Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

miyene zata sani tunda tana kaunar juwairiya sosai..

"Koda zainaba taji sallama na sanar da isowar jalal sashen ta ba karamin mamaki tayi ba..
Ta mike tsaye har ya shigo ya zauna kafin itama ta samu wuri ta zauna fuskarta dauke ta da tsantsar mamakin ganinsa..

  "Jalal ya sakar mata murmushi..
Yadai?wannan kallon fa?

Zainaba tace,wlh mamaki nakeyi wai ya jalal da kansa ne a sashena..
Jalal ya murmusa,nazo bada hkr ne nasan kanwata tayi fushi da yayanta ko?
Zainaba ta shagwabe fuska, ni na isa nayi fushi da Sarki?
Jalal ya shafa sa'jen sa,gashi har umma ma fushin da ake dani ya shafe ta,tunda ta fada min kin daina zuwa gaishe ta ko?
Zainaba ta turo baki..
Jalal yayi dariya..toh ya ake ciki ne menene lbr..?
Zainaba a take yanayin ta ya canza,damuwar dake ta cinta a rai ta rasa kuma dawa zatayi sharing yasa kwalla sulalowa akan kumatun ta..

   Jalal yaji hankalinsa yadan tashi,kodai wani abu ne ya samu juwairiya?dan a ganinsa zainaba bata tare da wani damuwa..

   Cikin kulawa yace,haba zainaba menene kuma na zubar da kwalla..
Zainaba ta kallesa tana nazari,maybe Allah ya turo mata ya jalal ne dan ya taimake ta..
  Gyara zama tayi sannan ta fada masa komai a tsakanin ta da Mustapha..

Jalal ya kura mata ido kawai yana fadi a zuciyarsa TIRKASHI..

  Zainaba ta katse shi da cewa,wlh yaya bana son ayimin wani auren hadi kamar yarda akeyi muku,ni Mustapha nake so kuma shi nake son na aura..
   Jalal a take zufa ta shiga ke'to masa..
Lallai akwai chakwakiya nan gaba...
Dan kuwa ya samu lbr a wajen gimbiya kilishi....
Tun ZAINABA  na yar jaririyar ta mai martaba ya bawa MAGAJI  ita,duk da shima magajin bashi da wani masaniya akan hakan...................


Toh fa........

Muje zuwa 👇
TEAM RUMFAR BAYI
[9/18, 3:22 PM] Aysha Galadima:             *RUMFAR BAYI*
         ( A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 27
Wattpad @afreey101

**********************

        "Jalal ya gyara zamansa yana kallon zainaba cike da tausayin irin tata kaddarar ..

"Ki kwantar da hankalinki kanwata kawai kici gaba da addu'a Allah ya zaba miki abunda yafi alheri kinji,ke da ma ko fara mgnr auren ki abba bayyi ba..

Zainaba tace,ah ah yaya dan Allah nidai ka taimake ni,nasan idan kayi wa abba bayani bazai ki amincewa ba..
Jalal ya rasa me zai ce mata,sbd dai magajin nan amininsa ne kuma yasan waziri ma bazai taba aminta ba ace an bawa dansa zainaba kuma taje ta auri wani can daban..

      "Zabba'u  ce ta shigo falon da sallama..
Zainaba tace,yadai zabba'u ya na ganki ke kadai?ina juwairiyar?

Zabba'u tayi fuskar tausayi..
Ranki ya dade juwairiya fa bata jin dadi tun kwana biyu da suka wuce..

Hankalin zainaba e ya tashi mutuka,a take ta mike tsaye tana fadin,shine baki sanar min ba?
Zabba'u tace,kiyi hakuri ranki ya dade amma itace tace min kada na fada miki dan tasan hankalinki ne zai tashi..

Zainaba jiki na rawa tace,muje na ganta..
Da sauri zabba'u ta shiga gabanta, ranki shi dade kin manta bazaki iya shiga rumfar bayi ba..

  Zainaba taja tsaki ta koma ta zauna cikin takaici..
  Jalal kuwa duk yana saurarensu,hankalinsa ba karamin tashi yayi ba shima..
Dama bata da lafiya ne?
Toh Meya same ta?
A wane hali take ciki yanzu?
    Mikewa yayi kawai ba shiri yayi sallama da zainaba sama sama ya fice..

"Gaba daya a ranar jalal tunanin yarda zai saka juwairiya a idonsa yakeyi..yana son yaji ko ya jikinta da sauki ko yayi tsanani?amma bashi da me bashi wannan amsar..

Da yamma magaji ne yazo yaja shi da kyal suka je yin wasan doki..(Polo )

Lkcn daya dawo sashen sa sai ya tarar da khadija a dakinsa tana zaman jiransa...
   Tsaki yadan ja yana mamakin nacin wadan nan matan nasa..kullum sai sun kawo kansu wajen miji..mtsw..

"Khadija kuwa tana ganinsa ta saki murmushi, ya jalal sannu da shigowa..
Jalal yace,yauwa a takaice..

Khadija taje ta kamo hannunsa  ya jalal wai nayi maka laifi ne?
Jalal ya kalleta,laifin me zakiyi min khadija..?

Ta shagwabe fuskarta..
toh ba naga ne daga ganina da kayi ba sai ka wani daure fusaka,kamar bakayi wani farin cikin ganina ba..

Jalal yayi murmushi ya shafa gefen fuskarta yace..
ba haka bane..kawai dai abubuwa ne sukayi min yawa..
Khadija ta rungume sa,kada ka damu komai zaizo maka da sauki idan akayi sabon na'din (palace counsel)...

*********
"Wasa wasa juwairiya jiki sai daya kai ta har kusan kwanaki biyar bata fita daga cikin rumfar bayi ba tana ta jinya...

Sai dai tana samun sako daga wajen zainaba dan har fulani kanta ta saka aka kawo me magani ta shiga har cikin rumfar bayi ta duba ta..

"Yau kam ta tashi jikinta da sauki sosai tana zaune ne kwanon abinci a gabanta tana ta faman tsakurar sa kamar bataso..

Tunani kawai takeyi yarda take jin zuciyarta kamar tayi tsuntsuwa ne taje sashen yarima ta dan gan sa..

hansai ce ta kalleta duk ta rame tace,juwairiya kodai sai na nemo miki maganin cin abincin ne?
Juwairiya tayi murmushi kada ki damu umma,kawai bakina din ne babu wani dadi shiyasa..hansai ta jinjina kai kawai..

"Mai martaba ina tunanin kawai a kai mutanen nan gidan yari..
"Magaji dake zaune gefen jalal suna cikin fada ya fada..

  Ji yayi jalal bai ce masa komai ba,dan haka ya dago yana kallonsa..
Ya rasa meke damun abokin na sa kwana biyu haka bashi da wani nutsuwar kirki kullum se dai ya zauna shiru..

    A hankali ya karasa gaban throne din jalal ya dafa shi..
Jalal ya kalleshi da sauri lafiya?
Magaji yace,dan Allah ka fada min abunda yake damun ka..

Jalal yasa hannunsa ya janye hannun magaji daga kafadar shi..yace
Na sha fada maka babu komai dake damuna wai meyasa ka cika naci ne?..
  Magaji ya jinjina kai yana bin shi da kallo..
ko yaushe jalal ya daina fada masa sirrin sa?oho...
Kodai ya daina daukarsa amininsa ne?

*********************
"Da yamma juwairiya ta fito can bayan rumfar bayi gaban kogi inda suke wankin kayansu ta tsaya..
   Iskan dake kadawa ta shaka...
Murmushi ta saki tana murnar samun lafiyarta,gobe dai inshaAllah zata saka jalal a idonta..

*********************
"Washe gari tun da asuba take ta shirinta..
Jakadiya na lekowa tayi saurin mikewa tace,inna muje na shirya..
Jakadiya tabi ta da kallo kin tabbata jikin naki ya warware?

Juwairiya tace kwarai kuwa inna..
Jakadiya tace toh muje dama nayi kewar ki...

"Suna shiga sashen juwairiya taji zuciyarta tayi wasai..
   Da saurinta ta fada cikin dakin..dan jakadiya ta sanar mata ta shiga kawai matan sarki basa ciki..

"Can kan gado ta hangosa a kwance..
  Tayi saurin karasawa tana kurawa fuskarsa ido...kamar yadan rame shima..

Gani tayi yana motsa bakinsa..
Bata ankara ba kawai taji yana kokarin furta sunanta..
Juwai....
Tayi saurin kai kunnenta kusa dashi dan ta tabbatar ko sunan ta din yake son furtawa..

Aikuwa dai juwairiya yake ta furtawa..
Washe baki tayi kafin tace a hankali..
Na'am ranka shi dade...
Ga babban mamkinta sai ta ga ya bude idanunsa tangaren ya sauke su akanta..

Ai a tsorace taja baya tana jin kirjinta na bugawa..
Shi kuwa jalal da sauri ya mike ya sauko daga kan gadon ya tsaya a gabanta..yana mamakin ganinta..

Murna sosai ya ziyarci zuciyarsa har baisan sanda yasa hannu ya fisgo ta zuwa jikinsa ba..
  A tare duk suka sauke ajiyar zuciya mai nauyi...

   Acikin kunnenta taji yace..
Ina kika shige uhm?
Juwairiya tayi murmushi tana shakar kamshin sa..
Bani da lfy ne..
Jalal ya dago ta daga jikinsa yana kare mata kallo duk ta rame tayi wani irin haske..

_"A Take ya tuna da amaryar sarkin zazzau AMMI,tabbas suna mutukar kama da juwairiya, amma taya hakan ya faru?wata zuciyar tace masa kana mamakin da ikon Allah ne?jalal ya girgiza kai da sauri,tabbas kamanni ne kawai daga da Allah..tunda dai bai ga wata alakar da zata hada matar sarki da kuma baiwar Rumfar bayi ba"_

Lumfashi yaja kamin yace..
Ya jikin naki yanzu?
Zatayi mgn ya sake cewa, ah ah ina zuwa ma dai...
Fita yayi bai dade ba sai gashi ya sake dawowa..

   Juwairiya zatayi mgn sai ji tayi jakadiya na sanar da shigowar me magani..
Da sauri ta kalle shi..
Kafin tace..
Mai martaba naji sauki fa..
Jalal ya zauna a gefen gado yana fadin..
Ina so ne kawai na tabbatar....

  Me magani ya shigo jalal ya nuna masa juwairiya yace..
ka duba min ita.
  Me magani yace..
Na duba ta?ya nuna juwairiya cikin mamakinsa..
Jalal bai tanka masa ba..
Me maganin ya bukaci data zo ta zauna..
A sanyaye taje ta zauna ya duba tan..
Sannan ya tabbatar wa jalal ta samu lafiya...ya amshi kudinsa ya fice..

Jalal ya dawo kusa da ita yace..
Kinga Yanzu na yarda..
Juwairiya ta gyada masa kai sannan ta nufi hanyar toilet..

"Jalal na tsaye yana sakin murmushi sai ji yayi ana sanarwa surayya zata shigo ciki..
Daure fuska yayi a take..
Surayya kuwa na shigowa ta rungume sa cike da murnar ta..tana fadin..

Sarkina kasan kasan yanzun nan na samu wasika daga masarautar mu matar yayana ZAID ta haihu..
   Jalal ya tabe baki yace,toh shine zaki fado min daki da sassafe haka?

Surayya ta sake matse shi ajikinta..
Wa nake dashi a duk fadin masarautar nan da zan(sharing)farin cikina dashi idan ba kai ba..

    Jalal na shirin mgn sai ga juwairiya ta fito daga cikin toilet idanuwanta a kansu..
   Ji tayi gabanta ya fadi..
Jalal da saitin kansa ke fuskantar hanyar toilet din ya hango ta a tsaye amma ga mamakinsa..
"Kishin sa sosai ya hango a cikin idanuwanta...
murmushi yayi a zuciyarsa dan kuwa yasan ta fara son sa ne..
shi kuma haka nan yaji zuciyarsa taji dadin hakan sosai...

     Surayya ce tadan sake shi jin yayi mata shiru sai kallon juwairiya yakeyi data dauke kai gefe..
   Surayya tadan kalli inda yake ta faman kallon har bai lura ta sake shi ba..
Ganin juwairiya ce wajen sai wani abu ya tsaya mata a wuya..
Ta daka mata tsawa..

"Ke!
Juwairiya tayi saurin karasawa wajenta..
Fita!
Ko baki san abunda ya dace bane?kika zo kika wani yiwa mata da miji tsaye a kai..kidahuma kawai mtsww...

juwairiya ta juya da sauri tabar dakin..
Jalal ya kalli surayya cike da takaici..
Surayya na kokarin kamo hannunsa tace,wlh na tsani wancan yarinyar sarkina..
gara ma dai da Allah yasa ta kone wannan fuskar mtsw..
Jalal ya kwace hannunsa bai ce mata komai ba ya shige toilet abunsa..
   Surayya ta bi shi da kallo tana wani tunani kafin ta juya ta fice itama...

****************
"Turaki ni fa ban fahimci abunda kake nufi ba... (fulani ta fada tana kallon turaki dake zaune a gabanta ya dukar dakai kasa)

  Fulani ta sausauta murya,Turaki inaso ka fahimci haka kaddarar GIDAN SARAUTA ta ga'da',kuma na tabbata mahaifinku bazai zaba maka abunda zai cutar dakai ba..
kayi hakuri kamar yarda saura sukayi ka rungumi auren nan ka fahimce ni?

Turaki kamar ya fasa ihu ya gyada kai..
Fulani tace yauwa,bana son wata dogon mgn nan gaba tashi ka tafi Allah yayi maka albarka.
A sanyaye ya mike ya fice jikinsa duk yayi sanyi...

******
From afrah...👇

_"Salam readers,pls ga masu complaining akan ina jefa English words a writing dina suyi hakuri. Dan ina sakawa ne if i lost d word in hausa,i knw its a historical story,bt ina kokarine kawai dan na samu nayi muku update da wuri basai na tsaya tambayar mutane me kaza ke nufi da hausa ba,no body is perfect manage d way i write pls am sorry_..

And yes

_Naga wasu comments dinku kuma naji dadin su sosai da sosai,NIMA INA YINKU IRIN SOSAI DIN NAN😘_
_Keep them coming..dan suna kara sakawa naji dadin yi muku typing da wuri..._


TEAM RUMFAR BAYI all d way.....
*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 28
Wattpad @afreey101


********************
"Bayan wata daya...

'A cikin wannan watan daya gabata, ba karamin shakuwa ce ta shiga a tsakanin jalal da juwairiya ba..
Duk lkcn zata shigo kyara masa daki toh sai sun samu lkc sun sha yar firar su duk da dai ba wani mgnr kirki bace amma hakan yana saka zuciyoyin su cikin tsantsar farin ciki...

"Kamar yau ma ta shigo sashen nasa danta gyara masa dakin ta tarar da baya ciki,tayi mamaki sosai da haka har ta kammala gyaran bata ganshi ba...

Ta fito falo kenan taji kuyangi nata kananan maganganu kasa kasa..
   Shiga tayi cikinsu dan taji me suke fada..jitai sunce..

"Gsky Allah yayi wa sarki jalal kyawu"kin ganshi kuwa?kamar wani balarabe..
A take duk Suka shiga leken kofar wajen shakatawar sa..
Juwairiya tabi su itama sai hango shi tayi kwance akan kujerar lilo barci ya dauke sa..fuskar sa kamar me murmushi ga cute lips dinsa da dogayen eye lashes dinsa..

     Ta kura masa ido tanajin yarda bayi keta kyasa sa,a ranta kuwa cewa tayi,duk son da nake maka nasan bazan taba samun ka ba...

Jakadiya ce tazo ta kore su daga wajen..
Sannan ta kalli juwairiya tace, kije waje magaji ya turo ayi masa kiran ki..
Mamaki ne ya kamata,me kuma zatayi wa magaji?

     Fita tayi tabi bayan bawan da aka aiko kiran nata..
  A gaban wata bishiyar mangoro taga bawan ya tsaya....
Sai hango magaji tayi a tsaye yana sakar mata murmushi ya jin gina jikinsa da bishiyar...

Tayi saurin gaishe shi..
Ya amsa mata a sake yana fadin..
    Kinyi mamakin kiran da nayi miki ko?
juwairiya ta gyada kai..
Yace dama ina so ne na baki wata yar kyauta..
Juwairiya ta dago ta kallesa..
Ya nuna mata bishiyar yace na baki wannan bishiyar mangoron...
Juwairiya ta kwashe da dariya.
Magaji yabi ta da kallo yana jin sa a wani a irin nishadi...

Kafin yace,ba wasa nakeyi ba fa?
Kinga wannan bishiyar duk lkcn(season) din mangoro toh sai kin samu wanda yafi na ko ina zaki a jikinta..kuma a yarda na lura ke mayyar mangoro ce ko?

Juwairiya tayi murmushi tace toh nagode ranka ya dade..
Magaji ya samu waje ya zauna..
Sannan ya nuna mata waje itama ta zauna a can nesa dashi..

Magaji yaja lumfashi kafin yace, na san rayuwar bauta acikin wannan masarautar ba karamin wahala ne da ita ba,amma zuciyata na son taji dan tarihin ki ko kadan ne..
Duk da nasan a tarihin bayin dake cikin masarautar nan kece kadai aka taba haifa a cikin RUMFAR BAYI...

  Juwairiya taja lumfashi, hakane ranka shi dade, amma ni rayuwata babu wani labarin da zan iya bada shi.. wanda baka sani ba..
Tun ina shekara goma na fara bauta..
   Magaji yaji tausayinta har cikin zuciyarsa..
Ya jinjina kai...(yana tunani a zuciyarsa,kodai ya fada mata sirrin dake zuciyarsa ne?sai kuma wata zuciyar ta hane sa)
Ya kalle ta yace..
zaki iya tafiya nagode da lkcn da kika banu..
juwairiya ta mike kawai tayi masa godiya kafin ta fice..

*******************
"Washe gari..

"Umayma ce ta kalli surayya,Allah ya kara miki yawan rai..
ina tunanin kawai yakumbo ta bamu damar zuwa wajen bokan ta,
tunda dai har wata daya ya shude babu wani alamun ciki a tattare dake..
kuma kar na fara jin kusun kusun daga bayin dake sashen gimbiya kilishi,wai ta fara mgn a rashin haihuwar ku har wannan lkcn..

Surayya cike da takaici tace,nima ina wannan tunanin umayma..kema kin sani bazan taba bari wata ta haifawa jalal yaron da zaya gaje shi ba sai ni!ta nuna kanta!ni surayya! Shiyasa har gobe bazan bar ciyar da khadija wannan maganin ba har sai na samu MAGAJIN'SARKI..

Taja lumfashi tace ya mgnr wannan yarinyar?
Ina fata kin dasa mana wacce zata saka musu ido dan ni wlh zuciyata bata kwanta da aikin da takeyi a sashen sarkina ba..
Umayma tace kada ki damu...koma miye sirrin da take boyewa muna daf da sanin sa..

Surayya zatayi mgn kenan sai ji sukayi ana sanar da shigowar khadija..
Umayma tace, ko wane gulmar ta kawo ta kuma?

"Cikin takon girma khadija ta shigo cikin falo tare da rabi a bayanta..
Surayya tayi murmushin yake,ah ah amarya da kanta da sassafe haka.?

  Khadija tayi murmushi,gani nayi kamar zumuncin dake tsakanin mu ya fara rauni..
Surayya ta tabe baki,zumunci?ta maimaita..
Khadija tace,daga sashen umma nake yanzu,tace nazo wajenki dan mu tautauna akan shirye shiryen auren su ya hamza da ya turaki..
Surayya ta gyara zaman ta,na dauka ai su umman ne zasuyi komai..
Khadija ta girgiza kai,mu a nan masarautar matan sarkine ke gudunar da duk shirye shiryen daya danganci gidan sarauta..
Surayya ta jinjina kai..

***************
"Ina jinki....
ina kika je jiya da safe?
juwairiya ta kalli jalal daya tsare ta da tambayoyi akan jiya daya tashi bai ganta ba..
  Ta dan sauke kai kasa tace...
Magaji ne yayi kirana..
Jalal ya daure fuska sannan bai ce mata komai ba kawai ya gama shirinsa yayi gaba..
Juwairiya ta saki murmushi,lallai yarima akwai shegen miskilanci..
Har ta mike dan ci gaba da gyaranta taga ya sake dawowa ya dauki hular sa ya sake ficewa..

*****************
"Biki ya matso ana ta faman shirye shirye masarautar ta cika tam da mutane sosaidaga kowane yanki na arewa..

"A yau ranar juma'a ne kuma Aka daura auren HAMZA DA NAFISA sai kuma TURAKI DA SAMIRA..

  "Yarima gaba daya ranar bai samu zauna ba ko kadan ba,dan Fada ma ba karamin cika tayi tba ab..bashi da ikon fita ko nan da  can,sai magaji dake ta kokarin ganin ya taimakawa amininsa nasa..

"A can cikin gida kuwa,matan sarki ne ke ta hidima da jama'a sai ka rantse da Allah kansu a hade yake,amma kowacce tana yi ne kawai dan burge sarki jalal da kuma gimbiya kilishi mahaifiyar sa..

"Amaryar hamza aka fara kawowa nafisa direct sashen gimbiya kilishi akayi da ita..
SAMIRA kuwa matar turaki sai yamma likis suka iso kasancewar daga kasar zazzau suka taho..
Ita kam a sasheen fulani diyya aka ajiye ta...

"Da daddare mai martaba sarki jalal ya shirya musu liyafa ta gani ta fada..
Gimbiya kilishi ta bukaci surayya da khadija dasu zaunaa wajen shirya nafisa..
     Surayya ta kalli kayan dake hannun khadija tana yatsine fuska,kina nufin wannan kayan zata saka?
Khadija tace eh mana..
Surayya taja tsaki sannan ta fito da wasu kayan tace,wannan na tanadar mata dan haka su zata saka bana son wani feleke..
Nan fada ya kaure a tsakanin su..
Nafisa kuwa sai kallon su takeyi cike da mamakin kishi irin nasu..

***************
"Jalal daga fa'da sashen baki suka nufa shi dasu magaji..
A nan ya tarar da yan uwan SAMIRA samari da manyansu daga kasar zazzau..

Khaleed ne kawai ya sani a cikin su..
Dan haka dashi ya fara gaisawa..haka nan kuma ya samu kansa da tambayar khaleed din ko ina AMMI?

Khaleed yayi dan murmushi,ai ka san yan mata kusan biyar aka daurawa aure a yau din,toh AMMI na can kasar bauchi sunje kai diyar wajen ya ladan..
Jalal ya gyada kai sannan ya karasa ciki ya shiga gaisawa da sauran....

"""A gajiye sosai ya shiga sashensa dan shiryawa kafin lkcn liyafar yayi..
Dakinsa ya shige Yayi wanka ya shirya cikin kayan sa da sukaji ado sosai,ga rawani na alfarma yasha..

Har sun fito tare da angona ya kalle su yace ina zuwa...
Komawa yayi cikin sashen nasa ya dauko wata sarka ta zinari irin chain dinnan,ya zura a cikin aljihunsa sannan ya fice..

"Zainaba ce ta saka ayi mata kiran juwairiya dan su shirya samira..
Juwairiya cike da murna ta shiga dakin na fulani..
Samira na zaune a gefen gado ta lullube kanta da babban mayafi..

Zainaba na ganin juwairiya tace,wai ina kika shige ne juwairiya ?
kinsan kuma dolene na bukace ki a kusa dani yau..
Juwairiya tayi murmushi tace..
kiyi hkr ranki ya dade ina can RUMFAR BAYI ne muna taimakawa a cikin madafa..
Zainaba ta jinjina kai,sanann ta kalli samira..tace..
Amaryar yaya bude fuskar taki mana mu gani?
Ko mu kike jiwa kunyar?

Samira a kunyace ta yaye mayafin..
Sai cin karo tayi da fuskar juwairiya..
Ware ido tayi tana kallonta kafin tace ,tana kama da AMMI wlh,ta fada tana nuna juwairiya, kallon rashin fahimta sukayi mata..
Samira ta shiga kallon tufafin dake jikin juwairiya, a take ta fahimci baiwa ce..
Mamaki ne ya kamata dan haka ta ja bakin ta tayi shiru...

"Cikin dan kankanin lkc zainaba, juwairiya da kuma laure suka shirya samira cikin kayan alfarma tayi kyau mutuka..

"Zainaba komawa tayi sashen ta ta shirya sannan ta bawa juwairiya kaya itama tace taje ta canza hakama zabba'u..

        Juwairiya komawa tayi rumfar bayi dan shiryowa..
  Lkcn da zata fito sai ta tarar kamar anyi shara a masarautar babu kowa duk an hallara acan wajen liyafar..
      Cikin sauri itama ta karasa wajen..
Angwaye da matansu ba karamin kyau suka kayi ba..

  Idanuwanta ne suka shiga neman inda zaga yarima..
Can ta hango sa tare da magaji suna mgn ta kura masa ido..
Kamar ance ya juyo sai hada ido sukayi da ita..
Murmushi ya sakar mata a fakaice..sanan da idanuwansa yayi mata signal akan ta bi bayanshi..kafin ya fara tafiya cikin takon kasaitarsa..

juwairiya ta kalli su umayma da rabi dake gefen ta tace dasu ina zuwa kafin tayi gaba...
Khaleed dake gaisawa dasu khadija ya hango ta kamar daga sama..
Kallo ya bita dashi,gefen fuskar ta kawai ya iya hangowa amma yaga dan kaminta da Ammi,da saurinsa ya sake binta da kallon tana kokarin wuce su sai hango dayan gefen fuskarta ta yayi a kone,nazari ya shiga yi,wacece ita????????

****
Juwairiya na tafiya...
Umayma ta bi bayanta da kallon zargi wata zuciyar tace mata ta bi ta kawai,ai da saurinta ta shiga bin bayan juwairiya..

Can nesa da inda ake liyafar jalal yaja ya tsaya yana juyowa dan ganin ko ta taho....

Juwairiya ta karaso wajensa da sauri tana mamakin irin kyaun da yayi yau se kace shine angon..
  Jalal yace wannan kallonfa?
Ko nayi miki kyau ne?

Juwairiya tayi saurin dukar da kai..
Jalal ya mika mata sarkar daya fito da ita daga cikin aljihunsa..
Amsa..
Ta bi sarkar da kallo sannan ta kalleshi..tace..
Ranka shi dade me yasa zaka bawa baiwa kamar ni irin wannan kyautar..
Ai bayi basu da ikon saka duk abunda ya danganci kwalliya...

Jalal yaji wani iri har cikin zuciyarsa. .....
Yana son ya sanar da ita sirrin dake cikin zuciyarsa amma yana ganin kamar lkc bayyi ba....
Sai ya tuna lkcn da ya fahimci cewa SONTA YAKEYI....

"_Suna zaune ne tare da magaji a cikin lambu da wani yammaci.._
  _Ya kalli magaji yana fadin..
Abokina dan Allah na tambaye ka mana?_
_Magaji ya ajiye tufar(apple)da yake ci ya maida hankalinsa wajensa..yace
Ina jinka AMALE fadi naji.._

_Jalal yaja lumfashi kafin yace..
Idan kamar haka mutum ya damu da wata sosai kuma a kullum zuciyarsa na muradin yaganta yana begen ta a kowane lkc...yana jin dadin mgn da ita,yana kaunar kasancewa da ita,yana tunaninta,amma ya kasa gane matsayin da zaya ajiyeta a ciki zu.....
Magaji ne ya kwashe da dariya sosai..
Jalal ya kallo shi yace meye haka?
Magaji yace,meyasa kawai ba zai gene cewa SON TA yake ba?.._

_Ko wanene shi dai bako ne a cikin soyayya nake gani, dan duk abubuwan da ka fada yanzu soyayya kawai ce ke kawo su..ya dai sake tunani,..._

_Dan ba karamin SON TA yakeyi ba,kuma ya kamata yayi gaggawar sanar da itama.._
_Jalal yabi shi da kallo kafin yace, idan kuma yafi karfin ta fa?ina nufin(level)dinsu ba daya bane.._
  _Magaji ya gyara zamansa,ni a ganina indai yana sonta har haka duk wani matsayi ba wani abun damuwa bane ,idan ya aureta ai duk sun zama daya ko?
Jalal ya jinjina kai yana nazarin kalaman magaji..."_





TEAM RUMFAR BAYI
           *RUMFAR BAYI*
        (A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 29
Wattpad @afreey101

_SORRY-am sorry fans jiya ban samu nayi muku update ba sbd school,kuyi hakuri da wannan..#teamjuwairiya #teamyarima #teamRumfarbayi_
     

****************

    "Juwairiya ce ta saka hannu ta amsa sarkar daga hannunsa ganin yayi shiru na tsawon wani lkc.
a tunanin ta ko fushi ne yayi dan taki amsar kyautar tasa..

   Jalal yayi firgigit yana kallonta cikin kwayar idonta..
Juwairiya ta sakar masa murmushi itama tace..
nagode sosai ranka shi dade Allah shi kara budi da tsawon rai..
Jalal ya rausayar da kai bai ce komai ba..
Sai hannu daya saka ya sake karbar sarkar daga wajenta sannan ya dawo zuwa bayanta ya tsaya..
  Yana kokarin saka mata sarkar ne yake fadin..
"Kici gaba da hakuri juwairiya ki bani wani lkc zan sanar dake amsar tambayar ki nan ba da dadewa ba...

"Umayma dake labe can bayansu tana leke dan ganin da wanda juwairiya take tsaye..taja tsaki..mtsw
Dan Duhu ne a wajen sosai sai inuwar su kawai take iya gani..gashi kuma mutumin ne a bayan juwairiya ta dan kare shi..

  Tsaki taja tana shirin juyawa ne kawai ta hango rawanin sa..
Gabanta ne ya shiga fadowa..
Dan kuwa babu wani mai dau'ra rawani haka face SARKI JALALLUDEEN,duk wanda yake kan mulki kawai ake yiwa wannan na'din rawanin...

Ta shiga girgiza kanta ,inaaa ai ko kallo ma juwairiya bata ishe sa,namiji kamar jalal yana kuma matsayin sarki bazai kula mace kamar juwairiya ba..
Tabi inuwar da kallo tabbas sarki jalal dogon namiji ne kamar haka..
Cike da tunani kala kala ta juya da sauri tabar wajen...har tana hadawa da tuntube...

* * * *
An tashi taro lafiya kowa yayi hanyar sa dan zuwa sauke gajiya..
   Ni kuwa afrah nace bari na dan leko muku dakin sababbin ma'auratan.

"""""Lkcn da turaki ya karaso sashensa.. bayi jar sun gama shirya samira cikin kayan barcinta masu saukin gaske..
Ga kamshi tanayi sbd gyaran data sha..

Please Login or Register in order to submit comment