Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya
rube yasa makami ya sare abinsa da
hannunsa,tundai munyi nadama bisa wannan
kuskure da muka tafka ai ya kamata ka yafe
mana ka sani cewa har abada mune iyayenka na
jini baka isa ka canja mu ba duk inda ka wuce
za'a nuna ka ace kai dana ne babu wanda ya isa
ya kankare wannan.
Kafin waziri ridwan ya gama rufe bakinsa tuni
yarima zainur ya tari
numfashinsa da kakkaurar murya yana mai cewa
kada ka kara cewa kai ubana ne na jini babu
wani uba na gari wanda zai kyamaci dan daya
haifa a cikinsa face idan wannan da bai kasance
jininsa
ba,laifin me nayi muku kaida mahaifiyata har da
zaku tsaneni kuki bani irin soyayyar daya dace?
shin saboda kawai ra'ayina ya bambanta da naku
ne?
Shin saboda ku babu abinda kukeso a duniya
sama da kudi,mulki da zalunci?
Koda Yarima Zainur yazo nan a zancensa sai ya
fashe da matsanancinkuka na bakin ciki.Waziri
ridwan ya matso gaba zainur yakai hannayensa
da nufin ya janyo shi izuwa kirjinsa ya
rungumeshi amma sai yaji an kirawo
sunansa.Yana jin muryar wanda ya kirawo shin
saiya juya da sauri sukayi arba.
Ba wani bane yake shigowa cikin gidan face
sarkin yakin haiman,cikin sauri haiman ya karaso
gaban waziri ridwan ya zube kasa bisa
guiwoyinsa ya kwashi gaisuwa sannan ya mike
tsaye cikin girmamawa kansa a sunkuye saboda
biyayya yace ya shugabana lafiya kuwa naga
kazo gidana a wannan lokaci na daf da ketowar
alfijir?
Ai kama ta yayi ka turo a kirawo ni idan kana da
wata bukata a gareni.Koda jin wannan batu sai
waziri
ridwan yayi murmushi yace ai wajen dana nazo
ba wajenka ba amma kaima inason mu gana cikin
sirri,kodajin
™Abbas Abdulkadir Hada-Hada™
haka sai sarkin yaki ya dubi yarima zainur yace
dashi ya tafi izuwa cikin dakinsa.
Ba tare da wata gardama ba zainur ya juya ya
tafi izuwa bangaren da dakinsa yake shi kuma
haiman saiya wuce gaba izuwa falonsa sai suka
zauna bisa kujerun,take wani hadimi ya kawo wa
waizir ridwan ruwan shayi a kofi ya ajiye bisa
teburin dake gabansa shi kuma haiman sai
yayiwa waziri tayin shayin.
Waziri Ridwan ya murtuke fuska ya dubi haiman
a fusace yace ba shan shayi bane ya kawo ni
gidanka nazo ne domin nayi maka wadansu
tambayoyi,lallai inason ka bani amsoshinsu bisa
gaskiya kuma sakamakon dazai biyo baya dama
ce babba a gareka,tambaya ta farko a gareka
itace me sarki ya gaya maka a cikin wannan dare
na yau sa'adda ya gaiyaceka har cikin
kuryar turakarsa?
Tambaya ta biyu itace me ka sani
dangane da babban abin dogaron sarki wato
wasikar jini,kuma a ina aka boyeta?
Tambaya ta uku wacce itace ta karshe inason ka
gaya mini wasiyar da sarki yabar maka akan
yarsa gimbiya nauwara tunda ya
tabbatar da cewa kwanakin numfashinsa yazo
karshe.
Take sarkin yaki haiman ya mike tsaye yaje ya
dauko takobinsa wacce ke rataye a jikin bango
wannan ya durkusa a gaban waziri ridwan bisa
guiwoyinsa kansa na sunkuye ya mika masa
takobin
da hannayensa biyu yace ya shugabana ga takobi
na ka kasheni da ita domin hakan zai fiye mini
sauki akan na bayyana maka sirrin dake
tsakanina da sarki.
Ka tuna cewa yau sama da shekaru arba'in kenan
kai ma ina rufe sirrinka bisa duk irin tuggu da
makircin da kake shiryawa sarki don mallake
karagarsa ta mulki amma ban taba gayawa sarki
laifinka ba,daidai da rana daya sarki yana yawan
tambayata akan sirrinkanka amma ko sau daya
ban yarda na sanar dashi komai ba duk abinda
kaga ya sani akanka to ta hanyar karfin sihirin
tsafinsa ya
sani ai kuwa tunda har ban tona sirrinka ba a
gareshi lallao shima bazan iya tona nasa sirrin ba
a
gareka,duk ku biyun shugabanni nane kuma
kamar yadda ya zamo sarki kaima zaka iya zama
sarki,ta
yaya zaka iya yadda dani a lokacin da ka zamo
sarki tunda kasan cewa bani da sirri zan iya tona
maka
asiri wata rana.
Koda sarkin yaki haiman yazo nan a
zancensa sai jikin waziri ridwan yayi sanyi kuma
ransa ya baci ainun,zuciyarsa ta kama tafarfasa
kamar zata kone,nan take jikin ridwan ya kama
tsuma ya fisge takobin daga hannun haiman ya
zareta daga cikin kufen ya dagata sama da nufin
ya sareshi amma saiya kasa don haka sai ya
maida ita cikin kufen ya jefawa haiman abarsa
yace ka rabani da dana,kuma kaki taimaka mini
na hau karagar mulkin kasar nan a saukake,to ka
sani cewa nasan babu abinda sarki ke so face
dana zainur ya sami karagar mulki ina mai
tabbatar maka da cewa muddin ina numfashi a
doron kasa zainur bazai hau kan wannan karaga
ba nine zan hauta don haka
daga yau bani da babban makiyi a doron kasa
sama da zainur kuma nine ajalinsa.
Koda jin wannan batu sai idanun sarkin yaki suka
zazzaro ya dubi waziri ridwan cikin alamun
tsananin mamaki da tsoro yace
haba yakai waziri shin ka mantane cewa zainur
ne kadai danka a duniya yanzu kana nufin kace
kafi
kaunar duniya akan danka?
Waziri ridwan ta gyada kai yace kwarai kuwa
akan wannan karagar mulki na kashe uwata da
ubana amma gashi ban samu ba don haka na
gaba ma zan iya kashe dana domin na sameta a
duniyar nan kaf babu wani abu dayafi wannan
karagar mulki daraja a wajena amma a yanzu na
gane cwa mutum uku ne manyan abokan gabata
masu son rabani da wannan karaga kuma ba
wadansu bane face kai,zainur da kuma gimbiya
nauwara,muddin ku ukun nan kuna raye koda na
hau kan karagar mulkin kasar nan bazan iya
aiwatar da komai ba face na kawar daku.
Na sani cewa zan iya kashe ka yanzu a cikin
wannan daki naka tunda na fika karfin damtse,iya
yaki da karfin sihirin tsafi,amma idan na aikata
hakan sarki zai iya
wargazamini dukkan shirina,nasan sarki yasan
cewa nine na sa aka sa masa guba a cikin
maganinsa yasha,kuma na tabbatar da cewa
bazai wuce nanda wata biyu ba a raye a doron
kasa,matsalata kawai
shine rashin sanin inda wasikar jini take,tabbas a
yanzu ko kai ko yarima zainur dayanku yasan a
inda
wasikar jini take amma nasan cewa ko kasheku
zanyi ba zaku gaya mini ba,babu komai zansa ido
sosai a kanku naga ta yarda zaku tafi izuwa inda
wasikar jini take batare da kun sani ba.
Koda gama fadin hakan sai waziri ridwan ya juya
ya fice daga cikin yabar sarkin yaki a durkushe a
kasa cikin tsananin tashin hankali da dimaucewa
domin bai san abinda ya kamata yayi ba.
washe gari da safe har yarima zainur ya gama
kalaci tare da sarkin yaki da matarsa,sarkin yaki
baice dashi komai ba,sai bayan sarkin yaki ya
gama shiri tsaf zai tafi fada saiga yarima zainur
ya fito cikin shiri zai tafi waniwani,cikin mamaki
haiman ya dubi zainur yace ina zakaje yanzu da
sassafe haka kuma gashi kayi
shigar farauta?
Batare da boye masa komai ba zainur ya risina
ga haiman cikin biyayya yace zanje kasuwa ne
domin nagana da wani bakon bafatake daga nan
kuma idan da sauran lokaci inason na leka daji
domin yin farauta.
Koda jin wannan batu sai Haiman
ya jinjina kai sannan yace,abinda zan gaya maka
shine ka kula da kanka kuma duk inda zakaje da
duk abinda zakayi ka tabbatar da cewar babu mai
biye dakai don ganin sirrinka.
Sa'adda zainur yaji wannan batu sai yayi
murmushi yace nagode
abbana har zainur ya juya zai fice daga cikin
gidan sai ya juyo yace yakai abbana waishin jiya
da daddare kiran me sarki yayi maka ne?
Koda jin wannan batu sai sarkin yaki haiman ya
murtuke fuska yace babu ruwanka da al'amuran
dake tsakanina da sarki kamar yadda babu
ruwana da naka al'amuran da
kake kullawa asirrance.
Gama fadin hakan ke
™Abbas Abdulkadir hada hada™
da wuya sai haiman ya dagawa wani hadiminsa
hannu ya kawo masa dokinsa yahau ya fice daga
cikin gidan,shima yarima zainur saiya ruga izuwa
inda nasa dokin yake ya kama yahau,ya fice da
gudu daga cikin gidan ya nausa izuwa cikin gari
yana mai bin hanyar dazata kaishi izuwa kasuwa.
Lokacin da yarima zainur yayi nisa ga barin gidan
yazo wani wuri inda babu mutane sosai inda yake
daidaikun gidaje ne sai kawai yaga wani narkeken
kato tsaye a gabansa cikin shigar arnan
daji.Katon ya risina ga yarima zainur ya kwashi
gaisuwa sannan yace ya shugabana sarauniya
tace ta aikoni gareka tace lallai intafi dakai
gareta yanzu,koda jin wannan batu sai farin ciki
ya lullube yarima zainur musamman da yaji cewa
a yau zai sake ganin kyakkyawar fuskar sarauniya
lazwara amma daya tuno da yanason yaje ga
bakonsa Yarima Yazid ayanzu sai ya duni wannan
manzo cikin murmushi yace naji dadi da
sarauniyarka ta cika alkawari amma idan da hali
inason ka rakani izuwa kasuwa yanzu domin
naga wani bako nawa.Manzo sarauniya lazwara
ya gyada
kai yace ai bazan iya sake tsayuwa ba anan koda
tsawon dakika arba'in bisa umarnin gimbiya
saidai kayi hakuri,kuma abinda nakeso dakai
shine yanzu
kabi wannan hanya ka fara yin gaba ni kuma zan
tsaya na tabbatar da babu wata matsala domin
na fuskanci kamar cewa akwai masu binka a
baya.
Gama fadin hakan keda wuya sai sukaji motsi
akan duhuwar ciyayi koda suka nufi wajen sukaji
an fita da gudu suka kasa tsere yabar yarima
zainur tsaye a wajen sai bayan lokaci mai dan
tsawo
sannan manzo ya dawo yace sun bace ni banga
ko su waye ba,ya shugabana saika kula da kyau
domin akwai masu sa ido akan al'amuranka,yana
gama fadin hakan sai ya ruga da gudu a kasa da
kafafunsa tamkar akan iska yake gudun.cikn sauri
yarima
zainur ya zuburi dokinsa da gudu ya bishi amma
saboda karfin gudun manzon sai gashi dokin
zainur ya kasa cimmasa,al'amarin dayai matukar
baiwa yarima zainur mamaki kenan domin bai
taba ganin mutumin da yafi doki gudu ba sai yau.
Nan take ya gane cewa lallai wannan manzo da
lazwara ta aiko shine mafi dacewa dayin wannan
aiki,haka dai wannan manzo da yarima zainur
sukayi ta sakin
gudu a cikin daji suna ketawa ta cikin
kwazazzabai,duhuwoyi kai wani lokacin ma har
takan wadansu duwatsun suka bi inda sai
kwararren masanin daji ne zai iyabi,amma sai
gashi wannan
manzo yana ta ratsa duk da cewa ko takalmi
babu a kafarsa.
Dan wata kaya kuwa take yake bi takanta tamkar
sawun kafarsa na karfe ne,wata barauniyar hanya
suka biyo ba waccen hanyar daya sani bace
wacce sukabi sukazo birnin arnan daji ko rabin
sa'a basu shafe ba suka iso birnin na arnan daji.
Da isowarsu sukaga gaba dayan jama'ar birnin
mazansu da matansu,yara da manyan sun taru
sunyi dandazo a cikin wani babban fili sunyi
kawanya ga dukkan alamu dai wani abu akeyi a
tsakiyar filin suke kallo,tun daga nesa aka hango
manzon sarauniya ya dawo sai aka busa wani
katon kaho.
Take hankalin kowa ya dawo izuwa bakin kofar
shigowa birnin kuma jama'ar suka dare a tsakiya
aka baiwa manzo da dokin zainur hanya suka
kunno kai,nan take zainur ya hango wadansu
zakakuran mayaka guda biyu suna ta fafata
kazamin yaki mai tsananin ban tsoro domin
kowannensu yana neman ran abokin fadan nasa
ne.
Sudai wadannan jarumai biyu sune mafi girma da
kira ta sadaukantaka a gaba daya mazajen dake
cikin birnin na arnan daji,kuma komai jarumtakar
mutum idan yayi arba da wadannan jarumai biyiu
dole ne ya tsorata don yasan cewa karo dasu ba
wasa bane saboda kai da
ganinsu kasan cewa suna da matukar karfin
damtse idan kuwa kaga yadda suke yaki da
tsananin zafin nama gami da jarumtaka ta ban
al'ajabi dole ne a sallama musu,acan gefe daya
kuma bisa wani gini
mai tudu sai yarima zainur ya hango sarauniya
lazwara zaune ta harde kafa daya bisa kan daya
ga
kuyanginta sama dasu dari a kewaye da ita,daf
da ita kuma dakaru ne dauke da makamai sama
dasu su dubu uku.duk inda yarima zainur ya
hanga sai yaga dakarun birnin rututu.
A tsaitsaye tamkar yaki zasu fita,babban abinda
yafi bashi mamaki shine tsananin yawan dakarun
sarauniya lazwara wanda indai lissafi za'ayi sun
ninka dakarun nasu birnin sau goma,to waishin
me yasa sarauniya lazwara batayi amfani da
wannan dama ba ta yakemu ta dawo damu
karkashin mulkinta?
Amsar da yarima zainur ya kasa baiwa kansa
kenan,abinda dai bai
sani ba shine yawa mayaka bashine nasarar yaki
ba,hanyoyin da akebi a samu nasara a yaki suna
da yawan gaske.lokacin da manzo da yarima
suka ratso ta tsakiyar yan kallo suka wuce
wadannan jaruman gasa masu fafata yaki sai
suka tunkari inda sarauniya lazwara ke zauna
koda lazwara ta
hangosu sai fuskarta ta fadada da murmushi ya
mike tsaye daga kan kujerar da take zaune ta
sauko
kasan ginin da take bisa tari yarima zainur ta
ruke dokin nasa tana mai yi masa barka da zuwa.
Al'amarin dayai matukar baiwa gaba dayan
jama'ar mamaki kenan domin wannan ne karo na
farko da akaga sarauniya lazwara ta taso da
kanta ta taryi wani bako.Yarima zainur ya sauko
daga kan
dokin nasa sannan ya risina ga Lazwara ya
kwashi gaisuwa,lazwara ta karbi gaisuwar tace
lale
marhaban da zainur dan waziri ridwan biyoni
muje izuwa cikin fadata domin mu zauna mu
kulla
yarjejeniya.Cikin mamaki yarima zainur ya budi
baki da nufin cewa wani abu amma sai lazwara
ta tari
numfashinsa tace ka cika gaggawa ai bai kamata
kayi mini wani korafi ba,kamata yayi ka tsaya kaji
abubuwan da zanzo maka dasu.Tana gama fadin
hakan saita juya ta nufi wani katon tsauni wanda
akayi masa kofar shiga ta farin karfe dakaru
shida na take mata baya,batare da fargabar
komai ba kuwa yarima zainur ya bita a baya.
™Abbas Abdulkadir hada hada™
koda suka shiga cikin tsaunin sai ka yarima
zainur ya daure kuma ya zama kamar wani dan
kauye ya
kama kalle kalle da waige waige ba komai ne ya
haddasa hakan ba face ganin yadda aka kawata
wannan fada wacce ko fadar sarki aiyuba bazata
fita komai ba,duk da cewa a cikin kogon tsauni
akayi
wannan fada amma ko ina a haskake yake yadda
ko allura ce ta fadi kasa sai ido ya ganta.
Girman wannan fada ya ninka ta fadar sarki
aiyuba sau uku
ga fadi da tsawon gaske amma ko ina a shimfide
yake da wani koren kilishi mai tudun gaske gami
da
tsananin laushi domin lokacin da yarima zainur
ya dora kafarsa guda akai saida da tsoro ya
shigeshi
don ya zata lumewa zaiyi.An zuba kujeru na
alfarma masu yawa, wadansu suka yiwa fadar
kyau,karshen fadar an girke wata katuwar karagar
mulki ta karfen zinare wacce akayi mata siffar
tsuntsun dawisu.
Dakaru sama da dubu goma ne suka kewaya
wannan fada sannan kuma ga bayi,kuyangi da
hadimai nansu da yawa suna ta aiyukansu kaca
kaca a cikin fadar.Koda shigowar sarauniya
lazwara cikin wannan bada sai gaba dayan
mutanen dake ciki suka tsaya cak a inda suke
suka daina motsi tamkar
gumaka saboda biyayya harsaida lazwara taja
yarima zainur izuwa can saman gini mai tudu
inda
karagar mulkin take,suka zauna tare sannan
hadiman suka ci gaba da harkokinsu kai kace
ruhinsu aka zare kuma aka dawo musu dashi.Nan
take aka kawowa yarima zainur abinci da abinsha
na
alfarma sama da kala da dari bisa faranta ake
jere a gabansa har da yayan itatuwa iri iri har
dama irin wanda idanunsa basu taba gani
ba,kuma harshensa bai taba dandanawa ba.
Nanfa mamaki ya turnuke yarima zainur ya
tambayi kansa a cikin zuciyar yace ta yaya
wadannan arnan daji suka sami wannan
gagarumar daula alhalin suna rayuwa a cikin
wannan kungurmin daji kuma ko wata suturar
kirki basa sawa face fatun dabbobin daji,amsar
da yarima zainur ya kasa baiwa kansa kenan.
Nan take lazwara tayiwa zainur tayin abincin
suka kama ci tare saida suka ci suka sha sukayi
hani'an sannan lazwara ta dubi yarima zainur
cikin nutsuwa tace yakai yarima zainur yaudai
gashi na cika alkawari na turo anzo dakai
dangane da bukatarka ta son koyon yaki a
wajena.
Na amince zan koya ma amma bisa sharadi uku,
sharadi na farko shine dolene ka fara jarraba
jarumtakarka akan jaruman nan nawa guda biyu
wadanda ka gansu a can kofar wannan fada tawa
suna artabu.Idan har ka sami nasarar kaisu kas
ko ka sami nasarar hallakasu a sannan ne zan
fara koya maka irin nawa horon yakin badon
komai ba
sai saboda nina fisu karfi da iya yaki sau uku
kuma babu wanda zai iya jure irin horon yakina
face yafi
wadancan jarumai biyu karfi da iya yaki.
Sharadi na biyu shine bayan na koya maka yaki
ka tafi izuwa dajin hajarul aswad ka sami nasarar
karanta WASIKAR JINI idan ka zamo sarki zaka
sadar da harkokin kasuwanci a tsakanin birnina
da
naka,ma'ana zaka bude mana kofar birninka mu
rinka shiga muma zamu bude muku kofar
birninmu ku rinka shiga kuma za'a yarda aure ya
rinka faruwa a tsakanin mutanenmu da naku,
sharadi na karshe zakayi alkawari a rubuce cewar
har abada birninku
bazai taba yin yunkurin kawo mana harin
sumame ba domin maishe damu karkashin ikonku
Lokacin da sarauniya lazwara tazo nan a
zancenta sai hankalin yarima zainur ya
dugunzuma ainun ya dubeta cikin alamun firgici
da tsananin damuwa yace haba yake
wannan sarauniya saboda me zaki shimfida mini
wadannan sharuda haka masu tsananin
tsauri,tabbas ko makaho ne ya shafi ni sannan ya
shafi wadancan jaruman biyu naki yasan cewa
bazan iya samun
nasarar yaki ba akansu ba domin kuwa ance
alamar karfi tana ga mai kiba,dangane da sharadi
na biyu kuwa dana uku ki tuna fa cewa fiye da
shekaru dari baya da suka shude babu wani sarki
wanda ya taba jarraba yin kasuwanci da ku koya
hada zuri'a daku kuma babu sarkin daya taba
daukar muku
alkawarin cewar bzai nemi birnin ku ba akan ya
dawo karkashinsa,akan wane dalili kike son ni na
karya tsohon tarihi wanda iyayena da kakannina
akansu suka gushe.
A gaskiya kinzo mini da babban al'amari wanda
yafi gaban hankalina da tunani na saboda haka
ina bukatar naje nayi shawara.
Koda jin wannan batu sai sarauniya lazwara ta
kyalkyale da dariya daga can kuma saita murtuke
fuska ta dubi zainur tace bazan hanaka kaje kayi
shawara ba,amma kasani cewa kwana goma sha
hudu ne kacal a gabanka ka koyi wannan horon
yaki wanda dole saika sameshi sannan zaka iya
ratsawa cikin dajin da zakaje ka sadu da wasikar
jini,har ka sami damar karantata in ba haka ba
kuwa har abada wanna dama ta wuce ka,na baka
kwana uku rak kaje kayi shawara ka dawo gareni
amma fa idan ka haura kwana ukun shike nan
damarka ta wuce.
Koda gama fadin hakan sai sarauniya lazwara ta
dubi wannan
manzo wanda yazo da yarima zainur tace yakai
saidur maza ka yiwa yarima jagora ya koma
izuwa cikin birninsu na latul harus amma kabi
dashi ta cikin boyayyiyar hanya ta uku.
Saidur ya risina ga sarauniya lazwara yace an
gama ya shugabata,nan take saidur ya nufi kofar
fita daga fadar shi kuma
yarima zainur saiya mike tsaye da sauri yabi
saidur a baya yana waigen sarauniya lazwara
yanayi mata wani irin kallo wanda ta kasa ne
ma'anarsa shin kallo ne na soyayya ko kuwa
kallo ne na takaici bisa zabin data bashi.Koda
taga ta kasa baiwa kanta amsar wannan
tambaya sai itama ta maida masa
martanin kallo mai dauke da alamar tambaya
wanda ya jefashi cikin rudani da wasi wasi.
Har yarima zainur ya kusan isa bakin kofar fita
daga fadar sai sarauniya lazwara ta kira sunasa
cikin matukar mamaki ya tsaya cak ya waigo
yana sauraron karasowarta a lokacin data durfafi
inda yake,da isowarta daf dashi saita dubeshi
tace idan ka isa
wajen abokinka bakon bafatake Wanda yazo daga
birnin Haural kace dashi inayi masa barka da
zuwa kuma shima ina gaiyatarsa izuwa nan
fadata a lokacin da zaka dawo tunda shima yana
sha'awar
ganin irin jarumtaka ta da iya yakina amma ka
gaya masa cewa duk abinda yake zaton zai faru
bashinezai faruba.
Koda sarauniya lazwara tazo nan a bayaninta sai
Yarima Zainur ya cika da tsananin mamaki Kuma
ya tsorata ainun da al'amarinta..
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Hudu (4)
Part B
.
Kuma ya tsorata ainun da al'amarinta ya gamsu
cewa lallai Lazwara ta cika gagarumar matsafiya
tunda gashi tasan abinda bata nan ya faru.
Nan dai yarima zainur ya juya ya fice daga cikin
fadar jikinsa a sanyaye kamar wanda ruwa
yaci,yana fitowa ya hango saidur ya nausa cikin
daji yana mai bin wata
sabuwar hanya,cikin gaggawa zainur ya kama
dokinsa yahau,ya zubureshi da gudu har yaje ya
riske saidur.
Saidur ya dubi zainur yace wannan hanyar da
zamubi doki bazai iya bin taba,ina mai
shawartarka dakabar dokinka anan idan har kana
bukatarsa in ka sake dawowa ka dauki abinka.
Har zainur yayi niyar yaki yadda da wannan
shawara ta saidur sai wata zuciyar tace dashi ai
kuwa masu iya magana sunce da dan gari akan
ci gari.
Tunda har saidur ya bani wannan shawara kama
tayayi nayi aiki da ita tunda shi ya fini sanin
hanyar kuma nasan cewa shi baya bukatar doki
tunda yafi doki gudu da juriyar tafiya a daji.
Nan take ya tsaida dokin nasa ya sauko daga
kansa kuma ya korashi da baya ya koma izuwa
birninsu saidur.
Koda ganin haka sai saidur ya falfala da
azababben gudu izuwa cikin dajin.
Aikuwa sai zainur shima ya take masa baya ya
mai tsala gudu iya karfinsa,in badon ya kasance
tsohon mzfarauci ba wanda ya saba gudu a cikin
daji yayin yin farauta da cikin dakiku kadan saidur
zai bace masa da gani.
Duk da hakan ma saida ya bashi tazara maiyawa
yayi masa fintinkau.
Inda ya rinka samun matsala mashine ya cikin
wadansu kogunan
duwatsu ya rinka bi dashi wanda mutum bazai
taba zaton cewa suna bullewa ba,kai wani kogon
dutsen ma baya bullewa saidai kaga munyi nutso
a cikin kogin dake cikinsa mun fito ta cikin wani
babban kogo sannan muci gaba da iyo a cikinsa
harmu fita mu cigaba da gudu mu sake fadawa
cikin wani
kogon,kai a wannan rana dai nasha bakar wahala
domin saida muka shafe sa'a uku cur muna tayin
wannan uban gudu a daji kuma muna ratsawa ta
cikin kogunan duwatsu da kogi kai kace gudun
ceton ranmu muke,
saida na gaji likis na rinka haki kamar raina zai
fita kuma ban kasa daina hango saidur ba har
muka iso iyakar birnin arnan daji.
A wannan lokaci ne na durkushe kasa bisa
guiwoyina ina ta fama hakin kamar raina zai fita
gashi makwogarona ya bushe saboda tsananin
kishirwa,shi kuwa gogan naka saidur ko alamar
gajiya ma babu a tare dashi,kuma babu wani haki
da yakeyi,kawai sai ya dubeni cikin murmushi ya
cire battarsa ta ruwan ya miko mini,cikin hanzari
na fisge battar daga hannunsa na budeta na kafa
abakina na kama kwalkwalar ruwan har saidai
nayi gatsa sannan na sauke kaina kasa na
mikawa saidur battarsa.Yana karbar battar saiya
risina a gareni
yace na barka lafiya yarima sai gani na biyu idan
ka dawo birnin mu.Yana gama fadin hakan ya
juya da baya ya falfala da wannan azababben
gudu nasa tamkar giftawar tauraruwa mai
wutsiya kafin kace wani abu tuni ya bace mini da
gani.
A sannan ne fana dawo cikin hayyacina sosai har
na tsaya ina mamakin yadda akayi ma har na iya
bin bayan saidur da gudu har yazamana cewa bai
bace mini ba alhalin gudun nasa tamkar walkiya
ne.Saida na shafe yan dakiku zaune a kas ina
haki da hutawa sannan
na mike tsaye na cigaba da tafiya ina mai
tunkarar cikin birnin latul harus kai tsaye na
durfafi kasuwa
ina isa gidan da yarima yazid yake sai na iskeshi
tare da abokin tafiyarsa Ardadu a tsaye a kofar
gidan suna shirin su yawata a cikin kasuwar
domin su sayi irin kayayyakin da suke bukata.
Tun daga nesa Yarima Zainur ya kwalawa yarima
yazid kira,sai
yarima yazid ya waigo cikin farin cki ya taryeshi
cikin alamun murna yazid ya dubi zainur yace
yakai abokina kayi sani cewa tunda muka rabu ka
barni a cikin zulumi da wasi wasi domin gani
nakeyi kamar ba zaka sake dawowa gareni
ba,kuma sai na fara
tunanin cewa duk yadda ake ciki ka zagaye ka
tafi izuwa birnin sarauniya lazwara ba tare da
kazo ka gayyace ni ba mun tafi tare bisa wannan
dalili ne zuciyata asare kuma guiwoyina sukayi
sanyi na
aiyana a raina cewa shikenan duk burina da
shirina ya ruguje bazan taba samun abinda ya
baroni da
kasarmu ba.
Lokacin da yarima yazid yazo nan a
zancensa sai yarima zainur ya dubeshi yayi
murmushi sannan ya zaiyane masa duk abinda ya
faru a gareshi tun daga lokacin da suka rabu
kawo iyanzu,koda jin wannan al'amari sai
hankalin yarima yazid ya dugunzuma ainun ya
dubi zainur cikin alamun tsananin damuwa yace
kai yanzu dawa zakayi shawara bisa wannan
sharadi da sarauniya lazwara tazo maka dashi?
Zainur ya gyada kai yace babu wanda zanyi
shawara dashi face kai.
Cikin matukar mamaki yazid yace saboda me
zakayi shawara dani alhalin kana da makusanta
kuma
aminai ai kamata yayi kaje kayi shawara da
sarkin yaki ko kuma gimbiya nauwara amma bani
ba,kai gimbiya nauwara ce ma tafi cancanta da
baka shawara tunda itace ta fara sanar dakai duk
sirrin dake cikin wannan al'amari.
Koda jin haka sai Yarima zainur ya kada kai yace
gimbiya nauwara ba zata iya taimaka mini ba
kamar yadda na gaya maka da farko cewar
inason ka dada gamsar dani akan addininka da
ubangijinka,saboda haka inaso mu ajiye batu
neman taimakon gimbiya lazwara a cikin tafiyar
da zamuyi izuwa inda wasikar jini take,me zai
hana mu dogara da ubangijinka akan ya bamu
kariya idan harnaga irin karfin ubangijinka da
kuma isarsa a cikin wannan tafiya mai mugun
hadari da zamuyi lallai zan karbi addinin naka
tunda gabannin ma mu isa inda WASIKAR JINI
take,
koda yarima zainur yazo nan a zancensa sai farin
ciki ya lullube yarima yazid yace na amince da
wannan shiri naka kuma ina mai tabbatar maka
da cewa ubangijina
bazai bani kunya ba lallai zaka sha mamaki kuma
zakaga abubuwan al'ajabi da idanunka yanzu
inda matsalar take shine ya za'ayi musan hanyar
daya kamata mubi
don zuwa inda WASIKAR JINI take?
koda jin wannan tambaya sai yarima zainur yaja
dogon numfashi ya ajiye sannan ya dubi yazid
yace kafin nanda cikar sati biyu zamu sani,yazid
yace yaya akayi kasan cewa zamu sani din kafin
cikar sati biyu?
Wanda ya sanar dani batu WASIKAR JINI shine
ya sanar dani hakan amma fa ina zargin cewa
sarkin yaki haiman ya san komai akan WASIKAR
JINI amma bansan
dalilin da yasa yake boye mini ba,kuma ina mai
tabbatar maka da cewa wadanda suka san batun
WASIKAR JINI A garin nan kaf basu wuce mutum
biyar ba daga ni sai nauwara,sai sarki da kuma
mahaifina waziri ridwan.koda jin wannan batu sai
yarima yazid ya jinjina kai ya dubi zainur yace
abinda nakeso dakai shine ka kula da kanka
sosai domin mahaifinka zai iya sa ido sosai
akanka kai da
sarkin yaki haiman kuma duk yadda zaiyi yasan
duk halin da kuke ciki sai yayi ba don komai ba
sai don yasan hanyar dazai bi ya rigaku zuwa
inda WASIKAR JINI take.
Zainur ya numfasa yace tabbas
sarkin yaki yayi mini nuni da hakan,ma yanzu dai
mubar wannan magana haka muje na raka ku
cikin
kasuwa don na fuskanci cewar so kuke kuje kuyi
siyayya.
Yazid yayi murmushi yace wannan gaskiya ne.
Nan take yarima yazid ya yafito Ardadu da hannu
ya taho garesu kafin Ardadu ya riske su tun sun
kara gaba inda zainur ya dubi yazid yace yakai
abokina inason fa ka sani cewa hali zanen dutse
ne don haka bana jin cewa Ardadu zai ajiye
dukkan miyagun halayensa gaba daya kuma bana
fidda ran
cewa wata ran zai iya cin amanarka don haka
jansa a jikinka abune mai hadari.
Naso ace tun sa'adda kukayi gamuwar farko ka
aika dashi barzahu domin barin mugun iri
kamarsa a doron kasa ba karamin ganganci bane,
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Hudu (4)
Part C
.
Naso ace tun sa'adda kukayi gamuwar farko ka
aika dashi barzahu domin barin mugun iri
kamarsa a doron kasa

1 Comments On WASIKAR JINI 1 to 8
avatar
abdulrasheed-yusuf

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment