Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muka samu
wacce bamu taba zato ba?
Koda jin wannan tambaya sai Nauwara ta girgiza
kai tace hakika
nayi matukar farin ciki bisa wannan gagarumar
nasara da muka samu amma duk sa'adda na
tuno yadda karshen rayuwar mahaifina zata
kasance sai bakin ciki ya turnuke ni na tsani
wannan akida daya dauka ta iyayensa da
kakaninsa.A kan wane dalili bazai karya alkawarin
daya daukar musu ba ya karbi addinin musulunci
yayi watsi da tsohon addininsu na bautar gumaka
da tsafi,yanzu gashi
ma lokaci ya kure babu mamaki tuni masu sarki
Marwatu sun shiga garin sun ci shi da yaki,nasan
cewa bazasu barshi a raye ba.Koda Gimbiya
Nauwara tazo nan a zancenta saita fashe da
kuka,al'amarin daya jefa yarima Zainur da kowa
kenan cikin matukar tausayinta,zainur ya
rungumeta a kirjinsa ya shiga rarrashinta yana
mai bata baki har izuwa tsawon yan dakiku.Koda
yaga taki ta daina kukan saiya janye jikinsa daga
cikin
nata ya mike tsaye ya tafi wajen yarima Yazid ya
jashi izuwa gefe daya sannan ya dubeshi cikin
alamun tsananin damuwa yace kai kadaine zaka
iya kwantarwa da yar uwata hankalinta ta daina
wannan kuka.
Koda jin haka sai idanun yarima
Yazid suka zazzaro ya dubi zainur cikin alamun
firgici da mamaki yace yaya kai da kake dan
uwanta na jini baka kwantar mata da hankali ba
sai ni.
Zainur yayi murmushi yace akwai dalilin da yasa
na fadi hakan amma bazan gaya maka dalili ba a
yanzu sai nan gaba,inaso ka sani cewa a duniya
babu abinda Nauwara keso sama da farauta a
cikin daji,inason a yanzu take ka gaiyaceta ku tafi
farauta ku biyu rak izuwa cikin daji nasan zata ci
duk abinda kuka farauto in ba haka ba kuwa
saidai ta kwana da yunwa tana kukanta.
Yayin da Yarima Yazid yaji wannan batu sai
hankalinsa ya dugunzuma yace shin baka san
cewa a addinin
musulunci haramun ne namiji ya kadaita da
macen da bata kasance muharramarsa ba?
Zainur yace nasan da haka amma ai addinin ya
yarda da wata lalurar don kawar da wacce ta
fita,bare ma na yarda da imaninka da kuma
tsoron Allah,nasan ba zaka taba yin abinda bai
dace ba ga yar uwata.Kada ka manta cewa shi
kansa mahaifin namu cewa yayi ya danka
amanar Nauwara a hannunka,ka biya mini
wannan bukata dana nema a gareka domin ka
ceto lafiyar Nauwara in ba so kake gobe da safe
ta tashi da matsananciyar rashin lafiya ba.
Koda jin wannan batu sai jikin Yarima Yazid yayi
sanyi ya rasa abinda zaiyi kawai sai ya mike
tsaye ya shiga cikin tantinsa ya dauko KWARI DA
BAKAnsa gami da takobinsa kuma ya gyara
damarsa.Koda ya fito daga cikin tantin sai yaga
yarima Zainur tsaye a gabansa yana jiransa,kawai
sai Zainur ya sanya hannu a cikin aljihun
wandonsa ya dauko wannan taswirar ta zuwa
kogon Hajarul Aswad ya mika masa yace idan
baka tare dani sanaji kamar bazan iya kula da
wannan taswira ba,ka ajiyeta a hannunka zanfi
samun nutsuwa da kwanciyar hankali koda wani
abu zai same mu anan inason kayi iya kokarinka
ka isa kogon Hajarul Aswad ka dauko wannan
wasikar jini ka koneta wannan ne kadai abinda
zakayi ka jadda addinin ALLAH a nahiyar nan
gaba dayan.
Koda jin wannan batu sai Yazid ya dafa kafadar
Zainur yayi murmushi yace yakai Abokina inason
ka sani cewa duk abinda zan iyayi kaima
zaka iya tunda munyi imani ne da abu guda.Duk
wata gagarumar jarumtaka da zakaga nayi....
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Bakwai (7)
Part C.
.
DUK WATA GAGARUMAR JARUMTAKA DA ZAKA
GA NAYI DA TAIMAKON ALLAH NAKE YINTA
BAWAI TSAGWARON KARFIN DAMTSE NA BANE
KO IYA YAKINA.
Zainur ya maida masa da martanin
murmushin yace nasan da haka amma na so ka
sani cewa ko yan yatsun hannunka ka kalla
akwai
bambanci wani yafi wani girma to haka ma
matsayi yake gami da baiwa.
Kada ka manta cewa a baya na fafata yaki
dakai,naga irin baiwar da Allah yayi maka ta
jarumtaka da juriya da iya yaki,tabbas na gamsu
da cewa ni ba sa'anka bane a wannan fanni haka
kuma kana da ilmi mai yawa a addinin musulunci
wanda ko rabinsa bani dashi don haka kafi ni
sanin addu'oin daya kamata kayi a duk lokacin
daka fuskanci wata hadari ko wata matsala,maza
kaje ka sami yar uwata kuje kuyi wannan farauta
ku dawo kafin magriba.
Koda jin haka sai Yazid yayi murmushi ya karbi
wannan taswirar yasa a cikin aljihunsa sannan ya
nufi inda Nauwara ke zaune wacce kanta ke
sunkuye
hawaye na diga kan kyakkyawan
kumatunta,kawai sai taji an kira sunanta da
muryar da tasa zuciyarta ta buga da karfi.
Cikin kaduwa da hanzari Nauwara ta dago kai
taga yarima Yazid tsaye daf da ita amma
fuskarsa na kallon gefe.
Yazid ya bude baki yace shiga cikin tantinki ki
dauko kayan farautarki domin ki rakani cikin daji.
Koda jin wannan batu sai Nauwara taji wani irin
gagarumin farin ciki ya baibayeta.Batare da bata
wani lokaci ba Nauwara ta mike tsaye da sauri
tana mai goge hawayenta ta fada cikin tantinta
tamkar ma bata taba yin bakin ciki ba a
rayuwarta.
Cikin kankanin lokaci Nauwara ta gama shiri tsaf
ta fito daga cikin tantin suka rankaya izuwa cikin
daji Yazid nakan gaba tana biye dashi,sarkin yaki
Haiman dasu yarima Zainur suka bisu da kallo
kawai fuskokinsu cike da annuri,su kuwa ragowar
dakaru mamaki ne ya kama su bisa ganin yadda
yarima Zainur ya amincewa Yarima Yazid ya tafi
da yar uwarsa izuwa cikin wannan mugun daji su
biyu rak.
Bayan kulewar Yazid da Nauwara ne sarkin yaki
Haiman ya dubi Zainur cikin murmushi yace yakai
dana hakika yau ne na dada tabbatar da cewa
kana da basira gami da hangen nesa waishin
yaya akayi ka gane cewa akwai soyayya tsakanin
Yazid da yar uwarka Nauwara kuma menene
dalilin da yasa kake son ka kulla shakuwa a
tsakaninsu?
Sa'adda Zainur yaji wadannan tambayoyi sai yayi
murmushi gami da ajiyar zuciya a lokacin da
mahaifiyarsa tazo garesu ta tsaya ta dubi
Haiman tace ga abincinku
can a cikin tanti na gama shirya muku ko kuwa
sai kun gama tattaunawa a kan waccan
MAKAUNIYAR SOYAYYA sannan zaku zo kuci
abincin?
Koda jin haka sai duk su biyun suka dubeta cikin
matukar mamaki Haiman yace menene dalilin da
yasa kika kira soyayyar tasu da matsayin
makauniya?
Dajin haka sai tayi murmushi tace ai duk
soyayyar da ake yinta a cikin zuci a ka kasa
baiyanata a fili
makauniya ce kuma tana da hadarin gaske domin
zata iya haifar da komai,na lura da Nauwara da
Yazid tun a farkon wannan tafiya tamu ko
wannnan
su na satar kallon dan uwansa amma basa yarda
su hada idanu don haka dayansu ya gane halin
da
kowanne ke ciki.
A halin yanzu ba karamar dabara Zainur yayi ba
daya hada su tafiya tare da samun kadaita.
Idan gumu yayi gumu dole ne su baiyana gaskiya
a fili koda kuwa bada furtawa bane saidai a
aikace,wannan kadaitaka tasu zata haddasa
saboda shakuwa kuma Nauwara zata karu da
ilmin addini dana rayuwa koda kuwa rabin sa'a
kacal zasuyi tare.
Bani ba kuma ba kuba gaba dayan jama'ar dake
cikin wannan sansani basu da wata shakka akan
hada su da akayi waje guda domin an tabbatar
da cewa Yazid bazai cutar da Nauwara ba kuma
bazai bari wani abu ya cutar da ita ba,ina
fatan wannan bayani danayi muku ya gamsar da
ku ba sai kunci gaba da tattaunawa ba akan
al'amarin nasu ba,sai ku taso muje cikin tantin
kuci abinci.
Tana gama fadin hakan saita juya da sauri ta
nufi tantin cikin murna da mamaki Haiman da
Zainur suke mike tsaye suna dariya suka bita a
baya izuwa tantin.
*
Al'amarin Yarima Yazid da Gimbiya Nauwara
kuwa tunda suka nausa cikin daji yana gaba tana
biye dashi a baya suka kama farauta suna dube
dube da hange hange ko zasu ga wata dabba ko
wani tsuntsu su kai masa hari amma shiru kamar
shirwa taci shirwa.Saida suka shafe kusan rabin
sa'a a cikin wannan yanayi ba tare da dayansu
ya ce uffan ba kuma sai taga dada kutsawa yake
yi da ita cikin dajin ba tare da sanin inda ya dosa
ba,gashi dajin yana da matukar kwarjini da ban
tsoro,adaidai wannan lokaci ne Nauwara taji ta
fara gajiya kuma kishirwa ta kamata.
Nauwara ta shafa kugubnta taji babu battar ta
ruwa ashe ta mantata a can cikin tantinta,ta dubi
jikin Yazid wanda ke gaba taga shima babu battar
ruwan a jikinsa.Nan take hankalinta ya
dugunzuma bata san sa'adda ta
ruga da gudu tasha gaban Yazid tana haki tace
kai nifa na gaji kuma kishirwa ta kamani sosai
yanzu a ina zan samu ruwan sha?
Koda jin wannan tambaya sai Yazid yayi guntun
murmushi a gareta a cikin zuciyarsa yana mai
cewa ashe dai dole kanwar naki ce,na zata zaki
cigaba da dauriya ne da nuna halin ko in kula din.
Kamar Nauwara tasan zancen zucin da yakeyi
saita dubeshi a fusace tace yaya ina tambayarka
inda zan sami ruwan sha amma ka dubeni kana
murmushi sai kace gonar auduga?
Koda jin haka sai shima Yazid ya dubeta a fusace
yace yaya zaki tambayi kaza hanyar rafi ai saidai
ki tambayai agwagwa kisha labari ko kuwa kin
manta ne cewa ni bako ne a wannan nahiyar,kefa
yar gari ce a cikin dajin yakin kasarku,kece ya
kamata ki fini sanin inda za'a je a sami ruwa a
cikin wannan daji.
Koda jin wannan batu sai Nauwara ta kyalkyale
da dariya sannan tace ai zanice ta tarar da
mu,muje domin kuwa
*Abbas Abdulkadir Hada Hada*
wannan ne karo na farko dana taba shigowa cikin
wannan daji.Kai bama ni ba jama'a da yawa
hatta manyan mafarauta,jaruman da suka yarda
da kansu gami da shahararrun matsafa tsoron
wannan daji sukeyi ba don komai ba sai kawai
saboda ya makwabci dajin da kogon Hajarul
Aswad yake,fiye da shekaru arba'in baya
mafarauta da fatake ma basa yarda su iso farkon
wannan daji ma bare su iso nan ma inda
muke.Yazid ya gyada kai yace to ai shike nan
saiki daure mu cigaba da lalube har sai mun
gano inda ruwan yake.Yazid na gama fadin hakan
sai ya cigaba da tafiya abinsa cikin matukar
karfin hali Nauwara ta bishi a baya.
Saida suka shafe rabin sa'a suna tafiya basu ga
wata korama ba ko fadama,tun Nauwara nayin
tafiyat da kuzarinta har saida ta fara sassarfa
sannu a hankali ta kama yin tangadi kamar wacce
tasha giya ta bugu a lokacin da labbanta suka
bushe sukayi fari fat saboda tsabar kishirwa,shi
kansa yarima Yazid din ba karamar juriya yayi ba
daya cigaba da tafiya a hakan amma shima ji
yayi kamrar ya zauna ya huta domin yaki yake ta
faman yi tamkar ya dade
yana gudu,duk bayan yan dakiku saiya juyo
bayansa ya dubi Nauwara da zarar yaga halin da
take ciki sai yaji ya kamu da matukar tausayinta.
Suna cikin wannan hali ne yaji wuf karar faduwar
wani abu a bayansa,cikin firgici da dimauta ya
waigo bayan nasa da sauri ai kuwa sai yaga ashe
Nauwara ce ta kife kasa da rub da ciki.
A guje ya karaso gareta bai san sa'adda ya kama
kafadunta ba ya juya da fuskarta kawai sai ganin
idanunta a wurkile alamar cewa suma tayi,cikin
bakin zafin nama da azababben gudu izuwa cikin
dajin cikin dimautacewa wani lokacin idan yayi
gabas baiga ruwa ba sai ya juya yayi yamma
sannan ya dawo kudu da arewa da dai yaga babu
ruwa a kusa kuma babu alamunsa sai yapara
kiran sunayen Allah tsarkaka yanayi masa kirari
da neman agajinsa.Allah maji rokon bawa fara yin
wannan addua'a ta Yazid keda wuya saiya hango
wata doguwar fadama wacce ruwanta daga kan
saman wani dutse yake kwaranya cikin tsananin
farin ciki Yazid ya rugwa da gudu izuwa inda
fadamar take yana sabe da Nauwara a kafadarsa
da zuwansa bakin fadamar bai tsaya bata wani
lokaci ba saiya daka tsalle ya fada cikin fadamar
gaba daya.
Ai kuwa ruwa na shiga bakin Nauwara da jikinta
saita farfado tana mai jan dogon numfashi
amma sakamakon ruwan daya shiga cikinta da
yawa sai numfashinta ya sake daukewa.
A firgice Yazid ya fito da ita daga cikin fadamar
ya shimfideta a kasa bakin koramar nanfa yayi
arba da irin kyakkyawar surar jikin da Allah ya
bata ya kai hannu da niyar danna cikinta kasa
domin ruwa
yafito amma saiya kasa saboda wannan ne karo
na farko a rayuwarsa dazai taba jikin macen data
kasance ba muharramarsa ba,Nauwara zata iya
rasa rayuwarta sai yayi sauri ya shiga danna
cikinta.
Ai kuwa sai ga ruwa yana fitowa daga cikin bakin
nata har ruwan ya gama fitowa Nauwara bata
farfado ba kuma duk jikinta a sandare yake kamar
gawa.Al'amarin daya dugunzuma hankalin Yazid
kenan ya kara dimaucewa fiye da ko yaushe bai
san sa'adda ya matse hancinta ba da hannunsa
guda sannan yasa bakinsa a cikin nata ya hura
mata iska.
Faruwar hakan keda wuya sai numfashin
Nauwara ya dawo ta mike zaune zumbur a firgice
ta kama kalle kalle ko dataga yarima Yazid
tsugune a gabanta kuma taji jikinta a jike sharkaf
da ruwa saita dubeshi cikin alamun tsananin
kunya da damuwa tace tsakaninka da Allah
menene ya faru
a gare ni?
Na rokeka bisa girman Allah ka zaiyane mini
iyakar gaskiya kada ka boye mini komai.
Koda jin wannan batu sai zuciyar Yarima Yazid ta
buga da karfi saboda ta daureshi da jijiyoyin
jikinsa.
A iya rayuwar Yazid bisa saninsa bai taba fadin
karya ba bare kuma yanzu gashi an hadashi da
girman
Allah ance ya fadi duk abinda ya faru bisa
gaskiya ba tare daya boye wani abu ba.
Cikin hanzari Yazid ya juyawa Nauwara baya
yace saboda me kike son kiji abinda ya faru
gareki,kawai ki godewa Allah tunda dai kin tsira
da rayuwarki.Nauwara ta gyada kai tace ai
dukkan mai rai mamaci ne don haka bana tsoron
mutuwa,fatana kawai Allah yasa na
sami shahada a cikin wannan tafarki da muke
kansa,saboda me baka son ka bani labarin duk
abinda ya faru,kana jin kunya tane ko kuwa kayi
wani abune ba daidai ba?
Koda jin wadannan tambayoyi guda biyu sai ran
Yarima Yazid ya baci ya dubi Nauwara cikin
alamun fishi yace ai ita kunya alamace ta imani
haka kuma ni dan adam ne
ajizi don haka zan iyayin ba daidai ba amma zan
faiyace miki duk abinda ya faru bisa gaskiya
kamar yadda kika bukata domin ki sami nutsuwa
a cikin ranki kuma ki cire dukkan zargi ko
kokwanto a
cikin ranki da zuciyarki.
Batare da boye komai ba Yazid ya kwashe labarin
duk abinda ya faru ya zaiyanewa Nauwara tun
daga lokacin da kishirwa taci karfinta ta yanke
jiki ta fadi kasa sumammiya kawo izuwa sa'adda
ya tsomata a cikin wannan korama ta sake suma
ya fito da ita ya ceto rayuwarta da kyar.
Koda Nauwara ta gama jin wannan labari saita
kyalkyale da dariya.Al'amarin dayayi matukar
baiwa Yazid mamaki kenan kuma ya firgita ainun
ya fara tunanin ko ta zautu ne har saida yaga
tayi shiru ga barin dariyar ta dubeshi cikin
nutsuwa sannan hankalinsa ya
kwanta.
Tsawon yan dakiku suna kallon juna
dayansu baice uffan ba sai Nauwara tayi gyaran
murya tace saboda me ka karya dokar Allah ka
taba jikin macen daba muharramarka ba,ka sani
cewa ni banda mahaifina da dan'uwana Zainur
kaine namijin farko daya fara taba jikina gashi ma
wai har bakinka ka...(uhmm Kunya).Nauwara ta
kasa karasa bayaninta a lokacin da Yazid ya tari
numfashinta yana mai daka mata tsawa yace
mahaifinki ya bayar dake amana a gareni kuma
na dauki
*Abbas Abdulkadir Hada Hada*
alkawarin kula dake da tsare rayuwarki da
mutunci,idan kece zaki ki cika wannan alkawari?
Nauwara tayi murmushi tace zan yarda da
wannan hujja taka amma ba itace kadai ba akwai
wata.
Ka gaya mini gaskiya bisa tsoron Allah wanda
yana jinmu kuma yana ganinmu,shin a cikin
zuciyarka bakajin komai dangane dani.
Koda jin wannan tambaya sai Yarima Yazid ya
murtuke fuskarsa ya mike tsaye yana mai juya
mata baya yace tashi mu koma can sansaninmu
mu hakura da batun yin farauta tunda rana ta
fadi magriba na daf dayi,yana gama fadin hakan
saiya cigaba da tafiya.Nauwara ta mike tsaye
zumbur ta ruga tasha gabansa ta tsayar dashi
tace bazan koma sansaninmu ba face ka bani
amsar tambayar da nayi maka.
Yazid yace dole ne na koma tare dake tunda
gadinki aka bani.
To idan naki binka zaka kamani ne da karfin tsiya
ka dora ni a kafadarka kamar yadda kayi mini
sa'adda na suma,idan a wancan lokaci larura ce
tasa ka taba jikina wannan lokacin kuma fa?
Yazid yace wata lalurar ce tasa na aikata
hakan,Kafin Yazid ya gama rufe bakinsa tuni
Nauwara ta juya da baya cikin shammace ta
falfala da gudun tsiya a cikin dajin,ai kuwa sai
Yazid ya bita da sauri a guje yana kwala mata
kira tamkar tseran gudu aka kasa tsakanin
barawo da mai kaya.
Karfin gudun Nauwara wanda har dan tashi sama
yakeyi tana shallake kananun duwatsu wanda ke
kasa da bishiyoyi.
Kash rashin sani yafi dare duhu,inda
Nauwara tasan cewa sunzo karshen dajin da suke
ciki zasu afka cikin dajin kogon Hajarul Aswad
yake ne da batayi gangancin yin wannan mugun
wasa ba ga yarima Yazid.
Nauwara na cikin falfala azababben gudu ne
kawai taji ta fanjam ta fada cikin wani kogin
kankara ga tsananin sanyi a cikinsa,domin tana
fadawa ta kama karkarwar dari tururin sanyi ya
fara fita daga cikin bakinta.
Nan take ta firgita ta taso iziwa saman kogin ta
fara iyo domin ta fito daga cikin a lokacin da
Yazid ya rugo bakin kogin da gudu.Saura kiris
Nauwara ta iso bakin gabar kogin sai kawai Yazid
ya hango wata murtukekiyar jela ta wata halittar
ruwa ta kanannade jikin Nauwara duka ta dagata
sama zata
makata izuwa kasan kogin.
Daga inda Yazid yake ya daka uban tsalle sama
yana mai kwala kabbara sai gashi a sama a guje
tamkar daga cikin baka aka harboshi.
Kafin jelar dabbar ta maka Nauwara izuwa cikin
ruwan tuni yasa takobinsa ya sare kasan jelar
dabbar kuma ya cafo kugun Nauwara da hannu
daya suka sake fadowa kasa cikin kogin.
Fadawarsu kasan ruwan keda wuya sai sukaga
abin al'ajabin daya daure musu kai.Dabbar da
Yazid ya sarewa jela ce ta taso sama daga
karkashin kogin ta baiyana gaba dayan surar
jikinta,ashe jela daya rak Yazid ya sare daga cikin
jelolinta guda arba'in da daya.
Ita dai wannan halitta siffar macijiya gareta
amma kanta irin na mage ne saidai katone
rafkeke mai girman gaske,bakinta wangameme ne
tamkar an fafe dirom.
Gaba daya jikinta daga kasan wuyanta zuwa
jelarta,hannayenta na hagu da dama guda shida
shida ne kuma yatsunta irin na birirai ne cike da
zakwa zakwan farata,idanunta manya manya
kuma jajaye ababan tsoro,kaurin jikinta kuwa
yakai na karamar bishiyar kuka.
Koda Yarima Yazid da Nauwara sukayi arba da
wannan mummunar halitta a lokacin data
wangame bakinta tayi wata irin kara mai karfin
gaske wacce ta haddasa girgizar kasa a cikin
dajin gaba dayansa sai Yazid da Nauwara
suka firgita ainun hatta su yarima Zainur dake
can wancan daji saida suka jiyo wannan kara
suka razana.
A daidai wannan lokaci ne Su Yarima Zainur sun
fara yin alwala domin su gabatar da sallar
magriba gashi har a sannan Yazid da Nauwara
basu dawo ba.Koda sarkin yaki Haiman da Zainur
da sauran dakaru suka jiyo wannan
gagarumar kara ta dabbar da baza'a iya tantance
taba sai kowa ya razana ainun amma saboda
Sallah za'ayi sai Haiman yace a bari sai an idar
da sallar sannan a tafi nemansu gimbiya
Nauwara.
.
ME ZAI FARU TSAKANIN YARIMA YAZID DA KUMA
GIMBIYA NAUWARA?
SHIN SU SARKIN YAKI HAIMAN ZASU ZO HAR SU
TAIMAKA MUSU?
INA LABARIN SU WAZIRI RIDWAN DA SARKI
MARWATU?
SHIN YARIMA YAZID,YARIMA ZAINUR DA SARKIN
YAKI HAIMAN ZASU IYA CIN NASARAR DAUKO
WASIKAR JINI?
TSAKANIN SU DA WAZIRI RIDWAN SU WAYE
ZASU SAMU NASARA?
Duk mai son jin wadannan amsoshi ya nemi
Littafi na takwas (8) a kasuwa wanda shi zai
zamo na karshe ,
inkuma naga masu so sunada yawa kamar 200
comment 100 like zan nacigaba da post muku
inkuma kasa da hakane saidai kunema a kasuwa.
END OF BOOK 7.
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Takwas (8)
Part A.
.
NAN TAKE KUWA HAIMAN YA SHIGE GABA YAYI
MUSU LIMANCI,BAYAN AN IDAR DA SALLAR ANYI
ADDU'A SAI KOWA YA KIMTSA SUKA DEBI
MAKAMANSU DA DUKKAN KAYANSU SUKAYI
GABA.
Tafiyar su yarima Zainur keda wuya bayan cikar
rabin sa'a daidai saiga rundunar su sarki
Marwatu sun baiyna,dukkaninsu a cikin shigar
bakaken tufafi kuma a kasa suke babu mai doki
guda daya,babu sarki Marwatu da Waziri Ridwan
a cikin wadannan zuga sakamakon dole ne su
kwanta suyi jinyar raunikan jikinsu.
Daga nesa suka fara sanda harma a cikin rub da
ciki suke tafiya suna jan jikinsu sai kace macizai.
Sa'adda suka hango sansanin sukaga fitilo a
kunne kuma ga
dakarun tsaro a tsaitsaye sun yiwa sansanin
kawanya,abinda basu sani ba shine babu kowa a
cikin sansanin kuma dakarun da suke hangowa a
tsaitsaye duk ba masu rai bane mutum mutumi
ne dukkaninsu.
Koda ya rage saura baifi taku ashirin ba
tsakakanin dakarun sumamen da sansanin sai
kawai suka fara harbo ruwan kibiyoyin wuta,nan
da nan tantunan da aka kafa suka kama cin
wuta,suma mutum mutumin dake tsaye suka
rinka faduwa kasa suna ci da wuta,cikin kankanin
lokaci komai dake cikin sansanin ya kone kurmus.
Duk wannan abu dake faruwa dakarun sumamen
na kwance a kasa cikin lambo jira suke kawai suji
dakarunsu Zainur sun rugo daga cikin wutar
sannan suma su taso su afka musu,amma sai
sukaji shiru abin daya kara basu mamaki ma
shine tunda suka harbo kibiyoyin wuta a cikin
sansanin kawo izuwa sa'adda komai ya kone
basu jiyo ihun koda mutum daya ba.
Koda fuskantar hakan sai shugaban dakarun ya
mike tsaye zumbur ya kura idanunsa da kyau
izuwa cikin sansanin take ya gane cewa lallai
makircin yaki aka nuna musu
saboda ko mutum daya mai rai babu a cikin
sansanin mutum mutumi ne kawai wadanda basu
haura guda ashirin da wani abu ba kwance a
kasa suna ci da wuta.Koda ganin haka sai
shugaban
dakarun sumamen ya kwarara uban ihu cikin
tsananin bakin ciki.Al'amarin da yasa gaba dayan
yaran nasa suka mike tsaye kenan suka dubi
cikin sansanin.
Koda suka fahimci abinda ke faruwa sai suma
ransu ya baci nan take shugaban dakarun ya
fiddo wani dan karamin madubin tsafi daga cikin
aljihu ya shafe shi sai ga fuskar waziri Ridwan ta
baiyana,kafin shugaban dakarun sumamen ya
bude baki yace wani abu tuni Ridwan ya tari
numfashinsa yana mai cewa kai shashashan
banza,abokan gaba sun yaudare ku ne kamar
yadda suka yaudare mu da farko,kai wane irin
dakiki ne ashe ban gargadeka ba akan kada ku
kai
hari sai kun tabbatar da cewa abokan gabar na
nan a cikin sansaninsu.
To ka sani cewa tuni sun matsa
gaba sun kafa wani sansanin kuma a yanzu haka
wasu daga cikinsu sun bar sansanin sun tafi
neman wannan bakon da gimbiya Nauwara
wadanda su tuni sunyi nisa a cikin daji babu
mamaki ma sun fada cikin daji da kogon Hajarul
Aswad yake.
Maza ku karaso sabon sansanin nasu ku kashe
duk wani abu mai rai dake cikinsa karku bar ko
kaza guda daya da rai.Ni da sarki Marwatu da
sauran dakaru zamu riske ku a sansanin nan da
zuwa gobe da safe.
Koda gama fadin haka sai hoton fuskar waziri
Ridwan ya bace daga kan madubin.cikin gaggawa
shugaban dakarun sumamen da yaransa kimanin
su dubu arba'in
suka nausa da gudu izuwa cikin daji.
Wani irin gudu sukeyi na ban al'ajabi saboda
karfin sihirin tsafinsu domin har tashi sama suke
suna dira a kan kololuwar dogayen bishiyoyi suna
karawa gaba.
*
A can cikin kogon kankara kuwa lokacin da
yarima Yazid da Gimbiya Nauwara sukayi arba da
wannan katuwar mummunar halitta mai siffar
macijiya dauke da kan mage,ga hannaye guda
goma sha biyu gami da jelar guda arba'in da
gutsiren daya wacce Yazid ya sare rabinta sai
suka firgita ainun.
Ba shiri Yazid ya tunkude Nauwara
bayansa ya daka mata tsawa yana mai bata
umarnin ta cigaba da iyo ta fice daga cikin kogin
kankarar ta isa can daya gabar tasa.
Koda halittar ta fahimci hakan sai ta tasam musu
su biyun tana jeho musu hannayenta da jelunanta
tana kawo musu mugun duka gami da sara da
suka da kaifin faratan hannayenta.
A karom farkon data kawowa Nauwara sara da
farcen hannunta guda Nauwara ta yunkura cikin
zafin nama ta zare takobinta ta kare saran ai
kuwa sai kafin farcen nata ya raba takobin
Nauwara gida biyu,kafin Nauwara tayi wani
yunkuri tuni halittar ta gabza mata wawan naushi
da jelarta guda a fuska.
Saboda Karfin Naushin saida Nauwara tayi sama
kuma tayi katantanwa sau uku a saman sa'adda
jini yayi feshi daga bakinta ta fado kasa cikin
kogin kankara a sume kuma ta fara lumewa
izuwa karkashin kogin.
Koda Yazid yaga abinda ya faru ga Nauwara sai
ya fusata ainun bai san sa'adda ya kwala
kabbara ba ya daka tsalle sama daga cikin kogin
tamkar daga cikin baka aka cillo shi ya
dankarawa halittar wawan sara a tsakiyar
kanta.Nan take takobin tasa ta rabe gida biyu
amma saboda karfin saran nasa saida halittar
tayi wani uban ruri sakamakon tsananin zafi da
zugin
da taji ta fadi da baya cikin kogin tsundum
tamkar daga sama aka jefo giwa.
kafin halittar ta taso saman ruwan tuni Yazid yayi
nutso kasa ya dauko
Nauwara yayi ninkaya izuwa bakin gaba ya
shimfideta a kasa amma ko alamar numfashi
babu a tare da ita.
Al'amarin dayayi matukar dugunzuma hankalinsa
kenan ya fara kokarin dawo da numfashinta yana
mai danna kirjinta.
Kawai sai yaji tasowar wannan halittar daga
karkashin kogin.
A fusace Yazid ya juyo ya kura mata
idanu.Halittar ta fito daga cikin ruwan tana tafiya
sululu a kasa tamkar macijiya kuma ta tunkaro
inda yake.Komai dakewar mutum gami da karfin
zuciyarsa idan yaga wannan halittar yayin
fitowarta daga cikin wannan
kogi tana mai baiyana gaba dayan surarta dole
ne ya
*Abbas Abdulkadir hada hada*
firgita.Cikin zafin nama Yazid ya mike tsaye
zumbur ya shafa ko ina a jikinsa yaji babu
makami ko guda daya kawai saiya dunkule
hannayensa yana mai gyara tsayuwarsa sannan
ya shiga
karanta wadansu addu'o'i na musamman a cikin
zuciyarsa a lokacin da halittar ta cigaba da
durfafo shi.
Koda ya fuskanci cewa halittar so take ta kawo
musu cafka su biyun har da Nauwara wacce ke
kwance tamkar gawa sai ya rugo da gudu izuwa
kan halittar ya tareta suka ruguntsume da
azababben yaki ya zamana cewa suna kaiwa
junansu naushi da bugu,ita halittar tana kai masa
duka da dukkan jelunanta amma sai gashi yana
iya kade hannayen nata da jelunan nata cikin
wani irin bakin zafin nama na gaban kwatance
kuma yana mai da mata martani.
Duk sa'adda ya sami nasarar naushin halittar ko
ina a jikinta sai tayi baya a sama tamkar da
majaujawa aka janyeta saboda
karfin naushin nasa amma saboda naci irin nata
sai kaga ta kuma tasowa sun cigaba da
artabun.Kokarin halittar kawai shine ta samu ta
kanannadeshi da jelarta guda amma ta kasa,shi
kuma kokarin da yake shine ya samu damar
naushinta a fuska ko a kanta saboda ya fuskanci
cewa nan ne lagonta yake,domin sa'adda ya
dankara mata saran nan a tsakiyar kanta saida
idanunta suka wurkile tayi rabin suma ta lume
kasa
a cikin kogon kankarar amma saboda bakin naci
tana farfadowa sai ta taso sama suka cigaba da
artabu.
Saida Yazid da wannan halitta suka shafe kusan
rabin sa'a suna kwamarzuwa tana bugunsa yana
bugunta ya zamana cewa kowannensu naji a
jikinsa amma an rasa wanda zai sami nasara a
cikinsu.
Ita dai halittar tana ta zane masa sassan jikinsa
da jelunanta amma ta kasa sukarsa ko yankansa
da faratan hannayenta,shi kuma ya sami nasara
yana ta gabza mata naushi a fuskarta har idonta
guda ya kumbura subtum yana zubar da
jini,kunnenta guda ya doshe ta daina ji dashi,ko
ina a fuskar tata ya kumbura yayi luhu luhu gashi
dai
ta

1 Comments On WASIKAR JINI 1 to 8
avatar
abdulrasheed-yusuf

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment