Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kure sai ya tada sallar har saida
yayi raka'a biyu sannan ardadu ya fito da
hannunsa rike da wandonsa alamar yana daure
mazarin wandon.Nan ya zauna yayi alwala kamr
yanda Yazid ya koyar dashi,da yake Yazid basa
kan hanya har
wadannan mahaya sukazo suka wuce yazid bai
lura ba haka suma basu lura dashi ba.
Bayan sun kammala sallah sai Yazid ya dubi
ardadu yace wai ina kaje ka dade haka?
Dajin haka sai Ardadu ya danyi murmushi yace ai
cikina ne ya murda dan har saida na kosa da
tsugunno.
Yarima ya dubeshi sosai cikin rashin yarda yace
ban yarda dakai ba yakai ardadu ka sanar dani
gaskiya.
Ardadu yayi murmushi yace wacce gaskiya kuma
ai batun boye boye ni
dakai ta kau bazanyi sata ba bazanyi cuta ba
haka bazan ci zarafin kowa ba,wannan shine
alkawarin dake tsakanin nidakai kuma bazan saba
maka ba.
Koda jin haka sai Yazid ya danyi shiru yace idan
ka saba fa wane hukunci zan dauka akanka?
Ardadu dajin haka sai shima yadan yi shiru gami
da duban Yazid da murmushin yake yace,ka
hakura da tafiya dani kamar yanda kaso hakura a
baya.
Ni bazan hakura da tafiya dakai ba domin ka
zamo wani jigo na wannan tafiya,hukuncin dazan
dauka daishine idan harka saba to babu shakka
yaki zamu sakeyi
dakai sabo wanda babu wanda zai rabamu saidai
mutuwa.
Koda Ardadu yaji wannan batu sai gabansa ya
fadi take ya dubi Yarima Yace a'a gaskiya a
wannan ba hukunci bane yakai shugabana kadai
samu wani.
Yarima Yazid ya girgiza kai yace ba
shawara na nema daga gareka ba babu abinda
zai hana haka face ka kadaita zuciyarka da
aikata sabawa mahaliccinka.
Ardadu yayi shiru yana tunani daga bisani ya
dago kai ya dubi Yazid yace amma...sai yayi
shiru da bakinsa Yazid bai damu da tambayarsa
abinda yayi niyar fada ba sai suka cigaba da
tafiya,basuyi nisa da tafiyar ba sai Yazif ya dubi
ardadu yace,menene labarin WASIKAR JINI?
koda jin wannan tambaya sai Ardadu ya fadada
murmushinsa domin tun dazu abinda yakeson yaji
Yarima ya tambayeshi kenan,amma yayi shiru
yayi biris,nan take ya gyara baki yace,WASIKAR
JINI wata wasika ce da aka samar da ita ta
hanyar yin tawada da jinin wasu manyan jarumai
da suka shude su tara a cikin kasar latul
harus,itadai wannan wasika
da itane ya jawo habbakar arzikin kasar latul
harus kuma da ita ne sarki aiyuba yake takama
domin shi
kadai ne ya samu ikon karantata saidai ayanzu
akwai waziri ridwan da kuma dansa Zainur suna
nan suna shirye shiryen neman wannan wasikar
su karantata.Idan har waziri ridwan ya karanta
wannan
wasikar to birnin latus harus zai wargaje,zama
lafiyarsa zai bankwana tashe tashen hankula
zasu tsaya kaida fata a cikin birnin wanda mu
barayi wannan itace damar da muke nema domin
muyi
+Abbas Abdulkadir hada hada+.wadaka.Koda
Yarima Yazid yaji wannan batu saiya daka masa
tsawa da cewa kai ka manta a wane matsayi
kake yanzu da kake kiran kanka da barawo?
Koda jin wannan batu sai Ardadu ya tsuke
bakinsa sannan yace tuba nake ya shugabana ina
amfani ne da shirinmu na baya.Yazid yayi shiru
yace ina saurarenka.Nan take Ardadu yacigaba da
sanar dashi in kuwa har yarima zainur ne ya
samu damar mallakar wannan wasikar har ya
karanta ta to birnin
Lahul harus zai kasance cikin zaman lafiya da
lumana.
Koda Yarima yaji wannan batu sai Ya dubi
Ardadu yace idan ni ne kuma na mallaketa?
Dajinwannan batu sai Ardadu ya tuntsure da
dariya saida yayi ta isheshi sannan ya dubi yazid
tace ai ko a mafarki bana jin zaka iya mallakar
wannan wasikar domin kuwa yarima Zainur da
mahaifinsa sune kadai suke da damar da zasu iya
daukar wannan wasikar
harsu karantata kai kuwa baka da karfin da zaka
gwabza dasu har ka hanasu dauka,
idan kuwa a misali ka dauki wannan wasikar to
baka da damar
yin aiki da ita domin kuwa bazata taba yin
amfani a gareka ba domin baka kasance jinin
sarautar kasar
latul harus ba.
Koda jin wannan batu sai Yarima
Yazid shima ya tuntsire da dariya wannan dariya
ita ta saka Ardadu shiga tsananin mamaki ya
dubi yazid yace ya shugaba na ina dalilin wannan
dariya ahalin da nake sanar dakai mummunan
al'amari.
Dajin haka sai Yarima Yazid yayi murmushi yace
ba komai ne ya bani dariya saida kake sanar dani
wahalar mallakar wani abu daga cikin kasar
mushrikai matsafa,meye abin wahalar raba arne
da makami?
Da zuwa nan a batun Yazid sai Ardadu tace ai
kuwa wannan arne ba karamin takadir bane
domin kuwa dukkaninsu sun fika kyakyawar
hanyar da zata kaisu
ga samun wannan wasikar domin kuwa shi
yarima zainur zai samu taimako daga wata
kankanuwar
yarinya dake dajin dake makwobtaka dasu,shi
kuma waziri ridwan zai samu taimako ne daga
tsafi da kuma amininsa sarki Marwatu,kai kuma
naga baka da wani taimako daya wuce nawa ni
kuwa bani da karfin dazan iya kallon wannan
zarata da niyar yin
yaki dasu.
Dajin haka sai Yazid ya daga yatsansa daya ya
nuna sama yace hakika babu abin bauta face
UBANGIJIN MUSULUNCI ni ko kai babu abin
dogaro a cikin wannan tafiyar ubangijin daya
haliccemu ya
halicci duniya da duk wani abu da yake cikinta shi
zai bani ikon daukar wannan wasika kuma ba
burina na karantata ba burina na hana azzalumai
yin aiki da ita dan haka muje zuwa.
Koda gama fadin hakan sai yarima yayi gaba shi
kuma Ardadu ya bishi a baya har suka isa wani
guri da dawakai guda biyu suke tare da tarin
dukiya a gefe ga abinci.
Da ganin wannan dukita sai Yarima ya dauke kai
shi kuwa Ardadu sai ya dubi Yazid yace ya
shugabana ina dalili zaka dauke kai daga kyauta
da ubangijin musulunci ya bamu,lallai wannan
kyauta ce daga
gareshi domin kawo mana dauki a bisa tafiyarmu.
Yazid ya dubeshi yace bata haka
ubangijinmu yace mu nema ba,wannan dukiyar
wani ce ba tamu ba dan haka kada ka kuskura ka
taba su kazo mu cigaba da tafiyarmu.
Koda jin wannan sai Ardadu yace kada kayi haka
yakai Yazid wannan
dukiya da dawakai bana kowa bane face na
wadannan mahayan da suka nufo mu ni na ruke
su
suka bani kaga kuwa idan har muka tafi muka
barsu anan zasu mutu su bushe ko barayi su
sace su dan haka kazo mu tafi dasu.
Dajin wannan batu sai Yarima Yazid ya dakata ya
nufi Ardadu ya zare gatari da takobin da suke
jikinsa ya mike masa daya yace
babu abinda zai rabani da kai sai mutuwa yakai
wannan mayaudari macuci maha'inci.
Koda fadar haka sai yaja da baya ya tsaya yana
jiran Ardadu amma ardadu ko motsi baiyi ba
ganin haka yasa Yazid ya daka tsalle ya nufeshi.
YAUSHE NE SARKI AIYUBA ZAI FADI YA MUTU?
TSAKANIN YARIMA ZAINUR DA WAZIRI RIDWAN
DA KUMA YARIMA YAZID WAYE SAI SAMI
NASARAR GANIN WASIKAR JINI?
WANE MATAKI SARKI MARWATU ZAI DAUKA IDAN
YA FARFADO DAGA SUMA DA YAYI YAGA AN
GUNTULE MASA BABBAN DAN YATSANSA NA
HAGU?
SHIN WANE IRIN BAKIN YAKI ZA'A KWAFSA
TSAKAKIN ARDADU DA YARIMA YAZID?
Mu hadu a WASIKAR JINI littafi na uku don jin
cigaban wannan labari.
Ina mai baku hakuri na rashjin jina jiya da kukayi
saka makon rashin chaji a wayana. Da patan
zakumin uzuri,
in Allah yakaimu anjima da dare ina dauke da
cigaban littapin ammana sai naga masuso da
yawa.
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Uku (3)
Part A
.
Lokacin da Yarima Yazid ya dako tsalle sama ya
kaiwa Ardadu Mugun sara da addarsa sai Ardadu
yai sauri ya kare saran don ceton rayuwarsa
amma sai Yazid yasa kafarsa ta dama ya doki
cikin Ardadu.
Take cikin nasa ya kulle ya fadi kasa yana
murkusu gami da kuma kallon wuya a lokacin da
numfashinsa ya kama sarkewa kamar zai
mutu.Har Yarima Yazid ya sake daga addarsa
sama zai fille
kan Ardadu cikin tsananin fishi sai kuma ya
fasa,cikin sanyin jiki Yazid ya ajiye addarsa
sannan ya dubi Ardadu cikin alamun tsananin
takaici yace abinda ya hanani kasheka yanzu abu
daya ne kuma
ba wani abu bane face kai musulmi ne.Babu wata
hujja da zatasa musulmi ya kashe dan'uwansa
musulmi face ya aikata zunnubin daya cancanki
kisa.
Ayanzu kai ka aikata laifin sata don haka
hukuncin laifin sata zan maka yanzu.
Kafin Ardadu ya budi baki yace wani abu tuni
Yarima Yazid ya shammace shi ya sare wuyan
hannunsa na hagu,nan take Ardadu ya kwala
uban ihu lokacin da hannun nasa ya guntule
kuma jini yai tsartuwa kawai sai Ardadu ya sulale
kasa sumamme.
Lokacin da Ardadu fardado daga suman da yayi
saiya tsinci kansa akan doki guda,doki na tafiya
dashi a gefensa kuma Yarima Yazid ne bisa wani
dokin.Suna hada idanu sai Yarima Yazid yayi
masa murmushi yace,yakai Ardadu ina tayaka
murna bisa sauke nauyin zunubin dake kanka na
sata,ka sani cewa idan ka sake yin sata zan sake
sare daya hannun naka lafiyayye ka zamo
cikakken kuturu mara yatsu goma.Kana gani dai
yanzu ka rasa yatsu biyar
saboda haka sai ka kiyaye,koda jin wannan batu
sai hawayen takaici ya zubowa Ardadu
yace,yanzu ashe
har hukuncin sata yakai matsayin a yankewa
mutum hannu?
Yarima Yazid yace kwarai kuwa ai sata babban
laifi ne a addinin musulunci saboda ayi nuni da
haka ne akayi wannan hukunci mai tsauri.Koda
gama fadin hakan sai Yarima Yazid yai shiru bai
kara cewa komai ba,shi kuwa Ardadu banda
kukan zuciya da tsananin bakin ciki babu abinda
yake fama
dashi a cikin ransa.
Haka dai suka cigaba da tafiya ba sassauci suna
masu durfafo birnin latul harus domin gano a
inda wasikar jini take.
Acan cikin birni na latul harus kuwa lokacin da
sarki marwatu ya farfado daga suma da yayi
sakamakon babban dan yatsansa na hagu da
sarki Aiyuba ya
guntule masa sai ya mike zaune zumbur kamar
wanda ya farka daga mafarki mai ban tsoro ya
kama waige waige gami da duban dakin da yake
ciki a lokacin da yake kokarin tunani domin ya
gano waishin abindake faruwa a gareshi mafarki
ne ko kuwa gaske ne kwatsam sai yaji an turo
kofar dakin an shigo.Ba wani bane ba ya shigo
face Waziri Ridwan fuskarsa cike da annuri nan
take sarki
marwatu yayi dogon ajiiyar zuciya ya dawo cikin
haiyacinsa kuma a lokacin ne ya tuno da duk
abinda ya faru tsakaninsa da sarki Aiyuba a
fada,cikin firgici ya daga hannunsa na hagu,koda
yaga babban dan
yatsansa na hagun a guntule sai ya takarkare ya
kurma uban ihu.A lokaci guda kuma ya fashe da
kukan bakin ciki,koda ganin haka sai waziri
ridwan ya zauna akan gefen gadon da sarki
marwatu yake ya dafa kafadarsa yace kwantar da
hankalina yakai abokina kayi sani cewa kada
mage ba yanka bane,tabbas yanzu sarki aiyuba
ya sami lagonka tunda ya rabaka da gaba daya
sirrikanka na tsafi kuma ya wulakantaka ya
tozarta darajarka a gaban mutane amma ka sani
cewa lokaci zaizo wanda zakayi ramuwar gayya.
Na sani cewa bazaka iya daukar fansa ba akan
sarki aiyuba amma zaka iya dauka akan 'yarsa
gimbiya Nauwara kuma ina mai tabbatar maka da
cewa wannan lokaci yana daf da zuwa,sa'adda
waziri ridwan yazo nan a zancensa sai sarki
marwatu ya dubeshi cikin alamun kaduwa da
tsananin mamaki yace yakai tsohon abokina
menene
hujjarka ta cewa wannan lokaci yana daf da
zuwa?
Koda jin wannan tambaya sai waziri ridwan ya
kyalkyale da dariyar mugunta lokaci guda kuma
saiya turbune fuska yace bincike ya nuna mana
cewa sarki aiyuba na dauke da cutar ciwon zuciya
kuma
ba komai bane ya haddasa masa wannan ciwo ba
face bakin cikin sani cewa 'yarsa gimbiya
Nauwara
bazata taba gadar karagar mulkinsa ba.tabbas
sarki aiyuba yaso ace 'da namiji ya haifa ba mace
ba,na sami labarin wannan cuta tasane daga
bakin babban
likitansa wanda ya aminta dashi dari bisa dari
abinda bai sani bashine a duniya bashi da
makiyin da yafi wannan likita nasa saboda
maganin ma da yake bashi yana sha yana karawa
cutar karfi a hankali ba tare da ya ankara
ba.Koda jin wannan batu sai mamaki ya kara
turnuke sarki Marwatu yace yakai abokina
menene ya haddasa kiyayya tsakanin sarki
aiyuba da wannan liktan nasa harda yake yi masa
wannan mugun tanadi?
Koda jin wannan tambaya sai
waziri Ridwan ta sake bushewa da dariyar
mugunta a karo na biyu sannan yace ai labarin
ne mai tsawo kayi hakuri Zan baka wannan labari
nan gaba idan
lokacin daya dace ka sani yayi,abinda nakeso
dakai yanzu shine kayi shiri ka koma izuwa
kasarka ka
cigaba da tafiyar da harkokin mulkinka kamar
yadda ka saba kada ka kuskura ka nunawa
talakawanka gajiyawarka harsu gane cewa yanzu
baka da karfin
sihirin tsafi,ka sani cewa kowa yana tsoronka a
kasar taka ko dan saboda karfin damtsenka da
iya
yakinka,ka cigaba da hakuri har izuwa lokacin da
hakanmu zai cimma ruwa,da zarar sarki aiyuba
ya fadi zan aiko kazo cikin gaggawa domin
musami damar cika burinmu.Koda jin wannan
batu sai sarki Marwatu ya dubi waziri ridwan
cikin alamun mamaki
yace bangane abinda kake nufi ba,zaka kirani
bayan ya fadi,kana nufin da zarar ya kwanta
rashin lafiya ko kuwa da zarar ya mutu?
waziri Ridwan yayi ajiyar zuciya yace ai da zarar
ya kwanta rashin lafiya a lokacin da ciwo yayi
tsanani zanyi wata gagarumar ta fiya neman
wasikar jini,dole saina sami wasikar jini na
karantata sannan zan iya hawa karagar mulkin
kasar nan,a halin yanzu duk duniya babu wani
mahaluki wanda ya isa ya iya karanta wannan
wasikar jini har ya iya zama sarki a wannan kasa
tamu kuma ya mallaki wannan dukiya mai
tsananin yawa ta sarki aiyuba face ni da dana
yarima zainur,amma duk yadda zanyi saina
tabbatar da
cewa hannu na ya riga na dana kaiwa kan
wasikar jini.
Koda jin haka sai sarki marwatu ya jinjina kai
cikin alamun mamaki yace to waishin yanzu
kenan kai da danka zaku iya zama ABOKAN
GABA.
Waziri Ridwan ya turbune fuska yace kwarai kuwa
kuma idan harna gama yana nema ya zarce mini
matsala zan iya kawar dashi.Koda jin wannan
batu sai mamaki ya turnuke sarki marwatu yace
haba yakai abokina yarima zainur nefa dakai
danka a duniya.
Waziri Ridwan yayi dan guntun murmushi yace
nasan da haka aini a wajena dashi da babu duk
dayane tunda tsakanina dash babu wata shakuwa
kuma yafi kaunar makiyana fiye dani.
Sarki marwatu ya gyada kai a lokacin daya mike
tsaye yace babu
matsala zan zauna a cikin sauraron jin sakonka
kuma ina mai tabbatar maka da cewa zan baka
dukkan gudunmawa wajen ganin burinka ya cika
amma ka zamo mai cika alkawari a gareni.
Waziri Ridwan yayi 'yar gajeriyar dariya yace
kada ka damu yakai abokina lallai zaka sameni
mai cika alkawari shin yanzu kana da wata
bukata da kakeson a biya maka kafin ka tafi
izuwa birninka?
Sarki marwatu yayi ajiyar numfashi yace kwarai
kuwa inada bukata guda daya inason ka turo mini
sarkin makera na garin nan
akwai abinda nakeson ya kera mini kafin na bar
garin nan naku.Koda jin wannan batu sai waziri
ridwan yayi murmushi yace nasan abinda kakeso
a kera maka kuma kayi babbar dabara domin ta
hakane kadai zaka kawar da tunanin mutane akan
abinda ya sami babban dan yatsanka na hagu ka
tafi izuwa masaukin naka yanzu nan zan turo
maka sarki makera.Gama fadin hakan keda wuya
sai sarki marwatu yayi murmushi sannan ya juya
ya fice daga cikin turakar.
Lokacin da sarki ya isa masaukinsa sai dakarun
dake tsaron masaukin suka tareshi da albishir na
cewa sarkin makera na zaune a cikin falonsa
yana jiransa.Cikin tsananin mamaki sarki
marwatu ya jinjina kai kawai saiya kunna kai
cikin
babbar turakar yana murmushi yana shiga kuwa
yayi arba da sarkin makera zaune akasa bisa
kilishin dakin.
koda sarkin makera ya ga sarki marwatu tsaye a
kansa sai ya zube kasa wanwar ya kwashi
gaisuwa
sannan yace ya shugabana na amsa kiranka me
kake bukata daga gareni?
Sarki marwatu yayi murmushi yace yakai sarkin
makera kayi sani cewa
ina da bukatar ka kera mini hannu na karfe
wanda zan sanyashi akan hannuna na hagu kuma
na iya sarrafashi ba tare da ido ya gane cewa na
sanya hannun ba.
Koda jin wannan batu sai sarki makera ya jinjina
kai yayi shiru tsawon yan dakiku kadan sannan
ya dubi sarki marwatu cikin biyayya yace ya
shugabana wannan aiki ne mai wahala wanda
ba'a taba yin irinsa ba kuma zaici kudade masu
yawa.
Kodajin haka sai sarki marwatu yayi murmushi
yace kudi ba matsala bane ko nawa ne ake
bukata zan bayar,matsala itace tsawon kwana
nawa zaka iya kammala wannan aikin?
Sarkin makera yayi dan nazari sannan yace zan
iya kammala
wannan aiki a cikin sati daya da kwana biyar.
Koda jin haka sai sarki marwatu ya kyalkyale da
dariya sannan ya fiddo jakar kudi cike da lu'u lu'u
ya yafewa sarkin makera ita batare daya kirga iya
adadin lu'ulu"un dake ciki ba yace,ga wannan
kaje
ka fara aiki idan basu isa ba ka aiko na kara
maka.
Hannun sarki makera na rawa ya dauki jakar
lu'ulu'u ya kama godiya kamar zai yiwa sarki
marwatu sujjada ya mike tsaye yana mai cewa ya
shugabana ai wannan kudi ya isa a kammala
komai.
Nan take sarki marwatu ya sallami sarkin makera
ya tafi shi kuwa marwatu saiya zauna a turakar
yayi tagumi yana mai fadawa cikin dogon tunani
na bakin ciki da takaici,
ba komai ne yaje fa sarki marwatu cikin wannan
hali ba face jin batun wasikar jini.Ada ba komai
sarki marwatu ke shirin yiba face yaudara gami
da cin amanar abokinsa waziri ridwan,abinda ya
aiyana aransa shine da zarar
sarki aiyuba ya fadi ya mutu zai kawo harin
bazata ya kama birnin da karfin tsiya kuma ya
dare kan
karagar mulkin sarki aiyuba,yanzu da yaji cewa
bazai iya hawa karagar sarki aiyuba ba face ya
karance wasikar jini kuma ya kasance jinin
sarautar latul harus sai murna ta koma ciki kuma
ya kamu da tsananin bakin ciki.Nanfa zuciyarsa
ta kama sake sake ta kulla wannan ta kwance
wance har sai da lokacin bari yayi,wato dare ya
raba sosai amma sarki marwatu bai sami mafita
ba ko shawara wacce zata fishshe shi,bisa dole
sarki marwatu ya hakura da
tunanin komai ya mike tsaye ya shiga cikin
turakar ya kwanta kwanciyarsa keda wuya kuwa
sai ya kama barci harda munshari.
Al'amarin Yarima Zainur kuwa lokacin daya rabu
da gimbiya Nauwara sai hankalinsa ya
dugunzuma ainun fiye da ko yaushe a
rayuwarsa,ba komai ne ya
tayar masa da hankali ba face jin batu cewa
shida mahaifinsa zasu zamo abokan gaba akan
neman
mulki,nanfa yarima zainur ya fara tunanin hanyar
dazaibi ya hana faruwar wannan gaba amma
daya
nutsu a cikin tunanin nasa saiya gane cewa babu
makawa sai wannan gaba ta kullu tunda daishi
yana kishin kasar da kuma jama'arsu,shi kuwa
waziri
ridwan akan biyan bukatarsa zai iya siyar da
kasar gaba daya,to waishin yanzu wane hukunci
ya kamata na yanke?
Shin idan lokacin tafiya neman wasikar jini yayi
zan hana mahaifina yin tafiyar ne ko kuwa zan
bar mu hadu acan wajen neman WASIKAR JINI
ne in yaso muyi yaki dayanmu ya kashe daya.
Koda Yarina Zainur yazo a zancensa
zucinsa sai hawaye ya zubo
+Abbas Abdulkadir Hada Hada+
masa nan take ya fashe da matsanancin kuka a
wannan lokaci yana cikin kuryar dakin sane na
gidan sarkin yaki haiman kuma a sannan dare ya
raba sosai,yana cikin wannan hali ne kwatsam
yaji an turo kofar dakin nasa a firgice bisa rashin
tsammani ya dago kasan yaga wanda ya shigo
ba wani bane face sarkin yaki haiman fuskarsa
cike da alamun
tausayawa a gareshi kuma idanunsa sun ciko da
kwalla.Maimakon sarkin yaki ya budi baki yace
dashi wani abu sai kawai ya zauna a gefen gadon
nasa ya janyo shi izuwa kan kirjinsa ya
rungumoshi sannan ya shiga rarrashinsa yana
mai cewa,yakai dana kayi sani cewa ita kaddara
ta riga fata babu yadda za'ayi
wani ya iya sauya maka kaddararka nasan duk
abinda yake damunka a yanzu amma shawara
daya zan baka shawarata kuwa ba komai bane
face ka tsaya kayi tunani da nazari a bisa duk irin
hukuncin daya kamata ka yankewa kanka,lallai
kada kasa son rai dason zuciya a cikin
al'amuranka duk abinda zai cutar da kasarka da
kuma mutanenka ka gujeshi
wanda duk kasan cewa zai taimaki kasarka da
jama'arka kuwa ka rumgumeshi ka soshi,koda yin
hakan zai zamo sanadin rasa rayuwarka kasani
cewa
bana nufin ka cutar da wani naka saboda ganin
ka cimma naka burin amma fa idan nine a
matsayinka
zan iya hakura da komai da kowa nawa don kare
kasata da jama'ata saboda yin hakan shike nuni
da shugaban dazai yi adalci.
Lokacin da sarkin yaki Haiman yazo nan a
zancensa sai mamaki ya turnuke yarima zainur
kuma ya kamu da tsananin bakin ciki
har idanunsa suka ciko da kwallah hawaye ya
subuto masa ya dubeshi yace ya shugabana
yanzu
ashe duk kasan da wannan al'amari tuntuni
amma baka sanar dani ba?
Koda jin wannan batu sai shima sarki yakin
idanunsa suka ciko da kwalla yace ka gafarceni
yakai yarima hakika bazan iya sanar dakai
wannan sirri ba saboda sarki ya gargadeni akan
kada na sanar dakai din kuma ina mai tabbatar
maka da cewa duk fadin garin nan mutum hudu
ne kacal suka san wannan sirri daga sarki,sai
waziri,sai gimbiya nauwara sannan kuma
ni.Gama fadin hakan keda wuya saiga wani
hadimin sarkin yaki haiman yazo kofar dakin da
suke yayi gyaran murya,koda jin hakan sai sarkin
yaki haiman ya fito da sauri ya dubi hadimin yace
menene?
hadimin ya risina cikin girmamawa yace ya
shugabana ai sarki ne ya aiko yanzun nan yace a
gaya maka cewa lallai ka hanzarta kaje
gareshi,cikin kaduwa da mamaki
sarkin yaki ya dubi hadimin yace lafiya kuwa sarki
zai turo ayi kirana a cikin wannan tsohon daren?
Ko harin bazata aka kawo mana?Hadimin yace
a'a inda hari aka kawo da yanzu kaji an busa
kahon
yaki,dajin haka sarkin yaki bai tsaya bata wani
lokaci ba sauya ruga izuwa inda bargar dawakai
take yaje ya kwance doki da kansa ya daura
masa sirdi yahau kuma ya zabureshi da gudu ya
fice daga cikin gidan sarautar.
Al'amarin Yarima Zainur kuwa lokacin daya sarkin
yaki ya fice daga cikin gidan shima saiya fito
daga cikim gidan ya nausa izuwa cikin gari ba
tare da sanin ma inda ya dosa ba gashi dai dare
ya raba
garin tsit baka jin sautin komai face haushin
karnuka da kuma sautin iska dake
kadawa.Tsananin
bakin ciki ne yasa Yarima Zainur ya kama tafiya
a kasa da kafafunsa ba tare da sanin inda ya
dosa ba
yana tafe kamar mahaukaci sabon shiga yana
kuka,duk da cewa yarima zainur bashi da wata
shakuwa tsakaninsa da mahaifinsa saiyaji ya
kamu da tsananin bakin ciki bisa jin cewar zai
zamo
abokin gabar mahaifin nasa,haka dai zainur yaci
gaba da tafiya har ya durfafi kasuwa kai
tsaye.Kasuwar tayi tsit tamkar babu mutum daya
mai numfashi a cikinta alhalin kuwa akwai gidajen
haya a cikin kasuwar inda baki ke kwana.Gaba
daya gidajen dake cikin wannan kasuwa na
hayane kuma mafi yawansu suna da
bene.Lokacin da Yarima Zainur yazo giftawa ta
tsakiyar kasuwar sai ya jiyo sautin muryar wani
mutum acan saman bene ta cikin wata taga har
zainur ya dangota tagar sai ya dawo da baya ya
tsaya kuma ya kasa kunne domin yaji abinda
mutumin yake fada,tunda yarima zainur yazo
duniya bai taba jin sauti mai dadi wanda
kunnuwansa keji ba a yanzu ba,sauti ne kamar na
waka ko kuma karatu cikin wadansu irin kalmoni
na hikima a daraja,nan take yarima zainur yaji
wadannan kalmomi sun ratsa zuciyarsa don haka
sai yaji babu abinda yakeso sama da ganin
mutumin da wadannan kalmoni ke fita daga
bakinsa,bisa wannan
dalili ne yarima zainur ya durfafi kofar gidan da
yake jiyo sautin karatun domin ya shiga kuma ya
hau harkan saman benen,da zuwa sai yasa
hannunsa ashe kofar a bude take don haka saiya
kunna kai
ciki ba tare da shakkat komai ba.Ashe ba wani
bane yake wannan karatun face Yarima Yazid
kuma
karatun alkur'ani yakeyi da farko ya fara karatun
ne a cikin zuciyarsa amma a lokacin da shaukin
karatun ya debeshi sai ya manta da cewa a cikin
kasar kafurai yake don haka baisan yana karatun
ba a fili kuma duk da cewar muryarsa akasa take
saida ta fito waje ta cikin tagar dakin saboda
kasancewar dare ya raba.
A wannan lokaci Yarima Zayid na zaune ne akan
wani farin buzu ya tankwashe kafafunsa kuma
yana rike da littafin alkur'ani a hannunsa wanda
yake karantawa,a gefensa na dama kuma daf
dashi takobinsa ce ajiye a kas,agefen hagunsa
kuwa Ardadu ne kwance akan shimfida yana ta
fama sharar barcinsa harda minshari.Dama a can
kofar gidan su Yarima Yazid suka daure dawakan
nan nasu wanda Ardadu ya sato.
Lokacin da Yarima Zainur ya turo kofar gidan ya
shigo saida
wadannan dawakai guda biyu suka dan tsorata
sukayi haniniya.Jin haniniyar tasune yasa Yarima
Zainur ya dora hannunsa guda akan kufen
takobinsa domin a zatonsa barayi ne suka kawo
ziyarar
bazato.Koda Zainur ya shigo cikin gidan saiya
wuce kai tsaye izuwa kan matattakar benen ya
fara
hawanta domin ya isa wannan daki inda yake jiyo
sautin karatun kuma karar takun sawun same
akan matattakalar na cigaba da cika kunne amma
ko a jikinsa,saida ya taka matattakalar karshe ya
dora hannunsa akan kofar dakin da nufin ya
turata sai kawai yaji hucin saran takobi a daidai
kunnensa.Cikin bakin zafin nama Yarima Zainur
ya sunkuya takobin Yazid ta sari iska amma kafin
yayi wani yunkuri tuni Yazid ya sake kawo masa
wani saran a ciki da nufin ya tsargeshi gida
biyu,aikuwa in
badon Zainur ya daka tsalle yabar wajen ba da
saidai wani bashi ba.
Aikuwa sai takobin ta dara matattakalar suka
rikito kasa tare,karar rugujewar matattakalar
benen tasa Ardadu da sauran mutanen dake cikin
gidan suka farka daga barci a gigice.Koda
Zainur da Yazid suka fado kasa daga kan
matattakalar benen sai sukayi wuf suka mike
tsaye zumbur ba shiri.Shima Yarima Zainur ya
zaro takobinsa domin ya kare kansa,nanfa suka
kacame da azababben yaki ya zamana suna
kaiwa junansu sara da suka cikin tsanamin zafin
nama, juriya da bajinta.
WASIKAR JININ!!!
Littafi Na Uku (3)
Part B
.
Cikin tsananin zafin nama,juriya da bajinta,nanfa
suka banko kofar gidan ta karye suka fado wajen
gidan suka dada mikewa tsaye zumbur suka
cigaba da bakin artabu kowannensu yana yin
wannan yaki ne iya karfinsa da ransa da jikinsa.
A tunanin Yarima Yazid yana yaki ne da rikakken
dan fashi wanda ya saba kaiwa fatake hari,shi
kuwa Yarima Zainur sai ya dauka cewar yana
yaki ne da dan leken asiri daga wata kasar koma
wannan karatu da yaji wadansu dalamisai ne na
tsafi ake karanta su domin a cutar da birninsu.
Lokacin da aka cigaba da wannan
mamakin yaki tsakanin Yarima Zainur da Yarima
Yaizd sai mutane sukayi ta firfitowa daga cikin
gidaje
suna kallon ikon Allah amma a tsorace,adaidai
wannan lokaci ne Ardadu ma ya fito da gudu
daga cikin gidan shima ya saje a cikin yan kallo
yana baiwa idanunsa abinci.
Saida Yarima Zainur da Yarima Yazid suka shafe
sama da rabin sa'a suna bakin artabu mai
tsananin ban tsoro da tashin hankali ba tare da
dayansu ya sami nasarar koda lakutar jikin daya
ba,kwatsam sai kowannensu ya samu nasarar
dora tsinin takobinsa akan wuyan dan uwansa
amma sai suka ki cutar da juna suka tsaya suna
kallon kallo,sannan ne ma suka lura da cewa sun
tara yan kallo.Koda sarkin kasuwa ya kyallar ido
yaga ashe da yarima zainur akeyin wannan
gumurzu da kuma bako yarima yazid saiya ruga
da gudu yace yakai Yarima menene ya hada ka
fada da fatakenmu haka?
Koda jin wannan batu sai jikin zainur dana yazid
yayi sanyi,
yazid ya dubi zainur cikin biyayya a lokacin daya
sauke takobinsa daga kan wuyan zainur yace ka
gafarceni ya shugabana kayi sani cewa na yake
kane saboda ina zaton ko dan fashi ne yake
kokarin shigowa dakinmu.
Koda jin haka sai Yarima Zainur yayi murmushi
shima ya sauke takobinsa daga kan wuyan Yazid
ya dubeshi yace nima nayi zaton ko kai dan leken
asiri ne daga wata kasar mai shirin cutar da
kasar nan sakamakon

1 Comments On WASIKAR JINI 1 to 8
avatar
abdulrasheed-yusuf

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment