Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abunda ya kawo mu sai dai a tunani na kai ma kasan abunda ka aikata ba zai....

Yarima ya tsayar dashi..
Na sani magaji,ba zai amince da deal dinmu ba...amma inaso dan Allah kada wannan lbrn yakai wa su mai martaba ko umma...
Magaji ya gyada kai kada ka damu zan gargadi dukka bayin da mukaje dasu..
Yarima yace yauwa sannan ya koma ya sake kwanciyarsa..
Magaji ya mike ya fita kice da tambayoyi a cikin zuciyarsa...

"Har dare ya tsala sosai juwairiya na takure a gefe tana fitar da kwalla, se yanzu ne ta fuskanci duk abubuwan da su ummanta ke fada mata..

Ita dai Tsoro takeji sosai,addu'ar ta daya Allah yasa gobene komawarsu, ta koma rumfar bayin ta wajen su ummanta masu sonta,Allah kadai yasan halin da zasu shiga idan sukaji abunda ya faru da ita yau....

Yarima ma dai bai samu barcin ba ko kadan,duk yarda yaso ya samu runtsawa kasawa yayi,yana nan kwance shiru..

Can ya mike yana fadin,ko ta bar kukan yanzu?
Ya ja lumfashi hade da mikewa ya saka riga ya fito waje..

   A gaban kofar su ya tsaya yana rike da kugunsa,kodai har tayi barcin ta ?
Yana kokarin juyawa yaji shashshekar kukanta daga cikin dakin...

Tsayawa yayi kawai ya rasa me ya kawo sa wajen ma?zuwa zayyi ya lallashe ta ko me?shi yarima jalal ya lallashi mace!!!!
inaa... ai hakan ze zubar masa ki'ma da girman sa ne...yadanyi tsaki yana jin kukanta na ratsa shi a sanyeye ya juya ya koma dakinsa..

***************
"Da safe idanun juwairiya duk sun kunbura dan bata samu runtsawa ba a wannan daren..
Har suka gama shirin su Rabi se faman sake lallashinta takeyi..

  Suna gama shirin ne magaji yazo ya sanar Musu da su fito za'a tafi yanzu,juwairiya tayi mamaki da yarima bai kirasu hada masa ruwan wanka ba da safen..

  " A tsaye gaban mota suka tarar da shi ya jingina, fuskarsa kawai zaka kalla ka fahimci baya jin dadi sosai..

Juwairiya ta kura masa ido,ya taimaka mata jiya taimakon da ba zata taba san yarda zata gode masa ba...

Ji tayi magaji na fadin,yarima ya jikin naka?kodai mu kara kwana ne sai ka kara jin sauki tukun?
Gabanta taji ya fadi,bashi da lafiya me ya same shi?kodai ta jawo masa wani babban matsalar ne jiya?
   Rabi taji tadan taba ta,suka shiga cikin motar su hankalinta na kan yarima...

**************
"Tafiya kawai sukeyi amma juwairiya tunanin yarima takeyi,ta rasa me yasa takejin tausayinsa dan bashi da lfy,tasan ita ba kowa bace a wajen sa,kodan ya taimaka mata ne jiya oho..

Lokacin da suka iso kasar daura dare ya tsala sosai..
  Suna fitowa daga cikin mota juwairiya ta hango yarima yayi sashen sa yana tafiya kamar bayaso...

    Lumfashi ta sauke,ko ya jikin nasa yanzu?
Wai meke damunta ne,yarima ne fa,yarima jalal,me jiran kujerar mulkin kasar daura,yana da wadan da zasu damu dashi da suka fi ta mahimmanci da daraja a rayuwarsa..

  Gyada kai tayi,dan kawai ya taimake ni shiyasa na damu da lafiyarsa,ta saki lumfashi tana murmushin jin dadin dowawar ta,kullin kayanta ta dauka tayi rumfar bayi da gudun ta..

Tana shiga duk suka zo suna rungume  ta cike da murnar dawowar ta,hansai ba karamin dadi taji ba ganin diyar ta dawo lafiya...

******************
   Washe gari..
Yarima ne zaune a gaban mai martaba..
Sannunku da dawowa jalal ina fatan kun dawo mana da labari mai dadi..

Yarima ya gyada kai,amma munyi dashi akan zai neme mu idan ya yanke shawara..
Mai martaba yace,babu damuwa sai mu jira shi muji ai...
Yarima ya mike daidai lkcn da aka sanar da shigowar su Turaki tare da zainaba..
       Zainaba ce ta fara gaida shi,a sanyaye ya amsa mata,suka gaisa da turaki kafin ya fito daga bangaren...

"Hango ta yayi a tsaye tana wasa da yatsun hannunta da gani jiran zainaba takeyi a wajen.

  Haka nan yaji wani sanyi ya ratsa sa hatta ciwon kan da ya tashi dashi se yaji ya tafi bat!..

     Ita kam juwairiya tana tsaye ne amma sai taji kamar ana kallonta..
Ta dago a hankali....

Sai Hango shi tayi cikin kayan alfarma kamar kullum,amma mai?sai kawai taji zuciyarta na ayyana mata cewa "yayi kyau"

Ta girgiza kanta da sauri ta sake yin kasa da kanta tunda tasan ya tsani ganin fuskarta...
Shi kuwa yarima tana yin da kasa da kai sai yaji wani iri,ya tuna yarda yake kyamatar ta a baya..
      Juyawa yayi a sanyaye ya fice...
********************
"Surayya na gani a tsaye a gaban sashen yarima,gaba daya hankalinta a tashe yake tunda taji ance ya dawo da zazzabi jiya bata runtsa ba..

     Tana hango shi ya tunkaro sashen tayi saurin zuwa wajen sa..
Yarima ya jikin ka?
Ya kalleta kawai yayi gaba ya shige ciki..
  Surayya ta kalli baiwar dake bayanta,ki jira ni a nan,itama ta shige ciki da saurinta...

     Yarima ta iske a kwance yana kallon sama...
Ta shigo ta zauna a kusa dashi tana kai hannunta saman goshin sa,zafi taji rau,da sauri ta dauke hannun tana kallonshi cike da tausayawa, a shagwabe tace,zazzabi ne fa a jikin ka..

Yarima ya lumshe ido,shi kansa ya rasa dalilinsa na kin shan magani tun jiya,duk runtse idon da zayyi se ya hango abunda ya faru tsakanin wannan yarinyar da mutumin nan,me ke damun sa ne haka?

   Surayya tadan turo baki,ka tashi muje sashen umma kasha magani,kasan dai idan taji baka da lfy kuma baka sha magani ba hankalin ta ne zai tashi...

Yarima ya bude ido ya sauke su akan surayya,me yasa bazai so ta bane?
Hannu yasa a sanyaye ya shafa gefen fuskarta..
Surayya taji wani irin yaar a gaba daya jikinta..se kallonsa kawai takeyi..ko me ya same shi haka kuma oho?

   Ka tashi...ta sake fada a sanyaye. .
Yarima ya mike zaune yana fadin..
Kije ki turo min da me maganin kawai..
Surayya cike da murna tace,da gaske?
Yarima yayi banza da ita yana juya mata lulu eyes dinsa..
Ta mike da sauri tayi waje..
Shi kuwa yabi bayan ta da kallo....

" _Kuyi hakuri baku ji ni ba jiya,data na ne ya kare,idan nayi subscription zaku ringa jina akan lkc"_

Please
Vote

[9/18, 3:14 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 15
Wattpad @afreey101


************

".....Bayan sati biyu...."

    "Juwairiya na zaune a cikin RUMFAR BAYI, lkcn karfe goma na dare ne amma a cikin rumfar se ka rantse da Allah ko shidda ta yamma batayi ba.
dan kuwa sai a lkcn ne suke samun yin duk wata hidimar kan su,irin su wanki,kitso da sauran su...

    " Rabi ce ta kalleta tana jefa gyadar dake hannunta cikin bakinta..
Ya dai juwairiya kinyi shiru sai mgn nakeyi kin wani share ni...

Juwairiya tayi dan firgigit ta dawo daga duniyar tunanin data tafi..
Kai Ina fa kinji rabi,kikace mai ma?
Rabi takai mata dukan wasa,ai dama nasan uwar shegu kikayi dani..

Laure ce ta karaso wajensu da yan kayanta a hannu..
   Juwairiya ta kalla tana narke murya,diyata ga ka'ron wankina..
Juwairiya ta zunboro baki,goggo laure duka duka fa sati biyu kenan danayi miki wanki..

Laure tace,ke yar gari yo ni wanki har nawa nayi miki da kina yar jaririyarki uhm!
Juwairiya ta juyar da kai,laure takai mata duka tace,ni kike juyawa ke'ya?yar fama kawai..

Hansai ce ta karaso wajen nasu, ta kamo hannun juwairiya, sannan ta kalli laure,babu ruwanki da diyarta ,wanki kuma bazatai ba,ai ba ajiyeta kikayi ba,muje ya'ta,laure ta rike baki,ni hansai?ni hansai?lallai ina nan zamana zaku dawo ai,kici gaba da shagwaba ta kema sai tace baki isa ba... ta ja tsaki ta juya tayi gaba..
Juwairiya da hansai suka shige daki suna mata dariya..

**************
"Da sassafe ranar alhamis juwairiya tayi shirin ta tsab sannan ta wuce wajen uwar dakin ta..

Tana shiga sashen zainaba ta same ta a zaune..
Ta gaishe ta tana kokarin shigewa ban dakine zainaba tayi saurin kiranta..
Juwairiya zo kiji..

Tazo ta duka har kasa tace gani..
Zainaba tace so nake kije min gidan waziri ki amso min wasikar da Mustapha ya aiko min da ita jiya,juwairiya tayi murmushi wato baki manta da ranar ta yau ba kenan?

Zainaba ta murmusa tana gyara zaman ta,ni kaina mamaki nakeyi wlh,kullum cikin addu'ar Allah ya kawo min wannan ranar nake,tunda yace min ze aiko min da lambar wayar su ta landline gaba daya na zaku dana kira naji muryar sa..

Juwairiya ta saki baki cike da mamakin kalaman zainaba..
Zainaba ta taso ta rufe mata bakin tana dariya..
Juwairiya tayi murmushi sannan ta mike tace toh bara naje na dawo, da sauri ta juya ta fice.....

**************
"A nutse take tafiyar ta har ta fito babbar kofar masarautar,can ta hango su a tsaye tare da wani bawa (wato yarima da magaji kenan)
Da sauri ta dauke kanta sannan ta karawa tafiyar tata sauri...

   Magaji ne ya fara hango ta,ya kalli yarima yana sosa kashin kansa yace,ni fa wancan yarinyar se na riga gani kamar na santa a wani waje..

  Yarima ya kalli gefen da magaji ke nuna masa...
Can ya hango ta sai buga sauri takeyi kamar zata tashi sama..
"Ina zataje?"
Ya fada acikin zuciyasa...

Magaji ne ya dafa sa ganin hankalin sa baya tare dashi..
Muje mana kasan fa yau inna ta hada abinci damu kuma tace dole na taho dakai,rannan haka kayi min wayo naje nasha fada na..
Yarima yayi murmushi dan kuwa yana jin dadin abincin innar sosai,kai fa ka cika korafi dayawa,ko ranar ma ai umma ce ta tsare ni a sashen ta,magaji yace,naji din muje dai kada muyi rana....
  
"Juwairiya har tayi musu nisa sai ji tayi kawai ta taka wani abu a kafarta..
da sauri ta dage kafar tana sakin ihun azabar da taji..
Waje ta samu ta zauna tana dago da kafar ta duba me ya tsake ta haka..
    Wata kwalba ce kuma ba kadan ba ta fasa mata kafar se jini ke fita..
Kuka sosai juwairiya keyi tana rike da kafarta ta...

*************
Yarima da magaji na tafe suna yar firar su sai jin shashshekar kuka zasuyi acan gefen hanyar..

Magaji ya girgiza kai,yanzu haka yaran nan ne masu guje guje a hanya..
Yarima yakai dubansa inda sautin kukan ke fitowa..
    Caraf ya hango ta a zaune rike da kafarta se jini ke fita...

   Gabansa ne ya fadi..
Me ya same ta?
Da gudunsa ya karasa wajenta magaji na kiran shi amma inaa...bai ma san yana yi ba..

Juwairiya kuwa ji kawai tayi ya fisgo kafarta..
A tsorace ta dago tana kallonsa cike da  mamaki..

'Yarima?'...ta fada a ranta...
Ai da sauri ta kwace kafar ta zube kasa a mutukar tsorace...
Kayi hakuri ranka shi dade,amma kama kafar baiwa iri na kaskanci ne a wajen ka...

Yarima ya tsaya yana kallonta,tun daga kan kafafunta da babu ko takalmi,zuwa kayan jikinta kodaddo
har kan fuskar ta...

Lallai ko mahaukaci ya kalleshi ya kuma kalli juwairiya sai ya fahimci level dinsu ba daya bane ko kusa,yarima yafi karfin yarinya irin juwairiya, ko ma a matsayin SA'DAKARsa bata kai ba..
Amma meyasa ya damu da ita ne haka?

Ya mike tsaye yana daure fuska,sannan yana jin haushin abunda ya aikata yanzu..

Juwairiya taji yayi shiru hakan yasa ta dago tana kallonshi..
Ita yake kallon shima,da sauri ta maida kanta kasa tana jin azabar zafi a kafarta...

Magaji ne ya karaso wajen shima..
Lafiya yarima wai baka ji ne ina ta kiran ka?
Turus yayi ganin yarima tare da wannan half burned face din...

    Juwairiya ta sake fadin,ka gafarceni ranka ya dade nayi sanadiyyar tsayar daku daga uzurinku,tana gama fadin haka ta shiga kokarin mikewa tana matse baki...

     Ji tayi kawai an kamo hannunta...
Ba ita ba har magaji se daya kalli yarima da mamaki..
  Yarima ya maida ita inda take a zaune...

Wani kyalle ya fito daga cikin alhujin wandon sa ya mika mata..
Juwairiya duk a tsorace take,wai meke damun yarima ne?me yasa yake yi mata haka?bai san cewa yafi karfin ya kyautata mata bane?

Me yasa yanzu yake nuna kulawa a gareta?ita dai tsoro takeji idan aka gansu a nan fa?wayyo Allah idan gimbiya kilishi taji wannan lbrn kashin ta ya bushe...

    Yarima kallonta kawai yakeyi jikinta har rawa yake sbd tsoro,idanunta cike da kwalla.
Ya ajiye mata kyallen a jikinta sannan ya mike tsaye baice komai ba yayi gaba...
Magaji ma yabi bayansa...

Kallon kyallen tayi se fitar da kamshi yakeyi,me yasa ya ajiye mata shi?
Ta shaki kamshin dake jiki...
Yarimaaaa me ke damunka kwanan nan ne?
Har ta mike taji kafarta na mata zugi,ta kalli kyallen yarima se lkcn ta fahimci me yasa ya bata kyallen,dan ta daure kafar ta ne..

Ina zata iya saka wannan kyallen me kyau da tsafta ta daure kafarta me datti..
Wani ganye ta dauka ta yagi rigarta kadan ta daure kafar dashi...sannan ta fara tafiya da kyal da kyal tana rike da farin kyallen a hannunta...

**************
Inna na zaune a tsakar gida tana dibar ruwa a cikin kofi su magaji sukayi sallama suka shigo..
Da fara'ar ta sosai ta amsa musu tana zolayar yarima..
Ango shikenan sai aka yarda mu ko?
Yarima na murmushi ya zauna akan taburmar dake shinfide a tsakar gidan..

   Magaji ne ya amsa innar da cewa..
Inna baki ga har wani haske ya kara bane?
Inna tayi dariya,sannan ta kwalawa khadija kira..
    Khadija kuwa dama tana jin muryarsu ta jawo kayan kwalliyarta ta shiga shafe shafenta..

Inna na kiranta ta gyara kayan jikinta ta fito...
Idanunta kyam akan yarima...tace..
Ya jalal ina wuni?

Ya dago a hankali yace lafiya kawai yana tunanin ko wannan sukuwar yarinyar ta gane manufarsa na bata kyallen oho..

  Inna tace maza khadija shiga madafa ki dauko musu abincin su..
Khadija ta juya cike da yanga zata shige madafar kenan taji muryar juwairiya tana rangwada sallama...

Da sauri ta juyo tana kallonta..
  Yarima da magaji ma sunyi mamakin ganinta a gidan...
Idanun yarima a kafarta suka sauka..
Ganin babu kyallen se wani ganye a kafarta yasa yaji wani iri a zuciyarsa,yasan tsoro ne ze hanaka daure kafar dashi...

Amma hakanan se yaji babu dadi..
Har zai dauke kansa ya hango kyallen a hannunta ta rike shi gam cike da daraja..
Murmushi kawai ya saki ba tare da ya sani ba..

   Juwairiya ta karasa ciki tana gaisar da inna..
Inna ta amsa mata a sake tana tambayar ta me yasame ta a kafar..

Kwalba ce na taka..
Ta fadawa inna a sanyeye..
Yarima kuwa gaba daya hankalinsa na kansu..
   Khadija ta shige kicin ta dauko musu abincin ta ajiye a gabansu,sannan ta karasa wajen juwairiya tana fadin,ayyah JUWAIRIYA sannu...

Yarima yaji gabansa ya buga JUWAIRIYA ya maimaita sunan,dama sunan ta kenan?ashe tana suna?wani irin dadi sunan yayi masa....JUWAIRIYA maimaita sunan babu adadi a cikin zuciyarsa......

"Khadija kuwa sbd ta burge yarima yaga ita me tausayin bayi ce,sai ta ce,zo ki zauna na saka miki magani..

Ta jawo hannun juwairiya..
Juwairiya ta shiga girgiza kai ah ah ki barshi kawai babu komai,sakon zainaba ne nazo na amsa nasan tana jirana sauri nakeyi...

  Khadija zatayi mgn se ji sukayi ance...
"Me yasa kika fiye gardama?!
Da mamaki duk suke kallonsa..
Ya dauke kai yana bude kwanon dake gabansa...kamar bashi ne yayi mgnr ba.

Khadija mamakine ya kashe ta,wai yau yarima jalal ne da kansa ke tsoma baki acikin mgnr da bata shafe shi ba,mai?"me yasa kika fiye gardama" yau she yasan juwairiya da har yasan ta fiye gardama din?oh!tafiyar su ko?toh amma a yan kwanakin ne har yasan ta haka?kishi ne ya cika zuciyarta..

  tunani kala kala khadija keyi har bata lura da inna harta bawa juwairiya wasikar ba ta mike zata fice..
Da sauri ta sha gabanta,haba juwairiya baki ga yarda kafarki ta fara kunbura bane?ta fadi da yanayin tausayi tana kallon yarima da gefen idonta..

Juwairiya ta dan kallo inda su yarima suke zaune har sun fara cin abincinsu..

Hada ido sukayi dashi,tana kokarin dauke idonta taga ya mata wani irin kallo,hakanan taji gangar jikinta ta fahimtar da ita me kallon nasa ke nufi.. (na amince da taimakon khadija)
Khadija tace muje mana...
Nagode juwairiya ta fada ta dawo ta zauna..
  
Khadija ta juya gunsu yarima tana matse muryarta tace..
Ya magaji ina wannan maganin naka?
Magaji yace ki duba cikin dakina..
Khadija ta mike ta nufi dakin..
Magaji kuwa mikewa yayi shima dan karo musu miyar fankasun da suke ci..
   Aka bar yarima da juwairiya a wajen su kadai........



_"Team RUMFAR BAYI ina gaisuwa,nagode da addu'o'in da kuke yimin,sannan ina ganin comments dinku i rlly appreciate alot,thanks alot,Allah yabar zumunci.._

*Team juwairiya*90%
*Team yarima*70%


Keep
Sharing
Voting
And
Commenting
[9/18, 3:14 PM] Aysha Galadima:           *RUMFAR BAYI*
      (A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 16
Wattpad  @afreey101


*****************
"Me yasa bakiyi amfani da kyallen dana baki ba?"

   Juwairiya taji muryar sa me dadin saurare a bayanta yana mgnr kamar bayaso dan itama zuciyarta na wajensa da bazataji me yace ba..

  Juyowa tayi kanta a kasa kafin tace a sanyeye..
Kayi hakuri ranka shi dade amma bazan iya daure kafata da abunda ya fito daga hannunka ba,dan ko kadan ban kai wannan matsayin ba..

  Yarima ya jinjina kai..sannan yace da ita,
Daga yau duk umurnin dana baki ina so ki bi shi inda har kin dauke ni a matsayin da nake din..
juwairiya ta gyada kai da sauri..

Kinci abinci?
Tambayar tazo mata a ba zata..

Juwairiya taji kamar ta nutse,miye na sa wai idan taci abinci ko bata ci ba..
  Girgiza kai tayi..

Yadan ja lumfashi idan kin koma cikin masarauta ki same ni a sashena...
Zatayi mgn taji karasowar khadija...
Khadija ta mika mata maganin tace ta shafa,ta amsa da hannu biyu ta shafa ,sannan khadija da kanta ta daure mata kafar..
Godiya sosai juwairiya tayi mata sannan ta fice....

***********
"Har ta kai wa zainaba wasikar amma ta rasa taya zata je sashen yarima,me yasa yace mata taje?tunani ne ya cika ta sosai har bataji firar da zainaba ke mata ba..

  Zainaba na lura da ita tace,lafiya juwairiya ko kafar ce?..
Kije kawai ki huta zuwa anjima.
zansa fulani ta aiko min da wata baiwar..
Juwairiya ta samu kanta da jin dadin hakan..
Ta mike tayi mata godiya kafin nan ta fice..

***************
"Tana fitowa daga sashen sukaci karo da turaki zai wuce ..
  Tayi saurin gaishe sa..

Ya amsa yana kallon kafarta..
Ciwo kikaji ne haka?ya fada cike da kulawa..
Juwairiya tace eh dazune wlh..
Turaki yace ayyah,muje na baki magani kiyi amfani dashi..
Juwairiya zata fara mu'sa masa sai kawai yayi gaba,dole tasa ne tabi bayanshi..

'Tafiya kawai takeyi,amma hankalinta na kan umurnin da yarima ya bata na zuwa sashen sa...
      Suna shiga sashen a bakin kofa taja ta tsaya,turaki ya shiga ya fito mata da maganin,amsa tayi tana masa godiya...

Turaki ya saki murmushi yace, ki rin ga kula da lafiyar ki..
Juwairiya ma murmushin tayi tace nagode sosai yaya turaki..
Juyowar da zatayi ta hango yarima da hamza a tsaye zasu wuce..

  Idanuwansa a kanta..
Gaba daya taji wani irin faduwar gaba..
Yarima ya dauke kai kamar bai gansu ba yayi gaba abunsa...

********
"RUMFAR BAYI ta nufa kai tsaye babu wadu bayi dayawa a ciki,dakin du'bu ta shiga,ta tarar itama bata nan..
Komawa tayi dakinsu ta canza kayan jikinta sannan ta zube akan taburma.

    Da sauri ta mike ta dauko kyallen da yarima ya bata dazu tana kare masa kallo,wata zuciyar na tunashe ta  umurnin sa na zuwanta sashen sa..
Ta mike da sauri ta fito kai tsaye tayi sashen nasa..

   Ta dade a waje tana tunanin ko kada ta shiga..
    Can dai ta tayi shahada ta shiga tana addu'a Allah yasa ba wani laifin tayi masa ba.
bawan dake waje ne ya sanar da shigowar ta...
    A sanyaye cike da tsoro ta shiga falon da sallama..

   Zaune yake ya lumshe idonsa..
Ta samu waje ta takure sannan tace..
Ranka shi dade gani nazo..
Har cikin ransa yaji sautin muryar ta..
A hankali ya bude ido ya sauke su akanta..

  Juwairiya tayi saurin dukar da kai..
Yarima yace,zauna yana nuna mata waje a nan kusa dashi kadan..
Juwairiya ta kalleshi taga yarda ya tsare gida dole yasa taje ta zauna wajen a takure..

Yarima bai bata lkc ba ya kwalawa bawansa kira..
Se gashi ya shigo cikin saurinsa..
Yarima ya fada masa dayaje ya sanar da du'bu a can rumfar bayi a kawo masa abincinsa yanzu..
Bawan ya amsa da toh kafin nan ya fice..

Juwairiya dai ta rasa me zatace masa,yace  mata tazo sashen sa amma ya ajiye ta a nan yayi shiru,ga ciwon dake kafar ta yana dan damunta kadan kadan...

A wajen Yarimakuwa  ya rasa meke damunsa,me yasa yake son ganin wannan yarinyar a kullum ne kusa dashi?me yasa ta dame sa har haka?

    Yadan kallo ta, tsoronsa ma takeyi daga gani,yaja lumfashi me dumi,kafi karfin baiwa kamarta yarima...ya fadawa kansa..

      Haka yayi ta tunani a zuciyarsa har bayi suka shigo da abincin jere a cikin tiren silver.
sai faman kallon juwairiya sukeyi cike da mamakin ganinta a sashen.
balle kuma a inda take zaune dan kuwa basu da hurumin zamaa  wajen,balle kuma wai tare da yarima cab...!

    Suna gama shirya abincin suka fice bakin su kunshe da gulma iri iri..

    Juwairiya ta lura da hakan dan kuwa tasan a Rumfar bayi gulma kala kala ake kawo musu..
Ta tabbata sai lbrn zuwanta sashen yarima  ya kai wa ummanta..

   Ta kalli yarima shi kam ko a jikinsa ma..
Mikewa tayi da sauri tace,uhm ranka shi dade bari na zuba maka abincin..
Jiki na rawa ta kai hannun ta dan daukar plate dake ajiye gabansa..
   Sai jin saukar lausassan hannun yarima tayi akan nata..
  Tsikar jikinta ce ta tashi..
Gabanta na faduwa ta kalleshi ido a bude...

Yarima ya motsa bakinsa,duk da shima baisan dalilinsa na taba jikinta ba kawai dai bayajin yin mgn ne kuma yana so ya tsayar da ita daga daukar plate din.
Ki barshi...ya fada yana dauke hannunsa daga nata..
Juwairiya tace toh!
Zan iya tafiya?
Yarima ya girgiza kai ,zauna kici...ya nuna abincin dake gabansu.
juwairiya ta waro ido ta dafa kirji Ni?
Yarima yace me kika dauke ni?Giwa?baki ga naci abinci bane dazun?

Juwairiya tayi wiki wiki da ido,nima zanci anjima...ta fadi kamar zatayi kuka..
Yarima ya daure fuska,umurni ne nake baki ba zabi ba...

A sanyaye ta zauna..
Yarima ya basar abunsa...
Juwairiya ta kalli delicacies din dake gabanta, miyau ta hadiye dan rabonta da abinci tunda safe da suka karya..
  Ta kalli gefen yarima taga ya dauke kai gefe..

Abincin ta diba ta hau ci da saurinta dan ta samu ta tafi da wuri..
   Yarima yayi murmushin gefen baki.
Tana kammalawa ta mike,nagode zanka shi dade Allah ya baka kujerar mulkin daura..

  Ya saki murmushin da bai san lkcn daya subuce masa ba..
Juwairiya mutuwar tsaye tayi...dan bata tunanin ta taba ganinsa yana murmushi haka,kyau da kwarjini yayi mata har bata san ta kafe shi da ido ba..

Yarima ya kalli kafarta...
Na lura kin samu masu baki magani dayawa ko? ba sai na baki wani ba...
  Juwairiya ta dauke idonta tana kallon kafar,murmushi ta saki tunawa da kyallen daya bata dazu..sai ta kwanto shi daga zaninta ta mika masa..

Ga wannan Allah ya baka yawan rai,nagode kwarai da gaske...
  Yarima yabi kyallen da kallo..
Sannan ya mike yazo kusa da ita ya tsaya..
     Bana amsar abunda na bada a matsayin kyauta..
Juwairiya ta dago da sauri,kyauta ya bata?ita juwairiya har ta kai yarima ya bata kyauta?
      Yarima ya lura da mamakin furucin sa takeyi,yace zaki iya tafiya..
Juwairiya ta juya da sauri tayi waje...

*************
"Tana shiga tafe tana tunane tunane,har ta kawo wajen ajiyar dawakai,hango mahaifinta tayi yana bawa dabbobin abinci...
Ai da sauri da gudunta ta karasa wajensa...

Lah baba! Ta fadi da karfi..
Ya juyo cike da farin cikin ganin ta,juwairiya kece haka?
juwairiya ta saki dariya baba yaushe ka dawo?shine umma bata sanar min da dawowarka yau ba?ta karashe mgnr cike da shagwaba..

  Baba ya kamo hannunta,jiya da daddare na samu dawowa,juwairiya tace nayi kewarka baba sosai,ka tafi ka barmu...
Baba yayi murmushi kiyi hakuri juwairiya kinsan fa cewa sarki da kansa ya bani umurnin tsayawa a can kasar kanon ta dabon,sannan shima mai martaba na can yaki barina na dawo kasata akan lkc, yanzu ma haka sati daya kacal zanyi na koma..

Juwairiya ta jinjina kai,su kenan basu da yan'ci sai yarda akayi dasu,gsky BAUTA batayi ba...
Zama tayi a wajen babanta suka sha fira har yamman dare sannan ta koma rumfar bayi...

"Tana shiga laure tazo ta fisgo ta cikin karfi,da mamaki take ta kallon yarda take ta janta  har suka shige daki... hansai na a zaune ta buga uban tagumi...

   Miye haka goggo laure?juwairiya ta tambayeta...
Laure ta kai mata dankwashi akai,ubanki ne !wato ke juwairiya duk yarda muke jan kunnenki ba zaki san matsayin ki ba ko?
  Juwairiya tace,na sani mana...me akace nayi kuma?tayi mgnr a sanyaye..dan tasan ruwa baya tsami banza..

Hansai tace,me ya kaiki sashen yarima?
Baki san waye shi bane? Acikin wannan watan fa zai zama sarkin daura !!!yafi karfin yarinya irin ki!bakya tausayin rayuwar ki ko!???

Juwairiya ta kalli hansai da mamaki,tace sarki?
Laure tace,kwarai kuwa,mai martaba zayyi murabus ya basa mulki kwanan nan!...

Hansai ta kamo hannunta, juwairiya a kullum ina fada miki,ke Baiwa ce!ki kare mutumcin kanki...

Juwairiya tayi murmushin yake,na fada miki umma ki yarda dani,kawai fa sako naje

Please Login or Register in order to submit comment