Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai baiwa mutum mamaki face
yadda Zainur ke sara ta gaba da baya kuma
sama da kasa kai kace iskace ke sarrafa
hannayensa ba wai shike sarrafa su ba da
kansa,nanfa arnan daji suka shiga uku suka rasa
yadda akayi wannan karamin yaro yake gasa
musu gyada a hannu.Saida aka shafe sa'a biyu
cif ana wannan bakin artabu Zainur yana
ragargazar arnan dajin amma an rasa mutum
daya dazai sami nasarar koda lakutar jikinsa,koda
arnan dajin sukaga irin mummunar barnar da
yarima Zainur yayi musu
domin ya kashe sama da kaso daya cikin kaso
ukunsu kuma ko alamar gajiya babu a tare dashi
sai suka fara cika wandunansu da iska suka juya
da baya da gudu izuwa cikin jeji domin su tserar
da rayuwarsu.Har Yarima Zainur ya fasa binsu
amma daya juya ya dubi inda aka jefa wannan
tsuntsu daya gasa cikin tabo aka tattakeshi sai
ransa ya baci ya falfala da gudu yabi bayan
arnan dajin duk wanda ya
riska saikaga yayi masa falan daya,
wohoho!ai koda arnan dajin suka waigo sukaga
Zainur ya taso su a gaba yana dadayi musu
barna sai suka kara ZAGE DAMTSEn gudun nasu
nanfa aka kasa uban tsere na GUDUN CETON
RAI!
sai gashi SA GUDU YA KORI KI GUDU,haka dai
akaci gaba da yin wannan tseren gudu baji ba
gani,abinda zai baka mamaki kuma ya baka
kunya shine wai yaro ne matashi dan shekaru
goma sha shi kadai ya koro karti majiyan karfi
sama dasu dari uku.Wannan karon dai da kyar
Zainur ya sami nasarar riskar mutum hudu ya
rafke har akayi gudu na tsawon sa'a guda
cur,kwatsam sai Yarima Zainur yaga gaba dayan
arnan dajin daya biyosu da gudu sun tsaya
cak,kuma sun juyo sun fuskance shi
suna haki ba tare da wata alama ta tsoro ba,koda
ganin haka sai shima ya tsaya cak a inda yake
saboda yasan cewa banza bata kai zomo kasuwa
kuma ruwa baya tsamin banza,adaidai wannan
lokaci
ne Zainur ya lura da cewa ai sun shigo cikin
yankin garin arnan dajin domin yana iya hango
gidajensu
tsilli tsilli a cikin dajin kuma yana iya hango
matayensu da 'ya'yansu da yayyansu suna
firfitowa daga cikin gidajen nasu daya bayan daya
tamkar daman sunsan da abinda yake faruwa.Ko
kuma abinda yake shirin faruwa,babu zato babu
tsammani sai Zainur yaji motsin wani abu a
samansa cikin iska
kamar kibiya aka harbo,kafin ya daga kansa sama
yaga ko meye tuni an doki kirjinsa.Saboda karfin
dukan da akai masa shima saida yai sama kamar
majaujawa aka jujjuya sannan aka janye
shi.Bayansa ya maku da wata bishiya sannan ya
fado kasa a galabaice yana aman jini da tari. A
fusace Zainur ya daga kansa da zummar ganin
wanda yayi masa wannan duka,koda yayi arba da
wanda yai masa wannan dukan sai ya kidime
kuma ya kamu da tsananin mamaki.Ba wani bane
face kyakyawar yarinya wacce batafi shekara tara
a duniya ba.Tana
sanye da sutura irin ta wannan arnan dajin,amma
a kanta akwai hular sarauta ta zinare kuma
gadon bayanta ta rataya wata sharbebiyar takobi.
Kawai sai Zainur yaga yarinyar tana kallonsa cikin
murmushi
kuma tana yafito shi da hannun cikin nuna
alamun cewa ya taho suyi yaki.Cikin tsananin
fushi da kunar rai Zainur ya mike tsaye zumbur
yana ware hannunsa biyu masu rike da adduna
kuma jini na zuba daga jikin addunan.Bai jira
wata wata ba ya ruga da gudu izuwa wajen
yarinyar yana mai
kwarara uban ihu gami da daga addunan nashi
sama cikin mugun nufi.Koda ganin haka sai itama
yarinyar ta zaro sharbebiyar takobinta daga cikin
kufenta ta falfalo da gudu ta nufi wajen da
yake.Kodaya rage baifi taku uku su hadu dashi ba
sai ta daka wani
uban tsalle sama takai masa wawan sara a
kai.Cikin zafin nama Zainur yai amfani da dukan
karfinsa da zummar kare saran data kai masa
amma duk da
haka bai samu nasarar kare saran data kai masa
ba saida saran nata ya zabtare wani bari na
bakin
gashin kansa.A haka ta shallake shi ta dirga a
bayanshi bata gama dirga ba tasa kafa ta baya
ta
daki gadon bayansa.Zainur ya tafi ya fadi a kasa
har saida bakinsa ya fashe jini yana zuba,amma
sai yai
zumbur ya tashi yana gyara jikinsa ya kuma
gyara tsayuwarsa.
A wannan lokacin yarinyar ta kuma
kyalkyalewa da dariya shi kuma sai ransa ya
kuma baci saboda ganin gashin kasan iska tana
daukarshi
tana yawo dashi,yakai hannunsa ya shafa lebensa
yaga jini yake zuba.Hakan yasa ya yunkura
zai taso mata,ganin haka yasa ta dakatar dashi
ta kalle shi cikin murmushi da kallon raini tace
masa....
Marbass Dan Aunty
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Daya (1)
Part C
.
Cikin murmushi da kallon raini tace masa,Haba
dan saurayi dakata mana shin fifikon nasara
dana samu akanka bata isheka ba har kasan
cewar nafika karfi na kuma fika iya yaki. Da
inason na kashe ka da tuni nayi fata fata da
namanka.Ka sani cewa ka aikata mummunan laifi
daya kamata na kasheka tunda ka kashe min
dakaru masu tarin yawa a cikin wannan daji
kuma ka karyan dokata ta shigowa cikin wannan
daji ayi farauta.
Yakai Zainur dan waziri Ridwan kayi
sani cewa nice Gimbiya Lazwara sarauniyar
wannan garin da kake ciki kuma na gaji sarauta
ne a wajen mahaifina fiye da shekara dari iyayena
da kakanni na suke zaune anan babu wani sarki
daga birninku daya taba tunanin ya yakemu ko
kuma ya cutar damu.Amma kuma na gani a cikin
madubin tsafina bayan mutuwar sarki Aiyuba na
yanzu wato
mahaifin Gimbiya Nauwara a lokacin yaki zai
barke tsakanin
mu daku, amma kuma na kasa gano barin dazai
samu nasara a tsakaninmu. Babu shakka zamu
zama Abokan Gaba tsakaninmu na tsiya-tsiya
saboda ra'ayinka ya banbanta ainun dana
mahaifinka.Sabo da kai baka damu da duniya ba
kuma baka kaunar
zalunci kuma baka son raini.Dan haka babu
shakka bayan mutuwar sarki Aiyuba mutum daya
daga cikin biyu dole zaiyi sarautar birnin Lailatul
Harus kuma a cikin biyun kodai kai ko kuma
mahaifinka.Idan
kaine ka zama nasan ba zaka yakemu ba amma
kuma idan mahaifinka ya zama babu makawa sai
ya yakemu babu makawa kaine kadai zaka iya
takawa mahaifinka burki,ko ka zamu masa
matsala akan wulakancin da yakeson yayi
mana.Wannan shine babban dalilin da yasa nayi
maka rai a yanzu,yakai
Yarima Zainur ina mai baka sharawa dakaje ka
karawa kanka ilmin yaki da fada domin akwai
babban aiki a gabanka nan gaba wanda ba zaka
iya dashi ba.Da wannan furuci nake yi maka
sallama sai watarana idan da rai da rabon zamu
sake saduwa inba a filin yaki ba.Koda gama fadin
hakan sai sarauniya Lazwara ta juya da nufin ta
koma cikin birninta ta cikin wata babbar
kofa,amma sai Yarima Zainur yayi wuf ya kira
sunanta,ta waigo sannan ya durkusa kasa bisa
guiwoyinsa cikin alamun biyayya kansa na
sunkuye yace,Ya shugabata kafin mu rabu
inason na nemi wata alfarma guda daya a wajenki
inason ki bani dama na sake kawo miki ziyara
domin nayi maki wadansu tambayoyi gami da
neman wata bukata guda daya.Koda jin wannan
batu sai Sarauniya Lazwara ta bushe da dariya
sannan tace,ai dama nasan sai ka nemi alfarma a
wajena a gaskiya a yanzu bazan iya saurarinka
ba saidai kaje
ka cigana da jirana,bayan nayi tunani da nazari
idan naga ya dace na saurareka zakaga manzo
daga
gareni.Tana gama fadin hakan sai ta juya da
sauri ta shige cikin birnin nata.Zainur yaga
gabzawa arnan
dajin masu kirar mutanen farko sunsha gabansa
bisa dole ya hakura ya juya da baya ya nausa
cikin dajin da gudu zuciyarsa cike da sake sake
gami da dinbin al'ajabi ya nufi birnun Latul
Harus.
