Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba karamin ganganci bane,
sa'adda yarima yazid yaji wannan batu sai yayi
murmushi yace tabbas abinda ka fada gaskiya ne
amma inaso ka sani cewa a halin yanzu Ardadu
yana cin albarkacin wata babbar rigane daya
sanya wacce ita ce take bashi kariya daga
gareni,ba
wata riga bace wacce Ardadu ya sanya ba face
addinin musulunci daya karba,muddin yana yin
abubuwan da Allah ya wajabta masa bani da ikon
kashe ko cutar dashi face ya kauce daga kan
hanyar tafarkin gaskiya abinda nasani kawai
shine indai bashi da rabo a cikin wannan addini
na gaskiya tofa watarana saiya saba dokar Allah
wacce zata bani
damar na kawar dashi don haka shine zai zabawa
kansa abinda zai fishsheshi.
Nan take dai su biyun sukayi shiru basu sake
cewa uffan ba sukaci gaba da kutsawa cikin
kasuwar kuma adaidai wannan lokaci ne ardadu
ya iso daf dasu suka cigaba da tafiya tare su
ukun.
.
Al'amarin Sarkin Yaki Haiman kuwa lokacin daya
baro gidansa bisa doki da nufin ya tunkari fadar
saiyabi wata hanya wacce bama ita ya saba bi
ba,ita dai wannan hanya yankece ta bayan gari
dole ne mutum ya ratsa ta gefen wani daji
sannan ya dawo kan hanyar cikin garin Hanya ce
mai sauri wadda nan da nan zata kai mutum
izuwa gidan sarautar birnin latul harus cikin
kankanin lokaci.
Koda sarkin yaki ya iso tsakiyar dajin dake
wannan hanya saiyaji alamun motsi a cikin
duhuwoyin dake zagaye da tsakiyar hanyar da
yake kai,abinka da tsohon mayaki wanda yasan
shirin abokan gaba kuma yasan duk irin tuggin da
ake amfani dashi wajen harin sumame sai yayi
sauri yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak ya baza
idanunsa da kunnuwansa izuwa cikin duhuwoyin
tsawon yan dakiku bai sake jin motsin komai
ba,kwatsam saiga wata barewa ta fito da gudu
daga cikin ciyayi ta nausa yamma ta kasa tsere
da wata damisa,koda ganin hakan sai sarkin yaki
yayi
murmushi kuma ya saki jikinsa yaci gaba da
tafiya abinsa cikin kwanciyar hankali.
Kash rashin sani yafi dare duhu ashe a can gaba
kadan wasu dakarun sumame ne a kwance cikin
duhuwar bishiyoyi suna
sanye da korayen tufafi wadanda kalarsu ta saje
data ciyawar wajen kuma duk sun rufe fuskokinsu
idanunsu kadai ake gani suna dauke mugayen
makamai boye a jikinsu.
Adadin wadannan dakaru sunkai dubu kuma sun
kware ainun a iya yaki.Saida sarkin yaki haiman
ya karaso tsakiyar wadannan
dakarun sumamen sannan suka mike tsaye a tare
sukayi masa kawayanya nanfa aka fara kallon
kallo a tsakaninsa dasu.A sannan ne shugaban
dakarun wani dogo mai kirar sadaukai ya ratso ta
tsakiyarsu ya iso kusa da sarkin yaki suka
karewa juna kallo
sannan shugaban dakarun sumamen ya tuntsire
da dariya.Lokaci guda kuma ya turbune fuskarsa
ya nuna haiman da dan yatsa ya daka masa
tsawa yace yakai haiman idan kanason ka tsira
da rayuwarka ka bamu abinda muke bukata
yanzu take.
Koda jin wannan batu sai sarkin yaki haiman ya
bushe da dariya sannan ya dubi shugaban
dakarun yace amma dai kai ka cika wawa mara
tunani in banda hankalinka ya gushe ta yaya kake
zaton zaka iya bani tsoro da batun mutuwa,shin
ka mantane cewa nine wanda ya siyar da
rayuwarsa sau babu adadi ya shiga tsakiyar
abokan gaba yana sara da suka,bansan iyakar
adadin rayukan da takobina ta dauka ba,zuciyata
ta dade da kekashewa ga barin tsoron ganin
zubar da jini,ai MAKASHIN MAZA MAZA KAN
KARSHI.
.
idan ku yan fashi ne masu neman abinci ku fadi
ko nawa kuke so zan iya baku amma idan wani
abu kuke nema wanda zakuyi amfani dashi
wajen cuta da kasata ko al'ummata tofa bazaku
samu ba saidai koni koku wani ya zama gawa
anan wurin.
Koda jin wannan batu sai ran shugaban dakarun
ya baci ya dakawa haiman tsawa yace kai
dakata haka ba cacar baki ce ta kawo mu ba ko
bata lokaci abinda muke so ka bamu shine
taswirar
hanyar zuwa inda WASIKAR JINI take wacce sarki
Aiyuba ya baka,bamu wannan taswirar yanzu
yanzu ko kuma mu kashe ka mu dauka daga
jikinka.
Sa'adda shugaban dakarun yazo nan a zancensa
sai sarkin yaki haiman ya kamu da tsananin
mamaki bisa yadda akayi wadannan dakarun
sumame suka san abinda ya faru tsakaninsa da
sarki alhalin a sirrance sukayi komai a cikin
turakarsa kuma gimbiya nauwata ce kadai a
wajen sannan yana da tabbacin cewa babu yadda
za'ayi nauwara ta tonawa mahaifinta asiri tunda
tamkar ta tonawa kanta ne,saboda makiyanta ta
baiwa makamin da zasu iya hallakata dashi ne.
Lokacin da sarkin yaki haiman yazo nan a
tunaninsa sai ya fusata ainun zuciyarsa ta kama
tafarfsa kamar zata kone kawai saiya zare
takobinsa ya dubi shugaban dakarun sumamen
cikin tsananin fushi ya daka masa tsawa yace kai
tsohon makiri karen farautar azzalumai kayi sani
cewa daku da
wanda ya turoku tsakanina daku sai kisa.
Kafin shugaban dakarun ya budi baki yace wani
abu tuni haiman ya dako tsalle sama daga kan
dokinsa ya kaiwa shugaban dakarun mummunan
sara a wuya da nufin ya cire masa kai,cikin bakin
zafin nama shugaban dakarun ya sunkuya ya
kaucewa saran amma duk da haka saida kafin
takobin ya shaftare wani bangare na rawanin
daya rufe fuskarsa dashi.
Take rawanin ya kwance ya fadi gefe amma sai
haiman yaga cewa bakuwar fuska ce wadda bai
taba gani ba a cikin birnin latul harus,al'amarin
daya tabbatar masa da cewa lallai wadannan
dakaru
hayarsu aka dauko.
Nan take sauren dakarun sukayi
caa akan sarkin yaki da nufin suyi masa rubdugu
su sassara shi amma sai ya zame musu alakakai
ya rinka tarwatsasu da karfin tsiya yana kare
dukkanin harinsu kuma ya kawo musu sara da
suka ta sama da kasa gefe da gefe.
Wani irin salon fada haiman ya rinkayi ya zamana
cewa yana katantanwa a sama da kasan dakarun
kuma ya hada da gabza musu naushi da bugu
amma saboda kwarewar dakarun a iya yaki gami
da tsananin nacinsu da taurin zuciya sai gashi
suna shanye duk irin dukan da yake musu duk da
cewa yana hada musu jini da majina kuma yana
saran sassan jikinsu jini na zuba amma basu fasa
kara matsarsana suna kai masu mugayen hare
hare.
Shi kuwa shugaban wadannan mugayen dakaru
sai kawai ya koma gefe daya yaja tunga ya zuba
ido domin yaga iyakar jarumtakar haiman da
iyakar juriyarsa.
Wohoho manyan jarumai sune wadanda suka
saba dayin karo da maza komai yawansu kuma
sune wadanda basusan tsoro ba sannan komai
wuya komai tsanani basa gudu a filin daga saidai
a gudu a barsu ko kuma a ci karfinsu a kashe su
a wajen.
Saida aka shafe sa'a uku cur ana bakin artabu
tsakanin sarkin yaki haiman da wadannan dakaru
ya zamana cewa ya kashe mutum dari uku da
arba'in a cikinsu amma shi baije kasa ba mma fa
anyi masa
manyan raunika gudu uku a jikinsa har jiri ya fara
dibarsa sakamakon jininsa dake zuba amma
saboda
bakin naci irin nasa yaki yaje kasa da zarar
dakarun sun yunkura masa sai kaga shima ya
afka musu yaci gaba da yakarsu cikin gagarumin
karfi tamkar a sannan ne ya fara yaki....
Nima ganin wannan gumurzu yasa na tsaya
kallo...
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Hudu (4)
Part D
.
Tamkar a sannan ne ya fara yakin.Al'amarin daya
fara tsorata ragowar dakarun kenan suka fara ja
da baya musamman da sukaga cewa gawarwakin
yan uwansu fa karuwa sukayi ba raguwa ba.A
hakan dai aka cigaba da wannan yaki har Haiman
ya sake samun nasarar kashe mutum dari biyu
da ashirin da uku ba tare da an sakeyi masa rauni
ko daya ba,al'amarin daya fusata shugaban
dakarun kenan ainun ya dakawa yaran nasa
tsawa yana mai umartarsu dasu ja da baya su
bashi wuri.Nan take
kuwa su duka sukaja da baya shugaban dakarun
ya zare takobinsa sannan ya kama rigar jikinsa
da hannu daya ya yageta koda Haiman yaga
tsananin
girmansa da kuma tarin kwarjininsa gami da
murdewar jikin nasa sai yaji zuciyarsa ta buga da
karfi domin ya tabbatar da cewar a yadda ya
jigata dinnan kuma jini ke zuba a jikinsa bazai iya
hallaka wannan basamuden kato ba,amma kuma
daya tuna
cewa wannan yaki fa da yakeyi yaki ne na ceton
kasarsa da al'ummarsa dama gaba dayan
mutanen duniya daga sharrin azzalumai sai yaji
dukkan tsoro ya kau daga zuciyarsa nan take yayi
wuf shima ya yade rigar jikinsa ya daure raunin
da yafi zubar da
jini a jikinsa don tsaida jini,sannan ya gyara
tsayuwarsa yana mai fuskantar shugaban
dakarun
suka fara kallon kallo,kwatsam sai suka rugo da
gudu izuwa kan juna suka ruguntsume da sabon
azababben yaki.
Wohoho!Masifa ba'a sa mata rana
duk sa'adda karfi ya hadu da karfi tofa bala'i
yazo kenan kuma sai mai rabon ganin badi shine
zaikai
labari.
Lokacin da wadannan zaratan jarumai biyu suka
kacame da masifaffen yaki suka wanzu suna
masu kaiwa junansu sara da suka cikin tsananin
bakin zafin nama da juriya da jarumtaka ta ban
al'ajabi sai suka dimautar da duk dakarun dake
wajen,kuma suka tashi hankalin duk wani abu
mai rai dake cikin dajin domin babu shiri
tsuntsaye suka kama yin kaura suna barin
shekarsu.
kananun dabbobi kuwa suka kama guje guje suna
fadawa cikin ramukansu suna buya,ba komai ne
ya haddasa hakan ba face bishiyoyin dake wajen
ma basu tsira daga sharrin kaifin takubban
jaruman biyu ba domin duk sa'adda dayansu ya
kaiwa dayan sara da zarar ya goce ya sami
bishiya saidai kaga bishiya ta rabe
gida biyu komai girmanta haka ma idan naushi ya
kawo ya sami bishiya komai girman saita jijjigo
daga cikin kasanta ta fadi kasa.
Nanfa suka tayar da kura dajin gaba daya yai
fururu,su kuwa sauran dakarun sumamen da suka
dimauce suka firgita bisa ganin wannan mugun
bakin artabu da akeyi da shugabansu basu san
sa'adda suka rinka cika wandunsu da iska ba
suna neman wajen buya,saida aka shafe sa'a
daya da rabi ana wannan fafatawa dayansu bai
sami nasarar cutar da daya ba,ba shiri
kowannensu yaja da baya sukayi cirko cirko suna
haki da kallon juna kamar zakaru,damar da suka
samu kenan suka dan huta kuma suka shiga
tunanin dabarar da zasuyi domin su sami
nasara.Ashe kowannensu dabara daya ce tazo
masa ta sauya salon fadan,aikuwa sai suka
yunkura suka tasowa junansu cikin mugun nufi
lokaci guda.
Suna haduwa suka kacame da masifaffen yaki
amma wannan karon sai suka hada da kaiwa
juna naushi da bugu da hannu da kafa,faruwar
hakan keda wuya sai yakin
ya sauya yanayi domin a sannan sarkin yaki
Haiman ya gane kuskurensa saboda shugaban
dakarun ya fishi karfin damtse nesa ba kusa
ba,idan Haiman ya
jurewa shugaban dakarun naushi biyar a lokaci
guda sai kaga ya shanye duka amma da zarar shi
kuma yayi masa naushi daya sai shugaban
dakarun ya yarda takobin hannunsa yacigaba da
gabzawa haiman naushi a fuska da ciki har sai
haiman ya yarda takobin nasa kuma ya rinka
faduwa kasa jini na tsartuwa abakinsa.
Saida shugaban dakarun ya yiwa Haiman laga
laga yaga ko kyakkyawan motsi bayayi sannan
yazo kansa ya tsaya ya zura hannunsa cikin
aljihun rigarsa ya fiddo wannan fata mai dauke da
taswirar dajin Hajarul Aswad.
Cikin tsananin farin ciki shugaban dakarun ya
bushe da dariyar farin ciki,kawai sai ya zaro wata
katuwar
wuka daga kugunsa ya daga sama zai kirbawa
Haiman a kirjin,kawai sai yaji an ruke hannunsa
ta
baya wani irin riko mai tsauri da zafin gaske har
yaji kamar hannun nasa zai karye.Ba shiri ya saki
wukar dake hannunsa ya juya da kyar.
Ba wani ya gani ba ruke da hannunsa face
Sarauniya Lazwara koda yaga ashe ma yarinya ce
ta ruke masa hannun nasa saiya
firgita ainun yayi zaton cewa aljana ce ta rukeshi
don haka saiya sume a tsaye nan take ta saki
hannun nasa ya sulale kasa,duk wannan abu
dake faruwa Haiman baya cikin haiyacinsa baima
san wanda ke tsaye akansa ba.Saida sarauniya
Lazwara ta gama
dinke raunikan dake jikin sarkin yaki haiman ta
shafa masa magani sannan ya farfado daga
dogon suman da yayi ya dawo cikin haiyacinsa
sosai,koda ya bude
idanunsa yayi arba da sarauniya Lazwara zaune a
gabansa sai shima ya firgita yadan ja da
baya,koda ta fahimci cewar ya tsorata da ganinta
saitayi murmushi ta dubeshi tace kwantar
dahankalinka yakai sarkin yakin birnin Latul
Harus ashe har zaka
kasa shaidani don mun rabu tsawon shekaru
takwas
kacal,nice fa sarauniya Lazwara.Koda jin wannan
batu sai mamaki ya turnuke haiman ya yunkuro
da
kyar ya gyara zamansa yana mai jingina bayansa
a jikin wata bishiya sannan ya dubi Lazwara yace
godiya a gareki ya shugabata tabbas kin ceci
rayuwata data dukkan al'ummar dake wannan
nahiya gaba daya,caraf sai Lazwara ta tari
numfashinsa tace
basai kayi mini bayanin komai ba domin babu
abinda ban sani ba,ina zaune a can cikin birnina
cikin turakata na ganka a cikin madubin tsafina
kanayin yaki da wadannan abokan gaba,koda
naga
sunci karfinka zasu hallaka ka sai nayi amfani da
karfin sihirin tsafina na baiyana anan na ceci
rayuwarka,yanzu ga abinda yaso ya
kwata a hannunka.Nan take Lazwara ta mikawa
Haiman wannan fata mai dauke da taswirar
hanyar zuwa dajin Hajarul Aswad ya karba
sannan tace ka
sake adana wannan fata da kyau domin wanda
yake farautarta yafi wuta zafi,kuma yafi annoba
masifa,kuma yafi kowane irin ciwo radadi da zugi
zan cigaba da baka kariya da taimako
gwargwadon
iyawata har izuwa ranar da zaka yadda kuka
shirya kai da sarki Aiyuba amma idan ka koma
gida ka
sadu da danka Yarima Zainur ka gaya masa nace
lallai ya saki reshe ya kama ganye,tunda ya hada
kai
da wannan bafatake domin bazai taba kaishi ga
nasara ba saidai hallaka.
Ka gaya masa cewar har yanzu lokaci bai kure ba
yana da sauran dama da zaizo har fadata ya
karbi taimakona bisa ka'idar dana shimfida
masa.
Koda gama fadin hakan sai sarauniya Lazwara ta
bace tamkar bata taba wanzuwa ba a wajen,cikin
karfin hali sarkin yaki haiman ya mike tsaye
yabar wajen yaje inda dokinsa yake yana dingishi
da kyar ya kama dokin ya haye kansa sannan ya
sakar masa linzami ya tunkari hanyar gidan
sarki...
SHIN SARKIN YAKI ZAI IYA TSARE WANNAN
TASWIRA HAR IZUWA LOKACIN DA ZAI DANKATA
A HANNUN YARIMA ZAINUR?
TSAKANIN WAZIRI RIDWAN DA YARIMA ZAINUR
WAYE ZAI ZAMA SARKI BIRNIN LATUL HARUS?
WACE IRIN BAKAR WAHALA YARIMA ZAINUR DA
WAZIRI RIDWAN ZASU SHA A CIKIN DAJIN
HAJARUL ASWAD?
SHIN ZAINUR ZAI CANZA SHAWARA YA KOMA
WAJEN SARAUNIYA LAZWARA?
WANE IRIN TAIMAKO YARIMA YAZID ZAI BAIWA
YARIMA ZAINUR A CIKIN TAFIYARSU TA ZUWA
DAJIN HAJARUL ASWAD?
YAUSHE NE SARKI AIYUBA ZAI MUTU KUMA ME
ZAI FARU BAYAN MUTUWARSA TASA?
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Biyar (5)
Part A
.
WAZIRI Ridwan na zaune cikin kujerar turakarsa
tare da matarsa Gimbiya Ra'isa suna cikin
matukar farinciki tana shayar dashi ruwan barasa
yana ta faman kyalkyala dariyar murna sai ta tari
numfashinsa tace,yakai mijina waishin meye
tabbacinka cewa wadannan dakarun sojan haya
zasu iya hallaka sarkin yaki su karbo maka
wannan taswira ta zuwa Dajin Hajrul Aswad?
Koda jin wannan tambaya sai waziri ridwan yayi
murmushi yace yake Ra'isa nasan iyakar
jarumtakar sarkin yaki haiman
kuma nasan ta wadannan dakarun sojan haya
don haka ko kada bani da shakka akan nasararsu
a kansa.Ina mai tabbatar miki da cewa daga
yanzu a koyaushe zaki iya ganin an kawo min
wannan taswirar.Gama fadin haka keda wuya sai
babban hadimin waziri ridwan yazo bakin kofar
turakar yayi gyaran murya yace ya shugabana ga
bakonka na dazu da safe ya dawo.Koda jin haka
sai waziri Ridwan ya mike tsaye zumbur cikin
dimbin farinciki
ya dubi Ra'isa yace ai dama na gaya miki bari
naje na karbo taswirar ki gani.
Kai tsaye waziri ridwan ya bude kofa ya fice daga
cikin turakar ya isa can babban falo inda yake
ganawa da dukkan bakinsa.Yana shigowa falon
sai zuciyarsa ta buga da karfi ba komai ne ya
haddasa hakan ba face ganin shugaban dakarun
sojan hayar nan a tsaye kansa a sunkuye cikin
alamun rashin nasara kuma babu taswira zuwa
dajin Hajrul Aswad a hannunsa.Koda ganin waziri
Ridwan sai shugaban dakarun ya zube kasa bisa
guiwoyinsa ba tare da ya dago da kansa ba ya
budi baki yace ya shugabana ka yafe min mun
kasa cika wannan aiki.Koda jin wannan batu sai
ran waziri ridwan ya baci zuciyarsa ta kama
tafarfasa kamar zata kone kuma jikinsa ya kama
tsuma kamar
wanda ake sokawa allura,bai san sa'adda yasa
kafarsa ba ya doki kirjin shugaban dakarun.
Duk da girman shugaban dakarun saida ya fadi
kasa.
Cikin tsananin fushi Waziri Ridwan yace ta yaya
kuka kasa samun nasara akan haiman alhalin na
tabbatar da cewa kun fishi karfin damtse da
juriyar yaki?
Yanzu kana nufin kace kenan duk makudan
kudaden dana baku sun zama a banza kenan?
Koda jin wannan tambaya sai shugaban dakarun
ya yunkura da sauri ya mike zaune ya dubi waziri
ridwan yace,ya shugabana hakika na sami nasara
akan sarkin yaki
haiman domin saida nayi masa laga laga na
sumar dashi kuma take na ciro taswirar zuwa
dajin hajarul aswad a jikinsa amma faruwar
hakan keda wuya sai
naji an cafke hannuna ta baya anyi mini wani irin
mugun riko wanda naji kamar hannun zai
ruburbushe.Koda na juya na kalli wanda yayi mini
wannan ruko sainaga ashe wata yarinya ce ma
karama wacce shekarunta ba zasu haura sha
ba.Take na gane cewa aljana ce bansan sa'adda
na sulale kasa sumamme ba.
Koda jin wannan batu sai waziri ridwan ya
kwarara uban ihu cikin tsananin takaici.
Al'amarin da yasa gaba dayan mutanen dake
cikin gidan nasa suka firgice kenan suka fita daga
haiyacinsu.
Waziri Ridwan ya dubi shugaban
dakarun a fusace yace kai shasha ba aljana bace
sarauniya Lazwara ce mai mulkin birnin arnan
daji.Itace daya babbar abokiyar gabata ta biyu
wacce take son taga
bayana kuma a shirye take ta taimakawa su
yarima zainur su rigani mallakar wasikar jini.
Koda jin wannan batu sai shugaban dakarun yace
ya shugaban ka bani dama ta biyu ina mai
tabbar maka da cewa a lokacin abinda bai wuce
kwanaki goma ba lallai zan kawo maka wannan
taswira idan kuma
na kasa zan dawo maka da dukkan kudadenka
daka bamu.Koda jin wannan batu sai waziri
ridwan ya
bushe da dariyar farinciki yace idan kuwa ka
kawo mini wannan taswira a cikin kwanakin daka
fada
zan sake baka kudi ninkin wadanda na baka
kuma nayi maka alkawarin cewar idan na zama
sarkin kasar na
sai farin ciki ya lullubeka.
Shugaban dakarun sojan hayan wanda ake kira da
suna Uraidu Bin Hamsar ya mike tsaye zumbur
yana mai dora tafin hannunsa na dama bisa
kirjinsa yace,na rantse da darajar gemun ubana
zanje nayi gagarumin shiri don cika wannan
aiki naka,kuma ina mai tabbatar maka da cewa
lallai nan da cikar kwana goma zanzo maka da
wannan taswira ta kowanne hali.Koda gama fadin
hakan sai sadauki Uraidu ya mike tsaye ya fice
daga cikin falon shi kuwa waziri ridwan saiya
bishi da kallo yana mai kyakyata dariyar farinciki
tamkar wasikar jini ce ta fado hannunsa.
.
Al'amarin su Yarima Zainur kuwa lokacin da suka
kutsa cikin kasuwa su uku suka gama siyayyar
da zasuyi sai suka shiga wata rumfa suka zauna
domin su huta kuma suci abinci saboda a
wannan lokaci
rana ta take kuma duk su ukun sun kamu da
yunwa.Nan take yarima yazid yasa hannu a cikin
aljihunsa domin dauko kudi ya baiwa Ardadu yaje
ya siyo musu abinci amma sai yarima Zainur yayi
wuf ya ruke hannunsa yace,Haba yaza ayi bako
ya ciyar da dan gari ai nike da hakkin ciyar daku.
Koda gama fadin hakan sai yarima zainur yasa
hannu cikin aljihunsa ya fiddo da kudi ya bawa
Ardadu.Cikin hanzari ardadu ya karbi kudin ya
nausa cikin kasuwa domin siyo irin abincin da
suka umarceshi da
siya.
Saida Ardadu yadan bata lokaci kadan yana yawo
a cikin kasuwar sannan yaga shagon siyar da irin
abincin dasu yarima zainur ke bukata,cikin
hanzari ya shiga shagon ya bayar da kudin aka
bashi.koda ya fito daga cikin shagon da niyar ya
koma can tsakiyar kasuwa inda su yarima yazid
suke sai yaga wadansu samudawan karti su hudu
sun sha gabansa.
Koda Ardadu ya karewa dakarun
kallo sama da kasa yaga cewa sun cika zaratan
dakaru masu tarwatsa maza a filin daga ya
tabbatar da cewar ba zai iya dasu ba sai ya
dubesu yace,me kuke bukata daga gareni?
Koda jin wannan tambaya sai babban cikinsu ya
daka masa tsawa yace Kai Ardadu shin arziki
kake nema ko tsiya?
To indai arziki kake nema kazo muje wajen
shugabanmu ka gana
dashi.Koda jin wannan batu sai Ardadu ya dubi
katon cikin zakuwa yace maza ka kaini wajen
shugaban naku.Nan take dakarun suka wuce
gaba yana biye dasu sukayi wani bangare daban
na
kasuwar har suka isa wani katon gida,kai tsaye
kartin hudu suka shige cikin gidan mai surkuki
Ardadu na biye dasu amma zuciyarsa sai daka
take duk da cewa shi mutum ne wanda ya saba
zama a daji yana tare ayari na fatake yanayi
musu fashi.
Ba komai ne yasa tsoro ya darsu a cikin
zuciyarsa Ardadu ba face ganin samudawan
dakarun dake cikin wannan gida dauke da
miyagun makaman yaki kuma
da ganinsu kasan cewa baki ne ba yan garin
bane,kuma yadda ya shigo cikinsu shi kadai din
nan
idan suka so zasu iya cinyeshi danye ba tare da
wani sami koda tsoka daya ba.
Haka dai aka cigaba da tafiya da Ardadu har aka
iso wani daki dake can karshne gidan sannan aka
bude musu kofa suka shiga,suna shiga yayi arba
da wani murgujejen
katon mutum zaune bisa wata babbar kujera ta
alfarma yana shan giya ga kuma gasasshen rago
a gabansa wadansu mata sunyi shigar banza
guda biyu suna yanko naman suna sa masa a
baki yana
ci yana rungume su yana kyalkyala dariya.Koda
katon yaga an shigo da Ardadu sai ya daga
hannunsa yabada wata inkiya
.Nan take kowa ya fice daga cikin dakin ya
zamana cewa an barsu su biyu kacal a cikin
dakin wato dagashi sai Ardadu.
Kawai sai murgujejen katon mutumin ya dubi
Ardadu cikin murmushi yace lale marhaban da
tsohon dodon fatake na dajin Aryas,
Ardadu bin Kaumar. Sunana
Uraidu bin Hamsar.
Koda Uraidu yazo nan a zancensa sai Ardadu ya
dubeshi cikin kaduwa da mamaki yace yaya akayi
kasan ni?
Uraidu yayi murmushi a karo na biyu yace ai na
dade da saninka domin kuwa sana'armu daya ce
wato fashi a daji daga bayane tun kafin ka hadu
da yarima yazid
nima tawa likkafar tacigaba na hadu da waziri
Ridwan na wannan birnin da muke ciki ya daukeni
akan makudan kudaden da ban taba tara
kamarsu ba a tsawon shekaru goma sha daya
dana keyin
fashi a cikin dazuzzukan dake can nahiyarmu.
Abinda na kasa ganewa akanka yanzu shine
mece ce ribarka da kake bin yarima yazid?
Mutumin da baya iya baka koda kyautar dinare
goma.
Baya iya tsinana maka komai face kyautar abinda
zaka ci da yar suturar da zaka sanya.Akan wane
dalili zaka yarda a rude ka da wani sabon addini
wanda babu komai a
cikinsa face talauci?
Koda Uraidu yazo nan a zancensa saiya mike
tsaye yaje ya dauko wata katuwar jakar fata ya
cirota ta dira a gaban Ardadu ya dubeshi yace
bude wannan jakar kaga abin dake ciki.Cikin
hanzari gama da rawar jiki Ardadu ya bude
jakar,koda yayi arba da abin dake ciki saiya
dimauce idanunsa suka zazzaro kuma gaba
dayan jikinsa ya
kama rawa,ba komai ya gani ba a cikin jakar face
tarin lu'u lu'u,tunda yazo duniya da duk tsawon
shekarun daya shafe yana harkar fashi a daji bai
taba ganin dukiya a cure lokaci guda mai yawan
wanann ba.
Koda Uraidu ya lura da cewa wannan dukiya ta
ruda Ardadu sai farin ciki ya kamashi ya sake
dubansa yace wannan dukiya somin tabi a
gareka,muddin zaka bi umarninmu kayi abinda
muke
so zaka sami dukiyar da har ka mutu ba zakayi
talauci ba,kai bama yayanka ba hatta tattaba
kunnenka sai sun mutu sunbar abin daka
tara.Kasancewar akwai taswirar zuwa dajin
Hajarul Aswad a wajen sarki yaki haiman marikin
yarima zainur abokin maigidanka yarima
yazid.Muna son kasan duk hanyar da zakabi ka
sato mana wannan taswira a cikin kwanakin da
basu wuce tara ba.Indai ka sami wannan nasara
kawai jakar lu'u lu'u irin wannan guda dari da
suke jiranka.
Koda jin wannan albishir sai Ardadu ya dimauce
kuma ya firgice nan take Ardadu ya zube kasa a
gaban Uraidu yace na rantse da darajar iyayena
ko zan rasa rayuwata saina kawo maka wannan
taswira a cikin kwanaki
taran daka umarceni.
Uraidu ya bushe da dariyar murna yace yanzu
saika dauki wannan jakar lu'u lu'u kaje can inda
zaka boye kayanka sannan ka koma
inda su yarima zainur suke ka kaimusu abincin da
suka bukata amma ka sani cewa cin amanata ko
yaudara a bakacin ranka yake.
Koda jin wannan batu sai Ardadu ya risina ga
Uraidu yace har abada bazan yi gangancin cin
amanarka ba domin kuwa ni a rayuwata kudi
suna gaba da komai ko wannan
addini na yarima yazid dana karba na karbeshi ne
bisa sa ran cewa zanyi amfani da shi wajen
samun
abin duniya amma kuma naga alamun cewa
hakina bazai cimma ruwa ba ashe kune silar cika
wannan babban buri na rayuwata ban sani ba.
Ardadu na gama fadin hakan saiya sunkuya ya
dauki wannan jakar luu luu ya sabata a kafadarsa
ya dubi Uraidu yace lallai ko ta yaya zan kawo
maka wannan taswira a cikin kwananki tara
kamar yadda ka
bukata.Koda gama fadin hakan sai Ardadu ya
sake sunkuyawa ya dauki akushin daya siyowa su
yarima zainur abinci ya fice da sauri.
Fitarsa keda wuya saiya tafi izuwa gidan sarkin
kasuwa akayi masa iso
kafin Ardadu ya isa gidan sarki kasuwa saida yayi
ta canja hanyoyi yana badda bami kuma yana ta
waige waige domin ya tabbatar da cewa babu
mai binsa a baya a matsayinsa na tsohon
masanin tuggu.
Abinda Ardadu ya aiyana a ransa shine su Uraidu
zasu iya yaudararsa anan gana su kwace duk
abinda suka bashi,lokacin da Ardadu ya isa gidan
sarkin kasuwa
ya kadaita dashi saiya gaya masa cewa babban
hadimi ne na yarima Yazid kuma babu wanda
hankalinsa ya kwanta dashi daya ajiye musu
hajarsu face shi don haka ne suka kawo masa
wannan haja domin ya ajiye musu sai ranar da
zasu bar gari zasu zo su karba.Koda jin wannan
batu sai sarkin kasuwa yayi murmushi yace yau
shekarata arbain da daya kenan ina kan wannan
matsayi nawa na sarkin kasuwa kuma duk abinda
aka kawo mini ajiya
™Abbas Abdulkadir Hada Hada™
za'a dawo a riskeshi kamar yadda ka bani indai
inayin son zuciya ta da ban kawo iyanzu ba akan
matsayina.
Da izinin ubangijina abin bautata zaka dawo ka
iske ajiyarka lafiya kalau saidai sharadi guda
daya,sharadin kuwa shine duk bayan kwana guda
zaka bani ladan dinare hudu na lada ajiya sannan
kuma ina son ka gaya mini wanda zai iya
wakiltarka yazo ya karbi wannan dukiya idan har
kai baka sami dawowar karbarta ba idan na
sanshi a fuska shikenan idan kuma bansanshi ba
sai ka gaya mini siffofinsa da kamaninsa.
Koda sarkin kasuwa yazo nan a zancensa sai
hankalin Ardadu ya dugunzuma ya rasa bainda ke
masa dadi saboda yasan cewa bashi da wanda
zai iya turowa ya
wakilceshi akan wannnan dukiya kuma idan yace
bashi da wakilin sarkin kasuwa zai iya zarginsa
akan
cewa akwai rashin gaskiya akan wannan
dukiya.Koda Ardadu yaga bashi da wata mafita
sai yasa hannu a cikin aljihun rigarsa ya dauko
wani tsohon hatiminsa wanda ya saba amfani
dashi lokacin da yake kan matsayin shugaban yan
fashi ya mikawa sarkin kasuwa yace duk wanda
yazo gareka da irin wannan hatimi to ka dauki
wannan dukiya ka bashi.
Nan take sarki kasuwa ya karbi hatimin sukayi
sallama da Ardadu ya tafi.
Acan tsakiyar kasuwa kuwa lokacin dasu yarima
yazid suka ga cewa Ardadu ya dade sosai bai
dawo daga siyo abinci da suka aikeshi ba sai
mamaki ya kamasu.
Yarima Zainur ya dubi Yarima Yazid yace anya
kuwa lafiya wannan yaron naka ya dade haka bai
dawo ba?
Ina ganin cewa zaifi kyau mubi bayansa tunda
bamu sani ba ko makiyanmu ne suka kai masa
hari.Koda jin wannan batu sai

1 Comments On WASIKAR JINI 1 to 8
avatar
abdulrasheed-yusuf

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment