuma babu abinda kake so
sama daka
mallake wannan kasa tawa da duk arzikin cikinta
amma saboda wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa
shi yasa ka hakura bisa dole nasani cewa duk
ranar da babu ni sai kayi yunkurin cika burinka
akan 'yata da
kasata don haka nima inanan ina shiri akan
hanyar dazan bi na baiwa 'yata kariya a bayan na
shude,na yarda zanyi maka alfarmar daka nema
akan mutanen
kasarka amma bisa sharadi guda sharadin kuwa
shine dolene ka zabi wata gaba daga jikinka
wacce
baka sonta nasa ayanke maka ita wannan shine
kadai abinda zai fanshi laifinka da kuma
jama'arka.
Koda sarki aiyuba yazo nan a zancensa sai
hankalin kowa a cikin fadar ya dugunzuma aka
cika da mamaki ita kuwa gimbiya nauwara
dariyar farinciki ta kama kyalkyalawa a lokacin
dashi sarki
marwatu ya firgice kuma ya dimauce bai san
sa'adda ya sake zubewa kasa a gaban sarki
aiyuba
yana mai yi masa sujjada yace,haba ya
shugabana saboda me kakeson ka wulakanta
sarki mai
cikakkiyar daraja kamata kamai dashi masaki?
Nikam na zabi ka kasheni dadai ka nakastani akn
wannan bukata tawa.Ka tuna fa cewa ni gwarzon
jarumi ne mai tarwatsa maza a filin daga dadai
ace na rasa
wani bangare a jikina akaron banza gwara ace a
filin yaki ne na rasa kaina ko kafata ko hannuna
domin zan mutu a cikin alfaharin cewa ni namiji
ne kuma jarumi abin kwatance,dajin wannan batu
sai sarki aiyuba ya bushe da dariya sannan yace
dukkan sarki na kwarai kasarsa da al'ummarsa
shine abinda yafiso,shin kasan irin tsananin
wuyar da iyayena da
kakannina suka sha kafin su sami nasarar gina
wannan kasa tamu,shin kasan irin rayukan da
suka
salwantar da irin dukiyar da suka salwantar kafin
su samo ilmin sihirin tsafin dana gada yanzu
harna iya baiwa kasar tsaro na musamman?
To ka sani rai da jiki ba abakin komai suke ba
wajen kafa tubalin ginin kasa,idan har kanason ka
gina kasarka ta sami kafuwa ta har abada dole
sai jikinka ya zuba akan
kasa wannan ce kadai
+Abbas Abdulkadir Hada Hada+
hujjar da zata tabbatar da soyayyarka ta gaskiya
akan kasarka da al'ummarka kai nake jira wane
bangare na jikinka kakeso mu cire don samu
biyan bukatarka a wajena?
Lokacin sa sarki aiyuba yazo nan a zancensa sai
sarki marwatu ya mike tsaye fuskarsa a murtuke
ya mikar da hannunsa na hagu ya dubi sarki
aiyuba yace na sallama hannuna na hagu domin
gina kasata da al'ummata.koda jin
wannan batu sai sarki aiyuba ya tuntsire da
dariyar murna lokaci guda kuma ya turbune
fuskar tasa ya dubi sarkin yaki haiman,take
haiman ya risina cikin biyayya yace an gama ya
shugabana.Yana gama
fadin hakan sai ya zare takobinsa mai tsananin
kaifi gayawa jini ya durfafi sarki marwatu.
Adaidai wannan lokaci ne tsirarun dakarun sarki
marwatu suka zube
kasa suna kuka suka kama rokansa akan kada ya
bayar da hannunsa a sare shi kuwa sai yayi biris
ko
kallonsu baiyi ba yabar hannunsa na hagu a mike
sauran jama'ar dake cikin fadar kuwa sai kowa
yayi
tsuru tsuru ana mamaki da tausayin sarki
marwatu sarkin yaki haiman ya tsaya daf da sarki
marwatu ba bayansa ya daga takobinsa sama zai
fille masa
hannun kenan sai kawai akaji tsawa daga bakin
kofar shigowa ana mai cewa a dakata.
Take kowa ya dubi bakin kofar domin aga wanda
ya bayar da wannan umarni,ba wani bane face
Yarima Zainur Dan waziri ridwan ya tunkaro fadar
kai tsaye ba tare da shakkar komai ba a lokacin
da mahaifin nasa ya bishi da harara gami da
kallon takaici.
Yarima Zainur ya iso har gaban karagar mulki
sannan ya zube kasa gaban sarki aiyuba ya
kwashi gaisuwa,zainur ya daga kai
ya dubi sarki cikin girmamawa yace,ya
shugabana a matsayina na jinin wannan
masarauta ina mai
nemawa sarki marwatu sassauci akan wannan
hukunci da aka yanke masa ya shugaban badon
komai nake nema masa wannan sasauci ba sai
saboda dalila gudu biyu,dalili na farko shine
nasan cewa kai adali ne kuma mai tausayi,sarkin
da ba'a
taba neman wata alfarma a wajensa an rasa ba
inhar masu neman alfarmar sun kasance masu
bautar abin bautarmu,afuwarka bata yankewa
komai rintsi a
tarihin sarakunan kasar nan,kaine kadai sarki
daya shekara arba'in akan mulki ba tare da anyi
yaki ba
ko sau daya,ya shugabana wannan hukunci da
kake shirin yankewa akan sarki marwatu zai iya
zama
sanadin barkewar yaki a tsakaninmu da sauran
sarakunan dake nahiyar nan saboda kaine sarki
na farko daya taba wulakanta sarki a bainar taro
cikin fadarsa,kodda mune zamu sami nasarar yaki
akan sauran sarakuna aisai munyi asara mai
yawa,
dalili na biyu shine ya shugabana a kullum
anason sarki yazamo mai rage makiyansa kada
ya zamo mai karasu sarki marwatu tsohon
makiyinmu ne kuma gaba ce data samo asali tun
iyaye da kakanni
wannan sassauci da zaka yi masa zai janyo karin
martabarka a idon duniya kuma a idon makiya.
Lokacin da yarima zainur yazo nan a jawabinsa
sai jikin sarki aiyuba yayi sanyi matuka su kuwa
sauran jama'arsa dake fadar sai suka cika da
tsananin mamakin yarima zainur bisa basirarsa
da hangen nesansa da kuma wannan kundumbala
dayayi wacce ko mahaifinsa sai yaji tsoron yinta
don
kada fishin sarki ya tabbata akansa saboda ko
kadan sarki aiyuba ya tsani wanda zaiyi masa
shishshigi
akan harkokinsa na mulki.
Waziri ridwan bai san sa'adda ya kama
murmushin farin ciki ba saboda ko kadan baya
son a taba sarki marwatu sakamakon cewar
tsohon abokinsa ne tun kuruciya tun sa'adda
mahaifinsu sarki da ya gushe yake kai ziyara
wajen
mahaifin sarki marwatu a wannan lokacin shi
sarki aiyuba ba'a zuwa dashi ko ina anata koyar
dashi
sha'anin mulki a gida saboda sani cewa shine zai
gaji karaga baya ga wannan dalili waziri ridwan
da
sarki marwatu sun shirya a sirrance cewar duk
ranar da sarki aiyuba ya mutu marwatu zai
taimakawa ridwan ta kowane hali ya zama sarki
mai cikakken iko kuma a kawar da gimbiya
nauwara
Sarki aiyuba saiya dago kai ya dubi yarima zainur
cikin alamun tsananin takaici wanda har saida ya
haddasa cikar kwalla a cikin idanunsa yace,yakai
dana kayi sani
cewa a iya sanina dakai baka taba neman alfarma
ba awajena sai yau,kash inda kasan abinda zai
faru nan
gaba da baka nemawa sarki marwatu wannan
alfarma ba tabbas bazan iya bada maka kasa a
fuska ba saboda ina matukar jin kunyarka fiye da
yadda nake ganin girman kowa a wannan
fada,lallai bazan janye alkawari naba akan sarki
marwatu na zubar da jininsa a matsayin fansa
akan laifin dayayi
mini,amma a maimakon hannunsa na dama da
zamu yanke inason a yanke mini babban dan
yatsansa na hannun hagu.
Koda jin wannan batu sai hankalin sarki marwatu
ya dugunzuma ainun fiye da koyaushe ya yunkura
da nufin ya juya da baya ya tsere amma sai sarki
aiyuba ya nunashi da sandar hannunsa ta mulki
take marwatu ya sulale kasa sumamme a lokacin
da guntulallen dan yatsansa ya fada kan tafin
sarki aiyuba
Koda sarki aiyuba yaga dan yatsan sarki marwatu
akan tafin hannunsa sai ya kyalkyale da dariyar
farin ciki kuma ya mike tsaye daga kan karagar
mulkinsa ya shige cikin gidan sarautar yana mai
mutukar murna,a wannan
lokacinne waziri ridwan yasa aka dauke sarki
marwatu da sauri aka tafi dashi gidansa inda
likita
ya shiga yi masa aiki.
Al'amarin gimbiya nauwara kuwa lokacin da fada
ta watse kowa ya kama gabansa sai ta taho
wajen yarima zainur ta dubeshi tace,inason ka
biyo ni yanzu domin muje muyu wata magana
mai muhimmanci,a cikin alamun mamaki da
biyayya zainur ya risina a gareta yace ya
shugabata
yanzu har inada wata daraja da zaki tattauna
muhimmiyar magana dani?
Koda jin haka sai gimbiya nauwara tayi murmushi
tace,ai darajar taka ma ta wuce haka yadda kake
zato domin inda baka da ita da babu yadda
za'ayi yau sarki ya saurareka
har ya
+Abbas Abdulkadir hada hada+
karbi alfarmar daka nema.Koda gama fadin hakan
sai gimbiya nauwara ta juya ta nufi wani bangare
na dabam na gidan sarautar cikin sauri yarima
zainur
ya bita a baya basu tsaya a ko ina ba sai cikin
wani kasaitaccen lambu.Bayan sun shiga cikin
lambun
sun zauna sai kuyangi suka kawo musu ruwan
inibi a cikin tambula da kofuna guda biyu akan
faranti suka ajiye a gabansu har daya daga cikin
kuyangin ta yunkura zata zuba musu ruwan ibinin
da hannunta sai nauwara ta hanata ta sallamesu
suka fice daga
cikin lambun suna waigenta cikin alamun
tsananin mamaki saboda yaune karo na farko da
suka taba
ganin gimbiya nauwara ta kebe da wani da namiji
a cikin gidan sarautar harma tana shirin shayar
dashi ruwan inibi da hannunta,shi kansa yarima
zainur abinda ya daure masa kai yayi matukar
bashi
mamaki amma sai ya dake.
Bayan nauwara ta zuba ruwan inibi a cikin kofuna
gida biyu sai ta mikawa zainur kofin guda ita
kuma ta dauki dayan saida kowannensu ya kurbi
ruwan inibin sau uku sannan nauwara tayi gyaran
murya ta dubeshi cikin murmushi tace,Yakai dan
uwana waishin yaya kake ganin zaka iya
kwatanta jarumtakar sarauniya lazwara akan
taka?
Koda jin wannan tambaya sai zuciyar yarima
zainur ta buda da karfin gaske ya dubi nauwara
cikin alamun tsananin mamaki yace,yaya kikasan
cewa nasan sarauniya
lazwara?
Nauwara tayi murmushi tace shin ka manta ne
cewa a nahiyar nan kaf babu matsafi kamar
mahaifina?To kasani cewa duk abinda ya faru a
gareka a cikin daji sa'adda ka fita farauta na gani
a cikin madubin tsafina,tabbas na yava da irin
jarumtakarka amma kuma da naga yadda
sarauniya lazwara tayi maka duka daya ta kaika
kas cikin
galabaita sai jikina yayi sanyi kuma na kara
tabbatar da maganar da mahaifina ya sanar dani
akanka,
mahaifina ya gaya mini cewa kaine kadai
mutumin da zai iya barwa amanata a hannunka
bayan
mutuwarsa amma kuma ba zaka iya rike amanar
ba face ka kara samin horon yaki ninkin wanda
kake dashi kuma sai ka nemo WASIKAR JINI ta
zame maka jagora a dukkan harkokinka.
Lokacin da gimbiya Nauwara tazo nan a zancenta
sai yarima zainur ya sake cika da tsananin
mamaki yace,meye kuma wasikar jini?
Nauwara tayi murmushi gami da gyara zama
sannan tace wasikar jini wata wasika ce ta
musamman wacce aka rubuta da tauwadar jini ta
mutane tara su dai wadannan mutane tara sune
asalin mutanen da suka fara zama a birnin nan
namu na latul harus kuma sa'ilin da kakannimu a
wannan masarauta babu komai a cikin wannan
wasikar mai shafi dari daya face sirrika guda
uku,sirri na farko shine gaba dayan dukiyar dake
karkashin kasa wannan nahiya gaba dayanta,sirri
na biyu shine duk wanda ya karance wasikar sai
ya zama sarki a birnin latul harus,sirri na uku
wanda shine na karshe wanda duk ya karance
wannan
wasikar jini saiya samu irin sirrikan tsafin da
mahaifina ke dasu,a bayan mutuwar mahaifina kai
da waziri ridwanne zaku bazama neman wasikar
don haka ne nake son kai kayi nasarar ganinta da
karantata kafin shi.
Ka sani idan ya rigaka ganin wannan wasika
shikenan karshen farin ciki da zaman lafiya yazo
kenan a birnin namu ,amma idan kaine ka rigashi
za'a cigaba da zaman lafiya da yalwar arziki har
izuwa sa'adda danka zai gajeka babu wanda zai
iya ganin wannan wasikar ta jini har ya iya
karantata face ya kasance jinin sarautar nan
gidan,bazaka iya zuwa inda wasikar jini take ba
face kafi sarauniya lazwara karfi da iya yaki,in ba
haka ba kuwa mahaifinka waziri ridwan zai
kasheka da hannunsa don kawai biyan bukatarsa.
Lokacin da gimbiya Nauwara tazo nan a zancenta
sai hankalin yarima zainur ya dugunzuma ainun
har hawaye ya zubo masa bai san sa'adda ya
takarkare ba ya
kwarara uban ihu kuma ya fashe da matsanancin
kuka,da kyar nauwara ta rarrashe shi tace hakuri
zakayi yakai dan uwana domin haka kaddararka
ta kasance ka zama babban makiyin
mahaifinka,ina mai shawartarka daka guntse
bakinka kada ka kuskura bari mahaifinka yasan
wannan al'amari tun yanzu domin idan ya sami
tun yanzu zai kasheka kuma ka
zauna a cikin shirin komawa birnin arnan daji
domin ci gaba da karbar horon yaki a wajen
sarauniya
lazwara nida kaina zan raka ka mu nemi wannan
alfarma kuma na tabbatar da cewa ba zata ki ba.
koda zainur yaji wannan batu sai yayi shiru ya
kurawa Nauwara idanu ba tare da yace komai ba.
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Biyu (2)
Part C
.
Koda Zainur yaji wannan batu sai yayi shiru ya
kurawa Nauwara idanu ba tare dayace komai ba.
*** *** ***
Al'amarin su Ardadu da Yarima Yazid kuwa
lokacin da suka cigaba da tafiyarsu kasar Lahul
Harus,tunda suka taho babu abinda yake dakatar
dasu face sallah da cin abinci kuma sun kwashe
kwanaki uku akan hanya suna wannan
tafiya,saida sukayi nisa sosai sai
suka hangi wasu matafiya a can gaba dasu sun
nufo hanyar daga gani sunje kasar latus harus ne
sunci kasuwa hanyar ta biyo dasu.Koda ganinsu
sai Ardadu ya cika da tsananin farinciki domin ya
gaji
da tafiyar kasar da suke gashi Yarima Yazid sauri
ne dashi tafiya suke kamar masu gudu gudu sauri
sauri dan haka ne baya korafi,idan an tsaya yin
sallah domin ya gwammace ayi ta sallah da
wannan
tafiya,sosai ya gaji.Dan haka sai ya dubi Yarima
yace,ya shugabana wai mai ya hana muka fito ba
tare damun samun dawakai ba,mun hau domin
rage mana nisan tafiya,kana sane da cewa tafiyar
da doki zaiyi ta yini daya itace wadda mu zamu
yita a kwana
uku,kaga kenan da akan doki muke tafe da tuni
yau kwananmu tara kenan akan hanya.
Koda Yarima Yazid yaji wannan batu sai yayi
murmushi yace ai tafiyar kasa tafi dadi,dalili
kuwa baka dauke da nauyi face nauyin kanka da
ace yanzu da doki muke tafe da tuni mun takura
shi kuma yanda mu kanmu bamu da yawan
guzuri shima zai kasance bashi da
guzuri,kaga kenan da tuni yanzu yunwa ta
addabeshi a uzurinsa da banasa ba,kaga yanzu
mu zamu iya
jakuri ba kamar shi ba yadda yake dabba.
koda jin wannan batu daga Yazid sai Ardadu yayi
shiru daga bisani yace maganarka gaskiya ce
amma kuma aishi dokin dama anyishi dan ya
taimakawa bani adama,in
hakane kuwa koda ya mutu wajen bauta mana
kamar yayi jahadi ne,dan haka inason kayi hakuri
da
abinda zai faru yanzu domin ya zama dole mu
samu dawakan da zasu rage mana nisan tafiya
sannan mu samu karin guzuri.Dajin haka sai
yarima ya dakata
ya nunashi da yatsa yace bana bukata in kuwa
ka kuskura ka kwace abin wani rabuwarmu
tazo.Ardadu dajin haka sai yaja bakinsa yayi
shiru badan ya hakura ba,tabbas ko baiyi kwacen
doki ba sai yayi na dukiya,koda Ardadu yayi
wannan tunanin saiya dubi Yazid yace todai ya
kamata mu tsaya anan mu yada zango ni yanzu
na fara gajiya baya ga haka ina jin bawali.Koda
Yazid ya dubi sama sai ya fuskanci rana tayi
haske sosai lokacin sallar azahar ya nufo
take ya aminta da batun ardadu duk da cewar bai
yarda dashi ba.Adaidai wannan lokaci shima
Yazid
ya dauki salkarsa na ruwa ya nufi can bayan wani
dutse dan yayi bawali shi kuwa Ardadu sai ya tafi
can yamma da inda Yazid ya nufa cikin sauri
sauri ya nufi cikin daji ya rinka gudu.
Shi kuwa Yazid sai ya fito daga inda ya nufo har
ya samu guri ya kwanta bai jima da kwanciya ba
lokacin sallah yayi koda yayi alwala ardadu bai
dawo ba dan haka sai
ya dan jirashi dansuyi jam'i amma shiru ganin
kada lokaci

1 Comments On WASIKAR JINI 1 to 8
avatar
abdulrasheed-yusuf

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment