Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ga irin kamannin da mukeyi ni dake ko?
juwairiya ta gyada kai dan shi yafi damunta,menene hadin ta da wannan matar..

  AMMI tace toh ke JIKATA ce diyar DIYATA fatima data ba'ce shekaru masu yawa da suka gabata...
   Gaban juwairiya ne ya fadi ras!!!!
Muryar na rawa tace..
Am am amma ai ni iyayena na can DAURA,kuma mu bayi ne..

  Ammi ta girgirza kai..
Ta kalli khaleed tace,yanzun nan khaleed ya sanar dani yarda iyayen naki na can sukayi sanadiyyar samun ki...
juwairiya ta waro ido cike da tsantsar mamaki tace,suka same ni!ban gane suka same ni ba,ta shiga girgirza kai,ni ummana ba samu na tayi ba ,haihuwa ta tayi da kanta!!!!

Ammi ta kamo hannunta,ki kwantar da hankalinki,ammi tayi kiran Marka..
Se gata ta shigo..
Shiga ki dauko min zanen (painting )din zarah'u a ciki..
  Marka tace toh uwar dakina..
Marka ta shiga ta fito da wata takarda ta mikawa ammi ita..
Ammi ta amsa ta bude ta mikawa juwairiya...

     Jikin juwairiya ne ya hau rawa..
Ta amshi takardar ta kurawa zanen matar dake jiki ido..
Wani irin abu ne takeji har cikin zuciyarta, tabbas wannan matar tana da alaka da ita,tabbas su hansai samun ta sukayi ba haihuwar ta sukayi ba,me yasa suka boye mata?

"sai ta tuna wani lkc da ummanta ta samu wani sabani da laure,taji lauren na cewa..

"Kin manta ba ke kadai bace me iko da ita?idan baki so asirin da muka dade muna boyewa ya tonu toh ki daina nuna min iyaka ta akan juwairiya tunda dai mu duka suka same ta bake kadai ba"

Kuka sosai ta shiga yi,tana tuna duk wani lkc da tayi dasu hansai,wayyo Allah ashe basune iyayenta na usuli ba...

Ammi ta rungume ta itama tana kukan sosai,tana jin bakin cikin hukuncin da suka yankewa FATIMA gashi yanzu ta tafi ta bar su har abada,diyarta kuma ta ka're a matsayin BAIWA...
 
Sai da suka sha kuka me isar su kafin Ammi cike da tausayawa rayuwar da juwairiya ta shiga tace,ki zauna a sashena har zuwa gobe kakan ki mai martaba ya dawo daga tafiya,zamu sanar dake labarin iyayenki...
Juwairiya ta jinjinar dakai kawai dan ita gani ma takeyi mafarki takeyi...

***
Saida ammi ta bata lkc sosai tasha kuka mai isarta sannan ta kamo hannunta suka shige uwar da'ka..
  Marka ce tare da wata baiwa..
Ammi tace,ina fata kin hada min ruwan?
Marka tace,anyi yarda kika ce ranki ya dade..

Ammi ta kalli juwairiya daga sama har kasanta kafin tace..
  Tube kayanki..
Juwairiya tayi saurin kallonta da jajayen idanuwanta..

Ammi tace,tube mu shiga ban daki kiyi wanka..
juwairiya tace a sanyaye,ai nayi wanka dazun..

Ammi tace,ba wannan wankan zakiyi ba yanzu..
wanka ne zan miki dan na goge duk wani dattin bauta dake jikin ki dan a yanzu kin dawo mahaifarki..

  Juwairiya tayi kasa'ke tana kallon Ammi..
Marka ce ta murmusa tace..
Ina tunanin kunyar mu takeji ne uwar dakina bari mu baku waje..
Marka ta jawo dayar baiwar sukayi waje..

Ammi da kanta ta shiga cirewa juwairiya kayan jikinta..
Juwairiya ta runtse idonta gam tana mamakin abunda ammi ke aikata mata babu ko kunya ta tube ta tas ta barta da yar shimin dake jikinta..

Ban daki suka shiga,ammi ta umurce ta data shiga cikin bahon wankan dake cike da ruwa me dumi sai kamshi yakeyi..

  Juwairiya gaba daya girman/kunyar ammi takeji kuma har zuciyarta tana jin kaunar matar..
  Batayi mata musu ba ta shige ciki..

Ammi da kanta da shiga wanke juwairiya tana bata labarai da suka danganci masarautar su..
      Juwairiya gaba daya ji takeyi kamar mafarki takeyi...

   Tasha mamaki sosai ganin Anyi mata wanka yafi kala biyar..
Data fito daga wannan ruwan ammi ta fita ta kirawo su marka su hada wani..
Ta wanko iya wankowa..
A take kuwa fatar jikinta ta canza..
Tayi wani irin fes da ita..
fatar ta tayi wani irin haske,gashin kanta sai baza kamshi yakeyi..

Tana fitowa daga baton ammi ta nade ta cikin bargo mai kauri ta saka marka ta dauke ta cak dama ita ba wani nauyi ba..

    A saman gadon ammi marka ta ajiyeta..
Ammi ta kalli marka..
Kije can MA'DINKA(wajen tailors)ki fada musu inaso suyiwa juwairiya kaya yanzun nan ki kawo min,marka tace toh ranki ya dade sannan ta fice..

    Ammi ta zauna a gefen juwairiya tana hada mayuka masu shegen kamshi tace..
    Ina so ki daina jin kunyata juwairiya,ni kakar kice babu wata kunya a tsakanin mu kinji?..

  Juwairiya ta gyada kai tana murmushi..
  Sallamar wasu yan mata guda biyu ne ya katse su..

     Ammi na jin muryar su tace..
Ku shigo ciki yan matana har an taso daga makarantar ne?
  Yan matan suka shigo ciki...Ammi kin san ko...
Mgnr ce ta tsaya musu a makoshi ganin juwairiya da sukayi akan gadon ammin su..

Kallon kallo suka shigayi wa juna..
A tare sukace..
Ammi a ina kika samo me kamar dake haka (her look alike)
Ammi tayi dariya, diyarku ce..
Cikin murna suka haye kan gadon suma suna saka juwairiya a tsakiyar su..

   juwairiya dai da kallo kawai take bin su..
farare ne kamar ammi amma da ganin su zaka gane yan biyu ne da suna kama da juna..
  Ammi na dariya tace..
Juwairiya wadan nan sune Autaye na,ga hassana ga kuma hussaina..

Juwairiya tabi su da kallo..
Hassana ta shafa fuskar juwairiya, diyar mu na kama da Ammi sosai..
Husssaina tace,sosai ma kuwa..
Ammi ta mike tana fadin,toh ku shirya min Jikata na bar muku wuka da nama a hannunku.

   Murna sosai suka shiga yi ....
Ammi ta fice tana sanar musu marka zaka kawo kayan juwairiya..

"Sun gama shirya juwairiya cikin kaya na alfarma ba karamin kyau tayi ba,zan iya ce muku kamar an canzo mana juwairiya ne dan gaba daya (transforming)tayi..kamar ba juwairiya BAIWAR RUMFAR BAYI ba..

"Jama'ar gidan ne suka shiga shigowa ganin ta,ana ta taya ammi da murna..
Ammi kam baki bar kunne..
Hassana da hussaina kuwa suna makale da ita..

  Khaleed ma sai da ya shigo,ya wara ido yana kallon juwairiya yace..
Ammi wacece wannan haka?
Ammi tayi dariya,diyarka ce mana..
  Hassana tace,ya khaleed kaga yarda juwairiya ke kama da ammin mu ko?
Khaleed yayi dariya na gani sarkin surutu..

Juwairiya ta dago tana kallon khaleed, wai dama wannan mutumin kawun tane?
  Khaleed ne ya kashe mata ido..
Yadai kina mamaki ko?
juwairiya tace ni gani nakeyi ma kamar mafarki nakeyi..

Ammi ta kamo hannunta tace..
ba mafarki kikeyi ba juwairiya duk abunda ke faruwa dake a yanzun GASKE NE.....

    Juwairiya ta saki murmushi me cike da farin ciki...
Lallai dole ta gode wa Allah daya bayyanar mata da ASALINTA.....





Team RUMFAR BAYI 
*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 33
Wattpad @afreey101


***************

"Washe gari...

"Mai martaba sarkin zazzau ya dawo daga tafiyar sada zumuncin daya tafi..

    Labari ne mai dadi ris'ke sa na bayyanar diyar zarah'u...
Bai ma san wane irin farin ciki zayyi ba, bai bata wani lkc ba ya saka akayi masa Ammi..

Ammi da kanta ta saka su hassana su shirya juwairiya tsab sannan suka nufi bangaren na mai martaba..
Juwairiya har cikin zuciyarta take jin dadi sosai zata ga kakanta kuma mahaifin ummanta ta gaskiya..

"Sun tarar dashi a zaune saman kujerar sa ta karfe a cikin dakinsa..
Tsoho ne da zaikai shekaru kusan tamanin haka,amma ba zaka taba cewa mijin Ammi bane dan kuwa ta fishi jikin yarinta sosai..tunda dai ya girme mata nesa ba kusa ba..

    "Tunda suka cikin shigo dakin sarki ya kurawa juwairiya ido yana kallonta cike da al'ajabi...
Tabbas wannan jinin diyar sa ce zarah'u ..
  Da hannu yayi mata alama dataje garesa..

Ammi juwairiya ta kalla..
ta gyada mata kai tace kije juwairiya..
   Ta taka har zuwa gabansa sannan ta duka kasa ta gaishe sa cike da girmamawa..

Hawaye ne suka cika masa ido..
Sai yanzu yake mugun dana sanin abunda ya aikawa diyar sa..
   Ya shiga shafa kanta hannayensa na rawa haka ma lebensa...
Yace...
Asma'u (AMMI)
Ina godewa Allah daya bayyana mana jinin fatima muka ganta tun muna da sauran lumfashi a duniyar nan.
ina farin ciki sosai dana samu ganawa da ke...
ya fadi yana dago dakan juwairiya, hawaye itama takeyi sosai..
  Ammi ta zauna tana fadin..
.. (note an sanarma sarki lbrn juwairiya duka)
Ba lkcn zubar da hawaye bane wannan,lkcn farin ciki ne da gode wa Allah...
Sannan kuma lkcne da zamu sanar ma juwairiya labarin mahaifiyar ta..
Mai martaba ya gyada kai,cike takaicin rashin zarah'u da sukayi yace,hakane dole ne mu sanar dake Wacece FATIMA wato ZARAH'U mahaifiyar ki....

*******************
*Masarautar zazzau A shekarun baya da suka gabata*..

"Zarah'u itace diya ta farko da Ammi ta fara haifa tun bayan auren su da mai martaba..
yarinya ce mai saukin kai da tausayin gaske gashi bata da wani hayaniya ko kadan,bazaka tabajin tayi fada ko gardama da wani ba..

    Ta taso ne cikin so da kaunar mutanen dake cikin masarautar nan..
Dan Ko ina a cikin masarautar nan shiga takeyi tun tana yar karamar ta dan haka babu wanda bai santa ba..

    "Zarah'u na da shekara sha bakwai mane ma aurenta sukayi mana caaaa..
Tunda ga yayan yan uwanmu zuwa masu kudin kasar mu..

"hakan kuwa ba karamin tashin hankali ya saka mu ba dan kuwa munyi wa zarah'u alkawarin zamu bata damar zabar mijin da zata aura..
   Kuma a wannan lkcn ma a yarda na lura da ita ba auren bane a gabanta karatun da takeyi shi ta saka a gaba..

Ana cikin haka ne kuma sai muka riski ziyara daga sarkin kanon dabo a lkcn daurin auren garba..

     Mai martaba ne yayi kiran dukka iyalensa dan gabatar dasu ga sarki ABU-TURAB...
    Duk muka hallara a cikin babban falon mai martaba dan gaisawa da babban bakonsa..

Amma banda zabba'u wacce take can bangaren kakarta suna shan firarsu..
Marka ce na aika dan ta sanar da ita neman gaggawar da mahaifinsu keyi mata...

   Zabba'u da gudunta ta shigo falon da sallama..
Kallone ya koma kanta..
A lkc guda kuma ta shiga zuciyar sarki ABU-TURAB farat daya....
  Bayan mun gama gaisawa ne da sarki duk muka tashi muka fice dan basu waje..

Sarki ya kalli mai martaba yace..
Takawa Duk wadan nan yan matan yaranka ne?
Mai martaba ya gyada kai yace,duka yarana na ne ni na haife su..
amma zarah'u ce karama ce a cikinsu duk da tafi su jikin girma...

Sarki abu-turab ya jinjinar da kai kafin yayi sallama da mai martaba suka kama hanya..

Sati daya da zuwa ziyarar shi sai ga waziri da wambai sun sake sauka a kasar zazzau...
Munyi mutukar mamakin ganinsu dan basu aiko mana da wasikar zuwan nasu ba..

    Mai martaba ya saka akayi musu tarba mai kyau suka ci suka sha kafin aka sake zama dan a gaisa..

Waziri bayyi kasa a gwiwa ba ya sanar da mai martaba sakon sarki abu-turah...
akan sunga IRI a cikin gidan sa kuma suna so..
   Murna sosai mai martaba yayi dan kuwa yayi wa AMINA sha'awar abu-turab din..
Yayi murmushin su na manya yace..
Toh madallah ai babu wata matsala tunda akwai dangantaka mai karfi ta zumunci a tsakanin mu..
   Waziri da wambai sukayi farin ciki sosai sannan cike da murna suka koma kasar kano...

Bayan sun sanarwa sarki abu-turab amincewar mai martaba ba karamin dadi yaji ba..
A take kuma yaje ya sanar ma mahaifiyar sa HAJJO..
Itama din taji dadi sosai dan kuwa tana mutukar son dan nata ya karo aure sbd irin rikicin da suke samu a wajen matar sa ta faro HINDU...

"Bayan wata daya ta shude sai ga sarki ABU-TURAB ya sake kawo mana wata ziyarar amma a wannan karon Zance ne ya kawo sa na Aure..
   Mai martaba ya tare shi cikin murnar sa ya kuma saka YAYA BABBA (kishiyar ammi)ta shirya AMINA dan su dan gana da abu-turab din..

A can falon baki inda ya sauka aka shirya musu wajen da zasu kebe dan fahimtar junan su..
   "Lkcn da amina ta shiga falon abu-turab ya kyalla ido ya ganta sai ya mike da sauri yana kiran waziri dake waje...
Ya nuna amina yace,ba wannan bace nake so..
Waziri mamaki ne ya kamasa..

   cikin Fa'da suka koma a nan abu-turab yake sanarma mai martaba shi ba amina ce yake nufi ba wata ce daban..
Mai martaba yayi mamaki dan kuwa a lkcn yan matan gidan duka basu fi guda uku ba..
HAJIYA (kishiyar ammi ce itama )ya sake sanar ma wa akan a shirya BILKISU ta zo fada yana nemanta..
Bilkisu na zuwa abu-turab ya sake cewa ba ita bace..
  Sai lokacin ne hankalin mai martaba ya tashi,dan kuwa yasan ba kowa bace abu-turab yake mgn face ZARAH'U ...

      Jiki a sanyaye ya saka aka zo aka sanar min dana shirya zarah'u taje fada..
   Nayi mutukar mamaki sosai sannan kuma hankalina ya tashi..
A haka na matsa mata ta shirya ta tafi..

Tana shiga Abu-turab yace ai itace yake mgn,shi itaa yake so a basa..
Mai martaba ya rasa yarda zayyi gashi kuma yayi musu alkawari tun da farko akan cewa ya basu..
damuwa sosai ne ya shiga dan ba'asan sarki da mgn biyu ba..

Bayan su abu-turab sun koma kasar su akan zasu dawo dan a saka ranar biki..
mai martaba ya same ni dan neman shawarata..

    Rasa abunda zan fada nayi dan kuwa ina son farin cikin ya'ta amma kuma rashin amincewa sarki ABU-TURAB kamar zubar da ki'ma da mutumcin masarautar mu ne..
   Cikin rasa wata mafita muka yanke shawarar aurawa abu-turab ZARAH'U...

Lkcn dana same ta da mgnr ba karamin tashin hankali ta shiga ba..
Kai tsaye ta fada min ita bata son Shi..
   Cikin lalama da dadin baki na samu zarah'u ta amince akan zatayi mana biyayya amma fa ita ba dan tana jin zata iya son abu-turab a zuciyarta ba..

Ba bata lkc Aka saka ranar biki..
Gaba daya jama'ar gidan suka hau jin haushi da kishin mu,har fadi sukeyi asiri naje nayi dan diyata ta auri sarkin kano...
   Duk habaicin su bai wani dame ni dan kuwa yarda zarah'u duk ta rame sbd damuwar data saka a ranta nima sai hankalina ya kasa kwanciya da auren dolen da muke shirin yiwa diyar mu..

Ranar asabar da rana aka daura auren zarah'u da abu-turab a ranar kuwa da wani mugun zazzabi zarah'u ta tashi..
       Jikinta babu wani sauki a haka muka lallaba aka kaita dakin ta a can babbar masarautar ta kanon dabo...

AMMI taja lumfashi tana share kwallar dake fitowa a cikin idanunta..
        Tunda zarah'u ta shiga gidan take samun matsala sosai a wajen uwar gidan abu-turab Hindu..
Sai dai saukin abun shine,mahaifiyarsa da shi kansa suna mutukar kula da ita..

Hakuri kawai takeyi a gidan dan kuwa a kowace rana sai ta hadu da tsangwama a wajen HINDU da ma yan uwanta..

Shekarar ta daya a gidan Allah ya bata ciki....
Wayyo zo kiga kishi karara a wajen hindu da tawagar ta...
  Lkcn ba karamin kula take samu a wajen abu-turab ba,kyaututtuka sosai yake bata yana nuna mata soyayya..

  Hindu ta kasa hakuri da irin bakin ciki da kyashin da takeyiwa zarah'u, dan haka suka hada baki da wani bawa me kula da sashen abu-turab suka kulla wa zabba'u sharri..

Akan tana gayyatar wannan bawan cikin dakinta suna ZINA..
     Sarki abu-turab ba karamin girgiza yayi ba da jin wannan zancen ba..
Duk da haka bai yarda ba..
Ya saka aka kirawo masa duka bayin dake aiki a sashen zarah'u dan su bada sheda akan zargin da akeyi mata..

     Ga babban mamakin zarah'u gaba daya sukace ai anyi haka,tabbas suna ganin wannan bawan yana shige da fice a dakin zarah'u kullum dare..

     Zarah'u ta fashe da kuka mai tsuma rai tana rokon abu-turab daya yarda da ita amma inaaa...yayi fir yaki yace ta kwashe inata inata tabar masa gidan sa...
   Cike da tsananin damuwa zarah'u ta dawo masarautar zazzau da karamin cikin ta wata shidda...

    Lkcn data same mu da wannan zancen ba karamin fusata mukayi da ita ba dan kuwa mun san zarah'u tasha fadin rashin son da takeyiwa abu-turab..
Daki nakai ta na shiga tuntubar ta ta fada min gsky ko da gaske ne ta aikata abunda ake zargin ta tayi.
Tana kuka ta shiga fada min ita shirri ne akeyi mata wannan cikin ma na jikinta na abu-turab din ne...
  
Mai martaba ba karamin fusata yayi ba,dan lbr ne ya shiga yawo a kasar zazzau akan sarki ya bar diyarsa tayo yaji kuma ya kasa daukar wani hukunci akanta..

  Watan zarah'u biyu mai martaba ya hadata da wasu yayyinta suka koma can kasar kano dan yin bi'konta..
    Da kyal abu-turab ya amince dasu bar ta su wuce komai ya wuce..
   
Rayuwa tayi wa zarah'u zafi..dan kuwa abu-turab banzatar da ita yayi acikin masarautar dan babu me kula ta,ko bayin dake tare da ita ma gulmar ta sukeyi..

Cikin ta na wata tara a wani dare hindu ta saka ayi mata (kidnapping)din zarah'u a cire dan dake cikinta a kashe shi ko kuma gaba daya a kashe zarah'un dan bazata taba bari ta haihu acikin masarautar ba.
dan dama tayi tayi ta zubar da cikin Allah bai bata iko ba..

Lkcn da aka fita da zarah'u wani bafade ne ya gansu,dan haka yabi bayan kattin har suka kaita wani daki suka ajiye..

  Bayan sun ajiyeta ne sai yaji suna mgn akan abunda hindu ta saka su suyi..
Hankalinsa ne ya tashi sosai..
Jiki na rawa yaje ya taimakawa zarah'u suka gudu...

    Suna cikin gudun sukaji muryoyin kattin mazan a bayansu..
Bafaden ya kalli zarah'u gaba dayan su sun gama jigatuwa..

Yace,ranki ya dade ki wuce abunki,ki gudu ki ceci rayuwar dan dake cikin cikin ki..
Zarah'u na kuka sosai ta girgiza masa kai..
Bazan iya tafiya na bar ka a wajen wadan nan mugayen mutanen ba..
Bafaden ya runtse ido sannan da kyal ya samu zarah'u tabar shi a wajen taci gaba da gudu dan ceto rayuwar ta dama na dan dake cikinta

Ba karamin wahala da jigata tayi ba,gudu kawai takeyi bata san inda zataje ba...
      Sai gashi ta shigo kasar daura,ta haife mana JUWAIRIYA sannan  tace ga garin ku nan......



Not edited pls am tire😌

Team RUMFAR
*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 34
Wattpad @afreey101


******************

"Ammi ce da kanta ta saka juwairiya a gaba suka ringa shiga bangare bangare na cikin masarautar dan gaisawa da matan mai martaba da kuma ya'yansa..

  Daga karshe Ammi ta kaita wani tsohon sashe na mahaifiyar ta zarah'u ..

    Hawaye ne suka shiga zuba daga idanuwanta..ba karamin tausayawa irin rayuwar da sukayi ita da mahaifiyar ta ba takeyi ba...

Kallon dakin takeyi cike da tausayin irin rayuwar da mahaifiyar tayi a baya..
Ammi ta dafa kafadarta,ki ci gaba da yi mata addu'a kinji?

Juwairiya ta gyada kai sannan tayi wa ammi tambayar dake ta cin ta a rai tun jiya..ta saukar da kai kasa tace..

   "Ammi yanzu shi sarki Abu-turab din har yanzu bai gano sharri akayiwa ummar ba?
Sannan har yanzu suna tare da matarsa hindu ne?

Ammi ta kamo hannunta suka zauna a gefen gadon dake gefen su..
  Ta kalli juwairiya tace, kin san indai mutum baya da hakkin wani...
Toh Allah sai ya san yarda yayi gaskiya ta fito koma daren dadewa..

   Wannan bafaden dai daya taimakawa zarah'u ta tsira daga hannun wadan nan mutane shine ya bayyanar da komai..

Duk da dai ba karamin wahala da azabtuwa yayi ba a wajen wadannan mutanen..
Sai da zarah'u tayi kusan sati daya da bacewa sannan Allah ya kubotar da wannan bawan..

  Kai tsaye yan farautan da suka taimake shi sukayi fadar sarki abu-turab dashi..
   Shi kuwa ya fayyace wa sarki duk abunda ya faru da zarah'u sannan ya sanar masa da sa hannun HINDU aciki..
  Abu-turab a take a rikice susuce..
Ya saka aje a kawo masa hindu da duk mutanen da suke da sa hannun aduk abubuwan da akayi wa zarah'u..
   Hindu na jin asirinta ya tuno ba karamin rikice wa tayi ba..
sbd tashin hankali da kuma mugun hali irin nata sai sakawa tayi yayanta ya taimaka mata ta gudu daga masarautar gaba ki daya....

   Toh a cikin ikon Allah kwana biyu da guduwar ta ta sai gashi an kawo gawarta har cikin masarautar kano..
wai yan fashi ne suka tare su a hanyar su ta shiga kasar nijar suka kwashe musu duk kudin dake garesu sannan suka kashe su..

    Abu-turab bai amsa gawar hindu ba,yace aje can akai wa yan uwanta shi babu ruwan shi da ita tunda ya dade da sakinta..
      Abu-turab ya saka mutane dayawa dan neman zarah'u hakama mu ma a nan amma shiru babu wani labari akanta....

  Mahaifiyar sa ce ta matsa masa akan sai ya sake wani auren..

Toh a lkcn mijin AMINA ya rasu sai mai martaba ya bashi ita,abu-turab bai wani musa ba aka daura musu aure bayan shekara daya kenan da batan zarah'u...
a halin yanzu kuwa har sun hayayyafa sannan kuma ya kara aure bayan ita,ya auri diyar sarkin AZARE JAMILA ....

Juwairiya taja lumfashi lallai ta tausayawa iyayen nata..
Ammi tace,kada ki damu idan kika kara kwana biyu zamuje ki gansa kinji?
Juwairiya ta gyada kai..
Mikewa sukayi suka bar sashen..

********
*Masarautar daura...*

"Bakin ciki ne da takaici suka taro sukayi wa surayya yawa..

Ace wai a halin yanzu ko kallo bata ishi jalal ba?
Sai dai ta ringa samun labarai daga wajen umaymah wai a kullum sai ya gayyaci khadija zuwa sashensa sannan yaje ya dauke ta su riga fita yawon shan iska da yamma...

Surayya ta dunkule hannu ta naushi gadon da take a kai..
    "Dole ne na san abunyi dolene na tashi tsaye ta nemo wa kanta mafita.....

"Jalal ne zaune a kan gadonsa yana tunanin ko a wane hali juwairiya take ciki yanzu?ba karamin kewar ta yayi ba,kodai ya shirya ne yaje zazzau din..?

    Sallama akayi ne ya katse masa tunanin sa...
Khadija ce ta shigo dakin..
Jalal ya kura mata ido yana wani nazari..
Khadija ta sakar masa murmushi, ya jalal ka tashi muje toh...ina can ina ta jiran ka ashe ko ma niyyar zuwa bakayi ba..

Jalal ya lumshe ido ya bude su ahankali...
yau gaba daya baya jin fitar nan gashi kuma ya sabar mata yadan ja tsaki..

Khadija ta karasa wajen sa tashiga jan hannunsa..
  Jalal yaki mikewa ko motsi bayyi ba ma..
tana ta faman jansa a dolensa ya mike yana fadin..
Kin cika rigima khadija..
Tayi masa gwalo tace..
naji din nidai muje yaya..
Jalal ya daura alkyabbar sa suka fito..

Suna tafiya a cikin masarautar bayi nata faman gaida su suna yaba dacewar jalal da khadija..

   Samira da turaki ne suka hango su fitowar su kenan daga sashen fulani diyya..
Karasawa sukayi wajensu..
Khadija da samira suka gaisa hakama jalal da turaki..
Jalal ya samu kansa da tambayar samira ko ta samu wasika daga can masarautar su?
Samira ta girgiza masa kai tace,ah ah ina dai saka rai a cikin satin nan.
Jalal ya jinjina kai kawai kafin yayi gaba khadija tayi saurin binsa..

********
"Rayuwa tayi wa juwairiya dadi..
ba karamin canzawa tayi ba a cikin yan kwanankin nan..
gashi kuma har tana neman kusan wata daya kenan mai martaba bai bada izinin tafiyar ta kasar kanon dabo ba..
Yau dai da kyal ta samu Ammi ta hada ta da wata baiwa suka fito zuwa sashen khaleed..
Suna shiga suka tarar dashi shima ya fito cikinsa..
juwairiya ta gaishe shi tana murmushi,KAWU irin wannan gayun haka?
Khaleed yayi dariya,diyata zance zani ..ko zakije ne ki gaisa da matar Kawu..
Juwairiya tayi dariya, khaleed ya kamo hannunta muje zakiji dadin haduwa da ita..
Wani bangare taga sun shiga duk a cikin masarautar..
Ta kalle shi da mamaki..
Kawu matarka acikin masarautar nan take itama?
Khaleed yace,kwarai kuwa diyar kanin me martaba ce fa..
juwairiya ta jinjinar dakai,ashe kuma a nan kuna auren hadi..
Khaleed yace,tsoro kikeji?
Juwairiya tayi dariya tsoron me?
Khaleed yace,a hadaki da wani mana..
Juwairiya taji gabanta ya fadi, a hada ta da wani?AMALEN ta fa?ta cije harshenta,zuciyarta JALAL take so bazata taba iya rayuwa da wani ba,ba zata maimaita irin rayuwar da mahaifiyar tayi ba.....

Budurwar khaleed,me suna sumayya tana da kirki sosai,a take shakuwa ta shiga tsakanin su da juwairiya...

Washe gari....

da yammacin ranar talata suka fito ita dasu hassana da hussaina..
    Juwairiya ta kallesu,wai na tambaye ku mana?
  Hassana tace muna jin ki..
Juwairiya tace,idan kamar mutum yana son ya aikawa wani wasika da baya cikin kasar nan taya mutum zayyi hakan?
Hussaina ta rike baki..badai diyar tamu har ta samo mana suriki ba?

  Juwairiya ta ware ido tana nuna kanta..
Ni ah ah wlh uwar dakina..ah ah zainaba kawata ce nayi wa alkawarin aikawa wasika shine nake son na cika mata alkawarin..

Hassana tace,nidai ban taba aika wasika ba amma muje bangaren hajiya na tabbata ya mas'ud zai sani..
Juwairiya tace toh muje dan Allah..ai kuwa duka dunguma suka tafi..

Suna shiga bangaren hajiya sukaci karo da yasira...
Yan biyu suka gaida ita juwairiya ma tayi yarda sukayi..

  Yasira ta kurawa juwairiya ido tana tuna kanwarta zarah'u da sukafi

Please Login or Register in order to submit comment