Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna mata dariya..

"Ta zauna shiru tana kare wa dakin kallo..
Wai fa nan Dakin da take shigowa gyara ne...
yau gata a cikinsa a matsayin matar me dakin..
Taja lumfashi tana shakar kamshi me sanyin dadin dake mamaye da dakin..
Ji tayi kamar ana shirin shigowa dakin..
Tayi saurin hayewa kan gadon ta gyara zamanta tana lullubawa kanta mayafi...

"Jalal kuwa dama ya matsu sosai ya dawo sashen sa dan kuwa yasan amaryar tasa na can na jiran sa..

   Cikin takun kasaitarsa ya shigo dakin..
Ya hangota can a zaune kanta a duke..
Wani irin murmushi ya saki sannan ya karasa ya zauna a kusa da ita..

juwairiya na jin ya zauna a kusa da ita taji gabanta yadan fadi..
Jalal yace..
Giwar amale ba zaki bude min fuskar taki na gani bane?ko sai na sake biya ne?
juwairiya tayi murmushi bata ce masa komai ba..
Jalal yabi hannayenta da kallo sunsha jan lalle ga zoben daya bata yayi das' a yatsanta sai kuma awarwaron azurfa data saka..

Ba karamin burge shi hannun nata yayi ba..
Ji tayi kawai ya kamo hannunta....ya murza dan karamin yatsanta sannan ya saka dayan hannun nasa ya yaye lullubin daga kanta yana karewa kyakkyawa fuskarta kallo..

    Juwairiya ta dago suka hada ido dashi..
Wani irin abune sukaji ziyarci gaba daya zuciyoyin su...
   Jalal ya lumshe lulu eyes dinsa yace..
   Ina gode wa Allah daya bani ikon mallakar ki Giwata..
Juwairiya ta sakar masa murmushi..
Ya saki hannunta ya shafa gefen fuskar ta...
juwairiya taji wani irin yaarrr a gaba daya jikinta...
jin dumin hannunsa a kan fatar fuskarta..
Jalal yace..
Kinyi shiru ko har an fara mulkin ne?
juwairiya ta girgiza kai tana murmushi..

Jalal yace toh tashi muyi nafila ranki ya dade..
Juwairiya ta kalleshi tace a sanyaye..
Ai nayi sallah ni..
Jalal yace,ai na sani,umurni ne nake baki,ki tashi kiyi alwala..
Juwairiya tadan turo baki kafin ta mike ta shige ban dakinsa..
Jalal yabi ta da kallo yana murmushin cike da farin ciki mallakar ta...
   
"Sai da sukayi nafila raka'a biyu kafin nan jalal ya shiga yi mata tambayoyi akan addini..

Yayi mamaki sosai da iliminta dan kuwa yasan irin rayuwar tayi a baya ta BAUTA...
     Gani tayi jalal ya shiga cire kayan dake jikinsa....

Tayi saurin dauke idonta daga gefen da yake zuciyarta na bugawa..
Me kuma yake shirin yi haka?

Jalal na lura da ita yayi murmushi kawai ya shige ban daki abunsa..

Lkcn da ya fito har juwairiya ta fara gyangyadi a saman dardumar da sukayi sallar..
   Ya dan girgiza kai..
Kafin ya karasa wajenta ya duka yana kare wa fuskarta kallo..
Kai yarinyar nan akwai kyawu yaji zuciyarsa na kyasa masa kyaun matar tasa...

   Idanuwansa ne suka sauka akan(dusty pink lips)dinta..yawu ya hade kut..
Ya maida kallonsa kan wuyanta,sarkar dake jikanta ya cire a hankali..ganin zatayi mata nauyi..

Ya ajiye sarkar a gefe sannan ya dawo ya zauna a gabanta yana ta kare mata kallo..
Can dai ya dan mike ya gama shirin kwanciyarsa tsab sannan ya sake dawowa inda take..

A wannan lkcn barci ne me karfi ya fizge ta..
   Yasa hannu ya dauke ta tamkar jaririya ya ajiyeta a kan gadonsa..