*** *** ***
Tafiya yake cikin sassarfa yana ratsawa ta
tsakakkaniyar duwatsu da suka yawaita a cikin
daular tasu ta Hindu,kayan jikinsa irin yanayin
suturun mutanen sin,kansa daure yaje da wani
jan kyalle,bayansa rataye da wata kufai na
masu,babu
takobi a jikinsa sai wata rantsantsiyar gwafa
duka rataye a bayansa.Takalminsa na fatar
bauna,sadauki Yazid daya fito daga kasar
Haural,cike da tsananin fushi mai tarin
yawa,baiko waigawa bayansa domin idan ya juya
ya dubi ganuwar birninsu sai yaji tamkar ya
koma da baya ya fasa wannan tafiya tasa dan
haka ya kautar da karkatar kansa ga barin
kallon bayansa yayi gaba abinsa.
Hankalinsa yayi gaba wajen nufar Birnin Latu
Hurus inda sarki Aiyuba ke mulki ba komai yake
jagorantar Yarima Yazid zuwa wannan birnin ba
face zuwa neman WASIKAR JINI,da saurinsa yake
takawa domin sanin cewa samun wannan wasika
shine kadai abinda zai zamo masa
yayewar masifar da take addabar yankinsu da
kuma tsira daga masifar sark Aiyuba duk da
cewar tunkarar kasar yake dan neman WASIKAR
JINI ba saukekken lamari bane.
Babu abinda yake tayar da hankalin Yazid face
cutar data kama mahaifinsa bisa jin irin asarar da
yayi wacce kuma bazata kawo zaman lafiya a
yankinsu ba,dan haka ya kara azama,shidai
wannan yanki na Haurul yana can ne a karshen
yankin kasar Sin inda sarki Aiyuba baki daya yake
mulka.Masifu da bala'i da yake addabar
birnin shi ya haddasa musu fari da
yunwa,kishirwa gami da farmakin arnan daji,da
kuma dodonni da
suke kawo musu bara a kowane karshen shekara.
Tsananin takaicin wannan masifa itace ta sawa
sarki ya kasance cikin tsananin cuta har ya
zamana abinci saidai a bashi ruwa ma
haka,wannan saida kyar yake iya sha,saboda irin
jiki da yake fama dashi.
Akwai arziki a cikin kasar Haural fiye da
kima,wannan dalili ne yasa a koda yaushe
barayi,yan fashi suke yin shigowar bazata cikin
kasuwar garin suyi fashi su kashe na kashewa su
kuma yi fyade ga matayensu,haka arnan daji idan
sunso mugunta saisu farwa wannan yanki su
ragargajesu su kwashe abinda zasu kwasa su
gudu.
A kwana uku da suka wuce,akwai wasu mahayan
yan fashi sukayi shigowar sumame cikin birnin
Haural cikin dare basu zame ko'ina ba sai cikin
kasuwar garin.koda suka shiga cikin kasuwar sai
suka farwa runfuna suka dinga kwasar kayan
al'umma ciki kuwa harda kayan da ake karbowa
daga kasar Latul Harus ake siyarwa kuma duk
kayan sarki ne yake karbowa daga can din ya
zuba a kasuwa idan an siyar a kaiwa sarki Aiyuba
dukiyar
da aka tara masa.
Daga cikin kasashen da suke kasuwanci da sarki
Aiyuba,kasar Haural suna daga na daya wadanda
suka siyar masa da hajoji,kayan abinci da sauarn
nau'ikan abubuwa da suke karbowa daga
kasar sarki Aiyuba.Saidai duk wannan wawash
kayan da kasar Haural suke sarki Aiyuba baya
daga musu kafa duk sa'adda akayi lissafi aka
samu akasi batare da dukiyar shi ta cika ba,sai
an samu matsala domin sai yayi musu bure ya
zare musu ido ya nuna cewar zai iya yaki dasu
idan har basu nemo masa cikon dukiyarsa
ba.Wannan dalili ne yasa a koda yaushe
idan kasar Haural sukayi lissafi idan zasu fitar da
dukiyar sarki Aiyuba idan suka lissafa sukaga
babu cikon kudinsa to idan hankalinsu yayi dubu
sai ya dugunzuma saboda tsananin tsoransa da
sukeji.Sannan su zauna suyi kama kama su hada
dukiyoyin attajiran kasar su hada masa dukiyarsa
saboda gudun masifarsa.
Da haka suke tsira daga azabar sarki Aiyuba
kuma babu dalilin da yasa yaki jinin ya tausaya
musu face sun banbanta a addini,shi yana bautar
gunki su kuma suna bautar Allah(SWT).Wannan
dalili ne yasa baya daga musu kafa baya jin
kansu ko tausaya musu dalili dayane ma yasa
yake basu kaya,dalilin kuwa shine suna tara
masa dukiya a bagas.Koda yan harin sumamen
yan fashin suka ragargaji kasuwar birnin suka
kwashe dukiya sannan suka shiga babban ofis din
ma'adanar
dukiyar kasar ta cikin kasuwar suka kwashe
komai sai suka haye dawakansu suka fice daga
cikin
kasar.Lokacin da gari ya waye,wasu dakarin da
suke tsaron kasuwar suka nufo gidan sarki cikin
tsananin dimauta hankulansu duka a tashe,cikin
tsananin firgici koda zuwa sai suka yi cirko cirko
suna
sauraren fitowar sarki,jim kadan saiga sarki ya
fito hankalinsa a tashe domin tun kafin zuwansu
ya riga ya gama sanin abinda ya faru tun da
akayi sallamar sallar asuba.
Koda zuwa gabansu sai sarkin kasuwa ya duka
gabansa cikin tsananin tashin hankali ya fara
zubar da hawaye kafin yace komai.Sarki ya
dubeshi cikin damuwa da dimauta yace,yakai
sarki
kasuwa abinda nakeson ji daga gareka yanzu
shine ina babban ofishinmu inda ake adanawa
sarki Aiyuba dukiyarsa da muka fitar aka tanada
ana jiran ranar dazai aiko a basa kayansa,ina
fatan dai ace a cikin wannan dukiya da take cikin
babban ofishin kasuwa
ba'a taba ta ba,in har wannan dukiya bata samu
tabuwa ba to babu shakka mun tsira daga azabar
rikicin dazamu fuskanta,in har kuwa Allah yasa
dukiyar sarki Aiyuba bata tabu ba to duk irin
asarar da mukayi saimu rungumi kaddarar Allah,in
kuwa dukiyarsa ta tabo to saimu ce inna lillahi
wa'innna ilahiraji'un,domin kuwa wannan babbar
masifar tafi dukkan irin masifun da suke kawo
mana barazana a cikin wannan yanki namu.
Koda sarki Arsanal yazo nan a jawabinsa sai
sarkin kasuwa ya dubi sarki cikin tsnanin
damuwa daga bisani kuma saiya fashe
da kuka,Al'amarin daya dugunzuma hankalin sarki
kenan,yayi matukar tashi cikin tsananin firgici
yace,mai ya faru yakai Zanur inason kayi maza
ka sanar dani abinda ya faru.Zanur najin haka
saiya goge hawayen fuskarsa cikin tsananin
dimauta yace,ya shugabana hakika wadannan
yan sumamen sunyi mana babbar illa ko
kwatankwacin irinta ba'a
taba yi mana ba,domin kuwa babu abinda suka
bari daga dukiyar kasar nan kama zuwa dukiyar
sarki
Aiyuba da sauran kayansa da suka rage,kama da
sauran hajojinsa.Duka wadannan yan sumame
babu
abinda suka bari yakai sarki mai iko da daraja.
Fadar hakan keda wuya sai zuciyar sarki Arsanal
ta buga take ya sulale kasa sharaf.Cikin azama
aka daga shi aka shiga dashi cikin gidan aka
kwantar dashi bisa shimfidarsa ana masa fifita,
Matarsa da dansa Yazid suka nufo cikin turakar
tasa a dimauce cikin tashin hankali,koda isowarsu
sai sukayi arba da sarki a kwance baya iya
motsawa wannan al'amari shiya kara dugunzuma
hankalinsu kenan,sukayi sauri suka
isa gareshi matarsa Barira ta durkusa idanunta
dauke
da hawaye tace,ya mai gidana mai ya sameka ka
shiga cikin wannan hali?
Yakai Mijina uban Yazid ka daure ka tashi gamu
gareka,Yakai Abu Yazid ka daure ka tashi.
Yazid ya risina ya kama hannun
mahaifinsa yace,Ya abbana shin menene ya saka
cikin halin suma alhakin yanzun nan ka fita cikin
koshin lafiyarka,babu ko damuwa a tare
dakai,yakai Abbana kada wani fushi yayi tasiri a
zuciyarsa har
yakai gamun rasaka,kayi juriya da dukkanin fitinar
data razana maka zuciya.Allah (SWT) shine mai
yayewa kuma ina mai rantsuwa da ubangijin
musulunci duk irin abinda ya raunana maka
zuciya zanyi iyakar nawa kokarin danna kawar
maka dashi.Koda kuwa masiface kwatankwacin
masifar dodannin da suke kawo mana hari a duk
karshen shekara ya abbana kayi dauriya ka tashi.
Jin wannan alwashi da Yazid yake dauka yasa
sarkin kasuwa matsawa kusa dashi cikin tsananin
tausayawa ya dafa kafadar Yazid yace,ya
shugaba kayi hakuri kabi
sannu a hankali domin shugabana yana cikin
tashin hankali da buguwar zuciya ta haifar
masa,abinda ya kamata kayi hakuri ka koma gefe
ka zauna yanzun
nan an tura likita yazo domin ya duba lafiyarsa.
Lokacin da Yazid yaji wannan batu saiya waigo a
hankali ya dubi sarkin kasuwa cikin ladabi
da biyayya yace,yakai sarkin Kasuwa sanar dani
meye yasa mahaifna zuciyarsa ta bugu harya
kasance cikin tashin hankali ya shiga hali irin
wannan?
Koda jin wannan batu sai sarki Kasuwa ya rike
hannun Yarima Yazid ya kuma jashi gefe guda
daga cikin babbar turakar sarki,ana cikin haka ne
saiga likitan sarki ya shigo da yar akwatunsa da
take
dauke da magunguna.Wannan al'amari ne yasa
shi mahaifiyar Yazid ta baro gurin mijinta ta
dawo gasu yazid da sarkin kasuwa a yayinda
yake shirin fara labarta masa abinda ya faru.
Sarkin kasuwa yayi gyaran murya cikin kallon
Yazid da muryarsa mai
nutsuwa da kwantar da hankali ga mai sauraro
yace,abinda ya faru shine,adaren yau yan fashin
sumame sunyi gangami wanda basu taba yin
kamarsa ba haka zalika sun shiga cikin kasuwar
garin nan sun kwashe duk wata
dukiya da kayayyakin abinci da suke kasuwa,basu
bar komai ba.Wani abin takaici bayan da suka
gama satar tasu,sai suka dinga bankawa cikin
gidajen da suke makota da kasuwa suna kama
mataye sunayi musu fyade suna kuma kashe duk
wanda yayi
niyaryi musu katanga daga abinda suke
aikatawa,tun a talatainin dare suka bayyana basu
suka bar cikin kasar nan ba saida alfijir ya keto
lokacin da aka fara kiran assalatu.Yakai Yarima
wannan labari daya riski sarki shine abinda ya
bakanta masa rai har yasa
zuciyarsa ta buga.
Koda sarkin kasuwa yazo nan a cikin batunsa sai
hankalin Yazid ya dugunzuma cikin zuciyarsa ya
fara tasbihi yana kiran sunan Allah,iyakar bacin
zuciya zuciyarsa ta baci hankalinsa ya
dugunzuma ainun.Domin lokaci guda jikinsa ya
fara rawa naman jikinsa yahau karkarwa tamkar
wanda ake sassara masa jiki.Duk irin sanyi
da yake ratsa turaka sai ya zamana Yarima Yazid
gumi ne kawai ke karyo masa.
Barira kuwa kuka ta kamayi saboda tsananin
firgici daga bisani tayi ajiyar zuciya ta dubi sarkin
kasuwa tace,yanzu kenan dukiyar sarki Aiyuba
duka har da ita suka
wawashe?
Sarkin Kasuwa ya jinjina kai ya amsa mata da
cewa ai babu abinda suka bari a babban ofishin
kasuwa komai sun wawashe hatta ragowar
kayansa da sukayi kwantai basu bari ba sun tafi
dasu.Nan take ta sunkuyar da kanta tasa bakin
zanenta ciki ta toshe bakinta dan kada sautin
kukanta ya cika
daki.A hankali take furtawa shikenan mun shiga
uku,mun lalace,shikenan sai mun dandana azabar
sarki Aiyuba domin kuwa bazai taba yafe mana
ba.
Yazid cikin tsananin mamaki ya dubi ummansa
ya durkusa gabanta yace,ya ummin waye sarki
Aiyuba?
Kuma mai zai sa mu dandana azabarsa dan
dukiyarsa ta salwanta shin baisan kaddara ba?
Ummansa ta girgiza kai cikin tarin takaici
tace,Sarki Aiyuba yasan kaddara kuma yana da
tsananin kirki yana kyautatawa al'uma domin
abinsa bai rufe masa ido ba,saidai duk wannan
kyautatawar dason taimakon al'ummar yanayinsa
ne akan kafurai
wadanda suke bautawa gunki,ko kuma suke tsafi,
baya afuwa ga duk wanda ya kasance yana
addini irin namu,baya kaunar musulunci da
musulmai,kuma wannan abu har idan yaje
kunnensa bazai damu ba da asarar da yayi ba,sai
dimbin
farinciki saboda ya samu hanyar dazai kuntata
mana ya samu hanyar dazai tozartamu,tabbas
idan har ba karbar addininsa mukayi ba babu
shakka ko wanda yake cikin kada saiya fimu jin
dadin rayuwa ko kuma wanda ya kasance cikin
karkashin ruwa yana
neman taimako.
Dajin wannan batu sai Yarima Yazid
yayi shiru yana tunanin tabbas yasan labarin
sarki Aiyuba yana ganin shagunansa a kasuwar
garinsu,kuma yanaji a yawan lokaci idan an tashi
lissafin dukiyarsa mahaifinsa hankalinsa kan tashi
ainun.Nan da nan ya shiga cikin damuwa ya
kuma
fara neman hanyar dazai magance wannan
matsala tunda duk rintsi duk tsanani sai ya fitar
da kasarsu
daga cikin masifar sarki Aiyuba koda zai rasa
rayuwarsa ne saidai hanyar dazai bi ya magance
hakan ne bai santa inda zai biba.
Muryar likitan da yake duba lafiyar sarki sukaji su
dukan suka waiga
gareshi,suka zuba masa idanu cikin firgici ba
komai ne ya jefasu cikin firgici ba face ganin
yanda alamun
damuwa karara suka baiyana a fuskar likitan,da
sauri Yazid,Barira da sarkin kasuwa suka nufi
inda likitan yake zaune kusa da sarki da yake
shimfide akan gadonsa na alfarma.Koda zuwa
gabansa sai Yazid cikin kagauta ya dubi likitan
yace,yakai babban amintaccen likitan abbana
shine meye yake damun abbana?
Koda likitan yaji Yazid da wannan tambaya sai ya
dago kai ya dubeshi sannan ya sauke ajiyar
zuciya yace,tabbas sarki ya samu tabuwa a cikin
zuciyarsa wanda ta haddasu bisa faduwa da
gabansa
yayi,ta yiyu sarki yayi gamo da wani abu ne mai
ban tsoro ko kuma akwai abinda ya sameshi
wanda ya firgitashi ainun,dan haka yanzu abinda
nake bukata
shine abarshi ya samu hutu,na tsawon kwanaki
arba'in a cikin wadannan kwanaki sarki zai
fardado a kwana biyu rak,amma koda ya farfado
zai kasance
cikin yanayin mantuwa har tsawan wadannan
kwanaki.
Abin kiyayewa a cikin wadannan kwanki shine
kada wani mahaluki ya sake ya sanar dashi wata
magana da zata tada hankalinsa in har kuwa aka
tunatar dashi to babu mamaki idan zuciyarsa ta
kara bugawa ayi asararshi baki daya.
Dan haka sai a kiyaye da wannan in Allah yaso
zai samu sauki a cikin wannan kwanaki kuma a
kwana arba'in din tunaninsa zai dawo.Koda likita
ya gama yin wannan
jawabi sai hankalin Yazid ya kara dugunzuma
musamman da yaji anacewa idan aka kara
tunatar
da sarki wani abu zai bata masa rai zai iya
asararsa.Nan danan ya dubi likitan yace,Ya likitan
mahaifina kamar wacce magana da wacce
magana ne ya kamata akadaita kunnensa dasu?
Koda likitan yaji wannan tambaya sai ya dubi
Yazid yace,ai duk wani abu da akasan bana dadi
bane kada a sake ayi masa maganar domin kuwa
yin hakan zaisai
danasani ta hau kanmu domin tabbas za'a iya
rasa sarki.
Yazid yayi shiru yana nazari.Ana cikin haka saiga
waziri da galadima duk sun shigo cikin turakar
hankulansu a tashe saboda tsananin firgici har
faduwa sukeyi saboda tsananin firgici.Koda
isowarsu sai Yazid da mahaifiyarsa suka duka
suka kwashi gaisuwa saboda tsananin tashin
hankalin da suke ciki basu ma samu damar amsa
gaisuwar ba,Barira ta fice daga cikin turakar
shima likitan ya tafi bayan yayiwa su waziri
bayanin irin abinda yake damun
sarki.
Waziri ya dubi galadima cikin damuwa
yace,hakika tashin hankali ya tabbata a garemu
wanda kuma bamu da mafita face ubangiji ya
samar mana mafita,masifar sarki Aiyuba lallai
saita tabbata a kanmu domin dama bashi da
wani buri face yaga
mun dakusar masa da dukiya,Gashi yanzu saura
kwanaki goma sha biyar ayi wannan lissafin duka
dukiyarsa anyi asararta.
Hudijam masifa bata da rana sai a lokacin data
tabbata,yakai Galadima ga sarkinmu rai a hannun
Allah,mene dabara?
.
En uwa masu karatu ku basu shawara me yaka
mata suyi?
.
Sai amin apuwa na rashin jina da wuri da patan
za a karbi uzurina.
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Daya (1)
Part D
.
Yakai Galadima ga sarkinmu yanzu rai hannun
Allah,menene dabara?
Koda jin haka sai galadima ya gyara murya ya
nutsu sannan tafe,babu dabara babu karfi saina
ubangijin musulunci ai bamu da abinda yafi face
mu mika ragamarmu ga Allah domin kuwa
shine kadai zai iya cetonmu.
Waziri ya girgiza kai gami da gyara zama ya dubi
sarki dake kwance bai
masan sunayi ba,ya maida kansa ga kallon Yazid
daya zuba musu ido cikin tsananin tashin hankali
sannan ya maida kansa ga galadima yace,hakika
maganarka gaskiya ce babu wanda zamu mika
lamuranmu face Allah da ya halicce mu,saidai
kuma ko ubangiji ya horemu da muyi yunkuri
wajen kare kanmu daga dukkan masifar datake
naman kawo barazana a garemu,wanda wannan
hubbasa din da zamuyi shi zaisa Allah yaji kanmu
da rahma ya taimakemu,amma muna kwance mu
dinga tunanin taimako daga gareshi tamkar mun
kasance lusaray ne.
Galadima ya danyi shiru daga bisani ya dubi
waziri yace,maganarka kaima gaskiya ce,ya zama
dole muyi hubbasa domin kare kanmu daga irin
masifar da zata tunkaro mu anan da kwanaki sha
biyar masu zuwa,saidai abin tunanin anan shine
fitinar da zata tunkaro mu ba irin fitinar da suka
saba kawo mana farmaki bane da zamuyi yan
dabaru mu korasu,inason ka sani shi sarki Aiyuba
matsafi ne,baya ga haka kuma ya mallaki dumbin
mayaka marasa iyaka,da idan ya turo mana kaso
daya daga cikin kaso dari na dakarunsa sai sun
cinye namanmu danye,bare nasan mugunta ta
sarki
Aiyuba domin ya tozartamu sai ya turo mana fiye
da kaso goma,yanzu idan ya turo mana kaso
goma daga cikin kaso na adawansa yaya kake
tsammani zamu karke dasu.Koda waziri yaji
wannan batu
saiyayi shiru kawai domin maganar da galadima
ya fadi gaskiya ce,dan haka sai ya gyara murya
yace,abinda ya kamata yanzu ayi shela ana
neman
kowa a fada gobe dan aji shawarwarin kowa akan
abinda zai kawo mana sauki daga cikin masifar
da zata tunkaromu.
Da wannan shawarar ta waziri suka
dasa aya,washe gari da safe bayan an zauna a
fada waziri ya wakilci sarki bisa girmansa da
kuma jin
maganarsa da ake a cikin kasar,ya fara bayani
kamar yanda suka farashi da galadima har kawo
karshen tattaunawarsu.Koda waziri ya gama
kawo musu
tattaunawar da sukayi shida galadima sai ya dora
da cewa duk wanda yake da wata shawara zai
iya kawo tasa domin dai a samu a tsira daga
masifar da zata addabemu.Waziri yayi shiru na
tsawan lokaci batare da kowa yace komai ba
kowanne dake cikin fadar
gabansa ne kawai yake faduwa.Domin tun lokacin
da labari ya iske kowa an sace dukiyar sarki
Aiyuba sai hankalinsu ya dugunzuma ya kuma
kasa kwanciya da kyar aka samu wani attajiri
wanda ake kira da suna Ishalu.Koda mikewar
ishalu sai ya gurfana a tsakiyar taron
yace,tabbas muna cikin tashin hankali da hali na
tsaka mai wuya,abinda nake nufi anan
shine muna cikin tashin hankalin da bamu da
tabbacin fita daga cikinsa sai yanda hali yayi,ni a
tawa shawarar ina ganin a samu mahayi ayi
rubutu na wasika zuwaga sarki Aiyuba a shaida
masa ga abinda ya samu dukiyarsa yayi mana
hakuri ya karo mana kaya idan shekara ta zagayo
sai mu biyashi rabin abinda zamu bashi a
wannan shekara sannan mu bashi na shekarar da
ake baki daya,inyaso wata shekarar ma sai ayi
hakan,kunga kenanan mun jefi
tsuntsu biyu da hogi daya,mun bi yasa kuma mun
cigaba da cinikayya dashi sabanin yaji wannan
batu ta sama,nasan halin sarki Aiyuba zai iya yin
hawa
da dakarunsa yazo ya wulakantamu.Koda
wannan
attajiri yazo nan a jawabinsa sai galadima ya
mike tsaye yace,yakai Ishalu wannan shawara
taka sam
batayi ba,in baka manta ba,akwai yarjejeniya a
tsakaninmu da sarki Aiyuba na rashin yin afuwa
akan duk abinda ya samu dukiyarsa,kada ka
manta sarki Aiyuba ya kwulla wannan kasuwanci
damu ne bisa yahudawa da suka umarce dayayi
hakan suka kuma kimtsa masa ta yanda zai ci
galaba akanmu
idan an kwulla wannan kasuwanci,kayi sani cewa
sarki Aiyuba bai kulla wannan kasuwanci damu
ba
dan samun ribarmu ko dan samun cigabanmu ba.
Ya kulla wannan kasuwanci ne dandai kawai yaci
zarafinmu
ya tozartamu ba dan komai ba duk a cikin
nahiyarsa mu kadai ne kasar da mukeyin addinin
musulunci,kuma yayi iyakarsa kokarinsa akan ya
dakatar damu daga bautar Allah amma hakan ya
gagara,tabbas idan aka tashi dan aike zuwa
kasar Lautul Harus tabbas kafin cikar kwanaki
hudu sai
mashuna sunyi zaman dirshen a cikin
kahonhunan zuciyoyinmu tabbasa sai jini ya
gauraye da kasar
wannan birni na Haural,in gar bamu kasance mu
kafirta ba munbi abinda suke bautawa dan haka
wannan shawarar taka sama bama kaunarta
wata kwatankwacinta duk wanda zai kawo
shawara ya zamana ya kawota daidai da
fahimtarmu.
Koda galadima ya koma ya zauna sai dukkan
jama'ar da suke garin sukayi shiru babu wanda
ya kare cewa kala har aka wuce dakika biyar sai
daga can wani shehin malami da ake kira da
suna Ibini Haisham ya mike tsaye cikin fararen
tufafi kansa da rawani,koda
mikewarsa sai yayi gyaran murya ya dubi
daukacin jama'r da suke zaune yace,hakika
zuciyarmu tayi
rauni kwarai da gaske zuciyoyinmu sun cika da
shakkun wasu zindikai kafurai masu bautar wanin
Allah,lallai daga cikin hasashen karshen duniya
wannan yana daga ciki yaku jama'ar musulmai
kuyi
sani cewa duk irin takamar da sarki Aiyuba yake
ba da koma yake takama ba face sihiri,sihirin
kuma
baikai ayar Allah ba,ina mai son kuyi sani cewar
bazaranar yawan dakaru da sarki Aiyuba yakeyi
akanmu basu isayin komai akanmu ba face mun
barsu duk irin yawansu da tarin bataliyarsu basu
isa suyi nasara akanmu ba saida ikon Allah,lallai
akwai bukatar jajircewa mu shirya kanmu kafin
zuwan wannan rana kamar
yadda kuka sani idan ranar da akai wannan
lissafi ta cika ba a kaiwa sarki Aiyuba dukiyarsa
ba babu
makawa washe garin ranar inuwar gagaruman
sadaukai zasu cika mana birni,zasu yi mana
rumfa da masu zasu haskaka mana rayuwa da
kaifin takubbansu,tabbas hakan gaskiya ne domin
babu
abinda zai hana faruwar hakan tunda dama
abinda suke jira ya samu kenan.To idan haka ne
mai zai hana muma muyi shiri mu fito mu kare
kanmu daga saukar kibiyoyinsu da
garkuwoyinmu,mai zaisa mu fito mu kare
haskakamu dazasuyi da takubbansu mai zai hana
mu zubar musu da jini kamar yadda zasu zubar
nama,idan har muka tashi tsaye da addu'a da
jajurcewa Allah daya haliccemu zai bamu sa'a
akansu to wai ma menene takamar sarki Aiyuba?
Ibn Haisham yayi ajiyar zuciya,Yarima Yazid ya
zuba masa ido tunda aka fara wannan batu sai
yanzu ne yaga abinda yake da bukatar ji,nan da
nan hankalinsa ya fara

1 Comments On WASIKAR JINI 1 to 8
avatar
abdulrasheed-yusuf

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment