Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

an rufe mata fuska da mayafi dayaji ado sosai..
      Yana shigowa dakin ya hangota a zaune kan gado mai rumfa irin na da din nan..

   Zuciyarsa ce yaji tayi masa wani iri,idan yana tuna irin mafarkin da yakeyi na son kasancewa da wacce zuciyarsa ke muradi..
Amma gashi sbd kawai suna jinin sarauta an tauye musu wannan hakkin..

Tsaki yaja kawai ya samu waje akan kujera ya zauna abunsa ..
Samira taji shiru na wani dan lkc..
Ahankali ta bude mayafinta sai hango shi tayi a zaune ya dafa kai..

  Lumfashi taja tana tuna kalaman kakarta..

"Samira Kada kice dan mijin da aka hada ki dashi baya sonki ki zauna hakan ya riga damunki har ki jawowa kanki wani ciwo,yarda akayi miki dole shima fa haka aka yi masa,dan haka inaso ki zauna ku fahimci junanku kin gane?"

Samira ta sauko daga kan gadon ahankali ta dawo wajensa ta zauna..
Turaki yayi saurin dagowa ya kalleta..
Babu laifi samira kyakkyawa ce gata kuma da fara'a sosai dan murmushi yaga tana yi masa..
  Jiyai tace..
Ka kwantar da hankalinka,nasan baka sona ko?

Turaki ya kura mata ido,ita kuma wannan ya take?kai tsaye tana fadin tasan baya sonta?
Katse mishi tunani tayi da cewa..
Nima kuma bana sonka..!

Se dayaji kalamanta har zuci..
Samira ta murmusa taci gaba da cewa dan haka kada wani abu ya dame ka,ai zamu iya kasancewa kawaye ko?

Turaki ya samu kansa da gyada mata kai..
Samira ta mika masa karamin yatsan ta toh yimin alkawari..
Turaki ya samu kansa da sakin murmushi yana mamakin yarinta irin ta samira..
Samira ta daure fuska..
Bani mana..
Ganin bashi da niyyar yin abunda tace, yasa ta fisgo hannunsa da kanta ta kulla alkawarin kawancen nasu..

   Turaki yabi ta da kallo..
Gani yayi ta haye kan dayan karamin gadon tana fadin..
Ka kwana a kan wancan dan nikam bani da wani isasshen tsawon hawan sa..

Turaki ikon Allah kawai yake kallo..
Yana nan a zaune se munsharinta kawai ya jiyo..
Ya mike yana fadin..
Lallai wannan bata da wani damuwa abunta..

"Can dakin su HAMZA kuwa..
   Yana shiga ya tarar da Nafisa a gefen gado zaune..
Ya karasa wajenta kanta a kasa ya zauna a kusa da ita sosai har jikinsu na gogar na juna.

Nafisa taji iri dan kuwa bata taba zama da namiji haka ba..
Tana kokarin dan matsawa ne hamza yayi saurin kai hannunsa kan kugunta ya janyota gaba daya jikinsa..yace..
Haba matas ai ba haka akeyi ba..tsoro na kike ne?

Nafisa ta girgiza kai..
Yace yauwa ko ke fa yanzu bari na tayani rage duk wadannan ya nuna kayan jikinta da kuma sarka da yan kunnenta..
Nafisa dai tayi masa shiru..
Hamza kuwa ya shiga cire mata yan kunnen yana kare mata kallo..
Cike da salonsa ya shiga shinshinar wuyanta..
Ni kuwa afrah nace,oh su hamza abun nema ya samu....

******************
"Washe gari kuwa da sanyin safiya umayma ta isa sashen surayya gulma na cin ta..

  Ta samu tashin ta kenan daga barci ..
Surayya ta kalli umaymah dake tsaye lost in her thoughts..dan se da tazo take tunanin ko kada ta sanar ma surayya?

Yadai umayma kika shigo kikayi min tsaye?
Umayma ta samu waje kasa ta zauna tana lankwashe kafafunta ..
Tace..
Ranki ya dade wani lbr ne na kawo miki amma ni kaina ban kai ga tabbatar dashi ba..

Surayya tace ina jinki..
Umayma ta kwashe duka zarginta ta fadawa surayya...
"Kan uban nan!!!!!

Surayya ta fada a mugun fusace..
Umayma jiki na rawa tace,amma fa ranki ya dade ba wai na tabbatar dashi bane ni a ganina ma bashi bane,dan sarki jalal yafi karfin baiwa kamar juwairiya ..

Surayya taja tsaki tana tuna lkcn da yarima ya fadawa zainaba ta basa ita(lkcn a cikin lambu).
tabbas ko ba shi bane dole ne ta koyawa wannan yarinyar hankali!!!harma ta isa ta hada miji da ita?ai ko a matsayin SA'DAKA baza ta taba bari yarinyar ta shigo rayuwar jalal dinta ba..dole ne tasan abunyi,
dan zuciyarta ta dade da zargin yarima da wannan yarinyar,
abu dayane kawai zai iya raba su idan ita yarinyar ce ta tona masa asiri a cikin al'ummar sa ta fadi meke tsakaninsu...
ta tabbata jalal bazai taba yafe mata ba, ace kamar shi sarki yana kebewa da baiwarsa a lungu cikin dare,ai girma sa ya gama zubewa a ikon mutane..

Umayma ta kalla tace, kije ki kiramin da ita..
Umayma tace,kin samu wani mafita ne?
Surayya tayi murmushin mugunta,dole ne itama ta dan rama dizgata da jalal yakeyi...

****************
"Juwairiya kam ta gama shirin ta tsab ta dauko sarkar da yarima ya bata jiya data cire ta boyeta..
Murmushi ta sakar kamin ta mike ta fito..

Karo sukaci da umaymah..
Umayma ta kalleta fuska a daure..
Kije uwar dakina na kiran ki..
Juwairiya taji gabanta ya fadi..
Tana kirana?
Umayma tace,kwarai sannan tayi gaba..

"Lkcn da juwairiya ta isa sashen surayya a waje ta tarar da ita zaune akan kujera tana shan kamshi tana ka'da kafarta.

    Juwairiya na shirin gaishe da ita taga wasu bayi su biyu sun finciko ta ta fadi a gaban surayya..
Surayya ta banka mata harara kafin tace..
'Na lura baki gama sanin matsayin ki a wannan masarautar ba ko?
Juwairiya ta duka da kai..
Surayya tace,dake nake mgn !
Juwairiya tace na sani ranki ya dade.
Surayya a fusace ta damko gashin kan juwairiya dake lullube cikin mayafi,tana kallon fuskarta tace, da wa aka kama ki jiya daddare?waye shi!!!!!!

Juwairiya gabanta nata faduwa,ta rasa wace amsa zata bata dan kuwa ko kashe ta zatayi zataba taba fadin sunan jalal ba..
Surayya ta kara kolewa..
tasa kafa ta hankade ta gefe..
Tunda bazaki fada min a lallama ba ina tunanin zaki fi son fadawa SARKIN DORINA !ko!!!!

Da sauri juwairiya ta dago ta kalleta idanuwanta kamar zasu zazzago sbd tsabagen tsoron daya shige ta.
Jiki na rawa ta rarrafo gaban surayya ta shiga bata hkr tana zubar da hawaye masu ciwo.

Surayya tayi murmushin takaici kafin ta kalli baiwar dake bayanta tace,ku dauke min ita daga gabana sannan ku Kaita can RUMFAR HUKUNTA BAYI inaso sarkin dorina ya tabbatar da ta fadi sunan wannan mutumin kafin yamma...

Bayin sukazo suka dauke juwairiya sai kuka take gwanin tausayi..
   Umayma tabi bayan surayya da sauri tana fadin..
Lallai ranki shi dade na yaba da hankalinki..
Kinga yanzu koma waye juwairiya take boyewa dolen ta ta fada mana,sannan idan tayi kuskuren furta sunan sarki jalal ko gimbiya kilishi kadai ta isa ta hallakar mana da ita..

Surayya tayi murmushin mugunta tabbas hakane umayma...

**************
    "Tunda aka taho da juwairiya daga sashen surayya bayin dake kan layin suka hau rike baki suna tauyawa kaddararta...

   An shiga da ita RUMFAR HUKUNTA BAYI sarkin dorina ya saka aka kwantar masa da ita flat..
Ya dawo wajen da kanta yake..
jikinta sai rawa yakeyi sbd tsoro..ta dago ta kalli jajayen idanunsa..
Cikin kakkausar murya yace..
Ki fada min sunan wanda aka kama ki dashi jiya daddare!!!!!
Juwairiya ta cije harshe ga mugun tsoron da takeji amma bazata iya taba fadin sunan shi ba..

Sarkin dorina yace,toh shikenan tunda girman kai ne dake ina tunanin wannan itace maganin ki...ya nuna katuwar dorinar dake hannunsa..
Ya dawo daidai saitin tafin kafarta ya shauda mata ita cikin kwarewarsa..

*****************
A hankali ahankali dai lbr ya fara yawo acikin masarautar..
Wannan bawan ya fadawa wancan baiwar gulma ta ko ina....

"Rabi Ce ta fito daga sashen khadija dan zuwa aiken ta..
Gani tayi bayi sai jinjina kai suke suna kusun'kusun..
Ta karasa wajen su ta shiga tambayar su dan tasan akwai lbr da dumin dumin sa..
    Ware ido tayi ta dafe kirjinta...
Juwairiya aka kai RUMFAR HUKUNTA BAYI?

Ai da saurinta ta koma sashen khadija ta zube a kasa tana maida lumfashi..
Khadija ta kalleta da mamaki..
Ke kuma ya haka?
Ina aiken da nayi miki yake?
Rabi ta kalle ta..
Ranki shi dade lbr ne naji yanzun nan..
Wai gimbiya surayya ta saka akai juwairiya can RUMFAR HUKUNTA BAYI  wajen sarkin dorina..

  Khadija ta ware ido..
Wajen sarkin dorina fa kika ce?bama wajen du'bu a cikin RUMFAR BAYI ba?
Rabi tace wlh haka akace..
Khadija tace,lallai surayya bata da imani ko kadan..
Toh me tayi mata ne haka?
Koma zainaba taji lbrn abunda ke faruwa?

Rabi ta kwantar da murya tace,dan Allah ranki ya dade ki taimakawa juwairiya..
Khadija ta tabe baki,lallai wato so kike naje na zubda girmana a wajen surayya sbd wata baiwa can ko!lallai kuwa kinyi kadan!!!

Rabi tabi ta da kallon takaici,su dai mutanen nan basu da ko digin taisayi a cikin zuciyarsu,wato dan kawai kaga ta zubda girma da ajinta a gaban kishiyarta shine bazata iya taimakawa baiwar Allah ba..mtsww wata sa'in mulkin ma jaraba ne..

"Lbr ya gama circulating acikin masarautar daura har ya kai ga kunnen gimbiya kilishi...(wai surayya ta saka akai wata baiwa can RUMFAR HUKUNTA BAYI)

    Kilishi ta kalli hansai dake mata fifita..
Lallai ya kamata na san irin takun da zanyi da wannan yarinyar surayya,
dan a yarda nake gani tazo ne da shirin shafe tarihina a cikin wannan masarautar..

Hansai(da bata da masaniyar diyarta ce wannan baiwar) ta jinjina kai tace..
ai Allah ya kara miki yawan rai,lbr ma har ya fara yawo akan,gimbiya surayya na kokari wajen siye zuciyar sarki jalal..dan ta samu dukkan (authority)a cikin masarautar nan..

     Gimbiya kilishi cike da bakin ciki tace aikuwa tayi kadan ... (dan kuwa a duk fadin masarautar daura gimbiya kilishi ce kadai mace da ake tsoro kuma ake jin maganarta fiye data sarki...
amma a yarda take ganin taken taken surayya yanzu tana dab ne da dauke mata wannan matsayin da ta dade tana gina shi..)

********
Turaki na hango yana kokarin karasawa gaban fa'da dan amsa kiran sarki jalal..

Caraf kunnensa ya jiyo masa firar da wasu bayi sukeyi..
  "Eh wlh wannan yarinyar me konannar fuskar nan ce,ai na tausaya mata wlh"

   Ribas yayi ya dawo wajensu..yace..
Me naji kuna fada yanzu?
A tsorace duk suka zube kasa..
Allah ya kara maka yawan rai ayi mana afuwa..

Turaki yace,mgnr da kuke fada yanzu ita nake so naji...dan haka kuyi gaggawar sanar dani..
Daya daga cikinsu yace..
Dama ranka shi dade gimbiya surayya ce ta saka aka kai wata baiwa can RUMFAR HUKUNTA BAYI...
   Gaban turaki ya fadi..a zuciyarsa yace..
Juwairiya ce...
Ai da sauri ya juya ya fice ko shiga cikin fa'dar ma fasawa yayi...

"Zabba'u ta shigo falon zainaba a rikicenta..
Uwar dakina kinji lbrn da naji yanzu..
Zainaba dake hakimce akan kilisar ta tace..
Wane lbr ne haka daya rikita ki..
Zabba'u ta zube akasa..
Juwairiya ce juwairiya ce ranki ya dade gimbiya surayya ta saka aka kai can RUMFAR HUKUNTA BAYI...
   Mai!!!!!
Zainaba ta mike da sauri,surayya!! Me juwairiya tayi mata haka?
  Jiki na rawa ta mike tace wa zabba'u muje...
Can sashen surayya ta shiga kai tsaye,ta tarar da ita hakimce tana cin kayan marmari ga bayi nan nata mata hidima..
Zainaba rai a bace tace..
Matar yaya,inaso kije ki saka a saki juwairiya yanzu..
Surayya tayi murmushi,tace..
Zainaba ina tunanin kin manta da wacce kike mgn ko?
Ta nuna kanta,gimbiya surayya ce fa uwar gidan sarki jalal..

Kuma akan mgnr wannan yarinyar bazan taba bari ta tafi ba tare da an hukunta min ita ba,dan haka zaki iya tafiya..
Zainaba a fusace ta fita..
Ta koma sashen fulani,nan ma babu sa'a,
'samira kawai ce tabi bayanta tana dan bata baki akan tayi hakuri sannan tayi tunani idan akwai wanda take ganin ze iya taimaka mata taje wajensa..
Zainaba ta jinjina kai kafin ta mike da gudu ta fice...

*******
Jalal kuwa baya da masaniya a kan komai ke faruwa.
Dan tunda ya shigo fada bai samu fita ba..

Ga zuciyarsa dake ta azazzalar sa da son ganin juwairiya, kome ya hanata zuwa yau da safe oho?ko rashin lafiyar ne ya dawo?
   Magaji ne ya dafa sa..
AMELE ina ganin ya kamata kaje ka huta hakanan..

Jalal yayi mika cike da gajiya yace..
Yanzun nan kuwa dan ba karamin aiki nasha yau din nan ba..
Magaji yayi dariya ai na lura hanklinka ma ya fara barin wajen nan..

Jalal ya mike fadawa suka zo suka zagaye shi suna masa kirari..
  Har ya fito daga fa'da sai ga zainaba ta karaso wajen hankalinta a tashe...

   Jalal ya kalleta yace,lafiya zainaba?
Zainaba ta karasa kusa dashi tace ya jalal ina son mgn dakai a sirri..
  Jalal cike da mamaki ya sallami fadawan wajen sannan ya maida hankalinsa wajenta..
Zainaba ta fashe da kuka...
Ya jalal bani da wanda zai taimake ni sai kai..

Jalal yace taimakon me kike so kanwata?
  Zainaba tace,dan Allah ya jalal kaje ka umarci surayya da ta dauke hukuncin da ta saka ayi wa Juwairiya a RUMFAR HUKUNTA BAYI...

    Dum dum dum kakaji zuciyar jalal na bugawa..
Mai!!!!!kike nufi da surayya na hukunta juwairiya? ????
ya fada cikin mugun tashin hankali...!!!!
Zainaba tace,nima ban san dalili ba amma wlh yaya juwairiya na cikin halin taimakon mu..

A rikice sosai jalal yace muje...
Zainaba ta sauke ajiyar zuciya dama ta sani ya jalal ne kawai zai iya ceton juwairiya daga wajen surayya tunda taje har wajen fulani amma tace bazata saka baki a cikin harkar surukan kilishi ba dan bata son wani tashin hankali ya shiga tsakani....
(Haka gidan sarauta yake,kowa na kokarin minding business dinsa)

********

"Juwairiya ba karamin jigata tayi ba dan har tafin kafarta sai da duk ya fashe jini nata fita..
  Surayya ce ta shigo wajen tare da umayma a bayanta..
Sarkin dorina ta kalla..
Ina fata ka samo min amsar tambayata..waye wannan mutumin da aka kama ta da shi jiya!!!!

    "NI NE NAN"
taji an fada daga bayansu...
Gaba dayansu suka juya cikin tsantsar mamaki suke kallonsa....
surayya da umayma idanuwansu kamar zasu fado kasa...

   Bakinta na rawa tace....
Dama kaine...?

Ya karaso har gabanta yace..
NI NE na kirata jiya daddare..

Surayya ta kura masa ido..

TURAKI ya daure fuska sosai...
Ni banga wata hujjarki na hukunta ta ba dan kawai tabi umarnina...
Dan haka inaso kiyi gaggawar dauke hukuncin ki a kanta...
  Surayya cike da bakin ciki take kallon shi..
Toh miye alakar ka da ita?
Me kake yi da ita acikin dare kuma a lungu?

  TURAKI ya fusgar da iskan bakinsa..
Cikin kakkausar murya yace....
SONTA NAKEYI...
Gaba daya wajen aka kura masa ido ciki tsananin mamakin furucinsa..
Surayya ta runtse wata zuciyar na mata dadi wata kuwa bakin ciki takeyi,taso sosai juwairiya ta fadi sunan jalal dan ya tsane ta har abada..
Amma wannan turakin yazo ya bata mata shiri mtsw...

Turaki ko a jikinsa ya karasa gaban juwairiya da har ta suma sbd tsananin azabar data sha..
   Yana kokarin daura hannunsa a jikinta..sukaji shamaki na sanar da shigowar SARKI JALAL (wanda yaji furucin Turaki har cikin kwarewarsa )...............



Not edited


TEAM RUMFAR BAYI

 *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 30
Wattpad @afreey101


*****************

"A mutukar fusace sosai Jalaal ya shigo wajen cikin tsananin bakin ciki da konar rai.. zainaba na biye dashi a bayansa..

Ai gaba daya jikin surayya ya shiga rawa..
Batayi tsanmanin lbrn nan zai je ga kunnen sarki ba dan kuwa ba karamin laifi bane ace matar sarki ta yanke hukunci a kan bayinsa ba tare da izinin sa ko masaniyar sa ba akai ...

       Jalal bai yi wani tunani ba ya wanke ta da mari mai rai da lafiya...
  Surayya ta dafe kuncin ta tana kallonsa cike da tsananin mamaki da takaici..

Jalal fuskar nan a daure ya kalli sarkin dorina da shima jikinsa ya fara rawan...yace,
Wato harda kai za'a hada kai a aikata irin wannan (abomination)din a karkashin mulkina!!!!!?

Sarkin dorina yayi saurin zubewa a kasa yana neman gafara awajen sarki hakama sauran bayin dake wajen..
Jalal ya kallo gefen da juwairiya take a kwance bata lumfashi runtse ido yayi cike da kunci sosai...duk shine ya jawo mata shiga cikin wannan halin..dolene yayi abunda ya dace..

Har ya yunkura dan zuwa gareta wata zuciyar ta shiga gargaden shi...
"(Idan har kayi kuskuren aikata haka a gaban jama'a a yanzun,toh ba karamin bakin jini zaka jawo mata ba,a hakan ma surayya tayi mata wannan danyen hukuncin...
toh balle idan ka bayyana sonta a bainar jama'a,ai ko mahaifiyar ka gimbiya kilishi ta isa ta cutar da ita)"

   "Surayya ta kalleshi rai a bace..
Sannan ta juya da gudu ta bar wajen cikin bakin ciki da takaici ...umayma tabi bayanta..

Jalal ya kalli zainaba yace,ku dauke ta daga nan a kira me magani a duba ta..yana gama fadar haka ya fice da saurinsa dan bazai iya jure ganinta a cikin wannan halin ba..

"Hansai,laure,jakadiya da lbr yaje musu acan rumfar bayi ba kamarin tashin  hankali suka shiga ba,gaba dayansu damuwa da tausayin halin da juwairiya ta shiga sukeyi..

hansai na kuka sosai tace,dama ashe juwairiya ce ake fada? naji lbrn nan tun dazun a sashen gimbiya kilishi amma zuciyata bata kawo min juwairiya bace ko kadan?

'Dubu tace wlh nima naji lbrn nan yana yana ta yawo a tsakanin bayi acikin rumfar bayi amma ban taba tsanmanin juwairiyar mu bace tunanina tana can wajen aikinta..

Laure tace,ni abunda ban gane ba anan shine..
Me juwairiya tayi wa surayya haka ne?
Jakadiya ta jinjinar dakai sannan tace mu karasa can rumfar hukunta bayin na tabbata zainaba zata ceto mana juwairiyar mu..

Suna karasawa suka hango rabi da zabba'u dauke da juwairiya ga kuma zainaba da turaki a bayansu..
   Da sauri sukaje suka kama musu ita suna kuka sosai suka nufa rumfar bayi da ita....

*****
"Jalal na shiga sashen sa ya kasa zaune ya kasa tsaye,zuciyarsa yake ji tamkar zata fashe..

      Babu abunda ya ke dawo masa a kwakwal'warsa sai furucin Turaki na dazun..INA SONTA?
Yaushe turaki ya fara son juwairiya? Yaushe hakan ya faru?itama tana sonshi

Yanzu menene mafita a wajensa, yana nan a zaune kaninsa zai dauke masa macen da yakejin sonta kamar ransa?
Inaa bazai bari hakan ya faru ba,dan a yarda yake jinta acikin zuciyarsa,bazai taba iya hakura da ita ba...

Tunaninsa ne ya katse jin mgnr jakadiya a kusa da shi..
  A sanyaye take kallonsa tana tausayawa halin da yake ciki sosai..

"Dan kawai yana a matsayin sarki shine bazai iya samun damar fitowa ya nunawa masoyiyar sa irin son da yakeyi mata ba..
Sbd wani mulki... oh wasu kuma har kwadayin mulkin nan suke....taja lumfashi kafin tace..
      Ranka shi dade ka kwantar da hankalinka..
juwairiya na samun kulawa sosai a wannan lkcn..

Jalal ya juyo ya kalleta da idanuwansa da suka canza launi..
Jakadiya tace..
Dama wani bawa ne yazo daga sashen tsohon sarki Abdul-Jabbar,ana neman ka acan..
Jalal jiki a sanyaye ya sake shiryawa ya fita,yana tunanin me yasa mahaifinsa yake faman sa..

************
"Yana shiga makeken falon ya tarar da family duka a zaune..
Ga kuma surayya acan gefe tana ta kukan bakin ciki,har ita yarima zai daga hannu ya mara a gaban wasu kanskantun bayi?
Toh wlh baza ta sa'bo ba....tafi karfin a wulakanta ta haka!...

'Abban ne ya kallesa ya shigo yayi musu tsaye yana mamakin taron me akeyi haka?..

Ka Samu waje ka zauna AMALE...
yarima ya zauna a kilisar dake gefe fuskantar tasu hamza da turaki..
   Abban yayi gyaran murya yace..

Amale ko zaka iya fada min dalilin da yasa ka marin matarka?
Gimbiya kilishi tayi katsalandar fadin..
Dan ya isa da ita mana..
Abban ya daga mata hannu,ba dake nake mgn ba kilishi..kai kuma ina jiran amsar ka..

Jalal ya dauke kai gefe..sannan ya sanar ma abban duk abunda ya faru..
  Abban ya kalli surayya..yace,
Wai anyi haka?
Surayya ta goge hawayen ta,anyi haka abba,amma ni kawai nayi hakan ne dan na san meke tsakanin turaki da wannan baiwar...bawai nayi niyyar na yanke hukunci da kaina bane..

Abba ya kalli turaki..
Meke tsakaninka da wata baiwa?ko ba jiya bane aka daura maka aure ba?

Ko so kake ka nuna mana bamu isa dakai ba..

Fulani ta shiga hararar Turaki..cike da takaici..
Turaki ya lumfasa, ba haka bane abba..
Ni sonta kawai nakeyi abba kuma inaso ku bani dama dan na YAN'TAR DA ITA...

   Jalal yayi saurin kallon sa..
Zuciyarsa na mutukar harbawa..
Surayya tayi wani irin shu'umin murmushi dan tana lura da irin yanayin jalal ya shiga.

    Samira kanta tayi mamakin furucin sa,wai mijinta ne ke son wata baiwa har haka?
oh ashe shiyasa yake yawan zaman tunani?
ko a jikinta ita kam dan tausayi ma ya ke bata sosai yarda aka saka shi a gaba ana masa tambayoyi..

   Abbah yace,kasan me kake fada kuwa?
Turaki ya zube kasa...
Dan Allah abbah ku taimaka min..na dade ina fama da sonta..
tun tana yar karamar ta Allah ya daura min sonta..
Wata irin tsawa fulani ta daka masa..
"TURAKI!

Yayi shiru yana zubar da kwalla..
Jalal mutuwar zaune kawai yayi..
Dama haka turaki ke son juwairiya?

   Fulani ce ta mike tazo ta wanke sa da mari..
Baka da hankali ne?
Me na fada maka uhm!
Gimbiya kilishi ta hau murmushi,ai dama dolene mu ringa fuskantar irin haka...tarbiyyar gidan sarauta bata ishe ka ba turaki..ka yan'ta baiwa ka aure ka a matsayin me...?
   Turaki yace,MATATa mana..

Abbah yace duk ku tashi ku fita idan na yanke shawara zuwa anjima zan neme ku..
Gaba daya suka mike suka fita cike da al'ajabi...

     Da daddare abban ya sakeyin kiran su..
  Ya kalli jalal..
Inaso ka bada izinin ka,turaki ya yanta wannan baiwar a gobe...
     Ga baki daya sai da gabansu ya fadi..sunyi mutukar mamakin yarjewar mai martaba Abdul-Jabbar..

Mamaki sosai ne ya rufe su..
Zainaba kuwa murna kawai takeyi,ji take kamar ta tashi tayi rawa dan farin ciki..

  Jalal ya rasa meke masa dadi..
Yana nan zaune juwairiya na neman subuce masa..
Kamar me koyan magana a haka ya bada izininsa,ko ba komai ya samu yin abunda ya dade yanaso yayi mata,wato ya yanta ta daga bauta..
    Surayya bakin ciki sosai ya rufe ta..
Koda ta koma sashenta...
Umayma ce tare da tulin tambayoyin ta.
Surayya taja tsaki kafin kawai tace,ki shirya zamu fita yanzu....

************

"Juwairiya ba karamin jiki ta sha ba dan har se da tayi awa daya bata farfado ba..
Kuka sosai takeyi tana jin azaba da radadi a gaba daya jikinta..

Hansai kanta kukan takeyi tana lallashin ta data sha magani..
Rabi da zabba'u na gefe duk sun buga uban tagumi suna tauyawa kawar tasu..
juwairiya har cikin zuciyarta batayi nadamar rashin fadin sunan jalal da batayi ba..

Oh ! ko yana ina yanzu?a wane hali yake ciki?ta tabbata hankalinsa a tashe yake...

Jakadiya ce ta shigo da wata me magani a bayanta da yarima ya sakata taje ta dauko ta..
Me maganin ta hau duba juwairiya..cike tausayawa.

**********
"Samira ta kurawa turaki ido ganin yarda yake ta faman sauke ajiyar zuciya..

ba karamin fada yasha a wajen fulani ba wai yana son ya zubar mata da mutumci ya juyawa yan uwansa baya akan mace.
ita ba wai yantar da juwairiyar da yayi bane damuwarta,ah ah furta Auren ta da yayi shine bacin ranta,duka duka jiya aka daura masa aure ko yan uwan matarsa basu gama watsewa ba yake so ya ballo musu ruwa...

   Samira ta tausaya mishi sosai dama haka So yake?
  Ta dawo gabansa ta tsugunna tace..
Turaki inaso na baka wata shawara idan bazaka damu ba..
Turaki ya dago yana binta da kallo..
Tace na tambaye ka?
Yayi shiru..
Samira taci gaba..
Ita baiwar da kake so din ka tabbata tana sonka ne?
Ko kuwa dai nuna mata iko da mulki zakayi ka aureta a cikin rashin damuwa da(feelings)dinta..

   Turaki ya kura mata ido yana wani nazari,tabbas yasan juwairiya bata son sa,dan da tana son sa da zai gane tuni..,yasan dai ta dauke sa a matsayin yayanta ne amma baya tsanmanin tana SON SA...

    Samira ta jinjina kai,yanayin ka ya tabbatar min da cewa ba sonka takeyi ba...
Ta riko hannunsa..
Idan zan fada maka cewa kaima ba sonta kakeyi ba zaka yarda da ni?

Turaki ya girgiza kai..yace..
Sonta nakeyi samira ba zaki taba ganewa ba..
yarinyar nan tun tana yar karamar ta take aikin bauta a rayuwarta,bata san wani jin dadin yarinta ba da kowane yaro yake samu..
bata da wani yanci ko zabi a rayuwarta,haka ta taso a cikin RUMFAR BAYI  babu wani digon farin ciki a rayuwarta..
Dan haka idan auren tane kawai zai sa na fitar da ita daga wannan rayuwar da take ciki toh zan iya sabawa da duk yan uwana dan nayi hakan..

Samira tayi murmushi lallai Allah yayiwa turaki zuciya me kyau..
  Tace,TAUSAYINTA kawai kakeyi turaki..

Dan haka a shawara ta indai har kana son kagan ta acikin farin ciki toh lallai ne ka YAN'TAR da ita kawai daga bauta amma kada kayi kuskuren danne mata hakki kace zaka aure ta...
Tana gama fadar haka ta mike ta fice...
Turaki ya shiga nazarin mgnr samira..

*********
    Jalal na kwance a kan gadonsa zazzabi ne sosai ya lullube sa...
  Khadija ce ta shigo dakin..
Ganin halin da yake ciki ba karamin tsorata tayi ba..
Da sauri ta fita tayi sashen gimbiya kilishi dan ta sanar da ita..

Hankali a tashe gimbiya kilishi ta shigo sashen nasa..
     Tausayi sosai ya bata,dan tasan ko da yana karamin sa baya son ko kadan mahaifinsa yayi masa fada akan gaskiyarsa...lallai dole ta koyawa surayya hankali,dan duk sbd ita ne haka ya faru..
Me magani aka kira ya shiga duba sa..
Khadija na gefe tana masa sannu..

*******
Mutanen ku kuwa su umayma...

Wani kauye sukaje can kusa da SANDAMU a nan suka samu wani malamin tsabbu..
   Surayya ta fayyace masa komai..
Dariya yayi ya buga kasa yace..
Ni ban ga wani aure a tsakanin wannan baiwar da kanin mijin naki ba...

Sai dai kuwa naga wani haske a tattare da yarinyar..
Surayya taja tsaki..ya wuce na yan'cin da take

Please Login or Register in order to submit comment