Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta bude gaban motarsa ta shiga.
Khalid bai kalleta ba ya dan duba agoggon wayarsa.

Kallansa tai tace "me zaka cewa yaya?"
Bai tanka ta ba sannan bashima da alamar kulata, tace "wai dan Allah kai da kake driver meye naka na shiga hurumin dabe shafeka ba?"

Yanzu kam Khalid ya kalleta, wayarsa ya dauka yai dialing  din  numberta.
Wayarta dake saman skirt dinta ne tai vibration.
Khalid ya kashe sannan ya sake kiranta, kallansa tai hankalinta a tashe, yace "kome kike shirin yi ki dakata dashi, ki koma inda kika fito."

Kallansa tai tace "bazan dakata ba wlh harsai naga rayuwar Adam ta salwanta."

Kallanta yai kamar zai kulata sai kuma ya fasa, dauke kai yai wanda hakan ya sake bata mata rai, kallansa tai tace "Zainab ce ta saka ka bincika? Me kake tunani in na tura mata wannan video din?"

Ta fada bayan ta zaro wayarta ta dana video din, bata nuna mai wayar ba sai dai ga nishi nan na an fada kogi ita da namiji, sannan ta dakko pic din da suke rungume a mota ta nuna mai tace "ko na hada mata da wannan?"

Duk yanda Khalid yaso ya danne abin baisan sanda ya wanka mata mari ba, ransa a matukar bace ya kalleta, itama kallansa tai ranta a bace, zatai magana Adam ya bude kofa cikin mamaki yace "Khalid meta maka zaka mareta?"

Kallansa Khalid yai sannan ya kalleta wacce ta fashe da koka tare da rike hannun Adam, tace "ya zamuyi yaya? Ya san niba kanwarka bace shine ya maren."

Adam ya kalleshi yace "koma menene baikai harka mareta ba, akan wani dalili?"

Kallansa kawai Khalid yake kafin yace "nasan ko a skul kwakwalwarka bataja sosai amma banyi tunanin toshewar kwakwalwarka takai haka ba."

Adam ransa ya baci balle haushin an gwaba mai magana a gaban Sadiya, yace "mene?"

Khalid yace "da nazo muyi magana ne amma yanzu na fahimci maganar batada amfani, ya tada mota tare da jawo kofar motar ya tafi.

Adam baki a sake ya bishi da kallo, yace "sai kace motar ubansa."

Sadiya ce ta kalleshi tace "Ya Adam garin ya ka dakko shi a matsayin driver? Ko Aunty ce ta dakko shi?"

Yace "nine wlh."
Tace "Yaya ina ganin kamar....."
Sai kuma tai shiru, kamar me?"

Kallansa tai tace "ni farkon zuwana dana gansu a mota ma na dauka mata da miji ne, yaya ina ganin kamar akwai abu tsakani.........."

Wani mugun kishi ne ya fito karara a idan Adam, yace "me kike san cewa? Kinsan Zainab kuwa? Tafi karfin tai abind kike tunani."

Ya juya ciki a kufule.
Yana shiga ta daga waya ta kira number "Bash ina san amin photoshop na wasu."
Turo hoton na gani, tace "kai zaka dauki hoton, zan saita lokacin da zan nemeka."

Yace okay.

Kashe wayar tai sannan ta shiga ciki.

Goggo na zaune suka shigo kallanta tai tace "ke zoki hada kayanki ki bar gidan nan in ba gidan tsohonki bane."

Sadiya ta kalleta tace "ba gidan tsoho na bane ba kuma mai fitar dani."
Ta shige daki.

Galala Goggo tai da baki tana kallanta, fuskarta ta girgiza da sauri anya ba mafarki take ba? Meya faru yanzu??

Nace oho 😏


*********

Ran Khalid yakai matuka sosai gun baci, meke faruwa? Wacece yayarta? Shiru yai kafin ya dau waya ya kira Salmanu.
Salmanu dan Allah dan jeka gida, akwai littafin da nake rubuta numbers ka dubomin number wani Ziyad a turon.

Salmanu yace to.

Wajen minti talatin Salmanu ya turo mai, Khalid ya kira number.

Ziyad ya dauka daga can bangaren.

"Khalid ne."

Kwaro? Ziyad yai tambayar cikin mamaki.

Khalid yace "eh, nace dan Allah da Adam yana budurwane kafin yai aure? Watace tace ta santa shine nake so naji ko karya take."

Dariya Ziyad yai yace "saboda haka ka kirani?"

Khalid yace "yahkuri."

Ziyad yace "yana da ita, Baby ni yama sunanta na gaskiya???"

Can yace ahhh Fiddausi, budurwarsa ce sosai, dan tun tana junior akeshan love, waya taba tunanin bazai aureta ba?"

Khalid yace "ohh ba itan bace."
Ziyad yace "ita wannan tana da sikila."

Khalid yace ayya, Ziyad yai dariya yace "ashe driver man ka koma?"
Wata dariya yasa yace "Adam ya fada mana, waya taba tunanin kwaro zai kare a tukin mota?"

Kashe wayar sa Khalid yai sannan yace "Sikila? Fiddausi?


***********
Ayusher ce🏌🏻‍♀
************
[11/13, 7:37 PM] Maman Zara Whatsapp: 🍀A GIDANA🍀
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

{26}


Goggo ta mike cikin mamaki ta murda kofar, sai dai tajita a kulle, bubuga kofar tai tace "Ke fito!"

Daga ciki Razy tana jinta batada alamar mikewa, Adam dake daki ne ya fito jin yanda ake buga kofa.

"Goggo lafiya?l

Kallansa tai sannan tace "so nake yarinyar nan ta maimaita metacemin."
Metace?"
Ranta a bace tace "kazo ka tattara yarinyar nan tabar gidan nan ko sai ranka ya baci?"

Kallanta yai yace "zan mata magana gobe ta tafi."

Tsaki tai cikin kuluwa sannan tace "kai dai kam wlh anyi soko, yarinya karama ka kasa sallamarta, naga uban abinda kake rikewa."

Juyawa tai ta koma ta zauna ta dau remote, shiru yai yana nazari kafin ya dau key yai hanyar waje.
Aikin kenan.
Ta fada rai a bace.

Adam na fita ya kira Ziyad, kana ina?
Ziyad yace "ina gida anjima zan tafi."

Nan yace ganinan zuwa.

Gun Ziyad yaje suka fara hira, can cikin hira Ziyad yace "oh ni kwaro ya kiran yana tambayata budurwarka ta da."

Budurwara?

"Eh ka manta? Fiddausi."

Idanu Adam yadan fito dasu dan sam ya manta da ita, sai an dade in ba da wani dalili bama baya tuna ta.

Meyace?
Nan Ziyad ya fadamai yanda sukai.

Adam cikin rashin kulawa ya cigaba da hirarsa.

***********
Washegari.

Sun taho a hanya suna tafe tana waya, daga yanda take wayar zakasan da mahaifinta ne, cikin jin dadi take wayar.

Khalid dake kallan glass din motarsa ta baya yana kara tantance mai motar dake biya dasu, wayarsa ce tadan yi kara, dauka yai a hankali yace "ka dubo?"
Salmanu yace "wanda kace na tambaya baisan gidansu ba shima."

Cikin rashin jin dadi Khalid yace "okay nagode."
Kashe wayar yai sannan ya kara kallan motar bayansu, parking yai yana shan kwana, motar daga dan baya itama tai parking.
Zainab wacce ta gama waya yanzu tace "ina zaka?"
Yace "yanzu zan dawo am sorry."
Fita yai tabishi da kallo tana leken abinda yakeyi.

Knocking din glass din motar yai, Bash daya waske dashan ruwa ya bude yana cewa "Ya akai?"

Khalid ya kalleshi yace "me kake?"

Bash yai dariya yace "ruwa nake sha."

Khalid ya kalli cikin motar sannan ya kalli wayarsa dake gefe camerar wayar a bude take, yace "dan mikon wayar ka."

Bash ya rufe ruwan yace "yanzu bawan Allah haka kawai ina tafiya kace in baka wayata? In baka kayi me?"

Khalid ya kalleshi yace "zaka bani ko sai na kira wacce ta saka?" Ya fadi hakan yana fatan bugar cikinsa.
Bash ya kalleshi yace "Ba ita ta sani ba ni na sa kaina."

Kenan sashi akai? Ita? Wacece kenan? Badai wata kuma Zainab ta sakema Laifi ba?

Daurewa yai ya kalleshi yace "bani wayarka."
Bash yace "wai a kan me zan baka wayata?" Yai maganar yana rike wayarsa.
Khalid ya zagay daya bangaren kafin Bash ya kulle ya shige.

Wayr ya amshe daga hannunsa sannan ya duba calls.
Razy yaga ansa, mamaki ne karara ya bayyana a idan Khalid cikin tsananin mamaki yai saurin duba photo ganin a camera wayar take da alama hoto aka gama dauka.

Zainab ce lokacin da take komarin bude mota, mamaki ne ya kamashi ya kalleshi da sauri yace "me kake shirin yi?"

Bash ya kalleshi yace "me kuwa? Ba abinda nake shirin yi."

Shiru Khalid yai ganin Zainab na zaune yasa ya kalleshi yace "koma me kake shirin yi karka kuskura na kamaka kana bina, inba haka ba duk abinda ya biyo baya kaika sani." Goge hoton yai sannan ya ajiye mai.


Ya bude motar yana tafiya zuwa taso motar yana tunanin meyasa bai goge hoton dake wayar Razy ba? Ko dayake inhar sharrinta ya kai haka ya tabbatar ta ajiye wani hoton a wani gun, meya faru haka? Wacece rayuwarta ta salwanta akan Adam?

Bude motar yai gaba daya yana tunani, Zainab wacce gaba daya tunda ya fita hankalinta ya tashi ne ta kalleshi tace "wanene? Turoshi akai?"

Kallanta yai kadan me kikeyi gidanki ya zama haka?
Ganin baice komai ba yasa tace "Magana nake."

Kallanta ya sakeyi yace "Will you please keep your eyes open?"

Mene?
Ta tambaya cikin bacin rai, makauniya ce ni ko me?

Kallanta yai kamar zai sake magana sai yaga in har baisan komai ba yai magana kamar yana neman raba aure ne.

Ranta a bace tace "uban waye a motar da har zaka fadamin magana?"

Khalid yace "am sorry."
Ya tada motar, bayan yaga waccen motar tabar gun.

Ran Zainab yakai kololuwa gun baci dan bakin ciki ya isheta da har ta kasa magana, wannan dan rainin hankali ita zaicewa makauniya ko me?

Da bakin ciki suka isa gida, yana parking ta fito a zuciye ta wuce ciki, ya sani sarai taji haushin abinda yace "amma garin ya suka bar yarinya karama take juyasu haka?"

Waya ya dauka ya kira number Adam.

Adam ne ya dauka yace "ya akai?"
Yanda yai maganar ne yasa Khalid yace "ka fito." Ya kashe wayar.

Adam ya kalle wayar yace "ka fito?" Sai kace wani danka? Har zai ci gaba da kallan ball dinsa sai kuma ya mike dan yana san jin meya kawo zancen Fiddausi.

Zainab ce ke gaida Goggo da gida fuskarta a hade, kallan Adam tai batace komai ba ta wuce ciki.

Gaban Adam ne ya fadi, meya faru? Honey? Sannu da dawowa.
Yauwa Honey kawai tace ta shiga daki.

Goggo ta tabe baki tace "oh ni!"

Kallan Goggo yai tace "ka gama boyewar? Kasan Allah kazo ka kuri magen nan? Dan gulma yau ko ganinta banyi ba daga kai har ita.

Adam yace "ina zuwa."

Fita yai tace "au kaima ka iya rainin wayan?"

Adam ya fita Khalid na tsaye a waje.

Kusa dashi ya karasa fuskarsa a hade, Khalid ko damuwa dashi baiyi ba ya kalleshi yace "Adam bakada hankali ne?"

"Banda hankali?" Adam ya tambaya ransa a matukar bace.

Khalid ya kare tamke fuska yace "wannan yarinyar daka dauko ka tabbatar ka sallameta yanzun nan in ba so kake ta tarwatsa maka rayuwarka ba gaba daya."

Adam a kufule ya kalli Khalid jinyake kamar ya makeshi, mene? Kai wanene da zakace inyi abu inyi? In taimakeka in baka aiki ka nemi maidani karamin mutun?

Ran Khalid ne ya baci cikin kufula yace "wato kai bakada hankali ko? Banda hauka uban waye zainkawo yarinya gida yacewa matarsa wai kanwarsa ce? Banda hauka da rashin tunani? In kanwarka tazo fa? Taya ma daga ganin yarinya zaka kawota gidanka?"

Adam ne ya dunkule hannunsa cikin kumbura fuska yake kallansa.

Khalid yace "Fiddausi, a ina gidansu yake?"

Fiddausi? Adam ya tambaya.

Khalid yace "ita kadaice ko tanada kanwa?"

Adam ya hade fuska yadan harareshi yace "meya kawo wannan zancen?"

Khalid cikin takaici yace "ban san Fiddausin ba balle nasan kamanninta amma ka tabbatar bata kama da waccen yarinyar?"

Hankalin Adam ne ya tashi ya kalli Khalid da sauri yace "me?"

Khalid yace "bansan wacece ba bakuma ni da masaniya akan meya kawota amma ka bala'in shiga hankalinka, har hotonka rungume ta tana dashi."

Idanun Adam ne suka fifito bakinsa na rawa yace "mene?"

Khalid yamai wani kallo yace "banda rashin tunani taya zaka nemi yin alfasha a gidan auranka? Dan hauka kuma da yarinyar da baka sani ba?"

Adam cikin tsoro yace "banyi zina da ita ba, tace ba zina bane."

Wani kallan takaici Khalid yamai yace "da alama kana bukatar komawa islamiya."

Harya dau jakarsa zai fita yace "a wace unguwa take? Fiddausin nake nufi."
Sunan babanta fa?

Adam baki na rawa yace "Basiru."


Adam hankalinsa a tashe yace "Naibawa suke yar lemo." Yanda yai maganar kadai zaka san hankalinsa baya jikinsa.

Fita Khalid yai ya bar gidan, direct Naibawa ya wuce yar lemo.

Gaba daya hankalin Adam ya gama tashi dan da kyar ya iya takawa zuwa ciki, dakin Sadiya ya bude.

Goggo ta mike da sauri tace "ina zaka?"

Shiga yai ya rufe kofar.

Hankalin Goggo a tashe ta sa bakinta jikin kofar tace "Adam ka fito ko sai kaci gidanku anan gun."

Sadiya dake waya da babbar wayarta shigowar Adam ne yasa ta dan zaro ido.

Kallanta yai yace "Me Khalid yake cemin?"

Mikewa tai tace "me yacema Yaya?"

Ta matso tana neman kamo hannunsa, hannunsa ya matsar sannan yace "hoton me kika dauka?"

Ganin tasan kwanan zancen yasa ta ja baya ta zauna akan gado.

Dama tana jin haushin Bash yace mata bazaiyi abinda ta sashi ba yanzu kuma nan ya bulo? Lalai Kwaro yake ko khalid? To ko kyankyaso ne sai ta saita mai kansa.

Adam ta kalla wanda yace "waccen wayar fa?"

Murmushi tai tace "ahhh am so tired! Na gaji da sa mask din da bai dace da ni ba."

Mask! Ya tambaya yana kallanta.

Fuskarta ta hade tace "me? Yanzu kana so ka koreni ne bayan kaji abinda yace?"

Kallanta Adam yai yanda take magana ne sam kamar ba Sadiyan daya sani ba.

Kallansa tai sannan ta dakko wayarta ta nunamai pic din da video din tace "inka isa kace na bar gidan nan, wlh kana fada ina turawa matarka, tasan wanene kai."

Gaba daya hankalin Adam ne ya tashi.

Mikewa tai ta zo kusa dashi ta sumbace shi, hannu tasa tana yawo dashi kan kirjinsa tace "in maye yaci ya manta uwar da bazata taba mantawa ba."

Gaba daya zufa ce ke zubowa Adam, yace "me kike nemana dashi."

Hannu tasa ta shafi fuskarsa tace "kana iya baccin yanzu? Na tabbatar sha'awa bata barinka kayi sosai."

Adam zufa ke zubo mai gaba daya kansa ya dau wani irin zafi......


Ayusher🏌🏻‍♀
[11/15, 9:44 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀
     ......................

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

{27}


Adam ya kalleta cikin tsoro yace "Sadiya."

"Tsi tsi tsi ni kanka ne baya aiki ko haka Allah ya halliceka? Har a wannan yanayin Sadiya zakace?"

Adam ya matso kusa da ita da sauri ya zube a kasa yace "na sani bake bace dan akwai abubuwa da dama da kike aikatawa ba a hayyacinki ba, taya daga taimako na taimakeki zaki......."

"Taimako?" Wata dariya ta sheke dashi sannan ta sa hannu a wuyansa sumbatar sa tai a bakinsa sannan tace " kule?"

Kallanta yai yaga hoton da aka dauka ta kalleshi tace "in tura mata?"

Da sauri ya mike zai warci wayar, mikamai tai tace "ba sai ka fadi ba."

Adam gaba daya sai ya kasa komai, Goggo dake wajen kofa ne taji kamar kanta baya aiki saboda abinda kunnenta ke juyo mata, baya tai tara dayin kara wayyoooo Allah.

Da sauri Adam ya bude kofa Zainab dake kan Sallaya ta idar da sallah kenan ita ma ta fito.

Zainab ta kalleshi ganin ya fito daga dakin Sadiya, sai dai bata kawo komai ba ta wuce gun Goggo tace "Goggo lafiya? Faduwa kikai?"

Kallan Zainab tai sannan ta kalli Adam tace "wayyo Allah na faduwa nai!"

Sannu, Sadiya ce ta fito ta tsaya a bakin kofa tana kallanta, Adam wanda gaba daya tsoro ya kamashi ya kalli Zainab yace " bari na kaita ciki."

Ta kalli Goggo tace "ba sai munje asibiti ba dai ko?"

Goggo ta zubawa Sadiya ido, kallan Sadiya, Zainab din tai, suna hada ido da Zainab ta fara matsar kwallar tace "sannu Goggona, tsoron matsuwa ma nake."

Adam ne ya taimaketa ta mike sukai daki, sai da taga sun shiga daki sannan ta shiga kitchen ta duba flask, ganin taliya yasa ta zuba a plate ta wuce daki.

Suna shiga daki Goggo ta kwace hannunta sannan ta dada mai wani dundu wanda sai dayai kasa.
Zubewa tai a kasa itama tana kara dukansa tana cewa "wannan wannan ka gama dani ka gama cutata, duk uban kudin dakaci kana makaranta gun sake jarabawa da wahalar da ka samu ban taba jin haushi ba saboda ina ganin ai kayi dacen mata wanda zan fanshe wahalata, yanzu dan hauka ka yadda wannan kuliyar ta kamaka a tafin hannunta."

"Wayyo na shiga uku wannan yaron shi zainkarasani lahira."

Adamu yai shiru yana zube a kasa, idanunsa yana neman kawo ruwa.

Goggo tace tashi ka kirata tazo ta bar gidan nan yanzu kafin rayuwarmu ta kare dan wallahi bazan koma kauye ba kafi kowa sannin matar nan taka in taji ko minti daya bazamu sake a gidan nan ba.

Adam ya mike jiki a sanyeye duk zafin dukan nan bakai zafin abinda ke ransa ba, dan har ga Allah yana san Sadiya a kasan ransa, yana san ya kasance da ita, yaushe yasan yaudararsa take?

Kallanta yai tana zaune akan kujera abinda kullum a kasa take zama yace "kizo inji Goggo."

Wani banzan kallo tamai tace "kace tazo in jini."

Baki ya bude yace "mene?"

Kallansa tai sannan ta nunamai tv, tace "ba a gaban tv take wuni ba? Kace tazo ina kiranta."

Tsayawa yai ya kasa ko motsi.

Zainab ce ta fito deban ruwa, kallansa tai a tsaye sololo.
Matsuwa tai tace "Honey!"

Kallanta yai yace "Hmm."

Ya akai? Jikin Goggon ne?"

Hannunta ya kama da sauri yace "ba shi bane muje."

Dariya tai tace "ruwa zan deba."

Shiga daki zan kawo miki ba'asan ana cin abinci ana tashi."
Murmushi tai cikin jin dadi, Sadiya ce ta kalleta tace "Aunty Yaya na kula dake sosai, irin su Yaya basa cin amanar matansu."

Zainab ta kalli Adam sannan tace "Shiyasa nake ji dashi ai."

Nan ta shiga daki, juyowa yai ya kalleta.

Kallansa tai tace "wuce ka kiramin Goggo ko kuma Allah yanzu na tura."

Juyawa yai sololo ya nufi dakin Goggo ya sanar da ita aiken Sadiya.

Baki ta bude tace "inzo?" Cikin bacin rai ta mike ta nufi falo zatai masifa.

A gaban tv ta ganta tana juna wayarta a jiki.

Cikin zuciya Goggo tace "ke dan ubanki bakiji ina kiranki ba? Yr banza karuwa, wuce ki hada kayanki kafin naci ubanki a gidan nan."

Bata kula Goggo ba sai data gama hadawa remote ta dauka ta zauna a kan kujera sannan ta danna video dinsu, baka gani sosai saboda da alama a jikin tv stand tasa wayar kafin ya ankara sai dai ga muryarshi nan sannan sanda yana tsaye fuskarsa ta fito, ga nishi da alama ya fada.

Jikin Goggo ne ya hau rawa, hotonsu ta bude inda ya rungumeta a mota.

Bakin Goggo na rawa ta kalleta.

Adam kam gaba daya ya sandare kai kace itace ne a gun.

Da sauri Goggo ta kashe socket sannan ta kalleta tace "meya hakan?"

Sadiya tace "in kika kara cemin karuwa ko kuma nabar gidan nan tabbas zaki tsinci wannan abin a wayar sirikarki."

Goggo idanunta ne suka fito cikin takaici ta kara mangare Adam wanda yakeji kamar yai kuka, meye laifina? Daga taimako? Ya fada tare da sa kuka.

Zainab ce ganin bai kawo ruwan ba yasa ta fito.

Kallan mamaki ta musu ganin Goggo da Adam a tsaye carko carko ga Sadiya a zaune, sannan Adam
Sai goge fuskarsa yake kamar mai kuka.

Cikin alamar Zargi tace "lafiya?"

Adam ya juya da sauri ya nufi kofar fita yai waje.

Goggo ce ta kalleta tace "fada nake mai ya nemi aiki wannan zaman ya isa."

Zainab tace "ai yace yana nema, komai sai Allah yayi, sannan shi kinsan baisan aiki irin namu ko na wahala."

Goggo tace "Hmm."

Wucewa tai ta debo ruwanta sannan ta wuce ciki, sai dai sam tana ganin akwai wani abin bayan fadan aiki, haka kawai Adam bazaiyi kuka saboda maganar aiki ba.

Sadiya ce ta kalli Goggo tace "nima bani ruwa nasha."

Wa? Ni?

Sadiya tace "me kike a gidan nan banda kallo? Bani ruwa tun kafin na tura."

Da sauri Goggo tai kitchen ta dauko ruwa kamar mai shirin kuka, yau meke faruwa da ita? Itakam da alama rayuwarta ta kare.

******

Duk yanda ya tambaya bai samu ansar komai ba a Naibawa, ganin haka yasa ya fito, ga dare yayi dole sai gidan Kawu ya nufa.
Shiru yai yana tunanin abinda ke faruwa kafin ya tambayi kansa, ni me nene nawa a ciki? Meye nawa na damuwa? Rayuwarsu ce sun san abinda ya kamata ai ba yara bane su.

Sai dai sam ya kasa bacci sai juye yakeyi, can yace taimakon datai na Abba na zan rama mata.

Da sassafe yana sallar asuba ya kara komawa can, sai dai yanzu ma ba wani labari.

*******

Wajen karfe 11 na dare Adam ya dawo, sum ya shige daki ya tura a hankali, ganin Zainab na bacci yasa ya lalaba ya kwanta cikin takaici da dana sanin abinda ke faruwa wanda tunda ya fita yake dana sani.

Hana kwanciya yaji ta rikoshi, a hankali tace "Honey ka dawo? Ina kaje kai da baka san fitar dare?"

Idanunsa ya runtse cikin takaicin abinda ke faruwa yace "na fita kawai yawo ne."
Murmushi tai tace "nace abokinka yai applying din aikinmu, kai haryanzu baka san aikin zirga zirgar?"

Yace "a'a." Shiru yai saboda gaba daya bai san magana.

Kara kwanciya tai a kafadarsa tace "Honey!"

A hankali yace "Hmm"
Tace "mun shirya da Dady."

Baisan abinda take cewa sosai ba kawai yace "Uhm Hmm."

Mamaki ne ya kamata, matsawa tai daga jikinsa sannan tace "abinda zakace kenan?"

"Me nace?"

Cikin bacin rai tace "bashi."
Jan bargo tai ta kwanta, Hm hm? Wani ya maidata makauniya mijinta kuma tana fadamai abinda ta matso ta fadamai shine zaice Uhm Hm?

Da safe tana tashi ta fita, tayi mamaki dataga yau Goggo bata fito kallo falo ba.

Mota ta shiga fuskarta a hade sosai.

Shikam ko a jikinsa dan gani yake duk matsalar tata ce wani irin rashin kula ne zaice ace bakisan kanwar mijinki ba? Shekara ba daya ba ba biyu ba da aure?


*****

Yau ba wanda yama wani magana har suka kusa isa, haushi ya kara kamata dan ta dauka zai bata hakuri.

Sai da suka kusa isa cikin bacin rai tace "kacemin makauniya sannan bazaka dau lefen ka ba?"

Khalid na tukinsa kamar bazai magana ba sai yace "in bakyasan ace miki haka ki sa ido a Gidanki."

A Gidana? Kai waye da zaka ce na sa ido a gidana?

Khalid yace "niba kowa bane sai dai duk abinda ya faru kisan kece kashi 60 na matsalar."

Ranta a matukar bace tace "da alama ka gaji da aikinka"

Shiru yai bai tanka mata ba.

Haushi ne ya kamata suna isa ta fita ta banko kofar da karfin tsiya.

Binta yai da kallo kafin yai ajiyar zuciya, meyasa yake saurin yin fada in tamai magana?

Sam ya rasa me yasa ransa ke saurin baci da yanayin yanda take magana, bayan yasan a karkashinta yake sannan ta taimakeshi.

Idanunsa ya runtse kafin ya ajiye motar ya fito dan komawa Naibawa.

Yanzun ma baisamu kowa ba yana kokarin juyawa ne ya kalli wayarsa, ganin date din yau ne yasa ya zaro ido da sauri, hannu yasa a kansa cikin dana sani yace "Oh God ashe yaune test din?" Sam ya manta da wanda aka turomai kwanaki.

Cikin rashin jin dadi ya juya, wanni magidancinya gani kamar bazai tambayeshi ba sai yaje gunsa yace "dan Allah bawan Allah kasan wata Fiddausai?"
Fiddausi? Ya tambayeshi.

Khalid yace "eh tanada Sikila sannan mahaifinta sunan mahaiginta Basiru.”

Shiru yai kafin yace “Tanada kanwa Raziya?”

Idanu Khalid ya bude kafin yace “kanwa?”

Mutumin yace “ita?”

Da sauri Khalid yace “eh.”

Mutumin yace “shiyasa baza’a gane ba da kace gidansu Raziya ne zasu gane, ita Fiddausin ai ta dan kwana biyu da rasuwa.”

Kallansa Khalid yai yace “ta rasu?”

Eh baka sani ba?

Idanun Khalid ne suka fito sosai.......

Ni kaina idona sai da suka fito😳🙊



*********
Ayusher🏌🏻‍♀
[11/18, 12:38 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

#OneLove❣

{28}


Khalid ya daure tsananin mamakinsa yace "kana nufin kanwarta ce kenan?"

Mutumin ya matso cikin rada da gulma yace "bawan Allah shawara zan baka ka tafi dan mu kanmu yanzu ba wanda yake kula zuri'ar gidansu."

Idanu ya dago ya kalleshi yace "mene?"

Ya kara matsowa har mamaki ya kama Khalid yace "babbar ta rasu, karamar ce Raziyar in santa kake ma ka koma dan....."
Sai kuma yai shiru yace "baruwana jeka kawai."

Khalid ne ya kalleshi, yace "menene dan Allah?"

Kamar zaiyi magana sai yace "ni dai ba ruwana nayi nan." Kafin Khalid ya sake magana yayi gaba."

Duk yanda yaso ya shirya tunanin dake yawo akansa ya kasa hadashi yanda ya kamata, duk da Adam ace ya yaudari yayarta ne ya auri Zainab

Please Login or Register in order to submit comment