Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwanciya yaji kumarinshi
ya fara dawowa yanzu ya fara jin baiyi asarar
zamowa mai kwazo ba sabanin a baya da yakeji
tamkar shi ba kowan kowa bane a filin daga,duk
irin kokarinsa na korar arnan daji da yanfashin da
yakeyi sai yaji ya tashi a banza,amma yanzu da
ibin Haisham ya fara
nuna cewa suma zasu iya sai hankalinsa ya fara
kwanciya.Ya tsurawa ibin Haisham idanuwa yana
son jin abinda zaice takamar sarki Aiyuba.
Ibn Haisham ya cigaba da cewa takamar sarki
Aiyuba bai wuce
rubutacciyar WASIKAR JINI ba.Wannan wasikar
itace takamar sarki itace takamar duk wani mai
neman daukaka a cikin wannan duniya.Bani da
tarihin WASIKAR JINI amma ina da sani cewa
itace karfin
sihirin sarki Aiyuba itace takamarsa itace sirrin
birninsa tabbas idan waninmu ya mallaki wannan
WASIKAR JINI to babu shakka duk irin takamar
sarki
Aiyuba da bunkasarsa da wani kuri nashi sai ya
saurara kuma sai yayi shayinka,dan haka kafin
cikar
wannan rana da tsufa bai riskeni ba sai naje
kasar na samu wannan wasikar domin na dawo
da ita cikin wannan al'umma tamu ta musulunci
tabbas idan yayi bincike ya gano cewar wannan
wasikar tana cikin wannan kasar,sai ya hakura da
duk wani mugun nufi a garemu sannan kuma
zamu
juyashi yadda mukeso kamar yadda ya juya
ragamarmu,inda ace wannan wasikar zata samu
da basai mun sha wahala mun gwabza yaki dasu
ba,da zarar sunji tana garemu hankulan baki daya
nahiyar nan zai tashi kamar yadda aka maida mu
makaskanta sai mun zo mun zama babu sama
damu.Abin takaicin da kaico babu yanda zamuyi
mu dauko wannan wasikar,amma da akwai
samartaka a tare dani babu abindazai hana ni yin
shiri na tunkari kasar Lautul Harus dan na dauko
wannan wasikar.
Koda jin wannan batu sai baki daya jama'ar dake
gurin sukayi shiru suka nutsu suna kallon Ibn
Haisham shi kuwa Yarima Yazif sai ya mike tsaye
ya dubi kowa dake cikin fadar sannan ya tsayar
da kansa ga kallon Ibn Haisham yace,zuciyata
bata karaya,kuma ban fansar da rayuwata ga
tsoron kafurai ba,zan iya duk abinda ya kamanayi
dan
fansar daukacin al'umma ta,yakai wannan babban
malami ina mai tabbatar maka da cewa a shirye
nake dana yi JIHADI dan haka na shirya yanzu
haka danayi jihadi dan haka na shirya yanzu haka
ka
sanar dani labarin WASIKAR JINI nayi alkawari da
yardar Allah ina nan tafe da ita a cikin kwanakin
da
suka rage mana.
Koda jama'ar dake fadar sukaji wannan batu sai
suka dinga kallon kallo suna masu mamakin
yarima ba don komai ya cikasu ba face shi
yarima tunda ya taso baya kaunar fita koda
wajen kasar dukda ya kasance gagarumin
sadauki bayason fita ko ina koda yan fashin
sumame ne suka kawo hari zuwa cikin kasar da
ya ratattakesu zuwa bakin ganuwar garin
shikenan sai ya dawo bai taba takawa yabar cikin
kasar ba tunda aka haifeahi kawo iyanzu bai san
ko ina ba.
Waziri ya dubi Yarima Yazid
yace,yakai Yarima shin kasan inane kasar Latul
Harus kasan kuwa hadarin da yake ciki
ballantana
kaje da zummar daukar abu mafi daraja daga
garesu tabbas idan kayi wannan gangancin kamar
kana kokarin neman tsayawar numfashinka ne,
yakai Yarima kayi hakuri kayi zamanka anan
domin mahaifinka yana halin MUTUWA KO
RAYUWA ka
duba halin da mahaifinka yake ciki mana,idan
kayi la'akari da irin halin da yake ciki na mutuwa
da rayuwa bai kamata ace kaima ka rasa
rayuwarka a kasuwar daukar rai ba.
Koda jin wannan sai Yarima ya sunkui da kai
daga bisani ya daga kai yace,duk abinda zai faru
rubutaccene daga Ubangijinmu,zamana a cikin
wannan kasa tamu ta Haura bata da wani amfani
inaso ka sani mahaifina yana cikin tsananin
rashin lafiya wanda bazai samu kansa ba sai
washe garin gobe inkuwa ya farka duk yanda
akayi aka sanar dashi abu mara dadi babu
shakkar likitansa ya tabbatar min da zai iya rasa
rayuwarsa, dan haka ya zama dole koda rundunar
mayakan kasar Latul Harus zasu tunkaromu na
fita na tare su dan gudun kada su shigo cikin
kasata har abbana ya farga da halin da ake ciki
hankalinsa ya
gushe zuciyarsa ta buga ya fadi ya mutu,dan
haka ya zame min dole nayi wannan fita a yanzu.
Koda Yarima Yayi wannan furucin sai ya fice
daga cikin dakin taron bai zame ko ina ba sai a
cikin gidansu koda ya isa sai ya riske
mahaifiyarsa a zaune a kusa da mahaifinsa tana
risgar kuka
Yarima ya risina a kusa da ita duk abinda ya faru
ya kwashe ya sanar mata.Koda jin haka sai ta
dubeshi tace,kai kuwa ta yaya kake hangowa
kanka nasara baya ga kaji irin hatsarin da yake
cikin kasar sarki Aiyuba,yakai dana mafi soyuwa
a raina wannan abu da kake kokarin yi tamkar
kana neman tarar aradu ne.Koda jin wannan batu
sai Yarima ya dubi umman tasa sannan ya nuna
mata mahaifinsa dake kwance rai a hannun Allah
yace,wannan Abba nane akwance mutuwa yau ko
gobe,ya ummina kina sane da cewa idan Abbana
ya farfado kafin cikar wa'adin da likita ya sanar
damu ba tabbas sai rundunar sarki Aiyuba ra cika
mana kasa ta batse ta yaya kunnuwan sarki zasu
rufe daga jin sautin karar karafkiyar takubba,ta
yaya kunnensa zai kange daga jin karar tafiyar
kibiyoyi,
ya ummina abinda nakeson sanar dake shine
babu abu mafi masalaha face nayi tattaki zuwa
kasar Latul Harus domin na nemo abinda zai
zamo garkuwa a tsakaninmu da zaluncin sarki
Aiyuba,babu abinda nake bukata daga gareki face
ki samin albarka ya ummina inaji a jikina akwai
alamar samun nasara a kudirina.
Koda yazo nan sai tayi shiru daga bisani
tace,yakai dana ya zama dole na barka kayi
wannan tafiya domin hujjarka tafi tawa saidai duk
da hakan idan ka tafi kana sane da cewa akwai
kananun ayari ko dodannin da suke kawo bara a
garemu,yanzu idan sukaji maganar tafiyarka
kasan saisun addabemu da kawo hari,in kuwa
zasu ci gaba da kawo hari to babu shakka sai
wata rana kunnuwan mahaifinka yaji kuma kasan
abinda yake
wakana daga lalurarsa,dole zaiji kuma zuciyarsa
zata iya bugawa domin kuwa duk cikin kasar nan
babu maharbin da ya wuce kai haka zalika babu
wanda ya
iya yakin sunkuru kamar kai,kai kadaine zaka iya
yin karo da arnan daji na tsawon kwana biyu ba
tare da wani yaji ba,saidai da wannan nake maka
bankwana domin tafiyarka tafi zamanka
alheri.Koda jin wannan batu sai yayi murmushi ya
kuma sumbaci Abbansa ya shiga dakinsa yayi
shigarsa ta mafarauta ya fice daga cikin gidan.
Wannan shine dalilin fitowar Yarima Yazid daga
gida.
Dan haka ya cigaba da nausawa babu ji babu
gani ko waiwaye bayayi,bashi da fata face yaga
yayi tsinke a cikin kasar Latul Harus.
Yarima Yazid yana cikin wannan tafiya saidaya
zo wata kwana da idan ya bita shike nan ya
daina hango ganuwar birninsu ya daina hango
sashin kasarsu gaba daya,koda zuwa wannan
kwanar sai ya
waiga koda waigawaesa sai gabansa ya
fadi,hankalinsa ya dugunzuma ya shiga cikin
tsananin tashin hankali,bai tsaya bata lokaci ba
ya fito da KWARI DA BAKANsa dake sakale a
kafadarsa ya danata a cikin mashi ya koma da
baya cikin tsananin gudu tamkar zai tashi sama.
MAI YARIMA YAZID YA HANGO?
SHIN INA LABARIN YARIMA ZAINUR?
SHIN YARIMA YAZID ZAI SAMU DAMAR
MALLAKAR WASIKAR JINI?
SHIN MECECE MA WASIKAR JINI?
Domin jin duk wadannan tambayoyi sai mu tara a
littafi na gaba don jin amsoshinsu.
Yakuka ce dan naga kamar ma littapin bai
mukuba dan bana kallon commnt din masu cewa
suna so.
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Biyu (2)
Part A
.
LOKACIN da Yarima Yazid ya juya rike da
gwafarsa daya danata sai ya kasance yana wani
gudu mai
abin al'ajabi duk inda yayi taku kamar sau arba'in
a kasa saiya daka tsalle sama ya tafi a cikin
iska,dan haka kafin kace meye wannan ya
kusanci kofar ganuwar birnin Haurul.Ba komai
yasa Yarima Yazid
yin wannan gudu ba face wata kura data taso ta
tokare sararin samaniya,kurar ta toshe kofar garin
ta hada gagarumin hadari a daidai kofar ganuwar
birnin Haural,tsilli tsilli idanuwansa ya fara hango
masa ayarin dakarun yan fashi sunkai kimanin
dubu goma,kowannensu rike yake da makami mai
barazana ga rayuwar dan adam.
Lallai wadannan ayarin yan fashi sun isa abin
tsoro da ja da baya,duk wata jarumtakla idan tayi
tozalo da irin girman wadannan ayarin na yan
fashi da kuma tarin mangara mangaran
makamansu dole shakku ya shiga cikin zuciyarsa
amma abin mamaki yadda Yarima ke cin uban
gudu bashi da buri face ya isa garesu ya hanasu
shiga cikin birninsu ko ta tsiya tsiya. Amma koda
ya kusanto su sosai sai suka
banke kofar birnin suka daga makamansu sukayi
kuwa akan dakarun da suke tsoron kofa.Nan take
suka murkushe su cikin kankanin lokaci suka
kama rufe kofar birnin suka ci gaba da nausawa
cikin garin.
Koda Yarima ya hango sun rufe kofar birnin sai
hankalinsa ya tashi ainun amma da fushinsa ya
kara
ninkuwa ya tabbatar idan ya tsaya kokarin bude
kofar zasu iya isa cikin birnin har suyi barna,sai
kawai ya daka wani uban tsalle ya tashi sama
kamar tsuntsu,koda yayi sama sai ya fara saki
mashin daya dana tun fara hangowarsa dasu.
.
Jarumi Yazid gwarzon jarumi ne masanin iya yaki
da gwafa wannan dalili ne yasa yake iya tarwatsa
dakarun duk yawansu domin idan yana harbi da
kibiya bazakayi
tsammani mutum ne yake tabewa ba yana
sakinta saboda tsananin karfin tafiyar kibiyar,a
duk sa'adda
ya saki mashi ya fita daga cikin gwafa baya
faduwa kasa face ya soke mutum biyar ko shida.
Idan kuwa a kuskure yayi harbin sai wannan
mashin ya soke mutum sama da goma.Dan haka
tun daga sama suka fara jin ana musu ruwan
kibiyoyi,kafin su ankara mazaje sama da arba'in
sun zube kasa matattu ko shurawa
basayi.Dakarun ayarin yan fashin suka ja tunga
suna masu mamakin daga inda akeyi musu
wannan dauki ba dadi,kafin su ankara sai ga
jarumi Yazid ya dira bisa kafafunsa a
gabansu,Yana dirga sai ya kara dame gwafarsa
ya sake jikin iska kafin ta isa garesu ya kara
sakin wasu guda biyu.
Aikuwa sai yanfashin nan suka ci gaba da
zubewa kasa matattu.Koda shugaban yanfashin
yaga irin barnar da Yarima Yazid yake yiwa
yaransa sai yayi wata hatsabiyar kara ya yunkura
ya cire wani
katon katari da yake rataye a kubin rigarsa ya
dagashi sama ya jinjina asama yayi kuwa ga
jama'arsa nan take su duka suka afka kan
Yarima
Yazid.Shi kuwa sai yaja da baya ya zuba masu
har guda biyar a cikin gwafar ya dame ya sakar
masu,nan yake ya rage wasu daga cikin masu
tunkaro shi.
A sannan ne ya daka tsalle sama ya nufi ayarin
yan fashin babu takobi ko gatari a
hannunsa,amma yana isa garesu ya tari wasu
karata
su biyar ya sunkuya ya kwashe kafafuwansu cikin
bajinta sukayi sama suka zube a kasa.
Makamansu sukayi kasa.Koda ganin haka sai ya
dauki takobi
gami da wani gatari yana daukar wannan ya rike
katamau nan take ya shiga cikinsu ya fara
kuntata
musu,cikin tsananin bajinta ya fara sare
kawunansu yana sare su da gatarin hannunsa.
Wohoho idan kaji ana sa gudu ki gudu ne bai
zoba,nan take Yarima
Yazid ya kuntatasu ya rage musu yawa duk inda
yasa gaba saidai yan fashin masu kumari da kai
bara sun koma suna rike kugu gami da yin
warwas a kasa.
Wannan al'amarin ba karamin tada hankalin
shugaban yan fashin yayi ba domin yasan cewa
dama inhar zasu yi karo da Yazid to babu shakka
sai ya zame musu matsala,yadda yaga Yazid
yake girbar yaransa tamkar ya hori kansa sai ya
fusata ganin idan har yabar Yazid yaci gaba da
karo da yaransa to babu shakka zai karar dasu
ya zamana sun kasance su kadai a filin gurin
wanda hakan ba karamin asara bace a
gareshi,babban dan fashi wanda ake tsoro da
gudu ace Yarima ya kunyata shi ya kama shi a
matsayin ribatacce.
Koda ya kada gatarinsa sama sai yayi ihu ya nufi
Yazid a yayin da
Yarima Yazid yake ci gaba da ragewa yan fashin
yawa.Cikin shammata wannan katon shugaban
yan fashin ya doki Yazid ta baya,saboda karfin
dukan
daya yiawa Yazid saida Yazid ya tafi da karfi yayi
tafiya mai nisa sannan ya zube kasa dukkanin
makaman hannunshi suka zube kasa.Da kyar
Yazid ya iya dagowa ya dubi shugaban yan
fashin,shi
kuwa shugaban yan fashin sai ya daka tsalle ya
nufo Yazid da niyar ya turmusheshi.
Koda Yazid yaga shugaban yan fashin da irin
wannan manufa sai ya mirgina gefe shugaban
yan fashin ya daki kasa.Saboda tsananin karfinsa
saida kasar gurin ta rabe gida biyu.Harsai da
kafarsa ta shiga cikin kasa.Da kyar ya cireta ya
dubi Yazid da fushi.Koda
Sukayi kallon kallo cikin tsananin fusata sai Yazid
ya karkade rigarsa ta kuma tofar da yawu,acikin
yawun daya tofar ya lura da jini,nan take
hankalinshi ya duguzuma cikin tsananin bacin rai
ya maida
kallonsa ga shugaban yan fashin shi kuwa
shugaban yan fashin sai ya kece da
mahaukaciyar dariya saida yayi dariyar ta isheshi
sannan ya dubi Yarima Yazid
yace,Yaro man kaza da kana tunanin akwai wata
rana da nasara zata gabato maka yayin da kayi
gaba da gaba da Ardadu shin kana tunanin akwai
ranar da zaka tsira a lokacin da aka bakantawa
Ardadu mai karfin doki saba'in,to ka kuka da
kanka,domin kayi gamo da katar yau hallaka zata
cudanya da rayuwarka zan tsawaitar da
numfashinka.Koda Ardadu shugaban yanfashin
yazo nan a batunsa.
+Abbas Abdulkadir Hada Hada+
sai Yarima Yazid yayi murmushi ya daga
hannuwansa sama ya hada su guri guda ya
murda suka bada wani sauti kararas,ya girgiza
jikinsa
domin ya samu kwarin jikinsa koda gama wannan
murde murden sai ya dubi Ardadu yace,wannan
duka
cika bakine yakai wannan kazantaccen mushriki
azzalumi inason kayi sani cewa kai kadai kayi
kadan dana gwabza yaki dakai abinda nake da
muradi dakai shine kayi umarni da ragowar
mutanen
ayarinka domin kuyi dandazo zuwa gareni kuyi
yaki dani mafi tsananin kwarewarku da hakane
nake da
kwarin gwiwar tunkararku amma sam kai kayi
kadan nayi yaki dakai.
Koda Ardadu yaji wannan mummunan lafazi daga
bakin Yarima Yazid sai ya fusata cikin tsananin
fushi yayi kansa cikin bakin kuduri.
Koda ya iso gareshi sai ya daga gatarinsa yakai
masa wawan sara babu ba gani sara Ardadu yake
kaiwa Yazid amma yazid yana kauwacewa saran
harsaida Ardadu yakai sara kusan sau tamanin
da uku,a sannan ne yayi nasarar gogar Yarima
Yazid da gatarinsa a dokin bayansa amma kuma
kafin ya
kara kai wani yunkuri tuni Yazid ya fusata yayi
tsalle ya saka hannunsa ya kirbawa Ardadu
naushi a fuska.Idanuwan Ardadu suka rufe cikin
tsananin jin radadin zafi,ai kuwa sai ya kama
dube dube dan
kada Yarima ya shammaceshi ya kara gabza
masa wani bahagon naushi,Kafin idanuwansa su
bude
Yazid ya kara daka tsalle sama ya dokeshi a
kirji,duk irin girman da Ardadu yake dashi sai
gashi saboda
tsabar karfin dukan da Yazid yayi masa ya tashi
sama tamkar wanda aka dauke shi da kugiya bai
zame ko ina ba sai cikin dakarunsa.Da sauri ya
taso cikin tsananin bacin rai ya dawo ga Yazid
kafin ya
karaso Yazid ya nufoshi yana isa gareshi ya
kaucewa wani wawan naushi da Addaru ya kawo
masa
naushin yabi iska kafin Ardadu yayi mamakin
rashin dalilin rashin sa'ar dayai sai Yazid ya
kwashe kafafunsa yayi sama ya fado kasa yana
fadowa Yazid ya take masa kirji.Nan idanuwan
Ardadu suka
zazzaro sukyi kuru kuru ya kasa daga kafar Yazid
sai uban haki da nemo dauki yake,koda yaga
cewar
idan ya jima a haka zai iya asarar rayuwarsa sai
ya daka wata tsawa ga dakarunsa nan take suka
nufo
Yazid da niyar su kamashi su cinyeshi
danye.Kafin su karasa sai Yarima ya daga
Ardadu yayi wulli
dashi izuwa garesu.
Koda sukaga shugabansu a sama yana reto sai
suka yi yunkurin su tareshi amma koda yazo
garesu sai suka kasa tareshi wanda suka nufeshi
dan kai masa dauki duk saida suka karkaye
saboda nauyinsa da kuma karfin dukan da Yazid
yayi masa.Koda ganin haka sai suka ruga ga
Yarima cikin fushi da dacin rai suna ihu suna
kururuwa dauke da makamansu a hannunsa.Kafin
kace meyewa wannan tuni gurin ya kara ya
mutsewa cikin tsananin kwarewa da iya salon
yaki Yazid ya dinga gididdibasu yana sokarsu tare
da naushi da bugu da kafa da hannu.Aikuwa
sunyi matukar tsananin danasanin tunkarar Yazid
domin a
tunaninsu akwai ayarin aljanun da suke kawo
masa taimako saboda duka daya yake yiwa
mutum sai
kaga ya baje kasa ko shurawa bayayi.Cikin
Azama kuma tamkar ba dan adam ba.
Lokacin da akayi sa'a biyu a na wannan gumurzu
sai gurin ya rage yawan kazaman yan fashin ya
zamana bai wuce mutum goma ba daga shi sai
ragowar ayarin su tara sai shugabansu da yake
kwance sharkaf.Koda Yarima Yazid ya dakawa
ragowar wadannan ayarin da suke rage a tsakiyar
filin tsawa sai suka razana suka zube kasa ko
shurawa basuyi ba,wannan ihun daya daka shine
ya farkar da shugaban Ayarin koda mikewarsa
saiya dubi Yarima Yazid yaga wayam filin gurin
babu koda mutum daya a cikin ayarinsa.Ganin
wannan mummunar barnar da Yazid yayi masa
sai tsoro da fargaba ya shiga zuciyarsa nan take
ya yanke shawarar yin sulhu da Yarima.Koda
Yarima Ya dako tsalle ya dirga a gabansa sai
yace,to uban dawa meye sauranka?
Ina kuma kokarin naka na iska,idan har ka isa kai
namiji ne inason kayi yaki dani hannuwanka na
masu rike da takubbai biyu,ni kuma zan zauna
batare da makami ko garkuwa ba,na kuma rantse
da girman Allah sai nayi maka KISAN
GILLAH.Koda zuwa nan a cikin batun Yazid sai
Ardadu ya zube kasa cikin risinawa yace,ya
shugabana kayi mini rai ko ba a gwadaba linzami
yafi karfin bakin kaza,na hakura kuma nayi
mubaya'a a gareka zan ta bauta a gareka har
lokacin daka yantar dani.Koda Yarima yaji
wannan batu sai yayi murmushi ya dubi Ardadu
yace bazan taba aminci dakai ba saidai zanyi
maka gargadi gami dayi maka katanga da cikin
wannan kasa,idan har na kara jin waninku ya
kusanto cikin birninmu mai tarin albarka to zai
dandani mutuwa mafi daci,dan haka ka kwashe
kaskantattun dakarunka ka wuce dasu zuwa
matsugunarku.Koda jin wannan batu sai Ardadu
ya kara risina yace,ya shugabana kayi sani
wadannan
ayari nawa tuni azabarka tayi sanadin
wanzuwarsu zuwa kiyama inason ka aminta dani
na zamo bawa wanda zaiyi maka rakiya a cikin
wannan tafiya taka,babu duk abinda zaka bukata
ba tare dana
samo makashi ba,dan haka kayi aminci dani yakai
wannan sadauki mai tarin jumurda.
Dajin wannan sai Yarima Yazid ya daka masa
tsawa yace kayi abinda
na umarceka inason kuma ka sani ruwa da wuta
bazasu taba yin shiri ba,dan haka ka fice daga
wannan yanki gaba daya.Koda gama fadar haka
sai Yarima ya tunkari kofar birnin da zummar ya
fice,koda Ardadu yaga Yarima ya wuce ya barsa
anan tsaye sai yayi sauri yabi Yarima da gudu
yana isa gabansa saiya zube yace,wannan damar
ita kadai zaka bani ta maidani mutumin arziki na
daina sata da fashi Yakai Yarima,in har ka tafi ka
kyale ni zan iya hada kai da wasu rukuni na yan
fashin da suke zaune a cikin wannan yankin na
cigaba da aikata mummunar sana'armu dako a
cikin addininmu ba abune mai kyau ba,ni kuwa
har inna kasance cikin duniya to zan kas
+Abbas Abdulkadir hada hada+
ance cikin dauwamar bakin ciki da radadin yanda
ka tozartani,ka wulakantani,ta yaya zan goge
wannan tabon dakayi min a gaban makiyana
abokana sana'ata na tabbata sai sun gorantamin
domin har a ranar da aka haifeka saida muka
shigo cikin birnin nan mukayi sata amma dan
abin kunya yau gashi ina mai kaskanta a gareka
tabbas idan ban zamo hadiminka kaicona yakai
Yarima da wannan kadai zan tsira daga gorin
dazan fuskanta daga yan uwana dan haka ina
mai neman alfarmarka daka tafi dani.
Koda Ardadu yazo nan a batunsa sai Yarima ya
kada kai yayi gaba ba tare daya kara duban
Ardadu ba.Ardadu koda yaga haka sai ya daga
murya da karfi yace,ina da labarin WASIKAR JINI
sannan inada labarin yanda zaka mallaki
WASIKAR JINI,Inhar kanason kasamu wadannan
labari to tabbas inada amfani a cikin wannan
tafiya taka,domin a karkaf wannan kasa babu
wanda yasan cikakken labarinta faceni.
Koda Yarima Yazid yaji wannan batu sai ya tsaya
cak ya waigo ya dubi Ardadu cikin sanyin
jiki,tabbas inhar yana da labarin WASIKAR JINI
ya zama dole yayi tafiyar nan dashi,domin shi
babu abinda ya sani dangane da WASIKAR JINI
kai hatta
birnin Latus Harus bai san ta inda zaibi ba,koda
yin wannan tunanin sai ya dubi Ardadu yace,In
har
kanason tafiya dani sai ka zamo mai addini irin
nawa sannan sai ka cire cuta da yaudara da
kwace
a cikin zuciyarka in har zaka karbi addinina ka
kuma cire wadannan abubuwa dana lissafa maka
a shirye nake da nayi tafiya dakai.
Koda Ardadu yaji wannan batu sai yayi murmushi
yace,na amince zan karbi addininka anan take
sannan zan daina yaudara da cuta,amma bazan
daina kwace ba domin kuwa
muddin akace na daina kwace ba abinda zamu ci
a wannan tafiyar tamu sai ya gagaremu sannan
zamu shiga cikin Birnin Latus Harus ba tare da
komai ba,hakan kuma na nufin kaskantarmu
saboda ita
wannan kasar babu talaka haka duk bakon daya
shiga kasar da talauci to babu shakka zamu
shiga
muna kaskantattu wanda ko kallo bazamu ishe
su ba,in har ka amince zanyi kwace har na tara
dukiya
mai yawa muci musha mu kuma shiga kasar
Latul Harus da yalwar arziki yanda jama'ar kasar
zasu
daraja mu da kimantamu.
Dajin wannan daga Ardadu sai Yarima ya girgiza
kai yace, ban yarda ba ka yarda da Allah ka
yarda da cewar shine mai yin komai ba waninsa
ba,in har ka aminta mu tafi in kuma baka aminta
ba ba zan tafi dakai ba.
Da Ardadu yaga Yazid da gaske yake inhar bai
aminta ba ba tafiyar za'ayi dashi ba sai ya yarda
ya bari
cewa aransa tundashi kwararre ne wajen kwace
zai iya yin kwace ba tareda sanin Yazid ba dan
haka sai
yace,na amince mu tafi.
Nan take Yazid ya musuluntar dashi suka dauki
hanyar tafiya basu jima da barin gurin ba saiga
dakaru sama da mutum dari uku sun nufo bakin
ganuwar bisa wani daya kubuta yaje ya sanar da
abinda ke faruwa a nan bakin ganuwar.Koda
bayyanarsu gurin sai mamaki ya kamasu ganin
gurin babu wani sadauki mai rai kowa
da kowa yayi warwas a kas ko shurawa basayi
da kyar suka samu wani wanda yake iya daga
kansa.Koda shugaban dakarun ya hango wannan
sai ya isa gareshi yana isa ya dago kansa cikin
fushi yace,yakai wannan DAN TA'ADDA ina dalilin
faruwar haka a gareku alhalin munsan bamu turo
kowa ba
dan ya tareku ta yaya akai haka ta faru a
gareku?
Koda jin wannan tambaya sai wannan danfashi
cikin nishi sama sama da kyar ya motsa baki
yace,ba kowa bane yayi mana wannan illar face
Yarima Yazid kuma a yanzu haka shugabanmu ya
bishi rakiyar inda ya nufa.Koda wannan shugaban
dakarun yaji wannan batu sai ya cika da mamaki
ainun ya mike tsaye kai tsaye yayi umarni da
wasu daga cikin
dakarun dasu kama ragowar dakarun suje su
haka rami a binnesu.Take sai shi kuma ya koma
cikin garin ya nemi waziri ya zaiyane masa duk
abinda ya faru.
Duk wanda yaji wannan batu sai mamaki ya
cikashi nandai suka hadu suka kara yiwa Yarima
fatan Allah ya dawo dashi lafiya ya kuma bashi
sa'ar samun abinda ya tafi nema dan kubuta
daga sharrin
sarki Aiyuba.
*** *** ***
ACAN kuma kasar Latus Harus lokacin da Yarima
Zainur ya isa cikin birnin sai ya wuce kai tsaye
izuwa gidan SARKIN YAKI Haiman yana shiga
cikin gidan sai ya iske Haima tare da matarsa
Lahisa
zaune a fargajiyar gidan suna cin abincin dare
cikin nishadi da hira suna ta kyalkyala
dariya,koda suka
ga Jarumi Zainur ya dawo daga farauta hannunsa
wayam ko zomo babu sai suka mike tsaye
zumbur
cikin firgici da mamaki saboda hakan bata taba
faruwa ba.Zainur bai taba dawowa gida ba cikin
latti
haka bayan magriba kuma bai taba tafiya farauta
ya dawo zakai ba face ya sabo katuwar dabbar
daji a
kafadarsa,sannan kuma fuskarsa babu annuri ko
kadan domin kallo daya mutum zaiyi masa ya
gane
cewa yana cikin matsanancin bakin ciki da
damuwa.
Kai tsaye Zainur ya wuce izuwa cikin dakinsa
kansa a sunkuye ko duban inda su Haiman baiyi
ba bare ya tsaya ya gaishe su kamar yadda ya
saba,kawai sai ji sukayi ya banke kofar dakin
nasa da karfi ta kulle.Cikin alamun tsananin
mamaki Haiman da Lahisa suka dubi junansu
kawai sai Lahisa ta mike tsaye da nufin ta tafi
dakin Zainur din ta tambayeshi abinda ke
damunsa,amma sai Haiman yai wuf ya ruko
hannunta yamai da ita zaune sannan ya dubeta
cikin nutsuwa yace,
Mune gaba dashi ko shine gaba damu?
Ai ko wani ne ya bata masa rai bai kamata ya
huce akanmu ba haka kuma idan wani abune
yake damunsa kamata yayi yasanar
damu ko zamu iya magance masa,ki rabu dashi
kawai idan abin ya isheshi da kansa zaizo yayi
mana
bayani.
Sa'adda Haiman yazo nan a jawabinsa sai Lahisa
tayi ajiyar zuciya cikin alamun damuwa
tace,aini babbar damuwata itace akwai alamun
yunwa a tare dashi domin bakinsa
+Abbas Abdulikadir Hada Hada+
ma a bushe yake kuma da sassafe ya fita ko
kalaci baiyi ba.Koda jin haka sai sarki Yaki
Haiman yayi
murmushi yace ai bari ba shegiya bace idan
haihuwa bata sa anyi biki ba ai mutuwa tasa
ayi,koda gama fadin hakan sai Haiman ya cigaba
da cin abinsa ko alamar wata damuwa babu a
tare dashi yana gama cin abincin sai ya mike
tsaye ya shiga cikin turakarsa yayi kwanciyarsa.
Saida dare ya raba Yarima Zainur na zaune a
cikin dakinsa cikin tsananin bakin ciki da tunani
ba komaine ya jefashi cikin wannan hali ba face
takaicin yadda yarinya
karama ta fishi karfi da jarumtaka alhalin shi
yana ganin yadda yake dakawa manyan mazaje
gumba a
hannu,waishin sarkin yaki ne bai koyar dashi irin
horon daya kamata bane ko kuwa malamin daya
koyar da Gimbiya Lazwara yafi malamin Haiman
iya yaki?
Amsar da Yarima Zainur ya kasa baiwa kansa
kenan a can wani bangaren yaji yana fama da
begen Lazwara domin dduk sa'adda ya rufe
idanuwansa sai ya rinka ganin fuskarta wani
lokacin kuma sai yayi ta tuno da duka abinda ya
faru tsakaninsa da ita.
Lokacin da dare ya raba sosai sai yunwa ta
addabi yarima zainur kuma tunanin gimbiya
lazwara ya ishe shi har shi kansa abin ya bashi
mamaki domin gani yayi in dai kyaune lazwara
take takama dashi gimbiya nauwara ta ninkata
amma ko sau daya bai taba jin zuciyarsa na
tunaninta ba domin ya dauketa a matsayin yar
uwarsa tamkar uwa daya uba daya suke duk
dacewar yasan akwai aure a tsakaninsu.
Babban dalilin dayasa zainur baya son ya rabi
gimbiya nauwara shine saboda harkar sarauta ko
kadan zainur baya son mulki kuma bayason sarki
aiyuba yayi zargin cewa yana da sha'awar
karagar
mulki.Shi kuwa sarki aiyuba yayi matukar mamaki
bisa yadda yaga jarumi zainur yake gudunsu shi
da
yarsa da yadda kuma ya sadaukar da rayuwarsa
a kan farauta da koyan yaki babu yanda sarki
aiyuba
baiyu ba akan ya janyo yarima zainur izuwa
jikinsa amma sai zainur ya zuke yama daina
zuwa fada da duk inda zai hadu da sarki ko
gimbiya nauwara wani iko na Allah kuma ita
gimbiya nauwara tana matukar kaunar zainur
domin jininta da nasa sun hadu amma
kaunace irin ta yan uwantaka.
Lokacin da yunwa ta ishe jarumi zainur yaji ya
kasa barci da sukuni saiya mike tsaye cikin sanda
yaje ya bude kofar dakin nasa a hankali yadda
baza aji motsin saba sannan
ya fice kai tsaye zainur ya wuce izuwa cikin dakin
girki yana shiga sai ya kama bude tukwane domin
ya debi abincin dazaici.
Ba zato ba tsammani sai yaga gaba dayan
tukwanen abincin ya kare cikin alamun karayar
zuciya da matukar damuwa zainur ya juya da
nufin ya fice daga dakin girkin amma sai yayi
kicibus da sarki yaki Haiman tsaye kuma ruke da
kwanon abincin yana yi masa murmushi kawai
sai Haiman yayi masa murmushi kaiwa sai
haiman
ya yafito zainur da hannu ya

1 Comments On WASIKAR JINI 1 to 8
avatar
abdulrasheed-yusuf

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment