Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yarima yazid ya
numfasa yace aini yadda nake tsoron Ardadu
bana tsoron
makiyan namu musamman tun daga lokacin
dakayi mini karin
bayani akansa,kasan sharrin wanda ke tare dakai
yafi na wanda ke nesa dakai saboda shi yasan
sirrinka.Cikin alamun mamaki zainur ya dubi
yazid yace yanzu kana nufin kace dani duk da
cewar ka yankewa ardadu hannunsa guda zai iya
sake yi maka laifi ko kuma yaci amanarka?
Yazid yace kwarai ma kuwa kasan ance ba'a
yabon dan kuturu da yatsa har saiya girma
sannan anan za'a fuskanci cewa abin duniya yafi
komai muhimmanci a cikin
zuciyarsa don haka yana da kyau mu zuba ido
akan Ardadu.
Yanzu dai tunda har yanzu bai dawo ba kawai mu
tashi mu tafi ya iskemu a can masaukina.Gama
fadin hakan keda wuya sai suka mike tsaye
domin su tafi kawai sai suka hango Ardadu daga
can nesa kadan ya durfafo su dauke da
akushin abinci kuma fuskarsa cike da annuri.Koda
ganin haka sai yarima zainur ya bude baki ba
tare da ya kallo yazid bayace jikina ya bani cewar
akwai wani mugun abu wanda wannan yaron
naka ke
shirin kullawa koma ya shirya shi domin bai
kamata muga annuri akan fuskarsa ba alhalin ya
bata mana rai bisa dadewar da yayi bai dawo ba.
Sai mun fara samun ishash shen comment kafin
mu kara yawan rubutu.
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Biyar (5)
Part B
.
bai kamata muga annuri akan fuskarsa ba alhalin
ya bata mana rai bisa dadewar da yayi bai dawo
ba.
Yarima Yazid yace nima dai naji hakan a jikina
domin masu iya magana sunce ruwa baya tsamin
banza.
Lokacin da Ardadu ya iso gabansu yarima yazid
saiya ajiye akushin a gabansu yana mai sunkui
da kansa kas yace,ya shugabana ka yafeni bisa
dadewar danayi ban dawo ba hakan ta faru ne
sakamakon karancin irin abincin da kuka
umarceni da siyowa a cikin wannan kasuwa.Koda
jin haka sai yarima yazid yayi murmushi
maimakon ya nuna fishinsa yace aini kaina nasan
cewa hakan zata iya faru,yanzu dai sai mu zauna
mu hanzarta cin wannan abinci kafin
lokacin rufe kasuwa yayi domin rana na daf da
faduwa.
Ba tare da bata lokaci ba kuwa suka zauna
sukaci wannan abinci su ukun,koda suka kare
suka
sha ruwa sai suka mike suka kama hanyar fita
daga cikin kasuwa,suna cikin tafiya ne yarima
zainur ya
dubi yarima yazid yace yakai abokina inason
yanzu mu wuce izuwa gidanmu ka kwana
wajena,kuma na gabatar dakai a wajen
mahaifina.Koda jin wannan batu sai yarima yazid
ya dubi yarima zainur cikin mamaki yace haba
yakai abokina me yasa kake son
ka dorawa kanka wahala,ai kawai ka kyale mu
mu karasa kwanakin da zamuyi a kasuwar nan
tundai
muma muna daf da barin garin.Yarima Zainur
yace haba ai abin kunya ne a gareni ace na kasa
baka
masauki na barka a gidan haya cikin kasuwa
alhalin yanzu ji nake kamar mun shafe shekaru
masu yawa muna yin wannan abota,zanyi
matukar bakin ciki idan har baka karbi wannan
tayi nawa ba don haka yanzu zamu wuce ne
izuwa masaukinku domin ku debo kayanku mu
wuce izuwa can gidanmu.
Koda jin wannan batu sai farinciki ya lullube
Ardadu a cikin ransa bisa cewa komai zaizo masa
cikin matukar sauki tunda dama baisan hanyar da
zaibi ba ya sami damar kusantarsa ba,shi kuwa
yarima yazid saiya nuna ko kadan baya son yaje
ya kwana gidansu zainur saida zainur ya matsa
masa.
Haka dai suka karasa masaukinsu yazid,yarima
zainur ya nemo mai
amalanke aka kwaso kayansu gaba daya suka
nufi gidan sarkin yaki haiman.