Ya kalli kayan dake jikinta leshi ne mai nauyin gaske..
   A hankali ya shiga zare zanin dake jikinta..yana jin bugun zuciyarsa yana linkuwa..

   Yana zare zanin dan siket dinta na ciki ya bayyana fari tas dashi....
Wani juyi tayi..cike da jin dadin barcin da takeyi..

Caraf idanun jalal suka sauka a kan santala santalan cinyoyinta....
Ya dafe kirjinsa yana jan lumfashi..
Bai taba tsanmanin haka yarinyar take ba..
Kodan yana sonta sosai ne? shiyasa surarta ke neman rikitar dashi haka?

Ya dawo kan rigar ta..
  Yadan dago da ita yana shirin cire rigar sai gani yayi kawai ta farka sun hada ido..
   Waro ido tayi tana kallonsa cike da mamaki..
Jalal yaja baya da sauri..
Juwairiya ta shiga neman jawo zaninta..
Jalal ya sake dawowa kusa da ita..
Batayi tsanmanin ba sai ji tayi kawai ya rungume ta tsam ajikinsa..
Yana sauke lumfashi ya shiga mata rada a kunne...
Jatai yace...

       Na dade ina mafarkin wannan ranar tare dake..
Kada kiyi min gardama dan Allah..
Ki taimaka min Giwar amale..
Ki mallaka wa amalen ki kanki a wannan daren...

Juwairiya ta rasa me zata ce dashi dan gaba daya ma kunya ce ta rufe ta..
Ta sunne kanta a kirjinsa..
Jalal ya murmusa kafin ya saka hannu ya dago da fuskarta..
Yana kallon cikin idanunta..
Sai ji tayi ya hade bakinsa da nata...
Sumbatar ta kawai yakeyi cikin salonsa...
Ni kuwa afrah nace...
Su AMALE manya...asha amarci lafiya ni nayi gaba💃

***************

"Lkcn da safiya zatayi gaba daya juwairiya ta gama galabaita..
Dan ko motsi bata iya yi..

Jalal kuwa duk ya rikice ganin halin da take ciki..
Ya rasa me zayyi dan taimake ta..
Fita yayi waje ya samu wata kuyanga dan jakadiya bata ma zo ba lkcn..
Yace taje tayi masa kiran jakadiya a cikin RUMFAR BAYI...

Lkcn da jakadiya ta iso sashen ba karamin murna tayi ba..
  Ta kalli jalal tace...
ka kwantar da hankalinka ranka shi dade,GIWAR ka zata samu lafiya da izinin Allah..
  Jakadiya ta fita ta sake dawowa tare da laure..
Sannan ta dauke zanin gadon da suka cire akan shinfidar sarki jalal tayi waje da gudun ta...cike da tsananin murna..

"Lkcn da jakadiya zata shiga sashen gimbiya kilishi..
Umayma ta hango ta tana ta buga sauri kamar zata tashi sama..
Da sauri itama tabi bayanta jiki na rawa...dan kwaso ruhoto..

Jakadiya kam na shiga sashen falon kilishi ta bayyana mata wannan zanin gadon...
Kilishi tayi murna sosai tana jinjinar da kai cike da gamsuwa ..sannan ta bawa jakadiya tukwici mai yawa..

   Umayma ce ta jawo wata baiwa data fito daga cikin falon kilishi..
Ta tambayeta ko me jakadiya tazo yi wajen gimbiya kilishi..ta ganta tana ta sauri...ko lafiya?
Baiwar na murmushin murna ta sanarwa umayma komai..

Gaban umayma ne ya fadi..
Ta dafe kirjinta da sauri..
Yanzu juwairiyar da suke kwana su tashi acikin RUMFAR BAYI a tare itace ta ha'da shinfida da sarki JALAL..?

  Kishi da bakin ciki ne sosai ya kamata,ta karasa sashen surayya da saurin ta..
ta fada abunda ya faru..
Surayya dake zaune kamar an dasa ta gun taji wani irin haushi da kishi sun tsaya mata a wuya..
Taja tsaki...kawai batace komai ba...

***********

Hansai da laure ne suka kula da juwairiya har dai jikinta yayi dan sauki..ta warware sosai..

Gimbiya kilishi ce ta aiko du'bu da kanta dan a kawo wa juwairiya farfesun naman shanu dayaji kayan yaji sai kamshi yakeyi..

juwairiya batayi mamaki ba dan tasan gimbiya kilishi indai ka cika (expectations)dinta toh zatayi dakai sosai..
Fulani diyya ma ba'a barta a baya ba,dan wasu takalma masu shegen kyau na asalin fata ta aiko mata dasu..

Khadija kuwa zainaba ce taje har sashenta ta kuma bata lbrn juwairiya kamar yarda taji itama..
Al'ajabi ne ya cika ta..
Wai juwairiyar me konannar fuskar nan data raina yau ita ce a matsayin kishiyar ta kuma wai diyar sarki ce ita?..lallai duk wanda ya dauki duniya da zafi zai kuwa ringa shan mamaki a rayuwarsa..

Taja lumfashi dan tasan juwairiya tayi mata nisa sosai a yanzu..ita da take diyar WAZIRI?..tab.

  Zainaba ce ta shiga yi mata dan fada akan ta zauna lafiya da juwairiya kada ta biyewa surayya dan kuwa jalal na iya tsanar ta idan ya gano suna ware juwairiya kai...

  Khadija ta jinjina mgnr zainaba sosai dan tasan tabbas jalal yana mugun son juwairiya..
Mikewa tayi ta shirya tace wa zainaba ta taso suje sashen juwairiya din..
Zainaba tayi murmushin murna sannan ta mike suka tafi..

Koda sukaje juwairiya ce da hanne a sashen suna yar firar su ,juwairiya na bawa hanne lbrn Rumfarbayi. .
  "Tayi mamakin ganin khadija sosai amma ta share..

Khadija kuwa kamar ta sume dan kuwa juwairiya ba karamin rikita ta tayi ba..
  Sama sama sukayi fira..
Zainaba ce ma karfin firar tasu..

Hanne ce ta shigo ta sanar ma juwairiya, wai su magaji da turaki sunzo gaishe ta..
Dukkansu suka fito zuwa falon..

zainaba ta kalli magaji tace..
Yaya magaji ina wuni?ya turaki ina wuni?
Magaji yadan bita da kallo..sannan yace lfy kanwarmu ashe kuna nan kuma?
Zainaba tace muna nan kuwa..
Turaki ya gaida juwairiya cike da zolaya..
Ta amsa a sake tana dariya..
Khadija ma ta gaishe su..
Nan suka shiga fira ana ta dariya..
Sai ga samira itama ta shigo...
Ta kallesu tace..
Wato duk kuna nan ashe?
Turaki yace,ke ba barci kike ba,uwar son barci se kace wata ka'sa kullum kina kan gado.

Samira zatayi mgn kenan se ga jakadiya ta shigo tana sanar da su zuwan jalal..sashen
Gaba daya suka shiga kallon kallon ..
Jalal na shigowa ciki yayi karo dasu su duka..ya shiga binsu da kallon mamaki..

Magaji ne yayi saurin mikewa..yace..

Tunda dai Amalen ya shigo da kansa mu ai sai mu yashi mu tafi hakan nan ko?
Jalal yace,wai tsaya me ya kawo nan din ma ne?naga an cika falo?
Ko Baku san bata jin dadi bane zaku zo ku saka ta a gaba da surutu..
Khadija tabi shi da kallo tana jin wani iri...
Zainaba tace,afuwa yaya..
Turaki ya kamo hannu samira ya jata sukayi gaba..
Khadija ma mikewa tayi,ganin jalal bai ma lura da ita a wajen ba,sai tayi murmushin yake tace,ya jalal dama gaisawa muka zo muyi da ita..
Jalal ya kalleta,duk ta rame,ko cikin ne?
Murmushi ya sakar mata yace..
Ai ita ya kamata taje ta gaishe ki tunda ke yayarta ce yanzu..
Khadija tace babu damuwa ai itace bakuwa..
Jalal ya jinjinar dakai..
Khadija ta rungume juwairiya sannan tayi gaba...
Magaji ma kallon zainaba yayi yana mata alama da su tafi...
Ta gyada masa kai suma sukayi waje suna dariya..
Jalal yaja tsaki yana maida duban sa kan juwairiya dake zaune shiru tana saurarensu..




