Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amsa a wajensa,kuma shi ya umurceni dana je wlh..
Laure tace,ki kula dai kinsan haukan kishin matarsa atooh..
Juwairiya ta gyada kai zan kula goggo...

**************
"Gimbiya kilishi ta kalli fulani diyya suna zaune a fadar mai martaba.
ina ganin tunda lkc ya matso kusa ya kamata mu fara shirye shirye a kan lkc..

Fulani tayi murmushi, hakane zan saka turaki ya hadu da hamza se suyi duk abunda ya dace..
Mai martaba ya murmusa, sai dai nima akwai alkawarin da nake so na cikashi a wannan babbar ranar..
Kilishi tace,muna jinka..
Mai martaba yace,akan auren yarima ne da diyar waziri nasan kun san da wannan mgnr amma ina ganin kamar lkc yayi dana cika alkawarin dana dauka shekaru dayawa da suka wuce,tunda dai anyi auren sa na farko ..
Kilishi tadan tabe baki,hakane tunda ya zama dole mu cika wannan alkawarin..
Fulani tayi murna sosai tace,lallai yarima ya cika dan gata,mai martaba yace,ai da mun gama dashi zamu zo kan sauran suma,sbd dai akwai diyar galadima da nake so a hada da shi hamza,shi kuma turaki nayi masa mgnr jikar sarkin zazzau...

Kilishi murmushin yake tayi dan ita kam tana wa hamza tanadin diyar sarkin katsina,mai zanyi da wata diyar galadima lallai kam....

"har an gama mgnr su kenan suma?fulani ta tambaya cikin tsantsar farin ciki ..
Mai martaba yace kwarai kuwa lkc kawai nake jira..
Fulani tace toh Allah ya kaimu lfy..

**************
Surayya ce ta karaso cikin lambun cike da fara'ar ta,yanzun nan ta samu labarin na'din yarima da za'ayi a karshen satin nan...

   Hango sa tayi a tsaye yana karewa wasu tsuntsaye kallo...
  Ta karasa da saurinta ta rungume sa ta baya tana murna sosai..

  Yarima yana jin kamshin ta ya gane itace..
Surayya tace,ina taya ka murna sosai sarkina...
Yarima yadan murmusa,kodai kina taya kanki murnar zama gimbiyar daura?...

Surayya ta dawo gabansa,duka biyun daidai ne...
yarima ya gyada kai..
Surayya ta kamo hannunsa,sai yaushe zaka bani damar shiga zuciyarka?
Yarima ya kura mata ido,surayya ta karkace kai,naji lbrn aurenka da diyar waziri,hawaye suka taro a cikin idanuwanta....

Yarima yace, na zata duk wannan bazai dame ki ba...
Surayya tace,inji wa?ai duk mulkin mace bazaso ayi mata kishiya ba..
Yarima ya jinjina kai....

************
Juwairiya tare da zainaba suna tafe sai lbrn wasikar da Mustapha ya aiko mata take bata...
Suna kawowa kofar lambu zainaba tace,mu dan shiga naji kukan tsuntsayena,ta janyo hannun juwairiya suka shige ciki....

  "Turus sukayi ganin yarima da surayya rungume da juna...
"Juwairiya taji gabanta yayi wani irin muguwar faduwa har se da ta saka hannu ta dafe shi..
  Zainaba kuwa sakin baki tayi..ganin basu ma ji shigowar su ba yasa tace, sannunku masoya...!

  Da sauri duk suka juyo suna kallonsu..
Yarima idanuwansa akan juwairiya dake tsaye ta dauke kanta gefe,haka nan takeji zuciyarta wani iri,meye nata aciki dan kawai miji da mata na more rayuwar su..tasan dai ita harta mutu bazata samu wannan ba..

   Zainaba tace,lallai yaya ashe haka kake kaima?
Yarima ya banka mata harara,sannan yace me ya kawo ki nan?

Zainaba ta kamo juwairiya dake tsaye kamar an shuka ta,laah toh kuyi hakuri idan dan mu ne yanzu ma zamuyi tafiyar mu..

Surayya sai wani murmushi takeyi,tazo zata kamo hannun yarima,ya kauce yana sake kallon su juwairiya dake shirin barin wajen..
   Zainaba!

Ya kira sunan kamar me koyon mgn,zainaba cike da mamaki ta juyo dan kuwa ta dade bataji yayan nata ya kira ta da sunanta ba..

  Ta dawo gabansa tace na'am yaya..
Yace inaso ne kiyi min wata alfarma,

zainaba tace ina jinka yaya...

Ki bani waccan....!

Ya nuna saitin da juwairiya take a tsaye..
    Ba zainaba ba har surayya da juwairiya se da gabansu ya fadi..

Sai a lkcn ne surayya ta shiga scanning din juwairiya tana jin wani irin tsanarta ta dasu a zuciyarta, wacce baiwa ce har ta isa ta saka yarima ya bukace ta...

Ruwan harara ta shiga zubawa juwairiya, ita kuwa baiwar Allah ma bata san tana yi ba..

    Zainaba da mamaki tace,wa kake nufi yaya,dan a iya sanina baka ma son ko ganin fuskar juwairiya...
Yarima ya kasa amsa mata dan kuwa sai a lkcn ne ya fara jin haushin kansa,me yasa ya bari mgnr ta fito daga bakin sa...

Gani sukayi kawai ya wuce abunsa kamar bashi bane yayi zancen..

Surayya ma tazo wucewa zuciyarta kamar ta fashe..ta tsaya daidai saitin juwairiya sannan taja dogon tsaki tayi gaba..
Zainaba tace oh iko sai Allah...


************************
WATTPADIANS

_"Announcement- its a RUMFAR BAYI GIVE AWAY..._
_Get 5 people to add n vote for RUMFAR BAYI on wattpad"_
_"Your reward- you will always be the first reader of every page i write till the end of the story inshaAllah "_
_Am waiting fans,all the best to the 2 winner's_

[9/18, 3:19 PM] Aysha Galadima:          *RUMFAR BAYI*
      (A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 17
Wattpad @afreey101



***************
"Gidan waziri suka shiga,mutane har sun fara tarowa kasancewar yau ne sa lallen khadija..
A dakinta suka tarar da ita tasha gyaran jiki se fitar da kamshi takeyi...

   Tana ganin zainaba ta fada jikinta tana murna sosai..
Zainaba tace,kai duk murnar auren ya yariman ne haka?

Khadija ta dago tana murmush sosai, kema ai kin sani,mafarkin da na dade inayi gashi har ya kusa zamowa gsky.
na kusa mallakar rabin raina,ta kamo hannun zainaba, zainaba gobe yarima  zai zama mijina,ina tunani a duk duniyar nan babu wanda tafi ni farin ciki...

    Surutai kawai khadija ke sakar musu cike da tsantsar murnar ta.
juwairiya kam gaba daya taji jikinta yayi sanyi,ta rasa dalilin da yasa duk lkcn da khadija zata ambaci sunan yarima toh sai zuciyarta ta buga..

    Ganin zaman na neman gagararta ne sai ta mike kawai ta fito waje..
Mata ta iske cike da tsakar gidan ana ta faman girke girke..
   Ji tayi kamar lumfashin ta baya fita sosai..

Da gudu ta bar cikin gidan ta karasa can bayan gidan kusa da ra'fi mai gudana da ruwa...

    Sauke ajiyar zuciya takeyi sosai,wai meke faruwa da ita ne,me yasa take mafarkin yarima? Meye hadinta dashi?yafi karfin ta me yasa zuciyarta bazata bar tunaninsa ba..!
    Zama tayi a wajen saman grass, jin iska na kadata sai lumshe ido takeyi...

***************
"Ango kasha kamshi!

Magaji ya fada yana washe baki..
Hamza yace,ai yaya kai kam dan gata ne wlh mata biyu cikin wata biyu kacal..

Turaki yayi dariya,yarima ya banka musu harara,sannan ya amshe alkyabbar sa dake hannun magaji yana tayashi shiryawa..
     Hamza yace,gsky wannan sa lallen ya kamata mai martaba ya bari mu dan cashe ko ya kuka gani?..

Turaki ya kai masa duka,kai fa hamza dan duniya ne wlh,a ina ka taba ganin maza sunyi rawa a sa lallen?
Hamza ya mike yana fadin,ba sai a fara a kan mu ba,ni dai Allah ya gani gobe  A na'din sarautar ya yarima se na cashe abuna,kasan fa har wannan mawakin na dauko dake can kasar nijar..

Magaji yace,kai hamza akwai son bidi'a,duk suka saka dariya..
   Daga waje ne aka shiga sanar da shigowar da surayya..

Duk suka kalli juna suna murmushi, kafin nan suka mike,magaji yace,a lallaba mata ita don Allah...

Yarima ya tabe baki yana basarwa..
Suna fita ta shigo cikin adonta sai baza kamshi takeyi...
    Kallon juna sukayi,yarima ne ya fara dauke idonsa yana kokarin saka hular sa..

Da sauri taje ta amshe hular sannan tayi murmushin yake tace..
Wannan aikina ne ...
Yarima yace,sai yau kika sani kenan?
Surayya ta turo baki,toh kana kiran na ne na saka maka?

Ya wani basar yana fadin,naga kinsha shiri sai ina?
Surayya ta dan harara shi,ina fa?gidan amaryar zamuje dasu umma..
Yarima ya jinjinawa makircin surayya,sannan yayi murmushi ya fice abunsa ya bar nan cike da takaici..

  Surayya ta jefar da yar jakar dake hannunta, cike da fusata tace, dole ne nasan abunyi,ya za'ayi ace kamar ni yarima yake wulakantawa son ransa,sannan hakan bai isa ba ma ko shekara banyi da aurensa ba zasu sake aura masa wata?

  Ta tuna zancensu da yakumbo,lkcn data fada mata mgnr juwairiya..
 _ ''Miye abun tashin hankalinki akan wata banzar baiwa can ke da za'ayiwa kishiya cikin kwanan nan,idan har kinaso ki siye zuciyar yarima toh ki tabbatar kece kika fara haifa masa Da wanda ze ga'je shi a mulki"_

  "Surayya ta ciji lebenta na kasa,taya zata samu damar wani haihuwa bacin sai yarima yaga dama yake kwana da ita,dole ne ta san abunyi,dan ta lura gimbiya kilishi ma zata iya juya mata baya indai har wannan yarinyar ta shigo kuma ta rika ta haihuwar...

**************
"An gama dukkan shirye shirye na sa lallen khadija..

Surayya , Fulani diyya ,gimbiya kilishi tare da sauran matar sarki ne suka zo gidan, tare da su jakadiya,du'bu da kuma sauran bayi dayawa dan kawo musu lallen amarya..

"Bayan an zauna ne sai ga tawagar su yarima tare da abokansa da kuma yan uwa..
Nan aka tanadar wa amarya da ango wajen zamansu kamar yadda al'adar tasu take,sannan aka fara gudanar da event din,su jakadiya ansha gu'da,hansai sai raba idanu take ko zata dan hango diyarta amma bata ganta ba. ko ina ta shige oho?.

         Zainaba dake rike da hannun khadija ta shiga neman juwairiya dan ta dauko mata wani sako a dakin khadija data manta.

"A tsakiyar su khadija da yarima dake zaune taje tace a hankali, khadija kinga bari naje na dan duba juwairiya tun fa dazun ban sa ta a idona ba ko gida ta koma oho?amma nasan ma da kyal ne ta koma can bata nemi izini na ba..

Khadija tadan tabe baki,toh shikenan amma kada ki dade dan Allah,zainaba tayi murmushi kada ki damu yanzu zan dubo ta na dawo...

Duk wannan zancen nasu yarima yanaji..
   Ina take?ya tambaya a cikin zuciyarsa sai lkcn ne ya lura da bata a wajen,hakanan yaji yana son yasan ko tana lafiya,zuciyarsa ke ta azazzalar sa...

   Kallon turaki yayi dake kusa dashi..
"ina zuwa"
bai bari ya amsa masa ba kawai yayi gaba abunsa...

Gimbiya kilishi na lura da tashin da yayi daga wajen,ina zai je?ta tamabayi hansai dake gefenta,hansai tace,gimbiyata wata kila ban daki zai shiga,kilishi ta jinjina kai cike da gamsuwa..

Shi kam yarima fita yayi yana ta dube dube,lkcn har duhun yamma ya farayi...
  
**************
Juwairiya kuwa barci ne ya dauke ta a wajen dan dama bata samu barcin kirki ba a daren jiya...

    Yarima na zagayawa bayan gidan ya karasa gaban rafin yana sauke lumfashi....
me yasa zai damu kansa sabida wata baiwa can?

Yaja tsaki yana shirin juyawa sai kawai can ya hango ta...ta jingina a jikin wani bishiya tana ta sharar barci a takure..
     Karasawa yayi wajen ya kura mata ido,zuciyarshi yaji wasai ganin tana lfy,amma wannan barcin fa?

  Bakinta yaga yana motsi...
Ya duko sosai ahankali kusa da fuskarta dan son jin me take fada...

Ya..ri...ma.....!
Yaji ta furta....
Ware ido yayi cike da mamakin jin sunansa a bakinta..

Murmushi ya saki yana kare mata kallo,tabon fuskarta ya kalla yana son yaji dalilin da yasa take yin sa?
      Bai ankara ba sai gani yayi ta bude idonta tangaram a kansa..

    A tsorace take kallon sa...
Shi din ma yadan tsorata da ganin ta bude idonta,yana kokarin gyara tsayuwarsa kawai yayi loosing balance dinsa sai tim!
Ya fadowa juwairiya ajiki suka zube a kasa su duka..

   Wani irin kamshi ne ya mamaye hancin ta,taja lumfashi mai karfi,nauyin yarima ne yasa tayi saurin dago da idonta.

Hada ido sukayi,ta hada duka karfinta ta sa hannu ta ture shi gefe...
  Yarima ya lumshe ido yana jin wani irin yanayi yana ratsa shi..
   Juwairiya tayi saurin mikewa tana kallonsa..
Sai kuma Da sauri koma ta zube a kasa tunawa da tayi waye ta ture yanzun nan,yarima jalal ne fa....

   Allah ya huci zuciyar ka,kayi min afuwa...
   Yarima ya mike yana kakkabe kayan dake jikinsa...
     "Ni kika ture a kasa?
Juwairiya a tsorace tace,kayi hakuri ranka shi dade, kayi min rai...

Yarima yadan murmusa,
me kikeyi a nan?
Juwairiya a zuciyarta tace,kai ya kamata na tambaya ai,me kakeyi a nan bayan ana can ana sa lallen amaryar ka....!

      kallon da yake yi mata ne yasa ta fuskanci katobarar da tayi,wato mgnr zucin da takeyi ta fito fili kenan?wayyo Allah ta shiga uku..

Da sauri tasa hannu ta rufe bakinta,gani tayi ya tako zuwa gabanta,kirjinta na ta bugawa ...jitai yace,

   "Kina son sanin meyasa na baro amarya ta nazo nan?
Juwairiya ta waro ido tana girgiza kai..
Murmushi yayi,juwairiya ta kura masa ido kyaun sa na kashe ta..
Bai sake cewa komai ba yabi ta gefen ta ya wuce abunsa......



