Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi yasa sam nikam banaji zan iya aure har na mutu, Aminiyarta, a kullum......”

Ya akai kika sani?
Tambayar da Zainab ta jefe ta dashi kenan tare da mata kallan zargi.


*Ayusher Muhd.*
[10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀 *A GIDANA*🍀

*Na Ayusher Muhd*

*Haske Writers Association*💡

*Shafi na bakwai*

Wattpad/@AyusherMohd.


  Idanunta Zainab ta kalla tace "Nabila!"

Nabila ta mike da sauri tace "ba abinda na sani, kawai dai maganar ce tazomin."

Zainab ta kalleta, da sauri ta shige daki ta maida kofar ta rufe.

Shiru Zainab tai tare da zubama kofar ido, kafin ta mike ta nufi daki, agoggo ta kalla taga karfe 4, computee dinta ta dauka ta koma falo ta zauna.
  Wajen karfe biyar ta mike ta shigo daki ta kalli Adam dake ta baccinsa, kusa dashi ta zauna sannan ta dan tabashi, tace "Honey a daure atashi aje masallaci."

Batare da ya bude idansa ba yace "bacci nakeji, nayi anjima."

Hannu tasa ta jashi ta zaunar dashi akan gadon, a hankali ya bude idanunsa yace "Honey Allah bacci nakeji."

Fuska ta hade tana kallansa batace komai ba.
"Na tashi shikenan?" Ya fada tare da bude idanunsa sosai, sakeshi tai sannan tai murmushi tace "ko kaifa."

Yake ya mata, gira ta daga mai ta nuna mai toilet da ido.

Ajiyar zuciya yai sannan ya mike yai alwala yana fitowa ta mikomai jallabiya ya saka yana ta dan zumbure zumburenshi kai kace yaro ne aka kwacemai alawa.

Fitowa yai daga gidan ya nufi hanyar masallaci.
Suna idar sa sallah shine na farkon mikewa ko addu'a bai tsaya ba ya fito, ganin Nazifi a masallacin yasashi saurin bi ta baya, dan bacci yakeji bashida lokacin tsayawa magana.

  Daga kungun da zai shiga kwanar gidansu yaji motsi, cikin tsananin tsoro ya matsa da sauri tare da zaro wayarsa ya haska fitila yana cewa "waye nan?"

Ganin ana kara buyewa ne yasashi kara matsowa gun yana haska fitilar duk da tsananin tsoron da yakeji.

Yana neman karasawa daf da mai boyewar aka saki kwalin da ake boye fuskar dashi.
A tare suka saki wani kara, yaja da baya da sauri, bayan sun gama karar ne ya haska fitilarsa a tsorace.

Tsayawa yai cak yana kallan ta, haska kansa yai hakan yasa ta gane shi.

Kallanta yai yace "bake bace ta dazu? Me kike anan?"

Kanta ta saukar kasa tace "komai na wa an sace kuma makaranta nazo, gashi bansan kowa ba, banko biya kudin hostel ba.
To me kike anan kina mace?

Bansan ya akai na ganni anan ba, shiru yai yana kallanta kafin yace "bakisan kowa ba a kano?"

Kai ta daga alamar eh, shiru yai yana kallanta kafin yace "to ki koma garinku mana in safiya tayi?"
"Ban isa komawa ba inba haka ba mijin mamanmu dukana zaiyi."

Shiru yai yana kallanta bai fahimceta duka ba, kamar yace ta biyoshi kuma yafi kowa sanin matarsa, da sauri yai gaba bai kara waigowa ba ya shige gida.
Yana shiga yai ajiyar zuciya yace " ashe dai inada tausayi."

Kai ya girgiza da sauri ya shige ciki.

A zaune ya taddata a falo taba kan sallayabga laptop dinta a gefe, da sauri ya wuce daki.
Ta fahimceshi wato kar ta mai magana shiyasa ya shige, yana shiga ya kwanta, kan kace me bacci yayi gaba dashi.


***********

A bangaren Khalid kuwa bayan yabar gidan cafe ya wuce ya duduba aiki, sai wajen magrib sannan ya nufi gidan kawu.

Sam ya tsani zuwa gidan dan yana shiga layin yaci karo da babbar 'yarsa mace, anci uban kwalliya a gaban mota itada saurayinta.
Yi tai kamar bata ganshi ba shima ya dauke kai.

Ji yake kamar karya shiga gidan, ya dade a tsaye a kofar gidan yana tuno bakincikin halayensu daya sha farkon zuwansa, harya juya da niyyar komawa danbatta inyaso da sassafe sai ya dinga fitowa yaji ance "Khalid?"

Juyawa yai, dan ya san wanene, Kawu ina wuni?

Abinda yace kinan yana rusunawa, Kawu ya dafa kafadarsa yace "ina zaka da?"
Muje muje, ya jikin Baban naka?

Da sauki, ai naso kara komawa sai dai bana zama ne nima.

Khalid dai baice komai ba, haka suka shiga ciki inda suka wuc falansa yasa a kira matan nasa.

Su uku ne suka shigo kowa sai yace "khalid yau kaine a nan?"

Bayan ya gaisu ne Amaryar ta kalleshi tace "da alama an dace an samu aiki kenan."

Kawu yai saurin cewa "haba?"
Khalid yai murmushin yake kawai, nan ya zauna sukaci abinci tare bayan sunyi sallah, nan ya fito ya wuce bangaren maza, yaran gidan sam basu da tarbiyya suna ganinshi fa amma kaf dinsu ba wanda yamai magana, kowa harkar gabanshi yakeyi, sai shine yace sannunku, kawai ya wuce dan dakin da yake zama, shi da Annur wanda yake karami ne shekarar sa 15 yanzu, Annur shima baya nan, jikinsa ne yai sanyi badai shima harya shiga sahun su ba?

Ajiye yar jakarsa yai sannan yace "bazan iya zama anan ba, daga gobe gwara na dinga zuwa daga danbatta da safe, kwanciya yai yana jin haushin amsar aikin nan dayai.

********

Haryai bacci baiga Annur ba sai da safe daya tashi ya ganshi yana bacci, tashinsa yai yace "sai a tashi a shirya ko?"

Annur yana mikewa ya rungume Khalid yace "ya Khalid."

Khalid ya tureshi yana dariya yace "mutum dai ya tashi kafin ya makara.

Annur yana dariya yace "jiya kawai na dawo naganka?"

"Kana ina har wajen 11?"

Annur yace "muna can muna hida da friends din mu."

Kamar Khalid zai sake magana sai ya fasa, shiryawa kawai yai ya dau jakarsa da niyyar zai dawo ya fita.

Mota ya hau ya nufi gidan.

  Karfe bakwai da minti takwas tamai a cikin gidan, tsayawa yai a waje suka dan fara hira da mai gadin.

A ciki kuwa Zainab ta gama shiryawa dan dama bata koma bacci ba, tana fitowa daga daki taga goggo ta fito tana murza ido, Zainab ta gaishet tana cewa "Goggo adan dai rage kallan nan, kamar yana yawa."

Tana fada ta nufi kitchen, Goggo tsayawa tai ranta yai mugun baci, harara ta bita dashi tace "wannan yarinya da ace ta hada jini da Ado da bamusan yana zata kareba, to sai kuma kikai sa'a bakuda hadi dashi yar kwal......"

Ganin Zainab ne yasa ta kalleta ta saki dariya tace "Gwara dai ki tafi da ko dan shayin ne, amma ace mutum ko abincin safe baya ci?"

Zainab tace "na wuce."
"To adawo lafiya, dan Allah ki tahomin da goro."

To kawai tace ta fita, tana fita Goggo ta tabe baki tace "a haka dai, an kasa bani jika sai feleke kamar, kamar."

Ta kunna socket ta zauna tana cewa "dole nasha ruwan tea dan sam jiya ranta ya baci dasu Nusaiba suka dafa macaroni, haka tasha kunu ta kwanta."

Zainab na fita ta ganshi suna magana da mai gadi, agoggon hannunta ta kalla, bakwai da ashirin, sam bati tunanin ganinshi ba, ta fitone ta fara aiki a cikin mota kafin ya karaso."

Tsayawa tai a bakin kofar, yana ganinta ya nufo inda take, kusa da ita yaje ya mika mata hannu, kallansa tai tace "no am okay, zan iya dauka."

Ta fada tare da dauke kai, "no ina nufin key."

Da sauri ta kalleshi, haushin kanta ya kamata, rikemin, ta fada tana mikamai tea din, ya amsa ta juya ciki, tana shiga ta fito, mikamai tai ya mika mata tea din sannan ya amsa ya wuce ya bude motar, wani irin kallo tamai sannan ta wuce ta shiga.

Sun fara tafiya taga anzo kwana, kafin yai magana tace "nan zakai."

"Na gane hanyar."
Juya kai tai dan dama batasan ya fara mata zancen left da right din nan ne yasata yin magana dan ba karamin haushi taji jiya ba.

So take ta tsaya ta sai biscuit dan na office dinta sun kare, kallansa tai tace "Excuse me dan gangara gefen titi nan."

Neman gangarawa yake ta kara cewa "Excuse me daga dan can."

Karasawayai yai parking, ta fita daga motar, tana fitar tai murmushin jin dadi tace "kaji ko da dadi."

Shikam sam bai kawo komai ba, harta dawo ta shiga.

A cikin tv station din yai parking, ta kalleshi tace "zaka iya zuwa ka dawo, in ina bukatarka zan nemeka."

Okay.

Shiru sukai sannan ta daure ta mikamai wayarta tace "zan kida Adam in na kusa gamawa."

Okay
Ya kara cewa, fitowa tai ta shiga ciki.

Tana shiga bakin gun ta hade fuska tamau, ko ina ta wuce gaisheta akeyi tana amsawa, kayanta kawai ta ajiye ta dawo ta hau aikinta.


***********

Karfe sha daya ya farka? Mika yai sannan ya fito daga daki, yana tafe yana hamma, a falo yana goggo tana ta maka dariya, kallanta yai ya girgiza kai, ya matso yana cewa "wlh Goggo jin dadinki yayi yawa."

Kallansa tai tace "kai kuma fa? Wai kai dan Allah bakajin kunya? A matsayinka na namiji kullum a gida?"

"Kedai kiyi kallanki dan ni ba kunyar da nakeji, ina wadancan yan rigimar?"

Suna kitchen dan wulakanci sai yanzu suke abincin safe

Dariya ya mata yace "to ai da ke kinyi Goggo ni me kikeyi ne a gidan?"

Tace "amma in basa nan ai inayi, in suna nan kam bazan ma katti abinci ba."

Kai ya girgiza, ya mike yana cewa "Goggo ta tv ni wai kina kallan shirin sirikarki ma?"

Tace "ina kallo mana, ba gwara ni ba kai sai karyar kana kalla bayan haryau bansan a inda kake kallan ba."



*AYUSHER MUHD*
[10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

Haske Writers Association💡

Shafi na takwas

Wattpad/@AyusherMohd.


*********

Bude kofar tai sannan ta shiga cikin inda ake editing.

Suna ganinta kowa ya zauna daidai, tare da maida hankali kan aikinsa.

Fitowa tai ta bude cikin news room suma gyare gyare sukeyi tana gamawa ta fito, da niyyar wucewa dan ta shirya saboda program dinta.

Tana shiga taga Ramla a zaune tana waya.
Sam bata kula tana bayanta ba sai da Zainab ta karasa gun, Ramla na juyowa sukai ido hudu da Zainab da sauri ta mike daga gun da sauri tare da cewa "Good Morr.."

Kallan da Zainab ta mata ne yasa ta yin shiru, sannan tace "ba laifi dan dama irinku kallo daya mutum dai muku ya fahimta."

Ramla cikin mamaki tace "ya fahimci me?"

Zainab ta mata alama da kai akan ta fita, Ramla idanunta suka ciciko, ta bude baki zatai magana  Zainab ta kalleta wanda hakan yasata yin shiru, hawaye ne suka zubo mata tasa hannunta share sannan ta fita.

Tana rufe kofa Zainab ta dan sauke numfashi kadan cikin takaici, sannan ta wuce ciki.

Ramla kam fitowa tai cikin station din tana dan hawayenta.

Kusa da wata mota ta tsaya ta share hawayenta sannan ta dau waya, bata dade da dialing ba aka daga, daga can ta fashe da kuka tana cewa "Yallabai.....kawai tasa kuka.

Daga cikin mota Khalid dake zaune yana waya da Abbansa ya kalli jikin windown.

Sallama sukai ya kashe tare da rufe idanunsa, kuka ta cigaba dayi tana cewa "Nikam matarnan ta tsaneni wlh, yaufa saura kadan ta kirani karuwa..."

Ta kara sa kuka, haushi ya kama Khalid ya kalli jikin window din gashi ta tsaya jikin kofar ba dama ya fita.

Ta cigaba "ni dai Allah bata sona, wai tsoran Zainab din kake?"

Can kuma ta kara sa kuka, sannan ta kashe wayar, tana kashewa ta kalli madubin jikin motar dan gyara fuskarta.

Kallanta taga anayi, idanunta zato da sauri sannan ta sa hannu dan bude motar, Khalid ya bude motar sannan ya kalleta.

Sai yanzu ta kalli jikin mottt are da take, gabanta ne ya fadi dan tasan motar Zainab, idanunta ne suka fifito ta kalleshi sannan ta danyi yake tace "ashe da mutum a ciki."

Khalid ya fito ya rufe motar yana neman tafiya.

Da sauri tace "kaji me nace?"

Kallanta yai sannan yace "daga ina?"

Ta dan motsa baki sannan tace "kaji daga farko har karshe kenan?"

Juyawa yai bai amsa ba, tai saurin cewa "dan Allah kayi hakuri karka fadawa Assistant director Zainab."

Ta ina zan fada mata? Abinda yake tunani kenan, da sauri tace "dan Allah, karka fada mata."

Juyowa yai ya kalleta, mota ta nuna mai tace "ba motarta bace?"

Sai yanzu ya gane, juyawa kawai yai ya wuce, dan wata irin yunwa yakeji, Ramla ta saki ajiyar zuciya tace "shikenan na gama yawo, you are fired."

**********

  Adam ne yai shiru a falo, Goggo nata waya tana ma mai dinki bayani akan dinkinta, Nabila da Nusaiba na gefe suna dane dane a waya, wata nannauyan ajiyar zuciya yai wanda Goggo tana waya tadan kalleshi, mikewa yai ya fita, bai dade sosai ba sai gashi ya dawo.

Goggo ta kalleshi tace "ina kaje?"

Kallanta yai yace "Goggo!"
Ta kalleshi ya mata nuni da daki.

Mikewa tai ta fito suka nufi daki, tana shiga tace "menene?"

Kallanta yai tare da zama yace "Goggo yarinyar can na bukatar taimako" kallansa tai tace "wace yarinya kenan?"

Labari ya bata na yarinyar sannan yace "Zainab bazata taba bari a taimaketa ba."

Goggo tace "ka sani kazo kana fada? Kai ba ka saki jiki komai sai dai a maka ba."

Yace "wai Goggo ba a dalilina kikejin dadin nan ba? Meyasa komai nazo miki dashi sai ki dinga fadamin magana?"

Goggo tace "to ya kake so ayi? Kafi kowa sanin Zainab, ko kawarta ka taba gani a gidan nan? Daga ita sai kanenta sai ni? Sai dai in kanwa ce dakai amma inba haka ba wa ka isa kawowa gidan nan?"

Shiru yai kafin ya kalleta da sauri yace "Goggo!"

Kallansa tai yace "in mukace mata Sadiya ce fa?"

Cikin mamaki ta kalleshi tace "mene?"

Yace "in muka dan kawota akan Sadiya ce in tai kwana biyu sai mu sallameta, bayan ta gama cike abin makarantarta."

Goggo ta saki baki tana kallansa tace "ne kake cewa?"

Kallanta yai yace "Goggo bakiganta ba haryanzu fa tana waje, abin tausayi."

"Ni wai yaushe ma ka fara tausayi ne? Sannan a ina ka santa balle kasan halinta? In aljana ce fa?"

Wata dariya ya saki yace "wani irin zance kike."

Tace "lalai Adam bakada hankali wasa wasa, kanwarka? To in abu ya tashi Sadiya tazo daga kura fa?"

Yace "lokacin sai musan me zamuce kuma hali ma irin na Zainab ganewa zatai."

Kallansa tai galala kafin tace "ka samu matsala wlh, kuma ni ba ruwana, in da raban garin taimako......"

"Haba Goggo meyasa kike haka ne? Taimako na kwana daya zuwa biyu sai ya zama haka?"

Tace "ni wai yaushe ka zama mai taimako ne?sannan taya zaka shigo da ita?"

Shiru yai kafin can yace "dama yanzu nake tunanin in shigo da ita a boye inyaso intai wanka sai.....".

Shiru yai dan kansa ya kulle, Goggo tace "sai me? Sai na bata kayana tasa?"
Tai maganar cikin gatse, da sauri yace "eh sai ki bata ta saka yanda inta dawo sai nace mata ga Sadiya tazoyin kwana biyu, a yanda take dawowa a gajiye ma ina zata ganeta? Sannan gobe kinga da safe zata sake fita, kinga tana gamawa sai mu sallameta."

Kai zaka biya mata kudin makarantar? Tambayar da Goggo ta jefeshi da ita kenan, kallanta yai sanan yace "Goggo wai meyasa kike haka?"

Tace "to wa zai biya mata? Zainab?"

Yace "in taji Sadiya ce ai zata taimaka."

Goggo ta mike tace "can kai ka sani ba abinda ya dameni, nidai wlh kaja aka ganeka abu ya shafeni ranka ne zai baci."

Adam yai shiru yana kallanta.


  ************

  Zainab na zaune a office tanacin biscuit da juice, badai yana waje ba? Abinda ya fado mata kenan? Mikewa tai bayan ta gama hartayi hanyar waje sai kuma ta koma ta zauna tare da cewa "ai yau dole yaje ya dawo saboda zaman yayi yawa.

Da wannan ta cigaba da aikinta, wajen sallar la'asar taga kiran Director, tana kallan wayar har sai da ta katse, sake kira akai ta kalli wayar sannan ta daga.

Zainab!

Tace "Yallabai ina wuni?"

Daga can ya amsa yana cewa "ya aiki?"
Tace "lfy."

"Ashe Ramla tayi laifi? Ayi hakuri kinsan yaran nan ne wlh sai a hankali."

Tace "saboda haka ka kira?"
Yace "no dama ina san fada miki ne wannan proposal din sunce gobe aje a musu presentation."

Tace "that's nice, zan shirya power point."

Yace "yauwa, sai gobe."

Nan sukai sallama ta kalli wayar sannan ta girgiza ki.

Sai karfe shida ta tashi? Ramla naganinta ta boye, Zainab ta wuce tana kiran Adam, duk da dai jikin ta na bata ya dawo.

Motar ta gani a waje hakan yasa ta nufi gun.

Ba kowa a ciki, hakan yasa ta dan wawaiga, daga gefe ta hangoshi ya nufo gun, da alama zama yai a gun.

Bude motar yai, ta bude baya ta shiga.

Shiga yai yaja suka fara tafiya.

Shiru suka danyi a motar, tana kallan wayarta, can tace "badai a waje ka zauna ba ko?"

Baiyi tunanin dashi take ba sai dayaji shiru alamar ba waya take ba sannan yace "cafe naje."

Shiru sukai ba wanda ya sake magana har suka kusa isa, daurewa tai tace "gobe daga gun aiki zamu fita zuwa kaduna, in na shiga gun aiki 1hr zanyi a ciki sai mu wuce."

Okay kawai yace suka karasa ciki......


*Ayusher*
[10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

Haske Writers Association💡

Shafi na Tara

Wattpad/@AyusherMohd.

Harta bude kofa zata fita tadan juyo, kallansa tai tace " yanzu zaka wuce?"

Yanzu kam ya juyo yadan kalleta kadan yace "eh zan wuce danbatta ne."

Danbatta?
Ta fada cikin mamaki, juya kansa yai yace "eh."

Fitowa tai batace komai ba, tana neman bude kofa taga an bude da sauri, Nusaiba? Ta fada tana kallanta.

Sam batama kula da ita ba ta wuce gun Khalid da gudu? Yana rataya jakarsa a baya taje kusa dashi tace "Ina wuni?"

Khalid ya kalleta murmushi yai sannan yace "ya gida?"

Tace lfy kalau, ga wannan.
Ta mika mai coke mai sanyi tace ga wannan kasha rana.

Kallanta yai sannan ya amsa, Zainab ta saki baki tana kallan ikon Allah sai jitai an rikota, juyawa tai ta kalli Adam wanda ya sa dariya yace "kwaro da alama kayi kasuwa."

Nusaiba ta rufe ido da sauri, ta juya ciki da gudu, har tafa dan bige Adam dake jikin kofar kadan.

Adam ya kara sa dariya, Zainab ce taja hannunsa suka shiga ciki.
Khalid ya juya ya fita.

Tasha ya wuce kawai ya hau mota ya tafi danbatta.

Bayan magrib ya isa, dukansu na zaune a waje suna cin tuwo sukaji sallama, da gudu su Amir suka tashi suka nufeshi suna cewa Yaya yaya

Khalid ya rungumesu sannan ya shigo ciki, Umma da Abba sunyi zuru suna kallanshi.
Asiya kam mikewa tai ta dauko plate ta ajiye, Khalid ya kalleta yace "yauwa kanwata nagode."

Umma ya gaida sannan ya gaida Abba ya tambayi jikinsa.

Abba ya kalleshi yace "meke faruwa?"

Khalid yace "kawai ina tashi naji gida nake so."

Asiya tasa dariya tace "sai kace dan boarding yaya."

Yace "dama inasan kaiki boarding da alama na kusa."

Dariya tai tace "boarding ina Ss2?"

Abba yace "ban gane ba? Yanzu kana tashi kawai ka taho?"

Yace "eh Abba naga hakan yafi sauki, nawa ma tafiyr take daga kano zuwa danbatta?"

Umma tace "to yanzu ci abinci kai sallah ka huta."
Ta kalli Abba tace "tunda yaga hakan yafi sauki sai ka barshi, sanda yaga bazai iya ba sai yaje can din."

Khalid yace "yauwa Umma."

Abba yai shiru bai kara cewa komai ba, Khalid ne ya zuge jakarsa ya ciro coke din nan yace "ga coke Abba."

Abba ya amsa yana cewa "to nagode."

Nan suka ci abinci, suna gamawa ya mike ya shiga daki.


*********

Fitarsa Sallar isha'i ya hangota a inda ya barta, meke damun yarinyar nan? Wai ba mutanene a unguwar da ba wanda zai taimaka mata?

Wucewa yazoyi tare da dauke kansa kamar bai ganta ba, ji yai ance "bawan Allah."

Gabansa ne ya fadi, ya juyo ya kalleta, tasowa tai daga inda take ta matso kusa dashi tace "ka taimakeni ka bani gun kwana dan Allah, jiya ruwan da akai tsakar dare a kaina ya kare, gashi ko ruwa ban samu nasha ba bare abinci."

Adam yai shiru yana kallanta, idanunta ya kalla duk ya jeme alamar wuya, yace "biyoni."
Nan tabi bayanshi da saurinta.

Shiru yai a bakin kofa gabansa na duka uku uku, cewa yai tsaya anan sannan ya shiga ciki, mai gadi ya kalla yace "Bala duba min ban dakinku ko kunbar fanfo a kunne, naji karar ruwa."

Cikin mamaki Bala yace "fanfo?"

Adam yace "eh duba."

Nan Bala yai hanyar bandaki, da sauri ya mata alama data shigo, ta shigo da sauri.

Adam ya nuna mata wani daki a can gefe, ta nufeshi da sauri.

Tana shiga Bala na fitowa yace "nikam banga komai ba."

Adam yace to kila ba nan gidan bane ya wuce.
Dakin ya shiga ya kunna fitila.

Tana tsaye, dayake dakin ba komai sai katifa katuwa dake kasa.

Adam ya kalleta yace "ki zauna anan zuwa dare zan ce ki shigo ciki."

Kallansa tai tace "zan iya zama? Karna ja wani abin ya faru."
Yace "karki damu zan kawomiki abinci, anjima zaki shiga ciki, ba dadi ne ban sanar asu ba su ganki."

Tace "nagode Allah ya saka da alkairi."
Fitowa yai ya wuce ciki.

Zainab na zaune a falo, Goggo na kan kujera daga gefe suna kallan sautin arewa wato inda Zainab ke aiki, gefe kuma Nusaiba ce da Nabila.

Zainab dake zaune tana cin abinci tna dan kallan tv din ta kalli Nusaiba tace "Wato harda daumin coke kiyi gwaninta dashi?"

Nabila tace "to da Aunty bakisan meta kinkimo zata kaimai ba."

Zainab tace me?

Abinci ta zuba a flask, ta sa coke tasa robar ruwa tasa apple a basket wai zata kaimai yai lunch.

Zainab batasan sanda tai dariy ba tace "sannu matarsa."

Nusaiba tace "Aunty dan Allah ku auramin shi."

Goggo tasa dariya tace "yaro yaro ne, wato wannan zamani ba kunya, wai yarinya ke cewa a mata aure."

Nusaiba zatai magana Adam ya shigo yana cewa "in kina sanshi tsaf zan aura miki shi."

Da sauri tace haba?

Zainab ta dan harareshi tace "karka tunzurata batasan gatse ba."

Tana gama cin abinci ta wuce daki, tana mikewa Goggo tasa cassette, Nabila tace "mu dai Goggo ki bari mu gama kallan shirin da ake."

Adam yai saurin mika ma Nabila remote yace "sa abinda kikeso."

Goggo ta kalleshi fuska a hade, yace "Goggo magana zamuyi." Yai maganar cikin rada.

Mikewa tai ta nufi daki, Nabila na cewa "Goggo fushi kikai?"

Adam yace "bari naje naji."

Nan yai ciki, suna shiga ya zauna kusa da ita yace "Goggo ya zanyi yrinyar tana dakin wajen can."

Kallansa tai galala tace "mene?"

Yace "baki ganta ba wlh duk ta rame."

Goggo tace "to meye damuwa ta?"

"Wai Goggo meyasa kike min haka? Taimakon rai zamuyi, dan Allah ki taimaka ma yarinyar nan.

Tace "naji amma kwana biyu, inta wuce kuma wlh duk abinda ya biyo baya kar ka sa dani."

Yace "ta ina ma zata wuce? Ai tana gamawa zan sallameta."

"Ynzu ya zakayi?"

Yace "idan wadancan rigimanmun sun kwanta zan shigo da ita tai wanka ta kwanta a dakinki, kinga ita da sassafe take fita, to inta dawo sai ince mata tazo."

Goggo ta tabe baki tace "wato kwakwalwarka bata tashi yin banban tunani sai kanasan abu."

Dariya yai yace "Yanzu zan kawo abinci na ajiye anan dakin karda daddare a gane in aka kamani ina zuba abinci."

Tace "can kai ka sani, nidai ka tabbatar randa zani bikin nan na yar kawata kai ka kaini a mota."

Yace "an gama Hajiya Goggo."

Fitowa tai ta dawo falo, shikuma ya wuce daki.

Zainab na ganinshi ta dan matsar da laptop din data kunna tana cewa "gobe kaduna zani."

Kaduna? Ya dada tare da zama kusa da ita, tace "eh wlh zamu presentation."

Ya kwantar da kansa akan cinyarta tasa hannunta acikin gashinsa tana cewa "ko zaka kaini?"

Idanu yadan zaro, yace eyee, dariya tadanyi tace "just joking, harna fadawa abokinka."

Sun danyi hira kafin ya fito falo, yana ganin yaran sun bar falo ya fita ya shigo da yarinyar da ko sunan ta bai sani ba.

Dakin Goggo yai da ita, sannan ya fita, Goggo na zaune a falo tana kallansa har suka wuce ciki, itadai sam hankalinta ya kasa kwanciya da wannan lamari, mikewa

Please Login or Register in order to submit comment