TEAM RUMFAR BAYI
*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 41
Wattpad @afreey101


**********************

"Sannu da shigowa Amale...
Ta fada tana dan rusunawa kasa kanta a sunkuye tana jin kunyarsa na mamaye zuciyarta..
Duk lkcn da zata zauna ita daya sai daren jiya ya fado mata a rai..
Ta gama tabbatar wa kanta cewa jalal na yi mata wani irin so sbd irin kalaman da yayi ta fada mata jiya..

"Jalal dake tsaye tsaye yana ta ka're ma ta kallo ya zauna a kusa da ita sosai yana fadin..

Da gani dai har kin warware daga gajiyar jiya tunda har kika zauna fira dasu magaji ko?ya karashe mgnr a shagwabe cike da kishi..

juwairiya tayi masa murmushi tace..
naji sauki kam ko kallon shi ta kasa yi..
Jalal na lura da ita dan haka ya jawo ta zuwa jikinsa...yana fadin..

ALLAH yayi miki albarka giwar amale.....dan jiya ba karamin faranta kikayi ba..
Ki fada min duk me kike so nayi miki shi..
ko wacce irin kyauta kike so nayi miki alkawarin zan baki ita a yau din nan..
dan kin cancanci kyauta mai girma daga gareni masoyiyata..

   Juwairiya ta dan dago suna kallon junansu cike da so..
Tace..
Nagode da kulawarka amalena..
Amma nikam bani da wani abu da nake bukata daga gare ka a yanzu..
Soyayyarka kawai ma ta ishe ni..nayi rayuwa me cike da farin ciki..
Jalal har cikin zuciyarsa yaji dadin kalamanta...

Ya shafa gefen fuskarta..yace
KE TA DABAN CE juwairiya shiyasa kike kasheni da soyayyar ki..
Juwairiya ta murmusa cike da farin ciki tace..

Sai dai Amale ina so na baka wata shawara idan ba zaka damu ba..
Jalal ya gyara zamansa yace..
Ina jinki tawan..
juwairiya ta kalleshi cikin ido kafin tace..
Ina so ne ka daina share matan ka sbd ni..!sbd na fara jin wasu maganganu suna fitowa daga zuwana..

Kasan dai yin hakan da kake ba karamin jawo min tsana zayyi ba a wajensu..
Ni kuwa nafi son muyi zaman mutumci dasu..

Jalal ya jinjina kai ,tabbas ta fadi gsky amma shi har cikin zuciyarsa yafi son ta dasu,kodan su ba auren soyayya yayi dasu ba?..

Ya jawo hannunta ya shi rike gam..kafin yace..
InshaAllahu zanyi kokari nayi adalci a gareku duka kinji?..
Ta sakar masa murmushi tace..
nagode sosai Amale ALLAH yaja zamanin ka..

*******************
Bayan kwana biyu..

"A cikin kwanakin nan biyu kacal da juwairiya tayi da jalal ba karamin soyayya da shakuwa ba ce ta shiga tsakanin su..
Yana nuna mata soyayya me tsabta,sannan komai take so yana yi mata shi,baya barin ta cikin tunani ko kadan..
Gashi tana samun kulawar su hansai,kullum sashen ta cikin zaman fira sukeyi,samira da nafisa ma suna shigo mata..
Taje har sashen gimbiya kilishi da fulani diyya ta kai musu gaisuwa,ba karamin murna sukayi dan laure da hansai sai da suka fada duk yarda zatayi ta siye(ex)iyayen gidan nasu..

"""""""Yau sati su daya kenan da aure
A yau ne kuma juwairiya ta gama kwanakin ta na amarci da aka basu ita da jalal..
"sai kuma girkin al'ada da gimbiya kilishi ta sanar mata zatayiwa jalal..
Dan haka suka hau shirye shiryen su..

Hansai da laure ne suka zabar mata duk kalar abincin alfarmar da zatayi wa jalal..
Hanne ce ta shige gaba wajen taimaka mata tare dasu zainaba da samira dan suma cewa sukayi baza'a bar su a baya ba suna tare da ita..

Ko da umayma ta samu wannan lbrn a cikin RUMFAR BAYI ba karamin bakin ciki bane ya lullube ta ba,wai wannan juwairiyar dai da sukayi wa wulakanci suka tozarta suka kore ta daga masarautar nan yanzu itace matar SARKI giwar amale? Ta cije yatsa da saurin ta tayi sashen gimbiya surayya...

Tana shiga ta sanar wa surayya lbrn abincin da juwairiya ke yiwa jalal.
Ta kara fadin..
Yanzu shi kenan ita kadai ce zata samu ya'bawar sarki kenan?

Ba karamin kishi bane ya turnike suryya sai dai babu abunda zata iya yi,ita yanzu ta kanta takeyi,ta samu ciki ta haihu da sarkina..
Ta kalli umaymah cike da rashin mafita tace..
Yanzu wacce hanya ce zamu bi dan mu tarwatsa wannan abincin da take yiwa jalal..
Sai kuma taja tsaki,kai ni duk wannan ma bashi ne gaba na ba,dan maganin malam dai shiru kakeji..

Umayma tayi murmushin mugunta tace..
Ki bar min komai a hannuna ranki ya dade..ni nasan abunda zanyi..

*************
"Sun kammala dukkan abincin da zasuyi ko ina a madafar ya dauki kamshi..
Zainaba ce ta matsa wa juwairiya akan taje tayi wanka ta shirya su zasuje su shirya abincin a sashen jalal..

"Sunje sun shirya komai a sashen na jalal ko ina ya dauki kamshi..
Zainaba ta kalli samira..
Munyi kokari,sukayi murmushin murna kafin dukkannin suka fice da zuwa sashen su...
juwairiya na can sashenta tana shiri hanne na tayata..

  a lkcn ne Umayma ta lallaba cikin sashen na jalal akan surayya ce ta aiko ta..
   Tana shiga falon tayi wajen abincin da sauri ta dauko wani kulli daga cikin zaninta ta bude kwanon miyar tana kokarin barbada maganin a ciki..
  
"Jakadiya da jalal ne suka shigo sashen...
daga can fa'da suke aiken gimbiya kilishi yaje masa akan ya koma sashensa yaci abincin amaryarsa..
Murna sosai yakeyi zai ci girkin Giwarsa..
Sai sauri yake bazawa,magaji ya kalleshi yace,gsky kayi gaba Amale ni kam bazan iya wannan saurin naka ba..
Jalal ya harare shi,toh a gaida su inna dai..
Magaji yayi gaba yana fadin,zasuji..
Jakadiya tayi murmushi tana jin dadin yarda jalal ke son juwairiyar su..

"Caraf suna shiga sashen sai kuwa sukaci karo da mutumiyar ta ku wato umayma tana ta barbada garin maganin ta a cikin lwanon miya..

  Kallon juna sukayi cike da Al'ajabi. .
Jakadiya ce ta da'ka mata tsawa..
A daburce ta juyo cike da tsananin fargaba...
Jikinta na rawa ta zube a kasa..

Jakadiya tace..
Me kike zubawa a cikin Abincin SARKI...!
Umayma ta shiga girgirza kai..
Wlh tallahi babu abunda na zuba a ciki jakadiya ,kawai dai naje ne na gyara zaman kwanokan..

Jalal ya cike da mamakin waye yake son kashe shi a cikin masarautar sa?ya rasa abun fadi..
    Jakadiya tace karyawata zakiyi?bacin da idanun mu muka ganni ki..kina barbada magani acikin abincin Amale..
Toh Yau taki ta kare!dan kuwa dole ne ki fuskanci hukunci mai tsauri!

Jalal ya dagawa jakadiya hannu sannan ya karasa wajen umaymah yace..
Kince baki zuba komai ba a ciki ko?
Tace wlh mai martaba ni babu abinda na zuba a ciki..

"Juwairiya da hanne ne suka shigo sashen sai tarar da su sukayi a tsatstsaye..
Jakadiya ta matso kusa da juwairiya ta fada mata duk abunda yake faruwa.
A tsorace juwairiya ke kallon umayma..
Ita dama tuni wannan yarinyar batayi mata ba..
Toh menene hujjar ta na saka magani acikin abincin jalal?
Kodai surayya ta aiko ta ne?
Juwairiya ta girgiza kai babu kyau zargi..
Toh me yasa umayma zata zuba wani abu a cikin abincinta?

Jalal ne ya kalli jakadiya yace,kije ki kira min dukka (family)din gidan nan,ni SARKI JALALLUDEEN ina son ganin kowa a nan Yanzu!!!!!

Jakadiya ta fice da sauri...
Juwairiya dake tsaye mamaki yasa ko koda motsi ta kasa yi..
Jalal ya karasa wajen ta ya kamo hannunta..

Hanne ta karasa wajen umaymah ta rike ta gam wai dan kada ta gudu..

    Jalal yaja juwairiya zuwa dakinsa..
Ya kalleta yace..
Ki kwantar da hankalinki zamu gano gsky yanzu inshaAllah..
Juwairiya ta gyada masa kai a sanyaye...kafin tace..

Amale na tambaye ka?
Jalal ya gyada mata kai yana jawota jikinsa..
Me ya hana ka cin abincin surayya a wancan lkcn?
Jalal yadan yi jim irin tunanin nan kafin yace..
Kasa ci nayi kawai sbd tsamin da yayi dayawa..
Juwairiya tadan murmusa tace..
Ai a lkcn dani akayi wannan girkin kuma tabbas na kama wata baiwa tana zuba wani abu a cikin abincin sai dai dana tunkare ta sai ta karyata kamar umayma take karyawata a yanzu...

Jalal yaja lumfashi yace...
Ni na rasa meke damun ku mata wlh..
Yanzu sbd son zuciyarku kun kwanmace ku cutar da mijinku dan kawai kada ya yabi kishiyar ku..?
Dan a take ya tuna abunda ya faru a lkcn khadija,yaci abincinta babu taste amma da magaji yaci cewa yayi masa lafiya kalau abincin yake..

  Juwairiya ta jinjinar da kai..
Jalal ya girgiza kai shima cikin wani irin yanayi..
juwairiya ta yakaci hancin sa..
Ya kalleta..
Ta sakar masa murmushi..tana shagwabe masa fuska..
Ya sumbaci lebenta..
Lkcn ne jakadiya ta shigo ta sanar dasu kowa ya hallara..su kadai ake jira..
juwairiya ta rike hannun jalal,jalal ya lumshe mata ido yace..
Kada ki damu nasan abunda zanyi..

************
Suna fitowa suka tarar da gaba daya an hallara..a cikin a falon..
Tunda ga kan gimbiya kilishi, fulani, hamza,nafisa,samira,zainaba, turaki,hamza,khadija..

Idanuwa akan juwairiya dake bayan jalal har suka samu waje suma suka zauna..
Gimbiya kilishi ta kalli jalal tace..
Amale ya mukaji kira haka daga sama ne?

Fulani tace da fatan dai lafiya dai ko?
Jalal ya kalli surayya da gaba daya jikinta yayi sanyi ganin umayma a wajen kuma da alamu bata da gsky dan kuwa jikinta gaba daya rawa yakeyi...

   jalal yace..
"Kada ku damu dama so nakeyi ne ku taya ni ganin wani abu..
Jakadiya!
Ya kira sunanta..
sannan ya umurce data zuba abincin a cikin plate ta mikawa umayma taci..
   Umayma faduwar gabanta ta tsananta sosai..
Jakadiya tayi yarda sarki yace sannan ta ajiye plate din a gaban umayma tace..
Maza ki ci!

Su dai sauran mutanen wajen kallonsu kawai sukeyi...
dan sun kasa fahimtar abunda ke faruwa a wajen..
Zainaba ce tace..
Haba yaya ya zamu gama wahalar hada maka abincin nan sai ka bawa wata baiwa can taci!

   Hamza yace,shine ai na gani nima kuma duk an tara mu a nan sbd mu ga cin abincinta..
Kilishi ta daka musu tsawa..
Sukayi shiru a tsorace ...

   Umayma ta kurawa abincin dake gabanta ido tana dana sanin zuwa sashen jalal yau din nan da tayi...

Gashi magani ne ta amso daga wajen wani bokanta dan itama Sarki jalal ya kaunaceta ta zama matarsa kamar yarda juwairiya ta zama..
Ta mallake sa ta raba shi da matansa ta zama(apple of his eyes😅)

Tsoro ne ya shige ta sosai dan kuwa boka sai da ya tabbatar mata da cewa idan wani yaci wannan maganin ba sarki jalal ba,toh kuwa tabbas sai ya haukace...!!

Jalal ya kalli hanne..yace
Zauna ki tura mata wannan abincin dan naga bata san menene umarnin sarki ba yanzu..

  Hanne kuwa ta sa hannu ta debo abincin nan me uban yawa..
Jakadiya ta saka wasu kuyangi suka kama umayma suka rirrike ta aka shiga tura mata abincin nan tana hadiye shi da kyal kyal...

     Sai gani sukayi kawai ta fara dariya kamar zararriya..
Ta kalli jalal tace..
Sarkina....bazaka so ni ba nima?
Duk falon hankalinsu ya tashi ciki kuwa harda surayya data gama tsorewa..

   Umayma ta sake yin dariya..tace
Nima fa ina sonka?
Inaso na zama matarka kamar yarda juwairiya tayi kokarin zama itama..
Shiyasa ma naje can wajen boka na amso maganin da zai saka ka ka so ni..
Ka aureni..na zama gimbiyar ka...
Abun sonka!
Na haifa maka ya'ya
Kamar uwar dakina surayya take ta kokarin zuwa wajen malam dan ta samu haihuwa...!

Dum dum dum..
Surayya hankalinta ya mugun tashi..
Yau ta gama yawo..
Kowa yaji tana zuwa wajen malam..

Khadija da juwairiya duk suka mike tsaye cike da al'ajabi..

Fulani ta mike itama tana kallon jakadiya tace,fita ki kirawo fadawa  a dauke mana wannan mahaukaciyar daga nan..

Jalal kansa se dayaji abun kamar wani almara...
Wai baiwarsa ce ta amso magani dan ya sota..
Sannan uwar gidansa har wajen malamai take zuwa..

Kilishi rai a bace take kallon surayya kafin ta wanka mata mari..masu kyau .
Take ta zube kasa tana kuka me ciwo..
Gaba daya falon kallonta sukeyi..

  Surayya na dafe da kuncinta tana hawayen bakin ciki..
ko a mafarki bazata taba tunanin wai baiwarta ta hannun damar ta zata ci amanar ta haka ba......kai mutum ba abun yarda bane ba...kwata kwata

Kilishi tace,wannan ba baiwarki bace?
Tana a karkashin ikon ki shine zaki bari har ta ringa mafarkin kasancewa da Sarki?
Surayya na kuka tace..
Wlh umma bani da saniya da wannan danyen aikin da tayi,ni kaina ban san tana da niyyar mallake min miji ba.

Kilishi tace,ai duk dake din kuke zuwa wajen bokayen..
Surayya tace..
Umma ni wlh nayi nadamar zuwana wajen wannan malamin,kuma wlh ita ke kaini,ku yafeni dan Allah
ta zube kasa tana kukan bakin ciki da nadama...

Dama haka umayma take?shiyasa take ta zuga ta akan hallaka juwairiya da khadija?ma kenan?
Wayyo Ashe itama nan gaba ita zata hallakar ta mallake musu jalal..

Jalal ne ya zo gaban kilishi yace..
Umma ki kwantar da hankalinki,tunda da dai asirin ta ya tuno yanzu,hukunci ne kawai zamuyi mata..

Turaki yace wannan hakane..dan ya zama ishara a wajen Bayi gaba daya..
Wannan ai (abomination )ne....
Kuma raini sosai ne a wajen SARKI..

****************

An kai umayma can rumfar hukunta bayi,an rufe ta acikin kurkuku (dakin duhu)ga hauka tana fama dashi sai surutai takeyi barka tai...
Sarkin dorina ya zane ta tasa tayi lakwas aka jefata cikin dakin aka kulle (oooh ke kuma haka karshen ki yake?)

Wannan al'amarin ba karamin ladabtar da surayya yayi ba..
Kullum tana sashenta zaune shiru tana mamakin irin munafuncin umayma..

Yau dai jalal da kansa ya saka a kira masa ita..
  Tana shigowa dakin nasa yabi ta da kallo duk ta rame tayi baki..
Zama tayi akan kujera tace..
Gani mai marbata ance min kana nemana..
Jalal ya mike ya dawo kusa da ita ya zauna..

Surayya ta dago ta kallesa..
Jalal yace..
Meyasa zaki ringa saka kanki a cikin damuwa ne haka?
Duk fa abunda ya faru ya gama faruwa...se dai Allah ya tsare gaba..

Surayya taji kwalla ta taro mata acikin idonta..
Tace...
Jalal bazaka gane bane..
ka yarda da mutum amma ashe munafukin ka ne(backstabber)...
Duk irin muguntar da take saka ni inayi ashe tana da wata manufar ta ta a akai..
  Jalal ya sauke ajiyar zuciya..
Yanzu dai ai kinyi hankali..ko
Se ki nemi gafarar wadan da kika zuluntar..
Tayi saurin kallonsa..
Yace kwarai kuwa..
Surayya tace..ta zube kasa..
Ka yafe ni sarkina...
Nasan nayi maka laifuka masu yawa..
Sannan...
Ka tayani neman gafarar juwairiya dan Allah..

Jalal yaji dadi har cikin ransa..
Yace..
Zan tayani rukon ta amma inaso kema keje da kanki ki nemi gafarar ta kinji..
Surayya ta gyada kai..zanje..
Jalal ya dagota ya jawo ta jikinsa ya rungume ..
Ta saki lumfashi me nauyi tana jin dadin kasancewa a jikin Sarkin nata..




Love you all
Sorry kwana biyu i hv nt been updating regularly..
Kunsan yarda abun yake sai a hankali. .

Team RUMFAR BAYI
    *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 42
Wattpad @afreey101

_"Fans please ina neman addu'ar ku,October dinnan zan fara exams dina inshaAllah,shi yasa zaku ga ina yanke lbrn dan na gama muku shi a cikin lkc na fara karatun jarabawata.._
_Thanks for all your love.._
_Ina Yin'ku sosai😘_

********************


"Surayya abun duniya ya taro ya fara yi mata yawa..
Girman kai gaba daya ya hana ta zuwa neman gafara a wajen juwairiya..

Gashi kuma yanzu jalal ya dauke mata kafa daga dukkan al'amuran ta ko sashen sa ya daina gayyatar ta..
tun ranar dayayi kiranta tayi masa alkawarin zata je ta nemi gafarar ta har yanzu bai waiwaye ta ba
Sai dai taji yaje wajen khadija da amaryarsa..

     Yau dai fada tayi wa zuciyarta sosai ganin bata da wata mafita..
ga kuma wannan ciwon cikin daya dawo mata kullum dare sai tayi fama dashi tun lkcn da tasha maganin malamin nan a kwanakin baya ta kasa ganewa jikinta gaba daya..
Ga mafarkai barkatai da takeyi,duniya dai tayi mata zafi sosai,taja lumfashi..
Gara naje na nemi gafarar ta wata kila na samu sausaucin abunda nake ji..

***************
"Abun mamaki juwairiya na zaune a sashenta dasu hansai sai ga surayya ta shigo da sabowar baiwar ta...
   Ga babban mamakin su juwairiya sai gani sukayi surayya ta dage sosai wajen neman gafarar ta..

Tayu mamaki sosai amma sai Tace.. babu komai ita ta yafe mata,Allah kansa ma muna masa laifi ya yafe mana balle kuma dan adam?..
Ita dama

Please Login or Register in order to submit comment