Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta..
Da sauri ta goge hawayen ta tayi wajen ta..

Zainaba na ganinta ta fara hawayen itama a shagwabe tace..
Yanzu fi sabilillahi dauke min ke yaya jalal zayyi..

Juwairiya tayi murmushi, kada ki damu zanki ya dade babu me dauke miki ni,tafiya kawai zamuyi mu dawo kinji..
Zainaba ta gyada kai,muje kiyi sallama dasu fulani...

Suna shiga sashen fulani diyya,juwairiya ta zube kasa tana kwasar gaisuwa..
Fulani a sake ta amsa mata tana fadin,ashe dake zasuyi tafiyar?

Juwairiya tace uhm,fulani tace,toh Allah ya dawo daku lfy,gaba daya falon suka amsa da amin..
    Suna fitowa waje suka ci da turaki..
Yana ganinsu ya sauke idonsa kan juwairiya,a take ya fahimci hankalinta a tashe yake..

   Gaida shi sukayi,yayi murmushi yace,ah ah yan matah ana ta bankwanar ne?
Zainaba ta shagwabe fuska,yaya harda kai zolayar ko?
Turaki yayi dariya,naga ai kwana uku ne kawai miye abun damuwa?ya karashe mgnr yana kallon gefen juwairiya..

    Juwairiya tadan murmusa kawai..
Turaki yace,addu'a kawai zakuyi abunda akaje nema a samo shi lafiya,yana gama fadar haka ya shige ciki cikin takunsa...

  Zainaba ta ja juwairiya zuwa sashen ta..
Wani kulli ta miko mata..
Gashi ki ringa ci ahankali a hanya kinji..
Juwairiya cike da murna tace nagode ranki ya dade...
Wani bawa ne yazo yana sanar dasu ana neman juwairiya...

*************
Motace irin ta da dinnan,sai wata bus..
Juwairiya da gudunta ta karasa wajen..
Yarima da magaji na tsaye da sauran bayin duka an gama saka kayansu a cikin motocin..

    Tana zuwa duk suka maida kallonsu gareta..
Yarima yaja tsaki...lallai ya gama kufsawa kansa yanzu haka zai tafi da waccan yarinyar yana kallon konannar fuskar sa,mtsw ..

Surayya ce ta karaso wajen tare da baiwa a bayanta..
     Wajen yarima taje ta mika masa kullin dake hannunta..
Se daya kalle ta sannan ya maida kallonsa kan kullin yace,menene?

Tadan karkace kai,
Ka amsa mana kaga fa akwai mutane a wajen,yadan yi yake sannan ya amsa ya shige mota,surayya tabi bayin dake wajen da kallon wulakanci balle ma juwairiya data gani duk a tsorace...
Suna shiga mota shamaki da galadima sukayi musu addu'ar suka lafiya sannan suka hau hanya...



"Toh ya kuke ganin wannan tafiyar zata kasance?"

Keep following rumfar bayi
[9/18, 3:14 PM] Aysha Galadima:          *RUMFAR BAYI*
      (A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 12
Wattpad @afreey101

*****************

"Sunyi tafiya mai nesan gaske kafin suka iso Daular borno..
   "Yarima dake zaune a bayan mota yace wa bawan dake tu'ka su,idan muka shiga  borno sai mu a tsaya a  masarautar su mu kwana zuwa gobe sai mu karasa chadin..

'Magaji ne ya gyara zamansa yace,ai mun shigo Daular borno tun dazu yarima tunanin me kake ne haka?ba dai har ka fara kewar surayyar taka ba..yayi mgnr cike da zolaya..
Yarima yaja tsaki kawai yana kallon window..

'A can cikin bus kuwa su juwairiya ne,tunda aka shigo kasar borno ta maida hankalinta akan kallon window tana karewa tsarin garin kallo...har taga sun shiga wata katowar kofa sai gasu acikin masarautar ta borno..

'Ido ta ware tana kallon mutane dake ta zurga'zurgar su duk da dare ne amma harkar gabansu kawai sukeyi..
Rabi ce ta dan tabo ta ganin motar su ta tsaya,muje juwairiya....

'A sanyaye ta fito daga motar jikinta duk a gajiye tana rungume da kullin kayanta..
Daidai lkcn ne shima yarima ya fito yana wani shan kamshin sa.
  
Har fadar mai martaba aka kai su suka kwashi gaisuwa sannan aka saka wasu matah su kaisu masaukin da zasu kwana zuwa goben..

Masaukinsu ya hadu sosai dan komai an wadata su,tunda Takawa (mahaifin jalal)ya riga ya turawa sarkin borkon sakon zuwan su.
daki daya aka ware wa su juwairiya ,sai daki daya na yarima, daya kuma na mazan bayi sai dakin magaji...

Suna shiga kowaccen su ta kwanta cike da gajiya,basu dade da shigowa ba sai ga sakon magaji ya iso musu daga wajen wani bawa,wai a cikin su ukun wata taje ta hadawa yarima ruwan wankan sa..

    'Rabi ta marairaice ta kalli juwairiya,waye zai je a cikin ku dan ni kam wlh bazan iya zuwa ba jikina ciwo yakeyi sosai..

"Zabba'u itace karama a cikinsu,dan haka tace,ni wlh tsoro nakeji kuma ni ban ma iya hada ruwan wankan ba  tunda ni a madafa nake dama..

  "Juwairiya tadan hararesu,kawai ku fito fili kuce ni naje mana..
Dariya sukayi sannan a tare sukace..
Dan Allah juwairiya ke kije..

"Juwairiya zatayi mgn bawan dake waje ya sake cewa, baku ji bane? !ba a barin yarima yana jira,juwairiya ta zunboru baki sannan ta mike tana sake gyara kayan dake jikinta kafin ta fito..

   Bawan na gaba tana binsa a baya har suka shiga bangaren su yarima..
  Magaji ne kawai a falon zaune..
Yabi juwairiya da kallo, shiga ga dakin can ya nuna mata wata kofa..
Toh tace kawai jiki a sanyaye ta shiga kofar..

   Yarima ta hango a zaune kan dago ya jingina bayansa a kan gadon ya lumshe idonsa..
Ta rasa me zatace masa, wace irin gaisuwa zatayi masa..

Dan haka se ta lallaba zata shige kofar data ke tunanin ta ban dakin ce..

     'Haka aka koyar dake!!!?

Muryar yarima ta da'ki dodon kunnenta..
Da sauri ta juyo ta hango shi yana kallonta fuska a daure..

Dawowa tayi baya tace,afuwa zanka shi dade na dauka barci kake ne...

Ya yamutse fuska yayi sannan ya maida idonsa ya lumshe..
  Juwairiya ta shiga toilet din ta hada ruwan wankan sannan ta fito ta tarar dashi a tsaye..tace..

Na gama...ta sunkuyar dakai..
Tsaki ya danyi haushin kansa kawai yakeji daya za'bi ta a tafiyar....ya kasa gane meyasa wannan yarinyar take shiga rayuwar sa..

    tsaki ya dan'yi kafin yace,Zaki iya tafiya,ya mike a natse yana cire alkyabbar dake jikinsa..
Toh tace kawai ta fice..

Tana fitowa falon ta sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi..

Magaji ne yayi dariya...
Tayi saurin kallonsa dan ta manta ma akwai mutum a falon..
Yace duk tsoron yariman ne?
Juwairiya tayi dan murmushi sannan ta fice tana jin kunya sosai..

Da asuba suka hau shiri,wannan lkcn rabi ce taje ta hada masa ruwan wankan dan juwairiya kekeme tace itama ta gaji..
    Da sassafe  kuwa sai ga kayan karin kumallo an kawo musu me rai da lafiya,suka ci sosai kafin suka hau hanya..

*************
"Sun sake shan wata tafiyar mai nisan gaske kafin suka shigo kasar chadi...
   Ba karamin mamakin nisan garin juwairiya tayi ba...

A wani wajen saukar da baki ne suka yi masaukin su..
  Su juwairiya na tsaye gaban kofar dakin da aka basu suna jira a bude musu magaji ya karaso wajen...

    Ya kalli juwairiya yace, yarima yace kije ki hada masa ruwan wankan sa..
Juwairiya ta gyada kai kawai amma can cikin zuciyarta haushi ne kawai takeji,ko ya dan bari ma su dan huta,koda yake su bayinsa ne bai damu da samun hutun su ba,shi kullum se shegen son wanka kamar wani kifi mtsww...

'Kullin kayanta ta mikawa rabi sannan ta juya tabi bayan magaji tana mamakin wai ita yarima da kansa ya kira bayan kullum se ya mata gargadin zuwa inda yake mtsww...

**************
'Ta same sa ne a cikin wani makeken falo..
Da sallama ta shiga ya amsa mata ciki ciki idonsa na kan wata takarda..

   Barka da hutawa ranka shi dade..
Yayi banza da ita,se hannu daya sa ya nuna mata kofar toilet kawai..
  Tadan ja lumfashi kafin ta shiga ban dakin...
 
Da kallo ta bi toilet din ganin irin nasa tsarin..
Toh fa ina zan samu ruwan a nan?ta fadi tana rike kugu...
   Ganin bata da masaniyar hakan ne yasa ta leko tana kallon yarima amma ta kasa magana..

Yarima naji a jikinsa kallon sa akeyi amma ya da'ke ya share ta...
  Juwairiya tadan ja tsaki kadan,sannan ta koma cikin toilet din tayi tsaye...

  Yarima ya mike tunawa da yayi famfo ne a cikin toilet din  kuma tabbas da wuyane ta san shi tunda can masarautar su, mai martaba da matan sa ne kawai ke dashi a ban dakin su..
    Toilet din nufa cikin tafiyar sa a sanyaye..

Ita kuwa juwairiya tabe tabe ta shiga yi dan gano inda zata samu ruwan..

   Sai ji tayi an bude kofar toilet din..
Ta juyo da sauri tana kallonshi..
  Yarima bai  ko kalleta ba ya shiga tafiya yana kusanto inda take a tsaye..

A tunanin juwairiya kashin ta ne ya gama bushewa tunda ta bata masa lkc har haka tasan bazai barta ba tsoro ne ya dirar mata..
    Yarima kuwa wajen fanfom dake kusa da ita yake son zuwa ya kunna...

Tana jin yazo kusa da ita sosai sai ta zube a kasa tana shirin mgn kawai taji saukar ruwa  a jikinta dan dama fanfom  bayanta yake a karkashin sa ta du'ka ..

    Yarima ya harde hannayensa yana kallon yarda ruwa yake wanke juwairiya tas...
    Ita kuwa a tsorace take sosai daga ina zuwan nan ya fitowa haka?

Ta dago fuskar ta da ruwa ke sauka a kai...
Yarima yaji gabansa ya buga,bum! Bum!

Minene haka?
Ya fada cikin tsananin mamakin ganin tabon dake jikin fuskar juwairiya yana wankewa a hankali ahankali ..

Kura mata ido yayi kawai yana kallon ikon Allah..
   Ita kuwa juwairiya jin ruwa ya cika mata ido yasa ta mike da sauri tasa hannunta tana goge ruwan daga idonta..

    "Sauke hannunta daga fuskarta yayi daidai da bugawar zuciyar yarima cikin tashin hankali...
Me zai gani haka?

I...TA...CE !!!!!

Ya furta da karfi....
Juwairiya ta tsorata sosai jin yarda yake ta furta itace itace kuma yana nuna ta..

  Yarima ya karasa gabanta....
kawai ji tayi yasa hannunsa me taushi yana shafa fuskarta...

Idanuwanta kawai ta zazzaro tana kallonsa..
Lafiyarsa kalau?
Taja baya da sauri a firgice ...
Hakan yasa hankalin yarima ya dawo jikinsa..

  "Haushin kansa yadan ji..
Ya daure fuska kamar ba shi ba yace kiyi sauri ki hada min ruwan..ya juya da saurin sa ya fito daga toilet din..

Daki ya shiga yana dafe kirjin sa..
Mamaki tsantsa a cikin zuciyarsa..
Dama itace?

Amma me yasa take boye fuskarta ne  da wannan tabon?
Lallai kuwa itace me wannan fuskar da ya dade yana son gani,ya shiga tuna duk haduwar da sukayi a baya..

Murmushi yayi kawai cike da farin ciki..
Wata zuciyar tace masa,yanzu tunda ka ganta se  kuma me?
Sonta kake ne?
Ah ah ya girgiza kai  da sauri ni nayi soyayya da wata baiwa?Allah ya tsare ni..
Dolene ya saita kansa kada yaja wo wa kansa raini a wajenta..
Haka nan yayi ta murmushi shi kansa ya rasa dalilin hakan...

***********
Juwairiya kuwa shaf ta manta da wani tabo a fuskata ,tana gama hada ruwan ta fito ta tarar da baya cikin falon..

Ta kalli kofar dakin..
Ko ta shiga ta sanar dashi ne?
Tadan girgiza kai,kada kije ya kuma ci mutumcin ki a banza..

Ta samu wuri ta rakube a gefe dan jiransa..
Sai jin fitowar shi tayi..
Yana ta wani kallonta bai ce mata komai ba ya shige toilet din..
Tadan ja tsaki,ko yace min zan iya tafiya ma mtsw..

Haka tayi ta zama har ya fito daga shi se dan wani yadi daya daura a kugunsa..
  Juwairiya tayi saurin dauke ido tana jin gabanta na faduwa......

Please
Vote
[9/18, 3:14 PM] Aysha Galadima:           *RUMFAR BAYI*
       (A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 13
Wattpad @afreey101

********************

   'kallon ta yayi Ya dan saki murmushi, kafin nan ya daure fuska yace,ke!...
Ta dago da kanta a tsorace amma bata kalli in da yake ba..

'Yarima ya shafi sumar kansa Yace,ki biyoni.....sannan yayi cikin dakinsa..
A sanyeye jikinta na rawa ta bi bayansa a tsorace...

  Tana shiga dakin ta iske shi a tsaye yana goge jikinsa cike da nutsuwa..
Tayi kasa da kanta da sauri..
Yarima yace,har yanzu baki san aikin ki ba ne?

A cikin sarkewar murya tace na sani?
Ya karasa gabanta ya mika mata dan karamin kyallen dake hannunsa..
Jiki na rawa ta amsa..

Ya koma ya zauna yana juya mata bayansa,kawai be ce da ita komi ba..

'Juwairiya ta karasa ta tsaya a bayansa da kyallen a hannunta..
Se data ja lumfashi sannan ta runtse ido ta shiga goge masa jikinsa..
Tana gamawa taja gefe da saurinta..ta runtse idonta kirjinta na bugawa..

'Yarima ya saki murmushi sannan ya mike ya karasa wajen kayansa ya dauki man shafawar sa .
yana shafa man yana kallon juwairiya dake rakube a gefe idanuwanta a kulle gam! haka kawai sai ya tsinci kansa a cikin wani irin nishadi..

"Zo ki taimaka min ya fada kai tsaye yana mika mata alkyabbar dake hannunsa..

Ta bude ido taga ya gama shirin sa tsaf cikin wani farin yadi mai sauki ,ta karasa ta amsa alkyabbar sannan ta taimaka masa ya saka..
       Maganar wani bawa sukaji daga can cikin falon...

Yarima ya fito tana biye a bayansa..
Abincine kala kala aka kawo masa..
   Bawan ya du'ka har kasa yace,ranka shi dade sun ce na baka hakuri akan kayi hakuri da wannan ya nuna abincin daya shigo dashi,saboda dare yayi ne basu samu damar gaba tar maka da abinci masu yawa ba..

    Yarima yace banu komi zaka iya tafiya..
Juwairiya ta dan tabe baki duk wannan kayan dadin shine harda wani bashi hakuri..tab lallai ta yarda yarima babban mutum ne..

'Yarima ya kalleta yaga idanuwanta kyam akan abincin..
Zama yayi kawai yana lankwashe kafafunsa..
Juwairiya ta dan hada karfin da gareta tace..
Ranka shi dade zan iya tafiya?

Yarima ya girgiza kai...
Juwairiya tace na shiga uku wai meke damun mutumin nan ne?(a cikin zuciyarta)..

Yarima ya lumshe ido ya bude,kafin yace,zo ki bani abincin..
Juwairiya a sanyaye ta duka ta zuba masa abincin a cikin plate sannan ta ajiye a gabansa tana kokarin mikewa yace..

A ba'ki zaki bani...dan na gaji dayawa..
Juwairiya gabanta ya fadi,...
'A baki'?ta fada a tunaninta cikin zuciyarta tayi mgnr se ji tayi yace..
Da a hanci zaki bani?
Ta girgiza kai,ai ko zainaba bata zama a bata abinci a baki..
Tsokali ta dauka ta debo abincin kadan a ciki sannan ta mika masa..

Yarima na kallon fuskarta ya bude baki ta saka masa abincin aciki..
Cike da takura take basa abincin har yayi mata nuni da ya koshi..
Dadi taji sosai dan ta san yanzu dolene ya sallameta tunda dai ba ita zatayi masa barcin ba..

   Ji tayi kawai yace..
'Saura ke ki ci'
Ta dago da mamaki tace,Ni?
Yarima fuska ya daure yace ban sani ba..

Juwairiya ta rasa yarda zatayi wai "saura ke ki ci"kodai kunnenta ne yaji mata badai dai ba..?

Yarima ya mike kawai yace,idan kin gama zaki iya tafiya...
Yana shiga daki juwairiya ta sake kallon delicacies din dake wajen ko kwatan abincin yarima bai ci ba..
     Gyara zamanta tayi a wajen tana fadin..

'Gwara naci dan kada ma ayi asarar abincin nan da mutane dayawa basu da halin kamar shi...
    Cin'yar kaza ta dauka tana yashe lebenta,se yau Allah yayi zata dandana irin wadan nan abincin oh"dama su ummanta na nan suci tare..

    Yarima dake labe a bakin kofa ya saki murmushi yana ta kallon yarda take cin abincin da gani ta kwaso yunwa sosai, tausayinta ne yaji ya kamasa..

  Juwairiya taci tasha sosai sannan ta kwashe sauran tayi gaba dashi dan ta kai wa su rabi suma su sa wa bakin salati.

Tana shiga dakin ta tarar basu a ciki ko ina sukaje oho,sallolinta tayi sannan ta zauna ta sake maida tabon fuskarta shaf bata kawo ya wanke bane a toilet din yarima duk a tunaninta a wajen alwala ne ta wanke sa.

"A daren yarima yayi barcin farin ciki sosai dan har mamakin kansa yakeyi,duk da baisan matsayin yarinyar a cikin zuciyarsa ba amma zayyi kokarin kyautata mata tunda dai ko ganin ta ma kawai a kusa dashi ya na saka shi farin ciki.

***************
"Da sassafe kuwa itace ta fara tashi taje tayi wanka sannan a cikin toilet din ta zauna ta maida tabon fuskarta.
   Suna zaune rabi nata lin ke musu kayan shinfidar su akazo yin kiran su,duk suka mike suka fito waje..

Sashen yarima suka shiga hade da sallamarsu..
Yana zaune tare da magaji suka shigo..

Idanuwansa gaba daya akan juwairiya suka sauka.
A take yaji kwanciyar hankali na ratsa sa duk da kuwa tabon dake fuskarta a yanzu bayajin kyamarsa ko kadan...
Shi dai kawai ya kasa gane dalilin ta na boye fuskarta da takeyi da wannan tabon na karya.

"Magaji ne ya kallesu..sannan ya amsa musu gaisuwar su..
Ga wannan ya mika musu wasu kaya dake ajiye a gefen sa..
Zaku saka su ne yanzu dan zamu fita daku..

Rabi ce taje ta dauki kayan sannan tayi godiya suka juya dan ficewa..se jin muryar yarima sukayi yace..

Ke!!!!
Su duka duk suka juyo a tare dan basu gane wacce 'ke' din bace yake nufi..

   'Shiga ki hada min ruwan wankana...'
Tsuru'tsuru sukayi dan basu gane wacece acikinsu yake bawa umurnin ba..

Magaji ne yadan fahimci rashin ganewarsu akan furucin da yarima yayi, dan haka sai ya nuna rabi dake tsakiyarsu,ke shiga ki had...

Bai kai ga gama maganar ba kawai sai ganin yarima yayi ya nuna juwairiya, waccan nake nufi...

"Juwairiya gabanta ya fadi,ta gyada kai a sanyaye sannan tayi hanyar ban dakin..
Magaji ne ya kalle shi,a zuciyarsa kuwa mamaki yakeyi,meye ke damun yarima da waccan yarinyarne,da zasu taho duk yawan bayin da aka kawo musu ita kawai ya zaba,Allah yasa ba abunda yake tunani bane,dan kuwa indai hakan ya faru,ya tabbata abokin nasa zai sha wahala ba karama ba...

  Ya dai da kallon?
Yarima ya fadi yana kallon magaji daya tsura masa ido..
Magaji ya mike..ah ah babu komai idan tayi tsami ai zan ji ..yana gama fadar haka ya fice..

Yarima yayi murmushi, tsami? Ya maimaita yana girgiza kansa..kafin ya mike ya shige daki..
   Juwairiya na gama hada masa ruwan wankan ta fito.

Bata iske shi falon ba dan haka dakinsa tayi sallama ta shiga..
Yana zaune wasu takardu ne a gabansa yana gyara wa,juwairiya tayi kasa da kai..

Na gama ranka shi dade..
Ya dago yana kallonta..
Kije ki shirya ki dawo...
Da mamaki tace,na dawo?
Yarima ya danyi tsaki bai amsa mata ba..
Juwairiya a sanyeye ta fita tana mamakin halayen yarima sam ta kasa gane me yasa ya canza mata haka..

"Bayan sun shirya cikin wasu riga da zani na hadin atamfa da shadda, rabi ta kalli juwairiya cike da sha'awa tace,lallai juwairiya kin ganki kuwa?

Juwairiya ta dan kalli jikinta me nayi?ko ba haka ake saka kayan ba ne?
Su rabi suka kwashe da dariya, ah ah kyau kikayi acikinsu wlh ,ko dan bamu saka kaya irin wannan ne?

Juwairiya tayi murmushi, gaskiya ne amma ni kam kayan nan sun takura ni dayawa,rabi tayi dariya dan bakya yawan daura zani ne shiyasa amma ni kam sun min wlh Allah yasa su bar mana kyauta ma..

Juwairiya na dariya ta fito dan komawa wajen yarima..
Da sallama ta shiga falon,yana zaune ga kalaci nan an kawo masa amma bai taba ba..

Barka da hutawa ranka shi dade..
Yarima ya dago yana bin ta da kallo daga kasa har sama..
Ba karamin canzawa tayi ba da kayan,a zuciyarsa yace,sai ma idan babu wancan tabon a fuskarta...

   Zo ki bani abinci...
Toh...
Tana a tsugunne ta hada masa abincin,ta dawo gefen daman'sa ta zauna a nutse sannan ta fara basa abincin yana ci kamar baya so..
Ya isa haka...ya daga mata hannu..

Gyada kai tayi ta mike tace,ranka ranka shi dade zan iya tafiya?
Ya girgiza kai..
Zauna ki ci'
Ta dan kalli fuskarsa babu alamun zata iya yi masa gardama..

Ta koma ta zauna amma ta kasa cin abincin..
Kina bata min lkc'
Ya fada a da'ke yana kallonta..
Afuwa nake ranka shi dade amma akwai abincin mu a can dakinmu..

Yarima ya tabe baki...
Na lura har yau dai baki gama sanin dokokin dake cikin bauta wa uban gidan ki ba, ba'a yiwa yarima gardama kin gane?

Ta gyada kai sannan ta jawo apple ta dauka ta kai baki hannunta na jawa..
Gani tayi yarima ya dauki plate ya shiga zuba abincin a ciki sannan ga mamakin ta a gabanta ya ajiye plate din..
Gabanta na faduwa ta kalleshi..
Ya harare ta,ki cinye shi tas!
Ta zaro ido'
Yace ni kike zarowa ido?
Tayi saurin sa'dda kanta kasa,afuwan ranka shi dade..

Yadan murmusa kafin yace,toh fara ci..
Ta saka hannu ta fara ci a kunyace,wai meke damun yarima ne?kodai duk so yakeyi ya siye ta da dan abincin da yake bata dan kawai ya kwanta da ita?

   A tsorace ta dago tana kallonsa..
Taga hankalinsa na wajen takardun da yake dubawa..
Anya?
Ai bata tabajin ance yayiwa bayi fyade ba,ta girgiza kai kila dan sunzo wani gari ne bayaso ace basa kula da bayin su,amma me yasa ita kawai yake kyautatawa haka?koma dai miye ita ba zata taba bari a lalata rayuwar ta ba ehe...

   Tunanin me kike?hala bakiji me nace bane ko?
Juwairiya ta dauke hannunta daga cikin plate din tace,na koshi ne ranka ya dade..
Yarima ya daga kafada, toh tashi mu je.. .
Juwairiya ta mike tayi gaba harda su tuntube..
yarima yabi bayanta da murmushi s "matsoraciya "


Yau kunji ni shiru,tun safe na fita schl ne daz y..

Pls
Vote
[9/18, 3:14 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 14
Wattpad


***************
"Gidan wani babban dan kasuwa sukaje wanda yana cikin manyan yan kasuwa na duniya gaba daya..
gidane na zamani mai kyan gaske gashi makeke sosai har yaso ya tsorata su juwairiya...

  ' Zo kuga kallo kuwa wajen su, rabi har dasu sakin baki,tana zungoro juwairiya da zabba'u..
    A waje suka zauna kan wasu fararen kujeru masu kyau su kuwa su yarima suka shige ciki dan an aiko wani ya shigar dasu...

"Sun dade a zaune wajen, juwairiya gaba daya zaman ya gundure ta,dan tun suna firar kyaun gidan har kowa ya gaji yayi shiru..

mikewa tayi tana dan shawagi a wajen..can ta hango wasu fure masu kyan gaske dan bata taba ma ganin irin su ba a can kasar tasu (rose flower)
Da sauri tayi wajen tasa hannu ta tsi'go daya tana murmushin ta mai kayatarwa..

***************
Yarima tare da magaji na tare da wannan babban dan kasuwan dan isar da sakon mai martaba na son fara fafada kasuwancin sa a nan kasar ta chadi.

  Yarima ya gama bayani ya dauki cup din tea da a gabatar musu yayi dan sipping kadan...
Ya gyara zamansa...
Open glass din dake gefen su ya kalla...
Can ta hango ta rike da furen a hannu ta na dama tana murmushinta...

Hakanan yaji ta burge sa sosai ga view din wajen se ya kara mata kyau a idon yarima,ya murmusa kawai yana kokarin dauke kansa ne kawai yaga wani saurayi na karasawa wajen ta...

********
"Yan mata ya kike?
Taji an fadi da hausar da bata goge sosai ba..
Ta dago ta kalleshi da rashin sani...
Lafiya ta fada tana rusunawa kasa..
Yace No ah ah basai kin rusuna min ba,kema din da mutanen nigeriyar kika zo?

Juwairiya tace eh tana dukar dakai..
Ya saki wani irin shu'umin murmushi yana karewa jikinta kallo...dan ya fahimce baiwa ce ita...
Furen hannun ta ne ya fadi kasa sbd tsabar a tsorace take sosai,jikinta har rawa yakeyi ganin irin kallon da mutumin yakeyi mata har da yashi leben sa..

  Da sauri ta du'ka dan daukar furenta tayi gaba..
  Kawai sai jin hannunsa tayi a kugunta yana shafata...
A firgice ta dago tana kallonsa cike da tsoro..
Miye....ha...ka?muryarta na rawa ta fada..

Yayi mata murmushin yaudara..
Yan mata ina son irin ki sosai,zaki zauna dani?zan siye ki da kudi masu yawa na baki ga'ta da yan'ci....
   Mamakin kalamansa tayi sosai...kuka ne yazo mata ba shiri dama abunda ake fada kenan?yau ta shiga ukun ta..
Shi kuwa ganin haka sai yasa hannu ya jawo ta jikinsa wai ze lallashe ta..

**************
"Yarima gaba daya wutar sa daukewa tayi,fushi da takaici ya mamaye zuciyarsa ,cup din dake hannunsa ne yayi wurgi dashi da karfi...

Duk su magaji suka kalleshi da sauri cike da mamaki.
Ya mike kawai cikin bacin ran da baisan me yasa yake jinsa ba yayi waje...
    
""""Juwairiya nata kokarin ture mutumin daga jikinta cike da tsoro,kuka takeyi sosai ganin wani irin sabon al'amarin da bata taba fuskantar irin shi ba,duk da tabon dake fuskarta amma wannan mayen mutumin sai da ya tunkare ta haka,ko su nan basa kyamatar masu tabon ne...

  Bata ankara ba sai ji tayi an fisgo mutumin cikin karfin gaske..
Tayi sauri ja da baya tana kallon yadda yarima ke saukar wa mutumin nan tagwayen marika..

  Mamaki sosai ne ya rufe ta,meyasa yarima ke taimake ta,wacece ita?ita ba kowan kowa ba banza baiwa marar galihu...
   Da kyal magaji ya amshi mutumin daga hannun yarima yana mamakin karfin halin sa..gashi kuma wannan deal din da sukazo dashi da kyal ne ya zama successful tunda yarima ya gama kufsa musu...

   Dan kasuwan kuwa ba karamin fushi yayi ba dan kuwa kanin sane yarima ya gama jubga,su tafi kawai yace musu zasu ji daga gare sa idan yayi shawara....
Yarima ko a jininsa suka tattara sukayi gaba.
Juwairiya kuwa hawaye basu dauke mata ba su rabi ne ke ta lallashinta...

******************
Koda su ka dawo masaukin su yarima kwanciya kawai yayi akan gado yana jin wani abu a cikin zuciyarsa.. tambayar kansa yayi miye dalilinsa na ka're mutumcin wannan yarinyar?
Duk yarda yaso ya gano dalilinsa kasa wa yayi...

Magaji ne ya shigo yana kallonsa kawai ya girgiza kai..
Zama yayi kusa da shi yace..
Gobe da sassafe zamu koma tunda dai mun zo munyi

Please Login or Register in order to submit comment