Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganin inuwar mutum a cikin labule dan kuwa ummansa ta shaida masa data kori kowa daga sashen na ta dan kawai yaje yayi shirin sa tunda nashi sashen cike yake da ya'yan sarakuna abokansa da sukazo dan daurin aure...
    
Bai bata lkc ba ya yaye labulen cikin zafin nama....

Idanuwansa ne sukaci karo da wata kyakkyawar fuska mai daukar hankali...

  Gabansa ne yaji ya fadi..haka kuma yaji gaba daya tunaninsa ya tsaya tsak..jinin dake jikinsa ma ya gaskare waje daya haka gangar jikinsa..

Juwairiya kuwa ganin an yaye labulen sai ta bude idanuwanta da suka fara cikowa da kwalla..
Ganin yarima jalal a gabanta sai ta dafe kirjinta.....
Abunda ya bata mamaki shine ganin bashi da niyyar hukunta ta sai ma wani kallonta da yakeyi..

Hakan ne Yasa tayi saurin zubewa a kasa dan ta sadakar yau ta'ta ta ka're....

Yarima kuwa baisan lkcn da yabi ta kasan ba shima,yana mata wani irin kallo data kasa gane na menene shi..

Can tabi kwayar idonsa ta fahimci fuskar ta yake yiwa wannan kallon..
Ai da sauri ta ware idonta tana saka hannayenta ta shafi fuskar ta..
Taji ta fayau,yau na shiga ukuna!

A Haka na fito?
Banyi tabon ba?

Ta mike ba saurinta jiki na rawa ta gudu tayi waje hankalinta a mutukar tashe....

   Shi kuwa yarima sai dai kawai yaga bata wajen dan ya lula cikin tasa duniyar.....

Da sauri ya mike yabi bayanta,amma ina....bai ga ko keyarta ba a wajen...

   Ya dafe kirjinsa dake bugawa..
Me ya faru dashi yanzun nan?
Wacece wannan aljanar yarinyar?
Ya lumshe ido yana tuna kyakkyawar fuskarta,kafin ya shige kur'yar dakin mahaifiyar sa yana tube kayansa yana murmushin da shi kansa bai san yanayin shi ba..

Juwairiya kam direct rumfar bayi ta koma cikin saurinta,Allah ya taimaketa duk babu jama'a a wajen suna can madafa, ta shige daki ta zube a kasa tana jin kirjinta nata bugawa..

Idan yarima ya gane ta fa?idan ya gano tabon karya takeyi fa?
Ta dafe kanta sannan cikin kankanin lkc ta maida tabon fuskarta sannan ta sake ficewa..

****************
"Tana shiga sashen zainaba ta zube a kasa tana neman afuwa..
Zainaba data zama cikakkiyar budurwa mai kyau da aji ta saki murmushi, ina tunanin kin manta da yau din bikin ya jalal ne ko..

Juwairiya tayi kasa da kai.. na sa ni ranki shi dade a gafarce ni...
Zainaba ta murmusa babu laifi,tashi muje sashen fulani...

'Koda suka zo shiga lkcn shima Turaki yake karasowa saurayi ne me cike da kamala sam yanayinsa ba kamar na yarima bane dan kuwa kullum shi kam fuskarsa dauke take da fara'a ..

      Yana ganinsu ya saki murmushi yace, gimbiya da kawarta,dan haka yake kiransu.
A tare sukayi murmushi kafin juwairiya tayi kasa da kanta ta gaisar dashi.
Ya amsa a sake sannan suka shige ciki a tare..

"Karfe biyar na yamma dangin amarya suka iso daga adamawa..
Gimbiya kilishi tare da mai martaba da fulani ne suka taro su da tarin bayi da yan ki'da...

"Bayan awa daya da aka basu dan hutawa da cin abinci..
Sai aka fito kuma babban fili a inda aka shirya musu babbar liyafa...

       Zainaba ta kalli khadija dake ta tabe baki tana yatsina fuska.
'Ke wai har yaushe zakiyi yawo ne,da ajinki ki zauna ana ta miki rashin mutumci..
Khadija ta shagwabe fuska,ai kin san dai ya jalal mijin mace hudu ne ko sannan kowa ma ai ya sani auren hadi ne akayi masa...

     Juwairiya ta girgiza kai dan kuwa har ta soma gajiya da surutan khadija kullum bata da abun mgn se ta yarima,ta tabe baki ita kam ko a kafa aka daura mata shi kwancewa zatayi ta yar ta tsani girman kansa da shegen gadara mtsw......

A tare suka mike bayan an aiko musu da sakon cewa za'a fara liyafar.
Khadija ta banka wa juwairiya harara.
Ke ina zaki?
'A hakan zamu tafi dake  ki sake tsorata ya jalal din?
Zainaba ta daure fuska,kinga khadija bana son shishshigi,abunda ya faru da dadewa shikenan kin din ga maimaita shi..

   Khadija tace haba zainaba,kalli fa shigar ta ki gani ga fuska kuma a kone..

Zainaba tabi juwairiya da kallo,ita bata damu da tabon dake fuskarta ba amma kayan ne ko irin su jakadiya ma da uwar soro da du'bu ai ba saka irin su sukeyi ba..

    Zainaba ta koma daki ta fito da wata jar atamfa...
Ta mikawa juwairiya amsa ki canza zuwa wadan nan..
Juwairiya ta ware ido ni?ta nuna kanta..

Khadija tace,da' wa?
idan ba ke ba uhm?
Juwairiya ta amsa a sanyaye sannan ta shiga ta sanyo kayan..

Tana fitowa sukabi ta da kallo...
Duk da dogowar riga ce a jikinta amma sai da shape dinta ya bayyana..

Ita kanta sai datayi mamakin irin dirin ta tunda dai bata taba saka kaya irin wannan ba...
ko kadan bataso ta saka kayan ba amma babu yarda zatayi tunda baza ta iya musawa hakan ba.

   Khadija ta tabe baki babu laifi... (nan kuwa kishi takeyi.)
Zainaba kanta sai data tsorata da ganin canzawar da juwairiya tayi amma ta da'ke tace muje...

'Wuri yayi wuri mutane kamar ba gobe..
Su khadija suka zauna a inda aka tanadar domin su..
Juwairiya kuwa ta koma layin yan uwanta bayi sai kalle kalle takeyi kada su ummanta su ganta da wannan shigar...
  

Wattpad @afreey101


[9/18, 3:13 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction )
Na Afrah bhai
Page 7
Wattpad @afreey101


******************************

"Ta'ro yayi taro anci an'sha anyi kuma wasanni sosai..
' sai wuraren karfe goma na dare sannan aka tashi,an kai amarya sashen ta dayaji gyara cikin tsari na gargajiya.

     'Surayya an sha wanka cikin turare ga turaren jiki kuyangin nayi mata kamshi kam ba'a mgn.
    Wata riga ta saka marar nauyi sannan aka daura mata alkyabba mai kyan gaske..
    Tana nan a zaune bayinta na ta kara gyara cikin dakin sai ji sukayi ana sanar da shigowar yarima.
Ta kallesu fuskar nan ba a daure tace,ku fita duka!
Jiki na rawa duk suka fice da saurin su..

  'Da sauri Ta sake gyara fuskarta tana kokarin rufe fuskarta taji shigowar ango..

'Yarima cikin kasaita ya karasa gaban gadon yana bin'ta da kallo...
ya rasa dalilin daya sa mahaifiyar sa ta matsa masa akan ya amince da auren wannan yarinyar..
'shi dai yasan ko'da ya fara ganinta lkcn da mai martaba ya matsa masa akan yaje zance dan su fahimci junansu kwata kwata batayi masa ba..
Tunawa da wannan kyakkyawar fuskar da ya gani dazu yayi,wacece ita?a ina kuma zai sake ganin ta?
 
'Surayya dake lullube taji wani irin haushi ya turnike ta,
miye haka zai wani shigo ya zauna shiru kamar ya manta da anyi ajiyar ta..mtsw....

    Ni kike wa tsaki...?
Taji an fada da murya me cike da gadara da kasaita..
Ware ido tayi dan kuwa duk a tunaninta a cikin zuciyarta ne tayi tsakin..
   Shiru tayi masa tana runtse idonta..
Yarima ya mike tsaye..yace...
'Naga alamar tun ba'a kai ko ina ba kin fara raina ni ko...

'Surayya tayi shiru tana jin haushin kanta data bari har tsakin ta ya fito fili..
Yarima yaja gundun tsaki,sannan yace bana mgn kana shareni kin gane?..
Surayya tace a sanyeye, kayi hakuri..
Ya sake tabe baki,
bude fuskarki...
Ta saka hannu a nutse ta yaye lullubinta...
   Yarima dake tsaye agabanta ya kura wa fuskarta ido..
Ko kadan baiji kwatankwacin abunda yaji dazu ba..meyasa?

Yadan ja tsaki..
Ya sunanki ma?
Surayya taji wani irin abu ya tukare mata wuya,mai?miye sunanta?dama bai san sunanta ba kenan?amma ai koda sukaje gidansu ta tabbata yaji sunanta..

'Tadan daurefuska, baka san sunana ba ashe..
Yarima ya shafa sa'jen dake kwance a fuskarsa..
  Tambaya kike?ko mamaki kikeyi?
Surayya ta dan murmusa idan nace duka biyun banyi laifi ba..?

  Yarima daya so gundura da mgnr yace..
Bana son ana maida min tamabaya ta da wata tamabayar..

Surayya tadan tabe baki,lallai wannan mutumin akwai son mulki..
Sunana SURAYYA...ta fada tana kafe shi da ido..

Yadan gyada kai,toh surayya dan matsa min na kwanta nima yayi mgnr yana karasawa gefen gadon..
'Surayya haushi ne ya kama ta,wane irin daren farkone haka ta matsa mishi? bashi ma da niyyar yin komai ma kenan?ita dai ba haka taji ana fadin daren farkon ba...
tana kallonshi ya rage kayan dake jikinsa yazo ya tsaya yana mata nuni da ido irin ke nake jira dinnan..

'Surayya taja gefe da sauri yarima ya hau ya kwanta yana runtse idonsa..

Duniyar tunani ya tafi,meyasa yake jin hakane?kodan baya son yarinyar ne?yadan bude idonsa,yasan cewa gobe dole ne gimbiya kilishi ta turo a duba mata ko wani abu ya shiga tsakanin sa da surayya tunda haka al'adar take,ya sake runtse ido,baya jin ze iya kwanciya da yarinyar can a yau, tunani kawai yakeyi har  barci me dadi ya dauke sa cike da mafarkin wannan kyakkyawar  fuskar daya gani..... .

********
'A wajen juwairiya kuwa,bayan taro ya tashi suka taho tare da zainaba,suna tafiya juwairiya taji kamar takon wani a bayansu,ta kalli zainaba a tsorace itama kanta zainaba haka jikinta ya bata,da sauri juwairiya ta jawo zainaba suka boye bayan wata bishiya,zainaba tayi kasa da murya..
  Waye yake bin mu?
Juwairiya ta girgiza kai nima ban sani ba ranki ya dade..

Zainaba ta matse hannun juwairiya cikin nata tace..
Yanzu ya zamuyi ? mun shiga uku...
Juwairiya ta jawo wani itace ta rike tana jira wanda ke bin nasu ya karaso wajen ta buge shi...

       Tafiya yake yi yana waige waige yan matan daya biyo daga wajen taro yake nema ina suka shiga ne?
     Baiyi aune ba sai dai yaji saukar itace a bayansa...

  Matse bakinsa yayi ya juyo yana musu kallon mamaki..
Gaba daya jikinsu rawa yakeyi..
Zainaba ce tayi saurin cewa..
Waye kai?meyasa kake bin mu?
Mustapha ya daga hannunsa irin surrender dinnan yace..
Kuyi hakuri yan mata dama zuciyata ce kuka taho da ita shine nake binku domin an amso ta..

Kallon juna sukayi,juwairiya ta shiga gaban zainaba wai ita nan tana kare tane..
Tace,malam kasan kuwa dawa kake mgn,gimbiya zainaba ce fa DIYAR SARKI kuma uwar dakin juwairiya...
Mustapha yace,madalla yanzu zan dan samu nutsuwa tunda na ji sunan masoyiyar tawa ZAINABA....yaja sunan yana lumshe idonsa..

Da kallo suka bishi..balle zainaba dake ta lekowa tana karewa fuskar shi kallo..
Kyakkyawa ne ,chocolate color kuma yana da tsayi sosai se de siririne..
    Juwairiya zatayi mgn zainaba ta dafa ta..

Mustapha yace,gimbiyata Allah yasa wani bai min shigar sauri ba ko,ya fada hade da karkace kansa..
Zainaba bata san lkcn da murmushi ya subuce mata ba sannan ta girgiza masa kai cike da kunya ta juya da gudu tayi gaba..
Juwairiya cike da mamaki tabi bayanta..

*************
'Da safe juwairiya na gani zaune laure na mata kwan'tar(tsifar)kai..

Laure tace,kedai yarinyar nan anyi kazama wlh kitso se ki barshi har kusan wata daya,gashi Allah ya baki gashi amma kwata kwata bakya kula dashi.. wai ni yaushe rabon ma da ki wanke shi ne?

Laure jin ita kadai keta zancenta yasa tadan kai mata duka..
Bakya jina ko?
Juwairiya ta kai hannu wajen da laure ta duke ta,ta turo baki haba goggo laure ina jinki fa wlh.
Laure tace karya kike,wai tunanin menene kikeyi ne haka?

Juwairiya tace babu komai,sai kuma ta mike da sauri tana kwace kanta daga hannun laure..
Goggo laure ina zuwa,ta shiga daki tayi shirin ta ta fito da gudu tayi hanyar sashen zainaba...

Tana shiga ta tarar da ita a tsaye,da sauri ta karasa wajenta lafiya ranki ya dade?..
  Zainaba ta sauke ajiyar zuciya yauwa dama ke nake ta jira,zauna..kiji....

Juwairiya ta zauna tana saurarenta.
Zainaba tace,dazu wannan saurayin ya turo min da wasika..

Juwairiya ta saki murmushi me yace ranki shi dade nasan dai da gani sonki yakeyi..ko?
Zainaba ta rufe fuska wai haka yace..

Juwairiya tayi dariya kasa'kasa dan ta lura uwar dakin tata ma ta fara zurmawa dayawa..
Zainaba ta gyara zamanta sannan ta buga tagumi,amma kinsan me yace?

Juwairiya ta gyara zaman itama ah ah se ranki ya dade ta fada min.
Zainaba ta turo baki..
Wai idan na amince masa toh naje da Fure (flower) na same sa a zaure na biyu yana jirana kafin su tafi..

   Juwairiya tayi murmushi, kada ki damu ranki ya dade akwai wani fure me kyau dasu yasira ke cirowa zan samo miki shi..
Zainaba tayi murmushi, yauwa juwairiya yi maza kije toh..
Juwairiya na murmushi ta mike ta fita..

"Sashen hamza ta nufa dan anan ne yasira ke aiki,ta jawo ta waje ta tambayeta ina ne take ciro furen?
Yasira tadan waro ido,juwairiya yaushe rabon da ki ganni da wannan furen?yanzu fa kinsan an tare sashen..

Juwairiya tace,wai dama sashen waye?
Yasira tace,sabon sashen matar yarima jalal ne..
Juwairiya hakanan taji gabanta ya fadi,ta juya kawai tayi gaba..

Tsaye tayi a kofar shiga sashen,tunani takeyi ko ta shiga ko kada ta shiga,bata son ko kadan ta hadu da wannan yariman...
   Leke tayi karaf ta hango itaciyar furen kuma akwai dayawa a jiki...
  Taja lumfashi sannan kai tsaye tayi wajen tana waiwayen bayanta..
  
*************
Yarima jalal ne na gani a tsaye gaban surayya dake ta kwasar baccinta a takure.
Ya kura mata ido ko tunanin me yakeyi oho..
Haske ya gani yana ratsuwa dakin daga window yana taba fuskarta..

  Juyawa yayi yazo gaban window din yana kokarin rufe labulen ya hango ta..

  Dauke kai yayi da sauri dan kuwa konannen sashen fuskarta yaci karo dashi ,zuciyarshi yaji ta baci,ya tsani yarinyar can baya son ganin irritating face dinta ko kadan,duk da ze iya kirga ganin ta da yayi a masarautar..

   Ya juya kawai ya fito a fusace dan bai ga me ya kawo ta sashen ba..
   Yana fitowa bayin dake tsaye bakin kofar suka shiga gaisar dashi..
Bai amsa musu ba kawai yayi waje abunsa..

******
Juwairiya ta ciro furen daya mai kyau sosai..
takai hancinta tana shakar kamshinsa me sanyi..
Ta tabbata dole ne zainaba ta yaba mata idan taga turen..
Har ta juya zata fice taji ance..

    Me ya kawo ki nan!

Da sauri ta tsaya tsak..
Cikin kasaita ya karasa gaban ta yana yatsine fuska..
Juwairiya ta zube kasa tana sunne kanta dan tasan babu abunda ya tsana kamar ganin fuskarta..

Dama...dama..uhm..na...
Yarima ya daka mata tsawa..
Ki bude baki kiyi min mgn!
Bana hane ki da nuna wannan fuskar taki a inda kika san ina nan ba?

Juwairiya tace,afuwa zanka shi dade uwar dakina zainaba ce ta umurceni da samo mata wannan furen ta nuna masa furen dake hannunta..
   Yarima ya tabe baki,ki ba'ce min daga gani...
yana gama fadar haka ya juya yai tafiyar shi..
Juwairiya tabi bayansa da harara sannan ta mike ta kakkabe jikinta tayi gaba.......

***********************
Pls share
Comments
And
Vote
[9/18, 3:13 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
NA Afrah bhai
Page 8
Wattpad @Afreey101

*************************

'Tana shiga sashen zainaba ta tarar da ita a tsaye sai safa da marwa takeyi.
Juwairiya ta mi'ka mata furen dake hannunta, ta amsa tana sakin murmushi me kayatarwa,gaskiya furen nan yayi min kyau sosai,se de akwai wata matsalar kuma juwairiya.. ta karashe mgnr kamar zatayi kuka..

     Juwairiya tace,matsalar me kuma ranki ya dade ba dai har sun tafi din ba?

'Zainaba ta girgiza kai,dazun ne fulani ta aiko min da sakon cewa kada na fita ko ina  zata aiko min da wata mai magani ta dubani akan yawan ciwon cikin nan da nake fama  dashi ,kin kuma san halin fulani, har fa wani bawa ta ajiye a kofata wai dan kada na gudu sbd bana son magani..yanzu ya za'ayi na fita kenan?

         'Juwairiya tadanyi tunani kadan sannan tace inda ranki ya dade ba zata damu ba ina da shawara..
Zainaba tace da gaske?
Juwairiya ta gyada kai ..
Zainaba tace fadi muji..
Juwairiya tace ko naje na sanar dashi bazaki iya fitowa se shi din yazo nan..

Zainaba ta ware ido...
Ah ah bana so yazo nan juwairiya..ta karashe mgnr a shagwabe tana kallon juwairiyar..
Can kuma tace,yauwa! Tasa hannu taja juwairiya zuwa dakinta...

'Cire.....ta fada kai tsaye..
Ciki da mamaki juwairiya ke kallonta..me zan cire ranki shi dade ?
Zainaba ta nuna kayan dake jikin juwairiya..cire kayanki ki bani..
A tsorace juwairiya tace,kiyi hakuri ranki ya dade amma.....

Zainaba tayi dariya,ba ina nufin ki tu'be min ba dan naga jikin ki ba..
Ah ah ina so ne muyi canjen kayane kawai kin ga babu wanda zai san ni ce na fita bake ba ko?

    Juwairiya ta gyada kai,wato wayo zakiyi wa fulani ko?amma idan aka kama mu fa?ni gsky tsoro nakeji..
Zainaba ta murmusa kada ki damu bazan jima ba zan dawo,kedai kawai cire kayan ki bani..

Juwairiya a sanyaye ta cire kayanta,zainaba ma ta cire nata ta bata..
Juwairiya tabi kayan da kallo,ina zata iya saka wadan nan kayan?
Ta girgiza kanta,ranki shi dade bani da matsayin da san saka wadan nan kayan..
Zainaba ta harare ta,amsa!
Kuma umurni nake baki daki saka su yanzun nan!
Juwairiya ta amsa a tsorace..
Tana kallon zainaba bata nuna wani kyama ba ta saka nata kayan tana dariya tace,lallai ke kam wannan kayan naki ashe walawa kike yi sosai..(ta fada tana jujjuyawa cikin katoton rigar juwairiya )

Juwairiya dai da kallo kawai take bin ta,a sanyeye ta saka kayan itama atamfa ce riga da zani sai wata alkyabba ja da ruwan madara,ita kanta tayi mamakin yarda kayan suka amshe ta....
Zainaba tabi ta da kallo,lallai juwairiya Allah yayi mata baiwa dayawa,se de kawai yanayin data tsinci rayuwarta ne...
     Zainaba tace,toh ni na tafi,ta dauki furen ta tana sake fadin,babu wanda zai gane ni ce,ta saki murmushi tayi gaba..

juwairiya ta zauna a takure tana tunanin idan wani ya shigo fa yanzu tasan tabbas kashin seya bushe..
    Motsin dataji ne a waje ana sanar da shigowar turaki yasa ta saurin komawa shinfidar zainaba ta kwanta hade da juya bayanta ta rufe rabin fuskarta..

   A tsanake ya shigo falon cike da takonsa yana mamakin rashin ganin juwairiya da bayyi ba..
    Yan matan fulani naji mun kusa hutawa da jinyar ciki ko?dazu fulani ke sanar min an kawo me magani daga cikin katsina..

     Juwairiya tayi wiki wiki da ido,bata so ko kwakwaran motsi tayi turaki ya gano ita ce..
Turaki ya zauna yana mamakin shirun da zainaba tayi masa..
To wai ko barci take ne ?
Yana wannan tunanin ya mike har ya kai bakin kofa yace, ko ina kawarta ta tayi yau oho..

   Juwairiya najin fitar sa ta sauke ajiyar zuciya sannan ta mike zaune,se a lkcn ta nuna da inda take zaune(wato akan kilisar zainaba ),ta mike da sauri tana sake kallon shigarta,tabbas bata taba saka kaya irin wannan ba,ta dan murmusa zataso ummanta dasu jakadiya su ganta a cikin irin wannan shigar..
Wani tunani ne yazo mata..
Da sauri naga ta shige dakin zainaba ta dauko mirror tana kallon kanta..

    Ita kanta wani lkcn idan taga fuskar ta a haka tsoro take bata..
Hannu tasa a hankali ta fara goge tabon har kyakkyawar fuskarta ta bayyana..

    Ta kurawa fuskarta ido..
Motsi taji daga falon..
Da sauri ta mike jiki na ba'ri ta fito zuwa falon tana leke...
Sai ji tayi bawan dake waje yana daukar izinin zainaba  dan zagawa bayan gida..
  TOh!
Kawai ta fada a da'ke sannan tace,wai ina zainaba ta tsaya ne?(tayi mgnr kamar ta fashe da kuka)
Gani nayi Tadan jawo hular alkyabbar ta rufe rabin fuskarta tana fadin,dole ne naje na dawo da ita tun kafin asirin mu ya tonu,ba tare da wani tunani ba tayi waje da saurinta..

**************
'Surayya na tashi daga barci taga wayam babu yarima a dakin.
tsaki taja cike da takaici,wai yau itace gimbiya surayya ake wulakantawa har haka,wulakancin ma wai daga namiji..

Ta juyar da kwayar idonta tana tuna irin  samarin dake tururuwa a wajen neman aurenta,amma gashi sbd wata tsohuwar abokantaka dake tsakanin mahaifinta da mahaifin yarima jalal an kawo ta nan se wulakanta ta akeyi..

      Ta kalli shinfidar gadonsu cike da takaici,ta tabbata duk bayin da zasu shigo da kuma yan uwanta da zasu zo mata bankwana toh gulma ce zata kawo su dan  ganin  yarda daren farkon ta da yarima ya kasance...

Abu daya data tsana a rayuwarta shine a ga kamar bata isa ba (she hates pple downgrading ha),bata son ko kadan a raina ta,sbd ta mallaki komai a rayuwarta, tana da kyau,gata diyar sarki,yanzu kuma matar yarima me jiran kujerar mulki...

Wani tunani ne yazo mata..
Ai da sauri Ta mike da ta tube duka kayan dake jikinta tas..
Sannan tasa hannu ta hargitsa shinfidar gadon,ta dauko yar karamar wuka dake cikin tiren fruits ta hawo kan gadon tasa wukar a finger dinta tana runtse ido ta tsakawa kanta wukar kadan'sannan ta samu jinin ta dake ta di'qa ta shiga shafawa a wani bangaren gadon....

       Yamutsa gashin kanta tayi dayasha gyara sannan ta ja bargo ta rufe kanta tana kuka kasa kasa..(yarima yayi kadan ya jawo mata raini,dolene ta nuna masa wacece SURAYYA)

   'Bayi ne tare da yakumbon ta suka shigo dakin da jakadiya a bayansu..
   Ganin halin da take ciki yasa duk suka saki murmushin murya suna gyada kai cike da gamsuwa..

Yakumbo ta karasa wajenta tana dago da ita zuwa jikinta..
Sannu surayya,sannu UWAR GIDAN YARIMA JALALLUDEEN...
ai duk mace idan tayi aure dolene ta fuskanci wannan  daren farin cikin,amma daurewa zakiyi kinji?
Surayya dake sunne kai ta gyada kai,yakumbo ta ciro zanin shinfidar  ta mikawa jakadiya dake ta gyada kai cike da farin ciki,lallai yarima an  girma...

     Jakadiya na amsar zanin da saurinta ta karasa sashen gimbiya  kilishi dan aiwatar da umurninta..

    Uwar soro na ganin jakadiya ta karaso sai washe baki takeyi..
yasa tayi sauri wajen fadin isowarta cikin kirarinta masu tsada...

    'Gimbiya kilishi na a kishin'gi'de jakadiya ta shigo tana bayyana mata zanin dake hannunta..
Wani irin murmushi ta saki..

Jakadiya tace, gimbiya uwar gidan mai martaba, ina miki albishir da a daren jiya yarima ya zama cikakken namiji....
   Kilishi ta gyada kai cike da gamsuwa tace,wannan albishir naki jakadiya ba karamin farin ciki ya saka ni ba,dan haka ina so ki samu shamaki a baki azurfa goma a matsayin Tu'kwicin ki.......
   Gu'da jakadiya ta saki hansai dake zaune kusa da kilishi na tayata sai murna sukeyi..ni kuwa afrah nace 'Oh"

***********

"Mustapha ya dade tsaye a babban zaure yana jiran zuwan zainaba..
Shiru har sai da abokinsa yazo ya sake sanar dashi  cewa shi kadai ake jira su tafi rana keyi...

  Ya cire rai kwarai da zuwanta har ya juya zai fito ya hango wata ta tunkaro wajen..se de shigarta kawai ya nuna masa ba ita bace ba..
     Yana fitowa tana karasowa wajen..
Ta yaye lullubin dake kanta tana sauke lumfashi sosai sbd tsabar gudun data sha..

Mustapha cike da mamaki yana bin ta da kallo,wai dama kice haka?
Zainaba ta gyada masa kai sannan ta fito da furen data boye cikin riga ta mika masa..

   Wani irin farin cikine ya lullube sa..
Yasa hannu ya amsa sannan yace..
Nagode kwarai da kika amshi tayin soyayyata,ina miki alkawari akan bazakiyi dana sani ba gimbiyata..

"Zainaba ta rufe fuskarta cike da kunya tana murmushi..
Mustapha yace,duk da baki damu da sanin sunana ba bari ni nayi karanbanin fada miki..

Zainaba ta bude fuskarta tana kallonsa kafin tace,kawai ka riga ni fada ne amma nima yanzu nake shirin tambayarka..

Mustapha ya gyara tsayuwarsa, kice ma har tunanin mu iri daya ne kenan ko?
Zainaba ta murmusa kawai..
Yace,toh sunana Mustapha dan gidan WAMBAN kano..ina fata matsayina yakai da yin soyyaya da diyar sarkin daura...
   Zainaba tace,kwarai kuwa..
Yace toh nagode....
A nan suka hau yar firar su sama sama...

*********
'A wajen juwairiya kuwa sauri kawai take bugawa,har tazo hanyar da zata kaita inda su zainaban suke amma sai ganin jama'a tayi sunyi yawa a wajen sosai..

Ta cije yatsan ta,yanzu ta ina zata bi kenan?
Hanya da'yace kawai zata iya kaita kuma sai ta bi ta sashen samarin gidan,wato sashen su turaki kenan..
Kafada ta daga lkcn data karasa sashen taga babu kowa a wajen,ta saki lumfashi tace, ina tunanin duk suna fa'da ne...

   Tafiya take cikin sauri kanta a kasa..
Batayi au'ne ne kawai taji taci karo da mutum..
  A tsorace ta dago da kanta.....

'HAMZA....
ta furta a cikin zuciyarta....
A take tsoro ya mamaye ta.
dan ba sau daya ba,ba sau biyu ba tana jin bayin dake aiki a sashen sa suna yawan fadar halayensa na mugunta idan har akayi masa ba daidai ba toh lalle a ranar kashin ka ya bushe ne..

    Fitsari ne kawai bai fito mata ba..
Amma mai?
Gani tayi hamza ya tsaya kamar an shuka shi a wajen...
Kallonta kawai yakeyi baya ko kyafta idonsa..

  Ta'ke tabi inda kwayar idonsa dan gano inda yake kallo ajikinta dan ita a tunaninta ko kayan dake jikinta ya gane na zainaba ne su..
Amma se gani tayi fuskarta kawai ya kura wa ido..

'A Take ta fahimci ta sake tafka kuskuren fitowa ba tare da tabon fuskarta ba..
   Hamza yaja lumfashi...yace,
Baiwar Allah kin samu batar hanya ne...?

Yarda yayi zancen cikin wata kaukausar murya ne yasa ta sake jin hanjin cikinta sun motsa..
   Da kyal ta iya furta.....
Eh..ka.. kayi hakuri...tayi kasa da kai tana shirin wucesa ne taji murya a bayansu..
Hamza me ya tsayar dakai haka?bana fada maka sauri nakeyi ba...
Yarima ne......( ta fada ba tare data kalleshi ba,dan ta gane muryarsa ce )...

'Yarima kuwa dake fitowa daga cikin falo

Please Login or Register in order to submit comment