"Thanks fans,i can see that some of you r doing well with the GIVE AWAY"

Please
Vote
And
Share
[9/18, 3:19 PM] Aysha Galadima:         *RUMFAR BAYI*
     (A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 20

_"Congratulations to my 2 winners @530_khadeejat and @haliemahtou_
_Thanks alot for ur effort i really appreciate muah😘_"

*************

"Rabi na fitowa jakadiya ta tare ta,har kin dauko sakon ne?
rabi da jikinta ke rawa tana tsoron kada layar dake jikinta ta fado a gani tace,uhm na dauko,jakadiya tace,sai kuyi haramar komawa ina ita juwairiyar?
Rabi kam sauri kawai takeyi tabar wajen dan haka tace ai ta dade da tafiyar ta,bata jira me jakadiya zata sake ce mata ba kawai tayi gaba abunta..

   Tana fitane,jalal ya shigo dasu shamaki a bayansa,TAKAWARKA LAFIYA TORON GIWA...!
Jakadiya ta shiga wa'sa jalal itama, sabon sarki mai mulkin zamani,an shigo lafiya?

Jalal ya daga mata hannu kawai yayi shigewar sa ciki..
   Direct kofar wajen shakatawar sa ya nufa dan anan ne kawai yake iya samun privacy dinsa.
yana bude kofar ya lumshe idonsa hade da jingina bayansa a jikin kofar daya kulle...

    Juwairiya dake tsugunne a gaban flowers sai ji tayi kawai an rufo kofa gam!.
A tsorace ta juyo....
Sai ganin jalal tayi a tsaye ya lumshe idonsa,ya kuma daura hannunsa daya akan goshinsa..
sanye yake cikin manyan kaya na alfarma ga sajen fuskarsa daya karawa fuskar tasa kyau,daga inda take a tsugunne ta kura mishi ido zuciyarta na kyasa kyau irin na jalal...

      Jikinsa ne kawai ya bashi kamar ana kallonsa..
Ya bude ido ahankali yana mamakin yanda akayi bayi suka samu shigo masa garden bada izinin sa ba...

   Caraf ya ganta a tsugunne kamar daga sama..
Ba karamin mamaki yayi ba,dan asalima gani yake kamar mafarki ne yakeyi..

Irin kallon da take bin'shi dashi ne yasa shima ya kura mata nasa idanuwan..
Sai da suka shafe minti daya a haka..kafin kafafun juwairiya sukayi mata tsami,sai alokacin kuma ta tuna da halin da take ciki,tayi saurin mikewa jiki na rawa tace...
  Allah ya huci zuciyar ka,kayi min afuwa dama batar hanya ne nayi...ku...ma..sai...na..ga..waj...
Jalal ne ya tsaida ita..da daga mata hannunsa dayayi..

   Shiiish ya daura yatsan sa akan leben sa..sannan ya shiga takowa har ya kawo gabanta ya tsaya..
  Kirjinta ne ya shiga bugawa....tayi saurin sauke idonta kasa..
     Jalal da muryarsa mai dadin amo yace, me ya kawo ki sashen na?ko baki san hukuncin shigowarki nan din ba ne?

Juwairiya ido ya kawo kwalla,na..na..sani..amma...ka..kayi hakuri dan..darajar Allah...
   Jalal ya murmusa yana jin wani irin nishadi na dibar sa..

  Dago ki kalleni...ya bata order..

Juwairiya ta sake kasa dakai,mai martaba yin hakan a gareni kamar raini ne..
Jalal ya sake murmusawa,sannan ya kama hannunta...
a tsorace ta dago da kanta suka hada ido dashi,ji tayi gaba daya jikinta yayi lakwas...
   Jalal ya janyo ta sannan naga ya bude wata secret door sun shige daga ciki...

      Bude baki tayi ganin su a cikin kogin mai martaba...
   Jalal ya kura mata ido ganin yarda ta saki baki tana kallon wajen..
Juwairiya ta juyo tana kallonsa..
Wani irin murmushi ta sakar masa da ita kanta bata san miye dalilin ta na yi masa shi ba..

     Jalal yaji bugun kirjinsa ya linku,bai taba ganin ta tayi murmushi haka ba..
  Juwairiya ta zare hannunta daga nasa tana sake juyawa tana kare wa wajen kallo..
"Jalal ya kura mata ido kamar ya samu TV..

  Wani tunani ne yazo mata acikin zuciyarta ,sake juyawa tayi ta dawo kusa dashi ta dukar dakai..
Cikin sanyin murya tace..

"Ranka shi dade idan bazaka damu ba ina so nasan dalilinka na kyautatamin da kakeyi a cikin yan kwanankin nan,nasan bani da hurumin yi maka wannan tambayar ,amma zuciyata na mutukar son taji amsar ka..

  Jalal ya lumshe ido ya bude..
Me zai iya fada mata,shi kansa bai gama sanin dalilin sa ba..
  Tambayar dake cin zuciyarsa ce ta fado masa shima ,meya sa take boye fuskarta da wannan tabon...?

    Juwairiya taji shirun yayi yawa..
Ta dago suka hada ido...
Gani tayi jalal yasa hannu ya fisgo ta da karfi..
A tsorace ta shiga bashi hakuri..amma inaaa bai tsaya ko ina da ita ba sai gaban kogin...

    Jikin juwairiya ya hau rawa..kayi hakuri ranka shi dade na tuba!bazan kara ba..kayi min rai!
  Jalal bai saurare ta ba.. kawai sai ji  tayi yasa hannu a wuyanta  ya tura kanta cikin ruwan..

   Wani irin ihu ta saki tana jan lumfashi kamar zata mutu,me yasa jalal yake shirin kashe ta?me tayi masa?tunani iri iri ke yawo acikin zuciyarta,ta sadakar da sake yin wata rayuwar sai ji tayi ya dago da ita ya fito da kanta acikin ruwan..
    Idanuwanta ne da sukayi ja ta kura masa ido cike da tsantsar tsoro da kuma mamakin abun da ya aikata mata a yanzu..

Jalal kansa kallon fuskarta yakeyi kafin nan ya juya ya koma kofar da suka fito...
bai dade ba ya sake dawowa gabanta dauke da mirror a hannunsa..
Duk abunda yakeyi kallonsa kawai takeyi,ta rasa me yake tunani haka,kashe ta yake sonyi???

Jitai yace...
   "Kalla nan"
  Madubin dake rike a hannunsa ta kalla...
Fuskarta ta gani tangaren babu ko di'gon tabo a jiki..
   Ware ido tayi sannan ta kallesa da sauri..

Jalal ya gyara tsayuwarsa..
Zaki iya fada min dalilinki na boye fuskarki da wannan tabon na karya?
Gabanta ne ya shiga faduwa jikinta ya hau rawa,tun yaushe yarima yasan wannan sirrin nata?yau ta banu!
  Jalal ya sake fadin..
Idan har zaki iya fadamin dalili toh nima zanyi kokari na samu amsar tambayar ki na kyautata miki da nakeyi...
 
"Juwairiya taji kuka yazo mata,me zata iya fada masa?taya zata iya fada masa ma sbd ta tsare mutumcin kanta ne yasa take boye fuskarta da tabon karya...

  Zubewa tayi a kasa tana kuka sosai..
Jalal ya dan dafe kansa..
Kafin ya duka kasan kusa da ita yace..
Ba kuka na tambaye ki ba!

Juwairiya ta dago da jajayen idonta tace.
Ranka shi dade  idan na fadi maka nayi hakan dan kawai na tsare mutumcin kaina ne zaka yarda dani?

Jalal cike da rashin fahimta yake kallonta..
Juwairiya ta shiga goge hawayen ta tana sake fadin..

A wajenku ku masu mulki da iko mu bayi ba komai bane ba,kun dauke mu tamkar kayan kazanta ko kayan da zaku iya sakawa ku yar ba tare da kun damu da feelings din mu ba..
bamu da wani galihu ko girma a idon ku..
ta nuna kanta tace,ni yarinya ce dana taso cikin tarbiyyar iyayena wadanda suke bayi a karkashin ikon ku,na taso ne acikin RUMFAR BAYI kuma tabbas naga yarda mata yan uwana suke fuskantar musgunawa da cin mutumci a wajen wadan da suka fisu karfi da mulki..
Taja lumfashi...
A lalata rayuwar su ko kuma a siye su a matsayin SA'DAKA ba'a damu da nasu ra'ayin ba.
mahaifiyata a kullum cikin tunanin yarda zata tsare min mutumcina takeyi,sbd haka ne sukayi min wannan tabon a fuskata dan ya  taimaka wajen tsare ni daga maza masu lalata rayuwar bayi mata irina..

Jalal tunda ta fara mgn yake saurarenta har ta kai Aya bai tsayar da ita ba..

Kukan ta taci gaba dayi cike da takaicin yarda asirin da suka dade suna boyewa ya tonu..
kuma wai Sarki jalal da kansa ne ya gano su shikenan kokarin su ya zama a banza...

      Ji tayi kawai an fisgo ta..
sai saukar kanta taji a fadadden kirjin jalal me fitar da wani irin kamshi me sanyi...
   Gaba daya wutar ce ta dauke...
Meke damun yarima?
Jalal ya rasa me yasa ya kasa controlling kansa,juwairiya ta fara kiciniyar kwace kanta..

Jalal ya sake ta yana maida lumfashi, sannan ya mike tsaye ya juya ya fice daga wajen cikin saurinsa..

Juwairiya ta bi bayansa da kallo,ta kasa yarda da zuciyarta, tasan jalal yafi karfinta nesa ba kusa ba amma me yasa tajiki ajikinta kamar ya fara having feelings akan ta,ta girgiza kai da sauri...
kai inaaa tausayi kawai take basa..

    Mikewa tayi da sauri tunawa da tayi dadewar da tayi a wajen,ta tabbata zainaba zata neme ta..
Da gudu ta fito falon tana yan leke leke ga mamakin ta babu kowa a wajen,ta sauke ajiyar zuciya sannan ta fito waje tana sake rufe rabin fuskarta ta da mayafin dake kanta...

     "Juwairiya "
Taji an kira sunan ta a lkcn da take kokarin barin sashen ..
A dan tsorace ta juyo sai ganin umayma tayi tana mata wani irin kallo..

Murmushin dole tayi mata tace,umayma ashe kece?
Umayma tace uhm ni ce,juwairiya tace,bari na karasa toh tayi saurin barinta a wajen tayi gaba ..
Umayma ta jinjina kai,mai ya kawo juwairiya turakar sarki jalal?lallai akwai wani abu kasa...
dole ne tasa ido akan ta..

"Umayma na shiga ta samu jakadiya ta fada mata sakon surayya na son ganin jalal..
Jakadiya ta shiga ta sanar masa yace shi bazai ga kowa a yanzu ba,dan yana hutawa ne..

Jakadiya ta fito ta fadawa umayma, ba haka suka so,umayma jiki a sanyaye ta koma sashen surayya..

   Murmushin mugunta surayya tayi,ta kalli umaymah tace, babu komai zanci gaba da jiransa,tunda dai mun samu wannan yarinyar tasha maganin hana daukar cikin ai bani da wata matsala dan yanzu ni kam..

Umayma ta murmusa kada ki damu ranki shi dade,na samu wata baiwa mai amana sosai a can madafar kuma na fada mata sakon ki,ta amince zata rinka saka maganin acikin abinci gimbiya khadija.
surayya ta jinjina kai cike da gamsuwa tace,aikin ki yana kyau umayma...

*************
"Khadija ta kalli rabi bayan fitar zainaba tace daga dakin,yadai kin ganta kuwa?
rabi ta fito da layar data kunshe acikin zaninta ta mika mata,khadija tayi saurin amsa tana fadin, ki kiyaye bakin ki!bana son jin sirrina yana yawo acikin wannan masarautar  kin gane?
Rabi ta gyada kai,khadija tace yauwa muje na koma sashena...

********************
Bayan sati daya...

   "A cikin yan kwanakin da suka wuce gaba daya jalal bai zauna ba,
kullum suna cikin fa'da aiki yayi masa yawa sosai,duk irin nemansa da matan sa keyi bai sa ya  kula kowaccen su ba.

   A yau ma dai sun samu dan hutu ne shine ya zo dan gaida mahaifiyar sa..
Gimbiya kilishi na hakimce akan kilisarsa..
Cike da kulawa tace, jalal kaga yarda ka koma kuwa? Ina tunanin lkc yayi da zaka canza bayin dake kula dakai kamar yarda al'adar masarautar  take..

   Jalal yace,ummana kenan,aikine fa kawai yakeyi min yawa,yadan langwabar da kansa ya sake fadin,kin san kuma ban saba da irin wannan aikin ba..

Kilishi ta girgiza kai ,gobe ka shirya dan dama mahaifinka yayi min mgnr da dadewa..
nace masa mu dan baka lkc ka kara hutawa,toh tunda dai na lura kai kullum acikin aikin kake sai nayi tunanin dole ne kawai na fitar da rana da kaina.

Jalal ya gyara zaman sa yana fadin,toh umma zan shirya idan har hakan kike so,kilishi tayi murmushi yauwa dan albarka ..

  Hansai ce ta shigo falon tana fadin,Allah ya kara maka yawan rai yanzun nan baiwar gimbiya khadija  tazo da sako a fada maka..
   Jalal yadan tabe baki,kilishi tace kai wannan yarinya da jaraba take..

Hansai tace, tace a sanar  maka tana son ganinka idan babu damuwa..
Jalal baice komai ba ya mike yana kallon kilishi,umma bari na tafi..

Kilishi taji gaban ta ya fadi,cike da bakin ciki tace,ban gane bari ka tafi ba duka duka yaushe kazo?
Kodan kaji kiran matar ka ne?

Jalal ya murmusa,haba umma ke kinsan danki ai..
Magaji ne na saka a kira min shi tun dazu kuma na tabbata yana jan yana jirana acikin Fa'da..
Kilishi tayi murmushi,toh yi maza kaje ai na dauka rawar jiki kakeyi wa wannan figaggiyar yarinyar.
Jalal na murmushi yayi ficewarsa..

"Khadija ta kalli rabi tace,kin tabbata sakona yakai gareshi?
Rabi tace,wlh a kan kunnena hansai ta fada masa..
Khadija taja tsaki,yanzu a kalla anyi  kusan 5hr amma shiru babu yarima..
Ta kalli rabi,jeki ki dubo min sashen surayya ko yana can..
Rabi tace toh ranki ya dade..

  "Rabi na isa sashen surayya ta shiga tambayar bayin dake waje ko mai martaba yana ciki?
Duk suka tabbatar mata da cewa baya nan kuma ya ma dade bai zo ba..
Ta dawo ta sanar wa khadija duk irin ruhoton data kwaso..
Dariyar farin ciki khadija ta saki dan a yanzu ne ahankalin ta zai samu kwanciya tunda dai ba ita kawai yarima yake sharewa ba...


_"Gaskiya readers ina jin dadin ganin comments dinku ba kadan ba.._
_@RALLYN SAMEENA_
_@MEELANCY #team_ _jalaljuwai_
_Duk naji dadin_ _comments dinku wlh Allah yabar zumunci_

*GODIYA NAKE PHERTY*


Muje zuwa...👇🏽
Team RUMFAR BAYI...

   
[9/18, 3:19 PM] Aysha Galadima:             *RUMFAR BAYI*
       (A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 18
Wattpad @afreey101

*************

    "A can cikin gida

Please Login or Register in order to submit comment