Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana zolayar du'bu dake zaune tana linkin kaya..
   Laure ce ta karasa ta zauna kusa da du'bu tana sanar mata umurnin fulani na son ganin juwairiya..

Du'bu ta gyara zamanta tana murmushin murna dan ita kam ta hannun damar fulani ce sosai sam bata son komai daya danganci gimbiya kilishi..

Tace Allahu akbar ai zainaba ba kadan ta biyo mahaifiyar ta fulani ba,na tabbata juwairiya zataji dadin zama da ita.

  Laure tace uhm,sannan taje ta kamo hannun juwairiya, juwairiya tace,goggo laure ina zamuje?laure tace badai ke yawo ba ai gashi nan jin jawo wa kanki aikin BAUTA..

"A kofar sashen fulani akayi musu iso..
Laure taja hannun juwairiya dake ta kalle kalle suka shiga ciki..

   Baki sosai juwairiya ta bude ganin kyau da tsarin falon ,can ta hango fulani hakimce akan kilisar ta..
  Tayi kasa da kanta,zainaba ce ta mike tana fadin,itace wannan umma kin ga ta nan..

Fulani tayi murmushi tana kallon juwairiya a ranta tace,yarinyar kyakkyawa, ta kalli laure toh kinji laure ita zainaba take so a matsayin kuyangar ta dan haka daga gobe zata fara yiwa zainaba hidima...

    Juwairiya tayi saurin kallo zainaba dake kallonta dauke da murmushi, sannan ta kalli turaki dake zaune shiru yana saurarensu..

Laure tace an gama ran fulani ya dade,zainaba ta kalli juwairiya sai mun hadu gobe ko?juwairiya ta gyada kai sannan suka juya suka fice..

"A daren ranar raba dare su jakadiya,laure da hansai sukayi suna fahimtar da juwairiya yanayin rayuwar da zata shiga..

Suka fara da gaya mata matsayin ta,ke ba kowa bace fa'ce BAIWA,
yanzu gimbiya zainaba itace uwar dakinki wacce zakiyi wa hidima..
komai takeso shi zakiyi mata babu gardama,
ko me tace dole ki amince dashi,
duk abunda take so shi zaki so,
duk abunda bataso kada kiyi,
ki guji bata mata rai,
kome zakiyi se kin nemi  izinin ta,
ki bauta mata dan a halin yanzu rayuwarki kamar tana hannunta ne..

   Juwairiya taji abun banbara kwai,tace amma umma jakadiya rayuwa  tana ga Allah ne ai ko?laure tace hakane amma rayuwarki da zakiyi a wannan masarautar tana hannun gimbiya zainaba ne,dan a kowane lkcn zata iya ba'tar dake...

  Juwairiya ta tsorata sosai,jakadiya ta shiga nuna mata yarda duk zata kula da gimbiya zaOneloveuk wata hidima da akeyiwa ya'yan sarauta an koyar da ita,sai cikin dare sosai suka samu rintsawa sbd tambayoyi da juwairiya ta rufe  su dashi....

" Wannan kenan "

Share pls n pls vote on wattpad @afreey101
#Onelove

[9/18, 3:10 PM] Aysha Galadima: 🏕 *RUMFAR BAYI* 🏕
(A historical fiction)

Na Afrah bhai
Page 4
Wattpad @afreey101
     


************************

       "Washe gari da sassafe,hansai ce ta shirya juwairiya cikin irin shigar tasu ta bayi, kayane irin na Sa'ki' dinnan riga da zani(blue color kayan fulani dinnan ),laure ta shigo taja hannunta suka fice..

   "Tafiya sukeyi juwairiya na ta kalle kalle tana tsallenta cike da nishadi..
' can ta hango wani yaro dauke da kwando a kansa aciki kuwa su mangoro ne da gwaba gashi tana mugun son mangoro sosai,nan ta kura mai ido tana tafiya tana waiwayen sa,yana dago da kai ya hango ta,ganin yarda take bin kwandon dake kansa da kallone sai ta bashi dariya har sai daya murmusa..

    Laure ce ta hadu da wata baiwa suka tsaya gaisawa,juwairiya ta tsaya tana tunanin irin girman masarautar dan sun sha tafiya sosai ga gine gine masu yawa ga shukoki masu kayatarwa..

  " Amsa.."
Taji ance daga bayanta,tayi saurin juyowa..
Sukayi ido hudu da wannan yaron..yana mika mata mangoro biyu fuskarsa dauke da murmushi..

Ta kalleshi ta saki wani irin murmushin murna,ji tayi laure tace,muje muje juwairiya....

  Da sauri ta amshe mangoron ta furta ngd da sauri tayi gaba...

Suna isa sashen zainaba ayi musu iso ciki..
Zainaba na hakimce a zaune ana ta mata fifita...
Juwairiya ta saki baki ganin kyawun dakin ya burge ta sosai..
Zainaba ta saki fuska sannan tace,wai ya sunan ki ne ma?
Sauke kanta tayi kasa tuna mgnr su  yaha ta jiya da sukace banda  hada ido da uwar daki,a sanyaye tace sunana JUWAIRIYA..

Zainaba tace toh muje makewayi (toilet ) dan ina son nayi wankana yanzu..
Juwairiya tayi saurin kallon laure,laure ta gyada kai sannan taje kusa da ita tace,kada ki manta da maganar mu ta jiya,tana gama fadin haka tayi gaba..

     Juwairiya kanta a kasa tace ina ne ban dakin ranki shi dade?
Zainaba ta dan murmusa sannan ta kalli baiwar dake kusa da ita tana mata fifita tace,kai ta ban dakina sannan ki nuna mata yarda nake son ruwan wanka na..

"toh ranki shi dade ta mike hade da kiran juwairiya suka shiga wata kofa data sada su da wani makeken toilet sai kamshin sabulai yakeyi ga wani bahon wanka na silver a ciki, baiwar ta kalli juwairiya tace,kingani ruwan zafin kadan zaki saka dan zainaba bata son ruwan wankanta yafiya zafi da yayi dumi ya isa'

,ta dauko wasu ganyayya'ki masu fitar da wani sanyin kamshi,tasa hannu ta damka kadan tace kinga haka?juwairiya ta gyada kai,toh haka zaki ringa sakawa duk lkcn da zaki hada mata ruwankan ta,juwairiya duk ta fahimta dan kuwa akwai ta da kaifin basira.

'Se data taimakawa zainaba ta cire kayanta sannan suka shiga ban dakin.

'zainaba ta shige cikin bahon wanka da dan shimin dake jikinta,ta kalli juwairiya,tace..

"cu'da min bayana"
juwairiya ta dauko soso mai taushi tazo ta fara cu'ta mata bayan a hankali sbd dai an sanar mata yarda akeyi.

   Sai da zainaba ta wanko sosai sannan suka dawo daki,ta kalli juwairiya dauko min wancan akushin,ta dauko tazo gabanta ta ajiye,zainaba ta bude kayan kwalliyarta ne a ciki.

  Ta kalli juwairiya......
miko mi'ni jan bakin can,juwairiya tayi sakatoto tana kallonta dan bata ma san minene shi jan bakin ba,zainaba taji shiru tace lah baki san shi ba ne?

"Ta gyada kai tana fadin,Allah ya huci zuciyar  ranki ya dade bani da masaniyar me kike bukata idan har ranki ya dade baza ta damu ba ina so ta ganar dani minene shi,zainaba tayi dariya sannan ta dauko jan bakin da kwalli da hoda duk ta nuna mata su'sannan ta tsara yar kwalliyarta da kanta,juwairiya cike da mamaki take kallonta ta saki baki ganin yarda zainaba tayi kyau abunta.

sai da ta taimaka mata ta saka kaya sannan suka dawo cikin falo...
cikinta ne ya hau rurin yunwa ganin irin delicious din dake jere a gaban zainaba tana ci tana wani yatsina.

Tunawa tayi da mangoron ta na dazu data ajiye akan ta'ga (window)lkcn shigowar su.
Tadan sadda kai kasa,ranki shi dade zan iya fita yanzu yanzun nan na dawo?
Zainaba ta kalleta da mamaki ina zakije?
Juwairiya ta dan dafe cikinta sannan tace wata ajiya nayi  a waje zan dauko.
Zainaba ta gyada kai zaki iya tafiya..
Da gudu ta fito neman mangoron ta,sai ko ta gansu a inda ta ajiye su din.
cikin murna ta dauka ta shiga shansa kamar an aikota duk tayi kaca kaca da bakinta..

    "Ashe ke kazama ce?

Taji an fada daga gefen ta,da sauri ta kallo wajen,turaki ne ta gani da bawan sa a bayansa..
Ta dan sude hannunta sannan tayi kasa da kai,barka da zuwa ranka ya dade..

Cike da mamaki yake binta da kallo wato yanzu ta fara sanin dokokin gidan kenan?
Yauwa kawai ya fada sannan ya shige wajen kanwar sa..

   'Yana shiga zainaba ta mike cike da murna,yaya ashe zaka zo?
Ya dan daure fuska miye na kirana da sassafen nan haka?
Zainaba ta shagwabe fuska,dama fa zan tuna maka ne yau nakeso muje na hau do'ki nima..

  Turaki ya lumfasa wato bazaki bar wannan zancen ba ko?
Daure fuska tayi,amma ai har fulani na fadawa kuma ta amince naje na da'na dokin nima..

  'Turaki ya girgiza kai sanin halin kafiya irin ta zainaba,juwairiya ce ta shigo kamar munafuka se goge bakinta takeyi..
    Zainaba ta kalleta ki shirya zamuje hawan doki,juwairiya tace toh ranki ya dade.

Tsaye suke a cikin wajen ajiyar dawakan sarki.
Zainaba se zumudi takeyi,ta kalli bawan dake tsaye wajen tace,wancan dokin nakeso na hau,ta nuna wani farin doki dayaji kayan ado sosai..

Zubewa kasa bawan yayi yace,kiyi min rai ranki shi dade wannan dokin musamman YARIMA yasa aka shirya masa shi yau din nan..
   Zainaba a take ta daure fuska ta kalli turaki dake gefenta,yaya kaji wai na ya jalal ne ta karashe mgnr kamar zatayi kuka..
Turaki yace,kiyi hkr ki zabi wani mana?

Zainaba ta zunburo baki,zatayi mgn suka hango yarima yana tahowa cikin kasaitar sa bayi na biye dashi a baya.
   Yana karasowa wajen duk suka tsaya kallonsa bayin dake wajen kuwa suka zube suna kwasar gaisuwa..

    Bai ko kallon inda su turaki ke tsaye bayyi ba..
idanunsa ne suka sauka akan juwairiya dake tsaye a bayan zainaba bata da ko niyyar dukawa ta gaishe shi..

  Ke!
Ya fada yana yastine fuska..
Juwairiya ta dago suka hada ido,dauke kansa yayi..
"Na lura har yanzu baki san matsayin ki ba ko?

  Sake dukar da kanta tayi tace'barka da fitowa ranka shi dade..
Yarima ya tabe baki sannan ya maida kallonsa kansu turaki..
Zainaba ta daure fuska Allah ya gani bata son girman kai da isa da ikon da ya jalal yake ji dashi..
Lafiya?...yarima ya fada yana musu kallon me kuke a nan?..

Turaki ya murmusa babu komai dama wucewa muka zo yi..
Yarima ya tabe baki ya karasa wajen do'kin sa wani bawa ya taimaka masa ya haye sama abunsa....

Zainaba kuwa ta banka wa turaki harara sannan ta juya a fusace tayi gaba,juwairiya tayi saurin bin bayanta ..

"Fulani ce a zaune saman kilisar ta laure na mata tausar kafa suka shigo bayan anyi musu iso..

Zainaba ta fada jikin fulani tana kukan shagwaba,fulani wai me yasa a gidan nan ne akafi girmama su UMMA babba (gimbiya kilishi kenan) da su yaya YARIMA?akan mu?

Naga ai mu ma baban mu daya dasu ko?tunda duk mai martaba ne ya haife mu..

  Fulani ta sa hannu ta dago fuskarta'da ta fara ji'kewa da ruwan hawaye..
girgiza mata kai tayi,zainaba nasha fada miki ke jinin sarauta ce ba'a san'mu da zubar da hawaye haka ba kaskancine a garemu....
   Zainaba ta goge fuskarta..
Toh umma na daina..
Juwairiya dake tsaye fulani ta kalla,sannan ta maida kallonta ga zainaba..

Ya baiwar taki?
Zainaba tayi murmushi,tana kula dani sosai umma sannan ta iya aikinta tana da kokari ..
Laure dake zaune ta saki lumfashi..

*********
'Sai da daddare bayan uwar dakin tata ta samu barci sannan a gajiye ta fito daga sashen tana hamma..cike da gajiya dan zainaba akwai shegen son yawo..

Tafiya takeyi cikin duhu sai dan hasken farin wata dake haska mata hanyar kadan..
        Maganganu ta fara jiyowa a tsorace ta shiga kalle kalle..

Can ta hango inuwar mutane biyu dake can wani lungu..
  Da sauri ta karawa tafiyar tata sauri amma me sai taji kamar muryar TALATU wata sabowar baiwa da'a kawo shekaran jiya..

   A hankali ta shiga labewa tana karasawa wajen duk da zuciyarta cike take da tsoro..
     Ware ido tayi ta dafe kirjinta ganin wani katon gardi yana neman ya'ge rigar dake jikin talatu dai fisgiwa takeyi amma ina.... yafi karfinta..

   Juwairiya ta rasa yadda zatayi gashi mutunen ya juya baya sai dai tufafin dake jikinsa ya nuna mata dan gidan masu dashi ne..

   Har ta juya zata wuce sai kuma ta tuna mgnr mahaifiyarta inda take ce mata idan har taga mutum cikin bukatar taimako toh lallai ta taimaka masa ..

    Sauke ajiyar zuciyar tayi kafin tayi saurin karasawa wajen wasu fadawa dake tsaron kofar babban zaure..
   Dan Allah ku taimaka min wata baiwa na cikin neman taimakon ku, da sauri suka bi bayanta,sai dai suna kawowa wajen suka ja suka tsaya,juwairiya ta kalle su,daya daga cikinsu yace yarinya kiyi hakuri amma nan ba hurumin mu bane ba kema idan har kina son rayuwarki tayi tsawo acikin masarautar nan toh ki kama hanyar gaban ki..

   Juwairiya na kallonsu suka fice,ta dafe kanta yau ta shiga uku yanzu ya zatayi kenan?

  Dubara ce tazo mata,se data je saitin inda suke har mutumen yayi nasarar kwantar da talatu a kasa ta daga murya sosai tana fadin..

Talatu ! Talatu wai ina kika shigane haka!
  Jin an ambaci sunan talatu kuma tabbas wajen da suke ne aka nufo,sai ya mike da saurin sa yabar wajen..
    Da sauri juwairiya ta karasa wajen tana kallon talatu dake kuka kamar ranta zai fita..
  Tasa hannu ta dago ta tana rarrashin ta..

Suna shiga rumfar bayi hansai da du'bu dake zaune gaban wuta sukayi kansu..
  Lafiya juwairiya ina kika tsaya haka?juwairiya ta kalli talatu dake bayanta tana goge kwallar bakin ciki..

Umma dama...
Ta sanar musu komai,nan matan bayi sukayi kan talatu cike da tausayawa suka shiga tambayar ta ko yayi sa'ar yi mata fyaden?ta girgiza musu kai nan aka shiga hamdala dan kuwa a wajen su bayi sun dade suna fuskantar  irin wannan kalubalen sosai,ayi musu fyade a banzatar dasu kamar kayan wanki..

Lamarin nan ba karamin tashin hankalin hansai yayi ba,ta jawo juwairiya har daki ta tsaya tana kare wa jikinta kallo daga sama har kasa.. yarinya yar shekara goma amma duk halittun girma sun fara bayyanar mata,bata so kadan a ba'ta rayuwar diyarta dan kuwa a yanzu ji takeyi juwairiya kyauta ce daga Allah a garesu..

    Ki zauna ki jirani ga abincin ki can a cikin dan chinan can..
Hansai na fita juwairiya ta jawo dan chinan tana kare ma tuwon dawar dake gabanta kallo,ta tuna da irin abincin da zainaba ta gama ci dazun,dafaffiyar kaza ce,miyar naman shanu ne,dambu dayaji zogaye da kayan lambu,ga juice din inibi ne da aka matse shi aka saka mazarkwaila aciki..

   Ta girgiza kanta da sauri dan ganin ta fara hadiyar yawu,oh haka rayuwa take"ta saka hannu ta fara kai wa towun ta loma..

Hansai dakin jakadiya ta shiga suna zaune da laure suna yar firar su..
Hansai ta zauna tana saka tagumi.

Jakadiya tace lafiya hansa'u?
Hansai ta kallesu,ni fa hankalina a tashe yake wlh,kunfi kowa sanin irin rayuwar da BAYI mata suke fuskanta a wannan masarautar, ina tsoron wani abu ya faru da juwairiya ganin yarda yanzu ko wane dare ake samun matsalar fyaden nan..

  Laure tace toh yanzu ya zamuyi?dan wannan yarinyar juwairiya da gani ba karamar mace za'ayi ba..
Jakadiya tace nima wlh ina cikin wannan tunanin amma miye abunyi?
  Hansai tace,ga shawara duk suka kalleta..
TABO (scar )
Tabo kuma?duk suka tambayeta cike da rashin fahimtar abunda take nufi..

  Hansai ta murmusa TABO zamuyiwa fuskarta dan babu abinda maza suka fi kyamata kamar TABO ajikin mace..duk wani basarake ko mai mulki da dukiya babu abunda ke saka shi kyamatar mace kamar TABO ...

  Laure ta kwashe da dariya kuma fa hakane,dan ko kadan idan bayin dake kula dasu ko SA'DAKA ce  suka samu wani dan Tabo ko Konewa a jikinsu toh fa  a ranar ake canza musu su..
Jakadiya tace wannan hakane,hansai ta mike tace kuzo muje..

Juwairiya na faman sude kwano suka shigo,ta gaida su tana fadin,goggo laure ina alkawarina yake?
Laure tace  ke fa yar nan baki mantuwa..
Hansai ce ta zauna a kusa da ita tace,juwairiya kina jina.....
Wattpad @afreey101
[9/18, 3:10 PM] Aysha Galadima: 🏕 *RUMFAR BAYI* 🏕
(A historical fiction)

Na Afrah bhai
Page 5
Wattpad @afreey101

************************

"Bayani sosai sukayi mata,a tsorace tace, ummana kada ki damu zanyi kokarin rike mutumcina insha Allahu..

'Jakadiya ta fita ta dawo da wani tire ta ajiye a gaban juwairiya, laure ta taso dan ita kam gwana ce sosai wajen harkar kwalliya nan duk masarautar ita tayi fice wajen yiwa matan sarki kwalliya ta fitar kunya..

   Wasu abubuwa naga ta hada sannan ta riko kyakkyawar fuskar juwairiya ..
  Cikin minti goma ta kammala sannan ta kalli hansai tace,ya kuka gani?

  Bude baki sukayi duka dan kuwa duk wanda zai kalli fuskar juwairiya  sai yayi tunanin konewa ba'rin fuskarta tayi..

    Murmushi sukayi cike da farin ciki,jakadiya ta miko mata wasu kaya ta amsa tana kallonsu,kayane manya manya dan se a saka irin ta biyu a ciki,yanzu wannan sune suturunki kinaji?,juwairiya ta gyada kai.

**************

'Da asuba kuwa sai ga fadawa uku sun shigo Rumfar bayi,du'bu ce tayi saurin tare su..
Lafiya?
Fadane daya ne yace,daga gidan GALADIMA muke,yaronsa GARBATI yaga wata baiwa acikin rumfar nan jiya shine ya turo mu mu tafi da ita..

    Gaba daya hankalinsu du'bu ya tashi dan sun fahimci garbati ya siya talatune a matsayin SA'DAKAr sa (concubine)..

Dakin da talatu ke ciki du'bu ta shiga ta fito da ita tana kuka sosai,fadawa suka fosgota suka gaba da ita..

'Juwairiya dake rakube duk tana kula da abunda yake faruwa,
'hansai ce ta kamota ta maida ita cikin daki,
'sannan ta sake yi mata nasiha akan kada ta sake a san tabon fuskarta na karyane inba haka ba itama haka za'a zo a tafi da ita kamar yarda aka dauke talatu..

gari  na yin haske haka laure ta shigo ta sake yi mata makeup din tabon ta.

   Tana shiga sashen zainaba ta tarar da ita tana ta sharar baccinta.
Ruwan wankanta ta shiga ta hado mata sannan ta zauna a gefe ta tsunduma a cikin tunani..

  Zainaba ce ta mike taci karo da fuskar juwairiya, da sauri ta dauke kanta tace,ke meya samu fuskarki haka?konewa kikayi?

Juwairiya ta mike da sauri tace Allah ya huci zuciyar ki ranki shi dade jiya ne ruwan zafi ya kifar min a fuskata.

Zainaba tayi fuskar tausayi Allahu akbar yanzu haka fuskar ki zata zauna kenan?ta yamutsa fuska
Juwairiya tayi murmushi kawai sannan ta sanar mata data hada mata ruwan wankanta..

'Da rana zainaba tace da ita suje gidan waziri..
Fafade daya suka dauka dan yayi musu rakiya..

Duk inda suka bi sai mutane su shiga nuna juwairiya dake bayan zainaba'
A haka har suka shiga gidan waziri..

    Hajara matarsa ce a zaune tsakar gidan sai diyarta KHADIJA dake gefe tana wasan diyar ka'ra..
    'Zainaba na shigowa khadija ta mike da sauri tazo ta rungume ta..

  Idonta ne yakai juwairiya dake can baya..
Taja baya kadan tana yastine fuska..
Wannan fa?ta nuna juwairiya..
Zainaba tayi murmushi sabowar baiwata ce..
Khadija tace,au ni tsoro ma ta bani wlh..

Zainaba tace konewa tayi fa,sannan ta karasa wajen hajara ta gaishe ta.
    Suna zaune suna wasan su juwairiya na rakube a gefe tayi shiru abunta.

Khadija tayi fari da ido tace,wai ina ya jalal ne?kinsan tun ranar dana zo wajen ki rannan ban sake ganinsa ba..

Zainaba ta tabe baki ai ke ya da'ma ni muna gida daya ma se mufi sati bamu hadu dashi ba..
  Sunyi fira sai da yamma sannan khadija ta shirya suka taho tare wai ita a dole sai taga yarima yau..

"Suna shiga cikin masarautar can a filin wasa doki ta kyallo shi a tsaye tare da wasu samari sa'annin shi..

   Khadija ta kalli zainaba tana washe baki,lah kin ga ma yayan can ashe..
Kafin zainaba ta amsa mata tuni ta ka'ra gaba cikin saurinta,zainaba ta girgiza kai lallai bata san wane irin so khadija kewa ya jalal ba duk da wulakancin da yakeyi mata ita bata ko gani.

    'Zainaba na cikin wannan tunanin ne khadija ta dawo da saurinta.
Zainaba tace,ah ah ya na ga kin fasa zuwan kuma?
Khadija tadan kwabe fuska ai bazan iya zuwa ni kadai ba kada ya gane dan shi naje wajen..

Ta riko hannun zainaba dan Allah muje ki rakani kinga se nace ki nazo yiwa rakiya muka ratsa ta wajen..
  Zainaba tace,wa!ni?ah ah wlh ban kije ke kadai abunki..

Juwairiya kuwa dake baya tana jinsu ne kawai,khadija ta hau magiya,dole tasa zainaba amincewa,ta juya tace wa juwairiya mu karasa can juwairiya, kai kawai ta gyada sukayi gaba...

*************
"Yarima gaskiya ni kam kayi min wayo gsky,duk yaushe ka kware a kilisa(wasan doki) haka ne?
Yarima ya murmusa cike da girman kai..zayyi mgn su zainaba suka iso wajen..

Khadija ta yi saurin gaishe shi ko amsawa bayyi ba ya wani dauke kai.
Zainaba ta tabe baki dama tasan haka zai faru ai.
Khadija tace,yaya kwana biyu?
Yarima ya juyo da shirin dizga ta idanunsa suka kai kan fuskar juwairiya...

Ai da sauri ya dauke kai yana fadin..
Menene wancan abun?
Wayace kuzo min da wannan abun?
Da mamaki duk suke kallonshi..
Ya kalli bawan dake gefensa,fitar min da wancan abun!(kice da kyamata)
Ya nuna juwairiya...
  Se sannan suka fahimta me yake nufi..
Zainaba ta turo baki,yaya baiwar tawa ce za'a fitar maka?

   Ya balla mata harara,bakya ganin fuskarta ne?(in a irritating tune)
Khadija ta fisgo juwairiya ta shiga janta daga wajen..
   Se da suka sha wata kwana sannan ta jefar da ita kasa tana fadin.
Kada ki kuskura ki kara tsayawa a gaban yaya  kinji na fada miki..ta tayi gaba..

Juwairiya taji wani abu ya tsaya mata a makoshi,tsanar yarima ta dasu a zuciyarta, itace wancan abun?
Kuka ta shiga yi tana tunanin wacce irin rayuwa ce haka suke fuskanta dan kawai su bayi ne se ake kyamatarsu ana zaluntarsu...
  Ta mike hade da kakkabe jikinta sannan ta rakube a gefe tana jiran uwar gidan ta zainaba....

***********
   A gajiye ta dawo rumfar bayi, fuskar nan babu walwala..
Tana shiga ta hango yan matan bayi nata wasan fado'wa wasu na gefe na langa..

  Hansai ta karaso wajenta tana fadin,sannu ya'ta se yanzu?
Ta gyada kai kafin ta karasa daki a sanyeye.
Har taci abinci ta kwanta,taga tunanin wulakancin da yarima yayi mata na neman yi mata yawa a cikin kwakwalwa hakan yasa ta fita waje itama ta shiga wasannin da akeyi abunta...




Wattpad @afreey101
[9/18, 3:10 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction )

NA Afrah bhai
Page 6
Wattpad @afreey101

*******************

**bayan shudewar shekaru bakwai**

'Gaba daya masarautar a war'gitse take.
A sanadiyyar bakin dauren auren YARIMA JALAL da diyar sarkin adamawa wato gimbiya SURAYYA da akeyi a ranar ta yau, wato shidda ga watan sa'tumba.

     'Mutane ne tan'kam cikin masarautar ko ina ka kai idonka bayi ne keta hidima ana ta shirye shiryen amsar dan'gin amarya dake tafe daga kasar adamawa...

   "Can na hango yan wasan doki suna ta kokarin shirya KILISA(wasan doki),A gefe kuwa yan busan algaita ne ke tayi masu kanguna ma nata bugawa take masarautar ta dau sautin ki'da me kayatarwa,yan wasan wuka da yan farauta ma nata nuna tasu bajintar..

*************
'Tun asubahi duk baiwar dake cikin Rumfar bayi bata zauna ba,rabinsu duk suna cikin madafa ne ana ta hada'hadar dahuwar abinci na gani na fada.
dan shanaye sun fi dari da mai martaba yasa aka yanka su banda kuma kaji da wasu kananan dabbobin.

"Hansai ce na hango duk hidima tayi mata yawa.
can sai ga wasu kuyangi sun shigo,wajenta naga sun nufa cikin saurinsu daya daga cikinsu tace,hansai wai ina JUWAIRIYA ne gimbiya zainaba na can nata faman nemanta.. tace idan mun ganta mu sanar mata da cewa su hadu da ita a can sashen gimbiya kilishi...

'Hansai ta girgiza kai...
lallai wannan yarinyar wato bata tashi ba kenan duk dukan da nayi mata da asubahin nan..
Laure ta kwashe da dariya,ai ni kam gara da Allah yasa zainaba ce uwar dakin juwairiya da ina fada miki tuni yarinyar nan zata jawo mana musiba sbd shegen son jikinta..

  Jakadiya tace,haba kun manta aikin data sha ne jiya daddare duk fa itace ta ba're wancan danyen waken.
jakadiya ta sake kallon laure dake faman wanke wanke tace,ke laure tashi kije ki sanar mata sakon uwar dakin tata ..

'Lkcn da laure ta shiga dakin juwairiya ta hango kwance akan taburmar ka'ba tayi dai'dai tana ta kwasar barcinta hankali kwance dan shaf ta manta da wani daurin aure da akeyi a cikin masarautar..

Laure ta shiga tashin ta..juwairiya maza ki tashi...!
A firgice ta farka tana gogar idanunta dake cike da barci..
Ni kuwa afrah na saki baki ina kallon kyakkyawar fuskarta,laure tace,se ki tashi dan yanzun nan uwar dakin ki tayi aiko a sanar miki daki same ta a sashen gimbiya kilishi...

Ai tun kafin laure ta rufe baki juwairiya ta mike da sauri ta zari gyelen ta tayi waje da gudu duk kiran da laure keyi mata bai sa ta tsaya ba .....

Gudu takeyi sosai dan shaf ta manta da maganar da sukayi jiya ita da zainaba..

Yau ta shiga uku!
Me ya same ni haka ne?
Wane irin bacci ne nayi haka!oh Allah!

'Abun mamaki tana zuwa sashen gimbiya kilishi ta tarar da sashen wayam babu kowa a wajen duk kuwa da  cikar da masarautar tayi a yau..
Ta karasa ciki tana kalle'kalle ko zata ga zainaba tunda tace kayan biki zasu zo amsa a wajen gimbiya kilishin...

    'tana faman leke'leke kawai taJi kamar wani ana kokarin shigowa..
Tsoro ne ya kama ta sosai dan kuwa tasan idan har aka kamata a ciki ba tare da zainaba ba kuma babu kowa acikin sashen toh kashin ta ya bushe...

   Bayan wani lalube ta boye jikinta na tsananin rawa..se addu'a takeyi Allah yasa ba gimbiya kilishi bace ta shigo ita tsoron matar takeyi..

   bata ankara ba sai Jin takon mutum tayi kawai..

Bugun zuciyarta ne ya linku...
Ta dafe kirjinta...ganin inuwar mutum a gabanta yasa ta runtse idonta gam dan ta sadakar da an gama kama ta....

  Shi kuwa yarima jalal mamaki ne yakeyi

Please Login or Register in order to submit comment