Da isowarsu gidan sarkin yaki aka bude musu
kofa suka shige ciki nan take zainur ya kirawo
hadiman gidan suka kwashe kayansu yarima
yazid aka tafi dasu izuwa dakinsa
sannan yaja yazid da ardadu suka nufi cikin
babban falo na gidan.
Da shigarsu sai sukayi arba da sarkin yaki
haiman kwance akan doguwar kujera likita na
dinke raunika a jikinsa a gefe daya kuma matarsa
ce a zaune ta hada kai da guiwa tana kuka.Cikin
firgici da dimauce yarima zainur ya ruga inda
haiman ke kwance ya kama hannunsa ya rike a
lokacin da
idanunsa suka ciko da kwallah yace yakai Abbana
wanene yayi maka wannan danyen aiki,ka gaya
mini ko waye naje na yakeshi.Koda jin wannan
batu sai Haiman ya mike da kyar cikin matukar
karfin hali ya dubi yarima yazid da ardadu sannan
ya dafa kafadar yarima zainur yace haba yakai
dana menene sabon labari don ka gannin a cikin
wannan hali,wadansu dakarun sumame ne suka
kawo min hari harna fafata
™Abbas Abdulkadir hada hada™
kazamin yaki dasu da kyar na tsira da rayuwata
saboda karfinsu da kuma yawansu,amma basu
sami
damar kashe ni ba.
Koda jin wannan batu sai hawaye
ya zubowa yarima zainur wani irin bakin ciki ya
turnuke shi ya rungume haiman a kirjinsa yace
yakai abbana gwara ace tsautsayin akaina ya
faru.Lallai koma dadewa saina dauki fansa akan
wannan
mutane.
Dajin haka sai haiman ya janye jikinsa daga cikin
na zainur ya dubi yarima yazid da kyau sannan
ya dubi Ardadu yace ina ka samo wadannan
manyan baki haka?
Koda jin wannan tambaya sai yarima zainur ya
kwashe labarin yadda ya hadu da yarima yazid
ya zainyanewa haiman ba tare daya boye masa
komai ba.
Koda jin wannan labari sai haiman
ya dubi yazid cikin farin ciki yace tabbas muna da
babban bako yau a gidannan,
Ummul Zainur ai sai kije a fara shiryawa bakinmu
abincin dare,kai kuma zainur saika kai abokin
naka dakinka domin su huta.
Ba tare da wata gardama ba kuwa sai matar
haiman ta mike tsaye cikin murna ganin yadda
haiman din ya sami karfin jikinsa harya iya
mikewa zaune yake magana,ta tafi izuwa dakin
girki domin ta fara shirya abincin dare suma
hadiman gidan kowannensu ya shiga aiki na
musamman domin karrama wannan baki.
Bayan yarima zainur yakai yazid da ardadu
dakinsa sun shirya kayayyakinsu saiya barsu a
dakin ya koma can wajen haiman
domin ya kara ganin yanayin jikinsa.Yana zuwa
sai ya iske haiman ya sallami likita ya tafi kuma
yana zaune yana shan wani ruwan magani a cikin
kofi.Da
shigowar zainur sai haiman ya dubeshi cikin
alamun tsananin damuwa ya yafitoshi da
hannu,cikin sauri da kaduwa zainur ya taho
gareshi ya zauna daf dashi.Haiman ya dubeshi
yace shin kasan sarauniya Lazwara?
Koda jin wannan tambaya sai zuciyar yarima
zainur ta buga da karfi ya sunkuyar da kansa kas
yayi shiru kamar bazai ce komai ba amma daya
tuna cewa bai taba yiwa haiman karya ba saiya
dago
kai ya dubeshi yace nasanta,haiman yayi ajiya
zuciya
yace itace ta ceci rayuwata daga hannun dakarun
sumamen da suka kawo mini hari,kuma tace na
gaya maka cewa kada ka dogara da abokinaka
wato wannan bako da kazo mini dashi domin
bazai iya
taimakonka ba bisa abinda kasa a gabanka,lallai
ka koma gareta kamar yadda kukayi alkawari
domin ta karasa taimakon da tayi niya a gareka.
Bana son komai dangane da abin dake tsakaninku
ko abinda kake shirinyi ba amma dai kada kayi
gaggawa a cikin dukkan sha'aninka ka tsaya kayi
tunani mai kyau domin ka yankewa kanka
hukuncin dazai amfaneka.
Lokacin da sarkin yaki haiman yazo nan a cikin
zancensa sai kan yarima zainur ya kara daurewa
ya rasa ma abinda zaiyi.
Daga can sai yayi ajiyar zuciyar ya dubi haiman
yace yakai abbana
kasha gaya mini cewa abinda babba ya hango
yaro ko ya hau tsauni bazai hangoshi ba,yanzu a
matsayinka na wanda ke gaba da ni wace
shawara zaka iya bani akan wannan al'amari?
Sa'adda haiman yaji wannan tambaya sai shima
ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan ya
dubi zainur cikin nutsuwa yace yakai dana kayi
sani cewa wannan
al'amari naka babbane kuma baya bukatar
gaggawar yanke hukunci,ka sani cewa ina hada
idanu da
wannan abokin naka naji jikina ya bani cewa
mutum ne mai daraja sosai wanda zai iya yin
abin al'ajabin da ba'a taba zato ba.Na sani cewa
itama sarauniya Lazwara tana da matukar amfani
a garemu baki daya,kuma tana da abubuwan
al'ajabi amma idan zaka iya auna wadanann
mutane biyu a sikeli kaga wanda yafi nauyi a
cikinsu saika sallama komai a
gareshi,ko kuma kaje ka kwanta da wannan
matsala a rana wanda duk kaga yazo maka a
cikin mafarkinka a tsakanin yazid da sarauniya
lazwara shi zaka mika wuyanka.Koda jin wannan
batu sai yarima zainur yayi ajiyar zuciya yace
nagode ya abbana lallai zanyi aiki da wannan
shawara taka.Har
zainur ya mike tsaye zai koma can dakinsa wajen
su yarima yazid sai haiman ya ruko hannunsa ya
zaunar dashi suka fuskanci juna yace dashi,kayi
hankali da wannan bawa na yarima yazid domin
akwai alamun butulci a cikin idanunsa gami
dason abin duniya zai iya cin amanarku a ko
yaushe don haka kusa ido akansa.Cikin alamun
matukar mamaki zainur ya dubi haiman yace
yakai abbana yaya akayi kasan wannan al'amari?
Kasani cewa hatta yazid dani
babu wanda ya yarda da wanann mutumin kuma
ada can baya tsohon danfashi ne.
Yarima Yazid shine yaci shi da yaki har yasa shi
ya karbi addininsa
amma duk da haka saida ya aikata laifin sama
shi kuma ya yanke masa hannunsa guda a
matsayin
hukuncin satar.Koda jin wannan batu sai haiman
yayi dan gutun murmushi yace ai kuwa shi hali
zanen dutse ne idan wannan bawa yayi wasa sai
yarima yazid ya sake yanke masa daya hannun
nasa
ya zama cikakken musaki.Nan dai yarima zainur
ya mike tsaye ya koma can dakinsa yana zuwa
ya iske yarima yazid da ardadu suna gabatar da
sallar magriba don haka saiya koma gefe daya ya
zuba
musu idanu yana kallon yadda suka gabatar da
ibadar tasu.
Koda ya zuba ido yana kallonsu cikin
nutsuwa yana nazarin yadda sukeyin ibadar sai
yaji abin ya birgeshi matuka,ko da yarima yazid
ya dago daga raka'ar farko ya fara ta biyu yana
mai karanta suratul fatiha da suratul ikhlas sai
yaji tsigar jikinsa ra tashi gaba daya,yanayin
kalmomin na Al qur'ani sai suka saita tunaninsa
saboda hikimar da yaji a cikinsu da kuma
girmansu,take yaji a ransa cewa lallai akwai
gaskiya da daukaka a cikin wannan addini.
Lokacin da yarima yazid da ardadu suka idar da
sallah suka jiyo sukaga zainur a zaune ya kura
musu idanu kawai yana al'ajabi sai yarima yazid
yayi murmushi a gareshi yace,yaya naga ka kura
mana
idanu ne tamkar baka taba ganinmu ba?
Koda jin wannan tambaya sai yarima zainur yayi
murmushi yace ai ba ku nake kallo ba
™Abbas Abdulkadir hada hada™
ibadar da kukeyi ce ta dauke mini hankalina na
rantse da darajar iyayena da kakannina ban taba
jin
kalmomin dasu ka ratsa raina ba da zuciyata ba
sama da wadanda naji ka ambata a cikin wannan
ibada taka.
Akwai hikima da daraja a cikinsu.Koda jin wannan
batu sai farin ciki ya lullube Yarima Yazid domin
ya fahimci cewa zainur na daf da gane
gaskiya tun kafin ma suyi gagarumar tafiyar dake
gabansu,kawai sai yazid ya dafa kafadar zainur
yace,ya kai abokina ai abinda kaji ma kadanne
daga
cikin kalmomi masu girma na ubangijin
musulunci,da sannu zaka gasgata wannan addini
nawa kuma ka gamsu cewa babu wani ubangiji
daya cancanci a bauta masa face ubangijin
musulunci.Koda yarima yazid yazo nan a
zancensa sai yaga wani hadimin gidan ya shigo
dakin dauke da abinci bisa faranti,take ya ajje ya
fita.
Fitarsa keda wuya sai Yarima Zainur ya dubi su
Yazid yace ai sai
kuzo kuci abinci.Koda jin haka sai Yazid ya dubi
zainur cikin mamaki yace haba yaka abokina shin
ka
manta ne cewar da yammacin nan muka ci abinci
a kasuwa saboda Ardadu bai kawo abincin da
wuri ba.
Zainur yayi murmushi yace ai na kawai ka cire
hannayenka muci abinci duk da haka nasan
baza'a
rasa yunwa ba a jikin ka.
Yazid ya sake yin murmushi ga yarima zainur
yace aini ban taba cin abinci ba sama da loma
uku tun daga kuruciyata kawo izuwa girmana
saboda a tsarin addini na anason mutum ya raba
cikinsa gida uku.Har Yarima Zainur ya bude baki
da nufin ya tambaya yazid
abinda yake nufi da raba cikinsa gida uku sai yaji
wani hadimin gidan yazo bakin kofar dakin yace
ga manzo daga gidan sarki a gareka.
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama
yarima zainur domin shidai a saninsa ba'a taba
aiko kiransa ba daga gidan sarki,don haka sai
yayi zaton kodai wajen
sarkin yaki haiman manzon yazo.Cikin sauri
zainur ya fito daga cikin dakin ya riski manzon ya
dubeshi
yace waye ya aiko ka kuma wajen aka baka
sako?
Manzon ya risina cikin girmamawa yace ya
shugabana mai girma galadima ce ta aikoni
gareka tace lallai tanason ganinka yanzu.
Koda jin haka sai zuciyar zainur ta buga da karfi
ya dubi manzon cikin
kaduwa yace ina fatan dai babu wani abu mara
dadi daya faru a gidan sarki?
Manzo yace mudai babu wani abu da muka gani
ko muka ji ya faru komai na tafiya kamar yadda
aka saba.Koda jin haka sai yarima zainur yayi
ajiyar zuciya yace shike nan bari naje na fito mu
tafi.Take zaimur ya koma cikin dakinsa da sauri
ya kama shirin fita.
Koda ganin haka sai yazid ya dubeshi yace yakai
abokina shin zan iya yi maka rakiya?
Har zainur yayi shiru kamar bazai amince da
rakiyar tasa ba sai kuma ya dubeshi yace babu
matsala ai tafiya mutum biyu tafi daya zo mu
tafi.Cikin murna yarima yazid ya mike da sauri ya
kimtsa suka fita batare da sunce da Ardadu uffan
ba
shima kuma da yake dama akwai mugun nufi a
ransa sai yayi shiru baice dasu kala ba.
Suna fita ya mike tsaye ya leke waje ta tagar
dakin kawai sai ya
hango yarima zainur ya tara gaba dayan hadiman
gidan yana gaya musu wani abu,inda matsalar
take
shine baya iya jiyo abinda yake fada musu.
Take Ardadu ya raya a ransa cewa an kara
matakan tsaro ne a gidan.Nan fa hankalin Ardadu
ya dugunzuma ainun saboda yasan cewa wannan
itace babbar damar da yake da ita wacce zai iya
sato wannan taswira daga jikin sarkin yaki
haiman tunda gashi a cikin gidansa gashi kuma
babu zainur da yazid a kusa,kuma shi kansa
sarkin yaki a kwance yake cikin jinya bashi da
wani karfin dazai iya kare kansa,don haka zai iya
karbar taswirar da karfin tsiya dama tun da suka
zo gidan yayi nazarin gaba
dayan dakarun tsaron yaga gaba dayansu basufi
su goma sha daya ba,su kuwa hadiman basufi su
bakwai ba,don haka ya tabbatar da cewar a cikin
abinda bazai wuce dakika dari biyu ba duk zai iya
gamawa dasu,koda yasuyi masa rubdugi a
matsayinsa na gwarzon mayakin daya saba
tarwatsa ayarin guda ma a daji.
Inda matsalar take shine idan har aka samu
kuskure ya zamana cewa bai sami nasarar dauko
wannan taswira ba tofa shikenan yayi biyu babu
ma'ana bashi babu samun cikon wadancan
makudan kudade wadanda Uraidu yayi masa
alkawari kuma sam bashi da ikon cigaba da zama
da yarima yazid bare ya sami dukiyar da yake
sa ran samu nan gaba a cikin tafarkin addinin
musulunci.
Abinda Ardadu yake kwadayi a cikin addinin
musulunci shine yarima yazid ya gaya masa
cewa akwai lokacin da za'a tafi Jihadi a yaki
manyan kafiran sarakunan nahiyar a sauke su
daga kan karagarsu ta mulki da karfin tsiya.Dajin
wannan albishir sai Ardadu ya aiyana a ransa
cewa zaiyi amfani da wannan dama wajen sace
dukiyoyin sarakunan da aka kashe yana zuwa
yana boyeta a
sirrance ba tare da an sani ba.
Kaico!wanda duk zuciyarsa ta mutu akan son
abin wani tofa mayuwaci
ne ya gane gaskiya saboda imanisa ya raunana
akan yarda da kaddara.
Haka dai Ardadu ya cigaba da sake saken zuci
yana tsaye a bakin tagar dakin yarima zainur har
zainur da yazid suka hau dawakai sukabi manzon
gidan sarki suka fice daga gida,suna fita sai yaga
gaba dayan dakarun gidan sun taru a kofar shiga
turakar sarkin yaki sun kama aikinsu na tsaro.
Koda ganin haka sai ya gane cewa lallai har
yanzu yarima yazid bai gama yarda dashi ba shi
yasa aka gayawa dakarun gidan su kara
tsaro.Kawai sai Ardadu ya bushe da dariyar
mugunta lokaci guda
kuma saiya turbune fuskarsa yace idan har na
bari wannan dama ta wuceni na zama cikakken
wawa.
Koda gama fadin hakan sai Ardadu ya zare
takobinsa ya fice daga cikin dakin Yarima Zainur
ya nufi kofar turakar sarkin yaki gadan-gadan ba
tare da shakkar komai ba,fuskarsa a murtuke
kaida ganinsa kasan cewa babu imani a tare
dashi,kawai so yake takobinsa tasha jini..
.
Toofah Ardadu yaci Amana kuma ya tabe.
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Biyar (5)
Part C
.
BABU Imani a tare dashi kawai so yake takobinsa
tasha jini.
Koda dakarun tsaron suka hango Ardadu ya
nufosu rike da takobi tsirara sai suma suka zare
takubbansu suka ruga izuwa gareshi,ai kuwa
shima saiya rugo izuwa kansu cikin mugun nufi
tuni ma ya gama aiyana yadda zaiyi musu kisan
farat daya tunda basu fi su goma sha daya
ba,saida ya rage saura baifi taku uku ba kacal su
hadu sai sukaji an daka musu tsawa dasu da
Ardadun duk sai suka tsaya cak suka dubi inda
sautin tsawar ke fitowa wanda ya kasance daga
wani bangare dabam na gidan ne ba daga wajen
turakar sarki ba.
Ba wani bane yayi wannan tsawa face sarkin
yaki,a wannan lokaci sarkin yaki haiman na rike
da wata sanda yana dogarata saboda rashin
karfin jikinsa kuma babu wani makani a
jikinsa.Kawai sai sarkin yaji ya dubi Ardadu yace
yakai wannan tsohon kasurgumin
dan fashi,Ardadu bin Aukas kada ka cutar da
kowa a cikin wannan gida nawa,abinda nakeso
dakai shine
ka fada min abinda kake bukata na baka ka tafi
salin alin,idan dukiya kake so ina da ita nau'i
nau'i shin
zinare kake bukata ko lu'u lu'u ko murjani,inada
yakutu,zubar daji da farar tasa.
Koda sarkin yaki yazo nan a zancensa sai Ardadu
ya gyada kai yace bana bukatar ko dinare daya
da abinda ya danganci dukiya.Abinda nake
bukata kawai shine taswirar zuwa dajin hajrul
aswad na sani cewa tana tare dakai idan har ka
hanani wannan taswirar sai na kashe duk wani
mahaluki dake cikin nan har kai da matarka.
Koda jin wannan batu sai idanun sarkin yaki suka
zazzaro ya dubi Ardadu cikin alamun tsananin
tsoro yace yanzu babu wani abu da zaka iya
karba maimakon wannan taswira,na sani cewa
makiyanmu
ne suka biyaka dukiya mai yawa domin kaci
amanarmu ka sace wannan taswira ka kai
musu,to
ka sani cewa a shirye nake yanzu na baka gaba
dayan dukiyar dake cikin gidannan domin ta
zamo
fansa a kan wannan taswira.
Kafin sarkin yaki haiman ya gama rufe bakinsa
tuni Ardadu ya tari numfashinsa yana mai daka
masa tsawa yace baka da abinda zaka iya
bani,ina mai umartarka daka hanzarta dauko
wannan taswirar ka bani ko yanzun nan takobina
tasha jinin kowa.
Koda jin haka sai hawayen takaici ya zubowa
sarkin yaki haiman cikin
alamun tsananin bakin ciki ya zura hannu a cikin
aljihunsa ya dauko taswirar ya mikawa Ardadu
hannunsa na karkarwa.Ardadu ya fisge taswirar
ya dubata sannan ya bushe da dariyar farin
ciki,kawai
saiya ruga inda bargar dawakai suke ya kwanto
doki guda ya haye kuma ya zabureshi da gudu ya
fice
daga cikin gidan yana mai kyalkyale dariyar farin
ciki.
Al'amarin daya dugunzuma hankalin dakarun
gidan kenan suka rugo izuwa gaban sarkin yaki
haiman,shugabansu ya dubi sarkin yaki a cikin
alamun tsananin damuwa yace haba ya
shugabana
saboda me zaka bari wannan tsohon azzalumi ya
tafi da wannan abu mai matukar muhimmanci da
yafi na rayuwarmu nan gaba dayanmu,shin banaji
kace idan
wannan taswira taje hannun azzalumai shike nan
talakawa sun shiga UKUBA.
Koda shugaban dakarun yazo nan a jawabinsa
sai kawai sukaga sarkin yaki ya bushe da
dariya.Al'amarin daya basu mamaki kenan gaba
dayansu.Haiman ya dafa kafadar shugaban
dakarun nasa yace kwantar da hankalin yakai
Ukasha kayi sani cewa shi kuda ko a wajen
kwadayi akan kamashi,tunda naga wannan
tsohon danfashi tare dasu Yarima jiki na ya bani
cewa saiya
ci amanarsu.
Duk da cewa na sami labarin ya karbi addinin
wannan bako yarima yazid,ina ganinsa a cikin
wannan gida nawa na dauki mataki a cikin raina
kuma na kirkiri dabarar daya kamata nayi.koda
haiman yazo nan a cikin zancensa saiya zura
hannunsa a cikin aljihun wandon ya dauko wata
taswirar wacce ta zama iri daya sak da wacce ya
bawa Ardadu ya nunawa su Ukasha yace,wannan
itace taswira ta gaskiya wadda na bawa Ardadu
jabuce bazata kai makiyanmu izuwa hanyar
gaskiya ba,yaku dakaruna daku da dukkan
hadiman
wannan gida nawa yau kusan shekaru ashirin
kenan ina tare daku,gaba dayanku marayu ne
kuma tunda kuruciyarku na deboku a yakokin
dana fita na rikeku
na raine ku tamkar 'ya'ya na bayan mutuwar
iyayenku babu abinda na rage muku dashi a
rayuwa.
Duk da cewa asalinku bayi ne amma duk aikin da
kukeyi mini biyanku nakeyi,na sani irin amincin
dake tsakanina daku dakuma kaunar da muke
yiwa juna,na sani cewa baku da wanda ya fini
a wannan duniya tunda babu wanda ya taso tare
dashi ya jibanci lamarinku face ni,bisa wannan
dalili
ne naki yarda na bari Ardadu ya yakeku domin
zai iya hallaka kuko cutar da lafiyarka tunda
nasan cewa yafi ku karfi da iya yaki,tunda ni bani
da karfin dazan iya tararsa a yanzu,na sani cewa
zaku iya rufe
sirrina kuma har abada ba zakuci amanata ba shi
yasa nake sanar daku dukkan wanann
al'amarin.Ahalin yanzu kasar nan tamu tana cikin
mugun hadari bisa tarkon makiya saboda a yanzu
haka sarki ya kwanta ciwon AJALI,Kuma
makiyansa so suke su karbe KARAGAR MULKInsa
wannan
taswira itace kadai ta hana su samun nasarar
cika burinsu.
Koda sarkin yaki haiman yazo nan a jawabinsa
sai gaba dayan dakarun da hadiman suka
rungume shi kuma suka fashe da kuka suna cewa
ashirye muke mu sallama rayuwarmu domin ceto
rayuwar jama'ar kasar nan,wannan shine abinda
ya faru a gidan sarkin yaki haiman bayan fitarsu
Yarima
zainur da yarima Yazid izuwa gidan sarki.
Al'amarin su yarima Yazid kuwa lokacin dasuka
iso gidan sarki sai wannan manzo ya shiga
bangaren
gin gimbiya nauwara yayi musu iso,ba tare da
bata wani lokaci ba kua sai aka shigar dasu har
can cikin
turakar tata suna shiga suka iske gombiya
nauwara a zaune ta juya bayanta kanta a
sunkuye.Koda taji motsin shigowarsu kuma ta
gane cewa mutum biyu ne suka
™Abbas Abdulkadir Hada Hada™
shigo sai tayi sauri ta goge hawayen idanunta
sannan ta waigo domin taga wanda yarima
zainur yazo dashi.
Koda ta waigo ta hada idanu da yarima yazid sai
duk su biyun ita dashi zuciyoyinsu suka buga da
karfin gaske.
Al'amarin da babu wanda ya taba jin irinsa a
cikinsu,da yake idanun nauwara sunyi jajur
sakamakon kukan da tasha sai yarima
zainur ya dubeta cikin alamun tsananin damuwa
da firgici yace yake yar uwata menene ya faru
gareki naga alamun kuka a idanunki?.
Koda jin wannan tambaya sai zuciyar gimbiya
nauwara ta karaya har hawaye ya subuto mata
ba tare data ankara ba kawai sai ta dubi yarima
zainur tace ahalin yanzu abbana ya kwanta cutar
ajali kuma baya um baya um um saidai akwantar
a tayar bai iya cin komai hatta ruwa saidai a dura
masa a baki wani lokacin ma ana dura masa
zaiyi amansa,kafin yakai ga
wannan hali yabar min wasiyya guda cewar yabar
amanata a hannunka kuma ya gaya mini cewa
kai da sarkin yakine kadai zaku iya tsirar da
rayuwata da kuma karagar mulkina.
Baya ga wannan yace na gaya maka cewa kada
ka bijirewa sabon abokinka dakayi kuma duk
shawarar daya baka kayi aiki da
ita,shin wannan saurayi dake gabana ma'abocin
kwarjini shine sabon abokin naka?
Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa
yarima zainur ya kama hannun yarima yace
tabbas wannan shine sabon abokina yarima yazid
'da ga sarki Arsanal na birnin haural yakai
abokina wannan itace yar uwata
gimbiya nauwara wacce na baka labari.Cikin
alamun girmama nauwara da yazid suka gaisar
dajuna sannan yarima zainur ya dubi gimbiya
nauwara cikin alamun tausayawa yace yake yar
uwata kiyi sani cewa ina bukatar naga sarki a
yanzu saboda nasan
cewa ganin karshe zanyi masa don abu ne
mayuwaci naje na dawo daga tafiyar dake
gabana na riske shi.Koda jin wannan batu sai
hawaye ya zubowa gimbiya nauwara tace kuzo
muje izuwa turakar tasa,nan take gimbiya
nauwara ta yunkura da nufin ta wuce gaba izuwa
turakar sarki amma sai yarima yazid yayi wuf ya
shige gabanta yana mai kama hannun zainur
gami da jansa gaba.Batare daya waigo ya dubi
nauwara ba sai yace kiyi hakuri yake gimbiya kiyi
sani cewa ni a addinina mace bata shiga gaban
namiji a yayin tafiya tunda dai zainur yasan inda
zamuje babu matsala.
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama
nauwara tace a cikin ranta
wannan wane irin addini ne haka mai alkunya da
kawaici.
Nandai suka dugunzuma su ukun suka shiga cikin
turakar sarki aiyuba.
Sarki aiyuba na kwance bisa gadonsa na alfarma
wadansu hadimansa sun kewaye shi anyi jugum
tamkar ana zaman
makoki,gashi dai sarki ba barci yake ba amma
idanunsa a rufe suka kuma a rame,matuka
sannan tunda ya kwanta wannan ciwo bai bude
idanunsa ba inba don ma alamun numfashin akan
kirjinsa ba da kawai zato za'ayi ya mutu.Da
shigowar gimbiya nauwara tare dasu yarima
yazid sai hadiman suka dare suka basu hanya
suka iso har gaban sarki aiyuba,nan take
nauwara ta zubar da hawaye
sannan ta dubi yarima zainur tace,kaga halin da
abbana yake ciki kuma lallai mutuwa zaiyi babu
yadda za'ayi ya tashi daga wannan cuta,saboda
yagaya mini cewa haka tsarin sirrin tsafinsa yake
cewar da zarar yakai adadin shekarun dayakai
yanzu
akan karagar wannan ciwo zai riske shi,kuma ya
gaya min cewa jinyar kwana gomasha hudu zaiyi
kacal ajalinsa ya cika.
Koda jin wannan batu yarima yazid yayi hailala
yace kaico waya gaya miki cewa akwai wanda ya
isa ya kashe bawa inba ubangijinsa ba?
Kada kuyi imani da tsafi ko camfi domin karyane
ba gaskiya ba ina mai tabbatar miki da cewa
ubangijina zai iya tashin kafadun mahaifinki ko a
yanzu take idan yaso.
Koda jin wannan batu sai tsoro ya kama gimbiya
nauwara,yarima zainur da dukkanin hadiman
dake wajen,nauwara ta dubi yarima yazid cikin
alamun fushi tace waye kai har da zaka tankawa
tsafin mahaifina?
Shin kanaso ne yanzunnan ka hallaka?
To ka sani cewa shekara da shekaru tun iyaye da
kakankin ban taba jin wanda ya aibata tsafin
gidan nan ba sai kai.
Koda jin wannan batu sai yarima yazid yayi
murmushi yace tabbas daku da iyayenku da
kakanninku tabbas kun dade a cikin bata
mabaiyani,da izinin ubangijina zan
nuna muku gaskiyar abinda nafada.
Koda gama fadin haka sai yarima yazid ya
tunkari gadon da sarki aiyuba ke kwance.
Faruwar hakan keda wuya sai wata irin iska mai
karfin gaske ta banko cikin dakin,wata katuwar
bakar inuwa doguwa sankaleliya
ta baiyana tana mai tsala wani irin kara mai ban
tsoro wacce ta firgita su yarima zainur suka fadi
kasa suna masu karkarwar jiki amma shi yarima
yazid yana tsaye yana fuskantar inuwar.Koda
inuwar ta taso masa zata afka masa saiya tofa
mata addu'a kawai sai akaji inuwar ta sake
kwala kara mai karfin gaske kuma ta fice da gudu
ta cikin tagar daki.
A sannan ne gagarumar iskar data addabi komai
da kowa a cikin dakin ta dauke dif tamkar bata
taba wanzuwa ba.Cikin tsananin mamaki
nauwara,zainur da hadiman sarki suka mike tsaye
suka kurawa yarima yazid idanu,nan take yazid
ya karaso daf da
sarki aiyuba wanda ke kwance kamar gawa,yasa
hannunsa na dama ya dafa goshinsa yana mai
karanta wata addu'a tare da tofa masa ita a
dukkan sassan jikinsa.Faruwar hakan keda wuya
sai idanun sarki aiyuba suka bude ya mike
zumbur ya kama kumallon bakin jini.
Al'amarin dayayi matukar baiwa su nauwara
mamaki kenan kuma ya firgitasu,saida sarki
aiyuba ya gama aman sai yayi ko kadan babu
kwari a jikinsa don haka sai ya koma ya kwanta a
lokacin daya kurawa yarima yazid idanu yana mai
zubar da hawaye.A sannan ne ya bude bakinsa
da kyar ya dubi yarima yazid yace me yasa kazo
ka
karya alkadarina?
Mai yasa kake son karya tasirin daukakata da
kuma gadon iyayena.?
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Biyar (5)
Part D
.
KAKESON karya tasirin daukakata da kuma gadon
iyayena.
Koda jin wadannan tambayoyi sai

1 Comments On WASIKAR JINI 1 to 8
avatar
abdulrasheed-yusuf

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment