Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani sauti danaji yana
fitowa daga cikin dakinku,ni sunana
Yarima Zainur da ga waziri Ridwan,kai kuma
waye?
Koda jin wannan tambaya sai yarima yazid yayi
murmushi yace sunana Yazid kuma na fito ne
daga can nahiyar dake gabashin wannan nahiya
taku,ba wani abu bane yasa nazoyin fatauci
wannan gari naku ba face na sami labarin cewa
kuna da arzikin ma'adanan kasa mai yawa,mu
kuma abubuwan da muke karanci kenan a can
nahiyar tamu.
Koda jin wannan batu sai yarima zainur ya jinjina
kai a lokacin da yayi masa wani irin kallo na
rashin yarda sannan yace,inason mu zauna ni da
kai mu tattauna wadansu maganganu masu
muhimmanci a sirrance,cikin mamaki yarima
yazid ya dubi yarima zainur amma sai yayi shiru
bai nuna amincewarsa ko rashin amincewarsa ba
akan batun
su zauna su tattauna,nan take sarkin kasuwa
yasa aka je aka dauko kujeru guda biyu aka kawo
wa zainur da yazid aka ajiye musu a gefe daya
sannan aka kori mutane kowa ya koma cikin
gidansa ya kullo kofa.
Ardadu kadai aka bari a tsaye a bayan yarima
yazid,kafin su fara tattaunawa sai yarima zainur
ya dubi Ardadu da kyau ya kare masa kallo yai
nazarinsa sannan ya dubi yazid yace,duk dana
lura cewa wannan mutum dake tare dakai
hadiminka ne babba,ban yarda dashi ba don haka
inason ya matsa can gefe daya muyi sirrinmu.
Cikin mamaki Yazid ya dubi zainur sannan ya
dubi Ardadu yayi masa inkiya take Ardadu ya
matsa gaba can nesa da su yana mai bata rai.
Yazid ya dubi zainur cikin nutsuwa yace yakai
yarima kai kuwa menene dalilin dayasa kace baka
yarda da wancen hadimin nawa ba?
Koda jin wannan tambaya sai yarima zainur yayi
murmushi yace ai wannan hadimi naka tsohon
danfashi ne wanda ake kira da suna Ardadu,babu
wanda yasan iyakar adadin rayukan da suka
salwanta a dalilin Ardadu da kuma dinbin dukiyar
da aka rasa,
shi mutumin kirki a fuska ma ana
ganeshi,yanzu gashi kaima da kanka ka datse
masa hannunsa duk da cewar ya zama babban
hadiminka.
Koda zainur yazo nan a jawabinsa sai yarima
yazid ya cika da tsananin mamaki ya kurawa
zainur idanu yace,dakata yarima shin kana yin
tsafi ne?
Indai ba tsafi kakeyi ba babu yadda za'ayi kasan
duk wadannan al'amura da suka faru a bayan
idanunka.
Dajin haka sai yarima zainur ya bushe da dariya
sannan yace bana tsafi amma ina da tsananin
bincike bisa abubuwan da suke faruwa a wannan
nahiyar tamu ciki da wajenta,duk wani babban
takadari inada labarinsa harma taswirarsa an
zana an kawo mini,kaga kenan bai kamata kayi
mamaki ba akan bayanin danayi maka na
shugaban yan fashi Ardadu,abinda nakeso dakai
yanzu shine ka fada mini gaskiyar wanene kai?
Kuma menene ya kawowa wannan birni namu?
Koda jin wannan batu sai yarima yazid ya kawo
gwauron numfashi ya ajiye sannan yace zan fadi
koma iyakar gaskiya a kaina amma kaima kayi
alkawari cewa zaka fada min gaskiya akan duk
lamarinka.
Yarima zainur yace na dauki alkawarin zan fada
maka iyakar gaskiyar badon koma ba sai don
saboda naga alamar cewa kai mutum ne mai
gaskiya maza ka bayyana min gaskiyar
matsayinka a birninku.
Yarima Yazid ya gyara zama yace sunana Yarima
Yazid da ga sarki Arsanal na birnin Haurul ba
komai ne ya kawo ni kasar ku ba face neman
wata Wasikar jini,
ba don komai nake neman wannan wasikar ba sai
domin na nemawa mahaifina da kasata kubuta
daga sharrin sarkinku,akwai dukiya mai yawa ta
sarki aiyuba a garinmu wacce ake juyata bisa
ka'idar za'a bashi riba duk shekara wannan
shekarar yanfashi sun kawo mana harin bazato
sun kwashe gaba dayan dukiyar kuma bamu da
yadda zamuyi mu iya biyanta
bisa wannan dalili ne muka shiga bincike har
muka gano cewar babu wata hanya da zamu iya
kare
kanmu daga barazanar sarkinku face mun rabashi
da WASIKAR JINI wacce itace
+Abbas Abdulkadir Hada Hada+
madogararsa akan karfin sihirinsa da karfin
mulkinsa,idan har bamu rabashi da wannan
wasika ta jini ba lallai zai turo dakarunsa su
shafe birninmu su kuma kame jama'ar duka a
matsayin bayi ko kuma ya jefemu cikin wata
masifar mai tsananin.
Koda Yarima Yazo nan a zancensa sai yarima
zainur ya cika da tsananin mamaki amma saiya
bushe da dariya,al'amarin daya baiwa yarima
yazid mamaki kenan,zainur yace yakai wannan
dan sarki kayi sani cewa kazo da wani babban
al'amari wanda ni kaina a yanzu na kasa fahimtar
abin a
rayuwata sama akan wannan batu na wasikar
jini,bisa binciken da nayi akan kasarku ta haurul
kuna yin wani addini ne wanda ake kira
musulunci kuma kunyi imani da cewa ubangijinku
shine mai iko akan komai da kowa idan har kunyi
imani na gaskiya akan wannan ubangiji naku me
yasa ba zaku rokeshi ba akan ya shiga
tsakaninku da sarkinmu tunda kun yarda cewa zai
iya magance komai.
Yarima Yazid yace tabbas abinda ka fada gaskiya
ne amma ka sani cewa ubangijinmu mai adalci
ne kuma baya zalunci bamu karbi dukiyar
sarkinku ba sai bisa ka'idar cewa zamu bashi
kaso daya jak cikin kaso uku na ribar da aka
samu a shekara.
Ga shekara ta zagayo bamu bashi ba,kaga kenan
mun karya alkawari don haka muna jin kunyar mu
kai karar sarkinku wajen ubangijinmu kuma
tsoransa ya hanamu muke mu sanar dashi
gaskiyar abinda ya faru,koma yu dace yayi mana
afuwa.
Sa'adda Yarima Yazid yazo nan a zancensa sai
yarima zainur yai ajiyar zuciya sannan yace
tabbas addininku akwai adalci a cikinsa tunda har
bakwa son cutar da wani akan gaskiyarsa to
amma ka sani cewa ina bukatar na sake ganin
karfin addinin naku da ubangijinku domin ina
ganin cewa shine kadai zai iya fitar damu gaba
daya daga cikin matsalar da muke ciki,ko kuna
cikin fargabar sarkinmu ni kuma ina cikin fargabar
mahaifina wanda idan harya hau kan karahar
mulkin kasar nan shike nan kasashen duniya ma
gaba daya sun shiga uku dimin zaluncinsa zai
tumbatsa ya kwarara izuwa dukkan nahiyoyin
duniya.
Koda jin wannan batu sai yarima yazid ya jinjina
kai yace aikuwa indai hakane ashe ba karamin
jihadi zanyi ba na tsaya har anan
birnin naku naga na taimaka mun hana
mahaifinka samun damar da yakeso ya
samu,amma inaso kayi
mini bayani ta yaya mahaifinka zai samu wannan
babbar dama?
Nan take Yarima Zainur ya kwashe
labarin duk abinda ya faru tundaga ranar daga
ranar daya fita farauta daji har yaje birnin Arnan
daji ya sadu da sarauniya Lazwara kawo izuwa
zaman da yayi da gimbiya nauwara da duk
bayanin datayi
masa akan WASIKAR JINI.
Koda yarima zainur ya gama baiwa yarima yazid
wannan labari sai yazid ya cika da tsanani
mamaki ya rasa ma abinda zaice masa can sai
yarima yazid ya dubi zainur yace nidai yanzu ba
zan komawa birninmu face da labarin mai dadi
wanda zai kwantar da hankalin mahaifina da
sauran mutane kasarmu don haka yanzu inason
ka
bani shawara bisa abinda zai fisheni.
Koda jin wannan batu sai yarima zainur yayi
shiru yana tunani har izuwa tsawon yan dakiku
daga can kuma saiya dago kai ya dubi Yazid yace
daga yau mun zama abokai na aminci nidakai don
haka inason ka cigaba da sauraro har izuwa
lokacin dazan tafi neman WASIKAR JINI domin
mu tafi tare kuma kamar yadda na gaya maka
dazu inason ka nuna mini isa da ikon ubangijinka
domin na gani ko zan iya dogara dashi na sami
biyan bukata ta,zaka cigaba da zama ne a cikin
wannan birni namu akan
matsayinka na babban bafatake daga wata
nahiya da wannan furuci nakeyi maka sallama sai
mun sake haduwa a karo na biyu,na barka
lafiya,koda gama fadin hakan sai yarima zainur
ya juya da baya ya bar cikin kasuwar,cikin
hanzari Ardadu ya ruga izuwa
wajen yarima yazid ya risina cikin biyayya yace
ya shugabana ina fatan dai yanzu ka samo mana
labarin inda wasikar jini take?
Cikin alamun fushi yarima yazid yadubi Ardadu
yace,waya gaya maka cewar ana samu komai a
saukake sai ansha wuya sannan akan sha
dadi,yazid na gama fadin hakan sai ya juya ya
koma cikin wannan gida,a lokacin ne sarkin
kasuwa ya ruga da gudu ya iskace cikin gidan
kuma ya risina a gareshi cikin matukar biyayya
kamar zai yi masa sujjada yace ya
shugabana kayi hakuri bisa katse maka barcinka
da yarima yazo yayi kuma lallai gobe da sassafe
zansa
magina su gyara wannan matattakalar benen
data rushe.
Koda jin wannan batu sai yarima yazid yayi
murmushi a lokacin da Ardadu ya karaso bayansa
ya dubi sarkin kasuwa yace ai dama ba barci
nakeyi ba sa'adda yarima ya shigo cikin gidannan
kuma yakin da mukayi bisa rashin sani ne amma
ai yanzu mun fahimci junanmu,yana gama fadin
hakan sai ya
taka rusasshiyar matattakalar benen ya haye
sama kuma ya shige cikin dakin barcin nasa
Ardadu na biye dashi.
Da shigarsu cikin dakin sai yazid da Ardadu suka
kwanta domin suyi barci amma sai Yarima Yazid
yaji idanunsa sun kekashe ba komai
ne ya janyo hakan ba face mamaki bisa ganin
yadda ya fafata kazamin yaki da yarima zainur ya
kasa
samun nasara akansa alhalin ba sa'ansa bane a
shekaru ya bashi kusan tazarar shekara biyar
zuwa
shida,abinda ya kara bashi mamaki mashine
labarin gimbiya Lazwara dayaji sarauniyar arnan
daji wacce
ma tafi yarima zainur karfi da iya yaki.To waishin
ma yaya akayi ta sami irin wannan gagarumin
karfi da kuma gagarumin horon.Nan take Yazid
ya aiyana a ransa yace duk ranar da yarima
zainur ya sami
damar zuwa daukar horon yaki a wajen gimbiya
Lazwara lallai tare zasuje domin yaga irin
jarumtakarta kuma yasa ido domin shima ya koyi
irin yanayin yakin nata.
Haka dai Yarima Yazid yacigaba da tunanin gami
da sake sake cikin zuciyarsa har barci ya saceshi
bai sani ba.
Al'amarin sarkin yaki Haiman kuwa lokacin
+Abbas Abdulkadir hada hada+
daya isa gidan sarki sai aka shigar dashi har cikin
kuryar turakar sarki yana shiga ya iske sarki
aiyuba
tare da gimbiya nauwara a zaune a cikin wani irin
yanayi mara kyau domin duk su biyun idanunsu
sunyi jawur alamar cewa sun hade suna
kuka.Koda ganin hakan sai hankalin haiman ya
dugunzuma ainun domin abinda yake tsoron
faruwa ga dukkan alamu shine yake shirin
faruwar.
Haiman ya durkusa kasa bisa guiwarsa guda
yana mai sunkui da kansa kas ya kwashi
gaisuwa.
Sarki Aiyuba ya masa gaisuwar sannan ya
umarceshi daya zauna akan daya daga cikin
kujerun na alfarma.Cikin sanyin jiki haiman ya
mike tsaye yaje kan kujerar ya zauna sannan ya
gaida gimbiya Nauwara ta amsa ba tare data
dubeshi ba a lokacin da wani siririn hawaye guda
daya ya gangaro akan kumatunta.
Sarki aiyuba ya fuskanci sarkin yaki haiman cikin
nutsuwa sannan yace yakai haiman inaso ka sani
cewa a duk fadin kasata kaine mutum na uku
wanda na yarda dashi nayi imani cewar bazaku
taba cutar dani ba,mutum na farko shine 'yata
wato gimbiya nauwara,mutum na biyu shine
danka yarima zainur sai kuma kai na uku kaga
kenan na aminta da danka ainun fite dakai
kanka saboda wata babbar hujja wacce bazan iya
gaya maka ita ba yanzu,amma ita ba yanzu
amma
indai kana raye nan gaba zakaga hujjar da
idanunka.
Ba wani abu bane yasa na kirawo ka nan ba
yanzu har cikin turakata face domin na sanar
dakai cewa kwanakina a duniya sun kusanto
karshe don haka ba lallai bane nan gaba na haura
sama da kwanaki sittin ba araye.
Koda jin wannan batu sai idanun sarki yaki
haiman suka zazzaro kuma hankalinsa ya
dugunzuma ainun cikin alamun tsananin firgici ya
dubi sarki aiyuba a lokacin da
zuciyarsa ke dukan uku uku yace haba ya
shugabana yaya gaka a raye kuma cikin koshin
lafiya zaune daram a gabana amma kana cewa
bazaka haura kwana sittin ba nan gaba shin wani
ciwo ne ya kamaka ko kuwa kashe kanka
zakayi.?
Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa
sarki aiyuba yayi shiru kamar bazaice komai ba
yana mai sunkuyar da kansa kasa daga can kuma
sai ya dago kansa ya dubi haiman yace babban
likitane na gidan sarautar nan yaci amanata ya
zuba mini guba a cikin maganin daya saba
bani,inasha
yanzu haka guba taci karfin jikina kuma nayi
bincike a cikin hallar tsafina na gano cewa a cikin
kwanakin da basu wuce sittin ba wannan ciwo zai
zamo sanadin ajalina.
Koda sarki aiyuba yazo nan a zancensa sai
haiman ya sake cika da tsananin mamaki bakinsa
na rawa ya dubi sarki aiyuba yace
ya shugabana ta yaya babban likita ya aikata
wannan babban laifi yayi babbar cin amana
alhalin shine
likitan kakanka da kuma mahaifinka ne?
Koda jin wannan tambaya sai sarki aiyuba ya
fashe da kuka yace ni kaina nayi matukar mamaki
bisa yadda akayi babban likita yaci amanata
amma danayi bincike
saina gano cewa ba laifin sa bane dan uwana
waziri ridwan ne ya kama iyalansa a sirrance ya
boyesu a inda babu wani daya sani yace dashi
koya zuba mini guba a cikin maganina ko kuma
ya kashe gaba dayan iyalin nasa saboda su
gomasha daya wanda suka hada da matansa
biyu da kuma
'ya'yansa,
nasa an nemo iyalan babban likita an mayar dasu
amma shi babban likitan nasa an kaishi Sijiil
Mausara an kulleshi tunda yafi son rayuwar
iyalansa akan tawa.
Koda jin wannan batu sai hawayen tausayi ya
zubowa sarkin haiman yace ya shugabana ai
gwara a kashe babban likita dadai kasa akaishi
cikin wannan mugun kurkuku wanda in aka
shigeshi ba'a fitowa face an zama gawa,to shi
kuma waziri wane hukunci ka yanke masa bisa
wannan babban laifi daya aikata na kokarin
hallaka?
Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya sake
zubowa sarki aiyuba a karo na biyu yace kanason
na kashe dan uwana guda daya tilo daya rage
mini a duniya ne?
Wanna shine abin kunya kuma abin gori na
karshe wanda zan barwa tarihin gidanmu bazan
yiwa waziri hukuncin komai ba amma inaso a
bayan mutuwa ta na dasa masa bakin cikin dazai
zamo sanadin ajalinsa kuma ya rasa komai da
kowa,bazan taba samu wannan nasara ba face
da taimakonka.
Cikin alamun kaduwa sarkin yaki haiman ya dubi
sarki aiyuba yace ta yaya zan iya taimakonka a
cikin wannan al'amari?
Sarki aiyuba ya mike tsaye daga kan kujerar da
yake zaune ya kama hannun gimbiya nauwara
yaja ya kawota gaba haiman ya dubeshi yace
idan harka tsare lafiyar gimbiya da ranta a
lokacin da ciwo ya kwantar dani,lallai zan cika
burina akan abokan gabata yakai
masoyina,nan da kamar sati biyu ciwon dake
cikina zai tashi ainun
harya kaini ga kwanciya asannan nakeson na tura
yarima zainur izuwa can inda wasikar jini take.
A wannan lokaci ne dan uwana ma waziri ridwan
zai bazama neman wannan wasikar kuma a
sannan ne
zaiyi kokarin sawa a kashe yata nauwara,inason
ka zamo mai tsaron lafiyar yata na musamman
tun daga lokacin da yarima zainur ya tafi neman
wasikar jini har izuwa lokacin da zai dawo cikin
wannan birnin namu,wannan shine alkawarin da
nakeso ka daukar mini kuma shine kadai abinda
zaka iya sakamini dashi bisa duk irin abubuwan
alherin danayi maka a tsawon zamana da kai.
Cikin matukar mamaki sarkin yaki haiman ya dubi
sarki aiyuba yace ta yaya zan fika iya tsaron
lafiyar yarka alhalin duk fadin duniyar nan babu
wanda ya fika karfin sihirin tsafi?
Koda jin wannan tambaya sai sarki
aiyuba ya sake zubar da hawaye a karo na uku
sannan yace ai sirrin wannan sihirin tsafi na
wasikar
jini shine duk ranar da maishi ya kwanta jinya to
ya daina iya cigaba da sarrafa sihirin kenan face
ta warke sumul.
A yanzu zan baka taswirar hanyar da za'abi aje
inda aka adana WASIKAR JINI daga na birnin
zuwa inda wasikar jini take tafiya ce ta kwana
goma sha bakwai,izuwa wani kogon dutse
boyayye...
.
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Uku (3)
Part C
.
Izuwa wani kogon dutse boyayya daka cikin
wadansu manyan tsaunika dake cikin dajin
Hajarul
Aswad,fiye da shekara dari uku baya babu wani
mahaluki daya sake shiga cikin wannan kogon
dutse face ni don haka wanda duk ya sake ya
samun nasarar shiga cikinsa a raye cikin koshin
lafiya har
kuma ya gano a inda wannan kogo yake mai
lakani da Gulsul Bamhari ya shiga cikinsa lallai
aishine zaiga wasikar jini ya karantata kuma shi
zai hau karagar mulkina,
yakai haiman kayi sani cewa tsananin karfin
damtse kona sihirin tsafi bazaisa mutum ya sami
nasarar keta cikin dajin hajarul
aswad lafiya ba face tsananin sa'arsa da kuma
kyan zuciyarsa amma akwai inda karfin damtse
da iya yakin zai iya taimakon mutum,bisa
wannan dalili ne nakeson ka jadddadawa yarima
zainur lallai yaje ya nemi sarauniya lazwara mai
mulkin birnin arnan daji ta kara masa ilmin yaki
kafin ya tafi izuwa dajin hajarul aswad.Koda
gama fadin haka sai sarki
aiyuba yaje ya bude wata kara,ar akwatin zinare
da karfin sihirinsa na tsafi,itadai wannan akwati a
shafe take bata da murfi ko mukulli kuma babu
wata huda ko kofa a jikinta amma sai gashi sarki
aiyuba ya budeta tamkar an tsaga tsakiyar
kabewa.
Nan take ya zabura ya zura hannunsa cikin
akwatin ya dauko wata tsohuwar fatar dabba
jimammiya,koda ya warware fatar saiga taswirar
hanyoyin da za'abi aje dajin hajrul aswad a
jikinta.Nan take sarki aiyuba ya mikawa sarkin
yaki haiman wannan fatar sannan
yace yakai amintaccen sarkin yaki na ka tabbatar
da cewa ka dankawa yarima zainur wannan fata
a sirrance ba tare da wani ya gani ba,amma kada
ka bashi sai a ranar dana kwanta jinyar wannan
cuta,kada ka kuskura ka bari wani yaga wannan
fata a hannunka kafin ka dankawa zainur koda
kuwa matarka ce ka kasance tare da wannan fata
a jikinka dare da rana har izuwa lokacin da zaka
dankawa zainur ita.
Koda sarki aiyuba yazo daidai nan a
zancensa sai sarkin yaki haiman yayi sauri ya
soka wannan fata a cikin can kasan aljihun
wandonsa
sannan ya dubi sarkin cikin alamun mamaki yace
ya shugabana naji kace akwai inda karfin damtse
da iya yaki zaiyi amfani a cikin dajin aswad kuma
a sanina da kai sam baka da wani karfin damtse
kuma baka taba rike takobi ba bare ma ace ka
iya yaki to yaya akayi ka kare kanka a cikin daji
hajrul aswad a lokacin da kaje wurin da karfi da
iya yaki yake da amfani,?
koda jin wannan tambaya sai sarki aiyuba yayi
murmushi na karfin hali kuma nan take hawaye
ya zubo masa yace mahafinka shine yayi mini
rakiya izuwa dajin hajrul aswad kuma shine ya
ceci rayuwata a wannan wuri a sannan banfi
shekara goma sha ba a duniya kuma yana kuma
yana kan matsayin sarkin yakin ubana.Tun ina da
shekara shida a duniya mahaifinka ya daukarwa
mahaifina
alkawarin kare lafiyata da rayuwata bisa wannan
dalili ne ya sallama rayuwarsa don kare
tawa.Shin baka taba jin tarihin yadda mahaifinka
ya rasa rayuwarsa bane?
Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa
sarkin yaki haiman yace tabbas uwata ta gaya
mini cewa mahaifina ya mutu a cikin gagarumar
jarumtaka a tsakiyar maridai yana fafata
kazamin yaki amma bata taba gaya mini a inda
ya mutu ba da kuma sanadin daya kaishi wurin.
Koda jin wannan batu sai sarki aiyuba da gimbiya
nauwara suka kamu da tsananin tausayin sarkin
yaki haiman suka kama zubar masa da hawaye.
Sarki aiyuba ya rungume haiman a kirjinsa yace
tabbas nine na baiwa mahaifiyarka labarin duk
abinda ya faru garemu nida mahaifinka cikin dajin
hajrul aswad sakamakon halaccin da mahaifinka
yayi mini na
sallama wata dukiya mai tarin yawa a gareshi
wacce ni kaina bansan iyakar adadinta ba.
Mahaifiyarka ce kadai tasan a inda wannan
dukiya take kuma itace kadai zata iya dibarta sai
kuma kai nan gaba idan har ta dankata a
hannunka.
Koda jin wannan batu sai sarkin yaki haiman ya
cika da tsananin mamaki saboda koda wasa
mahaifiyarsa bata tabayi masa batun wannan
dukiya ba kuma gashi tsufa ya kamata ainun
harma ta makance saboda tsufan kuma ko tafiya
bata iyayi sosai face da taimakon dogara
sanda.Kai magana ma da kyar takeyi.To
waishin mahaifiyar tawa mugunta tayi mini kenan
ta boye mini wannan sirri ko kuwa ta kwashe
dukiyar ne ta karar da ita ban sani ba?
Amsar da haiman ya kasa baiwa kansa
kenan,kamar sarki aiyuba yasan abinda yake
aiyanawa a cikin ransa sai kawai ya dafa
kafadarsa yace dubeshi yace ko yau mahaifiyarka
ta fadi ta mutu sai ka gaji wannan dukiya wacce
na
baiwa mahaifinka saboda sirrin dukiyar nan na
jikin wannan sanda wacce mahaifiyarka ke
dogarawa
yayin mikewa tsaye ko yin tafiya kuma
kasancewa kai da bakinka ka gaya mata cewa ko
a bayan ranta
babu abinda kakeso a tare da ita dare da rana
face wanna sanda ta hannunta saboda kayi imani
cewa
sandarce kadai zata iya debe maka kewarta.
Koda sarkin aiyuba yazo nan a zancensa sai sarki
yaki haiman ya kamu da tsananin mamaki gami
da tsananin farin ciki domin ko a mafarki bai taba
zaton cewa iyayensa sun mallaki wani abu ba mai
daraja a rayuwarsa,shi zatonsa kawai sun rayu
ne cikin
bautar gidan sarautar kawai shima kuma gashi
zai mutu a cikinta a banza.
Sarki aiyuba ya dubi haiman yace yakai sarkin
yaki ka sani cewa muna da makiya da yawa a
wannan nahiya kuma gashi bazan nisan kwana ba
saboda haka kai da yarima zainur ne kadai zaku
iya kare kasar nan daga kowace irin
masifa idan har ridwan ne ya zamo sarki to kai
da zainur ku kare gimbiya nauwara da talakawa
ta
hakane kadai zaku iya tabbatar da adalci a
nahiyar nan,kuma sarki ridwan babu yadda za'ayi
ya iya
cutar daku,kada ka taba tunanin cewa zaka raka
yarima izuwa dajin hajrul aswad kaidai kawai ka
™Abbas Abdulkadir hada hada ™
zauna tare da mahaifiyarka dare da rana har
izuwa lokacin dasu yarima zasu dawo daga
neman WASIKAR JINI.
Lokacin da sarki aiyuba yazo nan a
zancensa sai sarkin yaki haiman ya rude kuma ya
rikice yace ya shugabana ka gaya mini cewa duk
wanda ya karanta wasikar jini ya sami sirrikan
tsafi irin naku kuma ya zamana gagarabadau a
wannan
duniya ma gaba daya to amma gashi kana cewa
koda Ridwan ya zama sarki babu yadda zaiyi
damu nida yarima ta yaya hakan zata kasance?
Koda jin wannan tambaya sai sarki aiyuba yayi
murmushi yace akwai wani babban sirri na biyu
wanda zan sanar dakai shi yanzu,wannan sanda
wacce ke hannun mahaifiyarka tana da irin sirrin
da wasikar jini kedashi amma babu wanda zai iya
sarrafata har ya iya amfani da sihirinta face
wanda ya kasance jinin wannan gidan
sarauta,kaga kenan babu wanda
zai amfani wannnan sanda face yarima zainur
wanda ya kasance tamkar dan cikinka tunda kai
da matarka ne kuka raine shi kum a hannunku ya
girma,sannan akwai kauna da shakuwa mai yawa
a
tsakaninku,tunda dai baku da wani da a duniya
face shin don kun mallaka masa wannan sanda
ina ganin cewa babu wata matsala.Koda sarkin
yaji wannan batu sai ya dan gyara murya gami
dayin tari yace nidai babban burina shine a bayan
mutuwa gimbiya nauwara ta cigaba da rike
matsayinta na galadima a majalisar kasar nan
domin ta hakane kadai zata
zama tamkar itace ke mulkin kasar,shi kuwa dan
uwana Ridwan zai zamo tamakr gunki koda kuwa
shine akan karagar mulki,yanzu zan sanar dakai
wani babban sirri na biyu wanda ko ita kanta
gimbiya bata sani ba kuma bana son ta sami
saidai bayan raina.
SHIN SARKI YAKI HAIMAN ZAI IYA RIKE AMANAR
GIMBIYA NAUWARA?
WANE SIRRI NE SARKI ZAI SANAR DA SARKIN
YAKI HAIMAN WANDA HAR BAYASO GIMBIYA
NAUWARA TA SANI?
SHIN TSAKANIN YARIMA ZAINUR DA
MAHAIFINSA WAYE ZAI SAMU NASARAR DAUKAR
WASIKAR JINI?
WACE IRIN BAKAR WAHALA ZASU SHA KAFIN
ISAR SU DAJIN HAJARUL ASWAD?
WANE IRIN TAIMAKO YARIMA YAZID ZAI BAIWA
YARIMA ZAINUR?
SHIN ZASU KASANCE CIKIN ABOTA NE KO
KUWA?
YAUSHE NE SARKI AIYUBA ZAI MUTU KUMA MAI
ZAI FARU BAYAN MUTUWARSA?
Mu hadu a littafi na hudu(4) domin jin cigaban
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Hudu (4)
Part A
.
KODA Nauwara taji wannan batu saita fashe da
kuka ta dubi sarki Aiyuba tace yanzu dama akwai
wani sirri wanda zaka iya boye minishi?
Sa'adda sarki Aiyuba yaji wannan batu sai
hawaye ya zubo masa sannan ya kamo Nauwara
ya rungumeta a kirjinsa yace ya yata sanin
wannan sirri a gareki yanzu
bashi da wani amfani domin bazai haifar da
komai ba a gareki face damuwa da tunanin mara
tukewa.Sarki Aiyuba na gama fadin hakan saiya
janye jikinsa daga cikin na gimbiya nauwara ya
tafi izuwa ga sarkin yaki haiman yayi masa rada
a kunne sannan ya sallama shi ya fice daga cikin
turakar yana mai waigen sarki yana zubar da
hawaye saboda gani yake kamar ba zasu sake
ganin juna ba,fitarsa keda wuya sai sarki aiyuba
ya kama hannun gimbiya nauwara ya jata suka
tafi izuwa kan doguwar kujera suka zauna sannan
ya dubeta idanunsa cike da kwallah yace ya yata
kiyi sani cewa yanzu zaman farin ciki a tsakanina
dake na iya tsawin sati biyu ne kacal don haka
abinda kike son ki gaya mini ki fadeshi a cikin
wadannan kwanaki domin da zarar sati biyu sun
cika ko magana bazan iya ba,duk da cewa ina iya
kallonki dajin duk abinda zaki fada.
Koda jin wannan batu sai gimbiya nauwara ta
fada kan kirjin sarki aiyuba ta fashe da
matsanancin kuka na bakin ciki shi kuma saiya
shiga rarrashinta yana mai bata baki.
.
Lokacin da yarima Zainur ya baro kasuwa ya
dawo gida asuba ta kusayi,a wannan lokaci ya
gaji ainun kuma ga tsananin barci a cikin
idanunsa,kai tsaye ya shige
cikin gidan sarki yaki haiman da nufin ya wuce
izuwa dakinsa ya kwanta.Yana shiga cikin
harabar
gidan sai zuciyarsa ta buga da karfi yaja ya
tsaya cak a waje daya cikin tsananin mamaki,ba
komai ne
ya haddasa hakan ba face ganin mahaifinsa na
jini tsaye a gabansa fuskarsa cike da annuri wato
waziri Ridwan.
Cikin hanzari waziri ridwan ya taho ga yarima
zainur ya rungumeshi yana mai nuna tsananin
farin cikinsa bisa ganinsa amma sai yarima
zainur ya janye jikinsa daga cikin nasa da sauri
ya dubeshi cikin kaduwa da matukar mamaki
yace
yakai abbana meya kawo ka nan gidan a irin
wannan lokaci?
Koda jin wannan tambaya sai waziri ridwan yayi
murmushi yace yanzu don uba yazo ganin dansa
sai ya zamo abin tuhuma?
Yana gama fadin hakan sai idanunsa suka ciko
da kwallah ya dubi zainur cikin nutsuwa yace kai
dana kayi sani cewa nayi matukar nadama bisa
yadda nayi watsi dakai tun tuni ban jakaa jikina
ba har na bari wasu suka rabeka tamkar sun
haifeka.
Koda waziri ridwan yazo nan a zancensa saiya
durkusa kasa bisa guiwoyinsa a lokacin da
hawaye ya zubo masa ya kama hannun zainur ya
rike yace kayi mini aikin gafara yakai dana,kayi
sani cewa dani da mahaifiyarka duk munyi
nadamar nisantarka damu kayi don haka yanzu
nazo ne na daukeka mu tafi gida daga yau zaka
ga gata da kulawa irin wanda babu wani da daya
samesu a garin nan gaba daya face gimbiya
nauwara.
Koda waziri ridwan yazo nan a zancensa sai
yarima zainur ya kyalkyale da dariya,al'amarin
dayai matukar razana waziri ridwan kenan ya
cika da mamaki.
Lokaci guda zainur ya fincike hannayensa daga
cikin na ridwan yaja da baya yana mai murtuke
fuska ya dubi ridwan din a fusace yace meyasa
kai da mahaifiyar tawa baku nuna mini so da
kulawa ba a tsawon shekaru goma sha shida da
suka gabata ba,lallai banza bata kai zomo
kasuwa duk yadda akayi akwai wata bukata da
kuke da ita a wajena shi yasa yanzu kazo kana
nema na.
Nan take hawaye ya zubowa Yarima Zainur yace
tun daga kuruciyata kawo iyanzu ban san wani
abu waishi soyayya ta
iyayen da suka haifi da ba abinda zan iya fada
kawai shine mahaifiyata ta shayar dani,kai kuma
ka ciyar dani ka tufatar dani izuwa tsawon
shekara shida
amma daga sannan sarkin yaki da matarsa ne
suka cigaba da rukeni a matsayin dansu kawo i
yanzu,ya
zakuyi da irin shakuwar dake tsanani na dasu?
Tayaya kuke zaton cewa zaku iyarabani dasu
dare daya?
Koda Yarima zainur yazo nan a zancensa sai
waziri ridwan ya fashe da kuka yace yakai dana
kayi
sani cewa babu yadda za'ayi hannun mutum

1 Comments On WASIKAR JINI 1 to 8
avatar
abdulrasheed-yusuf

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment