Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ture plate din daga gabansa... ya tura mata shi yace..
Dandana kiji ma kanki mana!wannan ai muguntar banza ce..

Surayya hannu na rawa ta dauki tsokali ta soma dandana abincin..
   Da sauri ta zubar dana bakinta..tace..na shiga uku!
Meye haka?wallahi ba haka abincina yake ba..ta fadi kamar zata rusa kuka..
  Jalal yaja tsaki hade da mikewa cike da haushi ya fice daga sashen abunsa..

************
"Juwairiya gaba daya ta kasa tsaye ta kasa tzaune,tunanin halin da yarima yake ciki kawai takeyi,ta kagu duhu ya fara taje ta same sa a inda yace su hadu..

laure ce ta kawo mata kwanon abincinta da bataci ba.
kewai ban gane miki ba?tunda kika dawo kike a nan zaune kin buga uban tagumi sai kace wacce ta ka'yar da uwar miji..lafiya ?

Juwairiya ta girgirza kai tace,babu komai goggo laure amma ni na koshi da wannan abincin ki koma dashi..
Laure ta ajiye kwanon hannunta,nasan dai bakici komai ba dan haka ki ajiye zuwa anjima idan kin gama muraja'ar,tana gama fadar haka ta fice..
Juwairiya ta mike itama tana kallon jikinta,a haka zataje wajen yariman?taji zuciyarta ta fada ..
Wasu kayanta masu dan haske ta canza sannan ta lallaba tayi waje da gudu..

**************
"Tunda ta fito Gaba daya tunani takeyi,Allah dai yasa babu wani abunda ya faru da shi..

    Tana isa wajen ta samu wani dutse ta zaune akai tana buga uban tagumi..
Daga kai tayi ta kalli sama,garin yayi duhu amma hasken taurari ya kayatar da daren..

   Ta dade a wajen zaune,zuciyarta na gargadinta ko dai yarima bazai samu zuwa bane?wata kilan ma ya manta da haduwar tasu a nan..
    Ta mike a sanyaye, dama mai take tunani wacece ita da yarima zai zo ya same ta,wata zuciyar tace mata,toh ai shine ya bukaci ku hadun?
Mtsww....(whatever )

***************
"Koda ya fito daga sashen sa da hamza sukaci karo a hanya..
Hamza ya bishi da kallon tuhuma yace..
Yaya sai ina ne haka da daren nan?gashi babu wani bafade a tare dakai..
Jalal yadan dafa kafadarsa,hamza kenan kasan fa ko sarki yana son sirri..shiyasa ban gayyaci kowa a fitar tawa ba..

  hamza ya mishi kallon rashin fahimta..
Jalal ya murmusa..
Hamza..ya kwashe da dariya yana cewa ooooh sai yanzu na gane ai yaya,amma kasan dai duk inda zaka wuce a masarautar nan indai a haka kake... (ya nuna shigar alfarmar dake jikin yarima) to dole ne mutane su shaida ka.. kaga ba wani batun sirri kenan...

Jalal ya jinjina kai ganin lkcn da dan sauran haske ko ina zai wuce sai an lura dashi..

Hamza yace,kana son taimako na?
Jalal yace,wane irin taimako zakayi min kanina?
Hamza yace duk da bansan ina ne wajen sirrin naka ba amma ina tunanin da ka batar da kama zai fi..

Jalal yadan kwabe fuska,ni da masarauta ta ina matsayin sarki sai na batar kamanni na dan na samu sirri..
Hamza yayi dariya,ka yarda dani yaya..
Jalal ya danyi shiru,baya son kowa yasan inda zayaje,kuma da gskyr hamza, idan ya fita a haka akwai yan gulma da kai rohoto..
Na amince...
Hamza yace toh muje..
Sashen hamza suka shiga..
Hamza ya saka wani bawansa da ya kawo masa kaya irin na low class dinnan,ya mikawa jalal gashi ka saka..
Jalal ya yatsine fuska ni zan saka wannan?(ya yastine fuska yana kallon kayan dake hannun hamza)

Hamza ya zauna a gefensa,haba yaya ai a hakane kawai zaka iya fita cikin masarautar nan babu wanda zai gane ka..
Jalal ya jinjina kai kafin yadan ja tsaki ya amsa yaje ya saka..
Yana fitowa hamza ya kwashe da dariya..
Jalal ya harare shi..kafin ya fice abunsa cikin sauri yana jin haushin tsaida shi da hamza yayi..

*******************
"Juwairiya kuwa har ta fara tafiya abunta dan komawa rumfar bayi sbd dai ta cire rai da zuwan nasa...

   Jalal kuwa na can sai buga sauri yakeyi..(duk inda wuce se yaga kamar za'a gane shi,amma ga mamakinsa ko kallo bai ishe kowa ba).

Yana karasowa wajen ya hango ta tana tafiya zata bar wajen..
Karasawa yayi zuwa bayanta yace..

"Ji mana yan mata...."

    Juwairiya ta juyo da sauri tana kare masa kallo daga sama har kasansa..
     Waro ido tayi cikin mamaki tace..
Mai martaba kai ne haka?

Jalal ya samu kansa da murmusawa..
  Juwairiya tayi kasake tana kallonsa..

Yace mu karasa can..
da ina zaki tafi?
Juwairiya tayi kasa da kai tace..
na zata ai ka fasa zuwa ne..
   Jalal ya samu waje ya zauna..
juwairiya ta kura masa ido tana godewa Allah da babu abunda ya same sa..

   "se Ki zauna idan kin gama tunanin.."

juwairiya tayi dan firgigit..ta nemi waje itama ta zauna,gaba daya dadi ya lullube ta,wai ita juwairiya ce zaune da sarki guda a waje daya kuma a kadaice...
   Jalal kallonta kawai yakeyi..
Shiru har kusan minti talati bai ce komai ba..

juwairiya ta dago ta kallesa,gani tayi ita yake kallo,tace,mai martaba kace na same a nan..?
Jalal ya gyada kai...jitai yace..

Ina so na sake baki wani umarnin ne...
Juwairiya tace ina jinka..ranka shi dade..
Jalal ya gyara zamansa..kafin yace..

Akan tambayar da kikayi min ne jiya na son sanin dalilina na kyautata miki da nakeyi..
Juwairiya taji gabanta ya hau faduwa..
Yaci gaba..
A gaskiya ni kaina ban san dalili ba..
Amma inaso kiyi min wata alfarma..ko nace umarni nake baki,ki zauna tare dani (stay by mu side) har sai na samo amsar tambayar,dan ni kaina tana ci min tuwo a kwarya..

    Juwairiya taja lumfashi ,na zauna tare da shi?kamar ya kenan?

Jalal kamar yasan me take tunani..
Yace,ki zauna a sashena kiyi min hidima har lkcn da zan samu amsar..nake nufi..
Juwairiya ta gyada kai,ai ni dama bani da wani ikon barin sashenka mai martaba dan haka kada mai martaba ya damu..
  Jalal ya saki murmushi me kayatarwa sannan ya kalli jikinsa..yace..
Ban taba saka kaya irin wannan ba..
Juwairiya ta kalleshi itama tana dariya kasa kasa sai kace ba yarima dan gwalisa ba..yasha wasu tazarce..

   Jalal ya kura mata ido,
"ni kikeyi wa dariya?
Baki san duk sbd ke bane... !
Juwairiya ta waro ido...sbd ni?ta nuna kanta..
Jalal yaji haushin furucin da yayi..
Ya dauke kai kawai yana kallon taurarin dake sama..
Juwairiya ta mike tace..
Ni zan taf...
Mgnr ce ta yanke mata jin kukan da cikin yarima yayi..kululululu...

   Da sauri ta kallo shi..
tace ranka shi dade yunwa kake ji ne?
Jalal ya runtse ido, dan rabonshi da abinci tun da safe.. wai duk dan sbd wata al'adar masarauta..mtsww..
juwairiya da mamki tace a zuciyarta ,na zata ai se yafi kowa cika cikinsa a yau?,duk wadannan kayan dadi?ko bai ma ci bane?saboda yazo wajenta?inaaa ah ah ! Ai bata da wannan mahimmanci a wajen sa..

Jalal ne ya mike bai ce mata komai ba sai kawai ya shiga jan hannunta..
  Juwairiya a tsorace tace ina zamuje?ranka shi dade?

Yarima yaja burki kafin ya sakar mata hannun yace..
Rakiya zakiyi min,
kuma umarni ne nake baki..
Juwairiya tayi kasa da kai kafin tace,toh muje..
  Jalal ya juya cikin kasaita suka fara tafiya....



Muje zuwa...👇
TEAM RUMFAR BAYI

  
[9/18, 3:22 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 24
Wattpad @afreey101




I Pherty dedicate dis chapter to Zauren Biebie Isa Group, Sameena Aliyu Novel Group and Pherty Novel Group, Afrah na godiya❤



*********************

"Tafiya kawai sukeyi amma juwairiya sai ta tsinci kanta a cikin farin ciki sosai..
    Yarima ne zata yiwa rakiya?
Uhmm lallai ta samu wuri kam..
Tuntube ne tayi hakan yasa ta dawo hankalinta..

Sai Can ta hango sa yayi mata dan nisa..
kuma sai ta taga ya nufi hanyar fita daga masarautar ..
  Ai da gudun ta ta karasa gefensa tana fadin..
Allah ya kara maka yawan rai,dama wajen masarautar zamuje ne?naga dare yayi ne?

   Jalal ya tsaya tsak yana kallonta,kafin yace da ita kai tsaye..
tsoro kike ji?
Ta dago ta kalleshi itama..
Ta girgirza masa kai..
Yace,baki yarda dani bane?
Ta kafe shi da ido,kafin ta sake girgiza masa kanta..
Ya jinjinar da kai kawai yayi gaba..
Itama tabi shi a baya da saurinta...

"Sun sha uwar tafiya me nisa kafin suka kawo babban gate din fita....
Fadawa ne sun kai biyar dake gadin wajen..

"Tsayar dasu akayi..
"Kai sai ina!!
Jalal da juwairiya suka ja suka tsaya..
Fadawan suka sha gabansu..
Baku ji me akace muku bane? sai ina?
Jalal har ya dago a fusace dan yayi musu rashin mutumci sai kuma ya tuna da shifa a yanzu ba sarkin su bane....

Sunne kai ya shiga yi dan baya so su gano shi..
Juwairiya ta lura dashi dan haka tayi saurin dawowa gabansa dan ta kare shi...
kafin nan ta hada duk karfinta tace..
  'Umarni ne aka bamu daga wajen fulani,
masu fataucin kayane suka shigo kasar shine aka tura mu dan amso sakon ta sbd juyawa zasuyi da asuba..
   "Fadawan suka shiga gyada kai cike da gamsuwa kafin nan suka bude musu gate din sukace,kuyi hanzarin dawowa...
Juwairiya tayi musu godiya kafin nan suka fice..

"Cikin gari suka shiga,
juwairiya dai bin sa kawai takeyi tana mamakin abunda ya kawo su har cikin gari da daddaren nan..

  A gaban wani me gasasshen kifi da dankalin hausa ya ja ya tsaya..
Juwairiya ta kalleshi,uhm yunwar dai yaji kenan..

Gani tayi yayi tsaye kawai bai ce komai ba sai faman kallon kifin yakeyi..
  Kusa dashi ta dan matsa tace,ranka shi dade ba siya zakayi bane?
  Ya gyada mata kai..
Murmushi tayi dan ta fahimci cinikin ne bai ma san yarda akeyi yinshi ba.
(She don't blame him tunda dai komai yake so yana dashi a ajiye ba sai ya fita ya nema ba)

   "Me siyar da kifin ta kalla,malam a bamu kifi biyu da dankalin biyu shima..
Jalal dai kallonta kawai yakeyi,gani ma yayi ta shiga zabar musu manya mayan kifin tana fadawa me siyar da kifin su take so..

Me kifi ya saka musu acikin takarda..
juwairiya ta amsa ta mikawa jalal..
Ya amsa yana kallonta..
Tace mai martaba kudin sa fa?.
Ya saka hannu cikin aljihun sa yaji wayam..

Runtse ido yayi dan sai yanzu ya tuna da cewa ba kayan sa bane a jikinsa..
Juwairiya ta waro ido tana kasa da murya tace..
Badai baka fito da kudin ba?
Jalal ya gyada mata kai yana cije lebensa..
Juwairiya ta dafe goshi tace, yanzu ya zamuyi kenan?

Jalal ya kalli zobunan dake hannunsa a jere ya ciro daya daga ciki ya mika mata..
Ki biya shi da wannan dan na tabbata kudinsa kawai ze iya siyen daya wajen nan sau biyar..

  Juwairiya ta saki baki tana kallonsa..
Jalal Ya juya da kansa ya mikawa mutumin zoben sannan ya karasa wajen wani kututturen itace ya zauna..
Juwairiya ta juya wajen me siyar da kifin tace masa..

Malam Ka ajiye min zoben can gobe zan kawo maka kudinka na amshe shi..
Me kifi ya daure fuska a take.. dan shi kam har ya hau murna yayi kudi a dare daya..
Cikin haushi yace..Toh dai idan baki zo da wuri ba ki sani siyar dashi zanyi..
Juwairiya tace zan ma zo din ka ajiye min...

"Tsayawa tayi tana kallon yarda yarima ke cin kifin...cike da yanga yake tsakurar shi..
Baki ta tabe,ji abunda aka fito siya tunda masarauta amma kalla yarda yake cin sa..

  Jalal ya dago yace,magana kike?
A take ta daburce dan a tunanin ta acikin zuciyarta ne tayi mgnr..ni ni bance komai ba ranka shi dade..

Jalal ya nuna mata kusa dashi yace zauna..
Ta zauna babu gardama..
Takardar kifin ya ajiye a kan cinyar ta yace..
   Ciyar dani...
Ta waro ido..
Shima din yayi yarda tayi..
Wato ya waro idon shima yace..
Na ga ai kin fi ni sanin yarda ake cin sa ko?

Juwairiya tayi wiki wiki da ido..
Baki ya bude yana mata nuni da ido akan ta fara aikinta..
Juwairiya ta sauke lumfashi kafin ta saka hannu ta ciro tsokar kifi ta cire kayoyin sannan ta hada da dankalin ta kai bakinsa ta tura..
Ware ido yayi ganin ta cika masa bakinsa tab..

juwairiya tace,ka cinye ranka shi dade yafi dadi a haka,ta dage masa girar ta daya..
Jalal ya fara ci yana lumshe ido..
A haka tayi ta basa har ya daga hannu yace ya koshi..

Tana shirin cire hannunta daga cikin kifin yace..
Kema kici..
Ta girgirza kai,duk da itama din tana dan jin yunwar..
Jalal ya daure fuska..
Umarni ne..!
Ta gyada kai sannan ta fara ci itama,ya tsare ta da ido..

"Sai cikin dare sosai suka dawo cikin masarautar..
   Juwairiya taga yayi hanyar rumfar bayi..
Da sauri tasha gabansa tace..
Ranka shi dade ai dare yayi sosai kawai ka koma sashen ka..

Jalal ya kura mata ido..kafin yace..
Yaushe kika zama bai bani shawara ?
Juwairiya ta matse bakinta..
Yace wuce muje..
Ta gyada kai suka hau tafiya...

"Suna kawowa kusa da rumfar bayi yaja burki..
Juwairiya ta kallesa..nagode ranka shi dade..
Jalal ya jinjina kai,har ta fara tafiya sai jitai yace..

"Kada kije kina mamakin me yasa sarki guda zai jaki kuje kifi a waje..
  Juwairiya tayi saurin juyowa tana kallonsa...

Ya dauke kai yana ci gaba da cewa..
"Tun ina karami nake kwadayin naci kifin wajen nan watarana,amma ban samu damar hakan ba sai yau..
Juwairiya ta saki murmushi tana shirin mgn ne sukaji muryoyin bayi suna shirin fitowa..

  Ai da sauri juwairiya ta janyo sa suka boye bayan wani kango...

Jalal ya kura mata ido ganin yarda ta matse shi ajikin bango tana lekawa taga ko bayin sun wuce..
   Wani irin shock ne yakeji a gaba daya jikinsa..
Ya kurawa gefen fuskarta ido..

Juwairiya kuwa ganin bayin lekowa sukayi kawai suka koma ciki sai ta sauke ajiyar zuciya me nauyi..

Ina zata iya bari wani ya ganta da sarki jalal!?tab bazata taba bari asirin su ya tonu ba..
Ta dago da kanta..

Sai gani tayi fuskokinsu sunyi dab da juna har tsinin hancinsu na gogar na juna..
   Gabanta ne ya shiga faduwa..
Dama haka ta matse shi?wayyo...
Ai da sauri taja baya tana kasa da kanta..
Jalal ya murmusa kafin yabi ta gefen ta ya fice......

******************
"Surayya ta kalli umaymah tana damke hannayenta cike da tsananin bakin ciki da fusata.
   Na tabbata wani ne ya saka a batamin girkina!kuma wlh wlh bazan yafewa ko wanene wannan ba,ni surayya bana barin bashi!

Umayma ta dafa kafadarta,ranki shi dade kema ai kin san wacece zata iya yi maki irin wannan katobarar.. ina kyautata zaton gimbiya khadija ce....
Surayya ta gyada kai,lallai dole ne na koyawa wannan yarinyar hankali!!dan ta gane ni ba abokiyar yin ta bace!!!

**************
Washe gari...

"Juwairiya gaba daya tunda ta tashi daga barci take cikin farin ciki ..
Hansai ta lura da hakan dan haka tace,lallai diyata wannan murna haka meya farune ?

juwairiya ta murmusa,bata taba yin barcin me dadi irin na jiya ba..
Girgirza kai kawai tayi tace,umma babu komai wlh,kinsan haka Allah ke ikon sa watarana se kawai kaji ka tashi da farin ciki..

Hansai ta rungume ta,Allah ya baki duk farin cikin dake cikin duniyar nan diyata..juwairiya tayi dariya kema haka ummana..

***************
"Tana fitowa daga cikin rumfar bayi tayi hanyar sashen zainaba dan ta gaishe ta kafin tayi reporting wajen aikinta..

Tafiya kawai takeyi cike da murnarta har bata lura da turaki da hamza dake tsaye a gefen hanyar ba..
   Turaki ya kura mata ido tun kafin ta karaso wajen da suke..
Ga mamakin sa ko kallon inda suke batayi ba bare ma ya saka ran ta gaishe su..

      Hamza ya kalla yace,kayi gaba kawai ina zuwa...
Bayan juwairiya yabi yana mamakin me ya dauke mata hankali har haka...
Sai da suka kawo kofar shiga sashen zainaba sannan ya jira sunanta..

"juwairiya. ...
Ta juyo tana kallonsa da mamaki..kafin tace ranka ya dade ina kwana?

Ya murmusa lafiya lau,yau kin kawo wa kawar taki ziyara kenan?
Juwairiya ta gyada kai..
Yace toh yayi kyau,sannan ya juya ya fice yana sakin murmushi..

Juwairiya ta shige ciki da murnar ta..
   Zainaba ta tarar ta tule kaya a gabanta zabba'u na gyara mata linkinsu ..
Tana ganin juwairiya da murna ta tare ta..
Sun gaisa sosai kafin juwairiya tayi mata sallama ta fice...

******************

"Koda ta shiga sashen sarki jakadiya ce ta tsayar da ita akan surayya na nan cikin dakin jalal..
ta jira sai ta fita sai ta shiga ta gyara..
    Wani abune ya tokare mata makoshi,ta fito waje ta zauna a waje gaba daya duk farin cikin data fito dashi ya gushe...

*************
  "Sarkina ba zaka tashi haka nan bane?
Surayya dake zaune akan gadon jalal tana shafa kirjinsa ta fada cike da kissa..

   Yarima ya gyara kwanciyarsa barci ne sosai a idonsa kasancewar  bai kwanta da wuri ba jiya..
Cikin kasalalliyar murya yace..
Surayya ki fita ki bani waje mana,nace miki barci nakeji ko?
  Surayya ta tabe baki...tana tunanin a ina umayma ta tsaya?

**********
"Juwairiya na waje umayma ta shigo sashen dauke da tire ta rufe shi da wani dan kyalle..
   Juwairiya ta kalleta, su umayma manya..
Umayma ta washe baki,lah juwairiya ai ban lura dake bane ma,wai ni jiya ina kika shige ne da daddare ?
ta karashe mgnr cike da son jin gulma,
dan ta nemi juwairiya jiya a Rumfar bayi bata ganta ba..
juwairiya taji gabanta ya fadi..
Ina fa zanje?dare yayi sosai ina dakin du'bu tare dasu goggo laure..
Umayma tayi murmushi a zuciyarta,
lallai wannan yarinyar ita zatayi wa karya?har fa dakin du'bun ta shiga bata ganta ba,amma a fili sai cewa tayi..
  Allah sarki bari na shiga uwar dakina na jira..

***********
Jakadiya ce ta shiga dakin jalal ta sanar ma surayya zuwan umayma..
Murmushi tayi a zuciyarta..
Sannan ta mike ta falon..
Umayma ta cire kyallen data rufe tiren data shigo dashi..
Glass cup ne cike da fresh milk..
Surayya ta amsa tana kallonta..
Kinyi yarda nace..?
Umayma ta gyada kai..
Surayya tayi murmushi sannan ta koma cikin dakin da tiren a hannunta ..

   Ajiye tiren tayi a kan wani dan karamin table sannan ta koma kan gadon jalal ta kai bakinta saitin kunnensa tace..

Sarkina ga madara can na ajiye maka ,idan ka tashi dan Allah kasha kaji?
   Jalal cike da zakuwar tafiyar ta daga dakin yace..
Naji...
Ta murmusa hade da kai masa sumba a goshinsa sannan ta mike ta fita tana addu'ar Allah yasa yasha madarar..
Dan dolene itama ta zama wulakancin da khadija tayi mata..

****************

_"Ni kuwa nace kome surayya ta shirya oho...."_


Muje zuwa 👇
TEAM RUMFAR BAYI
[9/18, 3:22 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 25
Wattpad @afreey101
*Pls do visit n vote Me*

_This page is for you TEAM RUMFAR BAYI groups..😍_

******************

"Surayya na fitowa daga cikin dakin ta jawo umayma gefe tace da ita....
ki samu waje ki tsaya a nan har sai kin tabbatar min da jalal yasha wannan madarar kina ji?...
Umayma ta gyada kai kada ki damu ranki shi dade(ur wish is my commad) ...

Surayya tace yauwa, sannan ta nufi hanyar fita..
A nan ta hango juwairiya a zaune ta takure..
Ta watsa mata harara tayi gaba..
Juwairiya ta girgiza kai kawai tabi bayanta da kallo..
     sai ga Jakadiya tazo tayi kiran ta bayan fitar surayya da minti kusan talatin..

    **************
A hankali ta shiga dakin tana kare masa kallo..
Idonta ne yakar kan gadon..
A can ta hango sa ya takure waje daya yana ta barcinsa..

Me yasa jakadiya tace ta shigo bayan jalal din ma bai tashi ba..
Har ta juya zata fita sai kuma ta dawo da sauri ta je gaban gadon ta tsaya..
    Kirjinta na bugawa ta kurawa fuskarsa ido tana tunanin me yasa zuciyarta take son ta kai ta inda aka fi karfin ta ne...juwairiya jalal yafi karfin baiwa kamar ki...

   Taja lumfashi....zata juya ta fita kenan..
Sai Ganin wani kwaro tayi yana shirin hawa kan jikin jalal..dan har ya haye kan abun rufar sa..

Da sauri ta kai hannunta wajen ta kore masa shi..
Tana shirin gyara tsayuwarta ne kawai taji tayi losing balance dinta ta fado a kansa tim!

"Jalal ya farka a fusace yana fadin..
Surayya wai me nace miki ne huh!
Ga mamakin sa sai ganin juwairiya ce saman jikinsa tana mutsu mutsun tashi..gabanta nata faduwa..

    Har sa samu tayi kokarin dafawa da hannunta zata mike sai kawai taji ya sake fisgo ta ta koma fadawa a kansa..
   Waro ido tayi tana kallonsa cike da tsoro...

Jalal ya tsare ta da ido..jitai yace..
"Kinsan kuwa miye hukuncin abunda kikayi yanzun?
Bakin ta na rawa ta girgiza masa kai..

In a naughty tune yace....
Baki san da cewa duk baiwar da ta hada jikinta dana sarki ba ta zama mallakinsa.... (wato concubine dinsa)

  ta Sa'ke ware idonta dan ta tsorata sosai..
Jalal yayi murmushin mugunta..kafin yaja hancinta yace..
Haka kike so ai...
Shiyasa kika kawo kanki kan shinfida ta ko?
Juwairiya kamar ta nutse ta shiga kokarin tashi tana girgiza kanta..

Jalal ya sake ta yana kunshe dariyar sa..ta mike tana jin kamar lumfashin ta ya dauke..
se jan iska takeyi tana dafe da kirjinta..
  Shi kansa yarima ji yakeyi kamar gangar jikinsa kamar ba tasa ba dan duk jikinsa ya daskare waje daya..

"Juwairiya ta karasa wajen window tana jan lumfashi tana lumshe idonta,kafin ta dawo ta fara kimtsa dakin..

  Jalal ya sauko daga kan gadon idonshi yakai kan cup din fresh milk din da surayya tace ta ajiye masa..
Karasawa yayi ya dauka yashanye duka dan ji yake makoshinsa duk ya bushe..

   Ke...!
Ya kira juwairiya dake kokarin kakkabe kujera..
Zo ki fitar da wannan..ya nuna tiren gabansa..
Ta gyada kai tazo ta dauka ta fita..
Yabi ta da kallo kafin ya saki murmushi..

"Tana fita ta mikawa wata baiwa tace ta tayata fitar mata dashi..
  Umayma dake lebe tana kallonsu ta saki murmushin murna ganin kofin madarar babu komai a ciki..

Ai da gudu ta karasa sashen surayya..
Surayya ta mike da sauri ganinta..
Umayma tace, ranki shi dade sarki jalal yashanye madarar nan duka..

Surayya ta kwashe da dariya..
Haka nake so...!
Ai wannan shegiyar yarinyar sai ta raina kanta yau itama..
Umayma tace,kwarai kuwa ranki shi dade shiyasa na samo mana wannan maganin me fitar da dandanon harshe (lack of taste) kinga komai zata girka ma sarki jalal bazai taba jin dan danon sa ba..ko kokarinta zai zama a banza
Surayya ta gyada kai,shi yasa nake alfahari dake umaymah duk suka saka dariyar samun nasara..

*************
"Juwairiya na gyaran dakin jalal na zaune akan kujera yana kallonta..

Har dai ta fara tsarguwa da irin kallon nashi,duk dagowar da zatayi se sun hada ido dashi,..
Wai yau bashi da aikin yi ne ko me?
Ko wanka bata ga yana niyyar shiga yayi ba ma..
  
"Tana kammala gyaran ta kalleshi..
Na kammala ranka shi dade ka huta lafiya..
Jalal yayi saurin mikewa yasa hannu ya fisgo ta baya..
Ta kalleshi da tsantsar mamaki..
Langwabar da kai yayi yace..
Ke nake jira ki shiga ki hado min ruwan wankana..

Juwairiya tadan yi kasa da kai..
Amma mai martaba ai akwai kuyangin da suke hada maka..
Jalal ya samu kansa da fadin..

"Ke nake so kiyi min...."

juwairiya taji mgnr har cikin kokon zuciyarta wani dadi ne ya ziyarce ta..
Ta samu kanta da kallonsa cikin ido..
Sai dayaji gabansa ya fadi..
Can cikin kun'nansu suka jiyo jakadiya na sanar da shigowar kilishi sashen..

Ai Gaba dayansu sai da suka tsure.
Juwairiya ta rasa ina zata saka kanta..
Jalal kansa sai da ya dan rikice..
Tsintsiyar dake kasa ya dauka ya mika mata da sauri..
Sannan ya koma ya kwanta kan gado shi kuma..

Kilishi ta shigo dakin cike da takama..
juwairiya tayi saurin zubewa ta gaisar da ita..
kallon kyama tabi ta dashi sannan tace..
Bamu waje...
Da rawar jiki juwairiya tabar dakin..

"Kilishi ta kalli yarima..
Wane irin barci ne kayi yau jalal?
Baki na can a fada ka shanya su..
Jalal cike da rashin fahimta yace baki kuma?

Kilishi ta yatsine fuska..
Wai Galadima ne tare da mutanen sa suka zo wajen mahaifinku ajan mgnr auren hamza da diyarsa..
Jalal ya jinjina kai,ai ban san da zuwan su bane umma..ina jin magaji ya shafa'a ne bai fada min ba jiya...

Kilishi ta tabe baki,ni wlh bama son wannan hadin nake ba..
Jalal yace sbd me umma?
Kilishi tace,kai kana ganin dacewar jinin sarauta  kamar hamza ya hada zuri'a da wata diyar galadima can? ai yafi karfinta nesa ma ba kusa ba...
Ta gyara zamanta,shiyasa nake masa sha'awar diyar sarkin kano amma kasan halin mahaifin naku..

Jalal dai da kallo kawai yake bin ummar tasa,tun ba yau ba yasan ta da shegen son mulki,kwata kwata bata kaunar wanda bashi da mulki ko abunda duniya..
   Ya jinjina kai yace,umma ai hamza mijin mace hudu ne...ko ya aure ta ai zaki iya hadasa da yarinyar da kike so ko...

Kilishi tayi murmushi hakane kam ka kawo shawara..yanzu dai tashi ka shiga wanka ka shirya..
Yarima ya gyada kai sannan cikin subutar baki yace ,

"gashi kuma har ta tafi bata hada min ruwan wankan ba"(in a disappointing tune)

  Kilishi da mamaki tace..
Wacece?
Jalal yadan daburce..
Ah eh ina nufin baiwar data fita yanzun..
Kilishi tadanyi jim,kafin ta mike tace,ni zan tafi amma kayi da jiki dan Allah kada mahaifinku yayi fushi dakai..

*************
       "An saka bikin diyar galadima da hamza nan da wata biyu kacal,sannan tsohon sarki Abdul-Jabbar ya bawa jalal umarnin tafiya kasar zazzau a gobe kan maganar auren turaki da jikar sarkin..
   
"Su khadija manya kuwa ana can madafa an dukufa hadawa yarima delicacies kala'kala..
  Har gidansu ta aika rabi dan ta tambayo mata recipes din mamanta,sbd ta san jalal najin dadin abincin innarta sosai..

"Bayan sun dauki lkc me tsayi suka kammala komai sannan ta shige sashenta ta sake kimtsawa taci gayu kamar a sace ta..sannan ta nufi sashen jalal..

************
A gajiye sosai jalal ya dawo daga fa'da,dan haka jakadiya ta saka kuyangi suka hada

Please Login or Register in order to submit comment